Recent Updates

Akidata Book 1 Complete Hausa Novel

 


     Asslam Alaikum warahmatullah, A madadina, ƙungiya ta da kuma 'yan uwa na da abokan arziki, ina taya Ɗaukacin Al' ummar Musulmi barka da salla, tare da fatan anyi salla lafiya, ina fatan ubangiji Allah ya karɓi ibadunmu da mukayi a watan

Ramadan, sannan ina Fatan Allah yasa mu ɗore da ibadun da mukayi a watan Ramadan, Taku har Kullum
AISHA HUMAIRA (Daddy's girl) ko kuma ince Ayshercool 😍😍 kaman yadda wasu suka fi sani.

  TALLA! TALLA!! TALLA!!!

Ina masoya wanda suka bibiye ni a littafina na ABDUL JALAL, da kuma WATA KISSAR yanzu ma na shirya tsaf domin kawo muku wani ƙasaitaccen littafin me ɗauke da sabon salo da kuma sarƙaƙiya,
ga ɗanɗano daga cikin littafin
           

                       _*AƘIDA TA*_

           

     *PART1*         
                  _Page 1_

*written and edited by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*

Bismillahir rahmanirrahim, da sunan Allah me Rahama me jin ƙai, Wannan littafi ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan cin zarafi ko cin fuska ga wani ko wata ko wata ƙabila ba, idan har wani ko wata yaga wani abu daya yi kaman ceceniya da rayuwar sa ko ƙabilar sa Amin Afuwa banyi dan cin zarafin wani ko wata ba.
    Wannan littafin mallaka tane, ban yadda a juyamin labari ta kowane fanni ba ba tare da izinina ba.

What's App : 07063065680
Facebook : real Humaira
Watpad : Ayshercool7724
Gmail : Www.ayshertadam@gmail.com

Katafaren ɗakin Bacci ne me ɗauke da kayan alatu na more Rayuwa da jin daɗi, idan ka ƙarewa ɗakin kallo zaka tabattar da ma'abocin wannan ɗakin Allah yayi masa Ni'imar Dukiya dan ya ƙawatu da dukkan wasu kayan more rayuwa, kallo ɗaya zakayiwa ɗakin kasan mamalakin ɗakin mace ce, saboda kan madubin dake ɗakin shaƙe yake da kayan kwalliya da gyaran jiki, ga wani show glass ɗauke da takalma da jakunkuna na adon mata kamar wani kantin saida kayan ado, kai da ganin takalma da jakunkunan nan kasan bana talaka bane,  Makeken Gadon dake ɗakin ne ɗauke da wata kyakywar matashiyar budurwa ta baje gashin kanta tana bacci cikin nutsuwa.

Hasken ranar da ya ratso ta tagar ɗakin ne yake dukan fuskarta wanda hakan yasa ta motsa a hankali, ta buɗe idanuwanta.
Ɗan ya mutsa fuska tayi, ta miƙe zaune ta kalli Agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe tara da rabi na Safiya, a hankali ta zuro ƙafafuwanta ƙasa ta miƙe ta nufi banɗakin dake cikin ɗakin nata.
Aljannar Duniya shi kansa ba ɗaya nata ya isa a tsaya a kalla.

Wanka matashiyar tayi ta fito daga ita se towel, abun mamaki har an gyara mata inda ta tashi, ta zauna a gaban mudubi, ta shafa wannan ta goga wancan, gashi komai nata a hankali cikin nutsuwa take aiwatar dashi, riga da skirt na blouse ta ɗakko ta saka da ɗan guntun mayafi, ta ɗora akanta tasaka takalmin ta me matuƙar tsini da jakarsa, seda ta kalli agogon hannun ta ƙarfe goma da rabi dai dai sannaan ta buɗe ɗakin ta fito.

Wani irin taku take na ƙasaita, takalmin ta na bada sauti ƙwas, ƙwas, ta fito wani irin ƙaton falo ta zauna, ba ta daɗe da zama ba, me aiki ta kawo fruit gabanta ta ajiye, bata kalli inda fruits ɗin suke ba, se kallon tsintsyar hannun ta da ta ɗaurawa Agogo take yi.

"wato Isa rayuwar ƙauye akwai daɗi akwai wahala"
Wanda aka kira Isa yace

"Haba ɗan uwa wani irin daɗi a ƙauye? Kai ka taɓa ganin wanda yake birni ya koma ƙauye banda zunzurutun wahala mene ne a ƙauyen?"

"to ai Rayuwar ƙauye tafi ta birni kwanciyar hankali, ba tashin hankali ba fargaba, amma kaga birni a nan rashin gaskiya ya ƙare"

"tabdijan lallai ma sani, ai tunda Allah ya kawoni birni na samu aikin gadin nan, idan naje ƙauye to ziyara na kai Amma bani babu zaman ƙauye ina daf da dawo da iyalina  nan ma"

"kai gidan nan zaka dawo da iyalin naka, kaifa  kace min zaman fargaba kake a kowane lokaci za'a iya sallamar ka fa"

Isa yace "rufamin Asiri in kawo iyalina gidan nan Haya zan kama"

Suka ci gaba da hirar su tare da yin taɗi akan rayuwar birni da ta ƙauye



Sake kallon Agogon ta tayi har sha biyu saura minti goma sha biyar, miƙewa tayi cikin takunta na isa ta fito harabar gidan, kai tsaye ta nufi bakin gate, inda me gadi ke zaune yana hira da abokin sa sani suna cin gyaɗa.

Isa Yana hangota ya miƙe jiki na rawa yace "Allah ya temake ki, barka da fitowa" bata amsa masa ba tace

"har yanzu Sabo driver bezo bane?"

Cikin girmamawa yace "Eh ranki ya daɗe be ƙaraso ba"

Haɗe rai tayi ta jinjina kai ta koma cikin gidan

Sani yace "Isa ita kuma wannan wacece naga jikin ka se rawa yake dan tazo" sani ya tambaye shi

Isa yace
"kai bari kawai, itace 'yar masu gida bata da wa, bata da ƙani shalelen Alhaji kenan, watan ta uku da dawowa daga ƙasashen Turai, yarinyar nan sam bata taɓuwa, gaba ɗaya halin turawa shi take yi, yau kam kashin sabo ya bushe wallahi "

Sani yace "kamar ya kashin Sabo ya bushe meze faru?"

Be ƙarasa maganar ba aka fara bubbuga gate ɗin gidan, da sauri Isa yaje ya buɗe, wani mutum ne a ƙalla ze shekara Arba'in ya shigo kaman an koro shi.

Isa ya kalle shi yace "Taɓɗijan sabo yau kashin ka ya bushe, yanzu ta fito gurin nan neman ka"

Wanda aka kira da Sabo ya shiga rafka salati "na shiga uku yanzu ya zanyi, wallahi yarona ne babu lafiya na kaishi chemist"

Isa yace "ai bani za kayi wa bayani ba, seka je ka same ta"

Suna cikin maganar ta kuma fitowa, Fuskarta a haɗe babu annuri ta kalli sabo tace

"ƙarfe nawa nace maka zan fita?"

Jiki na rawa yace "ƙarfe sha ɗaya ranki ya daɗe"

"yanzu ƙarfe nawa ne?"

"shabiyu da minti goma"

"good, bani mukullayen motocina"

Sabo yace
"dan girman Allah kiyi hakuri ranki ya daɗe, wallahi yarona ne ba lafiya na kaishi chemist"

Cikin tsawa tace "shut up, did I ask you? Kabani keys ɗina"

Durƙusawa yake ƙoƙarin yi amma ta dakatar dashi "kai motocin na ubanka ne ko nawa?"

"naki ne Hajiya"

"idan har nawa ne, ka kawomin makullayena, na sallameka za'a bawa me gadi kuɗinka ya baka, daga yau se ya zama izina a gare ka, Alƙawari yana da mahimmanci cika shi alamace ta amana, lokacin aiki dana ɗauke ka mallakina ne ba mallakin ka ba tunda biyan ka nake, dan haka seda izinina za kayi duk wani abu komai girmansa in ba ibada ba tunda biyan ka nake"
tana gama maganar ta juya ta koma cikin gidan.
guri sabo ya nema ya zauna ya dafe kansa yana salati.

Isa yace "Sabo se dai haƙuri, Allah ya baka aikin da yafi wannan"

Cike da damuwa Sabo yace "Ameen Isa, Nagode sosai Allah yasaka da alkhairi, idan ta bada sauran haƙƙin nawa nazo in karɓa"
Sukayi sallama Sabo ya fice daga cikin gidan zuciyar sa a cunkushe babu daɗi.

Bayan tafiyar Sabo,

Sani cikin damuwa yace "wai Bala in tambaye ka mana, ita bata da mafaɗi bata san dai dai ba, bata san Afuwa da uzuri ba?"

Bala yace "Taɓɗijan kai kasan su amma ita kam bata sansu ba, wannan da kake gani tana da wata irin muguwar AƘIDA da ta tashi akai saboda rayuwa da turawa, zuciyar ta kaman Arniya gaba ɗaya Aƙidun turawa ne da ita bana musulunci ba, babu wanda ze iya raɓarta su zauna lafiya, Akwai matar mahaifin ta dake gidan nan ita da 'ya'yan ta, seta yi sati biyu seta ga dama za su ganta balle maganar fatar baki ta haɗa su, ta maida su tamkar bayin ta, idan kaga dariyar ta to da Mahaifin ta ne, da wani babban Aminin sa, ko wasu ƙalilan daga ƙawayen ta, bata da yadda sam, gani take duk wanda ya fiye raɓarta ba shi da gaskiya, Sabo shine driver na huɗu da tayi bayan dawowar ta Nigeria, ga Albashi me kyau ga mahaifinta da kyauta, amma kowanne ma'aikaci da ƙafarsa yake guduwa saboda izza da bala'in ta, 'yan aiki kuwa koni na kawo shida daga garin mu amma da ƙafarsu suke guduwa, yanzu kalli duk haƙuri da ƙoƙari irin na Sabo kaga yau yadda ta wulaƙanta shi ta kore shi"

Sani ya sauke nannauyar Ajiyar zuciya yace "to ina mahaifiyar ta? Ya aka yi aka bari ta tashi da wannan AƘIDA wadda tayi hannun riga da Akidunmu na musulunci da kuma na Al'adar mu?"

Isa yace "Mahaifiyar ta ta rasu, shi kuwa mahaifin ta duk abunda tayi dai dai ne a gurin sa, yace ɓata mata rai tamkar zuba wuta ne a zuciyarsa"

Sani ya dinga juya maganganun Isa a ransa yana tunani, Sallama yayi wa Isa ya fito ya tura wheelbarrow ɗin mangwaronsa ya bar arear.

************************************

Wani matashine da baze gaza shekaru talatin ba zaune akan kujera ya tattara dukkan hankalin sa da tunanin sa akan allon na'ura me ƙwaƙwalwa dake kan teburin gaban sa ko ƙyafta ido ba yayi da alama wani abu ne me mahimmanci yake wa wannan kallon ƙurrilar.

Ƙwanƙwasa ƙofar ofishin da'aka yi ne yasa shi dawo wa hankalin sa a hankali yace "yes bismillah"

Turo ƙofar ofishin akayi aka shigo, wata matashiyar budurwa ce ta shigo jikin ta sanye da suit baƙaƙe da ɗan ƙaramin veil shima baƙi hatta takalmin ƙafarta baƙine, cikin taku na ɗaukar hankali ta ƙaraso gaban teburin sa tace

"barka da hutawa ranka ya daɗe"

Fuskarsa babu yabo ba fallasa yace "yawwa sannunki ya aka yi?"

Cikin iyayi da yauƙi tace

"dama Yallaɓai ne yace yana son ganinka a office dinsa"
Ɗan jinjina kai yayi yace

"Alright zanje Insha Allah"
Cikin sigar shagwaba tace

"can i offer you something to eat, naga yau kaman ba kaci komai ba?"
Girgiza kai yayi tare da faɗin

"No thank you"

"Amma Yallabai dan Allah Yusuf fa?"

Ba tare da ya ɗago ba yace mata "be shigo ba"

Haka ta fita ta bar office ɗin gwiwa a saɓule tana tunani "komai za'ayi ba'a taɓa birge gayen nan daga shi har Yusuf, gara ma wannan akan waccan me kama da saƙagon da magana ma se ya ga dama yake yi" tai maganar a fili da sigar mita

Ya tattara system din ya kashe, ya ɗauki wayarsa da mukullin motar sa, ya ɗora top ɗin kayansa a kafaɗa da jakar sa ya fito ya nufi wani ofishin.

Yana shiga dayan ofishin ya ƙame cikin girmamawa ya sarawa wanda ke office ɗin da alama shugaban sa ne, be zauna ba seda aka yi masa izini sannan ya zauna suka sake gaisawa.

Mutumin ya ɗago ya kalle shi yace
"Abbas kana ganin babu matsala a wannan aikin da'aka baka kasan hatsarin dake cikin aikin zaku iya kuwa? Kana ganin akwai wani cigaba akan case ɗin?"

Wanda aka kira da Abbas yai murmushi cikin girmamawa yace "karka ji komai ranka ya daɗe Insha Allah zan iya, zamu yi nasara, kuma ina fatan nasara Insha Allah yanzu idan na bar nan zanje in samu Yusuf
ne kasan shine jigon aikin"

"hakane to shikenan Allah ya tabbatar da Alkhairi ya baku sa'a na yadda da ƙwazon ku, Allah ya bada sa'a"

"Ameen yallabai muna godiya".

**********************************

Zaune yake Ya barbaza takaddu da na'urori masu ƙwaƙwalwa har biyu akan gadon sa ya tattaɓa wannan ya taɓa waccan, kafin daga baya yayi zugum yana kallon hotunan wata tsaleliyar yarinya, yarinyar wadda zata yi kimanin shekaru goma sha takwas sanye take da farin gajeren wando, se wata 'yar riga a jikin ta itama fara, ta saka farar hula hat ta baza gashin da ya kasa tantance nata ne ko na sawa ne, ga ƙaton baƙin tabarau a idonta ta buɗe fararen haƙoran ta tana dariya, bayan ta wani irin makeken ruwa ne shuɗi sosai, hannun ta na hagu riƙe da igiya da aka saƙalo wuyan wani jibgegen kare, jikinsa fal farin gashi ƙal, ba ƙaramin kyau yarinyar tayi a hoton ba. ko ƙwakwaran motsi ba yayi hotunan kawai yake dubawa kaman yana ƙoƙarin gano wani abu a jikin hotunan.

Wayarsa ce ta fara ruri, wanda ya sashi dawowa daga dongon nazarin da yake yi, ya duba wanda yake kiran wayar tasa yaga sunan Abbas akan Allon wayar tasa, yasa hannu ya kai wayar kunnen sa yace "Assalamu Alaikum warahmatullah"

Daga ɗaya bangaren aka amsa sallamar sannan wanda ya amsa din ya ɗora da cewa " ina ƙofar ɗakin ka kana cikine in shigo? akwai labari da nazo maka dashi"

"eh ina ciki shigo kawai"
Kafin ya kashe wayar aka turo ƙofar akayi sallama a ɗakin nasa, tashi yayi zaune ya aje wayar yana faɗin

"kai tun shekaran jiya daka turomin hotunan wata yarinya bamu kuma haɗuwa ba, kuma ka kashe wayarka, gashi saboda aikin nan ko Office bana zuwa ina ta ƙara bincike, ina ka shiga haka?"

Abbas yace "ka bari in zauna se in maka bayani sarkin ƙorafi"

"to zauna maza ka koramin bayani, wani labari kake tafe dashi?"

Abbas Ya samu guri ya zauna ya ajiye jakarsa ya tattara hankalinsa kan Yusuf sannan yace

" Yusuf kaga hotunan yarinyar dana turo maka dasu ta email ɗinka?"

"Eh nagani, su nake ta nazari ban san dalilin da yasa ka turo su ba"

Abbas ya gyara zama yace "
hotunan 'yar gidan Alhaji Nasir Daula ce, kusan aikin mu gaba ɗaya akan ta yake, sati biyu kenan ina zuwa ina gidan su a matsayin me saida mangwaro da yankan farce, na samu karɓuwa a gurin megadin gidan su, hakan yasa idan naje se in zauna muyi ta hira da megadin su sannaan in tafi"

Yusuf ya gyara zama yace "to aini banga Alƙar binkicen mu da ita ba"

"Injiwa ai ta hanyar ta zamu samu duk abunda muke so, ita kaɗaice 'yar Alhaji Nasiru, kuma itace target ɗin maƙiyan sa, aikin mu ba' a akan iya bincike bane hadda bata Kariya"

Yusuf yace
"Abbas sanin kanka ne binciken nan na sirri ne, shi kansa Alhaji Nasir be san ana yin shi ba ta yaya zamu bawa 'yarsa kariya"

Abbas yace "Yawwa ɗan gari bazata taɓa sanin Aikin da muke ba, yadda mahaifinta be sani ba itama baza ta sani ba, a hirar da muke dame gadin su yau watan ta uku da dawo wa daga America a can take Rayuwar ta, maman ta ta rasu a hannun step mum ɗin ta take, a tsawon lokacin nan mahaifinta ya sangar tata da kuɗi a taƙaice dai muguwar taɓararriya ce me wata irin AƘIDA ta kafiya da taurin kai ga mugun tsatstauran ra'ayi kamar baturiya, yarinya ce da bata da yadda tafi bawa mage da kare mahimmanci fiye da mutanen dake kusa da ita, bata san zafin talauci ba balle tayi wa wani talaka uzuri ko ɗaga ƙafa hasali ma gani take kaman talakawa bayin sune masu kuɗi bata ɗaga ƙafa ko sassauta wa na ƙasan ta san.....

"kaga dakata wannan dogon labari haka, kamin bayani a taƙaice" Yusuf ya katse shi

Abbas yace "Dadina da kai ƙosawa, hotunan dana turo maka hotunan tane"

Yusuf yace "to me zanyi dasu?"

Abbas yace "Yawwa anzo gurin, da dawowar ta a wata ukun nan direbobi biyar aka sallama saboda baza su iya jure halin ta ba, tana da gadara da wulaƙanci, a gabana tayi wa direban ta korara wulakanci jiya, Yanzu haka megadin ya bani labarin mahaifinta yasa shi ya samo mata wani direban daze dinga kaita unguwa, yake gayamin ya gaji da samo mutane tana wulaƙanta su, akwai Albashi me kyau amma halin ta da AƘIDAR TA kesa mutum ya gudu da kansa, dan haka nace ni ya barni zan samo mata direba, kuma kai nake so ka zama direban nata!!"

Wani mugun kallo Yusuf yayi wa Abbas
"Ashe baka da hankali, kaime ya hana kaje ka zama direban nata?, ni zanje in dinga tuƙa ƙaramar yarinya tana wulaƙanta ni akan me? Bazan yi ba gaskiya, ai kaine gaba dani a gurin Aikin kai kaje mana"

Cikin sigar rarrashi Abbas yace

"Calm down brother, nasan zaka iyane kai ƙarshe ne gurin haƙuri, kaga ni bani da haƙuri zan iya lakaɗa mata duka idan tayi min ba daɗi ƙarshe in ƙare a prison in shiga uku, kaikuma kowa ya san ka akan haƙuri da hikima, dan haka zaka iya, ɗazu mukayi magana da Yallaɓai na tabattar masa zamu iya aikin nan, ita kanta yarinyar a cikin gagarumin hatsari take, akwai bukatar a bata kariya da kulawa "

Ɗan tsaki Yusuf yayi yace" gaskiya ni bana son wulakanci ne, yarinya ƙarama ta wulaƙanta ni dan ni talaka ne, gaskiya ni ka gama dani daka haɗani da wannan aikin, daka barni da kayan computers ɗina da damuwar da nake ciki da se yafi min"

Abbas ya kuma gyara zama yace "cigaban mu ne idan mukayi nasara dan Allah ka daure, Sannan Yusuf lokaci yayi da zaka cire damuwa ka fuskanci Rayuwa ka manta da ƙalubale ka gina Rayuwar ka"

Cikin takaici Yusuf yace
"Abbas kenan kana yiwa matsala ta kallon ƙaramar matsala, amma Allah shi ka ɗai yasan zugi da Raɗaɗin da nake ji a raina idan na tuna ni wane ne, wace Rayuwa zan gina bayan bani da dirakun da zasu riƙe min ginin Rayuwar tawa? Abunda ya faru dani yasa naji komai yafi ta daga raina, yanzu na barwa Allah al'amura na, in riƙe mahallici na, in rungumi ummana da Aikina nasan bani da kamarsu"

Abbas ya dafa kafaɗar Yusuf yace "Yusuf nasara bata samuwa ba tare da an jarabci ɗan adam ba, kayi haƙuri da taka ƙaddarar, Allah yana sane da kai"

Yusuf yace "Hakane Allah yabani ikon cin jarrabawa"

Abbas ya amsa da Ameen, sannan ya ɗora da cewa
"Aiki na gaba se bayan ka zama direban ta sannan zan sanar da kai shiri na gaba, zan gaya maka aikin da'a ke so kayi"

Yusuf yace "to Allah ya bani iko ya tabattar da alkhairi ya bamu nasara"

"Ameen ya Allah, ɗazu fa mutuniyar ka tazo office ɗina tana ta kwarkwasa, take tambaya ta kana ina?"

Yusuf yace "wa kenan?"

"kafini sani ai, wacece in ba Sakina ba"

Tsaki Yusuf yayi yace "dan Allah Abbas ka dena sa kamin wannan yarinyar cikin lamurana, ni tun abunda ya faru dani duk wata harka da mata gudun ta nake yi, wannan aikin ma da kuka bani kaida yallaɓai dan ba yadda zanyi ne harka ce ta aiki, balle wata Sakina, ni ina tsoron mata nafi ƙaunar tsira da mutunci na da kuma tsayawa matsayin da Allah ya ajiye ni, nayi darasi akan abunda ya faru dani"

Abbas yace "hakane kana da gaskiya Yusuf, Amma ka sani idan har mukayi nasara a Aikin nan cigabanka ne, sekafi kowa benefitting gaba kaɗan in aikin ya kankama zan ƙara sanar da kai wasu abubuwan"
Abbas ya ci gaba da kwantarwa da yusuf hankali tare da lallaɓa shi har ya ƙara gamsuwa ya Amince Amince akan zasu je gidan Alhaji Nasiru Daula da weekends domin a tantance shi in ze iya zama direban Wannan yarinya me muguwar AƘIDA sannan a gabatar da Yusuf  a matsayin Sabon direban wannan 'yar Hamshaƙin Attajiri Me murɗaɗiyar AƘIDA!!!.

Tun bayan da Abbas ya tafi, Yusuf yake ta tunani akan wannan gagarumin Aiki, yana ƙara duba kyawawan hotunan wannan yarinyar da ko sunan ta be sani ba, she has an innocent face a hoto, gata very young and beautiful amma ya akayi take da halaye marasa kyau haka?
Idan har ya kasance da gaske tana da duk wannan halaye da'aka faɗa masa anya ze iya aikin kuwa?
Amma meyasa Abbas be warware masa yadda aikin yake ba gaba ɗaya yace se ya fara yi wa yarinyar aiki ze gaya masa?
"Allah yasa ba cikin wata cakwakiyar zasu jefa ni ba" yai maganar a fili tare da miƙewa ya tattare kayan da ya baza a kan Katifar sa ya fito daga ɗakin nasa.
Kasancewar Yamma ce bashi da gurin zuwa da yake shi bame yawan shiga sabgar mutane bane, ya shiga ɗakin Umman sa ya ɗakko kayan wankin ta ya wanke tsaf, ya share ko ina, ya ɗora girki se kace mace, cikin nutsuwa yake Al'amuran sa ya kammala dafa shinkafa da miya ya zuba a flask, lokacin ana ta kiraye kirayen sallar magariba yayi Alwala ya fice Masallaci.


Ayshercool
07063065680
                       _*AƘIDA TA*_

             

     *PART1*         
                  _Page 2_

*written and edited by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*

Bismillahir rahmanirrahim, da sunan Allah me Rahama me jin ƙai, Wannan littafi ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan cin zarafi ko cin fuska ga wani ko wata ko wata ƙabila ba, idan har wani ko wata yaga wani abu daya yi kaman ceceniya da rayuwar sa ko ƙabilar sa Amin Afuwa banyi dan cin zarafin wani ko wata ba.
    Wannan littafin mallaka tane, ban yadda a juyamin labari ta kowane fanni ba ba tare da izinina ba.

What's App : 07063065680
Watpad : Ayshercool7724
Gmail : Www.ayshertadam@gmail.com

************************************

Wata Babbar Mace ce Zaune a cikin wani katafaren falo me girma sosai, cike yake da kayan more Rayuwa, Aƙalla zata kai shakaru hamsin, Amma kaman 'yar shekara talatin da biyar saboda hutu idonta sanye da glashi ta nutsu sosai tana danna Computer tana shan tea.

Wata matsashiya ce ta shigo falon a ƙalla za ta kai shekaru Ashirin da bakwai, tazo ta zauna a kusa da Matar.
Ba tare da Matar ta ɗago ba tace "Ya a kayi ne? Nasan akwai damuwa tunda na ganki yanzu meya faru?" ta ƙarasa maganar tana kallon matashiyar.

Ta ɗan yatsuna fuska tace " Mummy kin san wani abu?"

"A'a sekin faɗa" matar ta bata Amsa

Cikin shagwaba tace "Mummy ki duba girman gidan nan da cikar sa, kalli dukiyar dake cikin gidan nan, Amma mota ɗaya tak na mallaka, ko ɗan direba ma ba'a sama min ba, Amma kalli 'yar masu gida motocin ta nawa? Direbobi nawa ta wulaƙanta ta sallama a dawowar nan tata? Har motocin me gidan nan take hawa in ta ga dama gaskiya ana nuna mana wariyar launin fata, banda cin fuska da wulakanci da muke fuskanta seka ce wasu Bayi"

Matar ta cire glashin fuskarta tace

"Ramlah me kike so inyi? Alhaji Baya jin magana ko ganin girman kowa sena 'yar sa, abunda take so shi yake yi, Sannan duk abubuwan nan da suke faruwa na ɗan lokaci ne, Amma me kike so ayi? "

"Mum Mota nake so a canzamin sannan nima a ɗaukar min direba, bama mota ba motoci nima in dinga kece raini yadda yakamata, kalli daular da muke ciki, Amma a ce se abunda yarinya ƙarama take so akeyi, Mummy ina son inyi birthday ina buƙatar kuɗaɗe masu yawa fa wanda zan burge ƙawaye na dasu, Sannan naji labarin Akwai filayen da gwamnati za ta yi gwanjonsu a GRA ya kamata ace  kin mallaka"

"Hmm Ramlah kenan samun wannan abubuwane masu Sauƙin samu a hannun me gidan nan, Amma kin san seda izini kokuma ince yaddar 'yarsa ko?"

Ramlah tace "Amma Mummy ba yadda za' ayi in samu kuɗin a hannun ki? Kina matarsa amma ace se Abunda 'yarsa take so haba dan Allah, yakamata ace Akwai wata Dama da zaki dinga mallakar kuɗaɗe bayan wanda yake baki"

"babu wannan damar, dan duk kuɗin dazan fitar seda sanin Lawyern sa, dan haka ba yadda zanyi, Karki manta muna da kyakkyawan shiri a ƙasa shiyasa sam bana damuwa, ni yanzu so nake in lallaɓa shi Amal me ta tafi turkey ta ci gaba da karatu a can"

Ramlah tace
"shikenan Amma yakamata kiyi wani abu akai kar wannan damar ta wuce mu, Amma kafin wannan ya batun canza motarfa?"

Mummy tace "Wannan kuma sekin yi tsani da 'yar masu gida, tana magana ko mota goma kike so kamar kin samu, batun kuɗi kuma zan tura miki kuɗi Account ɗinki base munjira ba, Amma ki same ta in ta yadda za tayi masa magana a baki wata motar"

Ramlah ta yamutsa fuska tace
"A' a Mummy ke zaki mata magana, kin san ba shiga sabgarta nake ba, bana son wulaƙanci da rainin hankali, kin san bama shiri da ita"

Mummy tace "ke kina tunanin idan nayi mata magana zata saurare nine? Yau kwana biyar rabon da in sata a idona fa yarinyar nan barta kawai"

Ramlah tace "bari in kira miki ita dan Allah ki mata magana ko zata sa baki, ni kin san bama jituwa da ita"

Mummy ta ɗan jinjina kai tace "shikenan Allah yabada sa'a"

Tana zaune akan stool a gaban dressing mirror ɗin ta wanda yake shaƙe da kayan shafe shafe na mata, towel ne a jikin ta tana ta ƙoƙarin tsane gashin kanta.
Ƙofar ɗakin aka turo aka shigo, wata matashiyar budurwar ce ta shigo ɗakin ba tare da tayi sallama ba ko wata doguwar maganaba tace 

"Mum nasan ganin ki a cikin gida, zakuyi magana"

Wadda akewa maganar se kace da gini ake, ko gezau ba tayi ba ta ci gaba da abunda take yi,  bata kalli me mata maganar ba ta cigaba da abunda take yi .
Cikin ƙosawa da fushi matashiyar wadda aƙalla ta girmi wadda take wa maganar nesa ba kusa ba tace

"wai ba kyaji ina miki magana ne? Kin min banza kaman baki san na shigo ba?"

Cikin isa yarinyar ta Ajiye Ƙaramin Towel ɗin hannun ta, ta miƙe ta nufi wardrobe ɗin ta, Subhanallah koda ta buɗe wardrobe ɗin sutura ce a ciki kaman shara, kamar inji ne ya shirya kayan ba hannu ba, kai in akace suturar mutum ɗaya ce seka riƙe baki tareda tunanin ina mamallakin suturar ze kai ta?

Ta saka hannu ta janyo wata 'yar riga ja mara hannu, tana ƙoƙarin sakawa ba tare da ta waigo ba cikin ƙasaita tace

"Ramla ki koma ki gayawa wadda ta aiko ki banyi budget da lokacin da zan bata ba a yanzu, ko menene idan ta damu tazo da kanta ta sameni in gani ko zan iya saurarta, idan kuma bame mahimmanci bane zata iya haƙura har se lokacin da Allah yasa na shigo cikin gidan, you can go out i need privacy"

Cikin ɓacin rai Ramla tace "Waike wace irin mara ɗa'a ce haka? Mahaifiyar tawa ce zata zo ta same ki? Kika san me yasa ta kira ki? Se kace sa'ar ki?"

"koma me zesa ta kira ni nasan baze wuce biyan wata buƙata tata ba kokuma ta 'ya' yan ta, ni kuma da ku da ita bani da lokacin ku a yanzu, ɗan fitar min daga ɗaki, zan kaɗaice inyi tunani"

Ramla tace  "Amma baki da kirki, a gabana kike faɗan maganganu akan uwata, ke har Abada girma da shekarun mutum baya sa ki bashi girma, Ko ance miki rayuwar Turai hauka ce? Rayuwar turai fa  ta saɓa da Al'adunmu, Ko kuma akanki aka fara Arziki?"

"Enough Ramlah" Yarinyar ta katse ta  ta nuna Ramlah da yatsa ta ɗora da cewa

"Amma kamar kin san ba'amin shouting ko? You know the consequences of doing that. Mahaifiyar ku, ku ta haifa, ni kuma Babana take Aure bata haifeni ba, what's the meaning of respect according to you ne Ramla? Your mother is just a human being like everyone, she don't deserve any special respect, i will treat her the same way i treat every human being,  and mark you This is my father's house,  if you are tired of what am doing, go back to your father's house, nan gidan mahaifina ne ina da right inyi abunda nake so, and no one should stop me from doing what I want, if you are tired of what am doing park your things and go, madam get out from my room, kaina ya fara ciwo ki fitar min daga ɗaki "

Cikin faɗa take maganar, hannun ta ɗaya riƙe da kanta, tana nunawa Ramlah ƙofar fita

Ramla ta ƙulu matuka ta fice a fusace tare da buga ƙofar ɗakin da ƙarfi.

Falo ta koma inda tabar mahaifiyar ta, kallo ɗaya Mummy tayi mata ta ɗanyi murmushi tace "yana ganki a fusace?"

"Mummy wallahi yarinyar nan bata da mutunci, kinga rashin mutuncin da tamin kuwa, wallahi badan ina gudun abunda ze biyo baya ba sena shaƙeta kowa ya huta"

"hmm Ramla kenan, baki ga komai akan halin ta ba, ni da nake tare da ita ni nake ƙunsar takaici da baƙin ciki, Amma ina jiran lokaci ne wanda...
Bata ƙarasa ba tai shiru tareda yin murmushi ta dafa kafaɗar Ramla tace "karki damu daughter, saura ƙiris komai ya canza, na sama ya koma ƙasa, na tudu ya koma ruwa, a wannan lokaci da dariya zata gagari kare, hmm kiyi hakuri ni da kaina zan canza miki mota, in ɗaukar miki driver kinji?"
Shiru Ramla tayi ba tace komai ba se faman huci da take yi. kaman an mintsine ta tace

"wallahi na tsani yarinyar nan Mummy, bana ƙaunar ganin ta ji yadda aka maida ke da mu kaman wasu bayi ko 'yan Alfarma a gidan nan, ai ko Albarkacin kina Auren mahaifinta ya kamata ace muna da matsayi na musamman"

Mummy tace
"nifa nace kiyi hakuri ko? Komai ya kusa zama tarihi"

********

Yusuf Yana zaune har Bayan sallar isha'i yana kallon labarai, yaji anyi Sallama amsa sallamar yayi tareda ɗan ɓata rai.
Me sallamar ta shigo falon ta ajiye jakarta da mayafi ta ɗan kalli inda Yusuf yake tace
"fushi kuma ake dani, ko a kalli inda nake? Ai gani na dawo"

Yusuf yace "haba Umma tun azahar kika fita se yanzu bayan isha'i duk kaɗaici ya dameni"

Umma tace "kai tafi can, sekace wanda nake shayarwa ba damar in ɗan fita, ka dinga damuwa kenan"

Cikin shagwaba yace "wana keda shi inba Ummana ba? Dole in shiga damuwa duk lokacin da kikayi nisa dani ummana, daga Allah seke se kuma Aikina ku kenan nake da su, niba Abokai ba ko wasu mutane na musamman ke ɗin ce dai, Allah ya jiƙan Abba na, tun abunda ya faru Umma ke kaɗai nake da yaƙinin ƙaunar ki a gare ni baza ta gushe ba, shiyasa bana son kiyi nisa dani"

Tausayin Yusuf ne ya mamaye ta, har zuciyar ta ta karaya hawaye na ƙoƙarin fita daga idon ta, da sauri ta fice ta bar ɗakin da nufin yin Alwala.

Bayan Umman Yusuf ta idar da sallar isha'i suka ci Abincin dare tare suna hira, Yusuf yana ta so ya sanar da Umman sa batun Aikin da'aka bashi a Office amma ya kasa, dan yasan idan har ya gaya mata ranta zata ji babu daɗi, ace ɗanta Yazama direban yarinya, Yarinyar ma mara tarbiyya wadda bata san darajar ɗan Adam ba, dan haka ya bar abun a ransa be gaya mata ba.

Haka ya kwana yana tunanin wace karɓa ze samu a gurin yarinyar nan? Ya aikin ze kasance? Haka yaita tunani har bacci ya ɗauke shi.

Washegari ma Yusuf yayi ƙoƙarin yiwa Umman sa zanncen amma ya kasa, haka yai breakfast ya tafi gurin Aiki.

A office ma kasa wani aikin kirki yayi, wayar sa ya ɗakko yana kuma duba hotunan wannan tsaleliyar yarinyar, ya kuma tuna irin halayen ta da Abbas ya bashi labari. Ɗan tsaki yayi ya ajiye wayar ya jingina da kujera ya dafe kansa yana tunani.

Sallamar Abbas ce tasa ya ɗago kansa, Abbas yace "Yusuf dama ka shigo yau baka nemeni ba?"

"na shigo tun ɗazu ina aiki ne shiyasa ban neme ka ba"

"OK tashi muje, Yallaɓai Suleiman na son ganin mu yanzu"

Yusuf ya miƙe yabi Abbas suka fice, suna zuwa suka gaisa cikin girmamawa, yai musu umarni suka zauna.

Yallaɓai Sulaiman yace "Yusuf nace kuzo tare da Abbas ne dan tabattar da cewar aikin da muka ɗora muku zaku iya, mussman kai Yusuf nasan kana da kula da aiki kuma kana da haƙuri matuƙa"

Cikin girmamawa Yusuf yace "Insha Allah Yallaɓai baza'a samu matsala ba"

"Good kayi taka tsan2 kabi a hankali, karka kuskura wani yasan bincike ne ya kaika gidan, kasan aikin ka base na gaya maka ba, samun matsala a wannan aikin gagarumin hatsari ne da kuma Asara ina fatan kun san hakan"

Yusuf ya risinar da kai yace "Insha Allah ba zamu baka kunya ba sir"

"kai kuma Abbas ku kula yadda ya kamata"

Abbas yace "Insha Allah sir za muyi iya ƙoƙarin mu"

Haka suka ci gaba da tattauna wa akan harkar aiki, sannan Yallabai Suleiman ya sallame su.

Bayan fitowar su Abbas yaita bawa Yusuf ƙwarin gwiwa tareda bashi shawarwari, suka tsara yadda tafiyar tasu zata kasance ranar Asabar zuwa gidan Alhaji Nasir Daula.

Tunda gari ya waye Asabar gaban Yusuf yake faɗuwa, ya rasa dalilin da yasa tun da'aka gaya masa Aikin daze yi yaji gaban sa na faɗuwa a duk sa'ar daya tuna, har seda Umman sa ta fuskanci ya rage walwala, ta tambayeshi yace mata "bakomai" haka Yusuf yaci gaba da Adduo'i.

Yana nan zaune a ɗakin sa ya rasa abunda yake masa daɗi, misalin ƙarfe sha ɗaya na safe Abbas yazo, ya tsaya a tsakar gida suka gaisa da Umman Yusuf sannan ya shiga ɗakin ya same shi.
Abbas ya kalleshi daga sama har ƙasa yace

"gaskiya Yusuf wannan kayan naka ba suyi kama da wanda zeyi aikin direba ba, gaskiya ka canza kaya, ni baka ga kayan da na saka ba"
Se lokacin Yusuf ya lura da koɗaɗɗen Yadin dake jikin Abbas, Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "Taɓɗijan, wannan wane irin kaya ne?, ni ban san wani kaya zan saka ba"

Abbas ya buɗe wardrobe ɗin Yusuf, duk kayan Yusuf masu kyaune, da ƙyar ya ɗakko masa wasu ƙananan kaya ya bashi ya saka suma dai basu ji jiki ba, Yusuf ya karɓa ya saka, yace "Allah yasa kar Umma tayi min magana akan kayan nan"

har zasu fita Abbas yace "ɗan tsaya idan muka je gidan Sunana Sani me mangwaro ba Abbas ba "

Yusuf ya jinjina masa kai sannan suka fito, Yusuf ya kalli Ummansa dake kwashe kayan wanke2 yace "Umma zamu fita"
Umma tace "to Yusuf, Abbas ka gaida gida sekun dawo"

Har zasu fita Umma ta kira yusuf tace "Yusuf zo nan"
Dawowa yayi tace "Wannan wace irin shiga kukayi, kalli kayan jikinka be kamata ace ka fita da su ba, Allah ya rufa maka Asiri amma kasa wannan kayan kana yawo a gari"

"Umma shima hakan cikin harkar Aiki ne, idan na dawo zan miki bayani Insha Allah"

Umma tace "Amma harkar aiki shine zaka fita da wannan suturar kamar mara galihu"

"haba Umma wallahi kayan nan da kyansu, kiyi min Addu'a sena dawo"

Ɗan girgiza kai tayi yayin da Yusuf yayi waje da sauri.

Napep suka tara suka hau zuwa gidan Alhaji Nasir, yayin da gaban Yusuf keta faɗuwa.
Tun daga bakin layin shiga rukunin gidan jam'ian tsaro ne ke kaiwa suna komo wa, seda aka musu tambayoyi kafin su wuce da yake sun gane Abbas yana zuwa, aka barsu suka wuce.

Koda suka je gidan Abbas ne ya sallami me Napep ɗin, tun daga waje Yusuf ya fara ƙarewa gidan kallo tirƙash lallai mamallakin gidan yaci ai masa inkiya da Daula.
Suka ƙarasa ƙofara katafaren gate ɗin suka tsaya, Abbas ya ɗakko wayarsa ya kira Isa me gadi, yace masa suna waje.
Befi mintuna uku ba aka buɗe ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin ya leƙo yana ganin su Abbas ya washe baki yace

"bismillah ku shigo Ashe kaine"
Suka shiga suka tsaya suka gaisa da Isa.
Isa yace "Sani wannan ne ɗan uwan naka daze aikin?"

Abbas yace "Eh shine"
Isa yace "Ya sunan shi?"

"Sunana Yusuf" Yusuf ya bashi amsa

Isa yace  "masha Allah to Allah yaba ka iko, dan seka yi haƙuri aikin akwai samu amma babu sauƙi, bari inje in sanar wa da Alhaji zuwanku"

Abbas yace "shikenan babu laifi"

Bayan tafiyar Isa, Yusuf ya kalli harabar gidan, wasu irin motoci ne masu rai da lafiya a tsaye a gefe ɗaya, yayin da ainihin ƙofar shiga katafaren gidan se kayi wani gajeren tattaki daga gate ɗin kafin ka kai ga ƙofar.
Yusuf ya numfasa yace

"wai ni Abbas ya aka yi rukunin gidajen nan jam'ian tsaro ke gadi, Amma kuma nan gidan naga wannan ma shiriricin ke gadi"

Abbas yace "Sani dai ba Abbas ba"

Yusuf yace "Am sorry, Sani"

Abbas yace "duk yana cikin binciken da za kayi, ka kula kayi taka tsan2, banda sakin jiki da kowa dama nasan kai ba me son hayaniya bane"

Isa ya dawo yace "bismillah ku taho mu shiga, Alhaji yace a shiga daku"

Tunda suka kama hanyar shiga cikin gidan Yusuf yake ƙarewa ko ina kallo, an danƙarawa gidan dukiya kaman ba'a san ciwon ta ba.

Wasu irin faluka suka dinga ratsawa, kowanne da kalar sa da irin tsaruwar da yayi, shikan sa Abbas be san haka cikin gidan yake ba.

Sunyi doguwar tafiya kafin su iso wata ƙatuwar ƙofar glashi,Isa yasa hannu ya murɗa suka shiga da sallama.

Iya girman falon nan ya ishi wani talakan gina wadataccen gidan da ze zauna, Yusuf ya fara tambayar kansa shi kuwa wannan wane irin sana'a yake yi da har ya gina wannan gidan kamar baze mutu ba?

Babban mutum ne a zaune akan wata luntsumemiyar kujera yana karanta jarida gefen sa da wata mata, se 'yan mata biyu zaune akan kujerar dake facing ɗin su.

Aka amsa musu Sallamar, cikin girmamawa suka gaisa da me gidan tare da iyalan sa, yanayin gaisawar tasu ze nuna maka mutum ne me fara' a, dan kuwa fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa musu.

Isa yace "Yallaɓai sabon driver ne da kace a samo, shine suka zo yanzu"

Ya ajiye Jaridar hannun sa yace "Masha Allah wanne ne daga cikin su?"

Cikin girmamawa Yusuf yace "Nine"

Alhaji Nasir ya ɗan ƙura masa ido yace "masha Allah, ya sunan ka?"

"Suna na Yusuf"

Alhaji Nasir ya jinjina kai yace "Hajiya Halima kinji me sunan Yaya na ko?"

"Aikam dai me sunan shi" ta amsa

Alhaji Nasir yace "Allah sarki, Allah yasa me irin halin sa ne, ni duk Yusuf ɗin dana sani mutanen kirki ne, ina fatan kaima haka?"

Abbas yace "Alhaji ba ganin ido ba Shima mutumin kirki ne sosai"

Alhaji yace "ai dama na sani, ban taɓa ganin Yusuf mutumin kawai ba"

Ya kalli 'yan matan nan dake zaune yace "Amal jeki part ɗin gimbiya ta, ki gani idan idon ta biyu bata komai ki gaya mata Daddy na son ganin ta, idan kuma da abunda take yi ki ƙyaleta"

Wadda aka kira Amal ta miƙe tare da cewa "to Daddy" .

Babban abunda ya bawa Yusuf mamaki be wuce tun lokacin da' aka ce shine ze zama direban, matar da 'yan matan nan suke binsa da kallo ba, mussman wadda aka kira Amal yadda ta tsare shi da idanuwa.

Seda akayi Minti goma sha biyu da tafiyar Amal, sannan  ta dawo tace "Daddy tace tana zuwa"

Alhaji Nasir yace "to babu laifi"

Wasa2 seda sukayi minti Arba'in ba suga Alamar wadda aka kira ɗin zata fito ba, iyalan suka ci gaba da hirar su aka bar su Yusuf shiru kamar mayu.

Gaba ɗaya Yusuf ya gaji da zaman, ga sanyin A. C da kallon ƙurillar da'ake masa duk yabi ya takure.

Alhaji Nasir ya kuma cewa "Ramla bawa baƙin nan Abinci kafin ta zo"

Ba tare da Ramla tace komai ba ta miƙe ta fice, ruwa da fruits ta kawo ta ajiye musu.

Abbas da Isa suka dinga ɗauka suna ci suna kallon tv, shikam Yusuf ya kasa cin komai, gaba ɗaya a takure yake, gashi ko ɗaga kai baya son yi saboda kallon da'ake masa.

Kaman ance ya ɗaga kai idonsa yayi tozali da wata irin kyakywar halitta, babu shakka itace a jikin hoton da Abbas ya tura masa, Amma a zahiri tafi haka kyau, gabansa ne ya dinga faɗuwa ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi, yarinya ce sharaf amma se kwarjini fara ce ƙal tana sanye da skin tied iya gwiwarta, se wata over size shirt data saka har wajen gwiwarta, kanta babu ɗan kwali gashin ta a hargitse babu ribbon, ta sake shi a kafaɗun ta.

Fuskarta a haɗe babu annuri, ta ƙaraso cikin falon ta zauna kusa da mahaifin ta. Tana zama Hajiya Halima ta miƙe ta canza wata kujerar

Alhaji Nasir yace "Lovely daughter ina fatan ba'a takura miki ba?"

Girgiza masa kai tayi alamar A'a

Alhaji Nasir yace "Sabon driver ne gashi nan, yazo ki gani in yayi miki"

Kamar baza tace komai ba ta ɗago ta kalle su ɗaya bayan ɗaya ta tsaida idon ta akan Yusuf ta ɗan ɗau lokaci tana kallon sa kaman tana ƙoƙarin gano wani abu.
Ɗauke kai tayi ta haɗe rai cikin isa tace

"Ramla kawo min madara da cup, sannan kije falona ki kawomin wata folder akan kujera"

Waigawa Yusuf yayi ya Kalli wadda aka kira Ramla,  ta girmi yarinyar da har yanzu be san sunan ta banesa ba kusa ba, dan shi har yanzu beji wanda ya faɗi sunan ta ba,  ramla ta miƙe ta tafi cika umarnin ta.

Yarinyar da dudu bata fi shekaru sha takwas zuwa sha tara ba, a idon ta da yadda take magana zaka gano tsabar izza, da isa, Ta kalli Abbas tace "kai kaman na sanka ko?"

Abbas yace "eh ni abokin Bala ne, ina zuwa gurin sa"

"good, kai Bala meye aikin ka?"

Cikin Rawar jiki yace "gadi ranki ya daɗe"

"to ka tashi da kai da shi ku fita ka koma kan aikin ka"
Ba musu bala ya miƙe, Abbas ma ya miƙe, kafin su bar falon  ta kalli Hajiya Halima tace

"Madam i need privacy you can leave"

Ɗan taɓe baki Hajiya Halima tayi ta miƙe ta nufi wata ƙofar daban.

Ta kalli inda Amal take ta mata wani kallo, tun kafin ta furta komai Amal ita ma ta miƙe ta nufi barin falon.

Gaba ɗaya mamaki ya cika Yusuf, yadda take wannan izzar take wa manya magana babu respect kuma a gaban mahaifin ta amma bece komai ba, ya ma maida hankali akan jaridar sa kaman be san me take yi ba.

Ramlah ta dawo ɗakin ɗauke da cup da madara  tazo ta ajiye, sannan ta miƙa mata folder, taje ta nemi guri akan  kujerar da ta tashi zata zauna, Amma suka jiyo zazzaƙara muryar ta tace

"wait don't sit, get out from here, bana buƙatar wani a falon zan gana da shi"

Wata irin Ajiyar zuciya Ramlah tayi ta ɗan jinjina kai ba tare da ta waigo ba ta miƙe ta fita ta bar falon itama.

Madarar ta ɗauka ta zuba  a cup tana sha, tana kaɗa ƙafa kaman tama manta da Yusuf a gurin.

Alhaji Nasir ya kalle ta yace "gimbiyar Daddy bari inje in ɗan watsa ruwa zan fita anjima, yadda kuka yi dashi kya gayamin in na dawo, in yayi miki.

Ɗan ɗaga girar ta ɗaya tayi ta lumshe ido ba tare da tace komai ba.

Bayan tafiyar mahaifinta haka suka ci gaba da zaman kurame ita da Yusuf

Can ba zato ba tsammani yaji tace

"what's the level of your Education?"

Yusuf ya ɗanyi jim sannan yace "secondary school" yai maganar ƙirjinsa na bugawa

Shiru ta kuma yi tana kallon tv seda aka kuma jan wani lokacin sannan ta kuma cewa
"Meye sana'arka?"
Gumi ne ya fara tsatstsafo masa dukda sanyin AC da yake ɗakin, Yusuf baya son kuma yin ƙarya, Amma yace

"Eh ina ɗan zuwa kasuwa ne ina yaron shago"

Cikin Tsara magana da take daki daki, da muryarta me sanyi tace

"Anyway naga kaman za kayi hankali, zan iya yadda ka zama direba na amma ina da sharuɗai"
Ta ɗanyi shiru kaman ba zata kuma magana ba, sannan ta ɗora

"bana son ƙarya, duk ranar da na gano kayi min ƙarya zaka fuskanci hukunci me tsauri, bana son sa ido da shishigi a cikin lamurana, bana yafewa maƙaryaci ko wanda yaci amana ta, babu ruwan ka da irin mutanen da nake hulɗa dasu, bana yadda da mutum kowaye ni kaina wani lokacin bana yadda da kaina balle wani, dan haka duk lokacin da kayi motsin da ban yadda da shi bama zan iya sawa a kulle ka, ban yadda da saɓa lokaci ko Alƙawari ba, sannan lokacin dana ɗauke ka aiki mallaki na ne bana ka ba, ibada kaɗai kake da 'yancin yi, bayan wannan baka da hurumin yin wani aiki idan ba nawa ba, se dai idan ni na baka dama, in ka amince da sharuɗai na" ta ajiye wata takadda

"kayi signing anan, salary 200k and your hard work determines your salary promotions"

Shiruu Yusuf yayi yana tunani, gaba ɗaya ya rasa abun yi
Yusuf yace
"ranki ya daɗe ko zaki iya bani dama inje inyi shawara"

"I don't gives second chance, and I don't want too much waste of time" ta bashi amsa tana maida hankalinta kan talabijin

Shiru Yusuf ya kuma yi ya ɗauki takardar yana jujjuya ta ba tare da ya karanta meye a jiki ba, gumi se karyo masa yake ya ciro biro a Aljihun sa, hannun sa na rawa ze sa hannu yaji tace

"that means you accept the terms and conditions i have mentioned?"

Jinjina kai yayi alamar yana ƙoƙarin ya saka hannu tace

"if you are here to spy don't sign this paper"

(idan kazo nan ne dan leƙen Asiri kar kasa hannu a takardar nan)

Ras! Gaban Yusuf ya faɗi, Anya babu wata a ƙasa, yarinyar nan bata san komai ba? Cikin ƙwarewar Aikin sa ya dake  yace

"ranki ya daɗe menene Spy kuma?"

Banza tayi masa ba tace komai ba.

Seda Yusuf yayi Addu'a a zuciyar sa sannaan yasa hannu akan takardar.

Ta sa hannu ta ɗauki takardar ta jujjuya ta sannan tace

"signing this paper is like signing on your death contract!!! Jeka sena neme ka"

Tana gama faɗin haka ta miƙe ta bar falon

Ras! Ras!! Ras!!! Gaban Yusuf ya faɗi
A fili yace "My death Contract kuma?"!!!


Ayshercool
07063065680

                      _*AƘIDA TA*_

                 
                *PART1*      
                            _Page 3_

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Special thanks to my Association Members
Perfect writers Association



Maimaita death contract Yusuf ya dinga yi, ya rasa abunda ya kamata yayi, a hankali ya miƙe ya biyo hanyar da Isa ya biyo da su ya fice.

Abbas yana tare da Isa yana jiran fitowar Yusuf, kallo ɗaya Abbas yayi masa yasan akwai matsala, da ƙyar Yusuf yake ɗaga ƙafarsa,  Isa da Abbas suka dinga tambayar sa meyafaru? Amma yaƙi cewa uffan, Abbas yayi wa Isa Sallama ya ja Yusuf suka tafi, be ƙara tambayar Yusuf ba har suka je gidan su Yusuf.

Da suka je gidan ma Yusuf yai mursisi yaƙi faɗa wa Abbas yadda suka yi, daga ƙarshe dai Abbas ya ƙyale Yusuf ya ɗauka ire iren wulaƙanci ya fara fuskanta, dan haka yaita bashi haƙuri yana kuma rarrashin sa kan ya daure kar ya karaya.

Sam hankalin Yusuf baya kan Abbas, gaba ɗaya ƙwaƙwalwar sa ta shiga lissafe lissafe daban2, a karon farko da shigar sa Aiki wannan ne aiki me matuƙar wahala da sarƙaƙiya a gare shi, yana buƙatar nutsuwa da taka tsantsan akan komai.

"Yusuf naga kaman hankalin ka baya kaina fa?"
Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "ta yaya zaka samu hankali na, tace ba'a mata ƙarya bata yafe wa wanda yayi mata ƙarya, Nikuma akan ƙaryar ma naje nake aikin, yanzu idan ta gane gaskiya fa?"

Abbas yace "karka damu kayi abunda ya kamata kawai tana ƙoƙarin yi maka ba razana ne, idan kabi a hankali ba zata gane komai ba"

"to Allah yasa?"

Abbas yace "Ameen"

Bayan tafiyar Abbas fa tunani ya auri Yusuf, kasa jurewa yayi seda ya gayawa Umman sa aikin daze jeyi a matsayin direba gidan Alhaji Nasir Daula amma ya ɓoye mata gaskiyar halin yarinyar da sharuɗai da ta saka masa.

"Yusuf wace irin lalacewa ce kana aikin ka gwanin sha'awa zaka koma wani direba?"

"Umma ba lalacewa bace, harkar aiki ce ta kawo haka"

"hakane amma ni bana son sabga da masu kuɗin nan yaran su ba tarbiyya suka cika ba, bana so a wulaƙanta min ɗa a banza, gurin aikin naku babu wanda zasu saka se kai"

Yusuf yace "Umma Addu'arki da goyon bayanki nake buƙata, idan kika soki abun zaki kashe mun gwiwa ne"

Umma ta numfasa tace "shikenan Allah ya tabattar da Alkhairi, Allah yabada sa'a, ka kula da kanka"

"insha Allah umma na nagode sosai"

'yan kwankin nan Gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idaniyar ta, duk motsin da zata yi surar Yusuf take gani, rashin walwalarta da yawan son kaɗai cewa ne yasa 'yar uwatta lura da akwai abunda yake damun ta kasancewar ta me surutu da san hira.
Ramla ta dubi yadda' yar uwar tata tayi shiru tana jujjuya spoon a cikin cup ko sau ɗaya bata kai abunda ke kofin bakin ta ba, bayan shafe kusan mintuna goma da zaman da tayi da niyyar cin Abinci.

"Amal wai me yake damunki haka ne, na lura tun jiya kin zama wata iri"

Amal ta ajiye spoon ɗin hannun ta a ranta  tace "Mhmm Yaya Ramla ina cikin damuwa tabbas, kuma na shiga damuwa ne domin ƙoƙarin samo mafita akan gagarumin lamarin dake barazanar jefani wani bigire da be kamata ba, Amma nasan bazaki taɓa bani goyon baya ba" Amma a zahiri tace
"karki damu bana jin daɗi ne kawai"

"Amma yakamata kije kiga likita"

Amal tace "ba abun damuwa bane, zan ware Insha Allah"

Tun Yusuf yana fama da tunani tareda sauraren kira daga uwaɗakkinsa har ya fidda rai, ya fara mantawa ya shiga sabgogin sa.

Kusan sati uku kenan da zuwan Yusuf gidan daga nan Amal bata ƙara saka shi a idon ta ba, wasa wasa abu ya ci gaba da damun zuciyar ta, gashi abu na ta faman damun zuciyar ta.

Alhaji Nasir Daula ne zaune a wani ƙaton falo shida wani mutum wanda zeyi sa' ansa, sukw hira tareda ƙyaƙyata dariya kai da gani kasan akwai kyakkyawan kusanci da fahimtar juna a tsakanin su.

"Alhaji Nasir nikam daughter tunda ta dawo ƙasar nan bata zo mun gaisa ba, kota manta dani ne?"

Alhaji Nasir yace "haba Bulama yaza'ayi daughter ta manta da kai, kawai dai kasan halin ta ne Nason kaɗaici har yanzu a haka take, Amma insha Allah zan turo maka ita har gida ku gaisa"

Alhaji Bulama yace "kana nufin har yanzu bata dena wannan ɗabi'ar ba, ba ta warke ba kenan?"

"kai dai bari kawai, lamarin daughter yana damuna, ace kaf rayuwar ɗan adam be yadda da kowa ba, ba za ta sake da kowa ba, to koni wataran ina ƙasar nan idan bata ga dama ba se tace bata son inje inda take, narasa menene mafita "

Jinjina kai Alhaji bulama yayi yace" "wai shekarun ta nawa ne yanzun?"

"18 to 19, amma menene ma fitar?"

Alhaji Bulama yace "mafita ɗaya ce shine kayi mata Aure, idan har aka yi mata Aure zata dena wannan halin nata"

Alhaji Nasir yace "Aure kuma? Dudu du guda nawa daughter take? Yarinya ce ƙarama kuma waze iya jure halayen ta?"

Alhaji Bulama yayi murmushi yace "kai kake ganin yarintarta idan ka aurar da ita daram zata zauna, samun wanda ze zauna da ita da halin ta abune me sauƙi, semu haɗa ta Aure da Fahad yaron guri na da yake karatu a china, dama bata sanshi ba kaga se a haɗa su, hakan ze ƙara zumunci dake tsakanin mu, kuma kaga tunda ita kaɗai Allah ya baka seka samu 'yan jikoki"

"Masha Allah gaskiya naji daɗin wannan shawarar taka, amma kasan semun bi a sannu idan nace zan tursa sata, za' a iya samun matsala"

"bakomai mu bi komai a sannu insha Allah babu wata matsala"

Suka cigaba da hirarrakin su.

Misalin ƙarfe goma na dare Yusuf yayi shirin sa tsaf ze kwan ta, wayar sa ta fara ringing, Sunan Abbas ne akan screen ɗin wayar, ya ɗaga suka gaisa

Abbas yace "Yusuf ɗazu Isa megadi ya kirani, yace min yarinyar nan ta bada saƙo tace zaka kaita unguwa gobe misalin ƙarfe goma na safe, ta jadadda goma na safen nan dan haka ka kiyaye"

"Shikenan zan je Insha Allah"

Tunda Yusuf ya kwanta ya gagara cikakken bacci, da yaje sallar Asuba sam be koma bacci ba, ya zauna ya ci gaba da lazumi, da sassafe ya tashi yayi wa mahaifiyarsa aikace2, kaman yadda 'ya mace za tayi haka Yusuf ya share ko' ina yai wanke2 yai girkin karin kumallo.

Koda Ummansa ta tashi tayi mamakin inda Yusuf yake gaggawar zuwa, bata son yawan takura masa dan haka ta ƙyaleshi.

Ƙarfe tara dai2 na safe Yusuf ya isa gidan Alhaji Nasir.

Isa na ganin sa yace "kai sannu da ƙoƙari Allah yasa ka ɗore, idan ka ɗore da zuwa akan lokaci saura kuma ƙalubale na gaba"

Yusuf yayi murmushi yace "Malam Isa kenan, Kowace sana'a tana da ƙalubale, sedai fatan Allah ya bamu ikon aikata dai2"

Da yake Isa akwai surutu kaman an ƙona shi aka, haka ya dinga zubawa Yusuf surutu kuma surutun nasa ba'aakan kowa bane se kan 'yar masu gida

Yusuf yace "wai ya sunan ta ne?, nifa har yanzu ko sunan ta ban sani ba"

Isa yace "Ai abune me wuya kaji sun kira sunan ta, ban san sunan ta na gaskiya ba, amma sunan ma dai da' ake kiran ta dashi akwai wuya dan ban riƙe ba"

Yusuf yace "ikon Allah wahalar sunan ta kai ka kasa riƙewa"

"haba Malam Yusuf kaman baka san iyayinku na 'yan binni ba? Wasu sunayen ma karasa sunan tumakine kona taurari"

Ba ƙaramin dariya Isa ya bawa Yusuf ba.

Suna ta ɗan taɓa taɗi, Isa yace "Aff gata can ta fito"

Yusuf ya ɗaga kai ya hango ta, ba ƙaramin kwarjini take da shi ba, taku take na ƙasaita akan wani dogon takalmi, dogon wando ne a jikin ta dark blue da riga light blue me dogon hannu, ta ɗaure kanta da ɗan kwali, amma gashin ta seda ya fito ta baya, fuskarta sanye da wani ƙaton glashi, wayar tace kawai a hannun ta babu jaka se key ɗin mota.
Guri ta samu ta tsaya, yayin da Yusuf yai sauri ya ƙarasa inda take tsaye, gaban sa na ta dukan uku2, yaje gabanta ya ɗan risina yace "barka da safiya ranki ya daɗe"

Bata amsa ba, ta miƙa masa mukullin mota, yasa hannu biyu ya karɓa a hankali ta furta masa Lambar motar da zata hau, kowace mota dake parking space tana da lamba, dan haka be sha wuya gurin gano wadda take nufi ba, abun da ya ɗaure masa kai shine kaddai a haka da wannan shigar zata fita?.

Ya fito da motar, ya fito ya buɗe mata ƙofar Bayan motar, wuce shi tayi taje ta buɗe gaba ta shige ta zauna.
Ya zagayo ya buɗe shima ya zauna yana ta Addu'a, gashi besan inda za suje ba, haka yai shahada ya kunna motar Isa ya buɗe musu gate, taiwa Isa Alama da hannun ta yazo, a guje jiki na rawa Isa ya ƙaraso gefen window ɗin da take zaune ya risina

"kwatanta masa gidan Bulama" ta furta kaman wadda aka yi wa dole, Isa yace
"kina nufin Alhaji Bulama Abokin Alhaji?"
Ɗauke kai tayi tana kallon wani gurin daban, se Yanzu Isa ya tuna bata maimaita magana, ya gyara tsayuwa yayi wa Yusuf kwatancen gidan.

A hankali Yusuf yaja motar suka bar gidan, tunda suka fara tafiya babu wanda yayi wa wani magana, Yusuf ya dinga bin kwatancen gidan da Isa yayi masa, har zuwa ƙofar wani katafaren gida da suka zo ƙofar gate ɗin Yusuf ya kalle ta yace
"Nan ne ranki ya daɗe?"
Shiru tai masa ko motsawa ba tayi ba balle ta kalle shi, ɗan taɓe baki yayi, yai horn megadi ya buɗe ƙofa ya leƙo yana ganin motar ya ja da baya da sauri, ya koma ya buɗe gate ɗin gidan, gidan yayi kyau ya tsaru matuƙa sedai be kai gidan Alhaji Nasir ba.
Yusuf yaje parking space yayi parking, kafin ya sakko ya buɗe mata ta buɗe motar ta fita.
Fitowa yayi shima ko da wani abu dazata buƙata ya fito ya tsaya a bayan ta, me gadi ya ƙaraso cikin girmamawa yana gaishe ta, bata amsa ba tace "Bulama yana nan ne?"

"Eh ranki ya daɗe, Amma bana jin ya tashi"

"Ace masa gani na zo, ya tashi ko be tashi ba be dameni ba, bazan haura mintuna talatin a gidan nan ba"

Da sauri megadin yace "Angama ranki ya daɗe" nufi cikin gidan.

Ba tare da ta kalli inda Yusuf yake ba tace "biyo ni" ba musu yabi bayan ta, Wata rumfa dake harabar gidan me ɗauke da fararen kujeru ta nufa taje ta zauna akan kujera, bayan ta yusuf ya tsaya ba tare da ya zauna ba.

Me gadi ne ya fito tare da wani matashi, matashin na ganin ta ya fara murmushi ya ƙara so inda take zaune

Matashin yace "Manya maganin ƙanana, Dama yaran talaka irin mu na ganin ku?"

Ɗan taɓe baki tayi tace "Gurin Alhaji Bulama nazo, yace yana son gani na, a ce masa gani nazo"

Matashin yayi murmushi yace "Yau kuma a Alhaji Bulama yake ba Daddyn ba, WIDAD kenan, to ki shiga ciki mana ku gaisa da su Hajiya da Iman mana"

Yusuf a ransa ya maimaita "Ikon Allah wani irin suna ne wannan? Widad?

Widad tace "banzo da niyyar ganin su ba a yanzu"

"Shikenan bari ayiwa Daddy magana"

Har ze wuce ya kalli Yusuf yace "am Sorry young man bamu gaisa ba"

Ya miƙawa Yusuf hannu, Yusuf yayi murmushi ya miƙo masa hannu da nufin suyi musabiha, Amma Widad ta kalli Yusuf ta haɗe rai tace
"don't try it"
A hankali Yusuf ya janye hannun sa suka fasa gaisawar, saurayin ya girgiza kai yace "Hmm bari in kira Daddy"

Yusuf a ransa yace "wai ita wannan shikenan kowa se dai yabi abunda take so? Kowa ma wulaƙanci take masa?"

Sunan a harabar gurin, aka turo 'yar aiki da kayan drinks da fruit ta kawo musu, yadda aka ajiye kayan ko kallon su ba tayi ba.

Ba tare da ta kalli inda Yusuf yake ba tace "duk wanda yazo gurin nan ban yadda ka kula shi ba, ba ruwan ka da kowa"

Yusuf yace "angama ranki ya daɗe"

Wani babban mutum ne ya fito sanye da jallabiya fara ƙal, aƙalla zeyi sa' an mahaifin widad.

Ya ƙaraso gurin fuskarsa ɗauke da murmushi, yaja kujera ya zauna ya kalli widad yace
"daughter yau kuma cikin gidan nawa ne baza'a shiga ba?"

"Eh bazan shiga ba banyi niyya ba, yanzu ma Daddy ne yace kana nemana nazo" ta bashi amsa kai tsaye

Alhaji Bulama yace "yanzu daughter ace kina Nigeria amma ki kasa zuwa ki ganni mu gaisa, ko na miki laifi ne?"

Ɗan girgiza kai tayi tace "nafison zamana ni kaɗai ne"

Alhaji Bulama ya kalli Yusuf yace "daughter shi kuma wannan fa?"

"driver nane, ba ruwan ka da shi"

"Shikenan naji ba ruwana da shi, amma idan bodyguards kike buƙata ai za'a iya samo miki, wannan ba abunda ze iyayi miki"

Ba kunya Widad Ta kalli tsabar idon mutumin nan a gadaran ce tace "bana buƙata, bana son kowa ya raɓeni"

Alhaji Bulama yace "A'a daughter sama miki masu tsaron ki yana da mahimmanci, musamman tunda kin san amfanin hakan a tare da ke"

"Bana buƙatar kowa a tare da ni, bana buƙatar saka rayuwar kowa a hatsari, ban yadda da kowa ba dan haka bana buƙatar su"

Alhaji Bulama ya jinjina kai yace
"Amma daughter kin san likita ya hana ki wannan ɗabi'ar kaɗaice kan naki, rayuwa ba zata taɓa yuwuwa a ce kina gudun mutane ba, ya kamata ki samu kiyi aure zaki samu nutsuwa, da kuma farinciki zaki rage kaɗaicin nan"

Karon farko da Yusuf yaga dariya a fuskar ta, ba ƙaramin kyau tayi ba da tayi Dariya ta wani jinjina kai cike da rainin hankali tace

"Alhaji Bulama kenan, an gaya maka rayuwar kaɗaicin da nakeyi tana damuna ne? Karnuka na da maguna suna ɗebe min kewa sosai fiye da yadda mutane zasu yi min, tunda nasan sun baza su cutar dani ba"

Ta miƙe tsaye tsam ta kalli Alhaji Bulama ta haɗe rai kaman ba ita ta gama dariya ba tace

"Ka cire wa zuciyar ka cewar ni widad zanyi Aure, ban yadda in zauna a ƙarƙashin wani ba yana juyani yadda yake so ba, in anyi Aure ana neman Aljanna ne, ni kuma idan nayi Aure sedai Rahamar Allah ta shigar dani Aljannah, ba dan zanyi wa wanda nake tare da shi biyayya ba, na faɗa bazan zauna ƙarƙashin wani ba, babu wani farinciki da'ake a tsinta a Aure, babu komai cikin rayuwar aure se takura da matsaloli, NO MARRIAGE IN MY POLICY!!! Rayuwa ta da nake nika ɗai ta fiye min bazan gayyato wa kaina matsala ba bayan wadda nake ciki"

Ba Alhaji Bulama ba hatta Yusuf maganganun Widad sun ɗaure masa kai, ita kam wannan wace irin zuciya ce da ita haka?

Inda motar su take ta nufa, hakan yasa Yusuf bin ta da sauri ya riga ta ƙara sawa inda motar take ya buɗe mata.

Suna tafe yana lura da ita, ranta a ɓace yake sosai, haka yayi tuƙi a hankali koda suka je gida part ɗin ta ta nufa ba tare da ta kula kowa ba.

Yusuf kam rasa abunyi yayi, ita ba tace ta sallame shi ba ko A'a, ga mukullin mota bata karɓa ba.

Bayan ya kulle motar Isa ya nufoshi yana murmushi yana zuwa yace
"har kun dawo kenan?"

"Eh min dawo malam Isa"

"to yaya, fatan dai bata maka halin ba?"

Yusuf yayi murmushi yace "niba abunda tayi min, ni yanzu damuwa ta ban sani ba ko ta sallameni ba tace min komai ba, ina son tafiya gida ne"

Isa yace "kaje ina? ai zama zakayi setace ta sallame ka"

Harar Isa Yusuf yayi yace
"shikenan ni bani da Abunyi na kaita inda zan kaita meya rage banda in tafi tawa sabgar, mahaifiya ta Nason ganina dan haka bazan zauna ba"
Yana gama maganar ya nufi ƙofar shiga cikin gidan, yana jin Isa yana kiransa amma yai masa banza.

Yana shiga yayi karo da Amal ta taho da sauri zata fkta.

Tana ganin sa ta tsaya tana ajiyar zuciya, taji wani farinciki na ratsa zuciyar ta Yusuf yace "barka da rana"

"Yawwa barka ya kake ya aikin?"

"Alhamdilillah, ga key ɗin mota  nan bata karɓa ba ta tafi, ina son zan tafi gida ne inga mahaifiya ta"

Ya miƙawa Amal, be jira me zata ce ba yai waje abun sa.
Jinjina kai Amal tayi tace "lallai wannan besan wacece Widad ba, da alama shima kansa yana ɗan rawa"
Babban abunda ya bata haushi irin yadda be tsaya ko gaisawar kirki sunyi ba.

Koda Yusuf ya koma gida ya sha tambayoyi a gurin Ummansa, seda ya tabattar mata da babu wata matsala sannan hankalin ta ya kwanta.

Tunda ya shiga ɗakinsa yake saƙawa yana warwarewa, abubuwa da yawa sun bashi mamaki yana da tarin tambayoyin da besan me bashi amsar su ba, Amma kusan akwai alamar tambaya akan dukkanin iyalan gidan akwai wani ɓoyayyen abu da kowa yake ɓoyewa a ransa.

"Amma me yasa Widad ta zaɓi rayuwar kaɗaici akan rayuwa da mutane? Me yasa tayi wa Aure mummunar fahimta haka? Me yasa kowa yake biyayya ga Umarnin ta abunda take so, ko da kuwa hakan na nufin ɓacin ran mutane ne?"

Bashi da Amsar tambayoyin nan, Shi ze nemowa kansa amsoshin tambayoyin.

Widad tana kan gadon ta ta ƙurawa sama ido, Hawaye na bin gefen idon ta, Mahaifin ta yayi Sallama a ɗakinta, tana jinsa amma tayi masa shiru, ta miƙe zaune a hankali, ya ƙaraso gefen gadon ta ya zauna ya kalli idon ta yace

"daughter ya akayi ne? Meke faruwa? Abbanki ya gayamin ko gidansa baki shiga ba iyakarki harabar gidan, daughter me yasa?"

"Bana son hayaniya ne, shiyasa na tsaya kawai a harabar gidan" ta bashi Amsa

Alhaji Nasir yayi ajiyar zuciya yace

"Alhaji Bulama ya gayamin yadda kuka yi, Lovely bamu yanke shawarar batun yi miki aure ba sedan na gaji da ganin halin dake ciki, Widad zuciya ta na shiga ƙunci da irin wannan rayuwar da kike yi, kin san larura dake damunki, likita ya hana ki kaɗaicewa, idan kika cigaba a haka fa ze cigaba da taɓa ƙwaƙwalwar ki, dan Allah daughter ki amince da roƙona, kiyi Aure ina son ganin farincikin ki, ko baki yadda da kowa ba, idan dai zaki buɗe ido kiga 'ya' yanki da mijinki zakiji daɗi sosai, dan Allah Widad bani da kowa yanzu seke, se kuma Aminina Bukar Bulama, naso Inkuma samun yara bayan ke, Allah be bani ba, zanji daɗi idan naga 'ya' yanki, please Widad help your Dad, nasan bana tunanin akwai wanda kika tsayar kike so, Amma nida Bulama mun yanke shawarar zaɓa miki mijin da zakiyi Alfahari da shi, wanda ze nuna miki so ya kula dake ko bayan raina, Widad a yau idan na faɗi na mutu bayan Alhaji Bulama bana tunanin Akwai wanda ze kulamin da Rayuwar ki, sannan kinsan a haɗarin da muke daga ni har ke, please Widad ki Amincewa batun Auren nan, am sure if you got true love you will never regret been married, Akwai Soyayya da tausayi a cikin rayuwa da wanda yake son ka, na tabattar da Aure ze wanke miki dukkanin wani pain da yake ranki"

Tunda ta ƙura masa ido ko ƙyaftawa ba tayi, seda ta bari ya gama, ta miƙe tsaye ta fice ta bar masa ɗakin ba tare da tace komai ba.

Alhaji Nasir ya jinjina kai, babu alamar Nasara, Amma ya yanke wa zuciyar sa ze cigaba da lallaɓata yana bin kanta, dan babu wata mafita da ta rage masa se Amincewa da shawarar Alhaji Bulama.
A fili yace "Wannan karon ke zakiyi biyayya ga unarnina daughter, duk wannan abun inayi ne saboda ke"

Widad kam gaba ɗaya maganganun mahaifinta haushi suka bata, kaman korarriya haka ta sakko daga kan bene, ta samu corridor ta tsaya tana zancen zuci, "wai Aure, waya gaya musu akwai Aure a tsarin Rayuwar ta? Taɓɗijan inyi Aure in zauna a ƙarƙashin wani yana juya ni yadda yake so? Ko kuma a haɗa kai da shi a cutar dani, kaman yanda yake ɗabi'ar mutane ne cin amanar wanda ya yadda da su, idan har Akwai mutane masu amana da suka rage a doron ƙasa to sunyi nisa da duniyar da ni Widad nake ciki, waima waye ake cewa za'a haɗa da shi ne Aure? Idan kuma ya zamana yana ɗaya daga cikin mutanen da nake nema fa, hakan yana nufin in masa Alfarma ko in ɗaga masa ƙafa?

A fili tace

"Baze yuwu ba wallahi, ba wani Aure da zanyi, what is their in marriage apart from pains!, hurting each other!, tensions!, regrets and restriction of rights,!! No Impossible i want free life, i can't live under someone's control, i better live alone and die alone than to got married to irresponsible man of now a day's, bazanyi Aure ba, idan har Soyayya da shaƙuwa basa hana ɗan Adam ya cutar da ɗan uwan sa, to tabbas Love doesn't exist is just an imagination, love does not exist talk less of true love, So shike sa ayi Aure,  kuma yadda ce ke kawo so ban yadda da kowa ba, Daddy Bulama kayi min katsalandan bisa ga kawo wannan shawarar da ɗaya take da ƙarasa gurgunta rayuwa ta" hawaye ne ya wanke mata fuska sharkaf se ajiyar zuciya take yayin da take maganar.

Ramla da tazo wucewa ta tsaya taji surutan da Widad take yi, ta jinjina kai a ranta tace "to Aure kuma? Waye ze auri wannan Jarababbiyar? Kuma mahaukaciya? Anya Mummy ta san zancen nan kuwa?

Widad kam ji tayi zuciyar ta tana wani irin raɗaɗi, ta fito harabar gidan da sauri kanta ko ɗan kwali babu, dan gaba ɗaya ji tayi kaman tana cikin wuta dole ta fita dan ta samu sassauci,
Tana fitowa harabar gidan ta nufi inda Isa yake tace

"ina direban nan yake, yazo ya fita dani ya bar arear nan dani"

Isa ya kalleta ya kalli kayan jikin ta, mini skirt ne a jikin ta se wata riga armless, gashin kanta a baje kaman ta zare, Isa ya ɗan ƙare mata kallo, a ransa yace "Masha Allah, Allah ya yi halitta anan" yace
"Ranki ya daɗe a hakan za'a fita dake?"
Kallon da yake mata ne da tambayar da ya tsareta da shi, yasa ta ƙara fusata ba zato ba tsammani Isa yaji saukar lafiyayyen mari a fuskar sa.

Gigicewa yayi ya dafe kuncin sa yace "ranki ya daɗe ya tafi tun ɗazu, nace ya tsaya amma yace baze tsaya ba yana da uzuri"

Ƙanƙance ido tayi ta dubi Isa, a hankali tayi ƙasa sa muryar ta tace
"ɗan uban waye shi da ze saka hannu akan dukkan sharuɗai na, kuma yau da ya fara min aiki har ya fara saɓamin doka?"

Shiru Isa yayi yana sake shafa kumatunsa dan bashi da amsar da ze bata

"Wallahi sena masa wulaƙancin da babu wata halitta data taɓa yi masa, sena sauke dukkan baƙin cikin da nake ciki akansa, waye ubansa? Yana ƙasƙantacce zeyi watsi da dokokin da shi yasa hannu da kansa, Matsiyatan banza marasa Alƙawari, shiyasa wani talakan har ya mutu baze Arziki ba saboda rashin sanin mahimmancin Alƙawari da Amana, ya shirya karɓar hukuncin da ba'a taɓa masa makamancin sa ba"

(Nikam nace masu kuɗi ne kawai suka san Alƙawari da Amana? Ko kuwa Alƙawari da Amana ce tasa suka yi Arziki? Shikenan idan mutum yana aiki a ƙarƙashin wani me kuɗi se ya zama kaman Bawa? Shi besan jin daɗi ba se Bauta? Bashi da wani 'yanci na walwala da jin daɗi kenan? Tabbas da ba talaka ƙaryar me kuɗi yaji daɗin Rayuwar sa komai Arziƙin sa kuwa, Naga kowane ɗan Adam dai ajizine babu wanda baya kuskure, ke Widad ba kya kuskure ne ko kuwa? A ce mutum ya zabi Rayuwa shi kaɗai ƙwal ba mutane? Kowa be iya komai ba ciki hada mahaifinki, Gaskiya kin zafafa Aƙidojin ki, wata sabuwa kuma Widad tace "Love doesn't exist, is just an imagination talk less of getting true love" masu karatu wannan kaɗanne daga Aƙidojin Widad

TIRƘASHI!!!

Yaseen Akwai cakwakiya, Hassada, Munafunci, tsantsar Soyayya, Fuska biyu, kutsen ƙaddara me sauya rayuwar bawa ko be shirya mata ba, da sarƙaƙiyar gaske a cikin wannan littafin kar ku bari a baku labari dan ya haɗu.

Insha Allah ze cigaba da zuwar muku 1 ga watan September

Domin sharhi, gyara, ƙorafi ko makamancin haka ku tuntuɓeni akan
Wannan lambar ta what's app kawai
07063065680

Masu bina private akan in tura musu ABDUL JALAL dan Allah kumin afuwa, Abubuwa sunmin Yawa na kammala part two a document na sake shima, idan baku samu ba ku duba manhajar watpad a account ɗina
Ayshercool7724 insha Allah zaku samu dama sauran litattaafai na.

Masoya a cigaba da haƙuri dani, sakamakon harkar makaranta da wasu abubuwan da suka sani gaba Insha Allah wannan littafi ze fara zuwar muku 1 ga watan September, a what's App, da  telegram groups ɗina, da kuma Facebook a shafin mu na perfect writers Association, ko kuma YouTube channel dinmu

Ina godiya da Adduoin ku.

_*AƘIDA TA*_

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *

And now *AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Special thanks to all members of my Association
Perfect writers Association may Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will bring positive changes to our Community.

I won't forget you my fans 😍😍😍 you are always in my heart, my love to you is endless, especially those that shows me love support and follow me with prayers since my first Novel to date, i can't mentioned you all but am proud of you all 😍

HAUSAWA SUKACE KYAN ALƘAWARI CIKAWA, KAMAR YADDA YAKE KOYAR WAR ADDININ MU CIKA ALƘAWARI ABU NE ME MATUƘAR MAHIMMANCI, NAZO DOMIN CIKA MUKU ALƘAWARI, A BAYA NASAKA RAN KAMMALAWA DA MAKARANTA A AUGUST, KATSAM AKA ƊAGA JARRABAWA AKA MAIDA ITA 20 GA WATAN SATUMBA, AMMA TUNDA NI NAYI MUKU ALƘAWARIN CIGABA DA KAWO MUKU WANNAN LITTAFI A WANNAN WATA, NA SHIRYA TSAF DAN CIKA ALƘAWARIN KU 'YAN AMANA, WATTANI HUƊU KUNA SAURARE NA, INSHA ALLAH BAZAN BAKU KUNYA BA, KU SHIRYA DOMIN SALON NA DABAN NE, AKWAI TUFKA DA WARWARARA ME MATUƘAR SARƘAƘIYA A WANNAN LITTAFI DA KUKA DAƊE KUNA JIRA.
KARA ƊAYA ZAKUYI MIN, SHINE NUNAMIN JIN DAƊIN KU TA HANYAR YIMIN COMMENT TARE DA SHARE, LITTAFIN NAN KYAUTA NE DOMIN JIN DAƊIN KU MASOYA NA, AMMA A DALILIN RASHIN COMMENT ƊINKU KOMAI NA IYA CANZAWA, GA MASU MANHAJAR WATPAD KU GARZAYA KU NEMENI
@AYSHERCOOL7724
KU NEMI LITTAFIN A FACEBOOK A
GROUP ƊIN PERFECT WRITERS ASSOCIATION
ƘOFA TA A BUƊE TAKE DOMIN GYARA SHARHI KOKUMA SHAWARA
AYSHERCOOL
07063065680

YADDA NA FARA LAFIYA ALLAH YASA IN KAMMALA LAFIYA

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

BISMILLAHIRAHMANIRRAHIM

ELEGANT ONLINE WRITER'S



                         *PART1*
                      
                                  _Page 4_







Babu alamar sassauci fuskar Widad, yanayin fuskarta ze tabattar maka da gaske har cikin zuciyar ta zata aikata abunda ta faɗa, ta juya ta koma cikin gidan da hanzari.

Jinjina kai Isa ya dinga yi yana kuma sake shafa kumatunsa yadda yske masa raɗaɗi, tare da tausayawa wulaƙancin da Yusuf ze fuskanta.

Ramla kam cikin sassarfa ta nufi ɗakin mahaifiyar ta, tun daga waje take kiran "Mummy"

Hajiya Halima tace "Ramla wannan wane irin kira ne haka? Ke kam bakya girma"

Ramla ta ƙarasa kusa da mahaifiyar ta ta zauna tace "wai nikam nace me akayiwa 'yar gwal ne? Naga kaman ciwon nata na ƙoƙarin tashi fa? Kuma ga dukkanin alamu yau ta kwaɓe mata itada uban tane"

Ɗan tsaki Mummy tayi tace
"sakani yake cikin sha' aninsa shida 'yar sa ne? Ai sedai inga suna lamauran su ta yaya zan san meya sameta?"

Ramla ta sake gyara zama "hmm kinsan dai halin ciwon ta, a corridor ɗin ƙasa na haɗu da ita, tana ta surutai, wai Daddy Aure zeyi mata, se safa da marwa take tana zufa"

Zaro ido Mummy tayi tace "Aure kuma? Wane irin Aure ana zaman lafiya? Waye ze Auri mahaukaciya mara tarbiyya kamar wannan Yarinyar? Shi mijin da haukan zeji ko kuma da rashin tarbiyya?"

Ramla tace "waya sani musu?, sedai ki jiyo mana kanun Labaran muma ki fesa mana, Amma ina tunanin wanda ze kwashi wannan Mahaukaciyar"

"To nidai a iya sanina bata yadda da mutane ma, to ta yaya ta samo wanda ze Aure ta?"

Ramlah tace "Ai samun miji ba wuya ze mata ba, ko dan wannan haɗaɗiyar Daular, dan haka ko'a turu take dan hauka, za'a iya samun me sonta yace ze aureta a haka"

Mummy tace "hakane, Amma ya zama dole musan waye ze Aureta, dole in gano"
Haka Suka ci gaba da tattauna wa akan lamarin.

Yusuf kam kashe wayoyin sa yayi ya shiga sabgoginsa, duk yadda Isa yaso kiran Yusuf a waya ya gaya masa Saƙon Widad abu ya gagara wayar sa taƙi shiga, ƙarshe se haƙura Isa yayi.

Widad kam baranda ta samu ta kwanta, akan tiles ga sanyin tiles na ratsa ta amma sam bata ji, tayi ruf da ciki tana jin yadda zuciyar ta take mata raɗaɗi, kamar ta tsaga ƙirjinta ta fito, Babban Abunda ya ƙara bata mamaki shine yadda mahaifin nata be biyo sahunta ba balle ya rarrashe ta kaman yadda yake yi abaya, shima kamar yayi fushi da ita karon farko ya barta cikin damuwa, lallai wannan karon mahaifin nata dagaske yake.

Washegari Yusuf ba shida Niyyar zuwa gidan su Widad Sam, da ya tashi da safe ma shirin tafiya Office yayi abun sa, ya shirya ya fito Umman sa ta kalle shi tace
"Ya haka kuma? Yau ina zakane?"

Murmushi yayi yace "Yau Office zanje Umma"

"Kacemin kuma, an turaka aiki gidan Alhaji Nasir Daula, yanzu kuma kace min zaka gurin aiki ya haka?"

Yusuf yace "hakane Umma, an turani aiki gidan Alhaji Nasir Daula, Amma dole zan dinga leƙawa Office, ina documenting findings ɗina sannan indinga presenting sakamakon bincike na"

"shikenan a sauka lafiya, Allah ya tsare ya kiyaye hanya"

"Allah yasa Umma, dan Allah yau ki mana dambu kinji Umma na"

Umma tace "banyi Alƙawari ba, ka bari ranar da kake nan se kayi"

Noƙe kafaɗa Yusuf yayi yace "dan Allah Umma, ni gaskiya idan ba dambu kika yi yau ba bana cin Abincin"

"kar kaci ɗin, ai cikin ka ba nawa ba"

Haka yaita zolayar umman nasa sannan yai mata sallama ya tafi.

Da yaje Office ɗin ma Ayyuka sun ɗanyi masa Yawa, ya duƙufa sosai yana ta shigar da ayyukan sa cikin system.

Sallamar da'akayi a office ɗin ne ya sashi ɗagowa yaga me Sallamar, kamar yadda ya zata sakine ce ta shigo.

Kallo ɗaya yayi mata, ya Amsa sallamar ya maida kansa ya cigaba da danna system ɗin shi.
Yauma cikin baƙaƙen suit Sakina take, amma skirt ga ƙaramin hijjabi da ta saka, gaba ɗaya kayan sun bayyanar da surar jikin ta.
Kujera ta ja ta zauna tana facing ɗin sa.

"Yusuf sannu da Aiki"
Ba tare da ya kalle ta ba yace "lafiya kalau Alhamdilillah"

"kwana biyu baka shigowa Aiki, lafiya dai ko?"

Ɗan ɗagowa yayi yace "Eh an bani wani Assignment ne"

Cikin iyayi da lumshe ido tace "to Allah yaba da sa'a"

Ya amsa da "Ameen"

"Can i offer you something to eat?"

Ba tare da yace komai ba ya girgiza mata kai, Alamar A'a.

Miƙewa tayi ta zagayo inda yake tace
"ko Akwai abunda zan taya ka ne?"

Ɗagowa yayi ya kalleta a hankali yace "dan Allah ki fitar min daga Office inada Ayyuka da yawa kina takuramin fa"

A Shagwaɓe tace "Yusuf meyasa kake son yi mun wulaƙanci ne?"

"ba wulaƙanci bane, gaskiya ce, Aikine ya kawo ni gurin nan ki barni inyi aikina mana"

"Amma Yusuf meyasa zaka maida Soyayya ƙiyayya, tunda na nuna ina sonka kake wulaƙantani haba Yusuf"

"Sakina niba wulaƙantaki nake ba, yanzu lokacin aiki nane, dan Allah ki tashi ki tafi, bearable in shiga lokacin aiki ba"

"Yusuf" ta kira sunansa, ɗaga mata Hannu yayi ya dakatar da ita tare da faɗin

"Sakina dan Allah ki barmin office, kalli shigar jikin ki, kuma kinzo kin sani gaba, dan Allah ki tafi"

Suna cikin Jayayyar ne Abbas ya shigo, Sakina ta miƙe ta bar office ɗin a fusace.

Abbas ya kalli Yusuf yace

"Anya Sakina bata fara kama zuciyar ka ba Yusuf?"

Ɗan girgiza kai Yusuf yayi yace

"Abbas kenan anyi na farko, baza'ayi na biyu dani ba, bana son yi mata wulaƙanci ne amma taƙi ganewa, Soyayya kam sedai inga anayi, bazan sake ba, in Allah yayi zanyi Aure shikenan, Amma na gama Soyayya"

Abbas ya jinjina kai yace "shikenan Allah ya kyauta, na kiraka tun jiya bata shiga ya labarin mutuniyar ne?"

Shafa Aljihun sa Yusuf yayi, sannan ya jingina da jikin kujera yace

"Aini tun jiya dana dawo na kashe waya ta, bana son a dameni ne sam"

Abbas yace "kayi mata aikine jiya?"

"Eh munfi ta, na kaita wani gida, inaga gidan ɗan uwan mahaifinta ne ko makamancin haka"

Abbas yace "babu dai wata matsala ko?"

"Babu wata matsala, ba tayi min dai wulaƙanci ba, Amma fa naga izza wadda ban taɓa ganin makamanciyarta ba, dan cikin isa da gadara take wa kowa magana, bata shakkar kowa bata girmama kowa, kai ko Dariya banga tayi ba Jiyan nan, magana ma aiki ce a gurin ta"

Abbas yace "taɓ, aishi yasa nace bazan iya ba, saboda na samu labarin yarinyar, shikenan ka dai kula sosai akan abunda muke son ganowa"

Jinjina kai Yusuf yayi, tare da cewa "Insha Allah, komai ze tafi dai dai"

***********

Ƙarfe goma na safe Yusuf ya bar gurin aikin, ya koma gida seda yayi wa Umman sa cefane, ya kai mata markaɗe ya kama mata Ayyukan gida sannan ya sauya kaya, ya nufi gidan Alhaji Nasir.

Yau da yaje ya tarar da Isa mai gadi dashi da wani, Suka gaisa, Isa yayi farat yace
"Yusuf ga Nura shine direban megidan nan, lokacin da kazo yaje garin su ne, amma gashi ya dawo, shike kai Alhaji unguwa"

Yusuf ya miƙa wa Nura hannu suka gaisa.
Isa ya nisa yace "Yusuf kayi gangancin tafiya jiya, nan ta fito a birkice jiya kaman mara hankali tazo nan tana neman ka wai ka fita da ita, baka ga shigar jikin ta ba, daga tambayar ta a haka zaka fita da ita ta mareni, wallahi har yanzu ko ƙuda bana so ya taɓa fuskata dan ba ƙaramin shiga marin nan yayi min ba"

Zaro ido Yusuf yayi yace "mari kuma?"

"Wallahi Yusuf mari na tayi"

Nura yace "aiba abun mamaki bane, dama wani lokacin haka take birkice wa, kun san abunka dame rangwamen Ƙwaƙwalwa, aini tunda naji zata dawo naji aikin gidan nan ya fita daga kaina, Allah ya temakeni aka samo mata nata direban"

Kallon su Yusuf yake dan be fuskanci inda zancen nasu ya dosa ba.

Isa yayi ƙasa da muryar sa yacewa Yusuf
"wani lokacin birkicewa take kaman hauka hauka, shiyasa kaga bata son mutane suje inda take, tana da larurar ƙwaƙwalwa shiyasa....

Yusuf ya katse shi ta hanyar cewa
"Shikenan shikenan, Allah ya bata lafiya be kamata a dinga yayatawa ba, Addu'a ya dace ayi mata, faɗar bashi da Amfani sam"

Widad ce ta fito ƙaton falon gidan, ta tarar da matar gidan da yaran ta Suna ta ciye ciye suna hira, tana fitowa suka yi tsit suka shiga taitayin su, suka dena hirar.

Ta dube su ɗaya bayan ɗaya, kamar me nazari, sannan ta yatsuna fuska tace

"Amal jeki kira min wancan matsiyacin talakan direban, yau in fara gwada masa wacece ni"

Sam Amal ba taji daɗin kalaman da Widad tayi amfani da su akan Yusuf ba, Amma babu yadda ta iya ta miƙe ta tafi kiran sa.

Tunda Amal ta fito ta hangi Yusuf yana hira da su Nura, yayi kyau sosai komai nasa gwanin sha'awa, kamar ba direba ba.

Amal Ta ƙaraso inda suke bata kula su Isa dake ƙoƙarin gaishe ta ba, ta dubi Yusuf tace

"barka da rana Yusuf"

Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace
"Yawwa barka, ina uwa ɗakina?"

Bata jin daɗin yadda koda yaushe yake taƙaita magana da ita, Amma ta basar tace

"itace tace in kira ka ma"

Yusuf ya miƙe yace "shikenan muje"

Yabi bayan Amal, tsananin kwarjinin Yusuf ne yasa Amal sam ta kasa kuma ce masa komai, se ƙamshin turare yake fitarwa me daɗin ƙamshi kaman ba direba ba.

A falon suka tarar da hakimar ta harɗe da alewa me tsinke a bakin ta, tana danna waya tareda kaɗa ƙafafuwan ta.
Kamar kullum yanzu ma kanta babu ɗan kwali, ta baje gashin ta, Amma yau anyi sa'a skirt ne dogo a jikin ta da wata 'yar ƙaramar riga shara shara.
Tunda Yusuf ya shigo ɗakin ƙamshin turaren sa ya daki hancin ta taji ya saukar mata da wata muguwar kasala, a duk lokacin da Yusuf zezo gidan nan taji wannan ƙamshin turaren a jikin sa se kasala ta saukar mata.

Kallo ɗaya Yusuf yayi mata yaji ƙirjin sa ya buga da ƙarfi, da sauri ya ɗauke idon sa daga kanta, Sam fuskar ta babu alamar afuwa.

Ya kalli matar gidan yace
"barka da yamma Hajiya"

"Yawwa barka sannu ya aikin?"

"Alhamdilillah"
Ya juya ga Widad yace "sannu da hutawa ranki ya daɗe"

Dama be zaci zata amsa ba, dan haka be kuma cewa komai ba se sunkuyar da kansa ƙasa da yayi.

Ya shafe mintuna Arba'in a durƙushe a gaban ta ba tare da tace komai ba, shi kuma ko kansa be ɗaga ba.

Amal ji take tamkar ita ce a durƙushe a gurin, gaba ɗaya taji kaman ta cewa Yusuf ya tashi yayi tafiyar sa.

Ba zato ba tsammani ya tsinkayi maganar ta

"Waye ya baka iznin tafiya jiya?"

"ba kowa Ranki ya daɗe"

Seda ta kuma jan wasu mintunan sannan tace
"meyasa ka tafi?"

Ba tare da ya ɗago kansa ba yace

"na zata na gama aikina na jiyane shiyasa, Amma hakan ba zata sake faruwa ba Insha Allah, kiyi haƙu....

Cikin tsawa tace
"Shut up, what the hell are you trying to say? Do you sign my conditions based on Assumption? Don't you read what is in that paper? Why are you trying to applogise? Talaka baze canza hali ba, baku da Alƙawari baku san ƙa'idar Aiki ba, se an jima ku buɗe baki kuna zagin shugabanni da masu kuɗi, waye kai da zaka karyamin doka? Me kake taƙama dashi da zaka nemi ka raina min hankali? Ɗan uban waye kai? Ko ban gaya maka lokacin aiki nawane ba? Har da zaka fara da rainamin hankali"

Tunda Widad ta fara zazzaga rashin mutuncin ta Yusuf be ɗaga kai ba, dukda yadda zuciyar sa ke harbawa jijiyoyin kansa suka miƙe saboda ɓacin rai, Amma ya dake.

Amal kaman ta ɗora hannu akai tayi ihu, ji take tamkar ita Widad ke ciwa mutunci, ita kuwa matar gidan da Ramlah ko a jikin su dan babu wanda Widad ta bari a rashin mutunci.

"kasan tsanani baƙin cikin da na shiga zama na a gidan nan bayan an ɓata min rai, daka nan ka fita dani da ban shiga damuwar dana shiga ba, tun jiya nake fama da damuwa saboda sakacinka, nayi kwanan baƙin ciki da ɓacin rai, this is my last warning to you, idan makamancin haka ya kuma faruwa, sena nuna maka wace ce Widad"

Risinawa ya kuma yi da kai

"zan kiyaye ba zana kuma ba insha Allah"

Jefo masa key tayi fuskar sa tare da faɗin
"Car Number 8, to bulama's residence"

Yaji zafin yadda ta jefa masa key a fuska, da maganganu marasa daɗi da tayi masa, amma yasa hannu ya ɗauka, kaman wanda ƙwai ya fashewa a ciki ya nufi hanyar fita.

Fakar idon Widad Amal tayi ta biyo bayan Yusuf, wajen ƙofar fita ta cin masa, yana ta sauri fuskarsa babu Annuri, Amal ta kira sunan sa, dan tsayawa yayi ya waigo yana kallon ta

"Dan Allah kayi haƙuri da abunda Widad tayi maka, haka halin ta yake muma duk haƙuri muke da ita, dan Allah kayi hakuri"

Ga mamakin ta se taga murmushi akan fuskarsa yace

"aini banji haushi ba, tabbas laifi nane da banbi komai a ƙa'ida ba, bayan nasan hakan ya saɓawa Yarjejeniyar dana sakawa hannu, kuma nasan yana daga AƘIDAR uwa ɗakina girmama Alƙawari, ya kamata in nemi Afuwa ne ba jin haushi ba"

Ɗan zare ido Amal tayi "yanzu duk abunda tayi maka kana nufin ba kaji haushin hakan ba?"

Jinjina mata kai yayi alamar eh tareda faɗin,

"bari in hanzarta in fito da motar karta fito ta sameni anan ranta ya kuma ɓaci" yayi gaba abun sa yayin da shi kaɗai yasan me yake ji a ransa.

Yaje ya fito da motar da ce masa, ya buɗe ya shiga ya zauna ya kifa kansa akan sitiyari, tabbas badan duk cikin aikin sa yake wannan abun ba to da ko Gidan su Widad gold ake sarrafawa baze kuma aiki a gidan ba.

Jin ƙamshin turaren ta yasa shi saurin ɗagowa, ta buɗe gaban motar ta zauna, tace "jeka falo inda na zauna ka ɗakko min wayata"

Ikon Allah wayar ma bazata fito da ita ba seya ɗakko mata? Bece komai ba ya fita daga motar ya koma cikin gidan, yana zuwa ya tarar falon ba kowa wayar tana kan center table, ya ɗakko ya fito ya kawo mata.

Tasa hannu ta karɓa ba tare da ta kalle shi ba tace "A ina kaga wayar"

"Akan center table"

Murmushin gefen baki tayi tace "let's go"

Kamar yadda tace gidan Bulama ya kai ta, ya samu guri yayi parking ya fito ya buɗe mata ƙofa ta fito, ƙafarta sanye da takalmi me tsini sosai shigar nan tata baka ce musulma ce ba, kayan sun kamata tsam a jikin ta a hankali ta furta "do not accept any gift from anyone"
Gyaɗa mata kai yayi yace "Insha Allah"
"Follow me"

Haka yabi bayan ta, cikin hanzari take tafiyar yau.

Yau kai tsaye bata nemi iso ba cikin gidan ta nufa, Yusuf na bin bayan ta.
A babban falon dake gidan suka ga wata budurwa da wannan matashin da suka tarar jiya, da wata babbar mace da alama itace matar gidan.

Maimakon Widad tayi Sallama se tace "Hi how are you doing guys?"

Matar tace "Widad dama kina garin nan amma ko ganin ki ba'ayi"

Budurwar tace "Wallahi Mum Ramadan yace tazo jiya amma taƙi shigowa" Yusuf dai bece komai ba saboda jan kunnen da tayi masa jiya.

Ramadan ya kalli Widad yace "you look so Cute in this outfit Dear"

Ba ta amsa musu maganganun su ba tace "Is Daddy Around?"

Yusuf ya kalli kayan dake jikin Widad, da kuma abunda Ramadan yace kawai ya girgiza kai

Ramadan yace "yeah yana nan"

Ƙoƙarin hawa bene Widad take yi, budurwar tace

"hey Baby who is this gentleman with you?"

Aiko tsaya ba tayi ba balle bada amsa, ta haye saman benen da sauri, Yusuf bashi da zaɓin daya fi yabi bayan ta.

Wata ƙatuwar ƙofa ta buɗe, ta kutsa kai Yusuf yabi bayan ta, shima wani haɗaɗɗen falo ne me girman gaske, sanyi Ac ke rasa ko ina na ɗakin.

Alhaji Bulama ne ke zaune akan ɗaya daga cikin kujerun falon, yana shan tea tareda dannan system, Yusuf ne yayi sallama, Alhaji Bulama ya ɗago ya kalle su.

Murmushi yayi ya amsa sallamar Yusuf, yana ƙarewa Widad kallo, guri ta nema ta zauna tana fuskantar Bulama.

Bulama yace "Daughter wai shi wannan duk inda zaki se tare da shine? Ina direba ne kawai? Kodai Allah ya karɓi Addu'armu kin fara sakin jiki da mutane?"

Haɗe rai tayi tace "my policies remain constant, babu abunda ya canza, babu ruwan ka da dalilin da yasa duk inda zani yake bina"

Alhaji Bulama ya murmusa yace "shikenan Allah ya baki haƙuri"

Ya kalli Yusuf yace "Sannu ɗan Samari, daughter ɗin tamu seka na haƙuri, muma lallaɓata muke"

Da ido ta kalli Yusuf, dan haka Yusuf bece komai ba se ɗan murmusawa da yayi.

Alhaji Bulama ya maida kallon sa ga Widad yace "ina jinki?"

"Meyasa ka turawa Daddy na ra'ayin ayimin Aure?"

Ɗan girgiza kai Bulama yayi tareda murmushi "yaro yaro ne, Widad Aure shine ya dace dake, domin shine ze gusar miki da wannan larurar ki zama kaman sauran mutane"

"na taɓa ce maka ina son Aure ne? Ko kuma akwai shi a cikin tsarin Rayuwa ta?"

"look daughter, Aure shi ze gusar miki da dukkanin wannan halin da kike ciki, babu yadda za'ayi lafiyayyen mutum ya rayu ba tare da mutane a cikin Rayuwar sa ba, shi yasa muka yanke shawarar Aurar dake"

"ka dai yanke shawara sannan ka cusawa Daddy na ra'ayin hakan, ace har Daddy yamin laifi sannan ya fita harka ta dan naƙi yadda da batun Auren nan, duk kai ka jamin, sannan nida ban yadda da soyayya ba balle inyi ta har in samu mijin Aure, wazaku aura min?"

Gyara Zama Bulama yayi yace
"Fuhad mana first born ɗina, kun dace sosai, ze soki tsakani da Allah ya zauna dake, tunda ke 'yar uwassa ce"

Shiru tayi ta kalli Bulama sannan tace "what the fucking shit are you talking about? meye wani ze soni tsakani da Allah? Let me tell you something, i don't believe in Love talk less of true love, Love is just an imagination full of bull shits and stupidity, so ke sa ayi aure ko? To ban yadda yayi existing ba, dan haka ka gaggauta warware wannan maganar, dan ko aure zanyi bazan auri namiji bahaushe ba, you people that are not romantic at all, babu abunda kuka iya banda iko da ɗaukar matayen ku tamkar bayinku, baku damu da halin da zasu shiga ba idan har taku buƙatar zata biya, baku iya komai ba se masifa da hantara, don't you see how women are complaining about you? How Hausa women's are suffering because of your poor marital life? Women's are always complaining about marriage issues, this is type of life you want me to do? Do you think I can live with someone that will be shouting at me?"

Shiru Bulama yayi yana kallon ta, Ta gyara zama ta kalli cikin idon Bulama tace
" idan baso kuke ku ƙara tunzura haukan nawa ba kaman yadda kuke iƙrari ba, ya kamata ku ƙyaleni da maganar nan"

Numfasawa Bulama yayi yace "Amma kin san mahaifinki ma bahaushe ne, kike wannan maganganun akan mazan hausawa"

"da nace ban dashi a ciki ne? Shima badan yayi rayuwar Turai ba he will have the same negative habits on his wife, it seems it is in your genes, Alhaji Bulama daga yarin tata sanina da kai mata nawa ka aura bakwa tare yanzu? Go back to your senses Sir, Am not ready to ruin mad, i don't have interest of getting marriage, i don't know maybe later, but I can't married a man from hausa people, they don't value their wives "

Ba Bulama ba, Yusuf kansa yaji haushin cin mutuncin da Widad tayi wa ƙabilar Hausawa, duk lalacewar Al'umma akwai mutanen kirki ai, Amma ba shida ta cewa, tunda shi ɗan karere ne.

Ta miƙe tsaye tayi gaba abun ta, Yusuf ya rufa mata Baya, yauma har suka je gida ba wanda ya kula wani, sedai da suka koma gidan, a mota ta bar jakarta da wayarta, dole Yusuf ya ɗauka ya bita da su ba dan yana so ba, dan sam baya son shiga cikin gidan, ba ƙaramin tsarguwa yake da irin kallon da mutan gidan ke masa yake ba.

Yanzu kam ba 'a hankali take tafiya ba cikin gaggawa take tafiya, kaman tana son tayi wani abune, ta falon da zata bi ta wuce ta tarar da Mahaifinta a zaune da shi da matarsa, ko kallon su batayi ba tasa kai zata wuce.

"Widad" Mahaifinta ya kira sunan ta ba tare da juyo ba ta tsaya cak, be damu ba ya ɗora da cewa
"Munyi waya da Bulama ya gayamin abunda kika je kika ce masa, ki sani wannan karon dole kibi abunda nake so, bani zan biki ba, am doing all this for your benefit, in the next two Months insha Allah Fahad zezo ƙasar nan, ina son ayi Auren ku kafin ya koma"
Cigaba tayi da tafiyar ta ba tare da cewa Mahaifinta komai ba. Yusuf dake tsaye yana jinsu ya ƙarasa ya gaida mahaifin Widad da matarsa Hajiya Halima.
Ya amsa masa cikin, yayin da Hajiya Halima ta Amsa masa a ciki.

Yusuf ya miƙa wa Mahaifin Widad jakar ta da keys ɗin motar ta, yayi musu Sallama ya fice.

"Yaya Yusuf" yaji an kira sunan sa, tsayawa yayi ya waigo, Amal ce take tahowa da sauri hada ɗan haɗawa da gudu.

"Sannu ashe kun dawo?"
"Eh mun dawo, akwai wani abu ne?"

Ɗan sosa kai tayi tace "dan Allah in babu damuwa so nake ka raka ni Shopping"
"Shopping kuma? Niɗin?"
"Eh amma idan ban takura maka ba"
"ina batun takura ni da nake muku aiki, idan kin shirya kimin magana"
Murmushi tayi tace "nagode sosai Yaya Yusuf"
Shima murmushi ya mayar mata yai gaba abun sa.

(WASA FARIN GIRKI)

Share please 🙏 🙏 🙏

Comment nake so ba sticker ba ko kuma thanks ba, inda suka fi Comment su zasu dinga fara samun posting
Domin gyara, sharhi, kokuma ƙorafi a tuntube ni akan wannan lambar
07063065680
Watpad Ayshercool7724

_*AƘIDA TA*_

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                            PART1
                                  Page 5

Yusuf ya fita yaje yai alwala yai salla saboda lokacin salla yayi.

Widad kam tana zuwa ɗakin ta ta jefar da Jakarta da wayar ta akan gado ta fara safa da marwa a ɗakin ta

"Bulama ina ganin girman ka, ina maka kallon uba amma kana ƙoƙarin ƙetare gona da iri, kana ƙoƙarin tsallake iyakokinka, a tunanin ka yin Aure ze sa in canza ra'ayina? Daddy kunyi kuskure daga kai har Bulama, kuma bazan taɓa bari wannan kuskuren naku yayi tasiri a kaina ba, dole inyi wani abu" haka ta cigaba da surutai ita kaɗai.

Hajiya Halima ta kalli maigidan ta tace "Nikam wai Alhaji dagaske Widad zakayi wa Aure ko kuma yaya? Na kasa gane kan lamarin"

Ɗan shiru yayi sannan yace "Eh hakane, Bulama ya bani shawarar akan cewa muyi mata Aure hakan ne kawai zesa ta canza wannan halin nata, Amma yarinyar nan kin san halin ta da kafiya da taurin kai, ta tirje tace sam bata san zancen ba, Amma a wannan karon bazan canza ra'ayi ba, ina son inga ta dawo da walwalarta, wannan karon dole tayi biyayya ga umarni na"

"Amma Alhaji baka ganin yin hakan tamkar ze ƙara tunzura rashin lafiyar ta ne, zaka ƙara sawa rashin lafiyar ta ya tsanan ta, ko ka manta sharuɗan da likitoci suka gindaya ne akanta?"

Alhaji Nasir Ya numfasa sannan yace

"Shima zaman ta a hakan bakomai ze ƙara mata ba face cigaba da dawwama a cikin damuwa da rashin walwala, akwai buƙatar ko bayan raina Widad ya zama na tana da kafaɗar da zata tada kai, ya zamana tana da wanda ze kula da rayuwar ta"

"Amma Alhaji wa zaku bawa Auren ta? ina fatan wanda zaku bawa yasan yanayin larurar ta? Tunda kaga ba shiga mutane take ba balle a ce tana da wanda take so, kar a bawa wanda besan ya take ba abu yazo ya ɓaci"

Alhaji Nasir yace "Ai ba wani bane za'a aura matan, fahad ɗin Bulama ne, itace dai batayi wayon saninshi sosai ba, rabon da su haɗu tun tana yarinya ƙarama, Amma shi ya santa kuma nasan baze bamu kunya ba Insha Allah, tunda itama tamkar ƙanwa take a gurin sa"

Jinjina kai kawai tayi ba tare da ta kuma cewa komai ba.

Wajejen la'asar Amal ta shiryo cikin wata irin doguwar riga wadda ta kama jikin ta matuƙa, se zuba ƙamshin turare take wanda turaren har hawa ka yake yi saboda ƙarfin sa ta hau kan wani takalmi me uban tsini, duwatsun jikin rigarta se ƙyalli suke suna rawa.

Cikin iyayi ta ƙarasa inda Yusuf yake zaune da su Nura da sauran ma'aikatan gidan tace "Yaya Yusuf mu tafi ko na shirya"
Ba musu Yusuf ya miƙe yayi wa su Isa sallama.

Ya karɓi mukullin Motar Amal, suka shiga mota suka fice.

Yusuf na barin gurin Murtala me bawa shukoki ruwa yace
"wai kunga abunda na gani ko kuwa?"

Nura yace "mun gani, kai kaga wata irin kwarkwasa da take masa? , anya yarinyar nan Amal ba san shi take ba? Kaga wani iyayi da take yi tana fari da idi"

Murtala yace "Amma kuwa da ta faɗo, duk zuƙa zuƙan Samarin dake zuwa gurin ta? duk iya yin da wulaƙancin nata ta ƙare a direba, wallahi da tayi faɗuwar baƙar tasa"

Isa yace "to ai gara Amal ɗin akan yayar ta Ramla, kun san agola musamman in aka samu guri akwai iskanci, yadda suke hura hanci suna Wulaƙanta mutane kai kace gidan ubansu ne, Amma fa duk da haka gara nasu lafiya ne akan 'yar masu gida wai wa yaga Azaba, idan bata ga dama ba fuskarta idan ka kalla seka yi fitsari a wando, saboda sam bata da rangwame, Azababbiyar Yarinya idonta fiƙi fiƙi kamar me maye"

Nura yace "wallahi ko san haɗa hanya da yarinyar nan bana yi, nagode Allah da yasa ba ita nake tuƙawa ba baban ta nake tuƙawa, ni nayi mamaki ma yadda Yusuf ɗin nan har yanzu basu samu saɓani taci mutuncin sa ba, dan naga wani jin kan sa yake shima, musamman idan yana jan manyan motocin nan se kace na gadon ubansa, kamar har mantawa yake direba ne shi"

Isa ya gyara zama ya waiga sannan ya ƙara ƙasa da muryar sa yace

"ku nifa ban gama yadda da Yusuf ɗin nan ba, kuna ganin sa wani haɗaɗɗe da shi, kullum tsaf tsaf da shi, babu alamar wahala a tare da shi, ga jan aji duk yafi mu kyan gani sannan ace ya ƙare a direba anya babu lauje cikin naɗi a wannan harkar kuwa?"

Murtalah yace "Nima nayi wannan tunanin, amma ya zamu san gaskiyar lamarin? Dan ya fara bani haushi wallahi, yadda megidan nan ya fara wani girmama shi wai yana da sunan yayan sa, har wani Yaya na yake ce masa shi kuma yana washe baki yana sunkuyar da kai, damabidan mutum yavfiye sunkuyar da kai munafuki ne"

Isa yace "ku ƙyale shi zan bugi cikin sani inji ko zamu samu wani bayanin muji, ai duniya seda labari, Amma ina tunanin ta yadda za'ayi kamar wannan da beyi kama da wanda yake cikin wahala ba yazo yana aikin direba"

Yusuf ya ƙudurcewa ransa ze ɗan dinga sakarwa Amal, domin samun sanin wasu abubuwa da suka shige masa duhu game da yanayin tsarin Rayuwar mutanen gidan. Suna tafiya a hanya Amal tace

"Yusuf dan Allah ka dinga haƙuri da abunda Widad take maka, sam abunda tayi maka ɗazu banji daɗi ba wallahi haka take bata san darajar ɗan Adam ba mussman talaka, bata da mutunci, mu kanmu haƙuri kawai muke da ita sam bama jin daɗin zama da ita, shiyasa babu wanda yayi farinciki da dawowarta"

Yusuf da sauri yace "A'a uwa ɗakina ce fa ranki ya daɗe, ya zaki ce bata da mutunci a gabana? ai bazan ji daɗi ba gaskiya banji daɗin yadda kika aibata ta ba"

Kallon Yusuf tayi galala cike da mamaki tace "kana nufin baka ji haushin abunda tayi maka bane? Ai ba ƙarya nayi mata ba, da tana da mutunci da bata muzanta maka ba, harta jefe ka da key a fuska ba"

Yusuf yayi murmushi yace "yana da kyau mu dinga girmama doka kafin muyi ƙorafin anci zarafin mu, ko ba'ayi mana adalci ba, da hannu na na saka hannu akan dokokin ta kafin in fara mata aiki, na saka hannu na amince da zanbi sharuɗan data gindaya min, dan haka tunda ni na saɓa abunda na sakawa hannu, komai tayi min be kamata inji haushi ba, ko kuma ince bata da kirki ba, idan nayi haka banyi wa kaina adalci ba"

Amal tayi ajiyar zuciya tace "indai wannan ce kai da kanka zaka dawo daga rakiyar ta saboda wulaƙancin ta, dan wataran seta maka abunda zesa ka tsaneta tamkar mutuwar ka, tun bamu kai haka ba mahaifiyar mu ta auri mahaifin ta muke zaune tare, Amma bamu da daraja ko ƙima a idon ta, kai bamu ba har mahaifiyar mu bata ɗagawa ƙafa, Alhaji Bulama ne ya bada shawarar a bar ƙasar nan da ita, shine ma muka samu muka huta na wasu shekaru kafin ta dawo, se a dinga fakewa da bata da lafiya, tana taka mutane tana nuna isa da Izza"

Yusuf yace "bata da lafiya kuma? Kamar ya bata da lafiya, Meke damun ta?"

Ɗan taɓe baki Amal tayi tace "wai bata da lafiyar ƙwaƙwalwa, ko da yake me lafiyar ƙwaƙwalwa baze abunda take ba, wannan dukiyar ta mahaifin ta, da ita take taƙama da ita take wulaƙanta mutane, ta yaga duk wanda yayi mata abunda yake saɓanin raa'yin ta, aikin banza, dukiyar da'ake farautar ranta akanta, Amma take da damar Wulaƙanta mutane saboda ita"

Da sauri Yusuf yace "kamar ya farautar rai? Ranwa ake farauta, saboda dukiya?"

"Ran Widad ɗin mana, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta bar ƙasar nan fa, bayan larurar Ƙwaƙwalwa da take dashi ana farautar ranta ne, tunda maman ta ta rasu take fama da larurar ƙwaƙwalwa, kuma a kazo ana nema a kashe ta, abundai gashi nan, Amma kodan wulaƙanta mutane da take dole wani yai ƙudurin kashe ta ya huce takaicinsa, bayan wulaƙancin da take wa mutane, har ɗaure mutane take sa ayi"

Jinjina kai Yusuf yayi yana kuma nazarin maganganun Amal, baya so ya cika ta da tambayoyi, karta fuskanci wani abu dan haka yayi shiru yana ɗan satar kallon Amal yana tunani a ransa.

Yusuf ya kai Amal wani katafaren mall kaman yadda ta buƙata ta dinga ɗibar kaya, sannan tace Yusuf ya ɗauki abunda ya keso.
"A'a nagode amma ni bana buƙatar komai"
Amal tace "haba Yusuf dan Allah ka ɗauka, karka ji komai"
Fafur Yusuf yaƙi yadda ya ɗau komai se haƙura tayi.

Bayan sun dawo gida tace dan Allah ya taya ta ɗaukar kayan da ta siyo, babu musu ya ɗau kayan yabi bayan ta kamar yadda suke da Widad, Sedai tun a babban falon ƙasa suka ci karo da hakimar ƙafar ta ɗaya kan ɗaya tana shan tea, gefen ta kuma tana bawa magenta madara, bata kula su ba su kayi gaba za su wuce, muryar ta suka jiyo tace

"Stop there" ta faɗa kai tsaye cikin bada umarni, gaba ɗaya suka tsaya suna jiran me za tace.

Se da ta ja wasu seconds sannan tace

"Amal yaushe muka fara sharing ɗin abu nida ke ne ban sani ba? Ya akayi matsayinki har ya kai kiyi amfani da abina ba tare da kin nemi izini na ba?" tai maganar tare da miƙewa tsaye, tavtako ta zo har inda suke tsaye ta kalli Amal, ta tsaida dubanta kan Amal, Amma tace wa Yusu

"waye ya ɗauke ka aiki a cikin gidan nan?"

"kece ranki ya daɗe" ya faɗa cikin girmamawa

"Wa kayi wa aiki yanzu?" tai maganar me cike da bayyanar da tsantsar Izzar ta

" 'yar uwarki ranki ya daɗe" ya bata amsa

Ta ɗan lumshe ido sannan ta buɗe tace "Na taɓa gaya maka ina da ɗan uwan ko' yar uwa ne?"

"A'a"

"lokacin dana ɗauke ka aiki na gaya maka nida wani zakayiwa aiki?"

"A'a" ya sake bata amsa

Ta maida idon ta kan Yusuf cikin ɗaga sauti tace

"Ka karyamin doka karo na biyu da wani suna ya kamata in kira kane? Bagidajen ina ne kai? Ko kuma ince daga wani jejin kake? a haka you look civilized amma kwata2 shashasha ne kai, hala ka manta akan death contract kayi signing? Inaga ka manta ne, ko kuma ka ɗauka wasa ne shiyasa kake wasa da rayuwar ka"

Ya girgiza mata kai alamar A'a

Hayaniyar da Hajiya Halima take ji sama sama ne ya sa ta fito ita da ramlah suka tsaya suka yi cirko cirko a falon Widad tana ta zuba tsiyata kunta san ranta.

Widad tace "Yanzu ina maka hukunci se ka kirani azzaluma ko? Saboda haka ɗabi'ar ku ta matsiyatan mutane take, ku kullum akan daidai kuke masu kuɗi kuma Azzalumi ko?, dukda bana maimaita magana yau zaka sani na maimaita, Ni Widad ban yadda da kowa ba, duk yadda muke da mutum karyamin dokoki na daidai suke da yunƙurin cin amana ta, kuma penalty ɗin wanda yaci amana ta, bana jin tantirin talaka wanda bashi da komai kamar ka ze iya ɗauka "

Amal tace " haba Widad be kama......

Ɗaga mata hannu Widad tayi ba tare da ta kalli Amal ba tace "har yanzu 'yar alfarma ce ke a cikin gidan nan, matsayinki be kai na 'yar masu gida ba, karki ƙara gangancin ina magana ki katseni ko kisamin baki, idan ba haka ba kin san sauran, kai kuma daga yau nikaɗai kake wa aiki a cikin gidan nan, ban yadda wani ya saka aiki kayi ba, duk wanda yace kai wani abu kace Widad kake wa aiki ba wani ba, sannan kayi a rabin salary ɗinka shine hukuncin karya min doka da kayi har sau biyu dismiss from here"

Yusuf ya risina ya ɗanyi murmushi yace "godiya nake uwaɗakina, Allah ya ƙara girma Insha Allah zanyi ƙoƙari in kiyaye dokokin ki, bazan ƙara karya miki doka ba, Allah ya huci zuciyar ki"

Gaba ɗaya suka bi Yusuf da kallo wato shi duk wannan cin zarafin da aka yi masa godiya yayi, lallai wani talakan Jaki ne, besan ciwon kansa ba, Ramlah ta faɗa a ranta.

Widad ta kallesu ɗaya bayan ɗaya tace "bana buƙatar kowa a falon nan, madam zaki iya jan zugarki ku ɓace min daga nan"

Saboda tsabar baƙinciki da takaici Amal watsi tayi da kayan shopping ɗin da tayi a falon, tai cikin part ɗinsu da gudu tana kuka, abun yayi yawa taji zafin cin mutuncin da akayiwa Yusuf ga tsabar wulaƙanci da suke fuskanta a gidan nan se kace Almajirai, kokuma wasu bayi.

Ramlah ta kalli mahaifiyar su tace
"Mummy am tired wallahi enough is enough are we slaves? see how this little baby is shouting at both of us including you, Mummy you have to do something"
Kafin Mummy tayi magana Amal ta shigo tana kuka.

Mummy tace "Amal meya saki kuka?"

"gaskiya ni Mummy zan tattara kaya na in bar gidan nan na gaji, wannan wane irin cin zarafi ne?"

Mummy tace "duk nasan da haka amma kuyi haƙuri ku ƙara wataran se labari da munsamu abunda muke so shikenan fa an wuce gurin"

Amal tace "dan Allah Mummy yaushe wataran ɗin nan zata zo, shekara nawa muna zama kaman bayi? Wallahi nagaji kalli cin mutuncin da tayi wa wannan bawan Allah dan kawai ya kaini unguwa"

A fusace Ramlah tace "dallah rufewa mutane baki, dan taci masa mutunci seme ina ruwan wani? Shi ta fara yiwa cin mutunci? Dama naga yadda kike wani zaƙewa a kansa tun wuri ki nutsu dan ni natsane shi wallahi sam ban yadda da shi ba"

Amal tace "Malama ba ruwan ki da abunda nake yi seki ta tsanar tasa ai, seki kashe shi tunda kin tsane shi"

Mummy tace "kunga dan Allah ya isa haka kar kuyi min faɗa, ni kaina ban yadda da wannan Yusuf ɗin ba, narasa yadda aka yi megidan nan ya wani ɗaukake shi haka, ina son sanin daga ina yake"

Haɗe rai Amal tayi ta zumɓura baki

Mummy tace "ku kuke tada hankalinku, Ramlah zancen da kika yi min ranan na tambayi babanta ya tabbatar min da cewa Aurar da ita zeyi"

Da yake Amal bata san zancen ba da sauri ta waigo tace "Aure kuma? A hakan za ai mata Aure? Waze kwashi wannan Jarabar"

Ramlah tace "Mummy dama na gaya miki, Amma wane me tsautsayin za'a liƙawa wannan Mahaukaciyar? Nasan dai bata da saurayi to waze ma kulata taci masa zarafi"

Mummy tace "ba wani bane Fahad  ɗin Alhaji Bulama ne"

Asahar Ramla ta saki tace "Wane Fahad ɗin?"

Murmushi Amal tayi tace "Bulama nawa muke da shi? Fahad dai da kika sani, Fahad naki shine me tsautsayin"

Ramlah tace "Taɓɗijan wallahi da sake, baze yuwu ba akan me? Ita Hajiyar sa tana me za'a aura masa wannan tantiriyar ga hauka gashi maybe ta gama watsewa da turawa, shekararta nawa a turai, Allah kaɗai yasan me take acan baze yuwu ba"

Ta miƙe ta bar ɗakin tana masifa.

Yusuf be bar gidan ba ranar se bayan sallar isha'i.
Koda yaje gida ya tarar Umman sa ba taci Abincin dare ba shi take jira, seda sukaci Abinci suka yi hira sannan ya koma ɗakin sa.
Ya ɗakko laptop ɗin sa ya shigar da duk abunda ya faru da date da komai, dukkanin hirar da suka yi da Amla seda ya rubuta sannan ya kwanta.

Tun daga ranar Yusuf yake taka tsantsan gurin bin dokokin Widad, Sannan yana ta ƙara lura da yanayin mutanen gidan da ɗabi'ar kowa daga cikin su.

Widad ta aika Ramla ta kira mata Yusuf.
Ramlah tana zuwa inda suke zama ta kalle shi a wulaƙance tace
"kai wa kake kazo inji waccan yarinyar"

Yauma Yusuf ya shirya tsaf ze kai Widad Store za tayi siyayya bayan fitar su, Hajiya Halima ta aika aka kira mata Isa mai gadi, yaje ya same ta a ya durƙusa ya gaishe ta, ta amsa masa a wulaƙance sannan tace

"kaine ka kawo wa Widad direba ko?"

"Eh nine Ranki ya daɗe"

"Good, ina son sanin daga ina yake?"

Isa ya risina sosai sannan yace "Wallahi ranki ya daɗe ban san daga inda yake zuwa ba, nima wani abokina ne Sani ya kawomin shi yace ɗan uwan sane amma ban daga ina yake ba"

"ka buɗe kunnen ka da kyau ka saurareni"

Isa yace "to Hajiya"

"Ina so duk yadda za'ayi in san daga ina yake? Daga ina yake zuwa gidan nan, sannan ina so ka ƙara samun ido akan sa sosai ina tunanin akwai wani ɓoyayyen abu a tare da shi"

"An gama ranki ya daɗe insha Allah zanyi yadda kike so"

"sannan wannan maganar ina so ta tsaya daga ni se kaine, bana son wani ya san munyi ta"

"babu me ji ranki ya daɗe"

"tashi ka tafi" Isa ya tashi fita.

Yusuf kam wani katafaren shago ya kai Widad, ta siyi kayan da take buƙata, hatta ruwan roba da zata sha seda ta siya abun ta.
Banda kayan ciye2 da sauran kayan ƙyale2

Seda sukaje gurin biyan kuɗi ta kalli Yusuf tace "jeka mota ka ɗakko jaka ta"

Ba musu yaje ya ɗakko 'yar ƙaramar jakar ta ya kawo mata"

"buɗe ka ɗakko ATM card ɗina"

Ya ɗakko ya riƙe aka lissafa kuɗi, kuɗi ne masu yawan gaske, ko a jikin ta tace
"basu ATM ɗin" ya miƙa musu suka saka a POS suka miƙo masa yasa ka password ya sa hannu ya karɓa ya miƙo mata domin ta saka lambobin da zasu bada damar cirar kuɗin, a hankali tai ƙasa da muryar ta tace

"7724" Yusuf ya gane me take nufi haka ya danna lambobin ya miƙa musu.
Suka ciri kuɗin su yana mamakin me yasa ta gaya masa password ɗin cirar kuɗin ta.

Sun fito harabar Store ɗin zasu tafi suka wuce ta gefen wani mutum dake ƙoƙarin rufe motar sa yabi Widad da kallo tare da faɗin subhanallah.

Da sauri yabi bayan su Widad, Yusuf yayi gaba yana zuba kaya a mota mutumin ya sha gaban Widad yace

"Ahh excuse me Madam you look so hot"

Zare glashin fuskarta tayi tai masa kallon sama da ƙasa ta mayar da glass ɗin ta, tai gaba abunta.

Sake binta mutumin yayi ya sha gaban ta zeyi magana Widad tace "wai me kake nema ne?"

Yusuf kam ganin ta tsaya ya sashi komawa inda take tsayen dan ganin meke faruwa.

Mutumin yace "Wow ashe bahaushiya ce? Gaskiya beb bazan ɓoye miki ba kin tafi da imanina, kin min ina sonki, ki bani contact ɗinki mana se muyi magana, you look sexy" yai maganar yana wani kashe ido irin na 'yan bariki tare da miƙowa Widad wayar sa

Karɓar rantsatsiyar wayar tayi kaman gaske, ta sake ta a ƙasa ta fashe sannan tace "waya gaya maka samun lamabr mace kamar ni a gurin ƙasƙantattun mutane marasa amfani irinka abu ne me sauƙi, dalla matsa a gabana ko in tsinka maka mari sakarai kawai"

Waro ido mutumin yayi "ni zaki tsinkawa mari? Kin san waye ni kuwa? In baki wayata ki fasa min"

"Waye kai banda banza wofi, matsiyaci mara amfani? Kauce a gaban kafin inyi maganin ka"

Kan Widad mutumin yayo yana kumfar baki "Wallahi sena nuna miki koni waye a garin nan, 'yar uban waye ke da zaki min haka? Sena ci zarafin ki na wulaƙanta ki"

Tuni Attention ɗin mutane ya fara yowa kansu kaman ze daki Widad, Yusuf ya shiga tsakanin Widad da mutumin ya kalli mutumin yace

"kana ta mana kumfar bakin ba' a san waye kai ba, ita kasan wacece? Ina ruwan ka da ita da zaka biyo ta kafaɗi maganar banza akan ta, ka kiyaye harshen ka kafin a nuna maka ƙarfin ikon data ke dashi"

"Kaikuma waye kai waye ya sakoka a cikin wannan maganar?" mutumin yasa hannu a aljihu ya miƙowa Yusuf id card ɗinsa, kafin Yusuf ya karɓa Widad tasa hannu ta karɓe ta duba id card ɗin nasa sannan tace

"Ashema matsiyaci ne taƙamarka kaki ko?  Zan iya sawa a keta kakin naka a gaban mutane a wulaƙanta ka, a tozarta min kai, sannan in ɗaure ka, kuɗi sunfi wannan kakin banzar da kake tin ƙaho dashi, Widad Nasir Daula inada Arzikin da zan wulaƙanta ka ka ƙare a gidan yari sakarai kawai "
tayi jifa da ID card ɗin nasa ta tofa miyau akai

Ai Sunan ta data faɗa yasa mutumin nan wani mummunan zare ido tare da sauke numfashi yana kuma maimaita sunan nata.

Widad ta wuce mota Yusuf ya bita suka tafi, suna tafe tana ƙwafa tareda yin tsaki jefi2 kallon ta kawai Yusuf yake.

Suka isa gida ta buɗe murfin motar ta fice abunta, Yusuf ya ɗebo kayan ya bita dasu, matar gidan tana falo tana kallo, Yusuf ya shigo yabi bayan Widad har ɗakinta ya ajiye mata kayan, ze juya ya ɗebo sauran tace "ɗan tsaya" Yusuf yaja ya tsaya tazo ta duba kayan, ta ɗakko wata Jaka da turaruka a ciki ta ajewa Yusuf, cike da iko da kashedi tace

"daga yau karka ƙara saka wannan banzan turaren da kake sawa in zaka zo inda nake, ga wannan turarukan kar in kuma jin kasa wannan turaren dan yana samin tashin zuciya ina fatan ka gane?" jinjina mata kai yayi alamar Eh.

Ya ɗau ledar turaruka ya fita ya kwaso mata sauran kayan ya kawo mata, yana zuwa ya tarar ta shiga wanka, dan haka ya haɗa da ledar turarukan da ta bashi, ya ajiye mata akan gadonta yai ficewarsa.

Bayan Yusuf yayi sallar Azahar ya nemi guri ya zauna a inda suka saba zama da sauran ma'aikatan gidan, Isa mai gadi yace
"Yusuf manyan ƙasa, gaskiya ka ciri tuta a gidan nan, ina jinjina maka"

Yusuf yace "Mena yi na cancanci jinjina haka"?

"Ahh irin yadda kake jure cin mutuncin wannan yarinyar mana, naga da alama kaman kai bata yi maka wulaƙsncin, amma dukda haka kana haƙuri wallahi yarinya se kace sheɗaniya, zuciyar ta babu Imani se miyagun Aƙidun turawa to aibtama ci uwar turawa wannan"

Yusuf yace "kaga dakata Isa, kana gidan mahaifinta kana cin Arzikin su sannan kuma ka dinga zagin ta? Aiba'a haka a rayuwa, ni duk wannan abubuwan da kuke faɗa akan ta ni bana  gani, danni ba ta yi min ba"

Isa yace "ni na rasa me yasa kullum kake ƙoƙarin kare ta, da anyi magana ka hau kare ta, ina tausayawa ranar da zata maka mugun halin nata, naga yadda zaka yi ai"

"kaga Isa abar wannan maganar dan Allah"

Isa yace "shikenan tunda haka kace, nikam nace ina Sani kuwa? kwana biyu baya zuwa gidan nan ko a waya bana samun sa, nasan kai kuna haɗuwa tunda unguwar ku ɗaya"

Yusuf yace "waye ya gaya maka unguwar mu ɗaya?"

"Ai gani nayi ɗan uwanka ne shiya kawo ka gidan nan, dan haka nayi zaton unguwar ku ɗaya"

Yusuf ya murmusa yace "A'a ba unguwar mu ɗaya ba"

"to kai a wace unguwa kake? Ko ince inane ƙauyen ku? Dukda baka yi kama da 'yan karkara ba, ni mamaki ma nake yadda matashi kamar kai yake aikin direba"

Yusuf yayi murmushi yace "Isa kenan, dama su' yan ƙauyen wata kamace dadu ta daban ne? meyasa ka damu da sanin unguwar da nake?, indai Sani ne zan nemo maka shi dukda ba unguwar mu ɗaya ba, zan kawo maka shi har nan yazo"

Yusuf ya basar da zancen yaƙi gayawa Isa unguwar da yake.

Duk wasu hikimomi Isa yabi, Amma Yusuf ya nuna masa ƙwarewa irin ta jami'in sirri ya basar da zancen ya shiga wani.
Daga ƙarshe ma ya miƙe ya bar gurin, Isa yace  "wannan anyi Jarababbe me taurin kan masifa, ƙiri Ƙiri yaƙi gayamin, amma zaka ga tsiya, in kasan wata baka san wata ba, zan biyo maka ta inda koka ƙi Allah seka faɗa"

Share please 🙏🙏🙏

Masoya masu Comment ina godiya, Allah ya bar ƙauna 😍 😍 😍 ku sani yanzu aka fara wasan, amma gaskiya idan ba'a Comment yadda nake so zan ɗau matakin da ya dace, dan Allah idan kin karanta idan kin san Tanks kawai zakice koki turamin sticker ki riƙe abun ki please 🙏🙏🙏

Domin sharhi, gyara ko shawara ƙofata a buɗe take, feel free to contact me, sedai in ban buɗe saƙon da wuri ba ayimin afuwa, ina godiya 😍

Ayshercool
07063065680

                     _*AƘIDATA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends




ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

                          PART1
                               Page 6





Widad kam koda ta fito daga banɗaki, da jakar turarukan nan data bawa Yusuf ta fara yin arba akan gadon ta, ta ƙarasa a hankali ta duba, sune dai turarukan da ta bashi,
"lallai wannan ɗan rainin hankali ne, ni zan bashi abu yazo ya ajiye min?"

Fita tayi falo ba kowa dan haka ta wuce part ɗinsu Amal, tana zuwa ta tarar da su a kitchen suna ta girki suna hirarsu, Wai Ramlah zata yi baƙi, se hada hada suke da kaji da sauran kayan masarufi.

Basu san da zuwan Widad ba se muryarta da suka ji cikin isa tace
"Ramlah kije gate ki kiramin driver na yanzu"
Cike da ɓacin rai, ba tare da Ramlah ta kalleta ba tace "to"
Haka Ramlah ta fita tana ƙunƙuni ta nufi bakin gate.

Tana zuwa ta tarar Yusuf ya siyo Abinci ze fara ci, Ramlah tazo kansa ta tsaya ta ƙare masa kallon up and down a wulaƙance, ta kalli gurasar gaban sa ta masu balango da nama ta kuma kallon sa ta taɓe baki ta ɗanyi tsaji taxe

"kai kazo inji waccan yarinyar"

Banza Yusuf yayi mata ya cigaba da ƙoƙarin cin Abincin sa.

"Wai baka ji ne?" ta masa magana cikin tsawa.

Nura direban Alhaji yace "Yusuf da kaifa take magana"

Yusuf ya ɗago ya kalli Nura yace "yawwa Sunana ka ambata, meze hana ta kirani da Sunana dan me zata cemin kai, kuma ni ban san wata yarinya a gidan nan ba"

Mamakine ya kama Ramlah, dama yana magana haka da wulaƙanci amma yake iya tsayawa Widad taci zarafin sa? Ba mamaki saboda kwaɗayin abun duniya kar a kore shi shiyasa yake shnaye wulaƙancin Widad, amma har ita wannan talakan ze buɗe baki ya gayawa magana a fusace tace

"kai saurara bazan kira sunan naka ba, uban waye kai da zaka dinga tambayar ban san sunan ka bane? Kai a wa? Ka kiyaye ni wallahi bana son shirme idan kace zakamin rashin mutunci zaka ga abunda ze biyo baya, sannan idan kaga dama kaje, in baka ga dama ba karka je ka san sauran"

Yusuf yayi kaman ba da shi take ba ya ci gaba da antaya gurasar sa. Ran Ramlah ne yai mugun ɓaci da ganin wannan rainin hankalin na Yusuf, ƙwafa tayi ta koma cikin gida.

Nura yace "Yusuf dan me zakayiwa Ramlah haka? So kake kaja wa kanka a kore ka?"

Yusuf yace "Nura kenan, to a korenin mana seme?" ya ci gaba da cin gurasar sa seda ya gama cin Abincin sa, Sannan ya miƙe ba tare da ya kuma cewa komai ba ya nufi cikin gidan.

Yana zuwa ya tarar da hakimar ta ɗora kafarta akan centre table tana jiran isowar sa.

Yusuf ya ƙaraso cikin girmamawa yace "gani ranki ya daɗe"

Widad tace "se yanzu ka ga damar zuwa? Na tura a kira ka kace bazaka zo ba seka gama abunda kake?"

Da confidence ɗin sa yace "bance ba zanzo ba ina cin Abinci ne lokacin"

"ba tun ɗazu aka kaiwa ma'aikatan gidan nan Abinci ba?"

"Aini ban sani ba munfita tare da ke, kuma ni ba'a taɓa Abinci ba"

Tsuke Fuska Sosai Widad tayi tace "Ramlah kiramin larai" Ramlah ta juya ta tafi kiran larai, Widad ta kalli Yusuf a wulaƙance tace

"me kake nufi da in baka abu ka ajiyemin kayi tafiyar ka? Me kake nufi da hakan? Harni zan baka abu saboda wulaƙanci da girman kai irin na talaka harni zaka gwadamin halin naku na talakawa na girman kan banza akan abunda baku dashi"

Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "ba girman kai bane Madam, bakomai ne yasa na ajiye ba face abunda kika bani yafi ƙarfin talaka kaman ni in saka, duk wanda yaji ƙamshin wannan rantsatsun turarukan to tabbas zan zama abun tuhuma ga al'umma, kiyi hakuri wannan turaren seke"

Wani irin murmushi Widad tayi wanda ita kaɗai tasan ma'anar sa, sannan ta tsuke fuska tace

"Amma fa ka iya rainin wayo sosai, shikenan amma idan na kuma jin tashin wannan banzan turaren a jikin ka kasan sauran"

"Insha Allah bazan sake saka turaren da shugaba ba taso ba"

Ramlah ce ta dawo tareda 'yar aiki larai na biye da ita, jikin larai se tsuma yake tazo gaban Widad ta durƙusa.

"Larai Me yasa ake hana direba na Abinci?"

Larai ta kalli Ramlah a ɗan dirirce sannan ta dawo da kallon ta kan Widad za tayi magana, Widad tace "Idan kikamin ƙarya sena hukunta ki"

"Wallahi ranki ya daɗe Hajiya ce tace kar a sake a bashi Abinci, ba a cikin ma'aikatan gidan nan yake ba"

Widad tace "hmmm tunda ita ta siyo ta kawo ko? Ke Ramlah kije ki gayawa mahaifiyarku, ko kare na ajiye a gidan nan ya zama dole a bashi duk abunda yake buƙata tunda lokacin da'ake tara dukiyar gidan nan bada gumin ta aka tara ba, sannan....

Yusuf katseta ta hanyar cewa "Amma uwa ɗakina ina ganin idan kika yi haka baki kyau ta ba, ki bari...

"Shut up....., do you think am doing it because of you?, let me tell you something, ba nace a baka Abinci a gidan nan dan komai ba sedan kauce wa hatsarin dake tattare da hakan, karka manta YOU SIGN ON YOUR DEATH CONTRACT ya rage naka kula da rayuwar ka"

Ta miƙe ta nufi part ɗinta cikin takunta na isa.

Jiki a sanyaye Yusuf  ya fice yana mamakin waime take nufi da wannan death contract ɗin ne?

**********************

Manyan Mutane maza su uku, zaune a wani ƙaton falo, da ganinsu kasan suna da kuɗi saboda yanayin suturar jikin su, zaune suke suna tattaunawa fuskarsu ɗauke da damuwa
Ɗaya yace "nifa Al'amarin nan ya fara isa ta, tsawon shekaru muna fama akan abu ɗaya, amma abu yaƙi ci yaƙi cinyewa nifa na fara karaya"

"haba Alhaji Haruna, akan me zaka karaya haka? Ai ba gudu ba ja da baya, se burinmu ya cika se mun samu abunda muke nema, abun baƙin cikin yarinyar nan muguwar gaddamammiya ce, wani irin mugun Aƙida ne da ita tamkar tasan abunda muke nema, sam bata da wani mutum data aminta da shi ya shiga jikin ta balle mu samu abunda muke so"

Alhaji Haruna yace "kai bari kawai Alhaji Musa, Yarinya kaman ba jinsin mutane ba, duk na kusa da ita ba wanda bamu bi ba amma bamu samu abunda muke buƙata ba, Kalli yadda shirin mu na jiya ya wargaje.

"Hmmm bari kawai kaga jiya yadda ta wulakanta Jamil a harabar Store ɗin nan, ina zaune a mota na ɗauka zeyi ƙoƙari ta bashi lambar wayarta amma ta fasa wayar ta ƙare masa zagi a gaban mutane"

Alhaji Haruna ya girgiza kai "yanzu meye abunyi ko mu kashe yarinyar nan mu huta mu kama Nasir daula ta ƙarfin tsiya mu samu abun nan"

Alhaji Munir yace "kul Haruna, in baka iya kama ɓarawo ba shi seya kama ka, wannan ai wauta ne, kasan yarinyar nan a gurin sa ta gaji wannan taurin kan, idan muka kashe ta tamkar mun kashe Nasiru Daula ne, kuma kasan akwai hatsari sace shahararren mutum kaman Nasiru a ƙasar nan, dan haka ita yarinyar ya kamata mu ci gaba da farauta "

Alhaji Musa yace " to sace ta zamuyi ko yaya? Duk hanyoyin da ya kamata mubi munbi amma abu ya gagara, idan muka bari ta koma ƙasar waje aikin mu ze kuma komawa baya ne"

"to sace ta zamuyi ko kuwa?"

Alhaji Munir yace  "A'a a yanzu ba sace ta ya kamata mu yi ba, zamu ci gaba da bin diddigin ta, kun san sace wannan yarinyar se anyi kyakykyawan shiri"

Alhaji Musa yace "Anya Alhaji Bulama be san komai akan abun nan ba? naga amintaccen Nasiru Daula ne ko zamu gayyato shi cikin mu?"

"Taɓɗijan ashe tamkar mu fita mu
tonawa kanmu asiri ne, kome zamuyi kar mu shigo da bare cikin mu, zamu ci gaba da yin zagon ƙasa ne a sirri har mu samu abunda muke so"

Haka suka ci gaba da tattauna wa a tsakanin su.

**********************

Yusuf na bakin gate ya bada hankalin sa akan wayar sa, Amal ta fito yana ganin ta yai murmushi tace "Sannu da hutawa"

"Yawwa ranki ya daɗe ya gidan?"

"lafiya ƙalau, Widad na nemanka"

"to shikenan muje" ya tashi ya bita har part ɗin Widad, suna shiga Widad ta tsira musu ido, ta sauke idon ta akan Amal ta ƙura mata ido ko ƙyaftawa ba tayi, Sum sum Amal ta fita ta basu guri, zuciyar ta ɗauke da zazzafan kishin barin Yusuf daga shi se Widad a ɗaki.

Widad ta ƙare Yusuf kallo kaman bata sanshi ba kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai, dogon wando ne a jikin ta da vest ko kunya ba taji a irin shigar data keyi Widad tace "zan fita anjima ƙarfe huɗu  zanje gurin birthday, ƙarfe huɗu, in kaga dama ka tafi yawon ka"

Ya jinjina mata kai yace
"Insha Allah zan kiyaye lokacin" daga nan ya fice.

Ƙarfe huɗu saura kwata akayi sallar la'asar, Yusuf ya gabatar da sallar la'asar, sannan ya shiga cikin gidan.

Yana zuwa ya tarar da Alhaji Nasir da iyalan gidan, gefen sa ga trolley alamun tafiya zeyi.

Yusuf yace "barka da rana Yallaɓai"

Alhaji Nasir yace "Yawwa Yusuf ya aikin, ya haƙuri da Daughter"?

Murmushi Yusuf yayi yace "ai mune take haƙuri damu, Aiki kuma Alhamdilillah, mungode Allah"

Alhaji Nasir ya jinjina kai yace "tafiya ta kamani zani Paris, se shagwaba take wai bazan tafi ba, Yusuf ga amana ta nan, na bar amanar daughter na a hannun ka, har inje in dawo kar a bari tayi kuka, idan tana buƙatar wani abun akula ayi mata dan Allah"

Widad da sauri ta kalli mahaifin ta sannan ta kalli Yusuf a wulaƙance tace
"Allah ya kiyaye Ina da komai da nake buƙata, dan haka bana buƙatar taimako daga gurin kowa balle talaka kaman direba na"

Gaba ɗaya suka ɗauke wuta, shi kansa Alhaji beji daɗin abunda Widad ɗin ta faɗa ba.
Yusuf kuwa yai murmushi yace "indai wannan Amanar ce Alhaji na yadda na karɓa, Insha Allah zaka je lafiya ka dawo ka tarar da ita, Allah ya bani ikon kula da ita"

Alhaji Nasir yace "Ai dama nasani duk me sunan Yaya na mutumin kirki ne, ban taɓa ganin Yusuf wanda ba shi da kirki ba, Allah yayi wa Rayuwar ka Albarka"

Yusuf ya amsa da Ameen

Ita kuwa Maman su Ramla tamkar ta haɗiye zuciya, wai direba ake bawa amanar 'yar masu gida, tunda ita cinye ta zata yi ai dole a ce direba ya kula da ita, shikenan direba ya kula da ita in yasan wata ai be san wata ba.
Ba ƙaramin haushi take ji yadda Alhaji Nasir ke nuna wa Yusuf kulawa ba.

Yusuf ya ɗaukar wa Alhaji Nasir trolley ɗin sa suka fito harabar gidan, Nura ya taho jiki na rawa ya buɗewa Alhaji Nasir bayan mota ya shiga.

Ramlah ce ta taho da nufin itama ta shiga motar ayi rakiyar Alhaji Nasir da ita.

Widad ta kalli Ramlah tace "ba gurin ki a motar nan, dan bama buƙatar rakiyar ki"  ta kalli Yusuf tace "shiga gaban motar" .

Nura ya tsaya ya kalli Widad ya kalli Yusuf, Yusuf ma saroro yayi yana kallon Widad, Waidad tace
"ba kaji ba? ko sena maimaita"
Yusuf  ya buɗe gaban mota ya zauna, yayin da ita da mahaifin ta suka shiga baya suka zauna.

Nura ya ja mota suka tafi, Ramlah ta rasa me zata yi ne, Mummy tace
"yi haƙuri ƙyalesu, in sun san wata basu san wata ba"
Haka ta rarrashi Ramlah suka wuce cikin gida.

Jefi2 Alhaji Nasir da Widad suke hira, yayin da Yusuf da Nura suka yi shiru kowa da abunda yake saƙawa a ransa

Suna cikin tafiyar ne, Alhaji Nasir yace "daughter na dan Allah ina sake roƙon ki, karki watsamin ƙasa a ido, idan fahad ya dawo ku daidaita, ina son ganin ki cikin farin ciki ne daughter bana son irin wannan rayuwar takura kan da kike yi"

Banza tayi da Daddyn, seda aka ja lokaci sannan tace  "Daddy na fara tunanin ka dena sona, idan har kana tunanin yi mun aure ne ze sani farinciki, to tabbas zaka sake jefani ne cikin wata damuwar, kafi kowa sanin meye buri na, Aure ze zama tamkar barrier ne a cimma buri na"

"Daughter yanzu abun nan baze wuce a gurin ki ba? Ba zamuyi haƙuri ba mu barwa Allah, ba zamu yadda komai ya faru damu muƙaddari ne daga Allah ba?"

"Daddy bazan taɓa mantawa ba, kuma bazan yafe ba sena cika buri na, kuma ka dena min batun Auren nan bana so, bazan iya zama a ƙarƙashin wani ba inyi masa biyayya ko waye shi, ku ƙyaleni da zancen Auren nan please bana so"

Ta mirror Yusuf yake ganin Widad yadda Hawaye ya wanke mata fuska, ta rintse ido tana magana cikin kuka.

Alhaji Nasir ya rungume ta a jikin, sa cikin sigar rarrashi yace

"Am sorry my dear, i don't mean to hurt you, nasan tamkar na fama miki wani ciwo ne dake cin zuciyar ki, amma kiyi haƙuri ina ƙoƙarin wanke miki wannan damuwar ne, ina son komai ya wuce kema ki fuskanci rayuwar ki"

"No Daddy i can't, ta yaya zan manta da abunda ya faru, Daddy bazan ƙara yadda da kowa ba, yin aure na tamkar ƙara kusanto da maƙiya jikin mune, ni bazan yadda da kowa ba balle a sake cutar dani a karo na biyu ba, Daddy i repeat my self bana son kowa a kusa dani, bana so" sosai kukan nata yake ƙara ƙarfi harda sheshsheƙa.

"yi haƙuri daughter na, Amma ina sa ran Insha Allah zakiyi alfahari da auren fahad, yana da kirki sosai ɗan uwanki ne, tunda jinin Alhaji Bulama ne, bana tunanin akwai wata cutarwa da Alhaji Bulama ze mana"

Haka nan Yusuf yaji ta bashi tausayi, duk abunda zesa Widad ta sauke wannan izzarta ta, ta dinga irin wannan kukan lallai ba abune ƙarami ba.

Har suka je airport Widad kuka take, har kyawawan idanuwan ta sunyi ja, haka suka yi Sallama da mahaifin ta.
Alhaji Nasir ya dubi Yusuf yace "Yaya na a kulamin da amana ta"

A fusace Widad tace "Daddy karka ƙara cewa ka bar amana ta a hannun wani , ka barni a hannun Allah zaka je ka dawo ka tarar dani lafiya Insha Allah, amma zuwa yanzu yaci ace kayi darasin da bazaka ƙara bawa mutum yadda da Amana ba, narasa me yasa Daddy ka kasa fahimta ta"

Alhaji Nasir yai murmushi ya riƙo hannayen ta yai mata raɗa a kunnen ta, sannan a fili yace  "ina da surprise a gare ki idan na dawo, ku koma karku yi dare my lovely"

Haka Widad suka juya zuwa mota, yanzu ma Nura ne ke jan Motar

Widad tace "yi parking anan" Nura ya tsaida motar, tace masa

"gaya masa  inda farm house yake"

Nura ya gane abunda take nufi, dan haka yaiwa Yusuf kwatancen inda tace.

Daga nan ta ɗaga idon ta wanda suka jiƙe da hawaye tacewa Nura

"fita ka bar motar nan ka hau ta haya ka koma gida, Kaikuma ka karɓi tuƙin mu tafi"

Nura yace "Amma ranki ya daɗe motar Alhaji ce kuma....

"motar Alhaji ta ubanka ce? Ko ta Ubana?" ta jefo masa tambayar

"A'a amma ban fito da kuɗi ba"

"Idan ka bari na sake magana, zan ɓata maka rai fiye da tunanin ka, fita daga motar nan nace, idan ba tare muka haɗa kuɗi muka siya ba"

Haka Nura ya fice daga motar, Yusuf ya karɓi tuƙin.

Yusuf ya dinga bin kwatancen da Nura yayi masa, har sukaje gidan gonar Widad bata dena kuka ba, Sam Yusuf yaji beji daɗin yadda take kukan ba, gashi ita ba'a iya mata balle ya rarrashe ta
Wani irin tangamemen gida ne har yaso yafi gidan da su Widad ke Rayuwa a ciki girma, Yusuf ya fara tunanin anya wannan gidan gona ne? Horn Yayi aka buɗe masa wani jibgegen gate me matuƙar nauyi ya shiga da Motar cikin gidan.

Ma'aikatan gidan ne suka dinga tahowa cikin matuƙar sauri inda motar su Widad take, Kallon gurin Yusuf yake yi, dabbobi kala kala a ɓangarori daban daban wanda idon sa yake iya gani, gefe kuma gida ne sosai ginanne a ciki, cikin zafin Nama ta fito daga motar tana ta Hawaye, cikin girmamawa ma'aikatan ke zubewa suna gaishe ta, babu wanda ya samu Arziƙin kallo balle ta kula shi.

Cikin matuƙar sauri ta nufi ɓangaren da yake gida ne a cikin gurin, Yusuf ya bita shima cikin sauri, binsu ma'aikatan suka yi da kallo mussman Yusuf, Wani irin murgujejen kare ne fari da baƙi a jikin sa ya nufo inda Widad take yana wani irin gurnani gami da sufa.

Durƙusawa tayi ƙasa Karen yazo yana zagaye Widad yana shanshana jikin ta, shafa gashin karen tayi tana kuka tace "I miss you Miz"
Karen ya kwantar da kansa a jikin Widad yana zaro harshe, ko tsoron sa bataji balle ƙyama.

Haka karen yai lamo a jikin ta tareda ƙurawa Yusuf ido, ita kuma tana cigaba da kuka, can kuma ta shafa kan karen tace
"Excuse me Miz, I will see you later"

Ta miƙe zata yi gaba Yusuf ya bita, Karen nan ya bishi yana masa wani irin haushi da gurnani yana zubar da yawu, Yusuf a ransa yace
"Wane irin jarababben kare ne wannan se kace zaki?"

Widad ta juyo ta kalli karen tace
"don't Worry, I trust him Miz"

Daga nan ta miƙe ta ci gaba da tafiya, Aikuwa tana faɗar hakan karen ya dena bin Yusuf.

Sunyi doguwar tafiya sosai a cikin gidan, dabbobi daban daban wasu daka gansu kasan sun sha banban da kalar namu na Nigeria.

Gida ne sosai a ciki ginanne me matukar kyau, ya tsaru sosai sedai da alama babu mutane a ciki.

Wani ɗaki Widad ta nufa ya bita, suna shiga ɗakin Widad ta ƙara sautin Kukan ta, wani katafaren gado ta nufa ta zube a gaban gadon ta ci gaba da rera kukan ta, daga jin yadda take fidda sautin kukan kasan kuka ne me taɓa zuciya.

Yusuf se binta yake da ido cikin tausayawa halin da take ciki, amma bashi da damar yayi mata magana ko ya rarrashe ta dan bata son shisshigi, yanzu zata masa rashin mutunci.

Ba tare da ta kalli Yusuf ba, a hankali tace "Excuse me please" Yusuf ya jinjina kai ya fice ya tsaya a wajen ɗakin, kusan mintuna talatin yana tsaye yana jiran ta.

Fitowa tayi ɗauke da wata shigar ta daban, kamar ba ita ba, shigar jikin ta ba kace musulma ce ba.

Kallon ta Yusuf ya tsaya yanayi duk wani ilahirin surar jikin ta seda ta bayyana, Farar fatar ta se ɗaukar ido take.

"let's go" shine abunda ta cewa Yusuf, haka yabi bayan ta zuwa inda motar su take, nan ma ma'aikatan ne suka kuma biyo ta suna mata Fatan Alkhairi, gaban motar ta buɗe ta ɗebo kuɗi bandir bandir ta basu, ta shige motar Yusuf yaja motar.

Wani ƙaramin kati ta miƙawa Yusuf, kwatancen inda gurin partyn yake ne, shi sam ya manta tace ze kai ta gurin birthday ne, ga yamma tayi sosai, se dai bashi da ikon magana haka ya bi kwatancen.

"Hello ranka ya daɗe, bayan tsawon shekaru yaufa tazo gidan gona"

"Me tazo tayi?"

"Nima ban sani ba Yallaɓai"

"ta fita da wani abu daga gidan ne?"

"A'a bata fita da komai ba, kaya kawai ta canza sannan ita da wani matashi suka zo yana tuƙota"

"Direban tane kokuma waye?"

"Gaskiya ina tunanin ba direban tane ba kawai, dan a biye yake da ita, har cikin gida duk inda ta shiga yana binta"

"Good, ina so aje anemo min waye wannan matashin, me yake yi a tare da ita, Akwai yuwuwar ze mana Amfani"

"shikenan Oga an gama"

*******************

Koda sukaje gurin birthday ɗin a harabar wani katafaren gida, da ganin yaran da suke shiga suna fita a harabar gurin kasan sun jiƙu da kuɗi, fitowa Widad tayi daga motar, Yusuf ma ya fito ya kulle motar.

Wata 'yar siriryar Murya suka ji tace "hey beb you are here?"

Da sauri Widad ta juya suka rungume juna da matashiyar Yarinyar da zata yi sa' ar Widad, suna murmushi

Widad tace "Happy born day baby"

"Thank you sweetheart"

Wani matashi ne ya biyo bayan Yarinyar ya kalle ta yace
"Sweetheart who is this beb?"

"She's My best friend in UK, we take part in the same school, She's Alhaji Nasir daula's daughter"

Ta kalli Widad tace "Baby wannan cousin ɗina ne"

Matashin yai murmushi yace "wow Nice to meet you baby"

Ya miƙa mata hannu da nufin su gaisa, Amma cikin zafin nama Yusuf ya saka hannun sa a na Matashin wanda hakan ya hana Widad gaisawa da Matashin.

Kallon sa sukayi gaba ɗaya da mamaki, Widad kam mazewa tayi kamar ba taga Abunda Yusuf yayi ba, suka nufi gurin da ake Shagalin birthday ɗin.

Yusuf bin bayan su yayi, Nurat ta kalli Widad tace

"Beb waye wannan ne wai?"

"Why are you asking?" Widad ta tambaye ta

"Abunne ya bani mamaki, nasan baki da brother, Amma me yasa ze miki haka? Lallai kinyi sanyi ko kin fara sauka daga kan AƘIDAR taki ne?"

Widad ta girgiza kai tace "babu abunda ya canza, sedai kin san komai na Widad a lissafe yake"

Jinjina kai Nurat tayi tace

"Wannan ma cikin lissafin ne kenan?"

Widad tace  "Maybe"

Nurat tayi murmushi tace "You are wonder lady"

Sukayi Murmushi suka nufi kan stage ɗin, Widad na Hawa kan stage ɗin tare da Nurat aka ɗauki tafi ana shewa.

Cake Nurat ta yanka, aka dinga tafi ana ihu, tare da waƙoƙin birthday.
Kyautar Mota Widad tayi wa Nurat, a matsayin birthday gift, gurin ya hagirtse da shewa anawa Widad kirari, suka shiga cashewa a stage din nan kaman ba yaran musulmi ba.

Kiran Yusuf akayi a waya, ya fita waje domin amsa Wayar saboda hayaniyar da take tashi a gurin.

Yana ɗaga wayar yasa a kunnen sa tare da yin Sallama

"Idan har kana son tsira da Rayuwar ka, to ka tafi ka bar gurin nan a yanzu, in ba haka ba ko kai ko Uwarɗakin naka ɗaya ze iya rasa ransa"

SHARE PLEASE 🙏🙏🙏

Ayshercool
07063065680

_*AƘIDA TA*_
       




PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

_Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
_
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

                         PART1
                                Page 7


Da sauri Yusuf ya koma gurin partyn ba tare da fargabar komai ba ya shiga kutsawa yana neman Widad, amma babu ita babu alamar ta a gurin, can ya hango Nurat tana ƙoƙarin fita, seda ya bari ta fito daga gurin party, sannan yabi bayan ta a guje ya sha gaban ta, seda ta tsorata da ganin sa ta ɗan tsaya ta kalle shi tace "Are you ok?"

"Ina Widad?" ya jefo mata tambayar

"ban sani ba na barta akan stage tana rawa" tai maganar cikin wata irin gurɓatacciyar hausa.

Subhanallah shine abunda Yusuf ya furta, yai gaba yana sake duba gurin.

ba zato ba tsammani ya shammaci Nur ya fizgota ya shiga cikin duhuwar flowers  da ita, yasa hannu ya shaƙeta, ya kalle ta a hasale kamar wani mahaukacin zaki yace

"Ko ki gayamin gaskiya ko kuma zan fita dake daga gurin nan, zan riƙe ki a matsayin garkuwa harse Naga Widad, idan kuwa rayuwar Widad ta salwanta taki ma ta salwanta, ki gayamin ina take?"
Yai maganar cikin ɗaga murya tare da shaƙe Nurat.

"Dan Allah, please don't kill me I will tell you, please secure my life"

"Your life will be secured if you tell me the truth" ya faɗa yana zare mata ido

Cikin kokawa da numfashi tace "Ok zan gaya maka, Dad ne yasa aka busa mata wani abu, yanzu tana harabar gurin nan a ɓoye, wasu zasu zo su ɗauke ta, idan baka hanzarta ba komai ze iya faruwa"

"Meyasa Mahaifinki yake ƙoƙarin sace ta?"

Cikin kuka tace "I sure to the Almighty ban sani ba, trust me"

Tasa Nurat yayi a gaba ta nuna masa ƙarƙashin bishiyar da aka ajiye Widad, tana kwance helplessly a ƙasa, unconscious kaman babu rai a jikin ta, ga jakar ta a gefen ta.

Ya waiga ba kowa a gurin, Yasa hannu ya sunkuce ta ya tafi da ita motar su da sauri, ya buɗe bayan motar ya kwantar da ita, yaja motar da gudun tsiya ya bar gurin.

Da gudu Nurat ta koma cikin gidan su tana haki, da yake hall ɗin party a cikin gidansu yake, ɗakin ta ta tafi kai tsaye ta shige banɗaki tana sauke numfashi, ta wanke fuskarta, ta buɗe fridge ta sha ruwa me sanyin gaske, sannan ɗakko wayarta ta kira layin mahaifinta.

Seda ta kusa tsinkewa sannan ya ɗaga yace
"Yaya i hope everything is going according to how it's planned?"

Cikin rawar baki tace "No Daddy something is going wrong"

Cikin sauri yace "meya faru?"

Cikin Rawar Murya Nurat tace "Daddy basu ƙaraso da wuri ba, nayi abunda kace Amma..
" Amma me? Ki gayamin menene? "
" Daddy ita da wani tazo, nayi abunda kace, but someone intimidate me, yace in ban faɗi inda take ba ze kashe ni"
"Waye shi?" ya faɗa a fusace
"Ban sani ba Daddy, Amma tare suka zo"
"Wace irin wawuya ce ke haka? Kinsan lokacin dana ɗauka ina wannan shirin? Idan wasu suka rigani mallakar Abun nan mun kaɗe"
"Daddy ba laifi na bane, laifin wanda ka turo su ɗauke ta nefa"
"Shut up, kin ɓata min shiri kina gayamin maganar banza"
"Am Sorry Dad is not my fault, but....
" Common Keep quiet "  ya faɗa a Hasale, tare da katse wayar yana tsaki, tabbas ba dan wawancin nan 'yar cikin sa ce ta aikata masa ba da ba abunda ze hana yasa a Kashe ta.
A fili Yace
"dole in  toshe duk wata kafa da zesa su Alhaji Haruna su san nayi yunƙurin sace Yarinyar nan ni kaɗai, kuma dole in gano wane yaron ne suka je gurin tare"

Yusuf kam gudu yake bana wasa ba, ya dinga kauce wa dukkanin hanyoyin da zesa ya haɗu da cunkoson ababen hawa, ko kuma jam'ian tsaro, be sassauta da gudu ba seda yaga ya shigo layin su Widad, a hankali ya ƙara sa tuƙin yana zuwa ƙofar gate ɗin ya saki wani irin horn me gigitarwa, duk a ƙoƙarin sa na ganin ya kai Widad gida lafiya.

A gigice Isa ya buɗe ƙofar dake jikin tangamemen Gate ɗin ya leƙo ya fara masifa "haba Yusufa, wannan wani irin horn ne kaman me shirin sanar da tashin duniya"

Cikin harzuƙa Yusuf yace  "Open the Gate"
Dukda Isa ba turanci yake ji ba amma ya gane Yusuf na magana ne akan ya buɗe masa ƙofa, Cikin Sauri Isa ya buɗe masa Gate Yusuf ya shiga da motar yayi parking, ya sakko da sauri daga cikin Motar ya buɗe inda ya Kwantar da Widad, har yanzu bata hayyacin ta, Yasa hannu ya ɗakko ta tareda Jakar ta ya nufi Cikin gidan da ita, Isa ya biyo bayan sa da Sauri yana ƙasa da murya cike da gulma yake Faɗin

"Yusufa meyasami Uwar ɗakin naka kuma? Kodai Shaye2 tayi ne? Naganta kamar a buge"

Cikin tsawa Yusuf yace "Idan ka ƙara taku ɗaya daga inda kake zan ɓata maka rai"
Gaba ɗaya Isa mamaki ya kama shi yadda Yusuf ɗin ke wani magana cikin Izza da isa.

Babu kowa a babban Falon dan haka Kai tsaye part ɗin ta ya nufa da ita, Ya kwantar da ita akan gadon ta.
Yasa hannu a aljihunsa, ya ɗau wayarsa ya kira Abbas, bugu ɗaya ya ɗauka yace
"Kai ya haka? Zaka kirani a wannan daren?"
"Kai akwai matsala fa"
"Matsalar meke nan?"
"Widad na kai gurin birthday akayi barazanar za'a kasheni idan ban bar gurin ba, ina komawa na neme ta na rasa, da ƙyar na ganta, yanzu haka na dawo da ita gida Amma bata san inda kanta yake ba, I thinks they Use sedative substance on her, nayi niyyar in tsaya da ita a Asibiti Amma naga hakan hatsari ne babba"

Abbas ya numfasa yace  "Gaskiya kam zata farfaɗo Insha Allah, gobe in Allah ya kaimu ka shigo Office kawai za muyi magana"

"Shikenan Allah ya kaimu" suka yi Sallama, ya maida Wayar Aljihunsa ya kalli Widad da take ta bacci bata san meke faruwa ba se sauke numfashi take, Yusuf ya ɗauki bargon dake gefen ta ya rufe ta dashi saboda yanayin Sanyi, wayarta ce keta ringing a Jakarta ya buɗe Jakar ya ɗakko wayar ya kashe ta gaba ɗaya, Sannan ya kama hanyar fita.

Yusuf ya fito ya nufi hanyar fita, yaci karo da Ramlah a babban falo, share ta yayi ze wuce.

"Daga ina kuke a daren nan? Me kake a ɗakin Widad a wannan lokacin?" muryar Matar gidan ce, dake tsaye a ƙafar bene.

Yusuf ya juyo ya kalle ta sannan yace "Na kaita unguwa ne"
"Me kake a ɗakin ta a wannan lokacin? Bata da lafiya ne, na kaita ɗakin ta ne"
"Ka kaita ɗakin ta kai a wa?" Ramla ta tambaye shi.

"Ni ba a kowa ba, ni a ɗan uwan ta musulmi, kuma ma'aikacinta"

"Kai shashasha rufemin baki" Hajiya Halima ta katse shi cikin tsawa.

"Naga kanka yana rawa, to bari in tuna maka kai ba kowa bane face matsiyacin talaka, ka dena jin kanka kamar wani me iko dan kaga mai gidan nan yana wani baka girma na musamman kai ɗin ba kowa bane ba"

Amal da take jiyo hayaniya ta fito daga ɗakin ta, tana zuwa ta tarar da mahaifiyar ta ta saka Yusuf a gaba tana zagin sa
"Haba Mummy, me Yusuf yayi miki kike masa wannan cin mutunci haka?"
Ramla tace  "An zage shi ɗin, meye alaƙar ki dashi? Ɗan uban waye shi da ze dinga wani jin kansa, dan yaga ya samu gindin zama, saboda tsabar cin fuska akan wannan banzan waccan mara mutuncin ta dizgani"

Yusuf ya ɗan murmusa yace
"Nasani niba kowa bane, talaka ne ni gaba da baya, dan haka ku kwantar da hankalin ku,kuma ni bana sawa kaina ni wani ne" yana gama faɗin haka ya juya ya fice.

Amal tace "Mummy koma menene laifin Widad ne, ni banga abunda Yusuf yayi ba"

Hajiya Halima cikin tsawa tace "dalla rufemin baki banza, naga zaƙewar ki kema tana yawa akan yaron nan, ki shiga hankalin ki tunda wuri, ni sam yaron nan be minba, ya fiye kalar munafukai"

Ramla tai caraf tace  "wallahi kuwa Mummy, ni kaina ban yadda dashi ba, Ina jiran sakamakon binciken da kika sa ayi a kansa ne"

Amal tace  "Mummy koma menene Yusuf bare ne aiki ne ya kawo shi gidan nan, bekamata a saka shi a wannan sabgar ba"

"Amal kenan ke har yanzu yarinya ce, baki san inda rayuwa tasa gaba ba, kashedina dake shine, tun wuri ki fita daga sabgar yaron nan, dan muddin na gano wani abu saɓanin abunda nayi zato a tattare dashi ba abunda ze hana insa ayi masa abunda ya dace da shi"

"Amma mum....

"Ke rufemin baki, shashasha kawai"
Mummy tayi maganar tare da juyawa zuwa ɓangaren ta, Ramla ma tabi bayan ta suka bar Amal a falon tsaye.

Yusuf na fitowa, Nura ya biyo shi yace
"A'a kaga ɗan gatan 'yar masu gida, gaskiya Yusuf ka ciri tuta, naga' yar masu gida tana yi da kai, ƙiri Ƙiri ta koreni kuka tafi unguwa, naga duk inda zaka tare kuke tafiya"

Kafin Yusuf ya bashi amsa, Isa mai gadi ma ya nufosu yana cewa
"Nikam Malam Yusuf baka gayamin meyasami Uwar ɗakin ka ba, nifa abun ya bani mamaki, iya sanina dai bata shaye2, sedai taɓun hankali amma meyafaru da ita haka?"

Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya yana karantar tsantsar munafunci da son jin gulma a fuskokin su, sharesu yayi bece musu komai ba yai gaba abunsa ya fice ya bar gidan.

Yusuf na fita, Nura yace
"Ji shi se kace ɗan uban wani, muna masa magana amma yayi mana banza, da Alhaji ne uban sa bansan wulaƙancin da ze ba"

Isa yace  "Bar mara mutunci, ji yadda muna masa magana ya share mu, Anya Nura mutumin nan ba Asiri yayi wa me gidan nan ba?"

"Ni zance maka Asiri yayi masa hadda 'yar sa ma, kana gani ɗazu ta hana Ramla binsu saboda shi, da muka dawo daga filin jirgi se cewa tayi ni in sauka in hau motar haya in tafi gida, shi kuma ya kaita unguwa"

Isa ya jinjina kai yace  "Kana gani duk jin kai da izzar ta, duk Aƙidar ta ta rashin yadda da mutane Amma duk inda zata tare dashi suke tafiya, dudu yaushe yazo gidan nan? Ko wata ɗaya be cika ba ya samu wannan gindin zaman, mu kuwa shekara nawa muna aiki a gidan nan? Ba abunda yake haɗamu da ita se cin mutunci da wulaƙanci "

Nura yace "to ai magana ce a buɗe, Allah kaɗai yasan abunda suke yi"

Isa yace "kuma fa hakane zancen ka Nura, taɓ aikuwa zamu ƙara saka ido sosai, zamuyi maganin wannan gani-ganin da yake mana"

Haka suka zauna suka cigaba da gulma, suna muzanta Yusuf da miyagun kalamai.

Yusuf kam kansa ya kulle Sosai, daya koma gida ma kasa bacci yayi, yana ta nazari akan abubuwa da dama yana son gano bakin zaren amma ya rasa ta ina ze fara, gaba ɗaya Al'amuran a cukurkuɗe suke, me zesa Baban Nurat yunƙurin sace Widad? Waye mahaifin Nurat? Dole Akwai dalilin da yasa Widad take da wannan AƘIDA na ƙyamar talaka da nesanta kanta da mutane, yanayin Abubuwan da take yi wasu lokutan yasa Yusuf ya fara gazgata cewar tana da taɓin ƙwaƙwalwa, tunani ya haɗu ya cunkushe massarafar gangar jikinsa wato ƙwaƙwalwarsa, ba shiri ya tsagaita tunanin ya kwanta da ƙudurin dole yaje Office da safe, akwai buƙatar yaga Abbas.

A hankali ta motsa daga nannauyan Baccin da take, ji tayi kanta kamar an ɗora mata wani nannauyan dutse, gaba ɗaya gaɓoɓinta sun mata nauyi, a hankali ta buɗe idon ta ta ƙarewa ɗakin nata kallo, ta mayar da idanunta ta lumshe na wasu daƙiƙu sannan ta sake buɗe su, a hankali taja jikin ta ta miƙe zaune, kallon jikin ta tayi tare da ƙoƙarin son tuna abunda ya faru, sosai take takura ƙwaƙwalwarta don ta tuna mata abunda ya faru, Amma fafur ta kasa tuna komai, dafe kanta tayi wanda taji yana sara mata, ta miƙe jiri na kwasar ta ta tafi banɗaki.

Da sassafe ko karyawa Yusuf beyi ba ya fito ze fita. Umma dake kitchen tana ƙoƙarin haɗa Abinci ta leƙo tace
"Yusuf me zan gani haka? Ba zaka tsaya ka karya bane?"
Yusuf yace  "Umma sauri nake ne, bana son in makara akwai aikin da nake son yi"
"Yusuf nifa gaskiya wannan aikin da kake a gidan masu kuɗin nan ba sonsa nake ba, nasan halin masu kuɗi da rashin mutunci da wulaƙanta talaka, nidai gaskiya su canza maka wannan aikin su baka wani, danni gaskiya bana son kaje inda za'a wulaƙanta min kai"
Kallon Umman sa yayi, ya ɗanyi murmushi ya tako gaban ta ya riƙe hannayen ta yace
"Kyakkyawar Uwa, Uwa da babu irin ta, ina Alfahari dake Umma na, yadda kike kula dani Allah ya kulamin dake ko bayan raina, ki kwantar da hankalin ki, basa wulaƙanta ni, kuma yanayin aiki ne yazo a haka, dana Kamm zan koma Office, idan kuma kince ba kyason aikin se in haƙura gaba ɗaya"

Badan ranta yaso ba tace  "Yusuf ba aikin ne bana so ba, ni wannan aikin da suka baka ne bana so, yaushe rabon da muci Abinci tare, in ka fita tun safe se dare, Amma shikenan dai, Allah yayi maka Albarka, Allah ya sadaka da Alkhairi a duk inda kake"

"Ameen Umma na, bari in sauri sena dawo"

"Allah ya kiyaye hanya"
Ya amsa da "Ameen" ya fice.

Kai tsaye headquarters su ta jam'ian tsaro na farin kaya ya tafi.
Kasancewar Yusuf mutumin kirki yasa tun daga gate masu gadi suke gaida shi, ya tsaya suka gama gaisawa sannan ya shige ciki.
Ofishin sa ya nufa kai tsaye, yana zuwa ya tarar da shi tsaf ana shiga a gyara masa dukda baya nan, Na'ura me ƙwaƙwalwarsa ya ɗakko ya kunna, ya ɗan jira kaɗan sannan ya fara daddanawa.
Gaba ɗaya ya nutsu sosai hankalinsa kacokan yana kan Computer, da gani kasan ƙoƙarin gano wani abu yake me mahimmanci.

Sallamar da'akayi a office ɗin ne yasa shi ɗagowa, Sakina ce sanye da suit na aiki kamar yadda ta saba, fuskar ta ɗauke da murmushi ta ƙaraso tana wani fari da ido, Sam Yusuf baya ƙaunar mace mara kamun kai, shiyasa sam Sakina bata burgeshi.

Kujera taja ta zauna, ta kalle shi tace "wata sabon gani, aiki ya ɓoye mana kai gaba ɗaya haka, ba'a jin ɗuriyar ka ko a waya, na kira ka harna gaji baka ɗagawa"

Yusuf "Aikine ya ɗanmin yawa shiyasa, Ya aikin?"

Cikin iyayi tace  "Alhamdilillah, Fatan dai kana lafiya?"

Cike da basarwa yace "Lafiya ƙalau"
Ya cigaba da latsa computer sa.

"Kwana biyu da baka zuwa duk gurin nan ba daɗi, nayi farincikin zuwan ka sosai"

Bece mata komai ba ya ɗakko wayarsa ya ɗan daddana ya kanga a kunnen sa, ya ɗanyi shiru na wasu daƙiƙu sannan yace
"Ya Abbas ka shigo ne?"

Ya sake yin shiru sannan yace 
"Ok nima na shigo yau akwai buƙatar in ganka, bari inzo office ɗin naka"

Yana gama wayar ya miƙe ya fice ya bar Sakina a gurin, ba tare da yace mata komai ba.

Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokarewa Sakina zuciya, tabi bayan sa da kallo tare da yin ƙwafa.

Yana fita ya nufi Office ɗin Abbas, yaje ya tarar da shi yana karin kumallo, ya zauna suka gaisa, Abbas ya zubawa Yusuf shayi ya miƙa masa sannan yace "Mutumin ya? Yau ka samu chance ɗin ɓullowa kenan? Meye labari ne?"

Yusuf yace  "labari kam akwai shi Abbas, nifa gaba ɗaya a rikice nake wallahi, gaba ɗaya na rasa bakin zaren"

"Take it easy man, bi komai a sannu, me ake ciki?"

Nan Yusuf ya warware masa irin abubuwan da suka faru har zuwa ga yunƙurin sace Widad da'akayi jiya.

Shiru Abbas yayi yace  "Lallai lamarin akwai rikitarwa, Mahaifin Nurat ze shiga cikin suspects ɗinmu, yanzu abunda za'ayi ka bani Adress ɗin gidan, zamu je muyi bincike, semun fara gano waye ma mahaifin Nurat ɗin"

Shikenan zan turomaka Complete Adress ɗin ta Email ɗinka. Suka zauna suka cigaba da tattaunawa.
Wayar Yusuf ce ta fara ringing ya ɗakko ya duba, lambar Isa megadi ce a akan allon wayar tasa, ya ɗaga ya kara a kunnen sa, suka gaisa Isa yace masa  "Ana neman ka"

"Shikenan gani nan zuwa"

Yusuf ya kalli Abbas yace  "Abbas bari in canza kaya, waccan rigimammiyar tana nemana yau nasan zan sha tijara, dan titsiyeni za tayi tace sena gayamata meyafaru"
Dariya Abbas yayi yace  "Ina jinjina maka Yusuf, yadda kake iya aiki da wannan Yarinyar mara alƙibla"
"to ya zanyi tunda kun takura kunce se nayi, dole in kwantar da kai inyi haƙuri da halin ta, Amma kasan wani abu Abbas?"

"A'a seka faɗa"

"Ni yanzu gaba ɗaya tausayi take bani, gaba ɗaya rayuwar ta ba irin yadda kowa ke gudanar da rayuwar sa take yi ba, duk yadda zan kwatanta naka ba zaka gane ba, ina kyauta ta zaton akwai wani pain a zuciyar ta, da yake ƙara assasa condition ɗin da take ciki "

"Hmm Yusuf kenan ba wani pain, kawai iskanci ne na yaran masu kuɗi, ta taka wanda take so tayi rashin mutunci saboda tana da masu gidan rana"

Yusuf yace  "Haba Abbas, su talakawan me suka yi take musu haka? Wai waya gaya maka talakawa kawai take wa haka? Hmm ni nasan abunda nake gani kawai, ba iya Wulaƙanta mutane ba, Akwai wani ɓoyayyen abu da yake damun ta, ina jin tausayinta sosai"

Abbas ya ƙyalƙyale da dariya yace  "Kai mutumina, ko dai ka koma ruwa ne?"

"Na koma ruwa kamar Yaya?"

"To naji kace kana tausayinta, na sani ko babbar magana zaka janyo mana"

Shiru Yusuf ya ɗanyi jiki a sanyaye ya kalli Abbas yace
"Abbas ai na rufe wannan babin har Abada, sedai wani ikon na Allah, just recently ka manta abunda ya faru dani ne? Ina ni ina Widad, as i told you before i give up gaskiya babu yarinyar da zan ƙara cewa ina so, zanyi haƙuri da ƙaddara ta, in zauna Yadda Allah ya ajiye ni, ni yanzu bari in tafi kar in ƙarawa kaina laifi, dukda yanzu ma nasan laifi na riga nayi shi, zan sha tijara a gurin Widad"  yai maganar tare da miƙewa ya fice.

Abbas yayi shiru yabi bayan Yusuf da kallo, he's very gentle and innocent, abubuwa da yawa marasa daɗi sun faru da Yusuf, gashi shi kullum zuciyar sa a wanke take, baya nufin cutar da kowa.
A fili Abbas yace  "Anya kuwa nayi adalci idan aka haɗa kai dani, aka cutar da Yusuf, Kai Amma kuma Alherin da zan samu a wannan sabgar ya isa in ajiye wannan wahalallen aikin in more rayuwa ta"

Yusuf ya canza kaya ya tafi gidan su Widad, ya tsaya suka gaisa da ma'aikatan gidan sannan ya nufi cikin gidan, babu wanda yake da wannan damar ta shiga cikin gidan kai tsaye, ko ba Aiken sa akayi ba se Yusuf, shi Yusuf be san da wannan dokar ba ma sam, kai tsaye ya shiga Babban falon da yake shine mahaɗar iyalan gidan.
Ya shiga da sallama a bakin sa, ya tarar da Amal a zaune tana kallon zee world, tana ganin sa tayi murmushi tace
"Sannu da zuwa, yau ka makara fa"
Murmushi yayi yace  "Allah ya bada haƙuri, Madam ta tashi ne?"

Amal ta kwaɓe baki tace  "waya san mata, ka zauna mana ka tsaya a tsaye"

"karki damu nidai ace mata nazo"

"Ni ban zanjeba seka zauna"

Yusuf ya zauna a ƙasan carfet, Amal ta ɓata fuska tace  "ya zaka zauna a ƙasa kuma, haba Yusuf dan Allah ka zauna"

Haka Amal ta uzzura masa seda ya zauna akan kujera, ta miƙe tsaye tace
"bari in kawo maka ruwa, kafin ta fito bana so inje ta Wulaƙanta ni, idan ta ga dama zata fito da kanta" tana gama faɗin haka ta miƙe ta shiga wani ɓangaren.

Yusuf na nan zaune, ya ɗakko wayarsa yana ɗan daddanawa, sega Nura direba ya shigo da wata babbar jaka a hannun sa, da alama Aiken sa akayi yana ganin Yusuf a zaune akan kujera yayi turus yana kallon Yusuf.

Yusuf ya ɗaga kai ya dube shi yace
"ya dai Nura? Naga ka tsaya kana kallo na kamar baka sanni ba"

Kafin Nura yayi magana, sega Ramla da mahaifiyar ta sun fito, idon Ramla ya sauka akan Yusuf dake zaune akan kujera, buɗe baki tayi tace
"iyeee samun guri, ɗan kuturu da gaɗa cikin Rama, wato isarka da ƙasaitar taka harta kai ka dinga zama akan kujera sannu fa"
Rai a ɓace Mummy tace 
"Kai ubanwa ya baka izinin shigowa falon nan harka zauna akan kujera, gidan ubanka ne kona uwarka da zaka shigo min falo ka zauna akan kujera, kai na fuskanci kanka na rawa fa"

Amal ce ta fito da ruwa da cup a hannun ta, ta ƙaraso falon tace 
"Haba Mummy dan Allah kiyi haƙuri, wallahi ni nace ya zauna"

Yusuf kam shiru yayi bece komai ba, zama akaan kujera kawai yaja masa zagi da cin mutunci.

"dalla rufe min baki, se nayi maganin yaron nan, saboda jin kansa yake kamar ɗan uban wani, matsiyacin banza ɗan talaka, dama haka kuke baku iya samun guri ba, kana wani sumi sumi da kai mara mutunci, dama gaba ɗaya siffofifinka na munafukai ne bari Alhajin ya dawo, sena sa anyi maganin ka, bazaka tashi ba kana jina ina magana "

Gaba ɗaya ran Yusuf ya gama ɓaci, kujera kawai wannan akanta ake masa wannan cin zarafin.
A hankali ya yunƙura ze tashi rai a ɓace, cikin tsawa da rashin mutunci Ramla tace
"ba magana ake maka ba ba zaka tashi ba, banza kawai ɗan talakawa, an kusa korarka kowama ya huta, dalla tashi sakarai"

"baze tashi ba, Kujerar ba wani ya kawo ta ya ajiye ba se mamallakin gidan, dan haka babu wanda yake da ikon cin zarafi ko korara wanda ni yakewa aiki a gidan nan, baku kuka ɗauke shi aiki ba, Kuma duk wanda yake tunanin ze kori wanda na ɗauka aiki sedai ya bar gidan nan tunda mutum ba gidan nasa uban bane"

Widad ce tsaye sanye da gajeren wando, da vest a jikin ta gashin kanta a kwance a kafaɗarta kamar yadda ta saba shigar ta, cike da isa da nuna tsantsar iko tayi maganar.
Ramla ta harzuƙa za tayiwa Widad rashin mutunci Amma Mummy ta hana ta.
Widad tace "ki ƙyaleta ta faɗi abunda take so mana, keda ita kun sani banbancin ku da masu gadi da direbobin nan kaɗan ne ai, dan haka ku tsaya iya matsayin ku, kar wanda ya ƙara shiga hurumi na da wanda yakemin aiki, wannan ya zama kashe dina da gargaɗi na na ƙarshe a gareku, babu ruwan ku da ma'aikata na, wallahi duk wanda ya kuma karyamin doka zanyi ba dai dai ba, na gaya muku"

Wani ƙululun baƙin cikine ya ƙule zukatan su, a gaban masu aiki tayi musu wannan cin zarafin da wulaƙanci, saboda wannan sakaran talakan.

Widad ta ɗago idanunta cike da rashin mutunci da tsantsar izza ta kalli Yusuf tace  "kai kuma biyo ni"
Jiki a matuƙar sanyaye Yusuf ya miƙe yabi bayan ta, kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, dan yasan tistiye shi zata yi da tambayoyi.

Share please

Ayshercool
07063065680

_*AƘIDATA*_

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Special thanks to all members of my Association
Perfect writers Association may Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will bring positive changes to our Community.

                           PART1
                                   Page 8

Jinjina kai Mummy tayi ta juya ta nufi part ɗinta, jiki a saɓule yaranta na suka bi bayanta.
Koda taje ɗakin ta safa da marwa ta shiga yi tana sauke wata nannuyar Ajiyar zuciya me bayyanar da tsantsar baƙin ciki da takaici.

Ramla ta numfasa tace  "Mummy akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa akan wannan ɗan iskan mutumin, na rasa Wani asiri yayi wa wannan daƙiƙiyar da take tozarta ki akansa, kawai kisa a kawar da shi daga hanyar ki mana"

A gigice Amal tace  "A'a Ramla, meye laifin sa? Laifin sa fa kawai ya hau kan kujera, shikenan Amma Widad ce tayi laifi anan bashi ba, kiyi tunani mana"

Ramla ta daka mata tsawa ta hanyar cewa "dalla rufe mana baki, dalilin wa akayi mana haka, a gaban masu aiki aka Wulaƙanta mu? saboda wanna ɗan matsiyatan ne me kama da mataccen silifas, wallahi Mummy ko baki ɗau mataki akan sa ba ni zan ɗauka, zan ɗau matakin da ya dace da shi da gaggawa"

Cikin hanzari Mummy tace "A'a Ramla da alama akwai Amfanin daze iya yi mana a nan gaba, nasa Isa mai gadi ya binciko min ɗan wace unguwa ne"

Ramala tace "Mama Isa megadin me? Me ze iya tsinanawa, kawai Kisa abi bayan sa kawai a gano inda yake, kuma ɗan uban waye shi"

Amal cikin sanyin jiki tace "dan Allah Mummy karkisa a masa wani abu dan Allah, abi komai a hankali"

Mummy tace "dalla rufemin baki sakarya!"

Ramla tace  "Mummy ƙyaleta dan Allah, me abun haushi kawai, Amma Mummy ta yaya ze iya mana amfani a nan gaba?"

Murmushi Mummy tayi tace "zan miki bayani Ramla, ba zanyi a gaban wannan shashashar ba, dan yanzu na kasa gane inda tasa gaba"

Widad kam, suna zuwa falonta ta tsaya ta juyo ta kalli Yusuf, ta ƙure shi da ido tun daga sama har ƙasa, yayin da shi kuma ya ƙi yadda ya ɗago ido ya kalle ta, ta daɗe tana kallon sa tana nazarinsa.

"Look up" ta faɗa a taƙaice, ɗan ɗagowa yayi ya kalleta ya maida kansa ƙasa.

"Ya aka yi na dawo gidan nan jiya? Meyafaru dani a gurin party jiya?"

Dama Yusuf yasan a rina, dan haka a dake yace

"Eh kin faɗi ne akan stage, shine muka taho gida"

"Malam ƙarya kake, ka gayamin meyafaru? Ko kaima kazo ne dan a haɗa kai da kai a cutar dani?"

Yusuf ya girgiza kai yace  "Me yasa kike tunanin za'a haɗa kai dani a cutar dake? Meye riba ta in an haɗa kai dani an cutar dake?"

"Saboda talaka ba abunda baze iyayi akan kuɗi ba, An haɗa kai da kai an turo ka ka cutar dani, in ba hakaba meyasa lokacin da nace kasa hannu a death contract ka yadda ba tare da ko ɗar ba ka cigaba da aiki dani? Wannan shi ne karo na biyu kana min ƙarya, meyasa? Ta yaya zan faɗi haka kurum bani da wani special case, se taɓin hankali, shima kuma ƙaƙabamin shi akayi, ta yaya haka zata faru? Bana tunanin na samu mental attack ne haka kurum a gurin nan, Ka gayamin gaskiya you are here to kill me, you were sent by someone to kill me " cikin ɗaga murya, tare da tsantsar rashin yadda take maganar.

Gaba ɗaya ta birkice, Yusuf yai shiru ya ƙura mata ido yaƙi cewa komai.

A fusace tace  "talk to me!!"

"Am not here to kill you, na karɓi aikin nan ne saboda shine last option ɗina, idan banyi aikin nan ba babu wata hanya da zan samu abunda zan kula da kaina da mahaifiya ta, talaka ze iya komai akan kuɗi, Amma be kai yadda me kuɗi zeyi ba, me kuɗi yafi talaka son kuɗi da aikata komai dan ya mallake su, da zan cutar dake da tuni nayi tunda kika amince kije ko ina tare dani, someone attempts to kidnap you yesterday night, that's all I know"

Dafe kai Widad tayi ta shiga sintiri a gurin, gaba ɗaya idonta yayi Ja se gumi take, a hankali ta  furta
"Jeka falo ka jirani, zamuje gidan Bulama yanzu"
Yusuf ya jinjina kai ya koma babban falon.

Kusan mintuna sha biyar yana jiran ta sannan ta fito, yauma dai babu batun mayafi balle hijjabi a jikin ta, haka suka fita.

Alhaji Haruna ne mahaifin Nurat ɗauke da waya a kunnen sa yana waya, yana yi yana sharce gumi duk da sanyin Na'urar sanyaya ɗaki dake ɗakin amma gumi yake yakicewa, cikin inda inda yake cewa
"wallahi ranka ya daɗe seda aka shirya komai, dan yarinya ta Nurat ta tabbatar min da taje gurin party, taje gidana, dan an gama komai an sumar da ita, ana jiran sahu ya ɗauke azo a ɗauke ta, wani matashi yayiwa Yarinya ta barazana ya ɗauke ta ya tafi da ita, kuma ni a iya sanina ko su Alhaji Musa da muke komai tare dasu muke neman abu ɗaya basu san mun ƙulla alaƙa da kaiba balle ince haɗin baki ne"

Ɗaya ɓangaren yace  "Shikenan zanyi wani shirin na mussman, Amma idan ka bari muka kuma rasa damar mu a karo na biyu zan ajiye ka a gefe in nemo wani"

"Insha Allah baza'a sake samun matsala ba Alhaji Bukar"

Alhaji Bukar yace "Allah yasa, sannan batun wannan matashin kabar komai a hannu na, nasan abunda zanyi"
"Shikenan godiya nake ranka ya daɗe " daga nan suka yi sallama.

************************
Bayan fitar su Widad, Mummy tasa aka kira mata Isa mai gadi.
Isa yaje ya same ta a falo, cikin rawar jiki ya gaida ita ta amsa masa a wulaƙance ta kalle shi tace
"Kai na baka aiki amma har yanzu nani shiru ko bazaka iya bane?"
"A'a ranki ya daɗe, yaron ne gaba ɗaya baya sakin jiki damu yanzu, wani mugun jin kansa yake kamar wani basarake"

Ta jinjina kai tace  "tabbas nima naga hakan, kuma da sannu zan kawo ƙarshen wannan izzar da yake ji da ita, talakan banza asararre, kaje kayi abunda na saka, bana so yasan nasa a bibiye shi ne, ka nemo min inda yake zaune, zan sa ayi maganin sa, tashi ka koma bakin aikin ka"

Ya tashi sumi sumi ya fice.

***********************

Yusuf suna zuwa gidan Bulama suka yi sa'a yana nan, a harabar gidan suka ganshi yana shan lemo, hannun sa ɗauke da Jarida.
Ɗago idon da yayi ya sauke akan Widad yasa shi sakin murmushi, itakam fuskar nan a murtuke ba annuri.

Alhaji Bulama yace  "barka da zuwa lovely daughter"

A ɗan ciki tace  "barka da hutawa Daddy"

"Yawwa barka lovely daughter, ya akayi ne na ganki a haka? Meke faruwane? Ko ciki zamu shiga?"

Yusuf a ransa yace "wata sabuwa, yau kuma Alhaji Bulama take kira da Daddy, idan taga dama kai tsaye take kiran sa da Bulama, wannan yarinya akwai ta da rikici, bata da Alƙibila sam"

Ta yamutsa Fuska tace

"A'a nan ma ya isa, Amma Daddy akwai matsala fa"

Ya tattaro hankalin sa kanta yace  "matsalar me daughter"

"Ana farautar rayuwa ta har yanzu, daga fita jiya aka kusa saceni, nidai tunda Daddy baya nan kamin visa zan bar ƙasar nan, gara in ƙarasa Rayuwa ta a can ƙasashen wajen"

Alhaji Bulama yace "waye yayi attemptin ɗin sace ki, kuma a ina? Shiyasa tuntuni nace a samo masu tsaron lafiyar ki"

"Bashi da mahimmanci kasan inda naje, da wanda yai yunƙurin saceni, duba da tsawon shekaru kun gaza maida hankali ku gano hakan, kuna ɗaukar wasu maganganun nawa  a matsayin maganganub hauka, kawai ka nema min visa zan bar ƙasar nan"

"Haba lovely, saboda me zaki bar ƙasar ki ta haihuwa? kije ki cigaba da rayuwa ke kaɗai a wata uwa duniya? Nace a ɗaukar miki masu tsaron lafiyar ki da zasu dinga miki rakiya kinƙi, kin ɗakko wannan dogarin duk inda zaki yana biye dake kamar inuwa, shiba soja ba, shiba wata tsiya ba ta ina ze iya tsare lafiyar ki?" yai maganar yana nuna Yusuf

Widad ta haɗe fuska tace  "kaikam wani lokacin se in rasa meke damun ka, aini babu me tsaron lafiya ta se Allah, Akan me zan ɗau masu tsaron lafiya ta, haka kurum a haɗa kai da masu tsaron nawa a cutar dani? I don't trust anyone"

Alhaji Bulama yace "shi wannan ɗin kina da tabbacin baza'a haɗa kai dashi a cuce ki ba?"

Ta juya ta kalli Yusuf dake tsaye, sannan ta kalli Bulama tace  "Ba'a kansa muke magana ba yanzu , babu ruwanka kasancewarsa tare dani, muna magana akan Visa zakamin in bar ƙasar nan kawai"

"wai tayaya zan miki visa ki bar ƙasar nan? Keda muke saka ran Dawowar Fahad in next couple of weeks a fara zancen Auren ku, meya.......

"shut up please! " ta faɗa a hasale tana ɗaga masa hannu sannan ta ɗora da cewar

" wai har yanzu baka janye wannan banzan ƙudurin naka ba ko? Kana tunanin abunda na gaya maka ƙarya nake, let me repeat myself, bazan yi Aure ba, babu namijin daya dace dani, ni ba zanyi Aure in zauna a ƙarƙashin wani ba, Allah ya bani dukiya wadda ta isheni rayuwa, bana buƙatar wani Aure, hankalina na kan son ganin bayan maƙiya na, koni ko su, ko kuma muyi mutuwar kasko"

"Widad, dukiya shirme ce idan babu Soyayya da kulawa, ban hanaki gano wanda suka rusa farincikin rayuwar ki ba, Amma aure yana da mahimmanci a rayuwar ki, bakya son ganin 'ya' yan ki a duniya? Aure garkuwa ne Widad"

"Soyayyar banza, is just stupidity and form of mental disorder,  an imagination and bunch of problems, bana buƙatar soyayyar kowa, nikaɗai zan gudanar da rayuwa ta, na ishi kaina rayuwa bana buƙatar kowa yayi min garkuwa"

Zuwa yanzu Yusuf ya saba jin ire iren wannan maganganun na Widad, Amma yana kallon ta a wani iri idan yaji tana faɗin wannan kalaman, ta yaya mutum zece ze rayu shi kaɗai, ba abokin rayuwa ba 'yan uwa ba Abokan Arziki? Kafin ya bawa kansa amsar tambayoyin ya tsinkayi murayarta tana cewa

"Wallahi ko kana so ko baka so, ba zan cigaba da zama a ƙasar nan ana farautar rayuwa ta ba, kuma ba zanyi Aure ba babu shi a tsarina"

Bukama yace "Aini bance dama ki zauna a ƙasar nan dole ba, da zarar an ɗaura miki Aure ƙasar nan zaku bari gaba ɗaya keda mijinki, kinga kin tsallake tarkon maƙiyanki"

Cikin izza me bayyanar da tsantsar ikon da take dashi tace
"Wani tabbaci kake da shi shi ɗan naka baza'a haɗa kai dashi a cutar dani ba?"

"Idan har ɗan dana haifa ze cutar dake, da nine mutum na farko da ze cutar dake da mahaifinki, dan a yanzu mahaifinki bashi da ka mata"

Widad ta miƙe tsaye ta dafa teburin ta kalli idon Bulama tace
"Zan bar ƙasar nan ko kana so ko baka so, kuma bazan Auri ɗanka ba, babu Aure a tsari na, ina fatan wannan ya zama karo na ƙarshe da zan gaya maka babu Aure a tsarin Rayuwa ta, Ganin bayan maƙiya na shine a gaba na"

Ta juya ta nufi inda Yusuf yayi parking ɗin mota, da sauri Yusuf ya riga ta ƙarasawa ya buɗe mata gaban mota, dan bata zama a bayan Mota.

Yusuf ya fara tuƙi ba tare da ta kalle shi ba tace  "Muje Farm House" shima be ce mata komai ba, ya ɗauke kan motar zuwa hanyar gidan gona.
Suna tafe Yusuf yana tunanin wani dalili ne yasa kowa yake tsoron Widad haka? Take faɗawa kowa abunda ta ga dama komai tsufan sa kuwa? Indan Mahaifinta yana da kuɗi ne, suma ai masu kuɗi ne.

Bayan tafiyar su Widad Bulama na nan inda suka barshi yana zaune yayi shiru, Matarsa Hajiya Sarah ce ta fito da shirin ta tsaf, da alama fita zata yi.
Inda Alhaji Bulama ke zaune ta nufa, ta samu kujera ta zauna ta kalle shi tace 
"Ya dai? Wannan dogon tunanin fa? Shekaru sun fara ja, dogon tunani be kamace ka ba"

Ya sauke Ajiyar zuciya ya kalle ta yace  "dole inyi dogon tunani, Yanzun nnan Widad ta bar gidan nan, lamarin yarinyar nan kullum ƙara taɓarɓarewa yake, wai ita ba zata yi Aure ba kwata2, haka zata ci gaba da zama, Rayuwa zata yuwu a haka? "

Ɗan taɓe baki tayi tace  "waini Alhaji meye nasa damuwar 'yar wani a ranka? Naga dai ba kaine ubanta ba, taje tayi abunda taga dama mana"

"A' a Sara, Kin san yadda nake da Mahaifinta, damuwata tasa ce, damuwar sa ta wace, kuma har yanzu ana kainata hari, nace a samo mata masu tsaron lafiyar ta, taƙi se wannan yaron da take yawo da shi, kome ze tsare mata oho?"

"to ku ƙyaleta tayi abunda ta ga dama mana, tunda bata san abun Arziki ba, dama ba dole a cigaba da kai mata hari ba wannan Wulaƙanta mutane da take, Yarinya ƙarama se baƙar Aƙida"

"A'a be kamata a ƙyaleta ba Sarah, nifa mun yanke shawarar zamu haɗa ta Aure ne da Fahad"

Kallon sa tayi galala sannan tace 
"ban gane haɗa ta Aure da Fahad ba? Wannan Yarinyar mara tarbiyya da bata san Darajar mutane ba zaku haɗa da Fahad, ko manta Fahda ɗin shima yadda yake da saurin Fushi da zuciya? Tabbas babu inda wannan Auden zeje, gara ma karka fara"

"Babu ruwan ki, Insha Allah zasu zauna lafiya"

Miƙewa tayi tsaye tace  "Ai se ayi in gani, ni na haifi abuna ba wani ya haifar min ba, bame Aura masa Mahaukaciya mara tarbiyya"

Ta ɗau jakarta ta bar gurin tana ƙunƙuni.

Yusuf ne zaune ya zubawa sarautar Allah ido, Widad ce take zaga dabbobin gidan, wanda mafi Akasari karnuka ne da maguna se tsuntsaye, Abunda ya bashi mamaki shine yadda tasa aka fito mata da wani jibgegen ingarmar doki, aka ɗaura masa linzami, ta ajiye Wayarta ta da 'yar ƙaramar Jakarta, ba tare da an taimaka mata ba ta haye kan dokin nan.

Kasancewar harabar gidan ƙatuwa ce sosai, hakan yabawa Widad damar yin sukuwa akan dokin nan yadda take so, ba ƙaramin ɗaurewa Yusuf kai tayi ba, yadda take sukuwa akan dokin tana sarrafa akalar sa yadda take so, ze tabattar maka ta saba hawan dokin, kuma ga dukkan Alamu hakan yana bata Nishaɗi.

Seda tayi me isar ta sannan taci birki ta sauka daga kan dokin, ta shiga cikin gidan.
Yusuf yana nan zaune ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan wanda Aƙalla ze shakara talatin da wani abun ya ƙaraso inda Yusuf yake zaune shima ya zauna kusa dashi.
Ya miƙawa Yusuf hannu suka gaisa, ya kalli Yusuf yace
"ɗan Samari daga wani gari kake ne?"
Yusuf  ya ɗan ƙura masa ido Sannan yace  "Kano"
Mutumin Yayi Murmushi yace  "Ashema ɗan garin nan ne kai, a wace unguwa kake?"
Yusuf yace  "Me yasa kake tambaya ta ne?"

"Ahh karka damu kawai dai na tambaya ne, Amma idan ba zaka damu ba, dan Allah wani irin aiki kakewa Madam haka da take yawo da kai ko ina? A iya sanina da ita tun shekarun baya bata sake wa da mutane haka, Amma kai gashi tana yawo da kai ko ina"

Yusuf yayi Murmushi yace
"Ita yakamata ta baka wannan Amsar bani ba"

Suna cikin maganar ne Widad ta fito sanye da wasu kayan daban.
Ƙure Yusuf da Saleh tayi ido, tana musu kallo irin na tuhuma, ba tace komai ba ta nufi inda Motar su take, Ma'aikatan gidan suka biyo ta suna mata kirari suna Allah ya kiyaye, bata kula kowa a cikin su ba ta hau motar Yusuf ya ja suka bar gidan.

Suna cikin tafiya yaji tace 
"Me Sale yace maka?"

"Waye Sale?" Yusuf ya tambaye ta, shiru tayi masa tsawon wasu daƙiƙu sannan cikin maganar ta ta isa, tace 
"Kana jin daɗin rainamin hankali a lokuta da yawa, na kan ƙyaleka ne saboda ina jin nauyin hukunta ka a lokuta da yawa, saboda hatsarin da rayuwar ka ke ciki Kasancewar ka tare dani, Amma hakan baze hanani koya maka hankali idan ka saɓawa Yarjejeniyar mu ba, na tambaye ka ɗazu da Safe baka bani haƙiƙanin Amsar tambaya ta ba, ka rainamin hankali, yanzu ma na tambaye ka kana sake tambaya ta, wannan abubuwan da kake kana jawowa kanka zargi ne a gurina, karo na biyu Me Sale yace maka? "

Murmushi Yusuf yayi yace
"Ya tambaye ni Sunana ne, da kuma aikin danake miki, na gaya masa sunana, Amma aikin da nake miki nace ya tambaye ki"

Jinjina kai tayi tace  "Amma kamar na gaya maka duk inda muka je, ba zakayi magana da kowa ba se idan ni nayi maka izinin yin hakan"

Juyowa yayi ya kalli Widad, Yarinya ƙarama se izza da jin kai.

Yusuf ya ɗan rausayar da kai yace
"Allah ya baki yawan rai ya kare ki daga sharrin maƙiyanki, banyi hakan da saɓa dokarki ba, sedai idan nayi hakan mutane zasu ga tamkar wulaƙanci ne, nasan tsoron ki kar a haɗa kai dani a cutar dake, Amma ina tabbatar miki da cewa bazaki taɓa samuna da cin amanar ki ba"

Ba tare da ta kalle shi ba tace
"Zan gani ai"

Sunyi shiru na wani lokaci, can ta jinjina kai tace 
"Lallai Sale, kar nake kallon sa, yana son ganin bayana saboda abunda nayiwa ɗan uwan sa, duk randa na kama shi red handed wallahi se yaje inda ɗan uwansa yaje, babu Amfani zama da maƙaryaci me cin Amana"

Yusuf ya juya yana kallon ta, yana tunanin randa ta gano waye shi, wane irin mataki zata ɗauka akan sa?

****************************
A kwana a tashi Yusuf yayi wata guda cif yanawa Widad aiki, kullum cikin hantarar sa take da wulaƙanci amma sam seya nuna mata ko a jikin sa, duk abunda yayi baze burgeta ba, yayin da Amal keta ƙara tura kai a gurin Yusuf, dan ita nan duniya babu wanda yayi mata kamar shi tana matuƙar ƙaunar Yusuf saboda nutsuwar sa, Yusuf yana ta ganin Abubuwa na ban mamaki a game da uwar ɗakin sa yayin da gefe guda ya kasa gane bakin zare al'amuran gidan nan, gaba ɗaya yanayin yadda mutanen gidan ke gudanar da mu'amalarsa da ban mamaki dan kowa da inda yasa gaba kuma kowa akwai wani boyayyen abu da yake ɓoyewa a ransa.
Har wata ya cika, aka shiga wani watan Widad bata biya Yusuf haƙƙin sa ba, shi kuma bece mata komai ba, sannan duk lokacin da ta buƙaci zuwa wani guri, zeje ya kaita ba tare da ɓata lokaci ba.

Isa me gadi yana ta ƙoƙarin bugun cikin Yusuf yaji wani abu game da shi amma Yusuf yaƙi gaya masa komai.

Gaba ɗaya ma'aikatan gidan suka tsangwami Yusuf suna ganin ana fifita shi akan su.
Shikam ko a jikin sa, shima ya dena shiga harkar su, har gara Murtalah me kuka da shuke shuken gidan suna hira da Yusuf wasu lokutan.

Hajiya Halima na zaune a falo tana aiki a System, gefen ta kuma Amal ce ke cin Abinci, mai aiki ta fito daga sashin Widad, ta durƙusa a gaban Mummy tace
"Hajiya, Anty Widad fa tun jiya ɗakin ta a rufe, na ƙwanƙwasa taƙi buɗewa, tun jiya da safe naje in gyara mata amma ɗakin a rufe"
Tsaki Hajiya Halima tayi tace  "To ina ruwana, yarinya ce ita ƙarama da zan dinga binta, in taji yunwa zata kashe ta ta fito"

Amal tace  "Mummy kina tunanin Yunwa zata saka ta fito ne? In baki wasa ba sedai kiga gawar ta kin san halin ta, idan ta mutu da wani kalamai zaki ƙwaci kanki a gurin me gidan nan? Bama ke kaɗai ba dukkan mu, sannan Burinmu baze cika ba, ƙarshe ma dukkanmu sedai mu mutu a prison"

Ɗan zaro ido Mummy tayi tace  "Kuma fa hakane, tashi muje mu gani"

Suka nufi part ɗin Widad, Amma suka tarar ta rufe bedroom ɗinta, suka yi bugun duniya taƙi ta buɗe.

Rasa abunyi suka yi, suka kira Alhaji Bulama suka sanar masa da abunda ke faruwa, da kiran wayar tasa beyi mintuna Arba'in ba se gashi.

Yaje ya tarar dasu sunyi cirko cirko a ƙofar ɗakin Widad, ya taka yaje gaban ƙofar ya fara ƙwanƙwasawa
"Lovely daughter, Dad ɗinki ne, ki buɗe ƙofa kinji, karkiwa kanki illa"
Still Widad ba tayi responding ba, dan ko motsin ta basaji.

Alhaji Bulama yace 
"Kuma babu wani abu daya haɗaku da ita? Kowani saɓani ko ayi mata wani abun?"

Ramlah tace "waze nata wani abu kuwa? Ita wannan se an mata wani abu? Ai sedai tayi wa wanima,wataƙila haukan nata ne ya motsa"

Alhaji Bulama yace "ku bani mukullin ɗakin ta, a buɗe ɗakin karta"

Mummy tace  "taɓ wake da mukullin ɗakin basarakiya, ita da bata yadda da kowa ba, wa zata bari ya mallaki mukullin ɗakin ta ba wanda yake da mukullin ta"

Alhaji Bulama yace  "to ko maza za'a kirawo su ɓalla ƙofar a gani"

Ramlah tace  "A'a karka jamana Jaraba, a ɓalla mata ƙofa ka samu a tashin hankali da masifarta, a kira Baban ta aji meze ce"

Alhaji Bulama yace  "Keba babanki bane Ramlah"?

Cikin tsiwa Ramlah tace  "Niba baba na bane, kullum bata da gori seba gidan ubanmu bane, dan haka ubanta ita ya haifa bani ba"

Yau Yusuf ya makara dan se sha ɗaya ya tashi na safe, tunda ya koma bacci ƙarfe takwas na safe, dan haka a gurguje ya kintsa ya fito, yayi sa'a Umma bata nan ta fita, dan haka ya kulle gidan ya fita, ya nufi gidan su Widad.

Yana zuwa suka gaisa dasu Nura sama sama,suna masa wani kallon banza

Yusuf ya kalli Murtalah yace "Murtalah Madam ta fito kuwa? Ko tazo nema na naga yau na makara sosai"

Murtalah yace  "ina fa, tana can tun jiya taƙi buɗe ƙofa, ana can anata fama da ita, ba wanda yasan tana raye kota mutu, gashi babu wanda yake da mukullin ƙofar ta, ana tunanin ko ɓalla ƙofar za'ayi

Zaro Ido Yusuf yayi ba tare da yace komai ba, ya tashi da sauri ba tare da tunani komai ba ya tun kari cikin gidan.

Isa ya taɓe baji yace "kalli uban shisshigi, Allah yasa yana zuwa su Wulaƙanta shi su koro shi, banza me rawar kai kawai"

Murtalah yace  "Haba Isa, ka sawa Yusuf ido da yawa wallahi, gashi kullum ƙara samun matsayi yake a gidan nan fiye da kai"

"dalla rabu dani, se kace baka ganin yadda aka fifita shi akanmu a gidan nan, danma mun samu mu Hajiya tana bayan mu, duk yadda muka so samun gindin zama a gurin yarinyar nan muka kasa, Amma shi daga zuwan sa ga yadda ya samu sake yake wani zaƙewa kamar gidan ubansa"

Yusuf kuwa na shiga Babban falo ya gansu a zazzaune suna tattaunawa, Ya durƙusa ya gaishe su.

Alhaji Bulama ne kawai ya amsa, se Amal da tace "Sannu da zuwa"

Hajiya Halima tace  "To Munafuki me ka shigo yi uban iya"

Yusuf yace "Naji ance Madam bata fito daga ɗaki ba yau kwana biyu shine nace.....

Cikin hantara Ramla tace "shine me, mezaka iya? Bama son munafunci malam jeka mungode, Anjima baban ta ze dawo, yasan yadda zeyi da ita uban shishshigi"

Yusuf yace "Amma be kamata a barta har se ya dawo ba, babu wanda yasan halin da take ciki, ta rufe kanta a cikin ɗaki yakamata a duba halin da take ciki"

Hajiya Halima tace  "kai bana son rawar kai irin naku na matsiyata, ka fimu sanin abunda ya dace ne? Dalla ɓacemin daga nan"

Alhaji Bulama yace  "A'a Hajiya Halima, kika san Alaƙar dake tsakanin su?, ki ƙyale shi ya Jarraba mana wataƙila kiga ta buɗe ƙofar, kaga tashi kaje ko zata buɗe"

Yusuf ya miƙe ya nufi hanyar ɗakin ta.

Yana zuwa ƙofar ɗakin ba tare da ɓata lokaci ba, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko mukullayen motocin ta dake gurin sa, ya saka key ya buɗe ɗakin nata, da yake yasan mukullin ƙofarta ta falo da ta bedroom tunda tana aiko shi ɗakin.

"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!!!"

Shine abunda Yusuf ya faɗa

In an karanta ayi share please 🙏

07063065680
Ayshercool

_*AƘIDA TA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

                          PART1
                                Page 9


_Asslam Alaikum warahmatullah_da _fari dai zanyi wata magana_ _tun page ɗin farko nayi bayani_, _nace ina da Jarrabawar ƙarshe_, _ina ƙoƙarin cika Alƙawari ne yasa na cigaba da kawo_ _littafin nan ɗaya ga watan October_ _nace bazan samu yin posting kullum ba_ _amma ina iya ƙoƙarina inga nayi duk dan faranta muku_ _amma wasu na ƙorafi hadda gayamin baƙar magana_  _dan bana posting kullum_  _littafin nan dai nina sa kaina_  _kuma nace free ne balle ace siya akayi nake jan rai_ _babu wanda nayiwa dole seya karanta_ kuma ban karɓi kuɗin kowa ba, _ni nake saka data in ɓata lokacina inyi typing sannan inyi posting_  _dan haka wanda baze iya haƙuri ba ze iya dena karantawa_ ba zanyi _typing kullum ba tunda ba siyarwa nayi be_
_Ni bana Wulaƙanta kowa nasan soyayya ce tasa ake karanta littafina

_
_Masoya har kullum ina sake godiya da Comments ɗinku da Addu'oinku_ _zancigaba da ƙoƙarin faranta muku Insha Allah_





Widad ya hango zaune acan ƙarshen gado kamar Mahaukaciya tuburan, rigar jikin ta iya cinyar ta, gaba ɗaya gashin kanta a hargitse, ta sunkuyar da kanta jikin ta se rawa yake tana kuka, ta rufe ko ina babu haske a ɗakin, seda ya buɗe ɗakin sannan haske ya bayyana a ɗakin.

Babban abunda ya bawa mutan gidan mamaki be wuce yadda akayi Yusuf ya mallaki mukullayen ɗakin Widad ba, alhalin su raɓar ɗakin nata ma basu isa suyi ba, balle samun mukullayen.

Da sauri ya ƙarasa gaban gadon ta yana ambaton Subhanallah,tana  ɗagowa taga Yusuf ta gigice ta fara ja da baya tana girgiza kai.

Yusuf yace  "Meya sameki haka? Ki kwantar da hankalin ki, Yusuf ne direban ki fa"

Girgiza masa kai tayi tana kuka tace  "Ni karka kasheni"

"No ba kashe ki zanyi ba"

Ɗaga kai tayi ta kalli su Alhaji Bulama dake tsaye suna kallon su, riƙo rigar Yusuf tayi kamar zata yagata tace  "Suwaye wannan? kace su fita bana son ganin su, kace su fita su bar nan" ta faɗa cikin ɗaga murya da zubda hawaye.

Yusuf ya zauna yace 

"Calm down, kinga fa wancan Dad ɗinki ne Alhaji Bulama, ga Mummy, ga Ramlah ga Amal, sune baki gane ba?"

Alhaji Bulama ya tako yazo inda suke, ya miƙa hannu ze riƙo Widad.

Wata irin ƙara ta saki, ta rirrƙe Yusuf tana ɓuya a bayan sa tana girgiza kai, cikin ƙaraji take cewa
"Ni su fita, su fita su bar nan gurin, kasheni za suyi, kana kallo nima zasu kasheni, bana son ganin su ba wannan ne Daddyna ba kuma bashi ne Bulama ba"

Yusuf yace  "buɗe ido ki kalle su fa, ga Daddy Bulaman nan s tsaye a gaban ki"

Girgiza kai tayi tace "bashi bane ba, na gaya maka bashi bane"
Ta rungume Yusuf gam tana ci gaba da zubar da Hawaye.

Yusuf a ransa yace  "ta tabbata kenan Widad tana da taɓin hankali? In ba haka ba meze sa ta koma haka?"

Alhaji Bulama yace "Karka damu dama tana yin hakan wani lokacin, ciwonta ne ya tashi"

Ihun da take yi ne iya ƙarfinta, kai kace wadda ake yankawa, ba shiri suka bar ɗakin Amal wani irin baƙin kishi ne ya cunkushe zuciyarta, yadda Widad ta rungume Yusuf yafi komai yi mata ciwo.

A hankali Yusuf yace  "Kinga sun fita ba kashe ki za suyi ba, cikani ki ga wani abu"

Girgiza masa kai tayi "tace ni A'a tsoro nake ji, kasheni za'ayi nima an kashe Ammi nima kasheni za'ayi"

Yusuf ya girgiza mata kai cike da damuwa yace "Ai ina nan tare da ke, ba inda zani babu me taɓa ki idan ina nan insha Allah , ba wani abun tsoro fa"

A hankali ta cika Yusuf tana sauke Ajiyar zuciya, hawaye na cigaba da bin fuskarta.

Yusuf ya kalle ta yace  "je kiyi brush se kici Abinci, ance tun jiya baki ci Abinci ba"

Girgiza masa kai tayi Alamar A'a.

"Idan baki abunda nace ba, zan tafi in barki anan suzo su tafi dake"

A firgice ta kalle shi, ya jinjina mata kai alamar eh,  rigarsa ta kuma riƙewa gam ya rakata banɗaki ta wanke baki, ta fito, tana ta binsa da kallo kamar taga wata halitta daban.

Da yayi hanyar fita seta biyo shi tana sake rirriƙe shi, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi, ya ɗauki bedsheet ɗin dake kan gadon ta ya ɗaura mata, ya ɗakko hula ya saka mata.

Alhaji Bulama ya kalli Hajiya Halima yace "Nayi mamakin abunda ya tayar da ciwon Widad, na zata tuni ta warke?"

Hajiya Halima ta taɓe baki tace  "to ni ina zan sani, daga ita se ubanta se kuma kai suke sakawa a lamarin su, ta yaya zan san kota warke ko bata warke ba"

"Amma abun da mamaki, Akwai buƙatar ta cigaba da ganin likitan ƙwaƙwalwa kenan?"

"Wannan kuma ya rage shawararka kai da Mahaifinta, ni 'yar kallo ce ai tunda alamu sun nuna haukan yana nan tuburan"

Bulama yace "Hajiya Halima ai ba kyace haka ba ɗa na kowane"

"A'a wannan dai bata kowa bace, ta babanta ce kawi, ka dena wannan maganar nawa' ya'yan dai nawane, itama 'yar wasu ce"

Ƙyalƙyalewa da dariya Alhaji Bulama yayi yace  "Shikenan tunda haka kikace, ni dai na tafi, Munyi waya dashi Megida kafin inzo nan yace yana kan hanyar dawowa, zezo ya dubata idan jikin da sauƙi ya koma, idan kuma da yuwuwar a maida ita ga likitocin ƙwaƙwalwa shikenan, dan be gama abunda yake ba ze yanke ya dawo, kin san idan bata da lafiya baze iya komai ba, Allah ya bata lafiya"

Hajiya Halima tace "Karma Allah yasa tayi lafiyar, Ita da ubanta ya shafa bani ba"

Alhaji Bulama ya girgiza kai ya fice.

Yusuf Ya kira Amal a waya, ta ɗaga tana tura baki, dan gaba ɗaya kishin Yusuf take, Yusuf yace 
"Amal dan Allah ki kawo Abu me ɗan ɗumi a bata taci, da alama tana jin yunwa sosai"

"wallahi Yusuf ba dan kai ba ko zata mutu ba zan kawo komai taci ba, kaima ɗin dai kawai zan kawo ne"

"Yi haƙuri, Nagode sosai da kika min Alfarma"

Amal ta shiga kitchen ta haɗa kayan tea, Mummy tace "Me zakiyi da tea  ranar nan?"

"Widad za'a bawa" ta bata amsa

"ke meye naki a ciki to?"

"Mummy wai so kike se duniya tasan halin da muke ciki ne? Kar hankali ya dawo kanmu, Ai se munayi muna ɓadda sahu"

Mummy tai murmushi tace  "daɗina dake wani lokacin akwai hankali, ɗakkomin Jakata a ɗaki"

Amal taje ta ɗakko mata jaka ta dawo, sannan ta ɗau tray ɗin ta tafi part ɗin Widad.

Yusuf ya miƙe da nufin karɓo kayan tea ɗin, Amma Widad ta riƙe rigar sa tabi bayan sa tana zare ido.

Yusuf ya kalli Amal yace "dama Amal dagaske Widad nada taɓin hankali?"

Amal tace "gashi kuwa kana gani tana yinsa tuburan"

Cikin tsawa Widad tace
"niba mahaukaciya bace, ka gaya musu niba mahaukaciya bace, su suka haɗani da hauka, su suke maida ni mahaukaciya, Amma niba mahaukaciya bace"

Gaba ɗaya Yusuf ya rikice, yace "is Ok ai dama ke ba mahaukaciya bace, ki kwantar da hankalin ki"

Amal ta kalli Widad tace  "kina wannan tamɓelen kike cewa ke ba mahaukaciya bace? Kalli fa abunda kike yi mahaukaciya ce ke tuburan, dan me hankali baze abunda kike ba"

Yusuf yace  "Haba Amal, ya ana ƙoƙarin kwantar mata da hankali Amma kike tinzira ta"

Amal ta zumɓura baki tace "kaga ni karɓi kayan nan, kalli yadda take wani riƙe ka aikin banza kawai"

Widad ta shammace ta, tasa hannu ta kifar da farantin ruwan zafin, aikuwa ya zube a ƙafar Amal, Ihu Amal ta saki, wanda ya janyo hankalin Mahaifiyar ta da Ramlah suka taho da sauri.

Idan ba gizo idon Yusuf yake masa ba, tabbas kamar ragowar ƙwayar magani ya gani a ƙasan kofin da'aka zuba tea ɗin, sedai kafin yayi wani yuƙuri

Hajiya Halima taƙarsaso tana cewa  "lafiya, meye haka?"

Cikin kuka da azaba  Amal tace "Mummy, Widad ta ƙonani da ruwan zafi, Mummy ƙafata"

Mummy ta kalli inda Yusuf ke tsaye, Widad na riƙe da shi tace 

"To maye Jarababbe, ka lallaɓa ka Asirce ta ita da uban ta, shine ka koma da baya zaka illatamin 'ya ko? Wallahi ka kiyayeni, kuma kafin kasa kwaɓata tayi ruwa ni zanyi maganin ka, ke kuma" ta nuna Widad dake bayan Yusuf tace
"dan Ubanki ba dai hauka ba, a haka zaki ƙare, Hauka yanzu kika fara shi, daga nan har ƙarshen rayuwar ki, keda hankali sedai ki ganshi a gurin wasu, wannan haukan haka zaki mutu kina yinsa"

Widad ta Jijjiga Yusuf tace  "kai ka gaya musu niba mahaukaciya bace, kuma wallahi idan ta kasheni itama sena kashe ta, gaba ɗayansu sune zasu kasheni, suna tace min mahaukaciya zasu kasheni, wallahi in baka hana su ba ni zan kashe su"

Ramla tace "kaga Malam dalla cikata kazo ka bar gidan nan, tunda babu gadon ka a ciki, ba'a haɗa kuɗi da matsiyacin uban ka an gina ba"

Wani irin kallo Widad takewa Ramla daga bayan Yusuf.
Kallon da Widad kewa Ramla ne yasa taga kamar Widad ta dawo hankalin ta.

Widad tace  "idan ka tafi ka barni kasheni za suyi, kashe mutane suke yi fa"

Mummy tace  "uwarwa muka kashe miki? Mu bama kisa kumako bamu kashe ki ba mutanen da kike Wulaƙantawa suna nan suna bibiyar ki zasu kashe ki, Mahaukaciyar banza da ta wofi, Allah kaɗai yasan me sukeyi da harta yarda da shi haka, dalla kuzo mu tafi suje su ƙarata, Allah ya ƙara birkita ƙwaƙwalwar ki zauna a haka koma samu mu huta, in ƙwaƙwalwar ki ta birki ce ta Ubanki ma ta birkice kowa ya huta da iskancin ki"

Ramla tace " Mummy watch your words fa, kina ta sakin layi mu tafi kema Amal Allah ya ƙara, maganinki kina ma wannan ɗan isakan direban shisshigi, gashi ai sun ƙonaki a banza nan gaba ma illataki zasuyi"

Shiru Yusuf yayi yabi bayan su da kallo, gaba ɗaya tausayin Widad da Mahaifinta ya kama shi.

Ya lallaɓa Widad ya bata youghurt da ƙyar ta sha, tana sha tana masa surutai na shirme, irin na masu taɓin hankali.

"Menene dalilin samun taɓun hankalin Widad?" Yusuf ya tambayi kansa

Kwanciya tayi a jikin sa tana lumshe ido alamar bacci take ji, ƙirjin Yusuf se bugun uku uku yake, Kasancewar ya keɓance da Widad, abunda be taɓa yi ba, a duk lokacin da yayi yunƙurin rabata da jikin sa seta saka ihu kamar ƙaramar yarinya.

Yusuf yayi mamakin iri maganganun da Hajiya Halima da 'ya' yanta suka dinga faɗa akan Widad, koda yake ba abun mamaki bane, duba da Yadda Widad ɗin ke Wulaƙanta su, Amma me sukayi mata take musu haka? " Yusuf yayi Alwashin tone duk wani abubuwa da ake ɓoyewa, kuma ya ƙudurce a ransa zeyi duk me yuwuwa ya jure wulaƙancin Widad yaga ta ina ze temaki rayuwar ta.

Yusuf yai shiru yayi zurfi a cikin tunani, yaji Widad tana ajiyar zuciya alamun tayi bacci, a hankali ya zame ta daga jikin sa, ya kwantar da ita ya lulluɓeta ya fita ya kulle ta a ɗakin yaje yai salla.

Ana idar da Salla Isa yace " Yusuf ashe uwar ɗakinka ce babu lafiya? Ance taƙi buɗewa kowa ƙofa amma tana jin muryar ka ta buɗe, gaskiya kai ɗan baiwa ne, Amma naji ance haukan nata ne ya tashi ko?"

Yusuf ji yayi kamar ya kwaɗawa Isa mari, Amma ya ƙyaleshi ba tare da yace masa komai ba.

Ya koma ɗakin nata ya tarar bata farka daga baccin ba.

Falon ta ya koma yana tunani, Ba zato ba tsammani yaji sallamar Mahaifin Widad a falon, Amsawa Yusuf yayi cikin girmamawa tare da risinawa.

Alhaji Nasir a ɗan ruɗe yace "Sannu babban Mutum, ya me jikin kuma?"

"Alhamdilillah, ta samu bacci"

"Masha Allah"

Yasa kai ya shiga bedroom ɗin, ya taka a hankali zuwa gaban gadon Widad ya zauna a gefen ta ya ɗagota, idon ta a rufe tana bacci, ya shafa kanta yace
"Allah ya baki lafiya my daughter" ya kalli Yusuf yace  "Nayi mamaki data iya yadda da kai, idan ciwon nan ya tayar mata bata yadda da kowa seni, ko Bulama wani lokacin muɗinma bata yadda damu gaba ɗaya se an mata allurai"

Yusuf yace  "Wane irin ciwo ne haka?"

Alhaji Nasir ya ɗan na Numfashi cike da damuwa yace 
"Yusuf, nasan mutane da yawa suna mata kallon bata da kirki, wasu suna zargina da barin 'yata ta lalace, kawai ina kallon sune, ba tare da nace wa kowa komai ba, Yusuf Widad ita kaɗaice' yata dana mallaka, larurar nan ta same ta ne sakamakon kashe mahaifiyar ta akan idon ta"

Zaro ido Yusuf yayi yace  "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
Alhaji Nasir ya jinjina kai yace  "ƙwarai kuwa, Akwai abunda ya faru da Widad, wanda tun daga lokacin take gudun mutane, ta haɗu da larurar ƙwaƙwalwa, dukda partially ne larurar tata da farko, Amma daga depression ya zarce mata ta samu Arthropophobia,
larurar ƙwaƙwalwa me sa mutum ya dinga jin tsoron mutane, ba mutane ba wani lokacin idan tana cikin larurar ko haske bata so, muna ta magani Sedai har yanzu na gaza samun abunda zesa ta farinciki, kana gani ko fara'ar kirki ba tayi, na yanke shawarar in mata Aure amma tace bata so, dan Allah Yusuf na san kana haƙuri haka nan naji ka kwantamin, dan Allah ka tayani Addu'a, Allah ya bawa 'yata lafiya, ita kaɗai nake da ita, ba uwa ba uba"

Gaba ɗaya tausayin Alhaji Nasir da' yar sa suka cika shi, Yusuf ya numfasa yace  "Insha Allah Alhaji, Amma ba kayi......

"Yallaɓai ya akayi harka shigo ban sani ba? muna can part ɗina muna fafutukar a kira likita yazo ya duba ta, gaba ɗaya yau kwana mukayi ba muyi bacci ba saboda yadda jikin Widad ya rikice, ko Abinci ba wanda ya iya ci yanzu ma mun shiga muyi salla ne ka dawo ban sani ba" Hajiya Halima ke wannan maganar cike da salon bariki da Kissa.

Alhaji Nasir yace "Allah sarki, nasan kina ƙoƙari akan Yarinyar nan, Allah ya saka miki da Alkhairi, ina su Baby Amal ɗinne ko basu san na dawo ba?"

"Amal ma bata jin daɗi, Ramla kuma salla take, ina jiran Widad ta farka ne a bata Abinci, mun samu da ƙyar tayi bacci"

Yusuf kam bin Hajiya Halima yayi da kallo, yana mamakin wannan iya salon barikanci nata, gaba ɗaya ta juye kamar tana cikin damuwar gaske.

Yusuf yace "Bari inje gida Alhaji tunda ka dawo"

"Shikenan Yusuf ka gaida gida, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi"

"A'a bakomai Yallaɓai" Yusuf yasa kai ya fice, Hajiya Halima tabi bayan sa da harara.

Kan Yusuf ya ƙara ɗaurewa da maganganun da Alhaji Nasir ya gaya masa, yana daf da fita kawai yaga Ramla ta sha gaban sa.
Tsayawa yayi yana kallon ta, ta kalle shi cikin Isa tace
"Bani mukullayen Motar Widad dana ɗakin ta dake gurin ka"
Yusuf ya tsuke Fuska yace
"ɗan bani hanya zan wuce mana"
"Ni kake kallo kakewa wannan gadarar haka? Zaka bani ko sena maka rashin mutunci?"
"bake kika bani ba, ba kuma ke nakewa aiki ba, dan haka babu ruwan ki dani"
"Kai kalli tsabar Idona, karka kuskura kace zakayi Jayayya dani, naga se wani shisshigi kake kana cusa kai a gurin waccan Mahaukaciyar da ita da Ubanta, to bari kaji in gaya maka, idan ma wani abu kake kwaɗayin samu wallahi ba zaka samu ba, Kuma hauka yanzu Widad ta fara shi daga nan har ƙarshen Rayuwar ta, ba zata sake moruwa ba, gara ka cire wa kanka ƙwalamar wannan daular da dukiyar, yadda kazo a talaka haka zaka koma a matsiyaci, idan kaga dama kaje ka faɗawa duk wanda zaka faɗawa, shawara ta ƙarshe da zan iya baka itace, ka gaggauta Ajiye aikin nan ka ƙara gaba ya fiye maka Alkhairi akan wasa da rayuwar ka"

Murmushi Yusuf yayi ya dubi Ramla yace  "in kinga na bar aiki a gidan nan wanda nakewa aikin ne suka sallameni, kina wani iƙrarin dukiya, dukiya nawace taki a dukiyar nan? Ki kiyayi Yusuf, matsi da takura babu wanda Yusuf be gani ba a rayuwar sa, dan haka ƙaramar barazana irin taki ba zata hanani Aiki na ba, ni babu ruwana da rayuwar da kuke a cikin gidan nan ni aikina kawai nasani, ban guri in wuce ko in hankaɗeki"
Galala tabi Yusuf da kallo, da ma akwai Yadda yake mata magana cikin Izza shima, Me yasa ba yayiwa Widad da take Wulaƙanta shi, lallai maganar Mummy gaskiya ce, ya kamata ayi maganin Yusuf.

Yusuf fa kai ya sake ɗaukar wuta, abun da ya faru yau, ya ƙara tabbatarwa Yusuf akwai wani mugun nufi a zuciyar Hajiya Halima da 'ya' yanta.
Umman Yusuf ta lura da yanayin Yusuf ko iya sakewa yaci Abinci ba yayi, Umma ta kalle shi tace
"Yusuf wai meke damunka ne haka? Naga gaba ɗaya kwanan nan na kasa gane kanka, Allah yasa ba wani abun aka kuma yi maka ba?"

"Umma ni a rayuwa ta wani irin ƙalubale ne ban gani ba? Aini lamarin rayuwa ta na miƙawa Allah, aikin da aka bani ne me matuƙar rikitarwa"

Nan ya kwashe komai ya gayawa Umman sa, Umms tayi shiru na wasu 'yan mintuna sannan tace
"lallai wannan lamarine me sarƙaƙiya, nidai fatana ka kula da kanka Yusuf, kayi taka tsan tsan ka cigaba da Addu'a, Amma waye yazo ya nemi da a dinga bawa ita Yarinyar kariya?"

Shiruu Yusuf yayi sannan ya girgiza kai yace  "Wallahi Umma ban sani ba"

"Ta yaya za'a bawa mutum kariya ba tare da sanin sa ba? Kaima kamar baka san aikin naka ba?"

"Umma nasan aiki na, Amma nima umarnin manya na nake bi, wataƙila be kamata in sani bane"

"Hakane amma kayi taka tsan tsan, naji tausayin yarinyar nan, Amma ni jikina yana bani wani abu game da aikin nan da aka saka, Amma kasa gane ko menene, ina dai yi maka addu'a a duk inda kake Yusuf, ni dai fatana ka kula da kyau"

"Insha Allah Umma na"

Haka suka cigaba da taɓa hirarrakin su na ɗa da uwa.

Sosai tunani ya auri Yusuf, maganar Umma tana bisa hanya, waye wannan da ya nemi a  bawa Widad kariya a ɓoye, dole akwai wata a ƙasa.

*******************

Washegari da safe, Yusuf ya koma gidan su Widad, bayan sun gaisa da su Nura, Yusuf yace "Nura ya jikin uwa ɗakina kuwa?"

Nura yace "ta yaya zamu sani? Kaine dama aka ɗauka mutum a gidan nan, da kai ake komai mu ina zamu san wani abu? Ai kaine mutum a cikin mu"

Yusuf yayi Murmushi ya samu guri ya zauna. Murtalah ya ƙaraso inda Yusuf yake yana faɗin "Malam Yusuf, ɗazu Alhaji ya leƙo yana tambayar ko kazo, dama yace in kazo a shiga da kai ɓangaren sa"

Yusuf yace "shikenan babu laifi, muje"

Murtalah yayi gaba Yusuf ya bishi a baya, Sam Yusuf be taɓa sanin da wannan ɓangaren a cikin gidan ba, gjda se kace ba'a duniya ba, Yusuf ya buɗe ido yana bawa idonsa Abinci.
Suna shiga Ƙaton falon, Murtalah yace
"to ni na tsaya daga nan, dan bani da ikon ƙarasawa ciki, seka fito"
Seda Yusuf ya gama waige2 sannan ya kalli ƙatuwar ƙofar dake cikin falon, a hankali ya taka yaje ƙofar ɗakin ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama.

Alhaji Nasir ne ya amsa tare da cewa "Shigo"
Yusuf ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, Alhaji Nasir ne zaune Widad ta ɗora kanta akan cinyar sa, idonta biyu tana ta jujjuya ƙwayar idon ta, gefe kuma Alhaji Bulama ne zaune a kusa da Alhaji Nasir.
Yusuf ya durƙusa yana gaishe su, Alhaji Nasir ya faɗaɗa murmushinsa yace  "Me babban suna, ashe kazo?"
"Eh nazo ranka ya daɗe, yame jiki"
Alhaji Nasir yace
"Jiki da sauƙi, Alhamdilillah an samu ta dawo hayyacin ta, Amma taƙi magana sam"
Yusuf ya kalle ta yace "Sannu ya jikin naki?"
Haɗe rai tayi ta tura baki tace  "Malam ni lafiya ta ƙalau"
Alhaji Bulama ya jinjina kai yace 
"gaskiya akwai ka da sa'a, tun ɗazu muke magana taƙi kulamu amma kai gashi tayi maka magana"

Alhaji Nasir yace  "My lovely, kin san wannan?" yai maganar yana nuna mata Yusuf

"Daddy nifa ba mahaukaciya bace"

Daddy yace "Ai na sani Babyna, tambayar ki kawai nayi"

Ta tura baki tace "Nasan shi"

Alhaji Bulama yace  "to waye?"

"Direba ne" ta bashi amsa a taƙaice.

Daddy yace  "direban wanne daga ciki?"

Maimakon ta basu amsa seta kalli Yusuf tace 
"kai ka gaya musu niba mahaukaciya bace, naga suna yadda da maganar ka, wallahi ni ina da hankali"

Yusuf yace  "ai dama basu ce ke mahaukaciya bace, kina da hankali"

Ta kuma cewa "ka gaya musu wani na ƙoƙarin kasheni a gidan nan, ka cewa Daddy dan Allah ya ƙyaleni in koma England"

Yusuf yace "Shikenan ki kwantar da hankalin ki, zan gaya musu Insha Allah"

Alhaji Nasir yace  
"Naga taku tazo ɗaya da Yusuf Lovely, kamar shi kin yadda da shi ko?"

"Allah ya kiyaye, direba ne kawai, yana nan a matsayin sa na direba, karma ka faɗi wani abu da zesa yaji cewa shi na musamman ne, ko yana da wani matsayi, i don't trust anyone"

Alhaji Nasir ya girgiza kai yace  "Yusuf nagode sosai, zaka iya tafiya abunka kaje ka huta, dama na kiraka ne in ƙara maka godiya nagode"

Yusuf yace  "Ai babu wani abun godiya da nayi Yallaɓai, Allah ya bata lafiya"

Suka yi Sallama ze tafi, sedai yana ƙoƙarin barin ɗakin, Hajiya Halima ta shigo da tray da kayan marmari a kai, tana ganin Yusuf ta haɗe rai ta bishi da wata uwar harara ba tare da ta bari Alhaji Nasir yaga hakan ba.

Yusuf ya kama hanyar fita, yaji ance "Yusuf ashe kazo?"
Ya juyo ya kalli inda Amal ke masa magana yace "Eh nazo, tun ina ciki na duba jikin Madam ne"
Amal tace "shikenan ɗan jirani ina zuwa"
"to shikenan bari in jiraki a waje" Yusuf ya koma harabar gidan yana jiran fitowar Amal, mintuna kaɗan sega Amal tazo, kaya ne a jikin ta wanda sukai matuƙar matsarta, ta dube shi tace 
"dan Allah so nake muje gurin shan ice cream tare, Akwai maganar da nake so muyi"
"Kina ganin ba matsala kuwa? Kinga wancan karon, Madam bata ji daɗin fita da mukayi tare ba"
"Shikenan idan ba zaka iya min Alfarma ba, na fasa zuwa"

Ɗan shiru Yusuf yayi yana nazari a ransa, tabbas Amal bata da wayo sosai, idan ya bugi cikin ta ze samu bayanai, dan haka ze iya shanye masifa da tsiwar Widad, a fili yace "shikenan kawo car keys ɗin naki mu tafi"
Ta kalle shi tayi fari da ido tace  "Dan Allah meye matakin karatun ka ne? Ka iya turanci Yusuf"
Ɗan basarwa kawai yayi murmushi ya nufi inda motocin suke.

Wani Joint tasa ya kaita, tayi ordering Pizza da tea, ta tambayi Yusuf me zeci yace shi baya cin komai.

Yusuf ya kalleta yace  "Wai ya naganki duk wata iri ne yau?"

Ɗan taɓe baki tayi tace  "ba lafiya ba, shine ko ka tambayeni ya jikina? bayan a gabanka Widad ta ƙonani jiya ba abunda kayi, baka damu dani ba, Amma nasan saboda rashin lafiyar ta yasa kazo da wuri yau" ta ƙarasa maganar tana tura baki

Yusuf ya ɗanyi Murmushi yace
"kiyi haƙuri, kinga bata da lafiya wani mataki zan ɗauka akanta? kuma kinga kaman mamanki da Yayar ki basa Son ina yawan shiga al'amuran gidan ku"

Amal tace  "ba Al'amuran gidan nan ne basa son kana shiga ba, Al'amarin Widad ne da kake nuna damuwa dashi sosai ne basa so, ko baka ga Yadda take Wulaƙanta mutane ba?"

"Eh amma, ita ina maman ta ne take rayuwa ita kaɗai?"

Amal ta ɗan taɓe baki tace "Kashe ta akayi fa, shine dalilin da yasa ta zama mahaukaciya bata son mutane"

Zare ido Yusuf yayi kamar besan komai ba yace  "waye ya kashe ta?"

Amal ta taɓe baki tace "Oho wayasani? Kana gani dukda mahaifinta yana da kuɗi amma a binciko wanda yayi laifin abu ya gagara, shi ne ita kuma tace zata nemo wanda suka kashe mahaifiyar ta, akwai mutanen data sa aka kama aka kulle a prison ba tare data nada wata cikkakiyar hujja ba, dan haka itama ake farmakinta, sannan akwai wani abu da'ake so a karɓa a gurin ta wanda nima ban san komenene ba,  Shiyasa nake gujemaka yawan Shiga lamarin ta bayan Aƙidarta ta Wulaƙanta mutane, duk randa ka bari wani kusanci me ƙarfi ya shiga tsakanin ka da ita, ba shakka za'a fara farmakin rayuwar ka domin za'ace kasan inda abunda ake nema a gurin ta yake, shine death Contract ɗin data gaya maka ai!!!"

IN AN KARANTA AYI SHARHI PLEASE
SANNAN AYI SHARE

07063065680
Ayshercool.

                     

   
                       _*AƘIDATA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

ELEGANT ONLINE WRITER'S


https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

                      PART1
                             Page 10

Shiru Yusuf yayi yana bin Amal da kallo, tare da nazarin maganganun ta.

"Waye ya kashe Mahaifiyar Widad? Me yasa aka kasheta!!? Meyasa ake bibiya da barazana ga dukkanin wanda yake da kusanci da ita!!!? Meye dalilin rushewar binciken wanda suka kashe mahaifiyar Widad? Meye Alaƙar kisan Mahaifiyar Widad da wanda Widad tasa aka ɗaure!!!? Meye alaƙar ciwon Widad da ƙwayar dake cikin tea ɗin da'aka kawo mata?

Wannan sune jerin tambayoyin da suka shiga kaiwa suna komowa a cikin ƙwaƙwalwar Yusuf.

Ta ɗago ta kalli Yusuf tace  "let's keep this aside, Yusuf ka taɓayin budurwa? Ko kana da budurwa a halin yanzu?"

Jin tambayar Yusuf yayi wani banbarakwai, ta tuna masa da abu mafi ciwo a rayuwar sa da baze manta ba har ya koma ga Allah, ya kalle ta ya ɓoye damuwar sa yayi murmushi yace  "Budurwa kuma? Wacece zata so talakan mutum kamata? Ni bani da wata budurwa ni kaɗai ne, ai nayi ƙarami inyi budurwa"
Murmushi tayi tace "ka fiye abun dariya, a haka kamar baka magana, Amma ka iya sa mutum dariya, yanzu babba da kai kace kayi ƙarami da budurwa?"
"Eh mana ko dan kin gani ƙato? Yarone ni ƙarami"
Ta sake yi masa wani murmushin tace  "hmm Shikenan, kodai Widad kake so?"
Zare ido yayi kamar idon ze faɗo yace  "Ni, rufamin Asiri, inani ina 'ya' yan manya, ai iyakacin talaka daku yayi muku aiki ku biyashi"
"Amma meyasa kake nuna damuwar ka a kanta haka? Dukda tarin wulaƙanci da rashin mutunci da take maka a wasu lokutan?"
"Saboda batamin wulaƙanci se idan na saɓawa umarnin ta, kuma mahaifinta yana matuƙar mutuntani, kuma kinga nine a ƙarƙashin
ta, dole inyi haƙuri da duk abunda zata yi min"
Amal ta numfasa tace  "hakane, Amma ina shiga matuƙar baƙin ciki a duk lokacin da naga tana cin zarafin ka, shiyasa nake ganin meze hana ka ajiye mata aikin ta, in samo maka wani aikin ka huta da wulaƙanci?"

Yusuf yayi Murmushi yace  "Inajin daɗin wannan aikin a hakan, bana so kiyi wani abu da ze ɓata ran mahaifiyar ki, Amma ina godiya da karamcinki a kowane lokaci, tunda kin gama, muje in sauke ki a gida nima in tafi, kafin Madam ta farga tare muka fita dake"  yai maganar cike da ƙoƙarin basar da maganganun Amal

Amal ta jinjina kai ta miƙe, suka bar gurin.

***************************

"Bayanai sun sameni cewar, Akwai yuwuwar Bala ya tona mana Asiri, yayi iƙrarin cewa tunda aka kaishi prison babu wani ƙoƙari da muke dan fitar dashi, munawa kabmu ƙoƙarine kawai, dan haka na yanke shawarar in kiraka muyi wata magana, fatan zaka buɗe kunnenka ka saurereni"

"To Yallaɓai, ina saurarenka"

"Hashim, Abunda nake so da kai shine, So nake a zuba magani a Abincin daza'a bawa Bala, wanda ze sashi rashin lafiya, daga nan se a kaishi Asibitin doctor Mukhtar, a can nake so a ƙarasamin shi, a kauda shi daga duniyar gaba ɗaya dan baze ɓata mana shiri ba"

Hashim Yace "Amma Yallaɓai aikin nan fa yana da hatsari sosai, kasada ne me girma, idan aka gano da hannuna a ciki zan rasa aikina, kuma za'a kamani"

A hasle mutumin yace "Kowace irin kasada ce gara ayita matuƙar Sunana baze fito ba, bazan zuba ido suna na ya ɓaci a banza ba ba tare da na cimma burina ba, Amfanin Bala ya ƙare dan haka a kauda shi bashi da sauran amfani a gareni, kana da damar yin hakan, kana da dama a hannunka dan haka kayi yadda nace, tun kafin raina ya ɓaci"

Hashim yace "Amma Yallaɓai......

"Sadakin aikinka naira million biyu ne, idan ba zaka iya ba zan saka a gefe in saka wani yayi min, Amma kasani kaima bazan barka a doron ƙasa ba tunda kasan sirrina, tashi ka fita na gama magana da kai "

**********************

Widad ta koma normal kamar ba ita ba, dan haka Daddy ya fara shirin komawa saboda Ayyukan da yake dasu, sedai sun fafata da Widad sosai dan ya sake yi mata batun Aure, ita kuma ta ƙara tabbatar masa tana nan akan bakarta ba gudu ba ja da baya, hakan yasa suka ɗan samu saɓani, ya tafi ba tare da tayi masa rakiya ba.

Yusuf yaje ya tsananta bincike akan gano waye mahaifin Nurat, wadda suka je gurin birthday ɗinta shi da Widad, ya samu bayanin wasu abubuwan ne daga gurin Amal, wadda ta riga ta gama narkewa a ƙaunar Yusuf.
Mahaifin Nurat babban ɗan siyasa ne, sukan haɗu da mahaifin Widad a gurin kasuwanci, amma bayanai sun nuna akwai tsohuwar Alaƙa dake tsakaninsu wadda daga baya tayi rauni, 'yarsa da Widad sun haɗu a gurin karatu ne a ƙasar waje, ita kaɗaice ƙawar Widad a Nigeria, se
'ya'yan Alhaji Bulama, shima ba wata alaƙace ta kusa tsakanin su ba, dan bata yarda a raɓeta, ba kowa ke iya jure halinta ba.

Tsangwama ta yau daban ta gobe daban, haka Hajiya Halima, Ramla da ma'aikatan gidan suke nunawa Yusuf, shi kuma ko a jikin sa, aikin da yaje yi shi kawai yake.

Isa mai gadi yayi yayi yasan daga ina Yusuf yake zuwa, Amma fafur Yusuf yaƙi gayamasa, daga baya ma se ya janye jikin sa, bayan gaisawa babu abunda ke shiga tsakankanin su.

Wasa2 aka shiga wata na uku, Amma Widad bata biya Yusuf haƙƙinsa ba, shi kuma koda wasa be taɓa magana ba.
Yusuf yana zaune a harabar gidan yana danna wayar sa, daga sama yaji ance  "Ssss" ɗaga kai yayi ya hango Widad ta saman bene, tayi masa alama da hannun ta yaje.

Yusuf ya miƙe ya shiga, tana zaune a falo tana cin gugguru, tana ci tana bawa magenta, Su Hajiya Halima na falon ita da su Ramla gaba ɗaya.

Yana shigowa Amal ta kalle shi tana kashe masa ido, seda yakusa faɗuwa dan gani yake gaba ɗaya sunga abunda Amal tayi, Widad dake kaɗa ƙafa tana kallon Abunda Amal tayi, bata tanka ba ta cigaba da watsa popcorn ɗinta.

Gefen kujerar da Widad ke zaune yaje ya zauna a ƙasan carfet yace 
"Gani ranki ya daɗe"
Ta kalle shi ta yamutse tace 
"Kai nifa bana son all such kind of names, Malam sunana Widad, ka dinga kirana da sunana"
Murmushi yayi mata tare da ɗan girgiza kai yace  "Bazan iya ba, nafi jin daɗin ince Madam, ko ranki ya daɗe"

"to bana so, niba basarakiya bace, ka kira ni da sunana kawai"

"Aike kinfi basarakiya ma gimbiyar Daddynta"

Wani ɗan guntun Murmushi tayi, wanda ita kaɗai tasan ma'anar sa.

Wani uban tsaki Amal tayi wanda bata san ya fito ba, ta miƙe a fusace da nufin ta bar falon saboda haushi.

"Amal!" Widad ta kira sunan ta. cak ta tsaya ba tare da ta waigo ba.

"Me nayi miki ne?" Widad ta jefa mata tambayar

Fuska a cunkushe Amal tace  "bakomai"

Murmushi Widad tayi wanda ya ƙara fito da kyawunta, tana girgiza santala santalan ƙafafuwanta, sannan tace

"Kin san Widad bata Soyayya, balle ince zan so abunda kike so, shi kansa Son ban yadda dashi ba balle inyi shi, koda zanyi so bazan so maƙasƙancin Mutum kamar direba na ba, balle inyi wani abu da zesa kiji haushi saboda shi, ki kwantar da hankalinki ba abunda zanyi da wannan abun, rainin hankalinsa da ƙwarin gwiwarsa gurin karyamin dokoki ne ke burgeni wasu lokutan, ban taɓa ma'aikacin da yake rainamin hankali da son yimin katsaladan a cikin lamaurana yadda yakeso kamarsa ba, wani abu dana fuskanta shine, ze iya jure duk wani hali da AƘIDATA, hmm ki huta beb ba wani abun damuwa a cikin abunda nake" ta ƙarasa maganar tare da wani murmushi na rainin hankali.

Yusuf ya kalli Widad, yaji haushin maganganun ta, ya ƙudurce wani abu a ransa.

Ta kalli Yusuf cike da kashedi tace  "Kaikuma tara ka kawai nake, ina sane da duk abunda kake yi, ina gargaɗinka akan contract ɗin daka sawa hannu, Ni kaɗai na ɗaukeka aiki, ni kaɗai zakayiwa Aiki, idan har zakayi soyayya or what ever Rubbish you call it, kayishi bayan ka bar gidan nan, hope I made my self clear "

Yusuf ya jinjina kai, a fusace Mummy tace "Aikuwa se naci uban Amal akan yaron nan, ka kiyayi 'yata ba kai ba ita, banda tsiyar ɗan talaka ina kai ina Amal, ƙwarya tabi ƙwarya mana, wallahi duk lokacin da ka kuma shiga sabgarta sena saɓa maka"

"Cewa akayi ana sonsa bashi yace yana so ba, ko ba kya gani ne? Kina zaƙewa gurin ci masa mutunci wasu lokutan, na lura Daddy yana matuƙar ji dashi saboda biyayyarsa, yana girmama shi sosai, ko dan haka at least dole a ɗagamasa ƙafa saboda yana matsayi me girma a gurin megida, dan haka a dinga ɗaga masa ƙafa a dena son shiga hurumin dabe dace ba"

Ta kalli Yusuf tace  "Aiken ka zanyi, kaje ɗakina, ka ɗauki key a drower mudubi, ka buɗe wardrobe ɗina ta ƙarshe, ka ɗakko ATM ɗina kazo"

Ba Hajiya Halima ba har Ramla da Yusuf seda suka kalle ta da sauri.
Ta basar ta maida hankali kan talabijin, kamar ba ita tayi magana ba, jiki a sanyaye Yusuf ya miƙe ya nufi ɗakin ta, gaban sa se faɗuwa yake, inda ta kwatanta masa yaje ya ɗau key ɗin ya buɗe wardrobe ɗin da tace.

Ramla ta kalli Widad tace  "Amma Widad kamar be kamata kitura ƙato kamar wannan ɗakinki ba"

Widad bata kalle ta ba tace 
"gayamin abunda ya kamata Uwata"

Ramla taja bakin ta ta tsuke, dan tasan idan taja maganar se ranta ya ɓaci.

"Subhanallah" shine abunda Yusuf ya furta, dan bayan sutura dake cikin wardrobe ɗin Widad, hadda bandir bandir na kuɗi na Nigeria dana ƙasashen ƙetare.
A gagguce ya ɗau abunda ze ɗauka ya fita ya kai mata, maimakon ta karɓa se ce masa tayi "Kaje na baka hutu na sati ɗaya dan ba inda zanje a kwanan nan, ina so kaje da ATM card ɗin nan, ka cire kuɗi, ka siyomin latest trending phone me kyau guda biyu"

Yusuf yace "Yanzu zan siyo in kawo miki?"

Ƙura masa ido tayi ba tace komai ba, kallon gargaɗi take masa akan bata son rainin hankali, dan haja Yusuf ya girgiza kai ze fita, Widad tace "Ji mana" ya tsaya tare da waigowa ya kalle ta
"Yanzu idan na tambaye ka kasan inda rai yake, wace amsa zaka bani?"

Ɓoye mamakin tambayar da tayi masa yayi yace "Allah Mahalicci shikaɗai yasan wannan Amsar"

Ta jinjina kai tace "Good you can go"

Hajiya Halima a gigice tace 
"Widad baki da hankali ne? Ya zaki bawa baƙo wanda baki san daga inda yake ba ki ɗau ATM wanda Account ɗin cike yake da kuɗi, Yallaɓai ma yana zuba dukiyar sa a ciki, kodan baki san zafin dukiyar ba sama taka aka tara aka baki, yanzu idan ya gudu yaƙi dawowa fa?"

"Kalma ta farko kin faɗi abunda ya dace a kaina, kin faɗa daidai ba kuskure, bani da hankali ni mahaukaciya ce kamar yadda kuka saba faɗa, dukiya kuma ta ubana ce, idan na salwantar da ita ba abunda zece tunda nima akwai tawa a ciki, ki dena tada jijiyar wuya akan dukiyar daba taki ba, idan tunanin ki abunda zaki samu bayan me ita ya mutu, sena tabattar da na ƙarar da komai kafin ya mutu koni na mutu, shine hanyar da zan baƙantawa masu harin dukiyar nan rai, and Mark you idan wani abu ya samu dukiya ta a yanzu to ba shakka kece, saboda babu wanda yasan da ATM ɗina a hannun sa seke da iyalanki"

Widad ta miƙe ta barmusu falon suna kallon kallo.

***********************
"Mummy, me yasa Daddy yayi yunƙurin sawa a sace Widad ne? Am so much Confused fa, tunda akayi abun nan ta bar gidan nan bata ƙara kirana a waya ba"

Mahaifiyar Nurat tayi ajiyar zuciya tace "Nurat nima ban sani ba gaskiya, ni banda yanzu da kika gayamin ma ban san abunda yake shiryawa ba, yanzu ina magana ze iya ɗaukar mummunan mataki a kaina, kin san halin sa"

"Amma Mummy abun ya ɗauremin kai, kinji yadda ya dingamin masifa dan na bari an ɗauke ta, kuma fa wani ne yayi barazanar ze saceni nima in har ban gaya masa inda take ba"

"Mhmm Nurat, kija bakinki kiyi shiru da wannan maganar, dan muddin kika bari wani yaji maganar nan mun kaɗe a gurin mahaifinki"

"Insha Allah Mum ba wanda zan gayawa"

*************************
Tunda Yusuf ya tafi da ATM ɗin nan Hajiya Halima ke cikin zullumi, dan ba ƙaramar dukiya ce danƙare a account ɗin nan ba, tunani take yadda zata gano inda Yusuf yake, tasa a ƙwato mata ATM card ɗin nan.
Ramla ta aika ta kira mata Isa me gadi, ba tare da ɓata lokaci ba ya biyo Ramla jikin sa na tsuma zuwa falon Matar gidan.

"Kai wani irin sokon gara ne haka? Har yanzu ace ka kasa gano inda wannan talakan banzan yake?"

"Wallahi ranki ya daɗe ya dena zama a cikin mu ma, wani girman kai yake ji da shi, yanzu shi kaɗai yake al'amuransa ko inda muke ya dena zuwa, iyakacinmu da shi gaisawa"
Dogon tsaki Hajiya Halima taja tace  "dallacan sakarai ni rufemin baki, tashi ka bar nan sakarai kawai, ni na tsaya bi ta kanka, zan nemi wanda zasu yi min aikin".
Isa ya tashi jiki a sanyaye ya bar falon,
Mummy ta kalli Ramla tace  "Ramla meye abunyi ne? Me ya kamata muyi?"

"wallahi Mummy kaina ya kulle, na rasa abunyi, yarinyar nan ta tabbata mahaukaciya, Mummy idan dukiyar nan ta salwanta ya zamuyi?"

Hajiya Halima tayi ajiyar zuciya tace  "bana tunanin yaron nan ze gudu da ATM ɗin nan, Widad tana da wayo ze iya yuwuwa tarko tayi masa, Amma tunda harta yadda dashi haka, dole mu janyo shi cikin mu"

"Hakane Mummy zeyi mana Amfani, idan har ya kasance a ɓangaren mu, Ammafa kamar zeyi taurin kai gayen"

'idan yaƙi yin yadda muke so, then we should exact power over him, you know what I mean "

Ramla ta jinjina kai tare da yin murmushi tace
"Am proud of you Momma "

*****************************

Kwance yake akan makeken gado a wani tangamemen ɗaki me ɗauke da kayan alatu, ya mimmiƙe ƙafafuwan sa hannun sa riƙe da waya yana kallon hotuna. Gefen sa wani matashin ne zaune a gefen gado yana tattaɓa System.

Hotunan Widad ne akan screen ɗin wayar kala kala yana kallo yana murmushi, kowanne se ya tsaya yayi zooming ɗinsa ya ƙare mata kallo, yanayi yana shafa sajensa tare da tattausan murmushi, ga dukkan alamu yana jin daɗin kallon hotunan nata. A hankali ya furta
"Can't wait to see you darling"
Matashin da ke gefen sa ne ya waigo ya kalle shi yace 
"Nifa ka isheni, se kace akanka aka fara Soyayya, kullum se kayi zancen yarinyar nan seka kalli hotunan ta, kuma ban taɓa jin ko waya kayi da ita ba"
Shafa sumar kansa yayi tare da yin murmushi yace  "bazaka gane bane Fahad, yarinyar ce 'yar daru se hankali, dukda ƙanwa tace amma halinta daban yake, ina tunanin yadda zata karɓi soyayya ta idan na bayyana mata"

"saboda me kake wannan tunanin?"

"saboda tace shi kansa son bata yadda dashi ba"

Ƙyalƙyalewa da dariya Fahad yayi yace  "Wallahi Anwar kana ruwa, se kace ita kaɗaice mace kaje ka nemi wata mana, dama da ganin ta zatayi izza, nifa rabona da ita tun tana yarinya ƙarama sosai"

Anwar yace  "hmm tabbas da zaka ga Widad a yanzu ba zaka taɓa cewa in haƙura da ita ba, Ina matuƙar sonta, na ƙagu in koma gida, wallahi yadda na ƙagu in ganta be kai yadda nake son ganin su Amal da Ramla ba, gashi seka rigani komawa da sati biyu"

Fahad yace "lallai ka tsunduma da yawa, nima ina son in koma inga Ramla, dukda ni muna waya da chatting da ita"

"Aishi yasa nake ta Addu'a, Allah ya bani Widad a matsayin mata"

Fahad yace "Hmm Allah dai ya baka me sonka"

***********************
Gaba ɗaya hankalin Hajiya Halima yaƙi kwanciya, gashi duk wanda ze kaiwa Alhaji Nasir ƙarar Widad to lallai zasu ɓata, ranar kwana na bakwai da tafiyar Yusuf, Hajiya Halima se sintiri take tsakanin part ɗinta da babban falo, Widad kam ko a jikin ta shagalin ta kawai take.

Yusuf ne yayi Sallama a falon, Hajiya Halima na zaune a falon tun safe ta kasa sukuni seda  Yusuf yazo.
Abunda ya ɗaurewa Yusuf kai be wuce yadda yau ta sakar masa fuska ta amsa masa gaisuwar cikin mutunci ba.

Zeyi magana kenan yaji ƙamshin turaren Widad, wanda ya alamta masa ta fito falon, waiwayawa yayi ita ɗin ce kuwa cikin shigarta ta ƙananan kaya kamar yadda ta saba, bakin ta ɗauke da chew gum tana taunawa tare da lumshe ido, a hankali tana taku me ɗaukar hankali ta tako ta ƙarasa shigowa falon, ta samu guri ta zauna ba tare da tace komai ba.

Yusuf ya tako zuwa gaban kujerar da take zaune ya durƙusa a gabanta ze fara magana, katse shi tayi ta hanyar yi masa alama da hannun ta na ya zauna akan kujerar dake kusa da wadda take kai.

Seda ya ɗaga ido ya kalli Hajiya Halima sannan ya tashi ya zauna yace 
"Ranki ya daɗe ga saƙon"

Ya miƙa mata ledar wayoyin da receipt ɗinsu da kuma ATM card ɗin. Tasa hannu ta karɓa, ta buɗe ta ciro wayoyin manya masu kyau, ta jujjuya su a hannunta sannan ta kalli Yusuf tace "can i have your phone?"

Kallon ta yayi, tare da yin sororo
"are you deaf?" ta tambaye shi tana tsare shi da ido.

Ciro wayarsa yayi daga aljihu ya miƙa mata, Android phone ce, dukda ba wata me tsada bace Amma hoton sane da Ummansa akan wallpaper ɗin wayar, seda tayi nazarin hoton na wasu seconds sannan ta buɗe wayar Yusuf ta cire sim cards ɗinsa da memory ta haɗa da sabuwar waya guda ɗaya, da tsohuwar wayarsa ta bashi sannan tace

"i want see you tomorrow by 9:am Insha Allah, you will get your salary alert today, you can leave"

"amma ranki ya daɗe, wannan wayar ai tayi min girma, kuma..."

Ai ko kallon inda yake bata sake yiba ta miƙe ta nufi part ɗin ta.

Gaba ɗaya hankalin Hajiya Halima akan Yusuf yake, Yusuf ya fita daga falon, ganin bashi da wani aikin da zeyi ya sashi ya ƙudure tafiya gida, yana ta ƙara jinjina kyautar wayar da Widad ta bashi.

Yayiwa su Nura Sallama ya fice ba tare da ya gaya musu abunda Widad ta bashi ba, yana cikin tafiya kafin ya kai ƙarshen layin aka sha gaban sa da mota, tsayawa yayi cak yaga waye wannan.
Ramla ce ta fito daga motar tana masa wani irin kallo, ta kalle shi a yatsine tace  "Nasan zakayi mamakin ganina anan, saboda bakamata mace kamarni ta tsaya tana ɓata yawunta akan talaka mutum maƙasƙanci kamar ka ba, sedai ita kasuwar buƙata idan ta taso tamkar guguwa take bata da shamaki, magana nake so muyi da kai me mahimmanci, wadda zata amfaneka, idan ba zaka damu ba ina so ka shiga mota muyi magana"

"talakan mutum maƙasƙanci a gurin ki, amma wataƙila me matsayi a gurin Allah be cancanci ya shiga motar mace me girman kai da tinƙaho ko ince tagumi da haɓar wani ba, bana buƙatar dukkan wani abun Amfani da ze taso daga gare ki komai mahimmancin sa kuwa, a gurin Allah nake nema dan haka ki bar abunki koma menene kuma komai amfaninsa"

"karkayiwa kanka gaggawa, ƙarshe kazo kana cizon yatsa, da da nasanin fatali da abunda ya tunkaro ka kayi masa shinge da riskarka saboda girman kai na banza, talakan mutum me dakakkiya zuciya irinka, zuciyarsa cike take buƙatar samun damarmaki, dama irin wadda kowa ke lalube a duhu ko a sarari, katsam se gashi ka sameta a sarari, Amma ka kasa ƙafa kai fatali da ita, me yasa kayi hakan? "

"lokaci abune me mahimmanci a gurina, ina bashi mahimmanci fiye da yadda kike tunani, zefi kyau ki taƙaita wannan dogon surutan naki marasa amfani, a cikin taƙaitattun kalmomi kimin bayani gwari gwari kamar yadda Uwargida Widad keyi, hakan zefi min sauƙi, kuma ze adana lokacin mu".

Wani kallon banza ta watsa masa sannan tace  "ko Uwargida ko ubangida wannan kai ta shafa, ni daban ita daban, dama ta sameka amma ka watsar da ita a yadda kake gaka matashi har matashi, kai dai ba muni ba kuma ba nakasa ba, a wannan shekarun naka da ƙirar da Allah yayi maka kamata yayi ace kana wani ɗan ƙwalisa meji da kansa, katsam sega shi ka ƙare a direba, direban ma maƙasƙanci, kana tuƙa ƙaramar Yarinya tana cin zarafinka yadda taso, bata ganin gjrmanka da aikin da kake mata, da kasan maƙudan kuɗaɗen dake cikin Account ɗin nan da tabbas baka dawo gidan nan ba, dan da kai da talauci har gaban Abada, ba kaiba har  'ya'yan ka da jikokin ka ba zasuyi talauci ba, sedai kash garin yin gwaninta kayiwa kanka mugunta"

Yusuf yace "har yanzu jira nake ki faɗi abunda kike tafe dashi, na gaji da sauraren wannan salon maganar taki me tafiyar kura, kiyi gaba kiyi baya kamar kema baki yadda da kanki ba"

"Babu batun rashin yadda da kai sedai ina so muyi tarayya gurin temakon juna ne, ina son ka gayamin password ɗin Widad ne na banki, nayi maka Alƙawarin samun wani gwagwaɓan sakamako indai kayi abunda nace, hakan ze zama madadin wannan shiritar da kayi nayin wasarere da damar daka samu, kuma ze baka damar samun 'yantuwa daga wannan aikin dakake ƙarƙashin wannan Yarinyar me Baƙar Aƙida"

Wani irin kallo Yusuf yayi mata sannan yace
"dukda kasancewa ta talaka maƙasƙanci kamar yadda kuke kirana, Yusuf yafi ƙarfin karɓar abunda zaku bashi saboda wannan baƙin aikin da kuke so inyi, ku tara dukiya da guminku seku yi barazana da ita ko tinƙaho, Bana danasanin aiki na ƙarƙashin Widad, duk inda tayi faɗa ko tsiwa to tabbas an mata ba daidai bane, shiyasa komai tayi take birgeni, kasancewata meyi mata aiki be sa naji cewar ni maƙasƙanci bane, kasancewata me aiki a ƙarƙashinta na sani ƙara samun ilimin rayuwa, dan haka kece maƙasƙanciya da kika ƙallafa rai akan abunda ba naki ba, ni talaka ne me wadatar zuci, dukiyar Widad bata isa ta yanken talauci ba"

"haka kace ko, to shikenan zakaga abunda bijirewa buƙata ta ze haifar maka, ba dai shishshigewa wannan mahaukaciyar ka zaɓa ba, a haka zata ƙare a hauka, kuma death contract data gaya maka zaka ganshi dan kusancinka da ita tamkar kusancinka da mutuwar Kane, Akwai mutanen dake farautar mutane irin ka, wanda suka raɓeta, zasu cigaba da farautarka da bibiyar ka, zasu nemi wani abu a gurin ka, muddin ka gaza yi musu zaka ga abunda ze biyo ba, ka rubuta ka ajiye zaka ce na gaya maka, sakarai mara rabo kawai "

"Ke rabon ne yasa kike zaune a gidan mutane kina harin yin zamba cikin Aminci ai, dukda irin gata da sutura da akai muku"

Wani murmushi tayi me ciwo, badan Widad tana Wulaƙanta su a gaban Yusuf ba ya isa ya kalli idon ta ya gaya mata wannan maganganun, ta ɗaga ido ta kalle shi tace  "ka faɗi abunda kake so a yanzu, amma ka saurari ƙalubalen dake fuskantar ka" ta shige ta kunna motarta ta bar gurin a guje.

SHARE PLEASE 🙏

Please pray for my Dad, he is sick

Ayshercool
07063065680

.                   

                      _*AƘIDA TA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Special thanks to all members of my Association
Perfect writers Association may Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will bring positive changes to our Community.

                

                           PART1
                                  Page 11

Bin motar Yusuf yayi da kallo harta ƙure, sannan a sannu yaja ƙafar sa ya ci gaba da tafiya abubuwa daban daban na yawo a kwanyarsa.

Maimakon ya tafi gida seya tsaya yayi sallar azahar ya wuce gurin aiki, office ɗin Abbas ya tafi yaje ya tarar da shi yana tsaka da wani aiki, Abbas na ganin Yusuf  yai murmushi suka gaisa sannan yace 
"Yane mutmina? Akwai wani latest update ne?"

Yusuf ya ɗan ɓata rai yace "na baka abu kayi assisting ɗina kaƙi, seni nayi abuna bakomai nagode"

"wane abu kace inyi assisting ɗin naka naƙi?"  Abbas ya tambaya

"Akan mahaifin yarinyar nan Nurat mana, Nace ka tayani bincike akansa amma ƙarshe ni nayi abina"

Dafe kai Abbas yayi yace  "Sorry my man, wallahi aiki yayi min yawa na manta shaf"

"Shikenan amma ina tafe da Labari ne"

Abbas ya tattara hankalin sa yace  "ina jinka, dama kamar kasan jiya Oga Suleiman yayi min maganarka"

Yusuf yace "Abbas ina kyautata zaton akwai sa hannun matar Mahaifin Widad a farmakin da'ake kai musu"

Abbas ya ture System ɗin gabanshi ya sake tattara hankalinsa yace  "ta yaya kenan? Meka gano?"

Nan Yusuf ya gaya masa abubuwan da Su Hajiya Halima keyi, da kuma Yadda suka yi da Ramla"

Jinjina kai Abbas ya shiga yi yace  "Lallai biri yayi kama da mutum, amma kaga Oga yana Abuja akan wani case, Amma idan hakane meye alaƙar iyalan Alhaji Nasir da Mahaifin Nurat?"

Yusuf yace  "Abunda zan ɗora da bincike na akai kenan"

Waya ce ta fara ringing, Abbas da Yusuf suka shiga waige waigen wayar da take ringing ɗin, Abbas yace  "kamar daga jikin ka ringing ɗin ke tashi fa"
Se yanzu Yusuf ya tuna an bashi sabuwar waya, hannu yasa ya ɗakko wayar ya ɗaga, suka gama magana Umma ce ta kira shi.
ssebayan Yusuf ya gama Abbas yace 

"jar uba mutumina wannan latest phone ɗinfa? Miƙomin in ganta, yaushe ka siyi waya haka, kaida manyan wayoyi basu dame ka ba?"

Yusuf ya miƙa masa wayar yace  "Widad ce ta aikeni na siyo mata wayoyi masu tsada guda biyu, ina kai mata ta bani wannan"

Abbas ya dinga jinjina kai yana jujjuya wayar yace  "Lallai ka faso gari, amma kamata yayi ka siyar da ita kai sabgar gabanka da kuɗin"

"Idan kuma ta tambayeni wayar nace na siyar taji daɗin Yimin wulaƙanci ko?"

Abbas yace  "A'a ba haka nake nufi ba, Ashe dai har yanzu halin nata na nan, ai kwanan nan Insha Allah zan ɓullo gurin naku"

"to nidai in kazo ka kula, karka sake ka gaya wa wani unguwar da nake, haka kurun sun matsa da son sanin daga inda nake zuwa, dan nima kaina ban yadda da mutanen gidan ba"

Abbas ya kwashe da dariya yace  "ashe dai ta koya maka halin nata"

Alert ne ya shigo sabuwar wayar Yusuf  dake hannun Abbas, zare ido Abbas yayi yace "Yusuf an turo maka kuɗi"

Yusuf yace "waye ze turomin kuɗi tsakiyar wata haka?"

"wallahi dagaske nake, dubu ɗari shida"

Miƙewa tsaye Yusuf yayi yace "ni a wa? Waze turomin kuɗi haka?tabbas anyi kuskuren lambar account"

Abbas yace "dakata, kuma ba uwaɗakinka bace?"

Shiru Yusuf yayi yace  "to aini bata da Account number ɗina, sedai idan naje gobe in Allah ya kaimu in tambaye ta, Amma inma itace gaskiya kuskurene, Kaga Abbas se anjima akwai inda nake son zuwa"

Gaba ɗaya Yusuf ya ruɗe, mamaki ya cika zuciyarsa yafi tunanin ko Ramla ce, dan tana son ta siye shi yayi mata aikin data keso? Amma daga rabuwarsu ta ina zata samu Account number ɗinsa?.

***********************

A mugun fusace Ramla ta koma gida, tana zuwa bata tsaya ko ina bs se ɗakin mahaifiyar su, taje ta tarar da ita suna magana da Amal.

"Mummy akwai matsala fa"

"matsalar me?"

"Mummy this guy is very rude, we have to exact power over him, how dare will he look into my eyes and tells me that he won't do what i ask him to do?" ta ƙarasa maganar tana ta gauraya Numfashi.

"Kinga nutsu kiyi min bayani ya kukayi dashi?"

Ramla ta warware mata komai, Amal tace  "da anyi shawara dani da baza'a tun kare shi ba saboda nasan ba zeyi ba, Mutum ne me kafiya da dagewa akan gaskiyar sa"

Cikin fushi Ramla tace "A beg shut up Malama, wayafi kafiya talakan banza mara amfani, ni ya tsaya ya kalli cikin idanuna ya cimin mutunci, shikenan dani yake zancen wallahi se nasa zaman garin nan ya gagare shi banza da kansa kamar lemo"

Amal tace  "Wai kansa kamar lemo, kekuma naki fa"?

"dan Allah kuyi min shiru karku yi min faɗa anan, mafita ya kamata munema ba surutu ba, sannan Amal wallahi idan baki kiyayeni akan yaron nan ba sena saɓa miki fiye da tunanin ki wallahi, bazan taɓa aurawa maƙasaƙancin mutum ɗana ba, dan haka ki shiga hankalin ki, zaƙewar da kike masa tayi yawa "

Zumɓura baki Amal tayi ta bar ɗakin.

"Mummy inaga mubi Amal a hankali, tabbas son gayen nan take, Amma cikin hikima zata iya samo mana abunda muke so, ki dena yawan hantarar ta a kansa, karta zo ta bijire mana daga baya fa"

"Bazan bari alaƙar tasu tayi nisa ba, saboda yaron kalar mayaudaran mazane, yana da mu'amala me kyau, daɗin Soyayya ze iya sa Amal ta tona komai, kin san bata da hankali, Amma zan sanar dake mataki na gaba da zan ɗauka.

**************************

Safa da marwa yake yana kaiwa yana komowa a cikin wani matsakaicin Office, yana ta sake nanata maganganun da Oga ya gaya masa game da poisoning ɗin Bala a prison, wani mutum ne yayi Sallama a office ɗin yace
"Yallaɓai Hisham lafiya kake nemana?"
Hisham yayi ajiyar zuciya yace  "Oga Bukar ne ya bada wani aiki, kuma muddin aka samu kuskure bamuyi ba ze halaka mu"

"Kamar Yaya? Wai shi meyasa be maida kisan kai komai ba saboda buƙatunsa? Wallahi nayi dana sanin sabga dashi"

"Kwantar da hankalin ka Bashir, mu lallaɓa muyi masa wannan aikin bisa Yarjejeniyar shine na ƙarshe, idan ya cigaba da takuramu, semu ma mu ɗana masa tarko"

Tsaki Bashir yayi yace  "ina jinka, me kuma zamuyi masa?"

"yace so yake ayi poisoning ɗin Bala, yadda ze fara rashin lafiya, da an kai shi Asibiti kuma zesa a ƙarasa shi, saboda Balan yayi barazanar tona Musu Asiri, sun barshi a gidan yari tsawon shekaru takwas, sunƙi fitar da shi"

"wallahi Hashim mutanen nan basu da Imani, tsaf muma zasu iyayi mana abunda suka yi wa Bala, amma salin alin muyi abunda suke so, muna dafe kan madarar kawai zan ajiye aikin gidan nan in fece"

Hisham yace  "shikenan but you have to focus"

Bashir ya jinjina kai ya fice daga office ɗin.

*********************************
Dogayen kaya ne a jikin Yusuf, yayi kyau sosai ya shiga falon da sallama, ba'a amsa ba kasancewar ba kowa a ciki, ɓangaren Widad ya nufa kansa tsaye, yaje ƙofara falonta ya tsaya, tare da yin knocking.

Ƙasa ƙasa ya jiyo muryar ta tace  "Come in" da Sallama ya shiga falon, tana zaune tana shan tea, ya kalleta yace  "barka da Safiya ranki ya daɗe" jinjina masa kai tayi ba tare da ta amsa ba, ta cigaba da abunda take ba tare da tace uffan ba.

Haka ya shuɗe tsayin wasu lokuta yana zaune yana jiranta, ga shan tea ɗin take kamar tana shan magani.

Yusuf ya gyara zama yace 
"Ranki ya daɗe jiya naga an turomin kuɗi a account ɗina masu yawan gaske, ban sani ba koke ce, shine nace bari in tambaye ki"

"Kana expecting ɗin kuɗi daga gurin wani ne?" tai maganar tana ajiye cup ɗin hannunta

"A'a, bana yi" ya bata amsa

"Anyway salary ɗinka ne na 3 months da ban baka ba"

Zare ido Yusuf yayi yace 
"Amma sunyi yawa fa, ya zanyi da wannan maƙudan kuɗaɗen?"

"Zaka iya zubarwa, wannan kai ta shafa"

"A'a Madam, banyi aikin da zan karɓi wannan kuɗaɗen ba, sun yi yawa ban san....

"Kai ɗan Yimin shiru mana, idan ban manta ba kafin in ɗauke ka aiki na gaya maka salary ɗinka, kasan sunyi yawa meyasa kace zaka yi aikin? A beg keep this aside follow me"
Tayi maganar tana miƙewa tsaye ta nufi bedroom ɗin ta, jiki ba ƙwari Yusuf yabi bayan ta.

Wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗakko wayar nan da tasa ya siyo, ta tako zuwa gaban Yusuf, sedai tana zuwa suka ji wani shock a tare, ƙamshin turaren da Yusuf yake yasha banban da wanda ta hana shi sakawa, amma muddin zata ji ƙamshi a jikin sa se wata kasala ta saukar mata.

Shikam Yusuf ƙirjin sa ne ya shiga bugawa da ƙarfi ba tare da yasan dalilin hakan ba.

Widad ta tattaro nutsuwar ta ta dube shi ta miƙa masa wayar, yasa hannu ya karɓa yana kallon ta, a hankali tace

"Yanzu misali a ce wannan wayar ranka ce, a ina zaka ɓoye ta?"

Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "zan mata kyakkyawan ɓoyewar da babu wanda ze san inda take se Allah"

"Good haka nake son ka ɓoye wannan wayar tamkar na baka ranka, duk kusancinka da mutum karka kuskura yasan da wannan wayar a tare da kai, karka yarda da kowa, wannan wayar tamkar na baka ranka ne!!! ka kula da ita"

A diririce Yusuf yace "Amma me yasa zan kula da ita haka? Ban gane tamkar kin bani raina ba"

Ɗan taɓe baki tayi ta juya tace "bashi da mahimmanci kaji wannan a yanzu, saboda sanin hakan a yanzu tamkar sake jefa rayuwar ka cikin hatsari ne, let me tell you something, don't trust anyone, i repeat myself don't trust anyone, jeka ƙarfe biyar zan fita yau"

Yusuf ya jinjina kai yace  "Amma kuɗin nan da kika bani wallahi sunyi yawa"

Widad tace  "You can go, na sallame ka"

Yusuf yace  "Amma ban san yadda zanyi da wannan maƙudan kuɗin ba"

Ba tare da ta kula Yusuf ba ta shiga ƙoƙarin rage kayan jikin ta zata shiga wanka, ba shiri Yusuf ya juya da sauri ya bar ɗakin, yana mamakin wauta irin ta Widad.

*********************************

Alhaji Musa ne zaune a falon sa, 'yarsa Nurat na kujerar dake facing ɗinsa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunata.

"Wallahi Nurat na rasa me zan miki in huce, da tuni harkar nan ta kankama, amma kikayi mana wauta da hauka, idan abun da muke nema ya samu, se kinfini mora"

Murya na rawa da alama tana tsoron mahaifin nata tace 

"dan Allah kayi haƙuri, nima wani ne yace ze saceni idan ban nuna masa inda take ba"

"waye shi ɗin?" ya tambaye ta a ɗan hasale

"Wallahi ban san waye ba, nima bata gayamin waye shi ba"

"Ni zan gano ko waye inyi maganin sa, yanzu dole ki samo wata hanyar abunda zaki yi ta sake zuwa gidan nan"

Saurin girgiza kai tayi tace  "Ai kasan ba zata ƙara yadda dani ba, wallahi kome zanyi ba zata zo ba"

A fusace yace  "tashi ki bar nan, komai a kasa dake se kinyi wauta, ni nasan abunda zanyi"

****************************

Album guda na hotunan Widad yake dasu a System ɗinsa, ji yake kamar ya janyo kwanakin da ze koma Nigeria, kallon hotunan ta kawai yake hakan ke ƙara samasa nishaɗi.

Video call ya kira Mummy, Hajiya Halima na ganinsa tayi murmushi tace 
"'yan makaranta, lokaci ya kusa ko?"

Anwar yace  "Eh Mummy se missing ɗinku nake, ina su Ramla ne"

"Suna nan gasu a kusa dani"

"shine ba zasuzo mu gaisa ba, dama ba nemana suke ba"

Amal tace  "waze kira ka a kwashe masa kuɗi"
Haka suka dinga video call suna hira da 'yan uwan sa, can yace  "Mummy wai ina Widad ne? Naji ance tana Nigeria kuma tunda nake kira bana ganin ta"

Tsaki Mummy tayi tace  "Ban sani ba, ita ta haifeka koni? Idan bani kske nema ba shikenan, kullum baka da zance sena wanne banzar yarinyar?"

"yi haƙuri Mumsy, Yadda mahaifinta ya riƙemu ai senake ganin kamar babu laifi dan na tambayi inda take"

Ramla tace "Brother dan Allah karka ɓatawa mutane rai, waya ke maganar wannan mahaukaciyar"

Anwar yace "ni a ganina, Widad rashin me janta a jiki da kuma depression yasa condition ɗinta ya zama complicated, amma...

Cikin tsawa Hajiya Halima tace " Rufemin baki dan uban ka, kaga ka kiyaye ni ko in ɓata maka rai, in baka son ɓacin raina karka sake Yimin zancen yarinyar nan, ko dan kai kana can baka san irin zaman da muke a gidan nan ba"

Ramla tace "ina ze sani, muna nan ta mayar damu kamar bayi, cin kashi kala kala, ana Wulaƙanta mu muda mahaifiyar mu amma kana neman ta"

Anwar yace  "Amma Mummy....

A fusace tace "ke Amal katse min kiran nan, shashashan banza kawai"

Amal ta katse kiran.

Anwar ya turawa Amal message
"Amal ɗan turomin lambar Widad"

Ta masa reply da  "Taɓɗijan wa kake tunanin ze samu lambar wannan? Duk yadda kake tunanin abun ya wuce haka, ba ruwan ta damu fa"

Jujjuya message ɗin ya dinga yi, babban abunda yake bashi takaici be wuce duk lokacin da ya kira Mummy, ya tambayi ina Widad seta balbaleshi da masifa, duk wanda ya tambaya ya bashi lambar ta kowa se yace bashi da ita, ya rasa meye dalilin hakan.

Yana wannan tunanin Fahad ya shigo ɗakin da sallama, ya kalli Anwar yace  "Man what's wrong ne? Nayi sallama baka amsa ba"

Ɗan guntun tsaki Anwar yayi yace  "Fahad, ni gaba ɗaya na kasa gane kan lamuran nan dake faruwa, duk lokacin da zamuyi waya da Mummy, idan har zan tambayi Widad se taita faɗa, babban abunda yake bani mamaki shine, wai ace duk gidanmu babu me lambar Widad balle ya bani"
Fahad yace
"Widad Widad Widad, kai dai baka da zance se wannan Yarinyar, please don't kill yourself mana, Nifa yadda kake bani labarin ta sam bata Yimin ba, nifa tun tana ƙarama yadda take wannan Share mutanen haushi take bani, kuma gashi da bakin ka ka gayamin tana da taɓun hankali "

Anwar yace " shut up please, tunda ba zaka bani shawara ba ka ƙyaleni, baka san yadda nake ji akan ta ba, kai kana soyayya amma kamar baka san meye son ba, Ni anya ma in baka Ramla zaka iya riƙe ta kuwa? "

Fahad yayi murmushi yace
"Anwar kenan, aini Soyayya ta da Ramla tana sona ina sonta, amma kai banda wahala babu abunda kake yi"

"Kai kaga wahala, ni bangan ta ba, Ni na ƙagu kamar in janyo lokaci in koma gida, gashi seka rigani komawa Nigeria"

"Allah ya baka lafiya Anwar, dan ga dukkanin alamu ta shafa maka haukan"

Shiru Anwar yayi ya miƙe ya bar ɗakin, dan Fahad ya fara baƙanta masa rai.

Widad tana ta shirin fita, wayarta ta fara ringing, hannu tasa ta ɗau wayar tasa a kunnen ta, shiru ta ɗanyi tace 
"Ok, thank you very much, send the address via my email" ta ajiye wayar tana ci gaba da shiryawa.

Maimakon ta fito seta tsaya ta saman bene tana duba lokaci, Yusuf ta hango ya fito da Mota yana ta gogewa dukda a wanke take, abun da ta fuskanta da Yusuf mutum ne meson tsafta sosai, baya son datti sam.

Message ne ya shigo wayar Yusuf ya ɗaga ya duba.

"Ba'a wannan motar zamu fita ba, ka fita waje ka jirani"

Mamaki ne ya kama Yusuf, tabbas Wannan message ɗin daga Widad ne, 'Amma yaushe ta samu lamba ta?' ya tambayi kansa, basarwa yayi ya mayar da motar, yana fita wajen gate yaga wata mota, ba dai me tsada bace dan kamar ma ta ɗanji jiki.
Guri ya samu ya tsaya yana jiran fitowar ta.

Seda yayi kusan mintuna talatin kamar ance ya ɗaga kai ya kalli gate, ganin Widad ne yasa ƙirjin Yusuf bugawa da ƙarfi.

Wani arnen black leg jeans ne a jikin ta, da wata tied pitted blue body hook, tayi stocking ta saka beilt, ɗan ƙaramin baƙin veil ta ɗaure gashin kanta, dukda ƙasan gashin nata ya fito.
Google glass ne a fuskar ta baƙi, ga takalmi me matuƙar tsini, se 'yar ƙaramar jakarta, gaba ɗaya bazaka ce idan Widad ta buɗe baki zata yi hausa ba, duk wani shape da surar jikin ta ya fito.

Tabbas da Yusuf nada damar Mayar da Widad ta canza kaya da tabbas zeyi, dan haka kurum yaji takaicin fitar Widad a haka.

Ƙarasowa tayi ta miƙawa Yusuf key ba tare da tace komai ba, jiji a sanyaye ya karɓa, ya buɗe mata motar ta shiga ya rufe ya zaga mazaunin direba ya zauna, gaba ɗaya ƙamshin turaren da take ya cika motar, ya kalle ta yace
"Ina zamu je?" shiru tayi na ɗan wani lokaci sannan ta miƙa masa wayarta, yasa hannu ya karɓa ya duba.
Adress ɗin inda ze kaita ne, ya ɗago ya kalleta zeyi magana, amma yaga ta ƙara yi masa kwarjini, dan haka ya bata wayar ta ya kunna motar.

Yana cikin tuƙi wayarsa ta fara ringing, Umman Yusuf ne a jikin screen ɗin wayar, ya ɗaga wayar yasa a hansfree ya ajiye ta yace
"Umman Yusuf"

"Ɗan gidan Umman sa, yau zaka dawo da wuri ne, an kawomin wani kifi tun daga Yobe, nayi maka farfesu ka dawo da wuri karya huce, ko kuma in cinye abuna"

Duk da ransa a dagule yake wanda ya rasa dalilin hakan, Amma seda ya maze yace 
"Umman Yusuf, ai bazaki iya ci baki ajiye min ba, zan siyo gurasa yai akwai dinner me kyau"

Hirarsa yake yi da maman sa hankali kwance, se shagwaɓa yake yi kamar yaro ƙarami, Widad kuwa ƙura masa ido tayi ko ƙiftawa ba tayi, dukda ta cikin Glas ɗin idonta take kallon sa amma yadda yake wayar da Mahaifiyar sa ba ƙaramin birge ta yayi ba.

A ranta tace 'dama suma talakawa suna jin wannan shauƙin da ƙaunar na iyaye, inama Ammi na tana raye nima in kwanta a jikin ta in ji daɗi'
Ba tayi aune ba taji hawayen da bata shirya zubowarsu ba. Cire glass ɗin fuskarta tayi tana goge hawayen idon ta, katse wayar Yusuf yayi ya kalleta yace
"lafiya dai?"
"Lafiya cigaba da tuƙinka, ina so muje gurin nan kafin 5"
Ya jinjina kai ya ci gaba da tuƙin, wani katafaren hotel ne, motocine suke shiga suna fita a ciki, kowa harkar gaban sa yake yi, sedai mafi akasari kallo ɗaya zakayi wa mafi yawa daga mutanen dake shiga suna fita, ka gano rashin tarbiyya da ta ido a tattare dasu, musamman matan duba da yanayin irin shigar dake jikin su.

Yusuf yayi parking yana kallon Widad, ta buɗe motar ta tsaya tana ƙarewa harabar hotel ɗin kallo.
Da sauri Yusuf ya fito daga motar yana kallon ta, ta dubeshi tace  "wait for me here"
ta sa kai da nufin shiga cikin hotel ɗin, da yawa mazan dake gurin nan hankalinsu ya dawo kanta, Widad ta haɗu iya haɗuwa, wani takaici ne ya kama Yusuf, ace 'yar musulmi ce da wannan shigar a wannan gurɓataccen gurin.
Bin bayanta ya kuma yi da sauri, ta tsaya ta kalle shi tace 
"I said you should wait me inside the car, don't let anyone to see you here, don't tarnish your image because of me"
Ta sake juyawa, ba zato cikin zafin nama da zafin rai Yusuf ya riƙo Widad gaba ɗaya zuciyar su ta buga a tare, Yusuf ya kalli cikin idon ta yace
"Guri irin wannan be dace da mace me daraja kamar ki ba, Mahaifinki babban mutum ne be kamata aga 'yarsa a irin wannan gurin ba, ke mace ce kuma me daraja bekamata kowane gara ya dinga kallon surar jikin ki haka ba, think about it"
Nutsuwa Widad tayi seda ya gama tsaf sannan tace 
"Cikani tun kan in wanka maka mari a gurin nan, kai waye da zaka gayamin abunda ya dace dani? this is my life style not yours, dalla Cikani Malam kana ɓatamin lokaci ni"

A hankali Yusuf yace  "I am musulm, ina kishin yadda mutane ke ƙare miki kallo a haka, kalli irin mutanen dake gurin nan, da yawan su karuwai ne fa da mutanen banza, shigarki bata da maraba da wanda matan gurin nan marasa daraja suka yi"

Cikin isa tace masa "koba maruwanci ba, Nima shi nazo yi, am prostitute karka ƙara shiga rayuwa ta, na gaya maks"

Ta juya ta shiga Hotel ɗin da sauri, wani baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Yusuf, ya koma mota ya zauna yana tunani a ransa
'to wai kai Yusuf banda shisshigi ina ruwanka da ita ne?'
Wata zuciyar ta tambaye shi.

Yana nan zaune a mota kusan mintuna Arba'in, gajiya yayi da zaman motar ya fito ya zauna akan motar yana ƙurawa hanyar da Widad tabi ido.
Ba tsammani ya hangota tana fitowa, sedai fuskarta ɗauke da hawaye tana ta share hawayen da handkerchief, inda motar su take ta nufo idanunta jawur, wani ne ya biyo ta yana ƙoƙarin tsaida ita yayi mata Magana amma bata tsaya ba, tana zuwa ta buɗe motar ta shige.
Yusuf ya zagaya ya shiga ya kunna motar, gaba ɗaya se yaji ya tsargu da yanayin daya ganta, gaba ɗaya hankalinsa ya tashi "Are you ok?"

"Do you have any conscience with me being ok or not?" ta tambaye shi a hasale

"Yes i have" ya bata amsa, tsaki tayi ta ɗauke kanta tace 
"drive very fast please" gudu sosai Yusuf yake amma azalzalarsa take wai ya ƙara gudu, kuma still bata dena kukan ba, kuka take me fallasa da tsantsar ɓacin rai da damuwa.
Guri Yusuf ya samu yayi parking ya juyo yana kallonta, ba tace komai ba tasa hannu a jakarta ta ɗakko wayar ta, ta ɗan daddana sannan ta saka a kunnen ta, tayi shiru na wasu 'yan mintuna sannan tace "Hello Daddy"

Yusuf baya jin me mahaifin Widad ke cewa, cikin kuka tace  "please Daddy I want Flight back to U. K, i regret coming back to Nigeria, please Daddy talk to Bulama ask him to set up my visa"

Shiru ta ɗanyi sannan tace  "Daddy don't take it for granted please, i can't define what happens today, dan Allah kace ayimin visa in koma"

"Daddy why? Kayi shekaru ba tare da ni ba se yanzu zaka ce baka so inyi nesa da kai? Karo na biyu ina neman abu kana ƙin Yimin, shikenan Daddy bayan ciwon Ƙwaƙwalwa am at risk of having cardiac attack" ta saki wayar ƙasa ta cigaba da kuka.

Yusuf ya cika da mamakin meyasa Widad kuka haka? Akwai buƙatar yasan me taje yi Hotel.

"malam kayi sauri ka maida ni gida, ka tsaya kana kallo na"

"Bazan iya tuƙin ba muddin zan cigaba da jin kukan ki" yai maganar fuskarsa ɗauke da damuwa

A hankali ta ɗago idanunta da suka yi jawur, ta saka ana Yusuf tana son gano gaskiyar abunda ya faɗa

"to meye haɗinka dani da kuka na ze dame ka, just drive ba ruwan ka da kukana, kayi abunda ke gabanka"

A hankali ya kunna motar, ya bata wuta ya cigaba da tuƙi, sedai gaba ɗaya hankalin sa baya jikin sa, yana can yana tunani daban daban.

Ihun Widad ne ya dawo dashi hayyacin sa, sannan ya lura da abunda ke shirin faruwa, duk yadda yayi ƙoƙarin kaucewa motar, seda me motar ya daki tasu.

Dafe kai Yusuf yayi yace  "Subhanallah"

A fusace ta kalli Yusuf "Are you out of your sense, see how you ruin my life, kashe ni kake so kayi? Baka gani ne? Dama so kake ka kasheni, an haɗa baki da kai zaka kashe ni ko? Dama na sani"

Kafin Yusuf ya bata amsa tuni me waccan motar ya fito yana zazzaga bala'i, an lotsa masa mota se an biya shi.

Yusuf ya buɗe motar ya fita jiki ba ƙwari, ya kalli mutumin ze kai shekaru Arba'in, Yusuf yace 
"Dan Allah kayi haƙuri, birki ne ya ƙwacemin, kuma kaga traffic ta tsaida hannun ka amma baka tsaya ba, kuma ni na riga na taho da gudu, amma dai kayi haƙuri"

"Shut up my friend, ni zaka gayawa traffic ta tsaida hannu na? Titin naka ne kai kaɗai da zaka dinga wannan gudun, banza shashasha kuma wallahi seka biya ni asarar da kayi min kokuma kaga abunda zan maka"

Tuni mutane suka fara taruwa, suka cika gurin ana ta bawa Mutumin nan haƙuri, dukda zagin da yakewa Yusuf amma haƙuri yake bashi, amma mutumin nan ya rintse ido yana zazzaga masifa yana cin zarafin Yusuf, hakimar kuwa ko fitowa ba tayi ba tana mota a zaune.

Yusuf yace "Amma naga idan laifi ne fa kaine kayi bani ba, Amma se baka haƙuri nake kana cigaba da cimin mutunci a gaban mutane, shikenan Yimin duk abunda zaka iya ka huce"

Yusuf dama gashi a cikin damuwa yake, ga shi ze zagin sa mutumin yake, aikuwa nan da nan temper ɗinsa ta hau zuciyar sa ta shiga tafasa, dan haka se yayi shiru ya dena cewa komai.

Mutumin ya cigaba da zazzaga masifa "Do you know who I am da zaka dingamin magana da gadara,? I will show you what am capable of doing, sena nuna maka ni waye, sena sa an sauke maka wannan rashin ɗa'ar taka mara tarbiyya kawai"

"You are nobody More than stupid Malam, waye kai idan har kai wani ne bazaka tsaya kana ɗaga murya akan wannan banzan gwangwanin motar taka ba, kayi abunda zaka yi an bige motar taka, ina son inga kai waye, kuma me zaka iya?"

Gaba ɗaya suka juyo inda Widad ke magana da jajayen idanunta.

Mutumin ya kalli Widad yace
"Lallai ka ɗakko karuwa a mota, dole ka ɗagamin murya danka birgeta, zanyi maganin ku daga kai har ita"
Ya ciro wayarsa yana waya.

Yusuf a harzuƙe zeyi magana Widad ta ɗaga masa hannu alamar yayi shiru.
Ta ɗakko wayar ta tayi 'yan taɓe taɓe.

Mutane suka ja gefe suna son ganin ƙarshen dramar, mintuna kaɗan sega motar 'yan sanda, suka zo suna wuri wuri, mutumin ya nuna musu Yusuf yace  "gashi nan shine, ku kama shi shida wannan koɗaɗiyar Yarinya me kama da sadakar Yalla"

Tuni ɗaya daga ɗan sandan yaje ya cakumo Yusuf, sedai me ɗan sandan ya jiyo bindiga a jikin Yusuf!!!

SHARE PLEASE 🙏

__Masha Allah nagode da addu'oinku Daddy yana samun sauƙi Alhamdilillah nagode sosai Allah yasaka da alkhairi __

Ayshercool
07063065680

_*AƘIDA TA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum


https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in






ELEGANT ONLINE WRITER'S




                               PART1
                                     Page 12




Ɗan sandan ya zare ido zeyi magana, Yusuf yayi saurin girgiza masa kai, ya juya ya kalli Widad yaga hankalinta baya kansu.

A hankali ya zura hannu a aljihun sa ya ɗakko ID card ya nunawa ɗan sandan, washe baki ɗan sandan yayi yana niyyar sarawa Yusuf, amma Yusuf ya girgiza masa kai yace

"Dan Allah Yallaɓai ku duba lamarin nan, ni bani da laifi a abunda ya faru, kuma na bashi haƙuri yaƙi haƙura"

Mutumin ya ƙaraso inda su Yusuf suke yace  "kaga Ku tafi da shi ajiyata ne, ku kulle shi har se nazo station ɗin"

Ɗan sandan Ya kalli Yusuf zeyi magana, sega wasu 'yan sandan sunzo, motar da' yan sandan suka zo ze tabattar maka da manyan wanda mutumin ya kirane, nan na farkon suka shiga sarawa wanda Widad ta kira.

Widad tace  "ina so a duba Accident ɗin nan, idan direba nane yake da laifi, zan biya shi kuɗin motar sa uku, idan kuma shi yayi laifin ze durƙusa ya bamu haƙuri, saboda cin zarafi da ɓata mana lokaci da yayi, in kuma yaƙi a tafi da shi, ajiyata ne a kulle shi se nazo"

Nan fa kallo ya koma sama, nan 'yan sanda suka shiga dube duben su, aka tabattar da mutumin nan shine ya karya doka, nan fa mutanen gurin suka ɗau sowa.

Widad taje gaban sa tace " if you are somebody you won't say it yourself, don't ever say you are Somebody when you are nobody, yanzu ka durƙusa ka bawa direba na haƙuri akan cin zarafin da kayi masa"

"Wallahi baki isa ba keɗin banza, in bawa wannan wulaƙantaccen haƙuri, kin san koni waye?"

Ɗaya daga 'yan sandan daya kira ne yaja shi gefe yace  "kai wallahi wannan' yar masu ƙasa ce, idan taso zatasa a ɓatar da kai gaba ɗaya wallahi, kayi abunda tace kota sa a ɗaureka"

"wannan ƙaramar yarinyar 'yar cikina?"

"to karkayi cigaba da taurin kai, wannan' yan sandan data kira muma iyayen gidanmu ne"

Mutumin ya dawo a ƙule ya kalli Yusuf yace  "Yi haƙuri"

"Akan gwiwowinka zaka durƙusa ka bashi haƙuri" cewar Widad

Cikin tsawa wani ɗan sanda yace "ba zakayi bane? Semun tafi da kai?"

A hankali yaja da baya ze durƙusa, Yusuf yayi saurin riƙe shi tare da girgiza kai ya kalli Widad yace  "please Madam ina nema masa Alfarma, kiyi haƙuri dan Allah, ni zan durƙusa in baki haƙurin a madadinsa"

Dama Widad tasan Yusuf baze taɓa yadda hakan ta faru ba, tayi ne dan nunawa Mutumin shi ɗin bakomai bane.

"Shikenan tunda ya haƙura, gobe in Allah kaimu, yaje station ɗinka ya karɓi kuɗin motar sa, na ninka maka masa sau uku, Amma ya kiyaye gaba"

Ta juya ta tafi motar su, Izzar Widad da yadda ta tafi da al'amuran cikin isa da izza, da bajinta suka birge mutane, aka dinga sowa, anawa mutumin nan dariya.
Dare yayi musu a gurin nan saboda wannan incident ɗin, Yusuf yaja motar cikin nutsuwa suka tafi.

Amma still lokaci lokaci tana goge Hawaye a fuskarta, suka ci gaba da tafiya Yusuf na godewa Allah da Widad bata ga bindigar nan ba, tabbas yasan da Asirinsa ya tonu daya gama kaɗewa, ƙarshen ta seta kulle shi me fitar dashi se Allah.

suna zuwa gida Yusuf yayi horn Isa ya buɗe musu gate, Yusuf ya shiga da motar yayi parking, har ya gama abunda zeyi ze buɗe motar ya fita, Widad tana zaune ko gezau ba tayi ba, bata da niyyar fita daga motar.
fita yayi ya zagaya ya buɗe mata ƙofar, yace  "Munzo fa" ɗaga kai tayi ta kalle shi, a hankali ta zuro ƙafafunta da take jin kamar ba'a jikinta suke ba waje ta yunƙuro ta fito, sedai tana fitowa ta tafi luuu zata faɗi, cikin zafin nama Yusuf zama shamaki da faruwar hakan, ta hanyar  riƙeta ta faɗa a jikinsa.
Ƙirjinsa ya dinga bugawa da ƙarfi, saboda jin hakan wani irin abu daban, Isa me gadi ne ya zaro ido ganin abunda yake faruwa, Yusuf kamar me raɗa  yace  "Are you ok?"
Jinjina masa kai tayi ta sake ƙoƙarin miƙewa, amma still jiri ke kuma ɗibarta, tafiya take tana tangaɗi kamar wadda tasha wani abu, Yusuf yabi bayanta ya mata rakiya har cikin babban falo, hannunsa riƙe da ƙaramar jakarta da kuma wayar ta.

A babban falon ta zauna tana riƙe kai, hawaye nata zarya a fuskar ta, ƙoƙarin cire takalmin ƙafarta take, amma abu ya gagara, se kokawa take da takalmin.
Yusuf ya taka inda take  ya durƙusa ya kwance igiyar takalmin nata me tsinin tsiya ya cire mata.

Ta gyara kwanciyar ta sosai ta miƙe ƙafafunta akan doguwar kujerar tare da lumshe idonta, don bawa hawayen idon nata damar gangarowa.

Yusuf a ransa yace 'Ikon Allah, wannan wane irin kuka ne?'

"ko za'a kira likita ne?"

"Ni lafiya ta ƙalau" ta bashi amsa idonta a rufe.

"Jikinki yana rawafa, kamar zazzaɓi ze kamaki fa"

"to ina ruwan ka? Jikin ka ne ko nawa? Ni kaimin kayana ɗaki ka tafi ka ban guri"

Ɗan girgiza kai Yusuf yayi yaje ya ajiye mata kayan ta ya fito, tana nan inda ya barta, yasa kai ya fice.

Yana fitowa ƙofar da zata sa dashi da harabar gidan yaji an riƙo rigarsa, waigawa yayi yaga waye wannan.
Amal ce tsaye tana huci,
"Amal lafiya kuwa?"
"dole kace lafiya mana? Yusuf daga ina kake kai da Widad?, saboda tsabar abu harda cire mata takalmi, Yusuf wai kai wani irin mutum ne dan Allah? Me kake aikatawa ne haka Yusuf? me yasa lallai seka yi abunda zaka birgeta, bayan kullum baka da kima a idon ta? Sau nawa nake gaya maka kusanci da ita tamkar kusanci da mutuwarka ne? "

Yusuf yace " look Amal niba wani abu nake nema a gurin Widad ba, kuma ba neman kusanci nake da ita ba, kawai ina tausayinta ne, kuma ina jin daɗin yadda mahaifinta ke mutuntani"

"kace tausayi Yusuf? Yusuf daga tausayi so yake shiga, ban taɓa ganin mutumin daya samu damar da ka samu a gurin ta ba, Yusuf a gidan nan ba kowa keda ikon zuwa inda take ba in bada izinin ta ba, kai kuwa kana iya zuwa gurin ta duk lokacin da kake so a matsayin ka na direbanta, Yusuf ina kishin ka, Yusuf sonka nake wallahi bazan zuba ido abubuwa su cigaba da gudana tsakanin ka da Widad a haka ba"

"Amal, Soyayya tsakanina dake ba zata yuwu ba, Mahaifiyarki bata ƙaunar talaka, kuma ni talaka ne inani ina iya Soyayya dake Amal?Hausawa suka ce ƙwarya tabi ƙwarya, idan tabi akushi zata fashe"

"dakata Yusuf" Amal ta katse shi, hawaye tuni ya fara sintiri a idon ta, tace  "bazaka iya Soyayya dani ba, amma zaka iya da Widad ko?"

"Amal ni ba Soyayya nake da Widad ba, inani ina son mace kamar ta, ita a kanta bata yarda da wata soyayya ba, Amal nayi Soyayya a baya, abun da na fuskanta a soyayya bazan ƙara yadda in sake fuskantar sa ba, ke kanki da kin san wayeni bazaki soni ba, ba zaki so kasancewa da mutum kamar ni ba, kiyi hakuri "

"ba abunda ya shafeni, what I know is that ba zan zuba ido ka faɗa soyayya da mahaukaciya mara tarbiyya ba, kuma bari in gaya maka ba zaka taɓa kuɓucemin ba kasa wannan a ranka"

Tana gama faɗar haka ta juya da sauri ciki tana kuka, jikin Yusuf yayi sanyi a haka ya ja jiki ya fito.

Masallaci ya wuce yai sallolinsa, sannan ya zauna yana karatun Al'qur'ani mai girma, ya daɗe yana addu'a sannan ya miƙe ya nufi titi dan samun abun hawa zuwa gida.

Abunka da unguwar masu kuɗi, tuni unguwar tayi tsit se sanyi bishiyoyi dake kaɗawa, yana ta tafiya a ƙasa yana tunanin abubuwa da dama, ya baro layin su Widad sosai inda security suke, ba tsammani se gani yayi ansha gaban
sa da mota, tsayawa yayi cak yaga ikon Allah.

Wasu ƙarti ne suka fito daga motar suka zagaye shi, ɗayan yace  "kaine direban 'yar gidan Alhaji Nasir?"
Ba tare da tsoro ko shakka ba Yusuf yace  "Eh nine"

"Good labari ya ishemu cewar akwai kusanci tsakanin ka da ita, duk inda zata tare kuke zuwa, an samu mu ɗakkota kwanaki amma ka hana, bari in gaya maka wani abu, zamu ƙyaleka ne saboda zakayi mana amfani, zamu ci gaba da bibiyar ka saboda akwai wani abu da muke so ka karɓo mana a gurin ta" cewar ɗaya daga cikin ƙartin

Yusuf yace "Babu wani kusanci tsakanin mu, aiki nake mata tana biyana, ko meye kuje ku tambaye ta ta baku mana"

Ɗaya daga cikin sune ya sakarwa Yusuf wani mummunan naushi, da seda jini ya fito daga bakin sa, a zuciye Yusuf ya ɗago yana kallonsu, babban yace

"Wallahi idan baka kawo mana abun nan ba se mun kasheka, akwai wasu mahimman abubuwa da muke so ka karɓo mana a gurinta idan kaƙi semun maka yankan rago"

"Bayan yankan ragon se kuma me?" Yusuf ya faɗa babu alamar tsoro

Wani naushin suka ƙara masa a gefen ido,
Maimakon Yusuf ya tsorata, ko ya nuna jin zafin naushin, se yayi murmushi yace

"idan kunmin yankan rago, ku kuma ku zauna a naɗe duniya daku?, babu wani mahaluki daya isa yasa Yusuf yin wani abu dan son zuciya da zalunci, kuje ku gayawa wanda ya aiko ku cewar karya kuskura yayi gangancin cin iyakar gonar da ba tasa ba, idan kuma yaƙi zanwa shukokin feshi in ƙone nawa da nashi, kowa ya rasa, wannan saƙon Yusuf ne ga uban gidanku ko wayeshi"

Wani naushin suka yi niyyar kai masa amma ya riƙe hannun ɗayan.

"Waye kai? Waye ya gaya maka wanine ya turomu?" cewar ɗaya daga cikin su

"yadda kuka binciko kuka gano nine direban Widad, haka yakamata ku bincika kusan wayeni, nasani aikoku akayi ku koma ku ƙara tabbatarwa wanda ya aikoku nina ɗauke Widad lokacin da yasa a sace ta, ni aikina tuƙata a mota dan haka ya kiyayi yunƙurin cutar dani"

Hausawa sukace 'sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, sun daki Yusuf sosai, yaso yayi amfani da bindigar sa, amma yin hakan ze rusa masa da yawa daga shirinsa, dan haka ya fasa ɗaukar bindigar, suka daddake shi, wani yana iya ramawa wani kuma baya iyawa.

"zamu cigaba da bibiyarka, harse ka bamu abunda muke nema, zaka gane baka da wayo, Uban taurin kai, Ubangidanmu yafi ƙarfinka"

haka suka barshi a gurin suka tafi.

Da ƙyar Yusuf yaja jikin sa ya hau Napep ya tafi, hancinsa yana ta zubar da jini, jiri ne yake ta ɗibarsa saboda jinin da yake zubarwa da yawa, da ƙyar yaje gida, Allah ya temake shi Umma tayi bacci.

ya cire kayan jikinsa yana goge jinin fuskarsa, Aljihun wandonsa ya taɓa yaji wayar da Widad ta bashi ɗazu.

Hannu yasa ya ɗakko ta yana jujjuya ta  "Ka ɓoye ta kamar yadda zaka ɓoye ranka, wannan wayar tamkar rayuwar ka ce"

Maganar Widad ta dawo masa, kunna wayar yayi, Amma akwai password akai shiru yayi yana nazarin kamar yaya wayar nan tamkar rayuwar sa take? Ajiye wayar yayi ya shiga yayi wanka ya fito, nan ya shiga aikin nasa na tunani dan abubuwa da dama sun faru da suke buƙatar nazari.

"Me Widad taje yi Hotel? Me ta gani ya sata kuka? Waye ya turo mutanen nan? Ko waye akwai sa hannun wani a gidan su Widad? Amma dagaske Tausayin Widad zesa ya fara sonta? Me yasa tasa a durƙusa a bashi haƙuri yau? Tabbas zata iya yuwuwa akwai Alaƙa tsakanin wani a gidansu Widad da mahaifin Nurat"

Ji yayi kansa kamar ze fashe, dan haka ya rintse idon sa yana addu'a da fatan bacci ya ɗauke shi koze ɗan samu nutsuwa, Amal ta faɗo masa a rai itama, wai ita bilhaƙƙi son shi take.
Wani tunani ya shigayi watanni shida da suka gabata, da yanzu yana nan da Auren sa, katsam a dalilin irin tasa ƙaddarar aka fasa wannan Aure, bayan cin zarafi da wulaƙanci daya fuskanta daga iyayen matar daze Aura, bacci dai se ɓarawo ne ya ɗauke shi.

*******************************

Da safe Yusuf ya tashi da matsanancin zazzabi, kansa har sarawa yake sosai saboda dukan da yasha jiya, juyi kawai yake akan gadon gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, ganin har kusan ƙarfe tara be fito ba yasa Umma leƙawa ɗakin sa, ta tarar da shi kwance a kan gadon sa, ƙarasawa tayi ta taɓa jikin sa tace  "Yusuf lafiya kuwa? Naga har ƙarfe tara baka fito ba?"

"Bana jin daɗi ne Umma"
"dan baka jin daɗi seka zo ka kwanta kana juyi, ka tashi ka watsa ruwa, ka karya seka sha magani"
"to Umma"
Yusuf ya miƙe ya shiga yai wanka, kayan breakfast ɗin ta kawo masa ɗaki, ta kalle shi tace 
"Yusuf kamar kumburi nake gani a gefen idonka da bakin ka"

Yusuf yace  "Mun faɗi akan babur ne jiya da daddare"

"Amma ka kasa gayamin? Meye amfanin hakan, haba Yusuf"
Yusuf yace  "Yi haƙuri Umma, bana son ɗaga miki hankali ne"

"Amma ina fatan ba wani mummunan ciwo daka ji?" tai maganar cike da damuwa

"Eh banji ciwo me yawa ba"

Da kanta ta zauna tana bashi Abinci a baki, ta ɗakko masa first aid box ɗinsa ya ɗau magani ya sha, ya koma ya kwanta.

Kwanciyar sa ba daɗewa Abbas ya kira shi, da ƙyar Yusuf ya ɗaga wayar, Abbas yace  "Mutumina kana ina ne? Ina son ganin ka"

"Ina gida bana jin daɗi ne"

"Subhanallah, meya sameka?"

"Zazzabi ne" Yusuf ya bashi amsa

"Shikenan gani nan zuwa"
Su kayi sallama

**************************

Hajiya Halima na zaune falon ta tana shan tea, Isa mai gadi yazo yana kwaɗa sallama a ƙofar falon ta, A fusace tace "wai meye hakane? Lafiya kame do kamin wannan sallama kamar kana bina bashi?"

"Hajiya nine, Isa ne"
"to ya a kayi?"
"Hajiya gurin ki nazo"
Ta ɗanyi tsaki sannan tace  "shigo"
Ya shiga falon ya durƙusa yace 
"Ina kwana?"
"Kai bana son doguwar gaisuwar nan meke tafe da kai?"

"to Hajiya kin san shi sha'ani na rayuwa kiwon mutum ake ba dabba ba koba haka ba?"

"kai nifa bana son wannan surutam banzae, ka faɗamin kanka tsaye meke tafe da kai"

Isa ya gyara zama yace  "game da sabon direban nan ne Yusuf, gaskiya Hajiya akwai buƙatar kisa ido, jiya yadda na gansu Allah ya nuna min Annabi salallahu alaihi wassalam, kin san dai irin shigar da take yi, bayan kin fita ita dashi suka fita, basu dawo ba se ƙarfe tara na dare, bayan sun dawo a gabana da idanun nan nawa" yai maganar yana gwalo idon nasa ya cigaba da cewa
"da idanu na naga suna rungume juna, Hajiya a saka ido, kina gani idan ba kiranmu akayi ba bamu da damar shigowa kiga yadda take hantarar mu, Amma shi ba yau ba gobe cikin sintiri yake har cikin ɗakin kwanan ta, Allah kaɗai yasan me suke yi, gaki da 'yan mata kema kyawawa bekamata yana gardi baligi ya dinga wucewa yana kalle miki su ba, shiyasa nace bari inzo in sanar dake abunda ake ciki "

Dire kofin hannun ta tayi, taja wata nannauyar Ajiyar zuciya tace " Hmm naji maganganun ka, kuma kazo da magana abun dubawa, tashi kaje zan san abunda zanyi "

Isa ya miƙe yana murna yace
"shikenan Hajiya na barki lafiya "

Shiru Hajiya Halima tayi tana zake nazartar kalaman Isa megadi, tabbas Widad bata yadda wani ya Wulaƙanta Yusuf ba, lokacin da ciwon ta ya tashi taƙi yadda da kowa se Yusuf, idan har dagaske wani abu na faruwa a tsakanin su to tabbas akwai yuwuwar ta gayawa Yusuf inda abunda suke nema yake.

**************************

Widad kwana tayi da zazzabi da ciwon kai, da ƙyar ta samu tayi bacci.
Jikin ta sam babu ƙwari ta miƙe domin haɗawa magen ta abunda zeci.
Widad na matuƙar son dabbobi, tana tausayin su fiye da yadda take tausayin mutane, akwai shaƙuwa me ƙarfi tsakaninta da dabbobinta, mussman ma wannan magen nata pita, da kuma karen ta dake gidan gona, tana jin daɗin kasancewa da su, dan ba ƙaramin ɗebe mata kewa sukeyi ba.

Ta samu container ta zuba masa madara, ta samo wani ta zuba masa gugguru, ta koma gefe tana kallon magen, maimakon magen yaci seya koma jikin ta ya kwanta, dan ya saba idan lokacin cin Abinci yayi, ta zuba masa nasa yana ci itama tana cin nata

**********************************

Abbas ne yayi Sallama ɗakin Yusuf, da ƙyar Yusuf ya iya amsawa, ya miƙe zaune suka gaisa da Abbas.

"Sannu Yusuf, ko Asibiti za muje in sauke ka"

Yusuf ya girgiza kai yace  "A'a na sha magani kawai, ya kake ya aikin?"

"Alhamdilillah, jiya Oga Suleiman yake neman ka, shine kiran da nayi maka, kuma se kace baka jin daɗi, yanzu yau ba zaka gidan su mutuniyar taka ba?"

Yusuf yace  "bazani ba gaskiya, sedai zuwa gobe in Allah ya kaimu idan naji sauƙi"

Abbas yayi ƙasa da murya yace 
"Ya kuɗin nan waye ya turo dasu kuwa?"

"itace wai Albashi na ne na watanni uku da bata bani ba, nace mata yayi yawa ta rage taƙi"

"Taɓɗijan kaima Yusuf da wani abu, kamarya ta rage? Malam kawai kaci kuɗi, meye labari kuma?"

Yusuf ya gaya masa Hotel da suka je, da yadda suka dawo tana kuka, Amma be gaya masa zancen wayar nan ba data bashi.
Nan suka cigaba da tattaunawa zuwa wani lokaci Abbas yace ze tafi, Naira dubu ɗari Yusuf yayi masa transfer a cikin kuɗin, Abbas yaita murna yana godiya suka yi sallama.

Amma ƙasan zuciyar Abbas kamar ya fasa ihu
'dana san wannan alherin Yusuf zeje ya dinga samu da tun farko nina karɓi aikin nan, ya samu dubu ɗari biyar amma ya bani wata shegiyar dubu ɗari, ga danƙareriyar waya ya samu, na tura shi dan ina gudun wulaƙanci amma yaje yana samo abun Arziki, dole in san yadda zanyi a cire shi daga kan aika ni maye ni"

'Amma hatsari da kasadar dake cikin aikin fa?' wata zuciyar ta tambaye shi, tsaki yayi yana ci gaba da surutai.

*******************************
Shafa jikin magen take a hankali tana lallaɓashi yaci Abinci, wayarta ce ta fara ringing, muzurun nan ya kasa a guje yaje ya ɗakko ta a bakin sa ya kawo mata, shafa kan muzurun tayi tace  "thank you Roux"
Ta amsa wayar tasa a kunnen ta
"Ranki ya daɗe Bala fa babu lafiya, an ɗauke shi rai a hannun Allah an kai shi Babban Asibitin cikin gari, dan besan waye a kansa ba"

Miƙewa tayi tsaye tace  "what? How comes? Wace irin rashin lafiya ce wannan?"

"Nima ban sani ba gaskiya, Amma an fita da shi daga Asibitin cikin kurkukun gaba ɗaya"

Bata kashe wayar ba ta miƙe, da sauri ta shiga bedroom ɗinta ta canza kaya, dukda yanayi na rashin lafiya da take ciki, wayar ta ta koma ta ɗakko ta fara daddanawa sannan tasa a kunnen ta.

Yusuf yana jin wayarsa tana ringing ya ƙi ɗagawa yasa ta a silent, ya ajiye wayar ya cigaba da kwanciyar sa.

Jifa tayi da wayar akan kujera ta fice harabar gidan, gurin su Nura ta nufa, tana zuwa suna gaishe ta amma bata kula suba tace 
"Ku kiramin driver yanzu"
Jiki na rawa suja shiga kiran Yusuf babu ƙaƙƙautawa, Amma be ɗaga ba.

Ta kalli Nura tace "ɗakko mota da sauri, zaka fita dani"

Cike da washe baki yaje ya ɗakko mota, ta shiga Nura yaja motar suka fita, gaba ɗaya ji take kamar tayi Amai, dukda a bayan motar ta zauna amma warin hammatar Nura ya cika motar, se tsaki take yi badan ya zama urgent ta fita ba babu yadda za'ayi ta yadda wannan ƙazamin ya jata a mota, suna tafe tana masa tsawa gami da hantararsa, Amma Yusuf ze gane kurensa na ƙin zuwa da yayi yau sannan yaƙi ɗaga waya.

Prison tasa ya kaita, suna zuwa ta fita ta shiga, kai tsaye ofishin Hisham ta wuce.
Yana ganin ta yai murmushi ya sallami kowa daga office ɗin sannan yace  "barka da zuwa lady boss, Ashe kin dawo Nigeria?"

"Ya aka yi Bala ya kamu da rashin lafiya da har ta kai shi ga kwanciya, seda aka fita da shi daga gidan nan?"

"Ranki ya daɗe gaskiya dama yana ɗanyin rashin lafiyar a tsai tsaye, Kawai se ɗan uwansa ya kawo masa ziyara, bayan ya tafi jikin sa ya rikice"

"yanzu kana nufin kace min Ɗan uwansa ne ya kawo masa abunda yaci, jikin sa ya rikice kenan? Saboda sakaci da rashin sanin aikin ku?"

"A'a ranki ya daɗe kin san?...

"Yimin shiru malam, saura sati ɗaya tal a koma kotu, kawai se inji wannan banzar maganar mara tushe, shikenan amma kasani idan har rashin lafiyar Bala haɗin baki ne, duk wanda yake da hannu a ciki shima abunda ya samu bala ze sameshi. "

Ta miƙe a fusace ta fito, Hashim ya biyo ta da sauri amma ta shiga mota da niyyar ta ta wuce gurin lawyern Daddy, amma ba zata iya jure wannan tsamin da Nura yake ba, dan haka tace ya nsida ita gida, tana mamakin ƙoƙari irin na Daddy da yake iya shaƙe wannan warin hammatar, Yusuf kullum tsaf dashi cikin ƙamshi, amma wannan ƙazamin kamar baya jin yadda yake wari, seda ta bari sun koma gida, sannan tayi wa Nura ta tas akan ƙazanta da warin da yake yi a gaban sauran ma'aikatam.

Gaba ɗaya ranta a ɓace, ga jikin ta ba ƙwari gashi a ƙule take da Yusuf, tana shiga babban falo ta tarar da Hajiya Halima, bata kula ta ba tasa kai zata wuce
"Widad ina son Magana dake"

Widad ta tsaya ta juyo ta kalleta ba tare da tace komai ba.

"Widad bekamata ace kina fita lokacin da kike so ki dawo lokacin da kike so ba a matsayin ki na mace, sannan ki dinga dawowa sanda kika ga dama ba, Alhalin nida nake zaune tare dake ban san idan kike zuwa ba, Sannan wannan yaron da yake sintiri gurin ki har ƙuryar ɗakin ki, Sam be dace ba"

"kinga dakata Malama, zamanki nake a cikin gidan nan? Koke kika ajiyeni? In kun tashi taku yawon gayamin kuke? Kisawa ranki gidan nan tamkar bariki yake, kowa yayi abunda yaga dama muddin be ƙetare abunda masu gidan suke so ba, karki ƙara shiga sabgata, kuma kowa zan kawo cikin gidan nan gidanmu ne, kowa ze je har cikin ɗakina babu ruwanki, kome nake aikatawa karki ƙara shiga, dan ke ba uwa ta bace baki haifeni ba, baki da ikon ki samun ido, kema abar a sawa ido ce, kisa ido akan 'ya' yanki kawai, ba ruwan ki dani....

"Widad!!!" Ramlah ta kira sunan Widad da ƙarfi

"Ramla don't ever try to shout at me, a gidan mu kike ba gidan ku ba, dan haka ki iya bakin ki, tun kan in fusata"

Tana gama maganar ta juya ta tafi part ɗin ta.

"Tirƙashi Mummy dan Allah ki bani dama ko sau ɗaya, inci mutuncin yarinyar nan in koya mata hankali ko zanji sanyi a zuciyata"

Mummy ta girgiza kai tace  "Kina yin haka Ramla kin ɓata komai, rabu da ita lokaci ne, yana nan zuwa da zata girbi abunda ta shuka"

**********************************

Se wajen la'asar sannan Yusuf ya ɗanji sauƙi ya tashi, ya shirya yaje Asibiti, aka duba shi aka bashi magunguna.
ya dawo gida ya wuce ɗakinsa, wayarsa ya ɗakko ya duba, yaga missed calls rututu, ko ba'a  gaya masa ba yasan Widad ce take neman sa, bebi ta kansu ba ya ajiye wayar ya cigaba da harkokinsa.

Dayaji ya ɗanji ƙwarin jikin sa, seya shirya tsaf ya tafi hotel ɗin da suka je da Widad, Manager yaje nema amma be sameshi ba, ya cewa ma'aikatan su bashi lambar wayar sa, da farko suka ƙi, seda ya nuna musu id card ɗin sa sannan suka bashi, seda ya zagaya lungu da saƙo na Hotel ɗin, yana sake monitoring mutanen dake shiga da fice a hotel ɗin sannan ya koma gida.

Washegari da safe dukda ya tashi jikin sa babu daɗi, Amma haka ya shirya ya tafi gidan su Widad.

Tunda yaje Isa yake masa wani irin kallon banza, yanata habaice habaice
Shi dai Yusuf be kula shi ba, Nura yace

"Wallahi Yusuf yau kana ruwa, bama kusa da kada ba, cikin bakin kada, jiya ta fusata sosai, dan zata fita seni na kaita saboda baka zo ba"

Murtalah ya kwashe da dariya yace  "bayan kun dawo kuma tai maka tatas a gabanmu ba, saboda ƙazanta kai Nura jiya kaga tijara a tsakar rana, ai idan nine kai ko maganar ba zan ɗakko yau ba" yai maganar yana dariya

Nura ya haɗe rai yace
"Bana son rashin mutunci da Iskanci"

Ganin suna nema suyi faɗa yasa Yusuf yin gaba abunsa ya barsu a gurin, tafiya kawai yake yi amma jikin sa babu daɗi.

Yana shiga falon ya tarar da Ramadan ɗan gidan Alhaji Bulama da Amal suna hira.

Yusuf yace  "barkanku da Safiya"

Bata amsa masa ba se Ramadan ne yace  "Yawwa barka dai, bodyguard ɗin gimbiya" Yusuf ya ɗanyi murmushi ya nufi hanyar Widad.

Bayansa Amal tabi da kallo, taji wasu hawaye na ƙoƙarin zubo mata, ta tsani kusancin Widad da Yusuf gani take komai ze iya faruwa, wani sashin na zuciyar ta ma yana gaya mata akwai wata alƙar a tsakaninsu saboda kusancinsu yayi yawa.

Ramadan ya kalleta yace "lafiya kuwa my?"

Girgiza masa kai kawai tayi tace  "lafiya ƙalau"

Yusuf ya shiga ya tsaya a bakin ƙofar bedroom ɗin ta sannan yayi sallama kamar yadda ya saba.

Yayi Sallama kusan uku amma bata amsa ba, haka ya cigaba da tsayuwa a gurin, seda aka kwashi wani lokaci sannan ta fito, kallon sa tayi daga sama zuwa ƙasa sannan tace 
"Sannu ishashshe kaga damar zuwa kenan?"
Shiru Yayi ya sunkuyar da kai, ɗakin ta shige yabi bayanta da sallama

"Meya hanaka zuwa jiya? Kuma kaƙi ɗaga waya?"

"Bani da lafiya ne shiyasa"

"ƙarya kake" ta faɗi kai tsaye ba tare da duba ratar shekarun da Yusuf ɗin ya bata ba, shiru ya sake yi bece komai ba, ta tako tazo daf dashi tace 
"for the second time meya hanaka zuwa jiya?"

"bani da lafiya ne" ya sake bata amsa

"wai me yasa baka kunyar yin ƙarya ne, meyasa? Ban gaya maka bana son ƙarya ba?" tai maganar tana ƙoƙarin sa idon ta a cikin nasa

Babu zato ya janyota gaba ɗaya tana facing ɗinsa, ya kafe ta da idon sa, nata cikin nashi ya ƙura mata ido

Ayi sharing please 🙏🙏🙏

Ayshercool
0706306568_*AƘIDA TA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum


https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in






ELEGANT ONLINE WRITER'S




                               PART1
                                     Page 12




Ɗan sandan ya zare ido zeyi magana, Yusuf yayi saurin girgiza masa kai, ya juya ya kalli Widad yaga hankalinta baya kansu.

A hankali ya zura hannu a aljihun sa ya ɗakko ID card ya nunawa ɗan sandan, washe baki ɗan sandan yayi yana niyyar sarawa Yusuf, amma Yusuf ya girgiza masa kai yace

"Dan Allah Yallaɓai ku duba lamarin nan, ni bani da laifi a abunda ya faru, kuma na bashi haƙuri yaƙi haƙura"

Mutumin ya ƙaraso inda su Yusuf suke yace  "kaga Ku tafi da shi ajiyata ne, ku kulle shi har se nazo station ɗin"

Ɗan sandan Ya kalli Yusuf zeyi magana, sega wasu 'yan sandan sunzo, motar da' yan sandan suka zo ze tabattar maka da manyan wanda mutumin ya kirane, nan na farkon suka shiga sarawa wanda Widad ta kira.

Widad tace  "ina so a duba Accident ɗin nan, idan direba nane yake da laifi, zan biya shi kuɗin motar sa uku, idan kuma shi yayi laifin ze durƙusa ya bamu haƙuri, saboda cin zarafi da ɓata mana lokaci da yayi, in kuma yaƙi a tafi da shi, ajiyata ne a kulle shi se nazo"

Nan fa kallo ya koma sama, nan 'yan sanda suka shiga dube duben su, aka tabattar da mutumin nan shine ya karya doka, nan fa mutanen gurin suka ɗau sowa.

Widad taje gaban sa tace " if you are somebody you won't say it yourself, don't ever say you are Somebody when you are nobody, yanzu ka durƙusa ka bawa direba na haƙuri akan cin zarafin da kayi masa"

"Wallahi baki isa ba keɗin banza, in bawa wannan wulaƙantaccen haƙuri, kin san koni waye?"

Ɗaya daga 'yan sandan daya kira ne yaja shi gefe yace  "kai wallahi wannan' yar masu ƙasa ce, idan taso zatasa a ɓatar da kai gaba ɗaya wallahi, kayi abunda tace kota sa a ɗaureka"

"wannan ƙaramar yarinyar 'yar cikina?"

"to karkayi cigaba da taurin kai, wannan' yan sandan data kira muma iyayen gidanmu ne"

Mutumin ya dawo a ƙule ya kalli Yusuf yace  "Yi haƙuri"

"Akan gwiwowinka zaka durƙusa ka bashi haƙuri" cewar Widad

Cikin tsawa wani ɗan sanda yace "ba zakayi bane? Semun tafi da kai?"

A hankali yaja da baya ze durƙusa, Yusuf yayi saurin riƙe shi tare da girgiza kai ya kalli Widad yace  "please Madam ina nema masa Alfarma, kiyi haƙuri dan Allah, ni zan durƙusa in baki haƙurin a madadinsa"

Dama Widad tasan Yusuf baze taɓa yadda hakan ta faru ba, tayi ne dan nunawa Mutumin shi ɗin bakomai bane.

"Shikenan tunda ya haƙura, gobe in Allah kaimu, yaje station ɗinka ya karɓi kuɗin motar sa, na ninka maka masa sau uku, Amma ya kiyaye gaba"

Ta juya ta tafi motar su, Izzar Widad da yadda ta tafi da al'amuran cikin isa da izza, da bajinta suka birge mutane, aka dinga sowa, anawa mutumin nan dariya.
Dare yayi musu a gurin nan saboda wannan incident ɗin, Yusuf yaja motar cikin nutsuwa suka tafi.

Amma still lokaci lokaci tana goge Hawaye a fuskarta, suka ci gaba da tafiya Yusuf na godewa Allah da Widad bata ga bindigar nan ba, tabbas yasan da Asirinsa ya tonu daya gama kaɗewa, ƙarshen ta seta kulle shi me fitar dashi se Allah.

suna zuwa gida Yusuf yayi horn Isa ya buɗe musu gate, Yusuf ya shiga da motar yayi parking, har ya gama abunda zeyi ze buɗe motar ya fita, Widad tana zaune ko gezau ba tayi ba, bata da niyyar fita daga motar.
fita yayi ya zagaya ya buɗe mata ƙofar, yace  "Munzo fa" ɗaga kai tayi ta kalle shi, a hankali ta zuro ƙafafunta da take jin kamar ba'a jikinta suke ba waje ta yunƙuro ta fito, sedai tana fitowa ta tafi luuu zata faɗi, cikin zafin nama Yusuf zama shamaki da faruwar hakan, ta hanyar  riƙeta ta faɗa a jikinsa.
Ƙirjinsa ya dinga bugawa da ƙarfi, saboda jin hakan wani irin abu daban, Isa me gadi ne ya zaro ido ganin abunda yake faruwa, Yusuf kamar me raɗa  yace  "Are you ok?"
Jinjina masa kai tayi ta sake ƙoƙarin miƙewa, amma still jiri ke kuma ɗibarta, tafiya take tana tangaɗi kamar wadda tasha wani abu, Yusuf yabi bayanta ya mata rakiya har cikin babban falo, hannunsa riƙe da ƙaramar jakarta da kuma wayar ta.

A babban falon ta zauna tana riƙe kai, hawaye nata zarya a fuskar ta, ƙoƙarin cire takalmin ƙafarta take, amma abu ya gagara, se kokawa take da takalmin.
Yusuf ya taka inda take  ya durƙusa ya kwance igiyar takalmin nata me tsinin tsiya ya cire mata.

Ta gyara kwanciyar ta sosai ta miƙe ƙafafunta akan doguwar kujerar tare da lumshe idonta, don bawa hawayen idon nata damar gangarowa.

Yusuf a ransa yace 'Ikon Allah, wannan wane irin kuka ne?'

"ko za'a kira likita ne?"

"Ni lafiya ta ƙalau" ta bashi amsa idonta a rufe.

"Jikinki yana rawafa, kamar zazzaɓi ze kamaki fa"

"to ina ruwan ka? Jikin ka ne ko nawa? Ni kaimin kayana ɗaki ka tafi ka ban guri"

Ɗan girgiza kai Yusuf yayi yaje ya ajiye mata kayan ta ya fito, tana nan inda ya barta, yasa kai ya fice.

Yana fitowa ƙofar da zata sa dashi da harabar gidan yaji an riƙo rigarsa, waigawa yayi yaga waye wannan.
Amal ce tsaye tana huci,
"Amal lafiya kuwa?"
"dole kace lafiya mana? Yusuf daga ina kake kai da Widad?, saboda tsabar abu harda cire mata takalmi, Yusuf wai kai wani irin mutum ne dan Allah? Me kake aikatawa ne haka Yusuf? me yasa lallai seka yi abunda zaka birgeta, bayan kullum baka da kima a idon ta? Sau nawa nake gaya maka kusanci da ita tamkar kusanci da mutuwarka ne? "

Yusuf yace " look Amal niba wani abu nake nema a gurin Widad ba, kuma ba neman kusanci nake da ita ba, kawai ina tausayinta ne, kuma ina jin daɗin yadda mahaifinta ke mutuntani"

"kace tausayi Yusuf? Yusuf daga tausayi so yake shiga, ban taɓa ganin mutumin daya samu damar da ka samu a gurin ta ba, Yusuf a gidan nan ba kowa keda ikon zuwa inda take ba in bada izinin ta ba, kai kuwa kana iya zuwa gurin ta duk lokacin da kake so a matsayin ka na direbanta, Yusuf ina kishin ka, Yusuf sonka nake wallahi bazan zuba ido abubuwa su cigaba da gudana tsakanin ka da Widad a haka ba"

"Amal, Soyayya tsakanina dake ba zata yuwu ba, Mahaifiyarki bata ƙaunar talaka, kuma ni talaka ne inani ina iya Soyayya dake Amal?Hausawa suka ce ƙwarya tabi ƙwarya, idan tabi akushi zata fashe"

"dakata Yusuf" Amal ta katse shi, hawaye tuni ya fara sintiri a idon ta, tace  "bazaka iya Soyayya dani ba, amma zaka iya da Widad ko?"

"Amal ni ba Soyayya nake da Widad ba, inani ina son mace kamar ta, ita a kanta bata yarda da wata soyayya ba, Amal nayi Soyayya a baya, abun da na fuskanta a soyayya bazan ƙara yadda in sake fuskantar sa ba, ke kanki da kin san wayeni bazaki soni ba, ba zaki so kasancewa da mutum kamar ni ba, kiyi hakuri "

"ba abunda ya shafeni, what I know is that ba zan zuba ido ka faɗa soyayya da mahaukaciya mara tarbiyya ba, kuma bari in gaya maka ba zaka taɓa kuɓucemin ba kasa wannan a ranka"

Tana gama faɗar haka ta juya da sauri ciki tana kuka, jikin Yusuf yayi sanyi a haka ya ja jiki ya fito.

Masallaci ya wuce yai sallolinsa, sannan ya zauna yana karatun Al'qur'ani mai girma, ya daɗe yana addu'a sannan ya miƙe ya nufi titi dan samun abun hawa zuwa gida.

Abunka da unguwar masu kuɗi, tuni unguwar tayi tsit se sanyi bishiyoyi dake kaɗawa, yana ta tafiya a ƙasa yana tunanin abubuwa da dama, ya baro layin su Widad sosai inda security suke, ba tsammani se gani yayi ansha gaban
sa da mota, tsayawa yayi cak yaga ikon Allah.

Wasu ƙarti ne suka fito daga motar suka zagaye shi, ɗayan yace  "kaine direban 'yar gidan Alhaji Nasir?"
Ba tare da tsoro ko shakka ba Yusuf yace  "Eh nine"

"Good labari ya ishemu cewar akwai kusanci tsakanin ka da ita, duk inda zata tare kuke zuwa, an samu mu ɗakkota kwanaki amma ka hana, bari in gaya maka wani abu, zamu ƙyaleka ne saboda zakayi mana amfani, zamu ci gaba da bibiyar ka saboda akwai wani abu da muke so ka karɓo mana a gurin ta" cewar ɗaya daga cikin ƙartin

Yusuf yace "Babu wani kusanci tsakanin mu, aiki nake mata tana biyana, ko meye kuje ku tambaye ta ta baku mana"

Ɗaya daga cikin sune ya sakarwa Yusuf wani mummunan naushi, da seda jini ya fito daga bakin sa, a zuciye Yusuf ya ɗago yana kallonsu, babban yace

"Wallahi idan baka kawo mana abun nan ba se mun kasheka, akwai wasu mahimman abubuwa da muke so ka karɓo mana a gurinta idan kaƙi semun maka yankan rago"

"Bayan yankan ragon se kuma me?" Yusuf ya faɗa babu alamar tsoro

Wani naushin suka ƙara masa a gefen ido,
Maimakon Yusuf ya tsorata, ko ya nuna jin zafin naushin, se yayi murmushi yace

"idan kunmin yankan rago, ku kuma ku zauna a naɗe duniya daku?, babu wani mahaluki daya isa yasa Yusuf yin wani abu dan son zuciya da zalunci, kuje ku gayawa wanda ya aiko ku cewar karya kuskura yayi gangancin cin iyakar gonar da ba tasa ba, idan kuma yaƙi zanwa shukokin feshi in ƙone nawa da nashi, kowa ya rasa, wannan saƙon Yusuf ne ga uban gidanku ko wayeshi"

Wani naushin suka yi niyyar kai masa amma ya riƙe hannun ɗayan.

"Waye kai? Waye ya gaya maka wanine ya turomu?" cewar ɗaya daga cikin su

"yadda kuka binciko kuka gano nine direban Widad, haka yakamata ku bincika kusan wayeni, nasani aikoku akayi ku koma ku ƙara tabbatarwa wanda ya aikoku nina ɗauke Widad lokacin da yasa a sace ta, ni aikina tuƙata a mota dan haka ya kiyayi yunƙurin cutar dani"

Hausawa sukace 'sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, sun daki Yusuf sosai, yaso yayi amfani da bindigar sa, amma yin hakan ze rusa masa da yawa daga shirinsa, dan haka ya fasa ɗaukar bindigar, suka daddake shi, wani yana iya ramawa wani kuma baya iyawa.

"zamu cigaba da bibiyarka, harse ka bamu abunda muke nema, zaka gane baka da wayo, Uban taurin kai, Ubangidanmu yafi ƙarfinka"

haka suka barshi a gurin suka tafi.

Da ƙyar Yusuf yaja jikin sa ya hau Napep ya tafi, hancinsa yana ta zubar da jini, jiri ne yake ta ɗibarsa saboda jinin da yake zubarwa da yawa, da ƙyar yaje gida, Allah ya temake shi Umma tayi bacci.

ya cire kayan jikinsa yana goge jinin fuskarsa, Aljihun wandonsa ya taɓa yaji wayar da Widad ta bashi ɗazu.

Hannu yasa ya ɗakko ta yana jujjuya ta  "Ka ɓoye ta kamar yadda zaka ɓoye ranka, wannan wayar tamkar rayuwar ka ce"

Maganar Widad ta dawo masa, kunna wayar yayi, Amma akwai password akai shiru yayi yana nazarin kamar yaya wayar nan tamkar rayuwar sa take? Ajiye wayar yayi ya shiga yayi wanka ya fito, nan ya shiga aikin nasa na tunani dan abubuwa da dama sun faru da suke buƙatar nazari.

"Me Widad taje yi Hotel? Me ta gani ya sata kuka? Waye ya turo mutanen nan? Ko waye akwai sa hannun wani a gidan su Widad? Amma dagaske Tausayin Widad zesa ya fara sonta? Me yasa tasa a durƙusa a bashi haƙuri yau? Tabbas zata iya yuwuwa akwai Alaƙa tsakanin wani a gidansu Widad da mahaifin Nurat"

Ji yayi kansa kamar ze fashe, dan haka ya rintse idon sa yana addu'a da fatan bacci ya ɗauke shi koze ɗan samu nutsuwa, Amal ta faɗo masa a rai itama, wai ita bilhaƙƙi son shi take.
Wani tunani ya shigayi watanni shida da suka gabata, da yanzu yana nan da Auren sa, katsam a dalilin irin tasa ƙaddarar aka fasa wannan Aure, bayan cin zarafi da wulaƙanci daya fuskanta daga iyayen matar daze Aura, bacci dai se ɓarawo ne ya ɗauke shi.

*******************************

Da safe Yusuf ya tashi da matsanancin zazzabi, kansa har sarawa yake sosai saboda dukan da yasha jiya, juyi kawai yake akan gadon gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, ganin har kusan ƙarfe tara be fito ba yasa Umma leƙawa ɗakin sa, ta tarar da shi kwance a kan gadon sa, ƙarasawa tayi ta taɓa jikin sa tace  "Yusuf lafiya kuwa? Naga har ƙarfe tara baka fito ba?"

"Bana jin daɗi ne Umma"
"dan baka jin daɗi seka zo ka kwanta kana juyi, ka tashi ka watsa ruwa, ka karya seka sha magani"
"to Umma"
Yusuf ya miƙe ya shiga yai wanka, kayan breakfast ɗin ta kawo masa ɗaki, ta kalle shi tace 
"Yusuf kamar kumburi nake gani a gefen idonka da bakin ka"

Yusuf yace  "Mun faɗi akan babur ne jiya da daddare"

"Amma ka kasa gayamin? Meye amfanin hakan, haba Yusuf"
Yusuf yace  "Yi haƙuri Umma, bana son ɗaga miki hankali ne"

"Amma ina fatan ba wani mummunan ciwo daka ji?" tai maganar cike da damuwa

"Eh banji ciwo me yawa ba"

Da kanta ta zauna tana bashi Abinci a baki, ta ɗakko masa first aid box ɗinsa ya ɗau magani ya sha, ya koma ya kwanta.

Kwanciyar sa ba daɗewa Abbas ya kira shi, da ƙyar Yusuf ya ɗaga wayar, Abbas yace  "Mutumina kana ina ne? Ina son ganin ka"

"Ina gida bana jin daɗi ne"

"Subhanallah, meya sameka?"

"Zazzabi ne" Yusuf ya bashi amsa

"Shikenan gani nan zuwa"
Su kayi sallama

**************************

Hajiya Halima na zaune falon ta tana shan tea, Isa mai gadi yazo yana kwaɗa sallama a ƙofar falon ta, A fusace tace "wai meye hakane? Lafiya kame do kamin wannan sallama kamar kana bina bashi?"

"Hajiya nine, Isa ne"
"to ya a kayi?"
"Hajiya gurin ki nazo"
Ta ɗanyi tsaki sannan tace  "shigo"
Ya shiga falon ya durƙusa yace 
"Ina kwana?"
"Kai bana son doguwar gaisuwar nan meke tafe da kai?"

"to Hajiya kin san shi sha'ani na rayuwa kiwon mutum ake ba dabba ba koba haka ba?"

"kai nifa bana son wannan surutam banzae, ka faɗamin kanka tsaye meke tafe da kai"

Isa ya gyara zama yace  "game da sabon direban nan ne Yusuf, gaskiya Hajiya akwai buƙatar kisa ido, jiya yadda na gansu Allah ya nuna min Annabi salallahu alaihi wassalam, kin san dai irin shigar da take yi, bayan kin fita ita dashi suka fita, basu dawo ba se ƙarfe tara na dare, bayan sun dawo a gabana da idanun nan nawa" yai maganar yana gwalo idon nasa ya cigaba da cewa
"da idanu na naga suna rungume juna, Hajiya a saka ido, kina gani idan ba kiranmu akayi ba bamu da damar shigowa kiga yadda take hantarar mu, Amma shi ba yau ba gobe cikin sintiri yake har cikin ɗakin kwanan ta, Allah kaɗai yasan me suke yi, gaki da 'yan mata kema kyawawa bekamata yana gardi baligi ya dinga wucewa yana kalle miki su ba, shiyasa nace bari inzo in sanar dake abunda ake ciki "

Dire kofin hannun ta tayi, taja wata nannauyar Ajiyar zuciya tace " Hmm naji maganganun ka, kuma kazo da magana abun dubawa, tashi kaje zan san abunda zanyi "

Isa ya miƙe yana murna yace
"shikenan Hajiya na barki lafiya "

Shiru Hajiya Halima tayi tana zake nazartar kalaman Isa megadi, tabbas Widad bata yadda wani ya Wulaƙanta Yusuf ba, lokacin da ciwon ta ya tashi taƙi yadda da kowa se Yusuf, idan har dagaske wani abu na faruwa a tsakanin su to tabbas akwai yuwuwar ta gayawa Yusuf inda abunda suke nema yake.

**************************

Widad kwana tayi da zazzabi da ciwon kai, da ƙyar ta samu tayi bacci.
Jikin ta sam babu ƙwari ta miƙe domin haɗawa magen ta abunda zeci.
Widad na matuƙar son dabbobi, tana tausayin su fiye da yadda take tausayin mutane, akwai shaƙuwa me ƙarfi tsakaninta da dabbobinta, mussman ma wannan magen nata pita, da kuma karen ta dake gidan gona, tana jin daɗin kasancewa da su, dan ba ƙaramin ɗebe mata kewa sukeyi ba.

Ta samu container ta zuba masa madara, ta samo wani ta zuba masa gugguru, ta koma gefe tana kallon magen, maimakon magen yaci seya koma jikin ta ya kwanta, dan ya saba idan lokacin cin Abinci yayi, ta zuba masa nasa yana ci itama tana cin nata

**********************************

Abbas ne yayi Sallama ɗakin Yusuf, da ƙyar Yusuf ya iya amsawa, ya miƙe zaune suka gaisa da Abbas.

"Sannu Yusuf, ko Asibiti za muje in sauke ka"

Yusuf ya girgiza kai yace  "A'a na sha magani kawai, ya kake ya aikin?"

"Alhamdilillah, jiya Oga Suleiman yake neman ka, shine kiran da nayi maka, kuma se kace baka jin daɗi, yanzu yau ba zaka gidan su mutuniyar taka ba?"

Yusuf yace  "bazani ba gaskiya, sedai zuwa gobe in Allah ya kaimu idan naji sauƙi"

Abbas yayi ƙasa da murya yace 
"Ya kuɗin nan waye ya turo dasu kuwa?"

"itace wai Albashi na ne na watanni uku da bata bani ba, nace mata yayi yawa ta rage taƙi"

"Taɓɗijan kaima Yusuf da wani abu, kamarya ta rage? Malam kawai kaci kuɗi, meye labari kuma?"

Yusuf ya gaya masa Hotel da suka je, da yadda suka dawo tana kuka, Amma be gaya masa zancen wayar nan ba data bashi.
Nan suka cigaba da tattaunawa zuwa wani lokaci Abbas yace ze tafi, Naira dubu ɗari Yusuf yayi masa transfer a cikin kuɗin, Abbas yaita murna yana godiya suka yi sallama.

Amma ƙasan zuciyar Abbas kamar ya fasa ihu
'dana san wannan alherin Yusuf zeje ya dinga samu da tun farko nina karɓi aikin nan, ya samu dubu ɗari biyar amma ya bani wata shegiyar dubu ɗari, ga danƙareriyar waya ya samu, na tura shi dan ina gudun wulaƙanci amma yaje yana samo abun Arziki, dole in san yadda zanyi a cire shi daga kan aika ni maye ni"

'Amma hatsari da kasadar dake cikin aikin fa?' wata zuciyar ta tambaye shi, tsaki yayi yana ci gaba da surutai.

*******************************
Shafa jikin magen take a hankali tana lallaɓashi yaci Abinci, wayarta ce ta fara ringing, muzurun nan ya kasa a guje yaje ya ɗakko ta a bakin sa ya kawo mata, shafa kan muzurun tayi tace  "thank you Roux"
Ta amsa wayar tasa a kunnen ta
"Ranki ya daɗe Bala fa babu lafiya, an ɗauke shi rai a hannun Allah an kai shi Babban Asibitin cikin gari, dan besan waye a kansa ba"

Miƙewa tayi tsaye tace  "what? How comes? Wace irin rashin lafiya ce wannan?"

"Nima ban sani ba gaskiya, Amma an fita da shi daga Asibitin cikin kurkukun gaba ɗaya"

Bata kashe wayar ba ta miƙe, da sauri ta shiga bedroom ɗinta ta canza kaya, dukda yanayi na rashin lafiya da take ciki, wayar ta ta koma ta ɗakko ta fara daddanawa sannan tasa a kunnen ta.

Yusuf yana jin wayarsa tana ringing ya ƙi ɗagawa yasa ta a silent, ya ajiye wayar ya cigaba da kwanciyar sa.

Jifa tayi da wayar akan kujera ta fice harabar gidan, gurin su Nura ta nufa, tana zuwa suna gaishe ta amma bata kula suba tace 
"Ku kiramin driver yanzu"
Jiki na rawa suja shiga kiran Yusuf babu ƙaƙƙautawa, Amma be ɗaga ba.

Ta kalli Nura tace "ɗakko mota da sauri, zaka fita dani"

Cike da washe baki yaje ya ɗakko mota, ta shiga Nura yaja motar suka fita, gaba ɗaya ji take kamar tayi Amai, dukda a bayan motar ta zauna amma warin hammatar Nura ya cika motar, se tsaki take yi badan ya zama urgent ta fita ba babu yadda za'ayi ta yadda wannan ƙazamin ya jata a mota, suna tafe tana masa tsawa gami da hantararsa, Amma Yusuf ze gane kurensa na ƙin zuwa da yayi yau sannan yaƙi ɗaga waya.

Prison tasa ya kaita, suna zuwa ta fita ta shiga, kai tsaye ofishin Hisham ta wuce.
Yana ganin ta yai murmushi ya sallami kowa daga office ɗin sannan yace  "barka da zuwa lady boss, Ashe kin dawo Nigeria?"

"Ya aka yi Bala ya kamu da rashin lafiya da har ta kai shi ga kwanciya, seda aka fita da shi daga gidan nan?"

"Ranki ya daɗe gaskiya dama yana ɗanyin rashin lafiyar a tsai tsaye, Kawai se ɗan uwansa ya kawo masa ziyara, bayan ya tafi jikin sa ya rikice"

"yanzu kana nufin kace min Ɗan uwansa ne ya kawo masa abunda yaci, jikin sa ya rikice kenan? Saboda sakaci da rashin sanin aikin ku?"

"A'a ranki ya daɗe kin san?...

"Yimin shiru malam, saura sati ɗaya tal a koma kotu, kawai se inji wannan banzar maganar mara tushe, shikenan amma kasani idan har rashin lafiyar Bala haɗin baki ne, duk wanda yake da hannu a ciki shima abunda ya samu bala ze sameshi. "

Ta miƙe a fusace ta fito, Hashim ya biyo ta da sauri amma ta shiga mota da niyyar ta ta wuce gurin lawyern Daddy, amma ba zata iya jure wannan tsamin da Nura yake ba, dan haka tace ya nsida ita gida, tana mamakin ƙoƙari irin na Daddy da yake iya shaƙe wannan warin hammatar, Yusuf kullum tsaf dashi cikin ƙamshi, amma wannan ƙazamin kamar baya jin yadda yake wari, seda ta bari sun koma gida, sannan tayi wa Nura ta tas akan ƙazanta da warin da yake yi a gaban sauran ma'aikatam.

Gaba ɗaya ranta a ɓace, ga jikin ta ba ƙwari gashi a ƙule take da Yusuf, tana shiga babban falo ta tarar da Hajiya Halima, bata kula ta ba tasa kai zata wuce
"Widad ina son Magana dake"

Widad ta tsaya ta juyo ta kalleta ba tare da tace komai ba.

"Widad bekamata ace kina fita lokacin da kike so ki dawo lokacin da kike so ba a matsayin ki na mace, sannan ki dinga dawowa sanda kika ga dama ba, Alhalin nida nake zaune tare dake ban san idan kike zuwa ba, Sannan wannan yaron da yake sintiri gurin ki har ƙuryar ɗakin ki, Sam be dace ba"

"kinga dakata Malama, zamanki nake a cikin gidan nan? Koke kika ajiyeni? In kun tashi taku yawon gayamin kuke? Kisawa ranki gidan nan tamkar bariki yake, kowa yayi abunda yaga dama muddin be ƙetare abunda masu gidan suke so ba, karki ƙara shiga sabgata, kuma kowa zan kawo cikin gidan nan gidanmu ne, kowa ze je har cikin ɗakina babu ruwanki, kome nake aikatawa karki ƙara shiga, dan ke ba uwa ta bace baki haifeni ba, baki da ikon ki samun ido, kema abar a sawa ido ce, kisa ido akan 'ya' yanki kawai, ba ruwan ki dani....

"Widad!!!" Ramlah ta kira sunan Widad da ƙarfi

"Ramla don't ever try to shout at me, a gidan mu kike ba gidan ku ba, dan haka ki iya bakin ki, tun kan in fusata"

Tana gama maganar ta juya ta tafi part ɗin ta.

"Tirƙashi Mummy dan Allah ki bani dama ko sau ɗaya, inci mutuncin yarinyar nan in koya mata hankali ko zanji sanyi a zuciyata"

Mummy ta girgiza kai tace  "Kina yin haka Ramla kin ɓata komai, rabu da ita lokaci ne, yana nan zuwa da zata girbi abunda ta shuka"

**********************************

Se wajen la'asar sannan Yusuf ya ɗanji sauƙi ya tashi, ya shirya yaje Asibiti, aka duba shi aka bashi magunguna.
ya dawo gida ya wuce ɗakinsa, wayarsa ya ɗakko ya duba, yaga missed calls rututu, ko ba'a  gaya masa ba yasan Widad ce take neman sa, bebi ta kansu ba ya ajiye wayar ya cigaba da harkokinsa.

Dayaji ya ɗanji ƙwarin jikin sa, seya shirya tsaf ya tafi hotel ɗin da suka je da Widad, Manager yaje nema amma be sameshi ba, ya cewa ma'aikatan su bashi lambar wayar sa, da farko suka ƙi, seda ya nuna musu id card ɗin sa sannan suka bashi, seda ya zagaya lungu da saƙo na Hotel ɗin, yana sake monitoring mutanen dake shiga da fice a hotel ɗin sannan ya koma gida.

Washegari da safe dukda ya tashi jikin sa babu daɗi, Amma haka ya shirya ya tafi gidan su Widad.

Tunda yaje Isa yake masa wani irin kallon banza, yanata habaice habaice
Shi dai Yusuf be kula shi ba, Nura yace

"Wallahi Yusuf yau kana ruwa, bama kusa da kada ba, cikin bakin kada, jiya ta fusata sosai, dan zata fita seni na kaita saboda baka zo ba"

Murtalah ya kwashe da dariya yace  "bayan kun dawo kuma tai maka tatas a gabanmu ba, saboda ƙazanta kai Nura jiya kaga tijara a tsakar rana, ai idan nine kai ko maganar ba zan ɗakko yau ba" yai maganar yana dariya

Nura ya haɗe rai yace
"Bana son rashin mutunci da Iskanci"

Ganin suna nema suyi faɗa yasa Yusuf yin gaba abunsa ya barsu a gurin, tafiya kawai yake yi amma jikin sa babu daɗi.

Yana shiga falon ya tarar da Ramadan ɗan gidan Alhaji Bulama da Amal suna hira.

Yusuf yace  "barkanku da Safiya"

Bata amsa masa ba se Ramadan ne yace  "Yawwa barka dai, bodyguard ɗin gimbiya" Yusuf ya ɗanyi murmushi ya nufi hanyar Widad.

Bayansa Amal tabi da kallo, taji wasu hawaye na ƙoƙarin zubo mata, ta tsani kusancin Widad da Yusuf gani take komai ze iya faruwa, wani sashin na zuciyar ta ma yana gaya mata akwai wata alƙar a tsakaninsu saboda kusancinsu yayi yawa.

Ramadan ya kalleta yace "lafiya kuwa my?"

Girgiza masa kai kawai tayi tace  "lafiya ƙalau"

Yusuf ya shiga ya tsaya a bakin ƙofar bedroom ɗin ta sannan yayi sallama kamar yadda ya saba.

Yayi Sallama kusan uku amma bata amsa ba, haka ya cigaba da tsayuwa a gurin, seda aka kwashi wani lokaci sannan ta fito, kallon sa tayi daga sama zuwa ƙasa sannan tace 
"Sannu ishashshe kaga damar zuwa kenan?"
Shiru Yayi ya sunkuyar da kai, ɗakin ta shige yabi bayanta da sallama

"Meya hanaka zuwa jiya? Kuma kaƙi ɗaga waya?"

"Bani da lafiya ne shiyasa"

"ƙarya kake" ta faɗi kai tsaye ba tare da duba ratar shekarun da Yusuf ɗin ya bata ba, shiru ya sake yi bece komai ba, ta tako tazo daf dashi tace 
"for the second time meya hanaka zuwa jiya?"

"bani da lafiya ne" ya sake bata amsa

"wai me yasa baka kunyar yin ƙarya ne, meyasa? Ban gaya maka bana son ƙarya ba?" tai maganar tana ƙoƙarin sa idon ta a cikin nasa

Babu zato ya janyota gaba ɗaya tana facing ɗinsa, ya kafe ta da idon sa, nata cikin nashi ya ƙura mata ido

Ayi sharing please 🙏🙏🙏

Ayshercool
07063065680
                    
                    _*AƘIDATA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

      

                   



                           PART1
                              Page 13

ELEGANT ONLINE WRITER'S



Ba ƙaramin firgita tayi ba da abunda Yusuf ɗin yayi, sedai riƙon da yayi mata tana iya jin huci me zafin da jikin sa ke fitarwa, masifa take son yi amma gaba ɗaya Yusuf yayi mata wani irin kwarjini ta kasa cewa komai se binsa da tayi da manyan idanunta.

Cike da jarumta Yusuf yace "Meyasa koda yaushe idan nayi abu seki ƙarya tani? A koda yaushe ina ƙoƙarin gaya miki iya gaskiya ta amma seki ce ƙarya nake, kin san yadda mutum keji kuwa idan aka ƙarya tashi, it's really hurts, duk abunda nake yi ba inayi ne dan in samu kusanci dake ba, nasan AƘIDARKI nasan abunda bakya so, ina ƙoƙarin kiyaye dokokin da kika kafamin ne, dokokin dana sawa hannu amma koda yaushe burinki kici zarafina"

"Malam cikani ko"  ta faɗa tana masa wani irin kallo

Cikata yayi ya koma gefe ya tsaya.

Seda tayi ajiyar zuciya sannan tace

"hmm tunda nake babu wanda ya taɓa Yimin abunda kayi min a yanzu, ina ɗaga maka ƙafa ne saboda wasu dalilai biyu zuwa uku, dalilai biyu bakomai ne a gurina ba, dan ba zasu hanani yanke hukuncin dana ga dama akan ka ba, dalili ɗaya ne me ƙarfin da yazo da ƙaddarar da ni ban isa in canza shi ba koda hakan bemin ba, ba yadda zanyi da kai dukda har yanzu ina doubting akan wannan dalilin, Anyway zamu fita yanzu zamu je gidan gona"

"A wace motar?" ya tambayeta a taƙaice

"kowacce ta bashi amsa"

Har ya juya ze fita yaji tace 
"meya sameka a fuskarka?"

Ya juyo ya kalleta

"kar kayi min ƙarya" ta faɗa kafin ya bata amsa

"Duka ne" ya bata amsa

"Kamar ya ya duka? Suwaye suka dakeka?"

"Nima ban sansu ba"

Ɗan tsayawa tayi tana nazarinsa, yayin da ya ɗauke kai yaƙi kallonta

"Shikenan, muje"

Suka fito falo, yana gaba tana bayan sa, Amal ta bisu da wata uwar harara.

Ramadan yace 

"Allah ya temaki 'yar masu gida, Gimbiyar gida a biki a zauna lafiya, a ɓata miki mutum yai kwanan baƙinciki,' yar gaban goshi sha lelen masu arziki, tun ɗazu nake zaman jiranki anan, Megida ne ya aiko ni, yace yana son ganinki"

Ta yamutsa fuska tace  "Ina da abunyi, da  haka ba zani ba"

Ramadan yace "haka zanje in gaya masa"

"Eh haka za kaje ka gaya masa, bazan zo ba, bazan ƙara zuwa inda yake ba"

"shikenan, kunfi kusa keda shi"

Ta juya suka fice ita da Yusuf.

Amal tace  "Ramadan, dan Allah yanzu baka jin haushin irin abunda takewa mahaifinku?"

Ramadan yace  "to me zance Amal? Ni meye nawa a ciki? Da mahaifina da mahaifinta tashi nayi na gansu tare, kuma haka muka tashi muka ga an sangartata se abunda take so sukeyi, sun ɗauki son duniya sun ɗora mata, ba'a kwaɓarta komai tayi dai dai ne, meyasa zanji haushi, tunda ba yau ta fara ba, kuma idan tayi baya jin haushi, a gabana a gaban sa idan bata ga dama ba  Bulama take cemasa kanta tsaye, an riga an barta ta tashi akan wannan AƘIDAR"

"gaskiya ni abun yana damuna, mu kanmu a cikin gidan nan bamu tsira daga wulaƙancin ta ba, bamu ba har mahaifiyar mu fa"

"kin san wani abu? Ni yanzu babbar damuwa ta itace, Daddy yace  Fahad zasu aurawa ita, Fahad kuma mutum me faɗa baya son raini ni ban san ta yaya za'ayi wannan zaman auren ba"

Amal tace  "ai duk wanda ya kwashi wannan ya kwashi masifa, gata mahaukaciya ga ba tarbiyya, gaskiya ina tausayin Fahad"

***********************************

Yusuf yayi parking ɗin motar a gidan gona, Widad na fitowa kamar kullum haka ma'aikatan suka yo caa suna gaishe ta, ɗaga musu hannu tayi ta kalli Wani daga cikin ma'aikatan, wanda ya tsare Yusuf da tambayoyi wancan karon tace 
"Ya aiki ya kuma dabbobi na?"

"lafiya ƙalau ranki ya daɗe, ko za'a ɗakko dokin ne?"

"A'a sedai ina so kayi min rakiya in zaga su"

"to shikenan ranki ya daɗe" haka suka shiga suna zagawa, sosai Widad take jin nishaɗi idan tana kallon dabbobi, gaba ɗaya mantawa take da damuwar da take ciki, suna cikin tafiya tace

"Sale naji wata magana, ban sani ba ko kai ka jita, takanas nace bari inzo domin mu tattauna ta"

Saleh yace  "Allah yasa ba wani abun akace nayi ba ranki ya daɗe?"

"idan ka yadda da kanka ba kayi lefi ba meye na tsarguwa? Labari ya isheni cewar ɗan uwanka bala bashi ds lafiya, naje har prison dan in duba shi, amma akace min an fita da shi zuwa babban Asibiti dan be san wake kansa ba, ban kai ga zuwa duba shi ba har sena je naga lawyer na tukuna "

A gigice Sale ya kalle ta yace " ya za'ayi ace yana rashin lafiya, harta kai ga baya gane mutane? Shekaranjiya fa naje duba shi, na sameshii lafiya ƙalau, taya haka zata faru? "

"Nima abunda na gaza ganewa kenan, ace beyi rashin lafiya ba se daya rage 'yan kwanaki a cigaba da shari'a, Babban Albishir ɗin dana zo maka da shi shine, muddin na tabbatar da sa hannun ka, zaka maye gurbinsa ne"

Saleh ya kalleta da sauri, bata bari yace komai ba, ta juya ta tafi. Turus Saleh yayi yana nazarin maganganun Widad.
Tunda Yusuf ya fara aiki da Widad, a kullum se yaga abun mamakin daze kulle masa kai.

Ya kunna motar suna shirin tafiya wayar ta ta ɗau ruri, tana kallon screen ɗin wayar ta ɗan ɓata rai ta tura baki, ɗaga wayar tayi tasa a hansfree  "Hello Daddy"

"lovely fushi kike dani ko?"

"A'a"

"Fushi kike mana, Daddynki yace ya aiko a kira masa ke kince ace bazakiyi zo ba, Baby Why meyasa kike haka?" shiru tayi taƙi cewa komai.

"Yanzu haka munyi waya, ina so kije kiji meze ce miki"

"Daddy nifa yanzu wani gurin zani, Na gaya maka ina cikin damuwa kunƙi saurara ta, sema kawomin wasu abubuwa da bana buƙata yake, na gaya maka akwai matsala amma kunƙi saurara ta"

"Ba shawara nake baki ba, Umarni ne kije gurin Bulama yana son ganin ki"

Tura baki tayi ta ajiye wayar tana haɗe rai, Yusuf be nemi shawarar ta ba ya kaita gidan Bulama, Ranta a ɓace ta buɗe motar ta fita tana tura baki, har tayi gaba ta tsaya ta juya taga Yusuf yana rufe mota
"Malam ni ka hanzarta ba zaman jiranka zan tsaya yiba"

Yusuf ya biyo bayanta, suna shiga katafaren falon suka tarar da Iman, ƙanwar Ramadan, Iman tai murmushi tace  "Ohhh beb, ashe zaki zo yanzu Ramadan ya dawo"

Hannu kawai ta ɗagawa Iman ta nufi matattakalr bene.
Iman tace "Widad, Nurat ta kirani tace min tun ranar da kika bar gurin birthday ɗinta baki ƙara ɗaga wayarta ba, i hope ba saɓani kuka samu ba, dukda nasan halinki dai"

Shiru Widad tayi ta tsaya, saboda yadda abubuwa suka yi mata yawa, sam bata cigaba da bibiyar meyasa meta a gurin birthday ɗin Nurat ba, dan tafi tunanin ko ciwonta ne ya tashi a gurin, shiyasa ta kasa tuna komai, juyawa tayi tana kallon inda Yusuf yake, ya ɗauke kai yaƙi kallon ta.

Still ba tace komai ba ta cigaba da tafiya Yusuf na binta.

A babban falon dake saman benen wanda ya kasance na Bulama anan suka tarar da Bulama shida matarsa.

Yusuf ya gaishe su suka amsa, Widad kam kyam ta tsaya tana ƙare musu kallo, sannan ta nemi guri ta zauna abunta tana hura hanci, wata uwar harara matar Bulama take wa Widad.

Bulama yace "lovely ba gaisuwa?"

Tura baki gaba ta sake yi tana ƙunƙuni, Bulama yayi murmushi yace

"Ikon Allah, ƙiri2 'ya na fushi da babanta, har in tura a kiraki kiƙi zuwa ko? Duk dan nace a miki Aure kike wannan fushin dani haka?"

Cike da tsiwa tace "Eh dan kace ayimin Aure ne, nace maka bana so, bana so, Amma kaƙi ban sani ba ko kaima da wata manufar a ranka, nace a min Visa in koma inda na fito shima kace A'a, ba dole inyi fushi ba"

"Widad meyasa baki da kunya ne? Sam baki da ta ido" cewar matar Bulama.

"Ba dake nake magana ba, ina magana da mijin ki ne karki sake shiga harka ta" Widad tai maganar a fusace

Bulama yayi murmushi yace 
"Ummu Ramadan excuse us please"

A fusace Matar Bulama ta tashi ta bar ɗakin tana mita, Bulama ya kalli Yusuf yace 
"Young man can you excuse us please?"
Yusuf yace  "ok sir" ya juya ze fita

"ba inda zeje, ko mene faɗi a gaban sa"

"wow daughter kin yarda dashi haka yaji abubuwan da suka shafi rayuwar ki? Lallai sauƙi yana samuwa"

"ba wani sauƙi daya samu, ina nan a mahaukaciya ta kamar yadda kuka saba faɗa"

"waya isa yace miki mahaukaciya, ba mahaukaciya bace ke Daughter"

"Eh amma kuke kaini gurin likitocin mahaukata"

Alhaji Bulama yace  "Daughter a bar wannan maganar, magana ce Maman ki tazo min da ita"

"ni uwata ta mutu, an kasheta bani da wata uwa, ta haifi dai wanda ta haifa"

Bulama ya girgiza kai yace  "What ever dai, ta kawomin ƙorafi akan ki, kina fita lokacin da bata sani ba, ki koma bata sani ba, kuma kinsan babu tsaro haka kike yawo ga rayuwar ki a hatsari, kuma tayi koke akan wannan direban naki, bata jin daɗin yadda direban ki yake sintiri a sashenki, gaki budurwa ga ta da manyan yara mata, bekamata ya dinga sintiri kuna keɓewa dashi ba, daughter meyasa ba kya ɗaukarta kamar mahaifiya ne? "

Shiru Widad tayi tana jinjina kai, Yusuf kam gaba ɗaya ji yayi kamar ƙasa ta tsage ya nutse, dan shi kansa baya jin daɗin yadda yake shiga inda Widad take, yana ganin rashin dacewar hakan.

Bulama yace " Daughter baki ce komai ba"

"so nake ka gama tukuna"

"Na gama feedback ɗinki nake jira"

Widad ta gyara zama tace "Ka gaya mata wanda ze iya zama a gidanmu a ƙarƙashin mulkina shikenan, wanda baze iya ba ƙofa a buɗe take ya ƙara gaba, tunda basu da zuciya dole su zauna su cigaba da zama, yadda ba ruwana dasu to sudena samun ido, idan zargin da takemin kenan, to ka gaya mata idan maza nake son kawowa bata isa ta hanani ba, tunda gidan mu ne, sannan ni bani da uwa, Uwata ta bar duniya an kasheta, bazan ƙara yadda da wani ba, ban yadda da kowa ba kuma bazan yarda da wani ba, i start loosing trust on you Bulama, bani da uwa an kashe uwata! Karta ƙara kiran kanta uwata, ni bani da uwa! Bana son kowa ya raɓeni, ban yadda da kowa ba wannan AƘIDATA ce"

Jikin ta ne ya fara rawa, wasu irin hawaye na zuba daga idon ta, da sauri Yusuf ya tashi suna rige rige da Bulama zuwa ga Widad, Numfashi take da ƙyar tana kuka, Yusuf yazo kanta da sauri yace
"Are you ok?" jinjina masa kai tayi
Bulama jiki a sanyaye yace 
"daughter, ban faɗi wannan maganar dan in ɓata miki rai ba, Nayi ne dan in tunasar dake mahimmancin haƙuri, kuma koba komai matar mahaifinki ce sannan.. Ɗagawa Bulama hannu tayi ta miƙe ta nufi waje da sauri.

Bata tsaya ba seda taje mota, gaba ɗaya rayuwar Widad abun tausayi ce, tunda Yusuf yasan ta bata cikakken sati bata zubar da hawaye ba, Amma ina dangin mahaifinta kona mahaifiyar ta? "

A haka ya kaita gida, yana tuƙi kamar baya so, saboda yadda yake jin kukan ta me ban tausayi, kamar yadda ta saba indai sukaje guri suka dawo, kame tazo dashi a motar zata barshi, se Yusuf ya kawo mata.
Dan haka yana parking ta buɗe ta fice, ya ɗakko jakar da Wayar ta ya bita.
Sedai yana shiga Falon ya jiyo sautin kukan Widad cikin gurɓatcciyar hausar ta take faɗa
"danme zaki dinga zuwa kina kai ƙarata, bafa ki haifeni ba, keba uwata ce ba, kin sani meyasa kike shisshigi a al'amura na, idan baki dena min haka ba zan ɗau mataki mafi muni akanki, ki ƙyaleni inji da abunda nake ji, ki ƙyaleni inji da ƙunci da baƙin cikin dana ke ciki tsawon shekaru mana, danme zaki dinga min haka?"

Masifa take sosai kamar zata shaƙe Hajiya Halima, Abun na Widad ya fara wuce gona da iri.

Yusuf yace  "kina hayyacinki kuwa? Meyasa kike haka?, a haife ta haife ki, bekamata kidinga gaya mata wannan maganganun ba"

Ta juyo kan Yusuf cikin faɗa tace "Bana hayyacina, ni mahaukaciya ce, idan baka sani ba yau in gaya maka, bani da hankali har ƙasar waje ake kaini ganin likitan mahaukata, Amma baka san me nakeji a zuciya ta ba, An kashe mamana ban san kowa ba se ita, aka kashe ta ba wanda ya damu dani se Babana da Bulama, kowa kansa ya sani babu wanda ya damu da abunda Widad take ciki, kasan me nake ji a raina idan na tuna lokacin da aka kashe mahaifiyata? Wannan tabin baze bar zuciyata ba, a ƙyaleni inyi rayuwar da naga dama mana, "

Yusuf yayi ƙasa da murya yace
" is alright I feel your pain "

" you don't feel my pain, your mum is still alive but me... Kasa ƙarasawa tayi se sake fashewa da tayi da kuka, ta tafi part ɗinta da sauri, Yusuf kam kasa bin bayan ta yayi wannan karon,  Hajiya Halima kam ƙamewa tayi ta zubawa sarautar Allah ido.

Yusuf ya juya ze fice Hajiya Halima tace  "Ina zaka tsohon munafuki, zuwan ka gidan nan shiya hargitsa komai, da yarinyar nan duk rashin mutuncinta bata fiye magana ba, seda kazo kana hure mata kunne, to idan ma wani ne ya turoka to tabbas zanyi maganin ka, dan da zarar Alhaji ya dawo zansa ya sallameka, matsiyaci banza dana wofi kawai "

" Niba matsiyaci bane, Amma talaka ne me wadatar zuci, sannan kafin kisa a koreni da kaina nayi deciding yin resigning, zan bar aikin nan dan nima abunda yake faruwa ba daɗi yake min ba ko dan tsira da mutuncina, dole in bar aikin nan tunda bana shiga aljanna bane"

Fitowar Amal yai daidai da maganganun Yusuf da yace ze bar aikin, sakin ƙaramin plate ɗin hannun ta tayi, tabi bayan sa da sauri tana kiran sunan sa.

" Idan kika bar ƙofar falon nan da sunan bin bayan sa, zan sallamawa duniya ke in bar masa ke, tunda haka kike so"

Juyowa tayi tana kallon Mummy, ta juya da sauri part ɗinta tana kuka.

************************************

Abbas se juyi yake akan kujera yayi shiru, gaba ɗaya abun alherin da Yusuf ke samu a hannun Widad ya tsaya masa a zuciya, yaji meyasa yasa aka tura Yusuf aikin shi beje ba? Yayi gudun kar yaje a dinga masa wulaƙanci yasa aka tura Yusuf, yanzu gashi kuɗin data bashi Yayi Albashinsa uku, ga gefe ana biyan sa Albashinsa, Sallamar Sakina ce ta dawo da shi hayyacin sa, ya amsa mata sallamar ta kalle shi tace 
"lafiya kuwa Yallaɓai?"
"lafiya ya bata amsa"

Ta ɗan taɓe baki tace 

"dama zuwa nayi in tambaye ka, dan Allah meyasa Yusuf baya zama a office yanzu? Wane irin aiki ne aka bashi haka?"

Abbas dama a ƙule yake yana neman wanda ze gayawa matsalar sa, dan haka ya zayyane mata komai, ciki harda Aibata Yusuf, ba ƙaramin mamaki ne ya kamata ba, ganin duk headquarter nan babu wanda Yusuf yake sakin jiki dashi kamar Abbas, Amma ace Abbas ne da bakin sa yake faɗar wannan mahanga akan Yusuf, lallai ɗan Adam ba abun yarda bane.
A zahiri ta maze tace
"gaskiya kai yakamata ace kana samun wannan sha tara ta Arziki ba shi ba, yanzu kayi duk yadda zakai kasa a maye gurbin sa da kai, a karɓe aikin daga hannun sa, idan kana buƙatar taimakona ma zan maka, kasan mu mata akwai iya makirci"

Abbas ya washe baki yace 
"ƙwarai kuwa, amma fa nagode sosai Sakina"

************************************

Har Yusuf ya kama hanyar gida, kawai ya ɗakko wayarsa ya kira Manager Hotel ɗin nan, ai kuwa wayar ta shiga, Yusuf ya tambaye shi idan yana son ganin sa ya zasu haɗu? Ya gayawa Yusuf inda zasu haɗu a gidan sa, beyi wata wata ba yaje har gidan nasa.

Da ganin manager Hotel ɗinma kaga ɗan duniya, suka gaisa da Yusuf, Yusuf yace  "dama wata buƙata ce ke tafe dani, ina son ka nunamin mutanen da suka kama ɗaki a hotel ɗinku, tun daga farkon wannan watan"

Manager yace  "Kai Malam, ni na zata ma wata harkar cigaba ka kawo, wannan abun da kake tambaya sirri ne bama fitar dashi, manyan mutane ke zuwa Hotel ɗinmu, ba zamuyi exposing ɗinsu ba dan duniya babu yarda"

"ze kasance sirri ne tsakanina da kai, kasa a bani babu wanda ze sani"

"Malam bazan iyaba, ka tashi ka tafi kawai"

"zan baka dubu ɗari biyar, zaka bani akan wannan farashin?"

(Abunda yasa Yusuf baya son nuna shi waye, ma'aikaci ne na sirri, no need asan shi waye)

Murmushi mutumin yayi yace "yanzu naji batu, Amma tsakani da Allah turoka akayi, kokuma ma'aikaci ne kai?"

Girgiza kai Yusuf yayi yace 

"Dani ma'aikaci ne ko sisi bazan baka ba, sedai inyi amfani da ƙarfin aiki na, Matata nake zargi ina so in kamata red handed, kuma kona kamata bazan taɓa sako sunan ku a lamarin ba"

"Shikenan, Amma dan Allah ya zama sirri tsakaninmu"

"in Allah ya yarda babu meji, da gani se kai"

"shikenan muje se a baka"

Yusuf yace  "No bana son yawan zuwa gurin bana son a ganni a gurin, ta Email ɗina nake so ka turamin, zan baka ɗaya bisa huɗu na kuɗin seka turomin zan baka sauran, bana saɓa Alƙawari dan haka kaima karka saɓa"

Haka ya amince da wannan yarjejeniyar.

*********************************

Saleh ne yake kaiwa yana komowa, Alhaji Bukar ya fito ya sa meshi, ya kalle shi ya yatsuna fuska yace  "lafiya?"

A fusace Saleh yace  "dole ka tambaye ni lafiya, me kasa akayiwa ɗan uwana? Ta yaya zanje in ganshi lafiya ƙalau kawai labari ya isheni wai bashi da lafiya"

Alhaji Bukar yace  "dakata! Da ina son ganin bayan ɗan wanka da tun a shekarun baya gudun karya tona min Asiri da tuni ya bar duniya, zaman kotu daza'a koma bani da fargaba sam, inada ƙwararrun lawyoyi da na biya su wanda zasu tsayamin, dan haka ba abunda zesa in yiwa ɗanuwanka wani abu"

"Au haka ma zakece? Wato kai a wanke ka shikuma ya cigaba da zama a prison ko? Ga wannan mahaukaciyar Yarinyar taje ta sameni, tace muddin wani abu ya samu Bala ni zan maye gurbin sa, me kake tunani ne wai? Yarinyar nan tana da kuɗi zata iya aikata duk abunda taso"

Alhaji Bukar ya ɗan daki kafaɗar Saleh yace 

"shiyasa nace kazo mu haɗa kai mu raba ta da dukiyar, mu mallaki gundurin dukiyar da muke ta farauta muga ta tsiya"

Saleh ya make hannun Bukar yace  "Niba dukiyar tace a gabana ba, babu irin kyautatawar da mahaifinta be minba, ni dukiyar sa bata gabana, ni burina a wanke ɗan uwana a fito da shi daga kurkuku tunda bashi da laifi"

Wata uwar dariya Alhaji Bukar ya saki yace  "ubanwa yace maka bashi da laifi? Lallai har yanzu kanka a kwano yake, ka ƙyaleshi ya girbi abunda ya shuka, kazo a haɗa kai a nemi Arziki".

Yana gama maganar ya wuce ya bar Saleh a gurin.

************************************

Yusuf yaita safa da Marwa yana duba wayar sa, ba zato Sega abunda ya nema an turo masa ta Email ɗinsa, message ɗin na shigowa Manager ya kira Yusuf, Yusuf yayi masa godiya sannan ya tura masa sauran kuɗin, wanda kuɗaɗen da Widad take bashi ne, dan wani lokacin idan ta bushi iska se yaga alert.

Yusuf ya tura message ɗin cikin System ɗinsa da sauran wayyoyinsa, nan Yafara aiki akan bayanan da aka turo masa, ba ƙaramin mamaki ne ya kamashi ba ganin mutanen da suka ka kama ɗakuna a wannan watan zuwa ranar da suka je Hotel ɗin tare da Widad, wanda ya kama ɗaki ranar da sukaje shida Widad yafi bashi mamaki, Abun tambayar anan shine 'ya akayi Widad tasan da zuwan mutumin gurin? Me Widad taje yi? Gurinwa taje?' me ta gani ya sata kuka? '
Yusuf zuciyarsa ɗaya baya jin Widad zata aikata wani mummunan aiki na alfasha, amma akwai wani ɓoyayyen abu da yakamata ace ya sani.

Kamar wanda aka mintsina ya miƙe ya shirya, ya duba agogonsa ƙarfe takwas na dare, haka ya fita ya tari abun hawa ya tafi unguwar su Nurat.

Unguwar tasu shiru, amma haske ko ina da yake rukunin Gidajen masu kuɗi ne, har ƙofar gidan aka kaishi aka sauke.
Ya sauka ya nufin gidan su Nurat, ya tsaya suka gaisa da megadin, Yusuf yace  "Dan Allah gurin Nurat nazo"

Maigadin ya kalle shi yace "tasan da zuwanka ne?"

"A'a, bata sani ba, Amma ka gaya mata tayi baƙo"

Mai gadi ya kira Nurat a waya yasa a hansfreee ya gayamata tayi baƙo.

"Babu wanda zan haɗu dashi yau, dan haka ba zanga kowa ba"

Yusuf yace "kace mata Widad ce ta aiko ni"

Aida jin Widad ce tayo aiken Nurat ta rikice, tace "Kaishi guest room, ina zuwa"

Maigadin yayiwa Yusuf jagora, har wani katafaren Falo, Yusuf ya zauna yana jiran fitowarta.
Ko mintuna goma ba'ayi ba se gata ta fito, ta ƙaraso cikin falon da hanzari, sedai tana arba da Yusuf ta rikice ta buɗe baki zata yi ihu ta gudu, Cikin zafin nama Yusuf ya riƙeta tare da toshe mata baki.

"Meye haka kamar kinga wani aljani ko mugu? Kinga fa mutum ne ni"

Fizgewa tayi, ta shiga Ja da baya ta kwaɓe fuska zata yi kuka tace
"Nifa wallahi tun ranar da kuka bar nan, Widad bata ƙara zuwa gidan mu ba"

Gaba ɗaya Nurat ba tafi sa'ar Widad ba, sedai Widad tafi Nurat jiki sannan Izzarta da jin kanta yake sa ka ganta kamar Babba.

Yusuf yace  "Haba Nur, nifa ba wani abu zanyi miki ba kawai tambayoyi zan miki in tafi"

Girgiza kai ta shiga yi tana kiran sunan Daddy a hankali.

"Daddyn yana nan ne?" ya tambaye ta

Ta girgiza masa kai alamar A'a

"to ki nutsu ki zauna, hira za muyi in tafi"

A hankali ta zauna, tana rarraba ido dan a tsorace take da Yusuf, dan ba zata manta randa Yusuf ya shaƙeta ba, har yayi barazanar sace taba.

Yusuf yace "Calm down dear, hira zamuyi kawai in tafi"

Ganin taƙi sakin jikin ta yasa Yusuf ya miƙe ya zaro komai na Aljihunsa, dan ya tabattar mata da babu wani makami a tare dashi.

Ya kalleta yana ɗan nazarin ta sannan yace 
"ko ki tambaye ni ina Widad ko? Tun ranar da ta bar nan baki sake neman ta ba"

"Na kirata bata ɗaga wayata ne, nasan bazata sake yarda dani ba"

"Waye yace miki ba zata sake yarda dake ba? She's very simple and kind, but why do you attempt to kidnapped her?"

Kamar Nurat zatayi kuka tace  "bafa laifi na bane, Daddy ne"

Yusuf ya ɗan ƙara matsowa yace  "Amma me tayi wa Daddy haka da zesa a saceta?" yai maganar yana kallon idon Nurat, Yarinya ce dan haka yake binta a sannu cikin hikima

Ɗan shiru tayi sannan tace "Nifa ban sani ba"

"Haba me sunan manya, Haske maganin duhu, baki kama da maƙaryata ba, ni ya akayi ma kika san Widad har kuke hulɗa bayan bata son mutane?"

"Nifa ba wani hulɗa mukeyi sosai ba, da tun ina ƙarama, gidan su na U. K yana kusa da namu daga baya suka dawo Nigeria shine... Sekuma tayi shiru tana satar kallon Yusuf.

"Shine me? "

"Dad ɗina sunyi faɗa da Daddynta akan Siyasa, shikenan abunda nasani, Amma dan Allah karka gayamata Daddy nane yasa ayi kidnapping ɗinta idan ta sani, zata sa a kai Daddy na prison ne"

"bazan gaya mata ba, ai kin gayamin gaskiya, amma naga Daddynta ɗan kasuwa ne ba Siyasa ba me zesa suyi faɗa da Daddynki akan siyasa"

"to ainima bakomai na sani ba, muna yara lokacin Amma tabbas sunyi faɗa ne shine yake son ya rama akan Widad, amma ni ban san me yake so yayi mata ba"

Yusuf yace "shikenan nagane, gaskiya you are so kind dear, Insha Allah bazan bari taji ba, Amma dan Allah karki bari a cutar da ita, kinga marainiya ce ita abun tausayi, ke kina da Mum da Dad ɗinki ita kuma she's orphan"

Jinjina masa kai kawai tayi.

Yusuf yace "Bani wayarki in sami ki lambata, se mudinga gaisawa ni daga yau nayi ƙawa, ni zan maye miki gurbin ƙawancen ki da Widad"

Kallon sa tayi ta ɗanyi murmushi yadda yake magana ya burgeta, bashi da hayaniya, ya iya tsara magana daki daki, se yanzu ta gane ranar da yayi mata wannan barazanar ne ya koma kamar wani mugu amma ba haka yake ba, ta miƙa masa wayar sannan tace 
"Amma ni ban sanka a Family ɗinsu ba, waye kai a gurin ta?"

Yusuf yayi murmushi yace
"i don't belong to her family, but a very important person attached to her destiny"

Kallon sa tayi cike da rashin fahimta za tayi magana ya kashe mata ido ɗaya, gaba ɗaya seta sunkuyar da kai ta kasa maganar, ya daɗe yana daddana wayarta, ita kuma ta kasa cewa komai.
Seda ya gama abunda yake sannan ya miƙo mata wayar yace 

"Nagode sosai ƙawata, Allah ya bar zumunci, ni zan koma naji daɗin kasancewa dake da wannan hirar da mukayi"

Murmushi tayi tareda sunkuyar da kai tace  "baka gayamin sunan ka bafa"

"Sunana Abokin Nurat, Just call me Aboki or any name you like, good night Nur"

Ya ƙarasa maganar tare da nufar hanyar fita yana addu'a Allah ya  shiga lamarin sa akan wannan aiki me hatsarin gaske da yake yi, yasa hanyar da ya ɗakko ta zama mafita ga al'amuran.
Yayinda Nurat ta rakashi da ido har ya fice

Nurat tana komawa cikin gida Maman ta tace
"Ke lafiya kuwa? Waye wannan yazo kika daɗe haka?"
"Abokina ne yazo muka gaisa" tai maganar cike da basarwa ta shige ɗakin ta tana tunanin Yusuf

(Masha Allah, daga wannan posting bana tunanin zan kuma wani posting se Allah ya kaimu ranar Asabar insha Allah, gobe in Allah ya yadda zan fara jarrabawar ƙarshe ta makaranta, ku sani a addu'oinku please 🙏 🙏 🙏
Dana kammala exams insha Allah zanyi ƙoƙari ku dinga samun update akan lokaci, comments ɗinku zesa kudinga samun update kullum, idan kun shirya yanzu aka fara wasan, ba'a fara komai ba thank you for being with me 😍 😍 😍)

Domin gyara sharhi ko shawara, feel free to contact me
Ayshercool
07063065680                   

                     _*AƘIDA TA*_
   

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

                              PART1
                                  
                                  Page 14

ELEGANT ONLINE WRITER'S


Sosai Yusuf yake ƙara samun haske akan lamarin binciken da yake yi, Sam babu specific lokacin da Widad take bawa Yusuf albashi, duk lokacin da ta bushi Iska sedai yaga alert ɗin kuɗi, kuma kuɗi masu yawa, sannan be isa yayi magana ba.

Yana ta tattara bayananan daze gabatar a gurin aiki na sakamakon binciken da yake yi.

Tunda Yusuf ya tafi Nurat take tunanin, ko ta gayawa Mahaifiyarta yadda suka yi da Yusuf, wata zuciyar ta gargaɗe ta akan hakan.

********************************

Gaba ɗaya Widad ta takura kanta, sam ko Babban falo bata fitowa, tana iya sashin ta daga ita se magenta, duk da haka Yusuf kullum se yaje koda baze ganta ba kuwa.

Lambar wani abokinsa likita ya dubo a wayarsa ya kirashi, se da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.

"Yusuf kana da kirki kuwa? Ace ka ɓata ko neman mutane baka yi?"

Yusuf yace "Amma ka tsaya mu fara gaisawa, sarkin ƙorafi"

Nan suka gaisa suka taɓa hirar yaushe rabo, sannan Yusuf yace "dama doctor Hamza ina da wata 'yar tambaya ne, dukda nasan tambayar da zan maka ba a fannin daka karanta kenan ba, amma na sanka da shige shige"

Hamza yace "shikenan ina jinka, Allah yasa nasan amsar tambayar taka, in babu amsar ma  se'a nemo"

'Masha Allah, dan Allah Hamza wace irin larurar ƙwaƙwalwa ce take sa mutum ya dinga gudun mutane? "

Doctor Hamza yace
"Anthropophobia kenan, is a mental disorder, masu irin wannan larurar suna jin tsoron taron mutane, idan abun ya tsananta ma ko ahalinsu basa son su raɓe su, sedai wasu tsirari daga mutane, basu fiye son taron jama'a ba, ko shiga cikin mutane basa so"

Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "to me yake haddasa ciwon"

Hamza yace "eh to, abun da yake haddassa wannan larurar ga wasu, idan an taɓa cin amanarsu, mussaman wanda suka yadda da shi, ko kuma wani abu da ya taɓa faruwa dasu mara daɗi a rayuwarsu, wasu kuma hormones ne suke haddasa musu excessive fear ya danganta dai, zakaga wataran suna lafiya ƙalau ga wanda ciwon be tsananta a gare su ba, amma idan ya tashi zaka ga basa son haɗa ido da mutane, basa son suga ana kallonsu, kosu kasa bacci, ko yawan ciwon kai, bugun zuciyar su ya canza, wasu numfashinsu har ɗaukewa yake, ko su dinga karkarwa in sunga baƙo, ko wanda basu yadda dashi ba, ko kuma su dinga wrong perception akan abubuwa, ko su dinga ganin duk wanda ya raɓesu ze cutar da sune"

"Ok magana, nagode sosai Hamza amma meye maganin ciwon?"

"gaskiya babu wani sahihin maganin ciwon gaskiya, rehabilitation ne a dinga kwantar musu da hankali tare da ƙoƙarin canza musu tunani daga mummuna zuwa kyakkyawa, dan wasu in damuwar tayi musu yawa suna fara shaye2, ko dinga wasu tunani wanda ya saɓa da abunda yake a zahiri, ayi ƙoƙarin samar da wani abu daze dinga ɗebe musu kewa, koya ɗauke musu hankali daga damuwarsu, in kaga an basu magani mafi akasari sedai a basu magani akan sauran matsala, kamar bugun zuciyar, ko daidaituwar hormones ɗin ko makamancin hakan...

Shiru Yusuf yayi yana tunani, meye alaƙar ƙwayar daya gani a ƙasan kofin shayin da za'a bawa Widad da ciwon nata, Doctor Hamza Yana cikin yiwa Yusuf bayanin ne ya hango Widad ta fito, tana nufo inda yake zaune, gaba ɗaya fuskarta a haɗe kamar kullum, yauma shigar tata da ta saba ita tayi, jikin nan a tsuke a cikin ƙananan kaya.

Da sauri Yusuf yace "shikenan nagode sosai doctor, nagane Allah ya saka da alkhairi" ya katse wayar

Ya shiga wani tunanin, "to wace irin Allura akewa Widad haka? Amal tace masa ana mata wata Allura, ga kuma abunda likita yace"

Ta ƙaraso ta kalle shi a yamutse tace
"ɗakko mota, zamu airport ne yanzu"

Ya kalle ta yace
"me zamuje yi a Airport?"

"ban sani ba" ta bashi amsa

Ƙasa yai da idonsa yayi mata wani irin kallo sannan ya miƙe yai gaba, gaba ɗaya kasa gane kalar kallon tayi meya ke nufi da haka?

Ya ɗakko mota ya kunna suka fara tafiya, suna tafiya yana satar kallonta yana tunanin, me zeyi wa Widad wanda ze temaka gurin canza tunanin ta mara kyau zuwa me kyau, kamar yadda doctor Hamza ya gaya masa.

Yana cikin tunanin wayarsa ta fara ringing, sedai lambar ba suna, kuma yana tsoron ya ɗaga yaje a cikin abokan aikinsa ne, wani yayi masa kwaɓa, sekuma ya tuna halinta, yanzu yana ƙin ɗaga wayar zata masa wata fassarar, haka ya basar ya ɗaga wayar yasa a kunnen sa tare da yin sallama.

Siririyar muryar mace ce ta amsa tace
"Aboki ya kake?" se yanzu ya gane muryar Nurat, murmushi yayi yace "lafiya ƙalau, light ya kike?"
Wani murmushi ne ya suɓuce mata tace "lafiya ƙalau friend, dama cewa nayi bari in kiraka mu gaisa"

"Amma gaskiya kin kyauta Light, ina fatan kina lafiya ba kya cikin kowace irin damuwa? Kin san damuwa da yawan haɗe rai yana sa mutum ɓacin rai da saurin tsufa, kuma duk kyansa ya koma kamar wani abun tsoro"

Da sauri Widad ta juyo ta kalle shi, amma ya basar ya cigaba da wayar, yayin da Nurat tayi murmushi tace "Ni lafiya ƙalau nake, bani da wata damuwa ko matsala ina Widad?"

"tana gidansu, ko ince kina gaishe ta ne?"

Kamar Yusuf yana ganinta ta girgiza kai tace "Kamanta kace kar in gaya mata muna abota? Na tambayane kawai dan inji ko tana lafiya"

"Eh kuma fa hakane? Amma yaushe zakizo ki ganta?"

"Ai ban san wane irin kallo za tayi min ba idan nazo gidansu, inajin tsoror"

Tsaki Widad tayi ba tare da ta kalli Yusuf ba tace

"Malam ka isheni, ka cikamin kunne"
Murmushi Yusuf yayi yace
"light, se anjima Madam tace na cika mata kunne"

Jiki a sanyaye Nurat tace "Madam kuma? Dama kana da Aurene?"

Yusuf yace "Babba dani kice bani da Aure, ina da Aure mana muna tare da ita ma, munɗan fita ne, se anjima kar in sake ɓata mata rai"

Wani irin wulaƙantaccen kallo Widad tayi masa, dama yasan a rina
"ni kake cewa matarka? Baka da hankaline, ni ka kalleni ka cemin matarka"

"waye cemiki dake nake ne? Am just kidding idan ba haka nayi mata ba zata ga kamar na mata wulaƙanci ne, kuma babu daɗi ka Wulaƙanta mutum it hurts a lot, Yusuf baya Wulaƙanta mutane"

Wani tsakin ta kuma ja ta ɗauke kanta, yayin da shi kuma yayi murmushi, a ransa yace 'Insha Allah, sena canza miki dukkanin wannan gurɓatattun tunanin naki kafin in kammala bincike na"

Gurin wani restaurant sukabi, tace masa ya tsaya ai kuwa yayi parking, tana yi tana duba agogon hannunta, ta buɗe motar ta fita, shima ya fito yabi bayanta.

Cikin restaurant ɗin ta shiga ta samu guri ta zauna, Yusuf be jira unarninta ba shima yaja kujera ya zauna.

Aka kawo musu menu
(jadawalin Abincin da suke available)
Ta karɓa tana jujjuya menu ɗin, ɗan ɓata fuska tayi ta zaɓi Abunda take so,
Aka bawa Yusuf ma, ya kalli Menu ɗin ya girgiza kai yace
"Ni ban iya cin irin wannan Abincin ba gaskiya, Umma ta cika min ciki da ɗumamen tuwo dan haka ni ba abunda zanci"

Kallonsa tayi ta ɗauke kanta, yayin da waiter ɗin tayi murmushi ta karɓi menu ɗin ta tafi.

Karon Farko da Yusuf yaga Widad tana cin normal Abinci, sam bata damu da Abinci ba, sedai yaga tana 'yan ciye ciye, ta yaya mutum zeyi lafiya ba tare da cin cikakken Abincin da ze gina masa jiki ba, ko duk cikin rashin yardar ne oho mata.

Yanzun ma ba wani cin Abincin take ba, ɗan cakala take a jikin spoon, kamar wata ƙaramar Yarinya kamar me wasa da Abincin tana kaiwa bakin ta .

Yusuf ya ɗan ƙura mata ido yace "Madam are you really Hungry?"

Cigaba da cakalar Abincin ta tayi ba tare da ta kula shi ba.

Ko ɗaya bisa ukun Abincin bata ci ba, ko naman kai bata taɓa ba, ta ture Abincin ta ɗau tissue tana goge bakin ta, 'Iko se Allah, Abincin naira dubu huɗu akayi wa wannan cakalar aka barshi, wani yana nan yana fama da Yunwa'

"wai Harkin ƙoshi?"

"wai ina ruwanka dani ne? Ta yaya zan iya cinye wannan Abincin duka?"

"Amma kin san bazaki iya cinyewa ba kika sa aka kawo miki? Akwai dubban marasa ƙarfi da Abincin naira ɗari ma gagarar su yake a rana, kalli uban Abincin da kika bari, wataƙila yanzu wannan da kika rage sedai a zubar, ba kyau Wulaƙanta Abinci, wataran kema ze iya Wulaƙanta ki"

Ko kallonsa ba tayi ba, ta ɗauke kanta tana kallon wani gurin, amma tayi shiru tana saurarensa, gefe guda kuma ta shiga tunanin maganar sa, dagaske akwai wanda suke rasa Abincin naira ɗari ya gagare su? To wani irin Abinci ma mutum zeci da naira ɗari, se a samu mutum yace bashi da naira ɗari?.

Yusuf Yaja plate ɗin Abincin gabansa ya ɗau spoon ya fara cin Abincin da Widad ta rage.

Kallon Yusuf take, sosai mamaki yake bata shi sam be ɗau komai da zafi ba, Abincin data rage yake ci, ko dan dai shi talaka ne oho.

Yusuf ba ƙaramin mamaki yake ba yadda take ɗaga masa ƙafa, dan shi kansa yasan wasu lokutan yana wuce gona da iri, tana ƙyaleshi ne kawai

"ya naga kina kallona ko nayi wani abun ne na rashin yadda?"

Ɗauke idonta tayi daga kallonsa zuwa wani gurin daban.

Yusuf ya ciko spoon yace
"Kinga yadda ake cin Abinci a ciko cokali da Abinci, se mutum ya ƙoshi ba yadda kike yi ba, kamar kina wasan yara, koda yake yarinyar ce ai"

Ɗago ido tayi ta kalle shi, amma ya cigaba da cin Abincin yaƙi kallonta, lallai Yusuf ya samu dama a kanta ya fara rainata, tunda harya samu damar gaya mata maganganun da yaga dama, ita kanta Widad tana mamakin yadda take ƙyale Yusuf, ba yadda za tayi dashi wata ƙaddara me ƙarfi ta shigo dashi cikin rayuwarta, wanda ko dan albarkacin hakan yaci ta dinga ɗaga masa.

Seda ya kammala sannan ta ajiye masa ATM ɗinta, ta miƙe ta nufi hanyar fita, Yusuf kuma ya nufi gurin biyan kuɗin, kafin Widad ta kai ga ƙofar fita wani mutum da tunda suka shigo yake kallonta yabi bayanta.
Yusuf yace "ashe akwai mini Drama yau"

Ya biya kuɗin ya fito, sedai yana fitowa ya tarar tana zazzagawa Mutumin masifa.

"Kalle ka ni zaka biyo kace in baka lambata? Bazan bayar ba shashsasha an gaya maka kowa sakaraine irin ka?"

"Ni kike cewa sakarai?"

"Na gaya maka ko akwai abunda zaka iya ne?"

Yusuf ya ƙaraso da sauri gurin yace "haba bawan Allah, ya zaka biyo matar Aure kace kana so?"

Mutumin ya kalli Yusuf yace "Matar Aure kuma? Da wannan shigar tata?"

"koma wace irin shiga ce tayi ina ruwan ka? Haka muka tsara rayuwar Aurenmu, haka muka ga damar yi, idan har kasan shigar da tayi bata dace ba meye na biyo ta? Kana gurin nan muka zo tare mu kaci Abinci, danme zaka biyo ta kace kana so?"

Mutumin yace "Amma indai wannan matarka ce gaskiya kayi dacen Auren kyakykyawar mace, sedai bata da ɗa'a kuma bata san darajar Auren ta ba"

"bakomai a haka nake son a bata, sannan karka kuma gangancin kiran ta da wasu miyagun kalamai, ka gode Allah da ban ɗau mummunan mataki akanka ba"

Ya juya ya kalli Widad da mamaki ya hana ta magana, A fusace ta juya ta tafi mota ba tare da tace komai ba

Yusuf ya juya ya koma motar shima yana shiga ya zauna, ya kunna motar suka fara tafiya, ba tace komai ba se tafasa da zuciyar ta take yi

Ba zato ba tsammani, Widad ta Ƙanƙance ido tace
"i thinks you drunk something abusive today, kasan me ka faɗa kuwa? Which type of Weed did you take today? Wane irin rashin hankali ka aikata? Meye hakan kake ne dan me zaka dinga danganta kanka dani a matsayin mijina, kai ko Auren zanyi zan auri talakan mutum kamar Kane?"

Dukda yadda kalaman Widad suka daki zuciyar Sa haka ya daure, yayi parking ɗin motarsa, ya matsa Kusa da ita ya matsa yace "Abunda kika ci dai shi naci, dukda baki san meye So ba, ƙarewa ma kince baki yadda dashi ba, amma the magic behind Love is that, ba ruwan sa da talaka kome kuɗi, sannan wannan abunda nayi shine kaɗai mafita daze hana kowane kare da biri binki, da kuma ƙarewa surar jikin ki kallo, please Dress decently to avoid such type of people, dukda ina matsayin me miki aiki, aikin ma na direba, I have to tell you something, you have an attractive beauty Widad, stop exposing it anyhow yana taɓa zuciyata a duk lokacin da kika fito da wannan shigar naga wasu na ƙarewa wannan kyakykyawar halittar kallo, your beauty suppose to be only for your husband, duk wata mace me tsadace jikinta ma me tsada ne meyasa zaki dinga bari ana ganin naki?"

Ɗaga ido tayi tana kallon sa, gaba ɗaya Yusuf ya rufe mata baki, ya kulle mata kai, gaba ɗaya ta nemi izzar da jin kan da zata masa wulaƙanci ta rasa, yau wani irin kwarjini yayi mata data kasa cewa komai, shi kuma ya samu damar hakan yake ta abunda yaga dama, a baya zata iya rantsewa baze aikata haka ba, ganin yadda ko magana baya son yi.

Haka suka cigaba da tafiya kamar kurame, kowa da abunda yake saƙawa a zuciyar sa, gaba ɗaya tunanin rashin mutuncin da zata yi wa Yusuf take.

Har suka ƙarasa airport bata iya cewa komai ba, parking yayi amma bata buɗe murfin motar ta fita ba, shima zaman sa yayi yaƙi fita, ya sauke glasan suka cigaba da zama, lokaci2 ta dinga duba agogon hannun ta.

Buɗe ƙofar tayi ta fita, shima ya buɗe ya fito, Alhaji Nasir ne yake tahowa da brief case ɗinsa a hannun sa.

Yusuf ya ƙarasa da sauri yana gaida Alhaji Nasir tareda karɓar brief case ɗin hannun sa.
Alhaji Nasir yace "Yayana na kaina, fatan na sameku lafiya ya amana ta?"

Yusuf yay murmushi yace "Alhamdilillah"

Ya kalli Widad yace "my Lovely har yanzu kina fushi da Dad ko?" yai maganar yana rungume Widad, kamar anmata dole tace "Welcome Daddy"

Alhaji Nasir ya ɗan shafa bayan ta yace"thank you sweetheart" suka ɗunguma zuwa mota gaba ɗaya, suna tafiya Alhaji Nasir da Yusuf ne kawai ke hira, Amma Widad tunanin ta ta yaya zata hukunta Yusuf.

Har Yusuf ya gama aikin sa na ranar ya tafi Widad bata samu mafita ba.

***********************************

"Jama'a bafa a bori da sanyin jiki, wannan ce damar da yakamata muyi amfani da ita, tunda Allah yasa yarinyar nan tana ƙasar nan musan abunda za muyi" cewar Alhaji Munir

Alhaji Musa yace "Ni idan an samu abun nan falillahil hamd, amma babban burina be wuce in Wulaƙanta Alhaji Nasir a idon duniya shida ahalinsa ba kamar yadda ya Wulaƙanta ni ya ɓata min suna"

Alhaji Haruna yace "gaba ɗayanmu buƙatar mu ɗaya ce, kuma kunsan Alhaji Bukar shike bamu umarnin abunda zamuyi, karmu yadda muyi abunda ze waegaza shirin mu, yanzu yarinyar taje gidan yari tayi wa Hashim barazana akan indai da hannun sa akan wannan lamari daya samu Bala to tabbas zata ɗau mataki akansa "

Alhaji Musa yace " Umarnin Alhaji Bukar kawai nake jira, amma akwai yuwuwar shima a kauda shi, dan komai ze iya faruwa barinsa a doron ƙasa"

Alhaji Haruna ya zame akan kujera yana shafa tumbinsa yace
"Ni dai kam da zan samu yarinyar nan, So nake gaskiya, dan akwai ta da ƙira daidai gwargwado".

Tsaki Alhaji Munir yayi yace "kai ka fiye shirme, ana ta kai wake ta kaya, in in hutawa kake so, ka fita ƙasashen waje ga mata nan farare yadda kake so, amma yanzu ka bari idan muka karɓi abunda muke so, muka aika Nasir Daula kiyama, se kayi yadda kaso"

Wata uwar dariya suka saki hadda shewa.

**********************************

"Bulama tafiya tayi Alhamdilillah, na samu approval na fara business ɗina da China"

"Masha Allah, naji daɗin hakan, Allah yayi jagora"

Baban Widad yace "Ameen ya Allah, sedai ko kun samu saɓani da 'yar taka ne? Tunda na dawo naga bata walwala ko akwai matsala ne?"

Alhaji Bulama yai murmushi yace "hmm Widad' yata ta kaina, tabbas munyi faɗa, kasan tunda nace ayi mata Aure take jin haushi na, tazo ta sameni akan wai sena mata Visa ta koma naƙi, shine take fushi"

Alhaji Nasir ya girgiza kai yace "Nima wancan satin ta kirani tana kuka, akan lallai sena kiraka nasa an mata visa ta koma, ni kuma gaskiya bazan bari ta koma ba, idanma zatavkoma se bayan Auren ta da Fahad sa tafi tare"

"hakane, daga lokacin da ta fara tara iyali dole ta dena wannan halayen nata, sannan mamanta ta kawomin ƙararta akan yadda suke da direban nan, na kirata nayi mata faɗa, nanma ta sake yin fushi dani"

Alhaji Nasir yai murmushi yace "ina tunanin akwai wani ɓoyayyen al'amari a tattare da yaron nan, ba ƙaramin daɗi naji ba ganin shine mutum na farko bayan nida kai da Widad take sakewa dashi"

"Amma karfa muyi sake yazo suyi shaƙuwar da zamu yi da nasani"

"Insha Allah ba zamuyi ba, dan yaron yana da tarbiyya sosai"

"Amma idan soyayya ta shiga tsakanin su fa?"

Alhaji Nasir yace " Yarinyar da bata yadda da soyayya ba, ta ina zasu fara soyayya? Gaba ɗaya Widad ɗina a birkice take bata da alƙibla"

Bulama yace "Kasan bata da alƙibla ai kuwa ba abun mamaki bane ta fara soyayya da direban ta, tunda shi so baya sallama".

"to nidai duk abunda ze saka ta farinciki shi nake so, idan ta kawo shi tace tana so bakomai se in Aura nata shi"

Bulama yace "Allah ya kiyaye mu aura mata direba haba Daula"

"to masu 'ya, ai seka biye mata kuyi tayi"

Sukayi dariya suka shiga hirara duniya.

***********************************
Sintiri take a ɗakin ta, tana son gazgata abunda take ji a zuciyar ta game da Abokin ta. Dagaske na kamu da Son wanda yake daga ɓangaren maƙiyin mahaifi na, amma ban san alaƙarshi da Widad ba, amma tunda na gansu tare suna da alaƙa.
Shiru tayi tana tuna yadda ya zauna a kusa da ita yana mata magana, cikin rarrashi danta saki jiki dashi.

Kamar light da yake kiran ta dashi yafi komai yi mata daɗi, Amma dagaske yana da Aure? Ta tambayi kanta, anya za'a yarda a auramin me mata? Gashi kuma ɗan uwan Widad.

Dafe kai tayi tace "Subhanallah"

"ke lafiya kuwa? Sintirin me kike tayi haka kamar kinwa sarki ƙarya?"

Juyawa tayi ta kalli inda Maman ta ke tsaye tace "bakomai fa"

"bakomai, a hakan? Gaba ɗaya alamu sun nuna baki da gaskiya sam"

Ta ɗan tura baki tace "wallahi ina da gaskiya"

"shikenan, idan tayi wari maji"

Nurat ta koma kan gadonta ta zauna ta ɗakko wayarta ta shiga kiran layin Yusuf amma shiru baya shiga, tayi2 harta gaji ta ajiye, tana mamakin ya akayi hakan ta faru?

Shikuwa Yusuf tun ranar data kira shi agaban Widad, yana komawa gida ya cire layin ya ajiye gaba ɗaya.

**********************************

Oga Suleiman ne zaune akan kujera yana gwadawa Sakina wasu ayyuka a computer, sun maida hankali sosai kan aikin.

Abbas ne yayi sallama, suka ɗago gaba ɗaya suka dube shi tare da amsa sallamarsa, Sakina ta gaida Abbas, yayin da Abbas ya ƙamewa Suleman cikin girmamawa.

Suleiman ya bashi damar zama, sannan ya miƙa masa hannu suka gaisa, Suleiman yace "Abbas kwana biyu banga Yusuf ba fa, ya kamata ace yazo ya gabatar min da sakamakon binciken da yayi"

Abbas yace "ranka ya daɗe, nima kaina na kasa gane inda yasa gaba, gaba ɗaya kamar ba aikin yake ba, yaje ya shantake se abun Arziki yake samu a gidan, alherin da suke masa yasa gaba ɗaya hankalin sa baya kan aikin, da dai da hali a canza shi da wani kawai"

Suleiman yace "Amma kaika cemin ze iya aikin, da kai nace zan bawa ka nunamin ya fika haƙuri da juriya"

"Ai Oga sam ban san haka ze faru ba, ban taɓa sanin Yusuf yana da son abun duniya ba seda ya karɓi aikin nan, ba abunda yake se neman gindin zama a gidan da yake"

Sakina kam sakin baki tayi tana sauraren yadda Abbas ke ɓata Yusuf a gurin ogansu, wanda hakan ze iya jawowa Yusuf babbar matsala a gurin aikin nasu, Yusuf ya yadda da Abbas sosai, dan yana masa kallon ɗan uwa bama abokin aiki ba.

Oga Suleiman yace "shikenan, zan duba idan da dama zan kira shi a waya ma, inaga karɓar aikin zanyi daga hannun sa in bawa wani"

***********************************

Gidan shiru babu kowa, Yusuf yana inda ya saba zama idan yaje gidan su Widad, Murtalah ne yazo inda Yusuf yake yace "Malam Yusuf kana nan kana hutawa ashe?"

"wallahi kuwa Murtala ya aikin?"

"Alhamdilillah, ai kana fama Yusuf, kullum se kazo ko zakayi aiki ko ba zaka yi ba"

Yusuf yayi murmushi yace "to ya za'ayi tunda na yadda zanyi aikin, ai dole in cika ƙa'idar aikin"

Murtalah yace "hakane" suna cikin hirar Amal ta fito, ta ƙaraso inda Yusuf ke zaune, ranta a ɓace tace "kazo ana son ganin ka"

Ba musu ya miƙe yabi bayan ta, suna shiga babban falo har Yusuf zeyi hanyar ɓangaren Widad, dan yasan be wuce ace ita take kiransa ba, tunda Alhaji Nasir baya nan.

Amal tace "A'a,  ba a nan ake neman ka ba"
Ta nuna masa hanyar ɗaya part ɗin dabe taɓa taka gurin ba, seda ya ɗanyi jimmm ya kalle ta sannan yace "shikenan muje"

Suka rankaya ɓangaren data nuna masa, tana tafe yana binta a baya
Wata ƙofa ta buɗe suka shiga, matsakaicin bedroom ne, me ɗauke da kayan more rayuwa sedai be kai haɗuwar na gimbiyar gidan ba.

Amal ta juyo ta kalle shi tace "Yusuf Meka ke nufi dani ne?"

Cike da rashin fahimta yace "kamar yaya? Kince ana kirana kuma kin kawo ni nan"

"Yusuf nina nake nemanka ba wani ba, na gaya maka abunda ke raina amma ka maidani kamar wata banza, Haba Yusuf me yasa baka da tausayi ne? Soyayyar ka nata wahalar dani amma hankalin ka yana kan waccan banzar mahaukaciyar, har dama ka samu a kanta wanda zaka rama irin wulaƙancin da take maka, ATM ɗinta kwanansa nawa a gurin ka? kamata yayi kayi amfani da wannan damar ka azurta kanka, tausayin mara tausayi asara, asara ne gagaruma ko dai dan Widad tana da kuɗi shiyasa kake Wulaƙanta ni?"

Yusuf be taɓa jin son Amal a ransa ba, ta yaya suna muzanta wadda suke cin Arzikin gidan su, ina gashi da yake bare? Kuma suna ta jadadda masa yayi wannan gagarumar sata haka?

"Amal ki fuskance ni, niba na Wulaƙanta mutane, sannan bani na tara musu dukiya ba, ta yaya zan musu wannan mummunan aiki? Ni ba Ɓarawo bane, dukiyar Widad bata gabana mutunci da girmamawa ya fiye min wata dukiya komai yawan ta, indai ban rasa ci da sha ba Alhamdilillah a yadda Allah ya ajiye ni, Widad batamin laifin komai ba, babu wani abu da tayi min wanda zesa in cutar da ita ko mahaifinta, tsakanina da su in musu aiki ne su biyani bisa ga yarjejeniyar da na sakawa hannu, Amma Amal tsakani na dake babu batun Soyayya duba da banbanci da kuma tazarar dake tsakanin mu, ke 'yar masu kuɗi ce, ni kuma talaka ne matsiyaci kamar yadda mutan gidan ku suke faɗa"

"Yanzu kana nufin ba zaka karɓi Soyayya ta ba Yusuf, ka zaɓi cigaba da wahalar da zuciya ta, mace me kima kamata ince ina sonka amma ka watsamin ƙasa a ido? To wallahi baka isa ba, zaɓi biyu ke gareka kodai ka karɓi Soyayya ta, ko kuma in shirya maka gadar zaren da idan ta rufta da kai har Abada ba zaka sake wani Amfani ba"

'Kiyi duk abunda ki kiga dama, tabbas da soyayyar gaskiya kike min da baki faɗi haka ba, tabbas na taɓa Soyayya nasan zafin ta, Amma ba' a dole a soyayya "

Yana gama maganar ya juya ya fice daga ɗakin, biyo bayan sa tayi tana ƙwala masa kira, Amma yaƙi tsayawa yana buɗe ƙofar part ɗin ze fita yayi tozali da gimbiya 'yar masu gida, Widad ce a tsaye a bakin ƙofar dake facing ɗin wadda ya fito, se muzurai take idanunta sunyi Ja, tana masa wani irin kallo me wuyar fassara.

Me kuke tunanin ze faru?

(Masha Allah, am speechless wlh, Addu'arku tayi tasiri a gareni ina miƙa muku godiya, masu tambayar jikin Daddy Alhamdilillah ya warke ras💃💃💃  almost done with the exams only some part remains, saura fatan Nasara, farinciki yasa nace bari inyi surprising ɗinku da posting, ina jiran jin comments me fasa waya, idan anyi Comment yadda nake so gobema akwai posting insha Allah 😍😍😍 ina godiya masoya)

Domin sharhi, gyara, ko shawara feel free to contact me
Ayshercool
07063065680                    _*AƘIDATA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

                          PART1
                                Page 15

ELEGANT ONLINE WRITER'S

Turus Yusuf yayi ya rasa me yakamata yayi? Me zeyi wanda zesa Widad ta yadda da shi, Amal ma da ta ƙaraso domin cimma Yusuf, tana ganin Widad itama tayi Turus ta shiga rarraba ido kamar an sacewa karya 'ya' ya.

Widad tayi wa Yusuf alama da hannu ya biyo ta, ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige, haka ya bi bayan Widad zuwa part ɗin ta, gaba ɗaya ya saddaƙar yana jiran jin ruwan masifa daga bakin Widad.

Ta kalle shi tace "nayi list na abubuwa da nake buƙata ne, za kaje ka siyomin, ka lura da duka abunda na rubuta bana buƙatar product ɗin basu nace ba"

Jiki ba ƙwari ya jinjina mata kai, ta ɗakko paper ta miƙa masa tare da ATM card, a sanyaye yasa hannu ya ksrɓa, amma harya juya  zefita beji tace masa komai akan ganinsa ya fito daga sashin su Amal ba.

Har ze fita ya tsaya ya juyo ko zata yi magana, amma yaga tana danna wayarta, tana ɗaga ido suka yi ido huɗu dashi ta kalle shi tace

"Lafiya? Ka tafi mana"

Ya kalle ta yace "bakomai"

Ya juya ya fita yana sake waiwayen Widad ko zata yi magana.

Fahad ne keta shirya kayansa a trolley, Anwar ya kalleshi yace "Fahad ji nake kamar in bika mu koma Nigeria tare, amma ba yadda zanyi, munzo tare ka rigani kammaluwa"

Fahad yace "Ai kai ba komawa Nigeria ce ta dame ka ba, zuwa kaga wannan yarinyar ne ya dame ka"

"ƙwarai kuwa faɗi ka ƙara Fahad, ni kaɗai nasan abunda nake ji game da ita, nima ina nan dawowa ai Insha Allah, inga farincikin zuciya ta"

"Allah yayi maka magani, dan kaibnaga abun naka ka afka da yawa"
  "kadai bari kawai, dan Allah Fahad kayi ƙoƙari ka samo min lambar ta idan kaje Nigeria"
Yatsuna fuska Fahad yayi yace  "gaskiya ban maka Alƙawari ba, dan tamin rashin mutunci marinta zanyi"
Anwar yayi dariya yace 
"da kuwa ka ƙare rayuwar ka a prison"
"kaini ka isheni da zancen yarinyar nan haba"

Ƙarshe Fahad ya fice ya barwa Anwar ɗakin, dan ba ƙaramin haushi yake bashi ba idan yana zancen Widad.

***********************************

"Ana ƙoƙarin a hallaka min ɗan uwana, sannan kuna min barazana da rayuwa ta, gefe guda ga yarinyar nan itama ta sakoni gaba, anya Alhaji Haruna kunmin adalci kenan?"

Alhaji Haruna yace  "Adalci ɗaya za muyi maka Sale, kayi aiki nan na ƙarshe da muke so, in ba haka ba da kai da ɗanuwanka haka zaku ƙare kuyi biyu babu, tabbas muka samu abunda muke so zamu fidda ɗan uwanka, sannan baku ba na kusa da kuma seya azurta"

Saleh ya fesar da iska yace  "kamar yaya? Yanzu dai ta tabbata kune kuja bawa ɗan uwana abunda yasa rashin lafiya ta kama shi, don ku kasheshi karya tona muku asiri"

Alhaji Haruna yayi murmushi yace  "zata iya kasan mune, kuma zata iya kasancewa bamu bane ba, ka sani ko ɗan uwanka ya tona mana Asiri bashi da wata cikakkiyar hujja a kanmu, kuma muna da ƙarfin da zamu siye Alƙalai da lawyoyi, shari'ar ta tafi a banza, shi kuma a cigaba da tsaron sa, abu ɗaya ya rage maka, shine ka haɗa kai damu mu gudanar da wannan aikin tare "

Maimakon Saleh yayi magana, sema tsaki da yayi yai waje yana wani irin huci kamar kumurci.

***********************************
Kafin Yusuf yaje aiken da Widad tayi masa seya wuce gida ya ɗakko system ɗinsa ya wuce office.

Yana shigowa harabar station ɗin ya tsaya yana gaisawa da mutane, Sakinace ta hango shi, ta yunƙuro ta fito da sauri ta tare shi, ta kalle shi tace
"Sannu da zuwa yau ka leƙo mu kenan?"

"Yawwa sannu" kawai yasa kai ya wuce, ya nufi office ɗin Abbas, gaba ɗaya dirircewa tayi ta shiga tunanin ya zata yi ta fahimtar ds Yusuf, irin illar Kasancewar sa da Abbas.

Yusuf yana zuwa ya miƙawa Abbas hannu suka gaisa, Abbas yace "mutumina gidan daula sun ɓoye mana kai gaba ɗaya fa"

Yusuf yace  "bari kawai Abbas, kullum a cikin zullumi nake, the more nake binciken the more nake sake gano Wata sarƙaƙiyar, in taƙaice maka ma an fara bina wallahi"

"Kamar ya an fara binka?"

"Wai wani abu ake so in karɓo a hannun Widad, gashi yau na shiga wata cakwakiya a gidan nan, ina ta jira ta sauken kwandon bala'i amma taƙi kulani, ƙarewa ma aikena tayi, shine nace tunda na samu chance bari inzo inga oga Suleiman"

Abbas yace  "ka gan shi kayi masa me?"

"In fara presenting abunda bincike na ya nuna min mana, akwai buƙatar tsananta bincike a wasu guraren, amma kaga ai yakamata in gaya masa"

Abbas yace  "garajen Meka ke hakane Yusuf? Ka bari ka kammala binciken nan, idan ka kammala base ka kawo masa ba, Yallaɓan mafa baya nan ana nemansa a headquarter za suyi meeting, kasan koka bashi cewa zeyi kabi komai a hankali"

"So kake inzo inyi laifi kenan? Ni nafi ganewa in fara presenting ɗin aikin"

Abbas yace  "A'a karka damu, kabi komai a hankali"

Yusuf yace "shikenan bari in tashi in tafi, dama nan aikena aka yi"

Abbas yace  "Amma Yusuf akwai cigaba a cikin binciken kuwa?"

Yusuf yace  "Sosai makuwa, an samu ci gaba, the more nake binciken the more nake sake cin karo da wasu matsalolin, Amma idan bincikena ya tabbatar da abunda nake zargi, mutane da yawa a ƙasar nan za suji kunya"

Abbas yace  "wai tukuna ma inga abunda kayi kake son ka nuna masan, suwaye za suji kunyar?"

Yusuf yace  "kabari sena kuma dawowa se mu cigaba da zancen yanzu ina sauri tunda baya nan tafiya zanyi"

Yusuf yaja System ɗinshi yai waje, bayansa Abbas yabi da kallo yana ƙwafa, 'Sena sa an Ƙwace aikin daga hannun ka tukuna za kayi bayani'

Sakina tana so ta yiwa Yusuf magana, amma sam yaƙi bata fuska, tana ji tana gani ya fice daga gurin, tunani ta shiga yi, yadda Yusuf ya yadda da Abbas babu lallai kota gaya masa ya yadda da abunda tace.

Yusuf yaje yayiwa Widad siyayyar data aike shi, ya wuce gida ya gama abunda yake yi sannan ya koma gidan su Widad.

Har yanzu gabansa faɗuwa yake, ya ɗau kayan ya shiga ya kai mata, sedai da yaje bata part ɗin nata se maganta akan gado.

Ya ajiye mata kayayyakin, ya ɗaga ƙasan pillow ɗinta ya sa mata ATM Card ɗinta ya fito.

A falo ya ci karo da maman su Amal, ta masa wani irin mugun kallo tace  "kai daga yau, bana son sake ganin ka shigomin falo ba tare da ka nemi izini ba, na gaji da wannan sintirin da kakemin, baligi kana ratsawa kana wuce ɗakin ta, baze yuwu ba"

"kiyi haƙuri Hajiya, nima ba da san raina ba, sedai ita Madam bata jiran izinin kowa kafin ta yanke hukunci, dan haka wannan maganar a tsakanin ku ya kamata ku tattauna ta"

Har Hajiya Halima ta buɗe baki zata yi magana se kuma tayi shiru, waiwaya wa yayi yaga Shigowar Widad ce tasa ta yin shiru, bata kula su ba tayi part ɗinta, shima Yusuf ya silale ya bar falon.

*******************************

"Maman Yara ina cikin farinciki Ɗana ze dawo, yakamata ayi dukkanin wasu shirye shirye da suka dace domin tarbarsa, yasuhe rabon sa da ƙasar nan? Sannan ya dawo ya tarar da kyakkyawan Albishir"

Haɗe rai Hajiya Sarah tayi tace  "nikuma takaici ne fal raina wallahi"

"Saboda me takaici fal ranki, kamar ba ɗanki me ze dawo ba?"

"Eh ɗana ne, amma abunda kake shirin yi kaima kasan be kamata ba, ta yaya yarona lafiyayye zaka haɗa shi Aure da mahaukaciyar da bata san girman kowa ba, ga bata da tarbiyya"

Alhaji Bulama yace  "Easy Madam, Sarah shifa ɗa na kowane, bekamata ki cigaba da aibata Widad ba, itama kamsr 'ya take a gurin mu duba da yadda mahaifinta yayi mana halacci a rayuwa, muna ƙoƙarin yin abunda zesa ta dawo hayyacin ta ne, kuma kinga mu munsan larurarta, Fahad ze iya haƙuri ya zauna da ita, saɓanin a bawa wani a waje Auren ta"

"to kai kaɗai ne yakamata kayi tamakon? Ina sauran mutanen gari? Nidai gaskiya aka haɗa Auren ɗana da wannan tantiriyar mara mutuncin an cucemu, kai kanka da kake matsayin uba a gurin ta cin zarafin ka take, inaga ɗanka kuma?"

"Sarah, bazan zaɓawa yarona abunda ze cutar da shi ba, Aure yana gyara mutum, wuyarta su zauna a guri ɗaya ze iya canza ta"

"A'a canza halin wannan yarinyar banga ta inda ze yuwu ba Sam, kawai ka canza shawara da tunani"

Tai maganar tare da miƙewa ta bar masa ɗakin

************************************

Yallaɓai Suleiman na dawowa, Abbas ya miƙe ya tafi Office ɗinsa, ya shiga ya gaida Sulaiman cikin girmamawa irin ta masu ɗamara, se da yayi masa izini sannan ya zauna, suka sake gaisawa.

Abbas yace "Yallaɓai, lokaci fa na ƙurewa, game da aikin nan daka bawa Yusuf, bana tunanin abunda aka sashi yake yi, ɗazu yazo gurin nan, na ɗanyi masa tambayoyi akan aikin, Amma Amsoshin daya bani sam basu gamsheni ba, da alama dukiyar dake gidan da alherin da suke masa yasa ya bar aikin da 'aka sashi "

" Amma a iya sanina Yusuf mutum ne me hazaƙa, nasan shi da ƙwazo da himma akan aiki, ba shida kwaɗayi sam"

"Yallaɓai mutum na iya canzawa a kowane lokaci, Yusuf abokina ne, amma ba yadda zanyi, bana son inci amanar aiki ko' a samu matsala akan harkar aikin mu kimar mu ta zube a idon duniya, Amma ya kamata kayi wani abu yallaɓai"

Suleiman ya ɗanyi shiru sannan yace  "idan kuwa hakane, to tabbas Yusuf ya bani mama, sedai zan kira shi muyi magana, zan bibiye shi idan har na gano maganar da kake gayamin gaskiya ne, zan ɗau mataki na musamman akansa"

Abbas yace "Yallaɓai idan har ka kira shi kuyi magana ai zaka ɓata komai, zeyi duk me yuwuwa ya kare kansa koda kuwa ƙarya ze maka danka yarda da shi, tunda shima jami'in tsaro ne yasan duk hanyar da zebi ya kare kansa"

Suleman yace  "Abbas base ka nunamin aikina ba, Nagode da wannan bayani naka zan bincika, ka ciji jami'i nagari tunda har kishin aikin ka be hanaka ɓoye laifin Abokin ka ba"

Abbas ya miƙe ya sarawa Suleiman sannan ya fice.

Koda ya bar Office ɗin Suleiman Office ɗinsa ya koma yana tunani, tunani yake akanme zeyi wanda zesa gaba ɗaya aikin da Yusuf yayi ya lalace kowa ma ya huta?

************************************

Gaba ɗaya Nurat ta rasa abunda yake mata daɗi, ta shiga damuwa rashin samun wayar mutumin da ko  sunansa bata sani ba, dama Widad ta dena ɗaga wayarta gaba ɗaya, tun ranar da tazo birthday ɗin ta, abun nan ya faru, ta fara shawarar ko gidan su Widad zata je don ta tambaye ta wannan wanda suka zo taren.
Sedai kuma tayi wani tunani, aiki ne me matuƙar sauƙi a gurin Widad ta sa aka mata a ɗaure, bata da tabbacin Abokinta ya gayawa Widad abunda ya faru kokuma A'a, gaba ɗaya ta rasa abunda yake mata daɗi, komai ya dena mata daɗi se tunanin wannan bawan Allah, me matuƙar kirki, a farko tayi zaton shima mugu ne lokacin da ya ritsata har yayi mata barazana, amma yanzu ta gane ba haka abun yake ba, ranar da yazo gidan yanayin yadda ya mu'analance ta da kyakkyawar ma'amala.

************************************.

Fahad ne da Anwar tsaye a tashar jirgin Sama, Anwar yace "Fahad ina taya ka murnar kammala karatun ka, Allah ubangiji ya kaika gida lafiya, sena taho nima in next couple of weeks Insha Allah"

Fahad yayi murmushi yace  "to baban Soyayya, kaima ina taya ka murna, tsiran namu befi sati biyu, ina maka fatan Nasara ɗan uwana seka taho".

Suka rungume juna suna murmushi, sannan Fahad yaja trolley ɗinsa yayi gaba.

"Amal kin san wani abu kuwa? Munyi waya da Yaya Anwar yace min Fahad yau ze dawo Nigeria, baki ji daɗin da nake ji ba, dan Allah me ya kamata inyi wanda zan sake kama zuciyar sa, yaji in ba niba se rijiya"

Wani banzan kallo Amal tayi wa Ramlah tace  "Ban sani ba, kije kiyi abunda kika ga ya dace"

Cike da mamaki Ramlah tace  "lafiyar ki kuwa? Me yayi zafi daga neman shawara zaki hayayyaƙomin?"

"dole kice haka mana, da yake matsalarki itace damuwa kawai, ni ina lokacin da nake cikin tawa damuwar ziga Mummy kikeyi, kuka haɗemin kai kuka dinga hantara ta, har dena kulani kukayi saboda kawai nace ina son Yusuf, Ashe ke kaɗai kika san So, ni ban sanshi ba ko? Can ta mulmule miki gara tun wuri kema ki cire shi daga ranki, dan in kin manta bari in tuna miki, 'yar masu gida akace ze aura kuma kinsan baki isa kice kina da matsala da hakan ba, danke ba mutum bace a kanta, kuma kinsan baki isa kiyi takara da ita ba, akan haka ba' aƙi a baki red card daga gidan nan ba, you better go back to your senses "

Tana gama faɗin haka ta miƙe ta fice daga ɗakin, wani zazzafan gumi ne ya shiga karyowa Ramla, dan gaba ɗaya ta manta ds batun ance za'a haɗa Auren Widad da Fahad.
Gaba ɗaya kanta ys kulle dan bata san wama yakamata ta tunkara ba, Mummy ba abunda zata iyayi, shiru tayi tana tunanin meye mafita? "

************************************

Widad ta dudduba Aiken da Yusuf ya kawo mata, ya siyo komai kamar yadda tace, harda receipt ya kawo mata, tana duddubawa taci karo da wata leda, ɗakko ledar tayi ta buɗe me zata gani, wasu tsala tsalan Abaya ne kala biyar, kowacce da kalar ta sunsha stones se ƙyalli sukeyi, ta ɗauka ɗaya bayan ɗaya tana jujjuya su.
'me wannan gayen yake nufi?' ta tambayi kanta

'harni ze saiwa kaya ya bani? Meya maida ni ko nayi masa kalar saka wannan kayan?'

Tattare kayan tayi ta fito falo a fusace, da watsasu akan kujera, part ɗin su Amal ta nufa tana huci, babu ko sallama ta banka ɗakin su Amal, gaba ɗaya seda suka razana, mussman Amal dan a tsorace take tun ranar da Widad ta gansu tare da Yusuf.

Ta kalli Amal tace  "Kije bakin gate, ki kiramin wancan sakaran direban yanzun nan" tana gama maganar ta juya ta fice

Ramalh na ganin a yadda Widad ta shigo tayi magana, tasan akwai matsala dan haka ta miƙe ta fita dan ganin me ze faru,
Jikin Amal na rawa ta miƙe tayi waje kiran Yusuf.

Koda saƙon Kiran Widad ya riski Yusuf yasan a rina, yasan ze fuskanci wulaƙanci, Amma ya dake ya shiga cikin gidan.

A falo ya tarar da ita a tsaye, tana wani irin huci, haɗi da sauke numfashi, Tabbas Widad Yarinya ce ƙarama Amma Allah yayi mata kwarjini na musamman.

Yaje daf da ita ya tsaya ya sunkuyar da kai ba tare da yace komai ba.

"Kalleni nan"

A hankali ya ɗaga idonsa yasa a nata, dukda bugawar da ƙirjin Widad yayi be hanata cewa
"Nayi maka kama da matsiyaciya ko me neman temako?"

Kallon ta yayi bece komai ba
Cikin tsawa tace  "magana nake maka"

"temako ana yinsa ga kowa, duba da rayuwar gaba ɗaya taimakon juna mukeyi, dan haka ba fuska ake gane...

" Shut up!!! "
Tai maganar tare da ɗaga masa hannu

"waye kai? Me kake da shi? Me kake taƙama dashi wanda har yasa kake ganin kana da abunda zaka ɗauka ka bani? Me kake da shi? Ni zaka bawa wannan banzayen Abubuwan na maka kama da wadda zata saka wannan tarkacen, shara? Ka taɓa ganin na saka irin wannan kayan? Ko na ce maka ina da buƙatar su? "

Te Ɗebo kayan dake kan kujera ta watsa masa a fuskar sa tace " don't you ever try to make this mistake again, ka nemi mabuƙata ka basu  Widad tafi ƙarfin saka wannan tsumman"

Idon Yusuf jawur ya ɗago ya kafe ta da ido, ko ƙyaftawa baya yi, dukda hucin da take hakan be hana ta tsayawa tana kallon sa ba itama.

Ba zato ba tsammani suka ga Daddy ya ƙaraso cikin falon, ya durƙusa ya tsince rigunan, yazo gaban Yusuf ya kamo hannun Yusuf yasa nasa yace
"Yusuf wannan kyautar ni kayi wa, ba Widad ba, lokacin da zanyi tafiya ka kawo alheri ka bani kace in ƙara a guzuri, kuma ka nemi da kar in gayawa kowa, yanzu ma ka ɗakko kyauta ka bawa 'yata ɗiya tilo da nafiso, Tunda Allah yayi min Arziki babu wanda ya taɓa ɗaukar alherin naira biyar ya bani, saboda kowa gani yake ni me wadata ne bana buƙata, sedai ma kullum a nema a gurina, idan kuwa kaga anmin kyauta to wani abu ake nema a gurina, Mutum na farko da yayi min kyauta har sau biyu kuma saboda Allah, nagode sosai Yusuf, nasan kana haƙuri Amma ka ƙara zaka ga ribar sa, Widad ta gode da wannan kyautar"

Tabbas ba dan Alhaji Nasir ba, ko duniya yake samu a gidan nan baze sake zuwa ba, da babu abunda ze hana ya miƙa file ɗin aikin a ɗora wani dan ya gaji.

Yusuf bece komai ba, ya jinjinawa Alhaji Nasir kai ya fice, zuciyar sa na ƙuna dan gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun miƙe saboda ɓacin rai.

Alhaji Nasir yayi wa Widad wani irin kallo, ya wuce part ɗinsa da kayan a hannun sa.
Se a lokacin ta sha jinin jikin ta, bin bayan Daddy tayi da sauri zuwa part ɗinsa.

Ramla tace  "Allah ya ƙara, maganin me shishshigi kenan, da haka da haka wataran zata sallameshi kowa ya huta"

Amal tace  "kema kiji da abunda ke damunki mana, aikin banza kawai"

A ɗaki Widad ta riski Mahaifinta, tace "Daddy are you angry?"

Shiru yayi mata yana ƙoƙarin ninke rigunan.

"Daddy am talking to you, why will you be angry? Am I wrong?"

Shiru ya kuma yi bece mata komai ba.

"Daddy magana fa nake maka"

"Me kike so ince miki Widad? Yaron nan yana matuƙar ƙoƙari da haƙurin zama dake, Amma kalli yadda kike treating ɗinsa, yana miki biyayya yadda ya kamata amma bakya gani, can you remember when last someone offer you a gift, for the sake of God? Meye laifin sa dan ya baki wannan kayan, irin wannan rigunan Amminki take sakawa, sunfi mutunci akan wanda ke kike sakawa, bana son takuramiki saboda yanayin halin da kike ciki, Amma ba kya tausayin kanki, meye aibu da wanda yake ƙasan ka ya baka kyauta, dukda muzguna masa da kike da wulaƙanci amma ya miki alheri, meyasa zaki Wulaƙanta shi, Widad ko baki yadda da abunda na gaya miki kwanaki ba? "

Shiri tayi tana nazarin maganganun Mahaifinta.

"baki ga yadda ya fita ransa a ɓace ba? Baki kyauta ba sam"

"to yanzu ni me kake so inyi?"

"ki karɓi wannan kayan kiyi amfani da su"

"Over my death body, gaskiya Daddy bazan iya saka wannan kayan ba"

Daddy ya jinjina kai yace  "As you wish, zanje ganin likita gobe in Allah ya kaimu, sannan baƙonki yana nan zuwa da weekends ɗin nan"

"Waye baƙona kuma?"

"Fahad, mijin da zaki aura!!!"

Widad ji tayi tamkar Daddy ya watsa mata wuta me matuƙar zafi.

(MASHA ALLAH NA KAMMALA JARRABAWA ALHAMDILILLAH, INA GODIYA DA ADDU'OINKU NAJI DAƊI NAGODE SOSAI NA GAMA JARRABAWA YAU ALHAMDILILLAH)

Domin gyara sharhi ko shawara feel free to contact me
Ayshercool
07063065680

                     _*AƘIDATA*_

      
PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends



ELEGANT ONLINE WRITER'S

                          PART1
                              Page 16_17

(Ayimin afuwa jiya nayi mistake ɗin pages)

Ko kallon inda Daddy yake bata kuma yiba ta fice ta bar masa ɗakin.

Komawa ɗakinta tayi, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugu kamar zata fasa ƙirjinta ta fito 'kenan har yanzu Daddy be janye maganar nan ba? Daddy why?'
Tayi maganar da ƙarfi, tana sauke numfashi a hankali ta zube a ƙasan carfet, gaba ɗaya kanta ya kulle ta rasa abunyi, tabbas wannan karon Daddy dagaske yake, idan kuwa har Daddy ya dage a wannan ƙudurin nasa to tabbas zata bijre, koma hakan yayi sanadiyyar ya rasa ta gaba ɗaya, kuma seta shata babban layi tsakanin ta da Bulama.

Ramla tunani take me zata yi wanda zesa a janye maganar Widad da Fahad, ya za'ayi mutumin data daɗe tana tararirayar soyayyar sa lokaci ɗaya a wargaza mata komai, sam hakan bame yuwuwa bane, dole tasan abunyi dan yiwa wannan tufkar hanci.

************************************

Kallo ɗaya zakayi wa iyalan kasan suna cikin farin ciki, gaba ɗaya sun hallara a katafaren falon gabansu shaƙe da nau'ikan Abinci kala kala, kowanne fuskarsa ɗauke da farinciki.

Ramadan yace "Wallahi broz Fahad gaba ɗaya kaima ka zama kamar Bature, kaga yadda skin ɗinka tayi fresh kamar wani jariri"

Alhaji Bulama yace "Wannan Ƙaton ne fatarsa kamar jariri, kai dai Ramadan ka fiye shiririta"

Hajiya Sarah tace "Haba Daddy, ka kalli yadda ya wani murje yayi ƙalau dashi"

Iman tace "Nikam banga abunda ya canza ba sedai yayi haske ya ƙaro iyayi, ko hausarma bata fita sosai se kace Widad"

Ɗan ɓata fuska Hajiya Sarah tayi jin an ambaci Widad.

Alhaji Bulama yace "se suje can su cigaba da gwarancinsu"

Sam Fahad be fahimci abunda mahaifinsa yake nufi ba, haka suka ci gaba da ciye ciyensu suna hira cike da ƙaunar juna.

Yusuf kuwa tunda ya baro falon nan ransa a ɓace kai tsaye gida ya wuce, zuciyar sa nata faman tafasa, tabbas ƙarshen wulaƙanci yau Widad tayi masa, banda dalilin aikin sa da kuma mutuncin mahaifinta da baze sake komawa gidan ba.

Nurat bata da aiki se tunanin Yusuf, ko bacci ta kwanta mafarkinsa take, gaba ɗaya zuciyar ta ta kasa samun nutsuwa, ta kira lambar Yusuf harta gaji, ta koma kiran ta Widad, amma itama bata tafiya, abun duniya duk ya ishe ta.

Tana zaune tana wannan zaman tunanin mahaifinta ya shigo ɗakin ta, da sauri ta miƙe daga kwanciyar da take.
Ya kalle ta yace "ke meya ke damun ki ne?"
Girgiza masa kai tayi tace "bakomai Daddy"
"to naga Maman ki bata nan, gobe in Allah ya kaimu zamuyi baƙi ki gaya mata, za'ayi mana girki bana son na masu aiki fa"

"To zan gaya mata insha Allah"

"shikenan sena dawo"
"Adawo lafiya Daddy"
"Allah yasa"

Gaba ɗaya ɓacin rai ya hana Yusuf bacci, kamar shi dukda yasan ba wata uwace da shi ba amma Widad ta dinga gaya masa wannan baƙaƙen maganganun gaskiya idan ya ƙyaleta tabbas taci bulus.
Tunani ya shiga yi me ze mata wanda ze nuna mata mahimmancin ɗan Adam.
Da ƙyar bacci ya ɗauke shi cike da ɓacin rai.

Da gari ya waye so yayi yaje gurin aiki amma ya fasa, yayi zamansa a gida se bayan azahar sannan yaje gidan.

Nura da Isa se wani kallon banza suke masa, Yusuf bashi da lokacin su dan haka bebi ta kansu ba.

Be daɗe da zuwa ba Alhaji Nasir ya fito, yana ganinsa kamar babu abunda ya faru Yusuf ya miƙe ya nufi inda yake.
Cike da girmamawa kamar kullum suka gaisa, Alhaji Nasir yace "Yusuf kaga yau ma tafiya ta kamani, kar a gaji dani dai ga Amanar tilon 'yata nan, Fahad zezo gurin ta a satin nan Insha Allah, dan Allah a samin ido akan ta, sannan ka cigaba da haƙuri"

Yusuf yace "Insha Allah, Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya"

"Ameen Yusuf"

Ya shiga mota, Nura yaja suka fita.

Larai me aiki ce ta fito ta samu Yusuf tace "kaje inji 'yar masu gida"

Yusuf yace "Ina zuwa"

Yai zaman sa kamar bashi akace ana kira ba, Isa yace "da alama Yusuf ka raina Yarinyar nan, badan kaine ba akwai wanda ya isa yayi mata haka ta ƙyaleshi, turowa fa tayi tana kiran ka, amma ka basar kana shagalinka"

Ko gezau Yusuf beyi ba, balle Ya nuna yasan me Isa yake faɗa.

Isa yace "da kai fa nake magana"

Still be tanka masa ba, Isa yace "eh da alama kaima ta koya maka baƙin halin, kadai bi a hankali tunda kaima ɗan uwa talaka ne, inka ɗau wannan rayuwar ba inda zata kaika"

Yusuf be kula shi ba ya miƙe ya bar gurin.

Yusuf na tafiya sega Abbas yazo, Isa na ganin shi ya washe baki yace "Sani dama kana nan? Kwata kwata wayarka ta dena shiga"

"ina nan wallahi, na koma ƙauye ne, ya kake ya aikin?"

"Alhamdilillah, ya ka baro mutan gidan?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ina Yusuf kuwa?"
Isa ya taɓa baki yace "Yana nan yanzun nan ya shiga cikin gida, gimbiyar masu gida tana kiransa"
"Allah sarki, ina fatan yana aikin sa babu matsala?"
"Eh to yana yi, se shishshigi da zaƙewa, yaga ya samu gurin zama a gurin masu gidan, shine yake ta Wulaƙanta mu gamu gashi amma se yaga dama ze kula mu"

"Hmm ni kaina wannan baƙin halin nasa yana ƙular dani, dama haka yake se kunyi a hankali wasu lokutan bashi da kirki sam wallahi".

Yusuf seda ya ɗan tsorata, ganin Widad ta rame daga jiya zuwa yau, idanunta a kumbure da alama kuka tayi sosai, gaba ɗaya se yaji tausayin ta ya kama shi.

"Gurin Bulama zaka kaini yanzun nan"

Jinjina mata kai yayi, ta miƙa masa jakarta ya karɓa sannan suka fito.

Tunda suka fito Abbas ya ƙura musu ido, se kace mata da miji, tabbas Yusuf ya samu gindin zama yadda yakamata a gidan nan.

Yusuf na ganin Abbas tun daga nesa ya fara murmushi, suna isowa inda su Abbas suke kafin Yusuf yayi magana, Widad ta ƙurawa Abbas ido, shikansa Abbas seda yasha jinin jikin sa.

"Waye wannan?" Widad ta tambayi Isa megadi"

Cikin inda inda Isa yace "Amm... Am. Dama abokina ne, kuma shine wanda ya kawo Yusuf aiki a gidan nan, ina tunanin ma ɗan uwansa ne"

"Kar in ƙara ganin sa a gidan nan, ko a harabar area nan na sake ganinsa zan ɗau matakin da ya dace"

Binta sukayi da kallo, inda sabo Yusuf ya saba da wannan halin nata, dan haja yayiwa Abbas Alama da zasu yi waya.

Abbas ya miƙe cikin mamaki ya bar gidan.

Yusuf dama beyi zaton zata gaya masa dalilin ta na korar Abbas ba, amma abun ya bashi mamaki, seya barshi a matsayin kawai duk cikin hakinta ne na rashin yarda da mutane.

Koda suka iso gidan Bulama, kafin su shiga megadi ya sanar dasu cewar Bulama da shi da iyalansa basa nan sun fita.

Haka Yusuf ya juya akalar motar suka koma gida.

Abbas ba ƙaramin mamaki yayi ba, yaga dai farkon zuwansa gidan daya kawo Yusuf tare suka je, amma yau ta nuna bata sanshi ba wai kar ya ƙara, zuwa gidan.

Kai tsaye Abbas ya ɗakko wayarsa ya kira layin Saleh.

"Hello Saleh kana ina ne?"

"ina gidan gona bakin aiki, meyafaru?"

"ina son ganinka ne"

"ka bari zanzo in same ka a gidanka, karka zo nan babu security"

"shikenan sekazo"

Yusuf Alla Alla yake ya kai Widad gida ya tafi gurin Abbas.

Seda suka je gida yay parking, Widad ta kalle shi tace "Karka bar gidan nan se bayan sallar isha'i"

"Saboda me?" ya tambaye ta

Bata bashi Amsa ba ta fice daga motar ta barshi a gurin, ba ƙaramin haushi yaji ba, yasan dai duk abu ba wani gurin ze kuma kaita ba, Amma tace baze tafi ba, da niyyarsa yayi tafiyar sa amma se ya fasa, haka ya cigaba da zama har se lokacin da tace ya tafi.

Saleh ne zaune shida Abbas a wani ɗan madaidaicin falo, Saleh yace
"Neman me kake min ne haka?"

Abbas yace "dole in neme ka ai, Yusuf se alheri yake samu a wannan aikin da yake, ta sakarmasa kuɗi kawai take sakarmasa, seda nayi dana sanin rashin yin aikin nan da kaina"

Saleh yai murmushi yace "tabbas Widad akwai kyauta ta ban mamaki, Sedai kasan aikin da yake a rayuwar sa a hatsari take ko?"

"Nasani amma babban abunda ya ɗauremin kai shine yau naje gidan gurin sa, Amma tana ganina tace kar in ƙara zuwa ko area gidan"

"zata aikata saboda bata da yadda sam, dan haka bata son baƙuwar fuska, gani take kowa ma cutar da ita zeyi, yanzu ya ake ciki game da binciken da yake yi, naga alamar yaron yasan aikin sa, duk yadda kaso ka daki cikin sa ba ze gaya maka komai ba, na jarraba shi rannan da suka zo tare, Amma naga yana da wayo "

Abbas yace " Hmmm, aiki kam yasan kan aikin sa sosai, dan ina tabbatar maka da yana aikin yadda ya kamata yana tattara abubuwa masu mahimmanci sedai har yanzu ban san meye sakamakon binciken nasa ba"

Saleh ya numfasa yace "yanzu abunda nake so da kai shine, ka kawomin rahoton duk binciken da yayi, ka kawomin file ɗin zan miƙa shi ga wannan mutanen dan su sakarmin ɗan uwana dan ina zargin su suka yi poisoning ɗinsa yake kwance ba lafiya"

Abbas yace "yana na'aikaci ina ma'aikaci tayaya kake tunanin ze yadda ya bani kundin binciken sa?"

"wannan ya rage naka kuma Abbas, ni na gama magana kuma ka saka ido ka cigaba da bibiyar sa dan jin yanayin kusancinsa da ita"

"Shikenan zanyi iya abunda zan iya, Insha Allah zan kawo maka abunda ka buƙata.

Ba ƙaramin haushi Yusuf yaji ba da Widad ta hana shi tafiya da wuri, dan haka se bayan isha'i sannan ya tafi gida, bayan yaje gida yaci Abinci yana shirin kwanciya message ya shigo wayarsa

"HAR YANZU MUNA SANE DA KAI, KUMA ZAMU CIGABA DA BIBIYAR KA HAR SEKA BAMU ABUNDA MUKE SO A HANNUN WIDAD"

Tsaki Yusuf yayai ya ɗanyi shiru yana tunanin wai wani abubne wannan haka da'ake son karɓa a gurin Widad, da har ake masa barazana haka?
Ganin bashi da amsa yasa yai kwanciyarsa.

************************************
"Fahad kasan meyasa na kiraka muyi magana a daidai wannan lokacin?"

Fahad ya girgiza kai yace "a'a Daddy"

Bulama yace "Yawwa, na yanke wani hukunci ne kafin ka dawo, shine nake so ka baani aron hankalin ka da kunnuwan ka da kyau ka saurareni"

"To Daddy ina jinka"

"Kasan Widad ai ko? 'yar gidan Alhaji Nasir daula"?

"Eh Daddy nasani"

"Kasan alaƙar dake tsakanina da mahaifinta ko?"

"Nasani Daddy" Fahad ya bashi amsa

"Masha Allah, Kasancewar ka yaro me biyayya shiyasa na yanke wani hukunci wanda nasan ba zaka bijiremin ba Insha Allah"

"Ina jinka Daddy".

"Kamar yadda kasani, yarinyar nan ta gamu da larurar Ƙwaƙwalwa, ta ɗau wata AƘIDA da wata irin rayuwa ta nayi, ta zaɓi rayuwar kaɗaici wanda hakan ke barazana ga lafiyar ƙwaƙwalrwata, shine muka yabke hukuncin yi mata Aure nida mahaifinta, koda Allah zesa a dace a samo kan hankalin ta"

Fahad yace "to ai Daddy ni banga meye nawa a ciki ba"

"Fahad kai muka yanke shawarar zaka auri Widad"

A razane Fahad ya kalli Mahaifinsa yace "Kamar ya ni Daddy, kawai se in auri mahaukaciya kaifa kace bata da hankali ta yaya zan Aure ta?"

"ta yadda na gaya maka mana, aiba hauka take tuburan ba se lokaci lokaci yake tashi, dan haka umarni nake baka ba shawara ba, idan bamu haɗu an temaki yarinyar nan ba waze aure ta da wannan larurar?"

"Amma Daddy a rasa wanda za'a bawa seni? Ina da wadda nake so meyasa za'amin haka? Ta yaya za'a yanke min hukuncin yarinyar da zan aura ba tare da izinina ba"

Cikin tsawa Bulama yace "rufemin baki, na gaya maka wannan umarnina ne, kuma dole kabi gobe in Allah ya kaimu zakaje ku gaisa da ita, kuma wallahi naji wani abu daga gareka wanda be gamshe ni ba, kasan halina sakarai kawai"

A hasale Fahad ya tashi ya bar falon mahaifinsa, ɗakin mahaifiyarsa ya tafi yana kumbura fuska.

"lafiya ka shigomin ɗaki ba ko sallama kana ta haɗe rai kamar tsohon raƙumi?"

"Mumsy kina gidan nan, kina raye za'ayi min Auren dole? Kamarni ta yaya za'a auramin mahaukaciya?"

Ajiyar zuciya tayi tace "Fahad this is out of my control, I did my best to destroy this matter but is beyond my control, ba yadda banyi da mahaifinka ba amma fafur yaƙi, ya zanyi sedai kayi haƙuri"

"Au Hakama zaki ce? Wallahi se yarinyar nan tayi dana sanin Aure na, sena mata wulaƙancin daba'a taɓa yi mata ba se naci mutuncin ta, zata gane kuskurenta"

"Kai Fahad ka shiga hankalin ka, 'yar gidan Daula ce fa, ita zaka ciwa mutuncin? Amma kasan me ci mata mutunci ke nufi ko?"

"ko' yar gidan bushashace ba Daula ba ba ruwana wallahi"

"shikenan kaje kayi abunda ka ga dama kaida ubanka ba me ɗagamin hankali wallahi"

Fuuuu Fahad ya fice ya bar ɗakin yana tsaki

Da safe Yusuf yanata shiri, dan yau gurin aiki yake son zuwa dole yana son ganin Yallaɓai Suleiman, Amma message ya shigo wayar sa.

"ka tabattar ƙarfe takwas tayi maka a gidanmu, zakamin aiki yau"

Yana ganin message ɗin yasan daga Widad ne, haushi ne ya kama shi gaba ɗaya bashi da lokacin kansa sena wannan fitsararriyar yarinyar.

Haka ya shirya a gaggauce ya tafi gidansu Widad, mutan gidan ko tashi daga bacci basu yi ba, tsabar takura irin ta Widad da son nuna isarra yasa take masa wannan ikon.

Wani ɗan ƙaramin lambu dake gidan Yusuf ya tafi yai zaman sa, yana kallon shuke shuke da tsuntsayen dake gurin.

Jin tsayuwar mutum yayi a bayan sa dan haka da sauri ya juyo.
Amal ce tsaye a bakin lambun tana ƙare masa kallo "barka da Safiya Yusuf"

"Yawwa barka" ya faɗa a taƙaice

"Yusuf wai ya naga kana wani baya baya dani? Dan Allah kayi haƙuri da abunda ya faru, wallahi ina matuƙar kishin ka ne"

"Amal dan Allah kiyi haƙuri, ni bana son abunda zesa ki jamin matsala, ki ƙyaleni dan Allah"

"Idan kaga na ƙyaleka to tabbas ɗayan mu ruhinsa ya rabu da gangar jikinsa, ni matsala duk girmanta duk ƙanƙantar ta bana gudun ta, indai akan biyan buƙata tane, kalleni Yusuf me na rasa? Wace tawaye Allah yayimin da ban kai ka kalleni ka karɓi soyayya ta ba, kana ganin irin mazan da suke sintiri a gidan nan da sunan suna sona, Amma na ajiye class ɗina na ajesu a gefe nace kai nake so, me zesa kace baka sona"

"Saboda bana Soyayya, bata gabana babu ita a tsarina, dan Allah ki ƙyaleni"

"ƙarya kake Yusuf kana Soyayya, koma baka yi zaka fara a kaina bazan taɓa ƙyaleka ba, zan cigaba da bibiyar ka sena hanaka jin daɗi muddin baka amince da soyayya ta ba "

"Masoyiyar gaskiya ba zata taɓa faɗar haka ba, ke ba abun yadda bace dan haka bazan taɓa yadda da wannan shirmen ba"

"Yusuf ko nawa kake so zan mallaka maka, in har zaka yadda ka karɓi soyayya ta"

"Shi son gaskiya tsada ne dashi, kuɗi komai yawan su basa siyansa, dan haka Allah be baki arziƙin da zaki siyi soyayya a gurin Yusuf ba"

Yana gama maganar ya juya ya fice daga lambun yana mamakin wannan naci irin na Amal.

************************************
Ramla ce kwance hannunta riƙe da waya tana magana a hankali cikin iyayi

"Abun ƙauna ta, yau kwananka huɗu da dawowa Nigeria, yakamata ace kazo na ganka fa, Allah badan inajin nauyi ba da tuni ni zanzo inda kake in ganka"

Daga can ɓangaren Fahad yace "Am Sorry beb, ina cikin damuwa ne gidan naku ne gaba ɗaya bana son zuwa, Ramla wai Daddy ze haɗani Aure da wata mahaukaciya a gidan ku, Ramlah kamarni za'ayiwa Auren dole? Auren ma da mahaukaciya, kuma Daddy se masifa yake wai se nazo mun gaisa da ita"

"Fahad nasan maganar nan tun kafin ka dawo, ban gaya maka ba saboda bana son ɓacin ranka, Amma ina cikin damuwa Fahad you know I love you" tai maganar cikin damuwa

"easy baby, ki kwantar da hankalinki, idan nazo se nayiwa yarinyar nan rashin mutunci, ni bazan aure ta ba dan ba sonta nake ba, bazan taɓa yadda da Auren nan ba, naga Daddy ya fara fushi, in anjima zan shigo gidan naku in ganta, Amma ni ke zanzo gani Beb"

Murmushi tayi tace "Ohh my God, amma naji daɗi Fahad seka zo".

Ta kashe wayar tare da yin wani tsallen murna.

************************************

Se ƙarfe sha ɗaya na safe tayi miƙa, ta farka daga nannauyan baccin da take, ta sakko daga kan gadonta magen ta yana biye da ita.
Corridor ɗin ɗakin ta tabi wanda ze sada ta da barandar benen, miƙa ta sake yi tana ambaton sunan Allah tare da shaƙar sassanyar isakar dake kaɗawa, haka nan take jin wai irin nishaɗi da bata san dalilin jinsa ba, tsyawa tayi tana kallon komai dake harabar gidan.

Yusuf ji yayi kamar ana kallon sa dan haka ya ɗaga kansa sama, ai kuwa karaf idanunsa suka sauka a cikin nata, alama tayi masa da hannu ya zo, dan haka ya miƙe ya tafi.

Dukda yana jin haushin abunda tayi masa akan kayan daya bata, amma yau yaga fuskarta ba yabo ba fallasa haka nan yaji hakan yayi masa daɗi.
A ɗakinta ya sameta, tana tsaye a gaban madubi ta janyo drower mudubin tana ƙoƙarin ɗakko wani abu.

Idan kunnuwan ta ba ƙarya suke gaya mata ba tabbas Yusuf cewa yayi "Good morning daughter" kamar yadda Daddyn ta yakan faɗa, shiru tayi ta cigaba da duba abunda take nema tsawon wasu daƙiƙu, sannan ta ɗago ta kalle shi tace "Roux taƙi cin komai tun jiya, na rasa meke damunta na bata Madara taƙi sha, ka siyo mata ko cabin ne, in gani in zata ci ban san me yake damunta ba" (wato magenta)

Haushi ne ya kama Yusuf, saboda tsabar wulaƙanci mage ze fita siyowa Abinci.
Bece komai ba ya juya ya fita yana ƙoƙarin ɓoye jin haushin sa.

Yana tafiya ya tuna da Message ɗin da'aka turomasa da daddare dan haka ya samu guri ya kira Oga Suleiman.

Bayan sun gaisa Yusuf yace "Yallaɓai na so in shigo yau in nuna maka report ɗina amma abu ya gagara, Wannan rigimammiyar ta kasa ta tsare ban samu na shigo ba"

Suleiman yace "Aikam dan har na fara ƙorafin, yanzu me ake ciki?"

"Yallaɓai akwai abubuwa na ban mamaki a binciken nan, zan turomaka report ɗin ta Email ɗinka ka duba, Yallaɓai case ɗin akwai sa hannun mutanen dan ban zata ba, sannan karo na biyu ana min barazana wanda ya ƙara tabattar da tabbas ana bibiyar yarinyar nan ana son karɓar wani abu a hannunta wanda ni kaina ban san menene ba"

"Masha Allah, har kayi aiki haka Yusuf? Ka turo zan duba in Allah ya yadda inda yuwuwa zan miƙa report ɗin naka gaba, nasan zaka iya dama bazan can zaka daga kan aikin ba"

"Yallaɓai da karɓar aikin za kayi?"

"karka damu da wannan, ka turomin zan duba dan daga sama ana tambaya ta ina muka tsaya a binciken?"

Yusuf yace "Amma Yallaɓai wai wa yasa ayi wannan aikin ne? Waye yace ayi binciken?"

"Yusuf nima ban saniba, daga sama aka bada order ayi wannan aikin"

"Yallaɓai ya kamata kasan gawa zaka bada aikin, dan abun akwai sarƙaƙiya"

"Karka damu Yusuf, komai ze tafi daidai insha Allah, kamar yadda kace ana maka barazana, duk lokacin da ka buƙaci temako kayi magana, sannan ka kasance cikin shiri ka dinga yawo da makaminka"
"Ina lura sosai Yallaɓai, Allah yayi mana jagora gaba ɗaya"

"Ameen Yusuf Allah ya tsare"

Yusuf seda ya tsaya ya turawa Suleiman aikin sannan ya tafi.

Koda Yusuf ya dawo daga aiken yiwa mage siyayya, ya tarar da uwar ɗakinsa ta fito daga wanka, pink ɗin rigar wanka ce a jikin ta, ta naɗe gashin kanta da towel shima pink.

Zare towel ɗin dake kanta tayi, gashin ta ya zuba a kan kafaɗunta, Satar kallon ta Yusuf yake, tabbas Allah yayi mata halitta mekyau, tana da kyau sosai ga dogon gashi, Yarinya ce sedai izza da gadara, tana kallon Ya dawo amma taƙi kula shi.

Wani ƙaramin plate ta ɗakko ta miƙawa Yusuf tace "ka sa mata cabin ɗin anan, ga madara ka haɗa mata dashi"

Yusuf yai shiru yana sauraren ikon Allah, yanaji yana gani aka sashi haɗawa mage Abinci.

Still dai magen bataci ba se kwanciya da take.

Cike da damuwa Widad ta kalli Yusuf tace "taƙi cin wannan ma, inaga bata da lafiya idan akwai wani private veterinary se mu kaita" ta faɗa cike da damuwa tana sake shafa magen, hakan ya ƙara fito da tsantsar yarintar ta.

"waye ze buɗewa wani private veterinary? Babu wani private veterinary dana sani nidai, yunwa take ji kawai bata ƙoshi ne"

"kamarya? Ina bata Abinci sosai fa"

"Ai kema ba Abinci kike ciba balle magen, kullum abu ɗaya ai dole ta gaji ta dena ci"

Cikin damuwa tace "to me zan dinga bata?"

"Abinci me nauyi na hausawa, amma kullum daga popcorn se madara ai dole ta mutu"
Da sauri ta kalli Yusuf tana girgiza kai tace
"A'a ni bana so ta mutu ina sonta fa"

Gaba ɗaya yau Yusuf cike yake da mamakin yadda take masa magana cikin nutsuwa ba izza, yasan kuma saboda magen ne, dan ya lura tana tausayin dabbobi fiye da yadda take tausayin ɗan Adam, tana matuƙar ƙaunar dabbobi Yusuf a ransa yace "ta wani fannin rayuwar turai ba tayi ba"

"to muke rasa 'yan uwanmu mutane ma balle dabba, idan ta mutu seki ɗakko wata"

"Ni nafison wannan gaskiya, tun ire iren magunan Ammi ne, idan ta mutu zan shiga damuwa"

Shiru yayi yana kallon Widad data sunkuyar da kanta tana shafa jikin magen, magen tayi lamo a jikinta, gashin kanta har rufe mata fuska yake, Yusuf yana mamakin wannan dogon gashin na kan Widad dan har yanzu yana tantama idan nata ne.

A hankali ya matso daf da ita ya shafa jikin magen dake hannun ta yace "Allah ya bata lafiya, don't worry Madam zata warke Insha Allah"

Widad ta jinjina kai, tare da jin ƙaruwar bugun zuciyar ta kasancewar yadda suke daf da juna, ta ɗago idonta ta kalle shi tace "da ina so mu fita zanje Saloon, Amma zan zauna inga yadda jikin nata ze kasance ko zuwa yamma ne semu tafi"

Yusuf ya ɗan ƙura mata ido sannan a hankali yace "As you wish your majesty" ji tayi tsigar jikin ta tashi, wanda ta rasa dalilin jin hakan, haɗe rai tayi tace
"karka sake ka fita kaje ko'ina idan ba nina baka izini ba, ka zauna zuwa la'asar insha Allah zamu fita"
Murmushi yayi mata tare da ɗan duƙawa cikin girmamawa yace "Considered it done Gimbiyar Daddy"

Ya yunƙura ze miƙe Amal ta shigo hannun ta ɗauke da waya, turus tayi tana binsu da kallo, yayin da taji wani abu tundaga ƙafarta zuwa ƙirjinta ya to kare mata wuya.

Da ƙyar ta miƙawa Widad waya tace "gashi Daddy zeyi magana dake"
Widad bata kalle ta ba, bata bata amsa ba ta kalli Yusuf tace "bani wayata akan mirror"
Amal bata kuma cewa komai ba ta juya ta tafi a hasale.

Widad ta karɓi wayar ta kira lambar Daddy, ya ɗaga suka gaisa yace "Lovely meyasa wayarki bata shiga?"

"Jinyar Roux nake, bata da lafiya"

"To Allah ya bata lafiya, dama munyi waya da Daddynki yau baƙonki zezo"

"waye baƙona?"

"Fahad mana, zezo ya ganki ku gaisa dan Allah Lovely banda wulaƙanci ko makamancin haka, shima ɗanuwankine Yayan Ramadan ne, yana nan tafe Anjima Insha Allah"
Nan da nan dukkan annurin fuskarta ya ɗauke ta dire wayar tace

"Ina nan ina jiran zuwan sa, yazo ya sami Widad Nasir Daula, yazo yaga mahaukaciyar da'ake shirin ƙaƙaba masa"

Ayshercool
07063065680

                     _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 18



Binta da Kallo Yusuf yayi, ganin yadda ta canza lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke, tabbas akwai drama yau.

"Jeka anjima zamu fita" ta faɗa ba tare da ta kalli Yusuf ba

Miƙewa yayi ya fito daga ɗakin ya nufi hanyar fita, ba zato Amal tasha gabansa wanda ya tilasta masa tsayawa.

"Yusuf ka fara ƙoƙarin tsallake iyaka, Yusuf meyasa baka tsoron Allah ka dinga nuna kai na Allah ne amma baka kyautawa rayuwarka, Yusuf kai mugune mara tausayi baka da tausayi baka tausayina, ko kaɗan soyayyata bata da daraja a idonka, na rasa meye a tsakaninka da Widad, wallahi akan Son da nake maka banƙi komai ze faru ya faru ba, wallahi akanka koni ko Widad "

Girgiza kai Yusuf yayi yace " keya dace a nemawa maganin mahaukata ai, nayi iya ƙoƙarina in ganar dake amma kin kasa ganewa, bana Soyayya bani da ra'ayinki, ba abunda ya kawoni nan kenan ba, ki ƙyale rayuwar Yusuf ta huta, tun kafin in nuna miki ainihin kalata na gaya miki"

"Haka kace?"

"Eh haka nace, ko baki da kunne ne?"

"bayan ƙalubalen dake gabanka saboda Kasancewar ka da wannan mahaukaciyar, ka shirya ƙalubalen da zaka fuskanta daga gareni"

"duk wanda ya dogara da Allah, to ya isar masa"

Yusuf ya bata amsa yasa kai ya fice, ya barta tana mamakin wannan taurin kai irin na Yusuf.

Bayan Suleiman ya gama nazarin abunda Yusuf ya tura masa, yayi mamakin jajircewa da kuma ƙoƙarin da yayi, tabbas Yusuf jajirtacce ne me kuma hikima da iya aiki, amma meye dalilin da yasa Abbas yakeson lallai a ƙwace aiki a bashi? Lallai akwai wata a ƙasa Abbas yana da fuska biyu.

Yusuf yana nan zaune yana ganin yadda aketa aiken su Murtalah, anata shirye shirye da alama akwai baƙon da gidan zasu tara yau, shi dai yana guri ɗaya nasa ido.

Ƙarfe biyu na rana Yusuf ya dawo daga masallaci sallar Azahar, wata dalleliyar mota ta shigo gidan, wani matashi ne ya fito daga motar, jikinsa sanye da ƙananan kaya kallo ɗaya zaka masa kasan ɗan hutune, ya ɗaga kai ya ƙarewa gidan kallo tsaf, su Isa mai gadi suna gaisheshi yana ɗaga musu hannu ba tare da ya amsa ba.

Shidai Yusuf be kula shi ba, sema ɗauke kai da yayi kamar bega Matashin ba, ba zato suka jiyo muryar Ramla ta taho da gudu tana faɗin "Oyoyo my heart beat"
Ba kunya suka rungume juna a gurin.

Fahad yace  "I miss you so much Baby"

"I miss you too mine" Fahad yayi kissing ɗinta a forehead yace 
"kin ƙara kyau my Ramlat"

"Kyau ai kaine ka ƙara kyau, mutanen Amurka muje daga ciki ko"

Suka shige hannunsu saƙale da juna.

Nura direba yayi tsaki yace  "ƙaryar banza burodi a lefe, waisu a dole turawa ba kunya taje ta rungume ƙasurgumin gaddi tana ce masa Baby tir da wannan hali"

Shidai Yusuf bece musu komai ba suka ci gaba da gulmarsu.

A babban falon dake ɓangaren Hajiya Halima aka sauki Fahad, suka dinga hira yana basu labarin Anwar shima ya kusa dawowa.

Fahad ya ɗan ɓata fuska yace  "Hajiya wai ina Yarinyar take ne? Ance inzo in ganta karta ƙullamin wani sharrin a gurin father ta jamin magana, danni sam ba'a kyautamin ba da'akace zan Aureta"

Ɓata rai Ramla tayi ta miƙe ta bar falon, Hajiya Halima tace  "Aikuwa dai an gama da kai, dan yarinya ce ba tarbiyya ga kuma uwa uba hauka"

"wallahi Hajiya na rasa wani irin tunani Daddy yayi haka, da yasa yake son illata rayuwa ta, nazo ne dai kar'ace banzoba amma sena tabattar da na mata rashin mutunci yadda ko ganina tayi ba zata nuna ta sanni ba"

Amal ta kalleshi a yatsine, sam Fahad haushi yake bata yana ta wani iyayi shi lallai ya dawo daga Turai, indai Widad ce ze gane kurensa ne.

Ba kunya Fahad ya miƙe yace  "Hajiya bari inje gurin Ramla, naga tayi fushi"

"Shikenan kunfi kusa ai"

A ɗakinta ya sameta tayi kicin kicin da rai, ta haɗe fuska, ya zauna kusa da ita ya janyota jikinsa yace  "haba Baby, meye abun damuwa nifa danke nazo gidan nan, ba dan wata banza ba meye na ɓata rai, ki tsaya kiga matakin da zan ɗauka yau akanta"

"Fahad inajin tsaro fa, su Daddy suna san Auren nan naku, zasu iya tursasa maka fa"

"waye ya gaya miki? Kamarni aina wuce ajin amin auren dole, calm down Baby" ya faɗa yana jan hancinta

Murmushi Tayi tace  "bari in shirya maka Abinci a dining, na maka girki"

Kafin yayi magana wayarsa ta fara ringing yace "excuse me Daddy ne"

Ya ɗaga wayar yasa a kunnensa yace  "hello Daddy"

"Fahad kaje gurin nata kuwa?"

"Amm.. Eh ina gidan amma ban ganta ba"

"to ka tsaya ku gaisa, sannan yarinyar nan ka bita a hankali bata da cikakkiyar lafiya, kabi a sannu ka kwantar mata da hankali"

Tura baki Fahada yayi yace  "Haba Daddy sekace uwata, yarinyar ma ashe mahaukaciya ce"

"ba zakayi ba kenan?

" Naji zanyi "

" idan naji wani abu na rashin kyautawa daga ɓangarenka sena saɓa maka, shashasha wanda be san halacci ba, aiko wani kaga ze Wulaƙanta 'yar Nasir Daula kai me tare matane"
Bulama yayiwa Fahad tatas sannan ya kashe wayar

Fahad yace  "kar wannan abun ya ɗaga miki hankali kinji babyna, ina tare dake, nasan matakin da zan ɗauka"

Ta jinjina masa kai suka fito babban falo, Fahad yace  "kiramin ita".
Ramla ta nufi part ɗin Widad, a falonta ta tarar da ita tana kwance a ƙasa ta ɗora ƙafafunta akan kujera, mageneta na kan cikinta a kwance, itakuma tana danna waya.

Ramlah tace "Fahad yazo, yana falo yana jiranki"

Ai kamar da kujerun gurin Ramla ke magana ba da Widad ba, dan ko motsi ba tayi ba.

"Magana fa nake miki"

"And then? Ko bayan hauka kuma inada larurar kurmanta ne? Kinyi magan na jiki kin cigaba da tsayawa a kaina, ki matsa daga kaina"

"Amma se ki bani amsa ai, tunda keba kurma bace"

Miƙewa Zaune Widad tayi tace barmin falo.

"Amma...

" ki fice nace, ko Bulama ne yazo da kansa be isa ya tursasani in saurare shiba, kije ki gaya masa ya cigaba da jira idan ze iya daga nan zuwa lokacin da zan fito, idan baze iyaba ze iya komawa ya tambayi Bulama tsarukana, idan ya shirya ɗauka ya sake dawowa, fita ki barmin ɗakina"

Buɗe baki Ramla tayi tabi Widad da kallo, wato ita kullum rashin mutuncinta ƙara ta'azzara yake, ina ita ina zuwa ta Sanarwa da Fahad wannan baƙin saƙo, mussman shi dabe san kan Gimbiyar ba.

Ramla ta juya ta fice ta koma main falo tace  "Baby naje yanzu ta tashi daga bacci zata shirya ta fito"

Ramla ta zauna a kusa da Fahad suka shiga hirarsu, tun Fahad yana tsammanin fitowar Widad harya fara ƙulewa.

"Ramlah wai yarinyar nan ba zata fito bane?"

"Fahad baka ga komai ba, indai akan wannan Yarinyar ne, idan ka kuskura ka aureta taka ta ƙare wallahi"

"zan saita mata zama kuwa, dan nafi ƙarfin wata banza ta Wulaƙanta ni, bari inje akwai wani friend ɗina a quarters ɗin nan, inaso mu gaisa ina dawowa"

"to ka fara cin Abincin mana"

"karki damu yanzu zanje in dawo"

Ramlah ta rakashi har gaban motarsa, kallo ɗaya Yusuf yayi musu ya ɗauke kai, Fahad yace  "Baby wai waye wannan ne?"

Yai maganar yana nuna Yusuf, yamutsa fuska tayi tace  "Direban wannan sakaryar ce"

"yanzu wannan ne direba?"

"direba ne, sedai ya samu gindin zama fiye da duk wani me aiki a gidan nan, shiyasa har wani jin kansa yake"

"ku kuka ƙyaleshi baku saita masa zama ba"

"ni yanzu ba shine a gabana ba, kaje kayi sauri ka dawo kaci Abinci"

Suka yi sallama Fahad ya tafi, se bayan ƙarfe huɗu Yusuf yaga message ɗin Widad, ya miƙe ya shiga part ɗinta.

Yau dogon skirt ne a jikinta baƙi, da wata riga me dogon hannu ta ɗora ɗan ƙaramin veil akanta, tayi kyau sosai kayan sun zauna cif a jikinta sedai ana ganin duk wani shape na jikinta.

Tunda Yusuf ya shigo ba tayi magana ba, se sabgar gabanta take yi.

"Ya jikin magenki?" ya tambaye ta

Abunda Yusuf ya faɗa ne yasa ta ɗagowa da sauri tace  "i think she got better now, she's able to play"

"Allah ya bata lafiya, na ɗauka mutuwa zata yi ashe da sauran kwananta a gaba"

Harar Yusuf tayi ta ɗau jakarta tayi waje, binta yake a hankali baya sauri yana tafiya kamsr kazar da ƙwai ya fashewa a ciki , ta juyo ta kalle shi tace  "wannan wace irin tafiya ce kuma?"

"Nifa gaskiya Yunwa nake ji, tun safe ban kuma cin komai ba, kuma kince kar inje ko ina ban samu na fita naci Abinci ba"

Hararasa tayi tai gaba abunta, suna fitowa falo taga an shaƙe kan dining da Kulolin Abinci, wani murmushi tayi ta kalli Yusuf tace  "jirani anan"
Ta juya ta koma part ɗinta, fitowa tayi hannunta ɗauke da magenta ta nufi dining.

Alama ta yiwa Yusuf da hannu yaje, ya nufi kan haɗaɗɗen dining ɗin da'aka shaƙe da kayan Abinci.

Tai masa alama da ya zauna, yaja kujera ya zauna tace  "buɗe duk abunda kake so a gurin nan kaci"
Kallonta yay yace  "Amma ranki ya daɗe, naga kamar baƙo aka shiryawa teburin

" bana son musu ko jayayya, umarni na baka ba shawararka nake nema ba" ta faɗa cikin faɗa da bada umarni.

Yusuf ya shiga buɗe Kulolin, Abinci ne kala kala kamar ba'asan zafin nema ba, yasan duk tsiya wanda aka shiryawa Abincin baze iya cinyewa ba.

Widad ta zuba kifi akan plate  ta miƙawa magenta, Taja plate itama ta ɗiba ta zuba, dama Yusuf yunwa yake ji ga Abinci yayi daɗi nan ya dinga zurawa
(samun guri direba a dining 🤣🤣🤣)

Ramla ce ta fito itada Amal suna magana, me zasu gani Widad da mage ga direbanta suna cin Abincin da'aka shirya karɓar baƙon Ramla sannan baƙon Widad, Amal tayi saroro tana kallon Ramla.

A fusace Ramla ta ƙarasa dining ɗin kamarta fashe da kuka tace  "Widad wane irin wulaƙanci ne wannan, ta yaya za'ayiwa baƙo girki ki zauna kina ci naga dai idan munyi Abinci ba ci kike ba, dan kawai ki muzgunamin kika yi haka? Saboda wulaƙanci kuma ace harda direbanki saboda tsabar tozarci"

Shidai Yusuf bece komai ba, Widad cikin ko in kula tace  "Ramla me direban nan nawa yayi miki ne haka? Naga kuna takun saƙa sosai dashi, kina yawan manta wani abu Ramla, duk wanda yake aiki a ƙarƙashina matsayinsa ɗaya da duk wanda yake zaune a gidan nan ƙarƙashin kulawa ta, dan haka babu laifi dan na bashi Abinci ko?"

Cike da ɓacin rai Ramlah tace "Amma fa baƙo nayiwa, ta yaya zaki min haka? Ina laifin kice inda saura in zuba masa"

Widad tace "waini wannan baƙon gurina yazo ko gurinki?"

Ras gaban Ramla ya faɗi jin tambayar da Widad tayi mata,
"naga alamar gurinmu yazo nida ke, nasan kina tunanin me zakice masa ne, idan baki da abunda zaki gaya masa kice kinyi masa girki, 'yar masu gida tayi yadda take so dashi"

Hajiya Halima da ta fito ta riski rigimar tace  "Amma Widad baki kyauta ba, ya za' ayi kidinga nuna direba yafi 'yan gida"

"Ni bana abu dan in kyauta dama, bana abu dan in birge kowa, muddin zan cigaba da saka doka ana watsi da ita nikuma zan cigaba da ɗaukar matakin daya dace, if i can recall a falon nan nayi kashedi akan a dinga bawa direbana Abinci, akayi fatali da dokar aka barshi da yunwa tun safe, nayi abunda ya dace ne, ga ragowa nan mun bari idan baƙon naki yana buƙata seya ci dan naga ƙirarsa ta mayuntace dama kamar baya ƙoshi"

Tai maganar tana kallon Ramla, tare da goge hannunta da tissue.
Da gudu Ramla ta bar falon tana kuka, ita kanta Amal ba taji daɗin abunda Widad tayi ba taji haushin hakan.

Yayi parking ɗin motarsa a harabar gidan ya fito daga motar, yana rufe motar tare da amsa waya, kamar an ce ya ɗaga kai ya hangota tana fitowa, fara ce sosai fari me ɗaukar ido, tana da matsakaicin tsayi sannan tana da shape me kyau.

Tabbas idan ba gizo idonsa ke masa ba wannan itace Yarinyar da Anwar yake kallo a hoto yana nuna masa, kenan itace Widad ɗin daza'a haɗa shi Aure da ita? '

Cigaba da Ƙarasowa Widad tayi, Yusuf na bayanta da jakarta a hannunsa, tana kallon Fahad suka zo zata wuce shi
"Widad Nasir Daula" Fahad ya kira sunanta.

Ta tsaya cak bata juyoba tace  "Fahad Bulama"

"Amma kin san gurinki nazo kina kallona zaki wuce ki tafi"

A hankali ta juyo cike da izzarta ta ban mamaki, ta ƙare masa kallo sannan tace  "banyi tsammanin kaine Fahad ɗinba ai, na ambaci sunan ne dan tabattar da kai ɗinne ko ba kaiba, dan abun da mamaki ace kaine Fahad ɗin, ina jinka faɗi abunda ke tafe da kai"

Fahad ya jinjina kai yace "tun ɗazu nake gidan nan ina jiranki, meze hana mu shiga daga ciki mu samu guri mu zauna se muyi magana"

"bani da wannan lokacin, yi maganar ka anan inajinka" ta faɗa tana kallon Idon Fahad.

Fahad be taɓa zaton haka Widad take ba, ta kai mace har mace sedai tana da girman kai da izza.

Ya kalli Yusuf yace  "Amm ko zaka iya bamu guri, zamuyi magana"

"Ko da Bulama zanyi magana agabansa ake yi, dan haka cigaba da maganar ka" ta faɗa cikin isa

"Amma kin san Aure zamuyi, meyasa zaki dinga gayamin magana haka ba respect, har ki dinga kiran sunan mahaifina kai tsaye"

"Anƙi ayi respecting ɗin naka, Babana ma ina faɗar sunansa balle wani Bulama, kai a tunaninka  kai namijin daze tunkareni a matsayin wadda ze aurane?, ɗan sake kallon kanka mana sannan ka kalli da wadda kake magana kasan niba ajinka bace, haka Bulaman be gaya maka yadda mukayi da shi bane? Bana soyayya ban yadda da ita ba kuna ba zanyi Aure ba, ana ƙoƙarin cusamin kaine kawai kuma bani da ra'ayin Auren namiji irinka, dama ka kai Namiji ne zan iya maleji, amma sam baka da ƙira da zatin da za'a kalleka a kiraka Namiji balle ace mijin Widad, ka sani koda ace Widad nada ra'ayin Aure bazan taɓa zaɓarka a matsayin miji ba, banga alamar nagarta da kamala a tare da kai ba, idan kana da zuciya kaje ka gayawa Babana Bulama baka son haɗin Auren nan, 'yar tasa bata sonka, in baka da ita kuma kace masa kana son Auren kaga yadda zamu ƙareta da kai "

Aiba Fahad ba hatta Yusuf jikinsa yayi sanyi da wannan mummunan cin zarafi da'akayi wa Fahad, koba komai ɗan uwansa ne namiji.

Gaba ɗaya Fahad kasa magana yayi, be taɓa tunanin haka Yarinyar nan take ba, duk wadda za'ayi sedai ayi amma seya auri Widad, sedai hakan yayi sanadiyyar ɓatawarsa da Anwar, ze tabbatarwa da Widad shi Namiji ne, Namijin ma irin wanda kowace mace keda burin samu, be tsaya ba ya shige motarsa ya fice.

Yusuf yana diving ya kalli Widad data cika tayi fam yace  "Madam amma kamar abunda kikayi wa wannan bawan Allah be dace ba, bakya tunanin ya Alhaji zeji idan yaji labarin abunda kika yi, baki kyauta ba

"Yoseef!!!"  karo na farko da Widad ta kira sunansa cike da gargaɗi, koda wasa bata taɓa attempting kiran sunansa ba, danshi be zaci tasan sunan nasa bama, sannan yadda ta faɗi sunan nasa yasha banban da yadda ake kiran sunan nasa, dukda Wasu lokutan hausa bata isheta ba, idan ta faɗi wani abun yasha banban da yadda ake faɗa.

"karka kusakura in dawo kanka, meyasa kake son shiga rayuwata, ban taɓa ganin mutumin da nake ɗagawa ƙafa kamar kai ba, shiumrun da nake maka Albarkacin mahaifina kakeci, kar in ƙara yin abu kace zaka yi challenging ɗina, duk abunda kaga nayi inada dalili karka ƙara challenging ɗina if not i will teach you a lesson you never forget "

Tai maganar a matuƙar fusace cike da gargaɗi.

" Allah ya huci zuciyarki, Allah ya baki haƙuri insha Allah ba zan sake ba"

Ya kaita gurin saloon kaman yadda ta buƙata.

Ramlah tayi kuka sosai akan wannan wulaƙanci da Widad tayi mata, seda idanunta sukayi jawur saboda kuka, ƙanwar bayanta dan kawai suna zaune a gidansu ake musu wannan wulaƙancin haka.
Mummy ta tako tazo gaban gadon Ramla ta zauna ta dafata tace  "Am sorry daughter nasan....

"Mummy dan Allah ki ƙyaleni wallahi wannan karon sena ɗau mataki, haba abun ya isa haka wace irin rayuwace wannan muke a gidan nan se kace zamanin Bayi, wallahi sena ɗau matakin daya dace"

"A'a Ramla tynda kikaga na haƙura ban ɗau mataki ba kema haƙuri zakiyi, karki ja mana Asara goma da Ashirin, kin san taɓa wannan yarinyar dai dai yake da kawo ƙarshenmu a gidan nan"

"Niba ita zan taɓa ba, wannan sakaran zan nunawa kuskurensa, se yayi dana sanin zuwa gidan nan, zega abunda zan masa"

******************************

Alhaji Munir, Musa, Haruna se kuma Sale ne zaune a katafaren Falon suna tattaunawa, kana ganin fuskokinsu zaka san abunda suke tattaunawar yana da matuƙar mahimmanci a gurinsu.

Nurat ce ta shigo falon bakinta ɗauke da Sallama tana ɗauke da manyan kuloli a hannunta.

Gaba ɗaya suka bita da ido, kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon ta durƙusa tana gaishesu, Amsawa sukayi gaba ɗaya Alhaji Munir yace  "wai yanzu Nurat ce ta girma haka, gaskiya babu zumunci yakamata ace yaran nan suna zumunci suna a tsakaninsu"

Alhaji Haruna yace  "gaskiya kam danni banda yanzu ma ban santa ba"

Nan sukayi ta surutunsu, yayin da Saleh yake gefe yaƙi cewa komai, Nurat ta gana hada hadar kawo musu Abinci ta juya bar falon.

"Wai kai Saleh bazaka saki jiki damu bane? Akwai fa riba a harƙallar nan" cewar Alhaji Musa

"Niba ribar ce a gabana ba ɗan uwana ne a gabana, yana gadon Asibiti kunsa an bashi guba ku kuma kuna nan kuna cin Abinci"

Alhaji Haruna yace  "to kuka kake so muyi? Wallahi idan asirinmu ya tonu dagamu harshi sedai wasu bamu ba danme zamu bari ya fallasamu"

"shikenan a rayuwa kenan kowa kansa ya sani"

"ƙwarai kuwa ka bari harƙallar nan ta faɗa, idan ta faɗa ka samu kasanka seka fiddashi"

Alhaji Musa yace  "Wasan yana dab da zuwa ƙarshe indai abunda muka tsara ya tafi daidai"

Alhaji Haruna yace  "ƙwarai kuwa"

Suka maida kai suka cigaba da hirarsu yayin da Saleh gaba ɗaya abun duniya ya dameshi.

***********************************

Gaba ɗaya a sukwane Fahad ya koma gida, se huci yake kamar wani fusataccen kumurci, a falo ya tarar da mahaifiyarsa da ƙannensa, yazo ze wuxe fuuu Hajiya Sarah ta miƙe da sauri tace  "lafiya kuwa Fahad?"

Ya daki kujera yace  "harni za'a kalla ace ban kai namiji ba? Me take taƙama dashi ne haka? Ni Fahad Bulama har akwai Yarinyar da zata kalleni taci zarafina, dan kawai tana da kuɗi, toni na ganta kuma ina sonta sannan zan nuna mata ni cikakken namiji wanda mata je rububin samu!!! Meta taka da harta ke wannan izgilin da cin zarafi ga mutane?  "

"kuɗi yaro wanda hausawa kance masu gidan rana, tabbas Widad ko ba ran Mahaifinta tana da kuɗin da zata taka wanda taso, kar ka manta da bazarsu muke rawa Fahad, ina son saka alkhairi ne da alkhairi shiyasa nake ƙoƙarin haɗaka Aure da ita, karka kusakura inji kayi mata wani abu wanda ze ɓata ranta kona mahaifinta, bazaka taɓa gujewa wannan Auren ba"
Alhaji Bulama ne tsaye a ƙafar benen dake falon, yana wannan maganar

" dan tana da kuɗi, kuɗin banza kuɗin wofi, akanta aka fara arziki? Aiko da ance a gujewa Auren bazan guje masa ba ina sonta tayi min, amma wallahi na aure ta she must pay for what she did, kai kafin in Aureta ma zan Wulaƙanta ta wulaƙanci mafi muni wallahi ni za'ayiwa cin zarafi irin wannan bata isa ba Wallahi "

Ya juya ya bar falon a matuƙar fusace

Hajiya Sarah cikin masifa tace " Alhaji seda nace maka bana son wannan haɗin, kawai ka kaimin yaro ana Wulaƙanta shi daga dawowarsa yaje gurinta zata ci zarafinsa haka, yarinya babu tarbiyya babu ta ido, na gaji da wannan abu"

"maza ki ziga shi, wallahi duk wanda yayi yunƙurin kawowa auren nan cikas zega matakin da zan ɗauka, sannan kija masa kunne, wallahi idan yayi yunƙurin yi mata wani abu ta ɗaureshi wallahi ba zan sa baki a sake shi ba, kinji na gaya miki ku bar komai a hannuna nasan matakin da zan ɗauka"

Yai maganar tare da barin falon ya koma benensa

Yusuf kam tunda aka masa warning yaja bakinsa ya tsuke har sukaje suka dawo be kuma cewa komai ba, amma yana jinsa a ƙoshe saboda garar da ya kwasa yau.

Se bayan isha'i ya baro gidansu Widad, yanata sauri ya koma gida

Ba zato kawai yaga an saka masa wuƙa a saitin Ƙirjinsa, tasayawa yayi cak ba tare da yayi yunƙurin guduwa ba.

Kamar waccan ranar mutanen da suka tareshi ne suka sake tareshi.

"munzone dan mu cigaba da jadadda maka har yanzu muna bibiyarka, muna jiran karɓar wannan abun daga hannunka muna nan muna cigaba da sa maka ido da duk wani motsinka"

"Wai wani abune wannan kuke son karɓa? Ku gayamin in karɓo in baku ku ƙyaleni"

"An gaya maka bamu da lissafi ne? Ba zamu gaya maka menene ba, amma da zarar ka samu abun zamu sani, kuma zamu biyoka mu karɓa"

Suka koma cikin motarsu suka tafi, sedai sunyi ganganci dan tuni Yusuf ya ɗauke lambar motar akansa.

Yau yaci sa'a basu dake shiba suka tafi suka barshi, gida ya tafi yana tunanin meye wannan abun da'aka damu se an karɓa a gurin Widad.

A haka har ya ƙarasa gida, Seda ya zauna sukayi hira da Ummansa dukda abubuwa sun cunkushewa ƙwaƙwalwarsa.

Ya gama cin Abinci ya tafi ɗakinsa, dole zeyi tracking ɗin lambar motar nan ya gano motar waye.

Da ya koma gida Ummansa taita mita akan daren da yake kaiwa a waje, yaita bata haƙuri yana rarrashinta sannan ya tafi ɗakinsa, ya nutsa a duniyar tunani sosai wayarsa ta fara ringing.
Lambar Sakina ce kamar kar ya ɗaga, sekuma ya ɗaga yasa a kunnensa tare da sallama.

"Yusuf baka yi bacci ba?"

"Eh banyi ba" ya bata amsa a taƙaice

"dama magana nake so muyi"

"Amma kinsan dare yayi ko?"

"eh nasani, maganar tana da mahimmanci ne a gareka"

Yusuf yace  "to ina jinki"

"Yusuf akwai buƙatar ka dinga taka tsantsan da wasu abubuwan, akwai mutanen da suke nuna suna tare da kai amma a bayan idonka suna cin dunduniyarka, ba kowane mutum ne aboki na gaskiya ba"

Yusuf yace  "nifa bana son irin wannan ƙananan maganganun, ni ina zaune da kowa lafiya"

"ba ƙananan maganganu bane ba, ka dai yi a hankali sannan karka yadda wani yasan sakamakon binciken da kake komai kusancinka dashi in ba yallaɓai ba shawara ce yakamata ka kula"

"Shikenan nagode" Yusuf ya faɗa cike da ƙosawa, shi sam baya san abunda ze haɗa shi da Sakina baya son mace mara kamin kai sam.

Amma nazarin maganganun ta  ya shiga yi, wayarsa ce ta sake ɗaukar ringing har yayi tsaki ze kashe wayar yaga lambar Alhaji Nasir.

Cikin ladabi ya ɗaga wayar suka gaisa da Baban Widad, Alhaji Nasir yace  "Yusuf meyefaru ɗazu da Fahad yazo gurin Daughter"
. Cikin kame kame Yusuf yace  "Amm.. Yallaɓai yazo sun gaisa"

"Yusuf karka kareta, ka gayamin gaskiya me tayi masa? Wace irin karɓa tayi masa?"

"da alama dai beyi mata bane, ta ɗan dai nuna masa bata sonsa ne"

"Yusuf karka fara ƙarya saboda ka kare uwar ɗakinka, Bulama ya tabattar min da wulaƙanci tayiwa Fahad, kuma nasani zata aikata na kiraka ne dan in tabattar, saboda zan ɗau mataki na ƙarshe daya dace da ita, duk abunda nake dan gyaran rayuwar ta nake amma ta kasa ganewa, dan haka zan ɗau matakin da bata taɓa zata ba akanta wanda ze kasance hukunci na ƙarshe da zan yanke akanta "

Domin gyara sharhi ko shawara, feel free to contact me
Ayshercool
07063065680

                       _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 19_20

Gaba ɗaya Yusuf ya dirircei yace  "Amm... Amma Yallaɓai wani mataki zaka ɗauka haka akanta, ina fatan ba wanda ze mata tsauri bane?"

"Yusuf kenan, ka damu da al'amarin Widad haka nan naji na yadda da kai, shiyasa har nake saka a cikin abunda ya shafi rayuwar mu, na yanke shawarar tsayar da ranar Aurenta a ƙarshen wannan watan zuwa farkon wata me kamawa"

"Amma yallaɓai baka ganin hakan ze sake jefa rayuwarta cikin hatsari, duba da yadda babu Aure a tsarin Rayuwar ta?"

"Yusuf, Widad fa mutum ce kuma lafiyayyiya tana ƙin Aurene saboda wasu dalilanta da suke masu rauni a gurina, bana so in mutu in barta cikin kaɗaici, nasan Bulama baze taɓa barin ɗansa ya Wulaƙanta Widad ba ko bayan raina, dan Allah ka cigaba da yimana addu'a, Amma insha Allah ko ba taso zan ɗaura mata aure karo na farko a rayuwata da zan ɓata mata rai, amma ina fatan hakan ya zama alkhairi a gareta, Insha Allah gobe zuwa jibi zan dawk"

"shikenan Yallaɓai, Allah ya tabattar da alkhairi ya dawo da kai lafiya"

"Ameen Yusufa nagode sosai"

Tunda sukayi Sallama da mahaifin Widad abun duniya ya damu Yusuf, ji yake matakin da mahaifin Widad ke shirin ɗauka tamkar ƙarasa rugurguza rayuwar uwar ɗakinsa ne gaba ɗaya, matakin yayi tsauri sosai, haka nan yaji wani irin matsanancin kishi na taso masa game da Widad ɗin.

Dafe kansa yayi tare da faɗin "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ka tsareni da sake faɗawa hatsarin Soyayya, Allah yasa tausayinta kawai nake ji, tabbas idan na fara son Widad zan shiga matsala fiye da wadda nasha a baya"

Bacci kam se Ɓarawo ne ya kama Yusuf.

Kwana biyu a tsakani Yusuf yana zuwa gidansu Widad amma ba wani aiki da yake yi, kuma sam baya ganinta.

Abubuwa sun ƙara cakuɗewa Yusuf, tunani kala kala a zuciyarsa amma zuciyarsa tafi fargaba akan hukuncin da Daddy ya yanke ɗauka akan Widad.

Ya ɗakko wayarsa yana ɗan duddubawa kawai yaga message ya shigo wayarsa, anyiwa ma'aikata canjin gurin aiki ciki harda Abbas, an maida Abbas aiki a kudancin Nigeria, abun ya ɗaurewa Yusuf kai sosai, mafi akasari anfi yin wa mutum wannan canjin aikin ne, kodai dan wani mahimmin bincike, ko ƙarin girma kokuma dan hukunci ga wani laifi da ya aikata, sedai shi a ganinsa babu ɗaya da Abbas yayi wanda zesa ayi masa wannan transfer.

Ba shiri Yusuf ya bar gidansu Widad ya tafi gurin aikinsu, kai tsaye ofishin Oga Suleiman ya wuce, gaje suka gaisa Suleiman yace  "Yusuf naga aikin daka turomin, kayi ƙoƙari sosai Yusuf sannan ina taya ka murna da sabon muƙaminka"

Yusuf cikin rashin fahimta yace  "Yallaɓai nida ban fahimci abun nan ba, me Abbas yayi za'a ɗauke shi daga gurin nan akaishi wata uwa duniya?"

"Nima ban san meyasa hakan ta faru ba, sedai daga sama ne akayi wannan transfer sannan ka samu ƙarin matsayi"

Yusuf ya dafe kai yace  "Yallaɓai babu yadda za'ayi a bar Abbas a gurin nan ne? Bekamata a raba shi da iyalinsa ba zuwa wata uwa duniya ba, ni dai banji daɗin hakan ba, zanyi kewar abokina kuma ɗan uwana"

Suleiman ya jinjina sauƙin kai irin na Yusuf yace  "ya za'ayi se haƙuri haka sha'anin aiki yake"

Jiki a sanyaye Yusuf ya baro office ɗin Suleiman ya nufi na Abbas, se sarawa Yusuf ake ana masa murna amma shi sam hankalinsa yana kan wannan transfer da'akayiwa Abbas.

Da sallama ya shiga Office ɗin ya tarar da Abbas yana ta tattara kayansa dake Office ɗin.

"Abbas ya akayi haka? Me yasa akayi maka transfer haka ta gaggawa?"

Abbas yace  "nima ban sani ba Yusuf, jiya aka sanar dani kuma akace lallai gobe in Allah ya kaimu in tafi"

"yanzu babu wani abu da zamu iyayi a fasa wannan transfer ɗin?"

"Yusuf nayi duk ƙoƙarin da zanyi amma abun ya gagara"

Gaba ɗaya Yusuf ya rasa abunda yake masa daɗi, dan har cikin ransa yake jin rabuwa da Abbas ɗin, dan yana jin Abbas tamkar wani ɗan uwansa.

Wayar Yusuf ce ta fara ringing, ya ɗakkota daga aljihunsa ya ɗaga.

"Yusuf mai gida ya dawo yanzun nan, yace a kiraka"

"Shikenan gani nan zuwa"

Yusuf ya kashe wayar yace "Abbas zanzo gida insha Allah, zan ganka muyi sallama"

Abbas yace "Yusuf na ta yaka murna, an ƙara maka matsayi"

Yusuf yace  "Abbas sam bana murna da wannan ƙarin matsayin, ni tafiyarka ce damuwa ta, bari inje wannan kiran zan nemeka Insha Allah"

Sukayi musabiha, Yusuf ya juya ya fita, Abbas ya raka bayan Yusuf da harara tare da yin ƙwafa.

Tun daga harabar gidan Yusuf yaga manyan motoci da alama bayan dawowar maigidan anyi baƙi a gidan.

Kansa tsaye ya nufi cikin gidan, a falon ya tarar da Alhaji Nasir, Bulama, Fahad Hajiya Halima da iyalanta.

Yusuf ya ƙaraso yana gaishesu, Alhaji Nasir yace  "ƙaraso kusa dani Yayana, nace a kiraka aka cemin ka fita ne"

Yusuf yace  "eh naje wani uzuri ne"

Fahad se wani hararar Yusuf yake, shiko Yusuf ya basar kamar be gani ba.

Tsit falon yayi na wani lokaci, Yusuf ya rasa dalilin hakan, yana ɗaga kai yaga gimbiyar ta fito daga ƙofar part ɗinta, da alamu wannan zaman fitowarta ake jira, seda ta tsaya ta ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya sannan ta ƙaraso cikin takunta na isa, ta samu kujera ɗaya ta zauna ba tare da ta kula kowa ba.

Alhaji Nasir yace "daughter"

"Na'am Daddy"

"waye wannan?" ya nuna mata Bulama

"Alhaji Bulama"

"kin san matsayinsa a gurina?"

"Just a long time business partner to you"

"he is more than that to me, kuma kin sani danme zan baki umarni kiyi fatali dashi? Duk abunda mukeyi munayi ne dan rayuwarki, danme zaki ciwa Fahad mutunci? A gaban Yusuf komai ya faru, daughter nasan duk abunda kike yi, ina ƙyale ki ne saboda nasan halinda kike ciki na maraici, amma kina zarce ƙa'ida wasu lokutan, daughter farincikin ki muke fata shiyasa muke son aurar dake"

Gaba ɗaya Widad ta ɗauke kai daga kallon Daddynta zuwa wani sashin daban, tanajin ɓacin ran saboda wannan daƙiƙin talasurun Fahad ɗin yau Daddynta ke mata faɗa, ze gane bashi da wayo.

"dan haka whether you like it or not, i have took the final decision, ending of this month zuwa farkon wata na gaba zan ɗaura Auren ki da Fahad"

Zare ido Ramlah tayi, taji zuciyarta kamar zata faɗo.

Fahad ya wani gyara zama ya kalli Alhaji Nasir yace  "sannan Daddy gaskiya yakamata ayi mata magana akan tasan yadda zata dinga gayamin magana, ta tauna ta kafin ta faɗeta dan sam bata da ɗa'a"

Miƙewa Widad tayi tsaye a fusace tace  "Over my death Body Daddy, wallahi da in auri wannan mara amfanin gara in kashe kaina, kai ka isa ka kalli tsabar idona kace a koyamin yadda zan magana, waye kai"

"Widad!!!"  mahaifinta ya kira sunanta tare da Miƙewa kamar ze kai mata duka.
Cikin zafin nama Yusuf ya miƙe ya shiga tsakanin Widad da mahaifinta ya girgiza kai yace  "Yallaɓai ayi mata afuwa dan Allah, baka saba yi mata magana haka ba karka fara yanzu karkasa zuciyarta tayi rauni, kowa ya juya mata baya, ka sauraretaba zata rasa dalilinta na ƙinsa ba"

Alhaji Nasir yace  "Amma Yusuf yakamata Widad tayi min haka a gaban mutane ta nuna ban isa ba?"

Girgiza kai Yusuf yayi yace "ba tayi haka dan Wulaƙanta kaba, ta tashi a environment ɗin da kowa yana da 'yancin faɗan abunda yake ra' ayinsa, karka ɗau hakan a matsayin ta Wulaƙanta ka, kayi haƙuri dan Allah kasan bata da lafiya"

Tuni hawaye ya wanke fuskar Widad ta kalli Daddynta karo na farko a rayuwar ta da yaƙi bin abunda takeso, hannayenta biyu ta haɗa tareda duƙar da kanta alamar neman afuwa, daga nan ta juya ɗakinta.

Alhaji Nasir ya nemi guri ya zauna, Bulama yace  "lamarin daughter se haƙuri, Allah ya shirya mana"

Hajiya Halima ta gyatsine baki tace  "wannan direban ne yake hure mata kunne take iskancin data ga dama, na rasa wace irin alaƙace tsakaninsu banda haka ana mata faɗa meye na tsoma baki? Kaima Yallaɓai harda kai da kake saka bare a al'amuran gidanka"
  Alhaji Nasir yace  "ba ruwan Yusuf, a irin taurin kai na Widad da irin haƙuri na Yusuf be isa ya hure mata kunne ba, sedai haƙurinsa ne yasa suke tare har yanzu, dan haka karki ƙara aibata shi ko ɗora masa laifi, kaimu Fahad zan shawo kan komai insha Allah"

Yusuf ya miƙe yayi musu sallama ya fice suka cigaba da tattaunawa.

Cakwakiyar gidan nan akwai sarƙaƙiya da ban mamaki, yana nan zaune ya dafe kai yayi shiru Bulama da Fahad suka fito zasu tafi, Bulama ya shiga motarsa direbansa ya ja suka tafi.

Fahad ya tako zuwa gaban Yusuf ya zauna yana fuskantar Yusuf yace 

"kaine direban Widad ko?"

Yusuf yace
"Eh nine"

"Naga kamar matsayinka a gidan nan ya wuce matsayinka na zahiri, zan ja maka kunne ne idan har kana shishshigi da iyayi ka kiyayi Fahad, dan bana barin duk wani abu daze kawomin cikas, matsiyaci kawai kalli rigar wuyanka wai har kaine zaka shiga maganar da bata shafeka ba"

Yusuf yayi murmushi ya miƙawa Fahad hannu yace "Assalamu Alaikum warahmatullah"

Fahad ya kalleshi yace "ni zaka miƙowa hannu kace mu gaisa, kasan koni waye?"

"haka Addini na ya koyamin, ban saniba ko zama a cikin turawa yasa ka manta hakan, rigar wuyana zata iya fin taka daraja in har da gumin halak na sameta, sannan nafi kowa sanin ko kai waye, ɗan adam ne da'aka samar daga Najasa wanda ƙarshena ni da kake kira matsiyaci da kai da kake ganin kanka wani ƙarshen mu ɗaya wato turɓaya kuma Abincin tsutsa, kana fuffukar ban san waye kaiba, kamar ba'a gabana mace ta keta ka ba ta Wulaƙanta ka, wulaƙanci mafi ƙasƙanci shine yadda ake cusa mata kai tana cewa bata sonka "

Galala Fahad yayi yana kallon Yusuf, sam be zaci Yusuf ya iya yanka baƙaƙen magnganu haka ba, Yusuf ya miƙe yace " ka kiyaye gaba, dan idan baki yasan me ze faɗa be san abunda za'a mayar masa ba, bana shkkar kowa se Mahaliccina, kana gayamin abunda beminba zan rama, ni yanzu damuwata be wuce yadda a dalilinka aka samun uwar ɗakina a damuwa ba, damuwarta tafi komai tsayawa a zuciyata"

************************************

"Akan me za'a ayi maka transfer bayan bamu sallami wannan mutanen ba? Waima waye yayi maka transfer ne haka ba shiri? Aknme za'a ɗauke ka daga garin nan?"

Abbas yayi ajiyar zuciya yace " wallahi ranka ya daɗe ban san yadda hakan ta faru ba, Suleiman ya cemin daga sama transfer ɗin tazo, abun baƙin ciki aka maye gurbina dana bari da Yusuf, ni ina kyautata zaton shine yaje yasa akamin transfer dan ya gaji muƙamina, kuma da yake munafiki ne ya zo yana nuna damuwarsa akan transfer ɗin da'akayi min"

Saleh ya numfasa yace  "Abbas tabbas akwai babbar matsala wannan transfe da'akayi maka ba tare da samun binciken da Yusuf yayi ba, a ɗan ganin da nayi masa beyi kama da mugun mutum ba yana da nutsuwa, dan haka bashi da hannu a cikin transfer ɗin da'akayi maka, ni babban burina in samu binciken da yayi a hannuna in sallami wancan mutanen kafin su shiga target ɗinsu na biyu kuma na ƙarshe akan Widad, wanda target ne me hatsarin gaske"

Abbas yace  "nifa takaicina shikenan yanzu ba zan samu kuɗaɗen nan ba? Gaskiya na ƙallafa rai amma karka damu Yallaɓai, dukda zan bar garin nan dole a samu binciken da Yusuf yayi"

Saleh yace  "don't stress yourself i know what to do"

"Amma kana ganin rashin bada file ɗin akan kari zesa kaima ka shiga cikin matsala?"

"babu wata matsala am also planning something, karka damu ni zan tafi duk yadda ake ciki zamuyi waya"

Daga nan suka yi sallama.

Sam Yusuf ya dena ganin Widad, hakan yasashi shiga damuwa sosai, hakan yaso ya shafi aikin da yake yi, ya damu sosai yaga halin da take ciki, bashi da hujjar shiga cikin gidan tunda ba nemansa akayiba.

Mutanen gidan dama ba wanda yake saurarar Yusuf, dan haka haka yake zuwa ya wuni ya tafi zuciyarsa cike da son sanin halin da take ciki.

Yusuf yana zaune yana tunanin yadda zega Widad dan yasan koba'a gaya masa ba Widad tana cikin damuwa.

Fitowar Alhaji Nasir dasu Hajiya Halima ne ya dawo da Yusuf daga tunanin da yake yi, Fuskar Alhaji Nasir akwai damuwa amma ya danne damuwar tasa yana ta fara'a.

Yayiwa Yusuf alama da yazo, Yusuf ya taso yazo, Alhaji Nasir yace  "Babban Yaya, airport za muje zamu ɗakko ɗana Anwar, ya kammala karatun sa"

Yusuf yayi murmushi yace  "Masha Allah, shima Yayan uwa ɗakina ne?"

Alhaji Nasir yayi murmushi yace  "Yusufa kenan, ai uwaɗakin ka bata da wa ba ƙani, Amma Anwar ma ɗana ne tunda na riƙe shi"

Yusuf yace  "ba da ita zamuje bane? Naga ita bata fito ba?" Yusuf yayi maganar cike da son sanin halinda Widad take ciki.

"Kasan tana fushi dani ne, ta dena zuwa inda nake ma, na ɗan ƙyaleta ne ta huta, har seta gane mahimmancin maganata"

Har Yusuf zeyi magana, Hajiya Halima tace "Kaga ka ishemu da surutu, muyi mu tafi kar jirginsu ya sauka yazo yana faman jira"

Alhaji Nasir yace  "Bimin shi a hankali Halima, Yaya nane a girmama shi ko dan sunan nasa"

Nura yana gefe ji yake kaman ya shaƙe Yusuf, ba'a taɓa ma'aikacin da Alhaji Nasir ke nunawa soyayya kamae Yusuf ba dukda mutum ne me girmama na ƙasanshi, tsabar abu yanzu Alhaji Nasir be fiye damuwa da Nura yaja shi a mota ba sedai Yusuf.

Gaban Mota Amal ta shige, yayin da su kuma suka shiga baya, Suna tafe a mota iyalan suna hira kamar ba abunda ke damunsu, Alhaji Nasir yana dauriya ne kawai, yayin da Yusuf ko uffan yakasa cewa hankalin sa na kan Widad.

Koda suka je airport sunyi A ƙalla mintuna talatin, sannan wanda suka zo dominsan jirginsu ya sauka, matashin kamarsa ɗaya sak da Amal, kana kallonsa kasan ɗan uwansu ne, da gudu sukaje suka rungume shi cike da farinciki, ya ƙaraso gaban Alhaji Nasir ya durƙusa ya gaishe shi.

Bayan sun gaisa ya kalli Yusuf ya miƙa masa hannu sukayi musabaha, da alama Anwar shi a nutse yake ba kamar 'yan uwansa ba, daga nan suka nufi hanyar gida, suna tafe kamar zasu fasa motar da hayaniya da shewa.

Har sukaje gida hirarsu kawai suke, amma alamu sun nuna Alhaji Nasir biye musu kawai yake, sun Sakkowa sukayi cikin gida yayinda aka bar Yusuf da kwaso akwatunan Anwar.

Suna shiga falo kawai Yusuf yaga Widad a zaune tana shan ruwan roba, sedai idanunta a kumbure suke, alamar kodai bata bacci kokuma kuka take yi, gaba ɗaya Yusuf yaji babu daɗi.

Anwar yace  "Masha Allah, little queen ta girma Amma Daddy sha ka fashe ka bata dan yayi wuri ace tayi wannan girman"

Daddy yayi murmushi yace "gata nan tambaye ta, in da ragiwar sha ka fashe ɗin kaima ta sammaka"

Ba tsammani Yusuf yaga Widad ta ɗanyi murmushi, yayin da Hajiya Halima ta tsuke fuska tace "kaga muje ka wataa ruwa ka nemi Abinci"

Anwar yace  "bari Mummy in gama ganin lovely ɗin Daddyn ta inji dalilin da yasa ba tazo taroni ba"

Yai maganar yana ƙarasawa inda Widad take ya zauna, Alhaji Nasir kam part ɗinsa ya wuce yana murmushi saboda Anwar akwai barkwanci.

Ramla cikin tsawa ta cewa Yusuf "dalla malam ka ajiye kayan na ki fita, uban sa ido kawai"

"Karki kuma yi masa tsawa, na kuma gayamiki ba zamanki yake ba, idan kika ƙara hukuncin daze biyo baya ka iya ɓatawa kowa rai"  Widad tayi maganar ba tare da kallon Ramla ba.

Anwar yace  "Ramla baki kyauta ba, babu daɗi abunda kikayi fa"

A fusace Mummy tace  "dalla tashi ka wuce ciki, ina magana harda neman guri ka zauna"

Anwar ya miƙe yace  "Widad idan na fito zanzo mu gaisa sosai ki bani sirrin wannan girman naki"

"No need Anwar, yanzu ma mun gaisa yawan shiga harkata ka iya baka matsala da kai da Ahalinka, ina taya ka murnar kammala karatunka, Allah yasa al'umma su amfana"

Tai maganar tana miƙa masa hannu suka gaisa, from no where Yusuf yaji wani takaici ya tokare masa zuciya ganin abunda ya faru.

Mummy ta tasa ahalinta suka shige sashinta, aka bar Yusuf da Widad a falon har ya juya ze fita ya bar falon ya waiwayo, ba zato suka haɗa ido tai saurin ɗauke nata idon daga nasa, a hankali ya dawo ya kalleta yace  "Madam ko baki da lafiya ne?"

Girgiza masa kai tayi tace  "jirani a waje gani nan zamu fita" ya jinjina mata kai ya fita.

Cike da damuwa Anwar yace "Mumsy meyasa bakya son Widad ne? Me tayi mikine haka?"

Ramla tace  "yanzu daka dawo idonka ze gane maka ai"

"kar in sake magana ki samun baki, in bahaka ba sena tattakaki na gaya miki"

Ya maida hankalinsa kan Hajiya Halima yace  "Rayuwar ta abun tausayi ce, tana buƙatar kulawa meyw a ciki dan ki haɗemu gaba ɗaya kin nuna mata kamar ke kika haifeta"

Amal tace  "Taɓɗijan lallai baka san yarinyar nan da taurin kai kamar arnan farko ba, ba mutunci a lamuranta balle tausasawa bata ganin kowa da gashi waye za janyo ta a jiki?"

"Amla yaushe kika koma hakane? Gaba ɗaya kun zama fitsararru"

"karka ƙara ce musu fitsararru na gaya maka, bazan riƙe yarinyar da zata nemi ta halakani da baƙinciki ba, bata da tarbiyya sam bata da ɗa'a, shikansa mahaifin nata bata ƙyaleshi ba, weekends ɗin nan Fahad yazo ganin ta za'a haɗasu Aure da shi da ubansa ta haɗa ta wanke su da rashin mutunci tsaf, ubanta ya kirata yayi mata faɗa nan ma ta sake kunyata shi a gaban mutane ta hanyar nuna masa be isa ba"

Cike da ɗimuwa Anwar yace  "wait ji nayi kamar kince za'a haɗata Aurw da Fahad, wani Fahad ɗin wai?"

"Fahad ɗin Bulama mana" ta bashi amsa

A diririce yace "Mummy ta yaya haka zata farune? Ita tace tana sonshi? A zatona ai Ramla yake so"

Amla tace  "Ramla yake so, amma babansa da Babanta sukayi ƙarfa ƙarfa sukace zasu aura masa ita, tayi masa rashin mutunci amma yace ba gudu ba ja da baya seya aure ta"

Anwar yace  "Impossible wallahi sedai ayi biyu babu, Fahad yafi kowa sanin yadda nake son yarinyar nan danme zemin haka? Na tabbata da nine bazan masa haka ba, wallahi indai da raina Fahad be isa ba, sedai zumuncin namu ya watse"

"haka nima indai da raina baka isa ka aureta ba, sedai ka canza wata uwar bani ba, dan da hankalina ɗana baze auri dangin mahaukata gadon rashin tarbiyya ba"

Bin mahaifiyar tasa yayi da ido, tare da mamakin wannan magana data fito daga bakinta, be kuma cewa komai ba ya fice cikin hanzari.

Wata katafariyar ma'aikata sukaje, Yusuf yayi mamakin haɗuwa gami da tsaruwar ma'aikatar kamar ba'a ƙasa Nigeria ba, Widad ta dinga ratsawa Yusuf na binta kamar inuwa haka suka isa wani makeken Office.

Kai tsaye ba neman izina ta bankaɗa ofishin ta shiga, Bulama ne zaune da ɗansa Fahad suna dudsuba wasu file, Widad ta kallesu tana huci kamar mayuwanciyar Mesa.

"daughter lafiya kuwa?" Bulama ya tambayeta.

"Dole ka tambayi lafiya mana tunda kayi nasarar cusawa mahaifina ra'ayinka wansa yake barazana ga ratuwata, be taɓa fushi dani kamar wannan karon ba yana kallon hawaye akan fuskata amma ya kasa share min hawayen, ya barni tsawon kwanaki ina fama da ƙuncin zuciya "

Bulama yace " Calm down daughter, wannan fa duk ba abun zafi bane, ke kika kambama abun kika maida shi babba, meye laifin Fahad dan an Aure shi? Kuma daba'a aure a haifeki? "

" kai baka ga laifin ɗanka ba ni na gani, bashi da nagartar daze iya zama miji a gare ni, na tsane shi bana sonsa kuma bazan aure shi ba, sannan ka gaggauta zuwa ka janye wannan maganar daga gurin mahaifina ya dena fushi dani, fushinsa yana daga abunda ke jefa zuciyata cikin tashin hankali, be taɓa fushibdanibba se a dalikin wannan gurguwar shawarar taka, bazanyi aure ba ka janye wannan maganar idan ba haka ba Wallahi sena baka mamaki daga kai har ɗan naka"

"Ke jahila!" Fahad ya faɗa tare da yunƙurin kai mata mari, ganin yadda take wa mahaifinsa shouting, sedai ba zato yaji an riƙe hannunsa anyi gefe dashi.

"karka kuskura koda wasa ka kuma yunƙurin ɗaga hannu akanta, koda mafarki kake kaga hakan zata faru kayi duk me yuwuwa kaga ka farka da baccin dan mummunan mafarkine balle a gaske, sannan kasan da kalmomin da zakayi amfani gurin yi mata magana"

Yusuf yayi maganar cikin fushi da harzuƙa, wani irin kwarjini Yusuf yayiwa Fahad, dan a doke tsaf Yusuf ze bazar dashi a gurin.

Bulama yace  "ɗan samari kamar kana zaƙewa fa wasu lokutan"

Yusuf ya saki hannun Fahad cikin ladabi yace  "bahaka bane ranka ya dade, nayi ƙoƙarin hana faruwar tsamin alaƙar daze biyo baya idan har Alhaji Nasir yaji ɗanka ya dakar masa 'ya me"

Bulama yace "koda baka yi hakan ba ni zan ɗau mataki Yusuf, bazan bari hakan ta faru ba sam"

Widad tace  "naso ka bari ya dakeni, in sa a nuna masa shi ba komai bane, in nunawa duniya da bazata yake rawa, duk wannan fuffukar da yake da sena nuna masa in ba Widad babu shi, kuma Auren nan dole a fasashi, nazo ne dama dan in muku gargaɗi na ƙarshe a janye maganar nan kafin rugujewar duk wata alaƙa dake tsakaninka da mahaifina"

Sosai Fahad ya dinga huci, a gabansa yarinya ƙarama take cim zarafin mahaifinsa.
Bayan fitarsu Widad, Bulama yayi shiru yana tunani, Fahad yace  "Daddy wannan wace irin dabbar yarinya ce me kyan ɗan maciji, bata da tarbiyya bata da ta ido Sam, ta dubi mutum kamar kai ta dinga gaya masa wannan maganganun, kana kallonta kuma Daddy"

Bulama yayi ajiyar zuciya yace  "daka sake ka daki yarinyar nan da tabbas yanzu wani zancen ake ba wannan ba, koda wasa karka kuskura kayi gangancin cewar zaka dake ta, ta wuce yadda kake tunani, tabbas ba dan inajin nauyin Daula ba da se an fasa Auren nan, dan ina ganin ƙiyayyarka a idonta wanda har hakan yake son ya shafeni"

Fahad ya daki teburi yace  "Nikuma ina sonta a hakan, zan Aure ta koda zata kashe kanta sena Aureta na wulaƙantata na nuna mata ita bakomai bace zanga wanda ze Nasara tsakanin ni da ita"

Bulama ya girgiza kai yace  "Fahad kenan kai kana tunanin zaka iya Wulaƙanta ta idan ka Aureta, dole kayi haƙuri da duk abunda zata aikata maka, zamuyi mata aurene dan samun nutsuwar ta ba dan a muzguna mata ba, shiyasa tun da fari bamu nemi wani bare sekai"

Gajeren tsaki Fahad yayi yaja kujera ya zauna tare da dafe kansa.

Kallonsa take yana tuƙi fuskarsa ɗauke da ɓacin rai, tunani take a duk lokacin da yaga wani na shirin cin zarafinta ko ɓata mata rai se yayi duk me yuwa ya hana faruwar hakan, a duk lokacin da take cikin damuwa zataga damuwa a fuskarsa, wanda ko ɓata masa rai tayi be fiye nuna damuwa haka ba.
Ajiyar zuciya ta sauke seda Yusuf ya juyo ya kalleta yace "lafiya kuwa?"

Ta jinjina masa kai alamar eh, haka suka koma gida ranta a matuƙar ɓace.

Anwar suka gani a harabar gidan, ya ƙaraso da sauri inda take yace  "Widad ina kika jene? Tun ɗazu nake dubaki a gidan nan ban ganki ba" yai maganar cike da damuwa.

Widad tace  "Anwar bana son daga dawowarka ka fara shiga cikin matsalolin gidan nan, zaka fuskanci fushin mahaifiyarka idan haraka cigaba da shiga harkata, am sorry amma kayi harkokinka inyi nawa please"

Ze sake yin magana tayi gaba ta shige ta barshi a gurin, ya kalli Yusuf yace  "ɗan uwa dan Allah meke wakana a gidan nan ne? Ni gaba ɗaya abubuwan mamaki suke bani"

Yusuf yace  "gaskiya nima ban sani ba, tunda nima banfi watanni huɗu da fara aiki a gidan nan ba, bakomai nasani ba, sedai damuwa na damunta sakamakon Auren da za'ayi mata, bata fiye son a shiga harkar ta ba idan tana cikin damuwa shine kawai abunda nasani"

"dan Allah wai dama maganar Auren nan dagaske ne?"

"Eh gaskene" Yusuf ya bashi amsa

"Impossible" Anwar ya faɗa da ɗan ƙarfi

"Ni Fahad zeyi wa haka? Saboda cin amana da wulaƙanci" Anwar ya girgiza kai ya koma cikin gida fuskarsa ɗauke da ɓacin rai.

Washegari da safe Yusuf ya shirya ya fita, seda ya fara biyawa gidan Abbas amma ya tarar baya nan, kamar yaje office amma ya fasa ya wuce gidansu Widad.

"Yusuf gimbiyar masu gida da kanta ta fito nemanka, da alama ka makara fa"

Yusuf yace  "wani abune ya ɗan tsareni, bari inje in ganta"

Murtalah yace  "tana lambu ita da tsuntsayenta da ƙanwarta wato kyanwarta"

Yusuf yayi murmushi ya nufi lambun, kamar yadda Murtalah ya gaya masa tana lambun ita da magenta Roux, magana takewa magen nata kamar da mutum take magana tana cewa

"Roux har yanzu Daddy yana fushi dani, gaba ɗaya duniya tamin zafi, ba wanda ya goyi bayana ko ya tausayawa halin da nake ciki, ba zan iyayiwa Daddy biyayya in Auri Fahad ba, ji nake kamar zuciyata zata tsaya saboda ɓacin rai, amma dole in san hujjar da zan gabatarwa Daddy da zesa a fasa Auren nan, am so much disturbed Roux"

Tana maganar tana shafa jikin magen, yayinda magen tayi luf a jikin Widad kamar tasan me take gaya mata, lokuta da dama Yusuf yana jin Widad tana hira da Mage, hirar da be taɓa jin tana yi da ɗan adam cikin mutuntawa da nutsuwa haka ba.

Ji tayi kamar ana kallonta ta ɗaga kai suka haɗa ido da Yusuf, ta tsuke fuska tace "baka iya Sallama bane?"

"Ai idan nayi sallama bakya amsawa" ya bata amsa

"Se yanzu kaga damar zuwa ko?"

"Umma na taya aiki shiyasa banzo da wuri ba"

"shikenan, zamu fita yau ƙarfe tara"

"Amma ai tara ta wuce yanzu, sedai ta gobe in Allah ya kaimu"

"tara na dare" ta bashi amsa

"tara na dare kuma? Ina zamuje haka da daddare? Kuma mu dawo yaushe? "

Ba tare da ta kalli Yusuf ba tace "hmmm akwai ka da ƙwarin gwiwa, ƙarfin hali bin ƙwaƙwƙwafi da sa ido sekace ɗan Sanda ko wani jami'in sirri, za kayi kyau da Aikin ɗan sanda ko kuma fannin shari'a"

Wani abune ya tsarga tun daga kan Yusuf har yatsunsa na ƙafa.......

(INA BUƘATAR JIN SHARHINKU FANS, ME KUKE TUNANI NE AKAN WANNAN TURKA TURKA, INGA COMMENTS ƊINKU KO IN KOMA POSTING DA TSALLAKEN KWANA ƊAYA)

Share and share please
domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680

                      _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 20_21

Widad ta cigaba da cewa "da aikin shari'a zakayi zeyi wuya a iya kada kai, yakamata Alhaji Nasir yayiwa yayansa wani abu, yakamata ya nema maka makaranta ko dai horarwa akan aikin tsaro kokuma a nema maka aikin shari'a" ta ƙarasa maganar da wani ɗan guntun murmushi

Yusuf ya daskare ya kasa ko motsa ɗan yatsansa 'Widad ta gano shine kokuwa?'

"Jeka in lokacin yayi kazo mu tafi"

Kasa motsawa Yusuf yayi, ya tasaya yana kallon Widad, ta ɗago ta kalle shi tace "ya dai naga ka tsaya? Meyafaru?"

Girgiza kai yayi ya juya ze fita, beji takuma cewa komai ba.

Tunani ne ya shiga zarya a zuciyarsa, kodai Widad tasan waye shine? Amma ya tuna da sharaɗinta bata yafewa wanda yayi mata ƙarya, a rashin yarda nan tata tabbas da tasan waye shi da tuni tayi maganinsa ta ɗau mataki akansa.
A hankali ya furta "Ubangiji Allah ka shiga lamarina, Allah yasa har in kammala aikin nan yarinyar nan ba zata ganoni ba"

*****************************

"Amma ni tabbas ba'ayimin Adalci a wannan lamarin ba, nida ɗan uwana ku kusan halaka shi sannan ace bazan ganshi ba, wannan wane irin zalunci ne"

"zaka iya kiransa da duka abunda kaga dama, amma tabbas ba zaka ganshi ba, zamu ci gaba da ajiye shi a ɓoyayyen guri har se sakamakon binciken nan yazo hannun mu"

Saleh yace  "binciken nan bani na yake yi ba, kun san hukumar da sukeyi meze sa ku cigaba da azabtar min da ɗan uwa"

"saboda shi kaɗai ne hujjar daze fallasa komai a kotu, kuma yana nan shirin tona mana Asiri dan haka gara muyi maganinsa"

Cike da damuwa Saleh yace  "to ai wanda yake ƙoƙarin samo min sakamakon anyi masa transfer ya kuke so inyi, ni ko ganinsa inyi shikenan"

Alhaji Musa yace  "baja da wannan damar Saleh, kayi abunda muka ce kawai"

A fusace Saleh ya miƙe ya bar gurin zuciyarsa na masa zugi, tabbas su Alhaji Musa masifa ne a rayuwarsa da ɗan uwansa.

Anwar a cikin ɓacin rai yaje ya samu Fahad a gida, Fahad na ganinsa yace  "Ohh God, Anwar ai namanta gaba ɗaya jiya zaka dawo am so sorry brother"

Jiki a sanyaye Anwar ya kalli Fahad yace "Am disappointed Fahad, dole kace ka manta jiya zan dawo, yanzu Fahad yarinyar dana daɗe ina mafarkin aura ita zaka aura?"

Ajiyar zuciya Fahad yayi yace "am sorry, nima bani nace ina son ta ba cusa min ita akayi akace sena Aureta dan anga tana da taɓun hankali"

"Fahad, Widad ba irin matan da za'a cusawa mutum bane, sannan idan har cusa maka ita akayi saboda taɓin hankali, ni ka barmin ita in aura tunda ni ina son ta"

"nice maka akayi bana sonta? Ko kuma so kake in kalli mahaifina ince zan bijirewa umarninsa"

Anwar yace "ni bahaka nake nufi ba amma nasani ka sani Baka dace da Widad ba, nasan halinka gaba da baya"

"kasan halina amma ka barni nake soyayya da ƙanwarka? Ko abun naka son zuciya ne?"

"son zuciya be wuce wanda ake shirin yiwa Widad ba, Ramla tasan dai dai tasan abunda take yi dan haka idan ta zaɓeka a matsayin miji ita taso hakan, Amma Widad fa Yarinya ce sannan...

"kaga Anwar ya isheni haka" Fahad yai maganar a tsawace

"Idan har ba so kake abotarmu ta samu matsala ba ka ƙyaleni, ka fita daga batun Auren nan"

"Idan kuma naƙifa?"

"Komai ze iya faruwa"

Anwar yace  "to sonake koman ya fary Fahad, naga baka gane rarrashi zan ɓullo maka ta inda ya dace"

Fahad yace  "Anwar karka kuskura kaje ka faɗi wani mummunan abu a kaina a gurin mahaifin Widad"

"Fahad dani da kai a ƙarƙashin kulawarsa mukayi karatu, ba abunda be mana na gata a rayuwa ba, bana jin Widad kanta ta moreshi kamar yadda muka moreshi, idan har aka lulluɓe kura da fatar Akuya ba muyiwa Alhaji Nasir Adalci ba, kaima kasan baka dace sa Auren 'yarsa ba"

"Amma Anwar kasan taimakawa zan in Aureta tunda mahaukaciya ce?"

"kabar taimakon naka mana, kaje ka auri Ramlah"

"Amma Anwar meyasa kake fifita Bare akan ƙanwarka? Idan har dagaske kake Ramla yakamata kace bazan Aura ba"

"Fahad ba goyon bayan bare nake ba, goyon bayan gaskiya nake kuma kaima ka sani"

Yana gama maganar ya fice a fusace cikin sauri.

**********************************
Ɓangarren Nurat kam lamarin mahaifinta yana bata mamaki, gaba ɗaya babu wanda ya gane inda yasa gaba daga ita har mahaifiyarta, ga ta'amali da wasu irin ƙarti da yakeyi wanda daka gansu zaka san ba mutanen kirki bane, suyita musu zirga zirga a gida, babu me ikon cewa uffan saboda duk tsoronsa suke ji.

Gefe guda kam tunanin Abokinta ya cika mata zuciya, zuciyar ta na matuƙar begen ta ganshi amma abu ya gagara, tasan ko giyar wake tasha bata isa taje gidansu Widad ba, tunda ta dena ɗaga wayarta tasan akwai wata a ƙasa haɗuwarta sa Widad ze iya haifar mata da matsala ne kawai.

Ba zata iya ƙirga adadin saƙonni da kuma kiran da tayiwa Yusuf ba, gefe guda kuma dai zuciyar ta na kwaɗai mata son sanin me mahaifinta ke ƙullawa wanda yasa shi yin mu'amala da wannan mutanen haka, suke ta musu sintiri a gida.

************************************

Anwar ne ya shiga ɗakin Alhaji Nasir da Sallama, cikin sakin fuska ya amsa masa, sedai mahaifiyarsa tana tare da Alhaji Nasir ɗin a wannan lokacin, fuskarsa ta nuna yana cikin damuwa kuma yana son yin magana ne.

Alhaji Nasir yace "shigo mana Anwar"

Anwar ya ƙarasa ya zauna a ƙasan carfet yana sunkuyar da kai, can yace
"Daddy, naji ka yanke wani hukunci, wai dagaske nan da ƙarshen wata zaka aurar da Widad?"

"eh hakane Anwar, halin ƙanwar taka ne se ita, gashi har yanzu ciwon ta yakan tashi, bekamata ace mamanku ta cigaba da ɗawainiya da ita ba, akwai buƙatar itama tayi Aure tunda ta girma"

"Amma Daddy kayi bincike akan wanda zaka bawan kuwa?"

Alhaji Nasir yace  "bafa wani ne ba, Fahad ne ba wai wani guri aka samo mata mijin ba, Fahad ne Abokin ka ɗan gidan Bulama"

Irin mugun kallon da mahaifiyarsa ke jifansa dashi ne yasa ya kasa cewa komai yace  "shikenan Daddy, Allah ya Sanya alkhairi ya kaimu lokacin"

Ya tashi gwiwa a saɓule yana kallon mahaifiyarsa ya bar ɗakina.

Alhaji Nasir yace  "Halima kaman akwai abunda yake damun Anwar amma ya kasa faɗa"

"ba abunda yake damunsa, naga dai kamar ya ɗan damu ne da batun Auren Widad"

"ko dai yana sonta ne?"

Da sauri tace  "A'a kasan halinsa dai da tausayi, da yana son ta ai da tuntuni ya faɗa"

"hakane, aikam da ban bawa Fahad ba da Anwar zan bawa, dukda gaba ɗayansu 'ya' yana ne, amma wata kusan ai tafi wata"

"hakane kam, Allah ya wuce mana gaba"

Bayan ta sallami Alhaji Nasir, ta fito ta tafi ɗakin Anwar, yana zaune a bakin gado ya dafe kai yana tunani, jin motsin shigowarta ne yasa shi ɗagowa ya kalleta, Hajiya Halima tace
 
"kaga Anwar zuwa nayi in sake yi maka kashedi, wallahi tun wuri ka fita daga harkar Auren nan, wai ƙanwar uwarkace ita kota ubanka? Ka shiga hankalin ka na gaya maka"

Fahad yace "Allah ya baki haƙuri, Insha Allah zan kiyaye, amma dai Fahad be dace da Aurenta ba"

"da anyi magana ka iya bada haƙuri ai, ko waze aurawa ina ruwanka, shi ya haifeta ba in ya ga dama yaje ya aurawa kare ita mana ina ruwan wani?"

"Amma Mummy ya zakiyi da Ramla da take mutuwar son Fahad?"

"Ai magana ta ƙare tunda Fahad ze auri mahaukaciya, Allah ya bata wanda ya fishi seta haƙura"

"Amma ba kya tunanin yadda take son shi hakan ya haifar da matsala?"

"Kai rufemin baki, Allah ya tsaremu da matsala ina sake jan kunnenka ka fita daga sabgar yarinyar nan, in kuma kaƙi ji baka ƙi gani ba"

Anwar ya bita da kallo yayin da ta bar ɗakin, ya girgiza kai tare da sauke ajiyar zuciya.

Yusuf yana zaune a mota yana ɗan danna wayarsa yana jiran fitowar Widad, be san ta taho ba kawai yaji ta buɗe motar, da sauri ya ɗago ya kalleta, wato abun nata kullum ƙara gaba yake, yau shigar tata tafi ta kullum muni, kamar yadda ta saba gaban mota ta shiga garin zama seda jikinsu ya gogi juna, amma kowannensu ya basar.
Shiru Yusuf yayi bece komai ba, ta ɗakko wayarta ta miƙa masa, ya karɓa ya duba, kwatancen idan zasuje ne ya sake duba agogon hannunsa ƙarfe tara daidai na dare, zuba mata idanun yayi yayinda itakuma take kallon wani gurin.
Ba zato yaji ta fizge wayarta daga hannunsa tace

"malam bana son kallo"

"Aikuwa kallo kin gamu dashi muddin da wannan shigar zaki fita" ya bata amsa

"shikenan cigaba da kallona karka fasa, wallahi kasa na makara zuwa inda zanje se nayi mummunan ɓata maka rai"

Ta faɗa in a very serious tone, haka yaja motar suka fita, gaba ɗaya jikinsa babu ƙwari yake tuƙin.

Yusuf be tsinke al'amarin ba seda yaga sun iso wani katafaren Club a cikin sabon garin Kano, kallon Widad yake yaga me zata yi ganin yadda zaratan karuwai da 'yan iska ke shiga suna fita a gurin.

Yunƙurawa tayi da nufin buɗe ƙofar taji yasa lock, ta kalle shi tace "buɗeni zan fita"

"kije ina?"

"inda ka aikeni" ta faɗa cikin fushi

Gyara zama yayi ya ɗauke kansa daga kallon ta.

"magana fa nake maka"

"idan har na bari kika shiga wannan gurin a haka, ba yiwa kaina adalci ba kuma Allah ze kamani da laifin cin Amana"

"Dalla ka rufemin baki, ina ruwanka da nine? Ina ruwanka da rayuwata na gaya maka kadenamin shishshigi fa bana so, ina kunyar Daddy ne ba dan haka ba da tuni na daɗe da karta maka rashin mutunci"

Kashingiɗa Yusuf yayi yace  "kin daɗe baki yi ba, rashin mutunci wanne ne bakimin ba, ba wanda ban gani ba, dan haka duk wanda kika yi zan shanye amma ba zaki shiga gurin nan ba"

A cikin matuƙar hasala tace  "ka buɗemin ƙofa Malam, nima karuwanci nazo yi gurin nan ka ƙyaleni inyi rayuwar da naga dama"

"Aikuwa da ajinki ya zube beb, duk yadda kike yanƙwana gayu kizo nan kiyi karuwanci ba class, ki canza guri mana"

Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyarta, wai ita Widad yau direbanta yake yanƙwanawa yana raina mata hankali yadda yake so, hakan be taɓa faruwa ba a tarihin rayuwar ta

"Naji ajin nawa ya zube, malam ka buɗen ƙofa nace"

Ramawa Yusuf yayi kamar yadda takewa mutane, yayi kamar baya jin me take faɗa.

Jikinta har rawa yake saboda masifa tana zazzagawa Yusuf faɗa, a zafafe ta miƙa hannu zata yi unlocking ɗin motar Yusuf ya riƙeta, a tare suka ji wata irin faɗuwar gaba, Jikin Yusuf har rawa yake dan besan yadda akayi ya riƙeta ba, yayin da nata ƙirjin ya dinga bugawa fiye dana Yusuf.

Tattaro Jarumtarsa yayi ya maida ita seat ɗinta, ya saka mata seat belt yaja motar ya bar gurin.

Widad zata iya cewa tunda take bata taɓa haɗuwa da mutumin daya raina mata hankali kamar Yusuf ba, dukda yana matuƙar yi mata biyayya tabbas yau ya tsallake iyakarsa, da yasan me tazo yi a Club ɗin da be mata haka ba, dole ta nuna masa munin kuskuren daya aikata yau, bata kuma ce masa uffan ba.

Ta naji tana ganin ya maida ita gida, zuciyarta na cigaba da tafasa kamar ta tsaga ƙirjinta.

Seda suka koma gida sannan yayi parking, ya fito ya buɗe mata ƙofar motar, ta fito ta tsaya ta saka idonta a nasa tace

"ban taɓa sanin baka da hankali ba se yau, kana tunanin na manta da contract ɗin daka sawa hannu? Harka samu damae da zaka nunamin ban isaba, saboda jahilci da rashin tunani irin na talaka, kasan me na jeyi gurin? Har zaka nunamin isa da Izza, ina ruwanka dani meyasa kake son zaƙewa cikin al'amuran rayuwa ta?, ko dan ina ɗaga maka ƙafa shiyasa kake ƙoƙarin takani, yau zan nuna maka ka saɓamin doka kuma dole ka karɓi hukuncin abunda kayi, banza mara amfani ka lalata min komai saboda Jahilci da son nuna kai wani ne, kamin hauka da wauta ka wargazamin komai saboda ƙaramin tunaninka, Amfaninka shine kamin aiki in biyaka amma ka zaƙe, dan haka zan nuna maka kai ba wata tsiyar bane a gurina kuma ka tsallake gona da iri "

Shiru Yusuf tayi seda ta gama sannan ya kakmeta yace " da bani da amfani da Allah be halicceni ba, babu wata halitta da Allah yayi wadda bata da amfani, tunda bani da Amfani zan ƙyaleki ki amfani kanki, tabbas da Allah yayi kowa me kuɗi da babu wanda zeji daɗi, kuma babu wanda ze mori wani, talaka yana da amfani, muma ba laifi mukayi wa Allah yayi mu a ƙarƙashin ku ba"

Yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko key ɗin motar, ya kamo hannunta yace "bani da Amfani, dan haka ki nemo me Amfani ya cigaba da yi miki aiki, idan harni ɗan halak ne bazan ƙara miki aiki ba, ga mukullayenki nan talaka mutum ne kuma yana da zuciya tunda iyayene suka haifemu kamar yadda aka haifeki"
. Ya ɗanƙa mata key ɗinta a hannu, jifa tayi da mukullayen tace "baka isa ba, wallahi yadda kasa hannu a takardar yarjejeniyar ka fara aikin seka kammala shi, se anje ƙarshe da kai"

"sedai ki nemo me Amfani yayi miki amma bani ba"

cikin gida da sauri, hakan yayi daidai da shigowar motar Anwar.

Tana zuwa ɗaki tayi jifa da kayan hannunta ta shiga sintiri hawaye na bin idonta tace  "shikenan babu wanda ze fahimci halin da nake ciki? Wannan banzan ya ɓata min shirina ya wargaza komai, me yake tunani ne? Har na bashi damar daze shiga rayuwata haka ya yanke min hukunci, yanzu ina hukunta shi kuma Daddy ni ze ɗorawa laifi"

Anwar ne ya shigo da sauri ɗakin yace  "Widad lafiya kuwa? Meke faruwane?"

Girgiza masa kai tayi tace "bakomai"

"a'a ya bakomai naga kamar kuna cacar baki da direbanki, kuma gashi kina kuka meyafaru"

Shiru tayi masa ta wuce kan gadonta tayi zamanta.
Kusa da ita yaje ya zauna yace  "dawowata naga abubuwa daban daban wanda suka bani mamakiba gidan nan, wanda ban gane kansu ba, gashi Daddy yace wai Aure ze miki, meyasa zaki Auri Fahad"

Kallon Anwar tayi amma taƙi cewa komai.

"Say something please"
Lumshe ido tayi taƙi magana, duk yadda Anwar yayi taƙi magana haka ya ƙyaleta ya bar ɗakin jiki ba ƙwari.

Yusuf kam har ya koma gida zuciyarsa na tafasa, wai shine mara Amfani a tarihin rayuwarsa babu irin kalar cin zarafin da ba'ayi masa ba ya jure, Amma yau na Widad yaji zafinsu sosai.
Haka ya ƙarasa gida, Umma ta lura tunda ya dawo baya walwala sosai dan haka tace  "tilo meke faruwane? Naga kamar ranka a ɓace yake"

"bakomai Umma"

"bana son fulatanci fa, ko kana da wanda zaka gayawa damuwar ka bayan ni?"

Girgiza kai yayi yace  "Umma na rasa abunyi gaba ɗaya, Anyiwa Abbas transfer, yarinyar da nake wa aiki mun samu matsala na ajiye aikin, gashi ban sanar da shugabanni na ba kafin in yanke hukuncin, kuma ba aikin direba kawai nake mata ba kare lafiyar ta nake, ba ƙaramin hatsari take ciki ba ga mahaifinta wai Aurar da ita zeyi, Umma abubuwan dayawa nama rasa me zanyi "

"Allah sarki Jarumin ɗana, tun tasaowarka da jarumta na sanka da juriya meze sa ka karaya a wannan lokacin? Ni kaina ina jin tausayinka amma kasa Allah a lamarin ka sannan kayi haƙuri da komai, ɗaukaka bata zuwa ana kwance ba zato Aka ƙara maka matsayi a gurin aiki, jajircewarka ce tasa suka baka, dan haka ka zama Jarumi Yusufa, nan gaba iyali zaka riƙe kaga zama da mata se kayi haƙuri se Jarumin gaske, lokuta da dama bama gane Amfanin mutum se bayan ya matsa daga kusa damu"

Kallon Ummansa yayi yace  "wani irin iyali kuma?"

"kayi Aure mana kaima ka hayayyafa, nima inga jikokin tilon ɗana"

Girgiza mata kai yayi yace  "na yanke ƙauna Umma, kiyi haƙuri mu ƙarasa rayuwar mu a haka, nima na isheki"

"haba Yusuf, me rai ai baya yanke ƙauna daga rahamar ubangiji, dole kayi Aure wataran"

"Umma bana son tarihi ya maimaita kansa, bana son abunda ze sake ɗaga mana hankali, dan haka mu bar wannan maganar seda safe"

Ya miƙe yana tafiya a hankali ya bar ɗakin, Umman Yusuf ta dafe kai tace  "Allah ka kawo mafita da sauyi na alkhairi ga rayuwar wannan bawa naka, Allah ka kawo masa mafita ka yaye masa damuwarsa"

Yusuf ya kashe wayoyinsa gaba ɗaya, baya fita ko'ina kullum yana gida, Dama bashi da wasu abokai a unguwar, dan haka baya zuwa ko ina.
Umma bata takura masa ba ta ƙyaleshi.

Widad kam tun daga ranar ko falo ta dena fitowa, Daddy kam dama ba shiga harkarta yake ba, se bayan tafiyar Yusuf ta gane Amfaninsa ta ɓangarori daban daban, gashi taga dagaske Yusuf ya dena zuwa gidan kwata kwata.

Haka nan Alhaji Nasir yaji ya damu da son ganin 'yar tasa dan ba ƙaramin missing ɗinta yake ba, yanzun ma ya danne zuciyarsa ne kawai dan ya samu ta saduda amma abun ba sauyi.

Part ɗinta ya tafi domin ya ganta, sedai yana zuwa bedroom ɗinta ya tarar ta rurrufe ko'ina, da sauri ya ƙarasa ya tura ƙofar ɗakin nata, ɗakin duhu ta kashe fitulun ɗakin, kunna fitilar ɗakin yayi haske ya gauraye ko ina, yana kunna fitila ta saka ihu ta shige cikin bargo.

Da sauri Daddy ya ƙarasa yace  "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Babyna nine fa Daddy ne ɗago ki ganni"

Dunƙulewa ta sake yi tana karkarwa, a hankali ya ƙarasa ya ɗagota sedai taƙi yadda su haɗa ido.

Daddy ya girgiza kai yace  "ciwon ne ya dawo again? Kalli Yadda kika rame lovely, subhanallah meke damunki ne haka?"

Ba tace komai ba sedai kwantar da kanta da tayi a jikin Daddyn nata, jikinta kamar ana girgizata.

Yusuf ya ɗakko tsohon layinsa yasa a waya, sedai yana sakawa yaga saƙonnin Nurat na shigowa, messages ɗin ya shiga dubawa ɗaya bayan ɗaya sedai yana cikin dubawar kiran Nurat ya shigo wayar, kamar kar ya ɗaga amma ya ɗaga yace

"Assalamu Alaikum"

Wata nannauyar ajiyar zuciya Nurat tayi tace "Aboki anya duniya da gaskiya, ka manta dani ko?"

"haba ƙawata, ya zan manta dake light, wayata ce ta lalace shiyasa"

"Allah sarki, duk hankalina ya tashi na zata wani abun ne ya same ka"

"ba abunda ya sameni light fatan kina lafiya"

"Lafiya ƙalau, amma ina son ganinka ne Aboki"

"me zaki bani in kin ganni?"

"magana nake so muyi"

"muyi ta a waya mana light, abubuwa sunmin yawa sosai"

Ajiyar zuciya tayi tace  "zefi kyau dai in ganka, mahaifina ne naga yana harka da wasu irin mutane wanda da ganinsu kaga marasa kirki, ga yawan zuwa gidanmu dasu Alhaji Musa suke yi, kace idan naji wani abu wanda zesa a cutar da Widad in gaya maka, amma dai ban san meke faruwa ba"

Gaban Yusuf ne ya faɗi cikin sauri yace  "a ina zamu haɗune Nurat?"

"nace ina son ganinka kace ba lokaci, amma da yake nayi maganar Widad shine kace zaka zo"

"yi haƙuri Light"

Nurat tace "sedai kazo gidanmu, babana yana gari baze yuwu mu haɗu ba"

"shikenan insha Allah, zan san yadda zanyi mu haɗu"

"Aboki baka gayamin sunanka ba fa"

"ƙawa zan gaya miki very soon insha Allah, dan Allah in an samu wani update ɗin ki sanar dani, sannan akwai ajiyata a wayarki ki kula sosai light"

"Ajiya kuma? Wace irin Ajiya?"

Murmushi Yusuf yayi yace
"Light, light tabbas ina da Ajiya a gurinki, dan Allah ki kula da kanki da kuma wayarki, idaan nazo zan nuna miki ajiyar"

"shikenan Aboki, amma dan Allah ka dena rufe wayarka"

"to shikenan insha Allah"

Tunda Yusuf yaji labarin nan hankalinsa ya tashi, ya shiga tunanin ya Widad take, ba shiri ya miƙe ya shiga shiryawa.
Ya fito tsakar gida, Umma ta kalle shi tace "se ina kuma?"

"zanje gidansu Widad ne?"

"yau kuma, to Adawo lafiya"

Ya amsa da Allah yasa.

Yana zuwa gidan Isa yace "Yusuf ina ka shigane ka dena zuwa gidan nan kusan kwana tara, me gida yasa an kiraka a waya shima ya kira amma layinka baya shiga, ka dena zuwa ba tare da wani dalili ba"

Bece komai ba ya shiga cikin gidan da sauri, yana zuwa ɓangarenta ya nufa ya tarar bata nan, ya fito babban falo yaga Amal.

"Amal dan Allah ina Widad ne"

Banza tayi masa taƙi ce masa komai Anwar ne ya shigo hannunsa riƙe da leda yana ganin Yusuf yace  "bawan Allah kwana da kwanaki ake nemanka baka zuwa, daga samun saɓani ka ɗauke ƙafa Uwar ɗakinka na neman rasa ranta.

Ba ƙaramin razana Yusuf yayi ba yace " tana ina? "

Anwar yace " tana ɓangaren Daddy "

Da sauri Yusuf ya nufi sashin na Alhaji Nasir yana shiga ya tarar da Widad a zaune Daddy yana ta aikin rarrashi tace Abinci amma taƙi se kuka take.

Daddy na ganin Yusuf yace  "Alhamdilillah, Yusuf ashe zaka dawo saura ƙiris in fita nemanka da kaina"

Yusuf seda ya firgita Widad ta zabge gaba ɗaya, ta rame sosai ta ƙara haske idanunta a kumbure, juyawa tayi gaba ɗaya taƙi kallon inda Yusuf yake.

Yusuf yace  "Yallaɓai bata da lafiya ne?"

"ciwonta ne ya tashi, ta fara samun sauƙi naga baka zuwa na tambaya, tace min rigima kukayi ka dena zuwa, na mata faɗa naga ta sake shiga damuwa ga kuma batun Auren nan, ta dena cin Abinci ko magana taƙiyi, se kuka munyi magana da wani abokina a Abuja yace akwai babban likitan Ƙwaƙwalwa a international Hospital yana zuwa ranar Talata, idan ba zaka damu ba dan Allah ina so ka temakamin ku tafi tare, na yadda da kai Yusuf nasan ba zaka cutar dani ko 'yata ba, tafiyar tazo daidai da taronmu na shekara idan banje ba akwai matsala, seku sauka a gidan Abokin nawa kuje Asibitin daga nan duk abunda kukayi kuka gama ranar Monday jirginta ze ɗaga Zuwa England, ta koma taje ta ɗan huta, kafin in san me ya kamata inyi, naga tafi samun nutsuwa a can"

Jiki a sanyaye Yusuf yace " Shikenan an fasa Auren nata?"

"eh munyi magana da Bulama, mun yanke shawarar ɗaga Auren se ta samu sauƙi, idan babu matsala baka da wani abunda zakayi ban takura ka ba seku tafi"

"Shikenan Yallaɓai zanje in shirya insha Allah, Allah ya bata lafiya ko nan da birnin Sin ne zanje insha Allah "

"to shikenan masha Allah, nagode sosai Allah yayi Albarka ya jiƙan mahaifa, tafiyar safe nake son kuyi dan kuje da wuri, jibi in Allah ya kaimu zamu kwana a gidan gona, da an idar da sallar Asuba seku tafi, nace kubi jirgi tace A'a"

"Ameen ya Allah Bakomai Yallaɓai, zanje in shirya insha Allah"

Yusuf a ransa yace 'dole inje wannan tafiya, duk cikin aikina ne'

Kallon Widad yake amma sam taƙi kallon inda Yusuf yake.

Miƙewa tayi ta bar ɗakin daddyn gaba ɗaya.

Alhaji Nasir yace  "Yusuf tabbas nasan kana da haƙuri, shiyasa kuka daɗe tare da 'yata, kana da matuƙar tasiri a rayuwarta ko yanzu ka canza mata abubuwa da dama na rayuwarta nagode da wannan namijin ƙoƙari da sadaukarwa ga' yata"

"bakomai Yallaɓai Allah yasa a dace, Allah ya bata lafiya"

********************* **************

"Masha Allah, komai yana tafiya yadda muka tsara, komai zezo ƙarshe koda tsiya koda tsiya tsiya se mun mallaki abunda muke so" cewar Alhaji Munir

Alhaji Musa ya kwashe da dariya yace  "tabbas haka maganar ka take, nayiwa yaran nan jan kunne yadda yakamata baza'a samu matsala ba Saleh yace ze sanar damu duk wani abu da ake ciki"

Alhaji Munir yace  "ƙunrunƙus, yayin da muka ɗauke hankalinsa ta ɓangare ɗaya, ɓangare ɗaya kuma baze halarci taron kasuwanci ba"

Suka ƙyalƙyale da dariya gaba ɗaya.

(RASHIN SANI......)

Share and share please 🙏 🙏 🙏 🙏

Domin gyara sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680

                       _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 22_23

Yusuf yaso yabi bayan Widad dan ya duba ta, amma yasan halinta tsaf zata yanƙwanashi, dan haka ya yanke shawarar tafiya kawai.

Office ya wuce kai tsaye, ya tarar da Suleiman yana shirin fita suka gaisa Suleiman yace  "Yusuf akwai wani update ne"?

"Eh yallaɓai gurinka ma nazo"

"shikenan mu koma ciki" suka juya zuwa cikin office ɗin gaba ɗayansu.

Nan Yusuf ya zayyanewa Oga Suleiman komai da yake wakana, akan harkar binciken da batun tafiyar da za suyi, da abunda Nurat ta sanar dashi.

Suleiman yace  "Amma baka ganin mu haɗaka da abokan aiki, suyi muku rakiya a wata motar gudun samun matsala?"

Yusuf yace  "Insha Allah babu wata matsala Oga, kasan a slide mistake yarinyar nan zata iya ganewa nikuma bana son ta gane komai a yanzu har bincikenmu ya kammala".

"shikenan Yusuf Allah yayi mana jagora, Insha Allah zakayi Nasara ana ta samun haske akan lamarin, bari ni zan fita ne yanzu zanje headquarter"

"to shikenan Yallaɓai a sauka lafiya"

Bayan tafiyar Suleiman Yusuf ya fito yana shirin tafiya, Suka haɗu da Sakina, Sakina tace 

"Ashe yau ka samu ka shigo, ban samu na maka murnar ƙarin matsayi ba, Allah ya tayaka riƙo"

Yusuf yace  "Ameen nagode"

"sannan ina tayaka murnar rabuwa da mugun aboki wato Abbas"

Cikin mamaki da rashin fahimta yace "kamar yaya?"

"Kamar yadda na gaya maka, Allah ne ya dube ka ya rabaku, a baya nasan koda na faɗa ba zaka yadda ba, yanzunma ban sa ran ka yadda ba amma wataran zaka ce na gaya maka, Allah ya bada sa'a ya tayaka riƙo"

Tayi gaba ta bar Yusuf a gurin yayinda ya bita da kallo.

Da Yusuf ya koma gida yayiwa Umma bayanin tafiyar da zasu yi ya raka Widad, da farko taƙi yadda tace sam bata san zance  ba.

Yusuf yace  "haba Umma, ya za'ayi nida na ɗau Alƙawarin Yiwa jama'a aiki aikin ya taso kice baza'ayi ba, bayan ke kike cewa inyi gaskiya a aikina? Kina so in bari a cutar da ita ne, ba zan iya jure in ga wani mummunan abu ya sameta ba"

"nifa na kasa gane meke wakana tsakaninka da wannan uwar ɗakin, ka damu da ita dayawa"

"ba wani abu da yake wakana Umman Yusuf, kawai dai mahaifinta na mutuntani ne sosai"

"shikenan Yusuf, Allah ya bada sa'a zanyi kewarka zakayi kwanaki ba tare da Umma ba"

Yusuf yace  "nikaina ina tunanin hakan, Amma insha Allah ba abunda ze faru kwana biyar ne kawai tafiyar"

"to Allah ya bada sa'a"

Ya amsa da "Ameen"

Haka nan Umman Yusuf take jin kamar akwai wani abu daze faru dalilin tafiyar nan, sedai ta kasa gane na daɗine ko akasin hakan.

Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, Yusuf ya shirya jakarsa da kayansa da ze dinga sawa da ɗan sauran kayan buƙatarsa a traveling bag.

Yaje gaban Ummansa yace "Umma na fito zan tafi, zan kwana a gidan gobe in Allah ya kaimu da Asuba zamu tafi"

Umma ta riƙo hannun Yusuf tace  "ka kula da kanka Yusuf, kai kaɗai ka ragemin, Allah yayi maka Albarka ya sadaka da dukkan Alkhairi, Allah yayi maganin maƙiyanka ya karemin kai.."

Kasa ƙarasawa tayi ta fashe da kuka, gaba ɗaya jikin Yusuf yayi sanyi yace "Umma ko in fasa tafiyar nan?"

Ta girgiza kai da sauri tace  "A'a bakomai yi tafiyarka, ban san kayi nesa dani ba shiyasa naji ba daɗi"

Haka sukayi Sallama ya tafi.

A can gidansu Widad da yaje, yaje ya sameta a ɗakinta tana ta aikin kuka, magenta se kewayata take itama tana kuka gwanin ban tausayi.

A sanyaye Yusuf yace  "waike abun kuka baya miki wahala, kiyi ta azabtar da rayuwarki, kiyi haƙuri ki dena kuka koma meye yake damun ki Allah yana sane dake"

Sallamar Alhaji Nasir ce ta katse Yusuf daga maganar da yake yi

"Yusuf ka shirya ne?"

"Eh ranka ya daɗe na shirya ni"

"to shikenan ta haɗa nata kayan, bayan la'asar semu tafi can farm house"

Yusuf yace "to shikenan ranka ya daɗe"

Alhaji Nasir yace "daughter ki tashi ki haɗa kayan naki, ya kaiki gidan daddynki Bulama kuyi sallama"

Cikin kuka Widad tace "bazan ƙara zuwa inda yake ba, baya sona yafi san ɗansa"

Alhaji Nasir yace  "Allah ya baki haƙuri tashi ki hada kayan, ko inyiwa Halima magana tasa a haɗa miki"

"Ni ba wanda ze haɗamin, zanyi da kaina"

Haka Widad taita daru san ranta, Daddy ya dena mata faɗa lallaɓata yake yanzu.

************************************
"Daddy wai yanzu shikenan an fasa ɗaura mana Auren?"

Bulama yace  "Eh, an ɗaga dai akwai buƙatar taga likita, har yanzu bata da lafiya"

"Daddy wane irin likita kuma? Naga dai da hankalinta ba hauka take tuburan ba"

"eh mahaifinta ne yacemin akwai buƙatar a barta ta ɗan huta, dan gaba ɗaya tana nema ta illata kanta, ta damu sosai bata son Auren nan, dan haka ma zata Wuce England ta huta"

"wace irin maganace wannan, an samin rai kuma ace an fasa?"

Mahaifiyar Fahad dake gefe, tunda suka fara magana ba tace komai ba se yanzu tace 

"kai Dalla Allah ya rufa maka Asiri kana nema ka tonawa kanka, Allah ya rabaka da Auren mara tarbiyya mahaukaciya"

Fahad yace  "Ni gaskiya ina sonta a haka, kuma nasan Anwar ne yaje ya kai gulma ta gurin Alhaji Nasir, shiyasa yace haka, ko yana so ko baya so se anyi auren nan dani mu zuba mu gani"

Bulama na ƙoƙarin dakatar da Fahad, amma yaƙi tsayawa ya fice.

Yana fita ya ɗau mota ya nufi unguwar su Widad, yana zuwa beyi wata wata ba ya nufi boys quarters inda Sashin Anwar yake, Anwar yana zaune yana kallon labarai Fahad ya shigo bako sallama.

Anwar yace  "Lafiya zaka shigomin ba sallama?"

"dole ka tambayi lafiya mana, ai ban san haka kake ba, ban san ka iya munafunci ba se yau, saboda rashin son cigabana shine ka shiga ka fita aka ɗaga Aurena da Widad bayan ina can inata shiri"

"kamar yaya kenan? Waye ya gaya maka ni na hana aurenku ko nace a ɗaga?"

"Au kai tunaninka wanine ya gayamin, bayan da bakinka kazo ka faɗamin, kayi Nasara Amma kasani Aure yana nan daram tsakanina da ita kuma se nayi maganinka"

Anwar yace  "Yanzu Fahad akan Mace kakemin wannan cin mutuncin? Ina ɗan uwanka kuma abokinka?"

"na maka ɗin, haifata kayi da ba zan maka ba?"

"Ni bam rufe ido maci mutuncinka ba saboda cin amanar abota na amincewa da Auren Yarinyar da nake so, se kaine zakamin?"

Fahad yace "Ai ban ma yi maka komai ba, kuma wallahi ko bangon duniya zata zan bita sena Aure ta"

Anwar ya kashingiɗa a jikin kujera yace "Ashe dai haɗin da'akayi ita za'afi cuta, saboda naka haukan yafi nata fitowa"

"Anwar ni kake cewa mahaukaci?"

Banza Anwar yayi masa be kuma ce masa komai ba

"zakaga ƙarshen rashin mutunci kuwa"

"Ya ƙare akanka" Anwar ya bashi Amsa

A fusace Fahad ya baro part ɗin Anwar yana huci, yana ƙoƙarin shiga motarsa Ramlah ta ƙaraso da sauri tana faɗin haba "Fahad yanzu har kazo gidan nan amma ka tafi ba tare da ka ganni ba"

"Am sorry, zuwan gaggawa ne shiyasa yakike?"

Ramlah tace  "gaskiya ban yadda ba, kazo mu shiga ciki"

"A'a Ramlah ina sauri ne, zamu haɗe insha Allah"

Ya shige mota ya bar Ramlah a gurin.

Da Yamma ƙarfe huɗu Yusuf ya shiga gidan, sedai yaga Hajiya Halima na masa wani irin mugun kallo, wanda be gane dalilin hakan ba, ko kulata beba ya wuce part ɗin Widad.
Tana zaune a gefen gado tana shafa jikin magenta, tayi shiru kana kallonta zaka san ɗauke take da damuwa.

Yusuf yace "Ya jiki kuma?"

Wata uwar harara ta aika masa ta ɗauke kanta.

Akwatunan ta data shirya manya guda biyu da ƙarama, abun har mamaki ya bawa Yusuf me zata yi da wannan uban kayan haka oho?

Ya ɗauki trolleys ɗin ɗaya bayan ɗaya ya kaisu Mota.

Alhaji Nasir ya fito cikin shirinsa tsaf, yaje ya fito da Gimbiyar 'yar tasa a falo yana shirin fitowa Hajiya Halima ta tarar da shi tace  "Nifa Alhaji ban gane ba? Ina zaka ne haka ba bayani, naga har ana fita da akwatuna"

Alhaji Nasir yace "eh zamu ɗan fita ne, ba zamu kwana a gida ba Lovely zataje Abuja ganin likita daga nan kuma zata wuce UK"

"Amma shine baka gayamin ba se yanzu, sekace kana zaman gaba dani? Ace Widad zata tafi amma baka gayamin ba"

Wata uwar harara Widad ta aikamata dashi haɗe da tsaki tayi waje abunta, Yusuf ma be tsaya a gurin ba yabi bayan Widad a hanyar da zasu fita harabar gidan Amal tace  "Allah ya raka taki gona, ma huta na kwana biyu kafin ki dawo, kai kuma ka dawo ka sameni"

Daga Yusuf har Widad ba wanda ya tanka mata sukayi gaba, kamar kullum gaban motar ya buɗe mata ta shiga, shima ya zagaya ya shiga suna jiran fitowar Alhaji Nasir.

Kusan mintuna sha biyar sannan ya fito shima ya shiga motar, Anwar ne ya fito ya ƙaraso da sauri yace "ina zakuje ne haka Daddy?"

Alhaji Nasir yace "zamuje farm house ne, gobe in Allah ya kaimu Yusuf ze raka Lovely zataje ganin likita Abuja, idan ta gama zata koma England ta huta"

Turus Anwar yayi yana kallon su, jiki a sanyaye yace "Shikenan, A dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya"

Ya juya ze koma BQ, da sauri Widad ta buɗe motar ta kira sunansa, ya tsaya ta ƙarasa da sauri inda yake ta kalle shi tace  "Anwar lafiya kuwa?"

Anwar ya ƙaƙalo murmushi yace "lafiya ƙalau Widad"

"Amma naga mood ɗinka ya canza"

"zanyi missing ɗinki ne"

Ɗan tsayawa tayi tana kallon sa, jiki a sanyaye tace "Anwar haka kurum naji bana son tafiyar nan, ji nake kamar akwai abunda ze faru a tafiyar nan, dan Allah idan na tafi ka kularmin da Daddy dan Allah ji nake kamar wani abu ze sameshi idan na tafi "

Tai maganar hawaye na bin fuskarta.
Anwar yace "Widad akwai matsala ne?"

Girgiza masa kai tayi tace "ni dai ka riƙemin Amana dan Allah"

"shikenan karki damu, Insha Allah zan kula dashi, zakije ki dawo ki sameshi lafiya"

Ta jinjina masa kai tayi murmushi tace  "Nagode Anwar"

Ta juya ta koma mota, shikam Yusuf wani takaici ne ya ƙule shi yadda taje ta tsaya tana magana da Anwar.

Yusuf yaja motar suka nufi gidan gona, tunda ma'aikatan suka ga tare da Alhaji Nasir ne suka dinga tururuwar zuwa kwasar gaisuwa, dan ya daɗe beje gidan gonar ba, nan ya dinga musu fara'a ya zolayi wannan ya zolayi wancan yana musu kyautar kuɗi.

Saleh ne ya shigo harabar gidan ya ƙaraso gaban Alhaji Nasir yana murmushi yace  "Barka da sauka Alhajin Allah yaushe rabonka damu a gidan nan, sedai muji labarin kazo gari
"

Alhaji Nasir yace  "Abubuwa ne sunyi yawa Saleh ya aikin, ya haƙuri damu?"

Saleh yayi murmushi yace "Yallaɓai ai kuke haƙuri damu"

"to Allah ya ƙara mana haƙuri da juna, zan maka transfer ɗin kuɗi aje ayo order Abinci gaba ɗaya ma'aikatan gidan nan Vip kowa yaci ya ƙoshi"

"Allah ya temakeka Alhaji namu, Allah ya ƙara nisan kwana da Arziki me Amfani"

Alhaji Nasir yace "Ameen Saleh, soja marmari daga nesa"

Saleh yayi murmushi ya fita, yana fita ya samu wani guri ya laɓe ya ɗakko wayarsa ya daddana yasa a kunnensa

"Oga sunzo, kuma da alama a gidan nan zasu kwana gaba ɗaya"

"shikenan kasa mana ido akansu sosai, sannan ka lura da motar da zasu yi tafiyar a cikinta kasa tracker dan karsu tafi kafin su Dage suje"

Saleh yace  "shikenan as you wish, amma dan Allah karku saɓa Alƙawari"

"karka damu kai dai kayi abunda muka ce"

Alhaji Nasir ya turawa Seh kuɗi, yayo order Abincin ma'aikatan gidan nan kowa yaci yasha yana walwala, aka kaiwa Alhaji Nasir nasu, Alhaji Nasir ya haɗe nasa da na Yusuf yace suci tare, ba ƙaramin mamaki abun ya bawa Yusuf ba, ace babban mutum kamar Alhaji Nasir yace zeci Abinci kwano ɗaya da ma'aikacin 'yarsa lallai be ɗau duniya da zafi ba.

Widad kam sam bata walwala, Ƙarewa ma ɗaki ta ɗaya ta samu ta shige tayi kwanciyar ta.

Yusuf kam suka zauna da Alhaji Nasir suna ta hira, kamar ɗa da Uba yana bashi labarin tafiye tafiyen da yayi da ƙalubalen kasuwanci da kuma nasarorin daya samu.

Can Alhaji Nasir ya nisa yace

"kaga gidan nan shine gidana na asali, ina jin daɗin unguwar nan amma tun bayan rasuwar mahaifiyar Widad naga bata son zaman gidan, saboda ita na canza gida, nan kuma aka zuba dabbobi a wani ɓangaren saboda tama son dabbobi"

Yusuf yace  "Allah sarki, tabbas naga tana matuƙar son dabbobi kam"

 Alhaji Nasir yace "Yusuf dan Allah ka ƙara haƙuri da 'yata, na yaba sosai da ƙoƙarin ka Allah ya saka maka da Alkhairi, dan Allah idan ta gama ganin likitan, ranar da zata bar ƙasar nan dan Allah ka tabattar jirgunta ya tashi, da ni naso in kaita da kaina, amma akwai taron kasuwanci na shekara da nake halarta, idan har ban halarta ba akwai matsala ga dukiyata, wadda take gauraye data al'umma"

Yusuf yace "dukiyar ka data al'umma kuma?"

Alhaji Nasir yace "Eh mana, akwai hannun jarin mutane a cikin kasuwanci na, wanda ciki harda masu ƙaramin ƙarfi idan har ban halarci taron nan ba to tabbas dukiyoyin wasu zasu halaka"

"Amma meyasa dukiyar wasu zasu halaka, dan baka halarci taron ba? '

Alhaji Nasir yayi murmushi yace
" karka damu, idan Allah yasa kuka dawo zan gaya maka yanzu dare ya fara yi "

Yusuf a ransa yace" to ko dai Alhaji Nasir yasan maƙiyansa ne? "

A fili kuma yace "Amma yallaɓai kana ganin za' a samu Nasara idan taga wannan likitan?"

"To abun duk lalabune a duhu Yusuf, bamu san inda zamu dace ba"

Suna cikin maganar saƙo ya shigo wayar Alhaji Nasir, ya ɗakko wayar ya duba
Jikin Alhaji Nasir ne ya kama rawa, a ɗan gigice yace
"Amm.. Ammm Yusuf jeka ka kwanta dare yayi, saboda ku samu ku fita da wuri gobe in Allah ya kaimu, kabi wannan varrender akwai ɗaki yana kallonka acan zaka kwanta"

Yana gama faɗin haka ya shige wani ɗaki ya rufe ƙofa, mamaki ne yakama Yusuf ya miƙe ya nufi inda Alhaji Nasir ya kwatanta masa ya shiga.

Masha Allah, ɗakine tangameme babu abunda babu na jin daɗin rayuwa a ciki, gadon kansa abun kallo ne kamar ka sace ka gudu, hotunan Widad ne ko ina a ɗakin, Yusuf ya dinga ƙare musu kallo, idonsa ya sauke akan haɗaɗɗen hoton Widad.

Tayi kyau sosai tayi murmushi cikin wata jar doguwar riga, ta baje gashin kanta kamar ba ita ba.
Ya daɗe yana kallon hotunan dake jikin bango, sannan ya ajiye jakarsa, yana sake ƙarewa ɗakin kallo.

Ya shiga banɗakin yayi alwala ya dawo yayi nafilfili yayi karatun Al'qur'ani da addu'oi sannan ya nemi guri ya kwanta.

Wajen ƙarfe biyu na dare cikin bacci Yusuf yaji muryar Alhaji Nasir na rawa yana kiran sunan Yusuf, a gigice Yusuf ya farka ya tashi zaune.

Alhaji Nasir ya kamo hannun Yusuf yace "taso Yusuf akwai matsala"

"matsalar me Alhaji?"

"Yusuf rayuwar Widad, ni idan tawa ta salwanta bakomai, bana son Widad ta rasa Ranta"

Cike da mamaki haka Yusuf ya biyo bayan Alhaji Nasir,  suka tarar Widad na tsaye a falo tana kuka, gaba ɗaya Yusuf ya rikice yace

"Alhaji meke faruwa ne"

Jiki na tsuma Alhaji Nasir ya miƙawa Yusuf wayarsa

"RANA BA TA ƘARYA SEDAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA, YAU ZAMU KAWO ƘARSHEN WASAN KURAR DA MUKE, KODAI KA YADDA KA BAMU ABUNDA MUKE BUƘATA KA HALARCI TARON KASUWANCI, KO KUMA KA HANAMU KA RASA RANKA DA NA 'YARKA, KOMU KASHE TA AGABANKA MU BAR MAKA MUGUN TABO, WATAƘILA HAKAN YASA KA BAMU ABUNDA MUKESO"

Yusuf yace "to koma mene ka basu mana, saboda rayuwar ka da tata su tsira"

"Yusuf ni kaina abunda suke so in basu ba nawa bane, nayiwa kaina Alƙawarin bawa meshi abunsa, dan haka bazan basau ba"

Yusuf yace  "to ko ka kira jami'an tsaro"

"A' a Yusuf hakanma matsala ne, dan Allah ka ɗau Widad ku tafi maza ku tafi yanzu"

Fashewa da kuka Widad tayi tace  "Ni bazan tafi na barka ba Daddy, bana son wani abu ya same ka, Daddy bana son tafiya kai kaɗai ka ragemin"

Dattijon yana zubar da hawaye yace

"Widad bana son rayuwarki ta salwanta, nima ke kaɗaice dani, idan suka kama ki komai ya ɓaci, ki tabbatar kin miƙa amanar nan ga masu ita, karki yards ta salwanta ko a karon banza wasu su karɓa, maza ku tafi"

Ƙanƙame mahaifinta tayi tana kuka tace "Daddy ba inda zanje, kome ze faru ya faru muna tare"

Daddy da kansa yaja hannun Widad ya kaita mota, ya kalli Yusuf yace "Allah ya kiyaye ku Yusufa, na yarda da kai ka kularmin da Amana
ta, ka kula da Widad kayi haƙuri da ita, karku sake ku dawo idan bani na kira ku ba, zaman Widad anan tana cikin hatsari mutanen nan dagaske suke"

Haka Yusuf ya shiga motar yaja, Widad tana wani irin kuka me ban tausayi.

Su kansu ma'aikatan sunyi mamakin fitar su Yusuf a wannan daren.

Saleh ne ya samu Alhaji Nasir yace  "Alhaji lafiya kuwa? Meke faruwane haka?"

Daula yace  "Wata 'yar ƙaramae matsala ce, Amma komai ze daidaita insha Allah"

Alhaji Nasir ya koma cikin gidan yana safa da marwa ya rasa abunyi, wayarsa ya ɗakko ya kira Bulama a waya ya sanar dashi halin da yake ciki.

Yusuf kam a besan inda ze nufa ba a wannan tsohon daren, gaba ɗaya sahu ya ɗauke se abunda ba'a rasa ba,gudu yake yana ratsa tituna ba tare da yasan inda ze dosa ba.

Befi mintuna talatin ba sega Bulama yazo gidan a sukwane, suka haɗu da Alhaji Nasir a harabar gidan, Bulama a gigice yace "Daula ina Widad ɗin take yanzu?"

A kiɗime Daddyn Widad yace "na haɗata da direbanta nace su tafi"

"su tafi suje ina?"

'Bulama na rasa yadda zanyi ne, ina tsoron rayuwar Widad ta taɓu, nasan yaron baze cutar da ita ba"

A fusace Bulama yace  "kayi hauka ne Nasiru, kamar ya ka haɗata da direba? Kasan daga ina yake ko kuma ina ze kaita, memakon ka kira' yan sanda kawai seka haɗata da direba idan kuma bakinsa ɗaya da mutanen fa"

Girgiza kai Alhaji Nasir yayi yace  "bana tunanin haka Bulama kaina ya gana kullewa ne"

Alhaji Bulama ya ɗau waya ya fara kiran 'yan sanda.

Sosai Yusuf yake gudu akan titi, yayin da Widad ta dunƙule tana aikin kuka, Yusuf ya kasa cewa komai se tunanin ya zasu tsira, sedai babu zato yaci karo da wata mota anyi parking ɗinta a tsakiyar titi, wani irin parking na rashin mutunci yanda babu damar Yusuf ya iya wucewa, ga gefe jeji ne, yayi reverse ze juya kan motar wata motar tazo ta ƙara rufe bayan tasu Yusuf aka sasu a tsakiya.

Wasu irin ƙarti ne suka fito daga motocin suka kewaye su Motarsu Widad, gaba ɗaya Widad ta rikice ganin suna tunkaro su, suna zuwa suka buɗe ƙofofin motar, suka sawa Yusuf bindinga aka suka ce Widad ta fito.

Ko motsi ba tayi ba balle ta ɗaga kai ta kalle su, cikin tsawa ɗaya yace  "ba magana ake miki ba"

Sunkuyar da kai tayi taƙi motsawa, ɗaya yasa hannu ze fizgota aikuwa ta riƙe Yusuf gam tana kurma ihu

"Yoseef karka bari su tafi dani"

Yusuf ya riƙe hannun ta yace  "me mu kayi muku kuke ƙoƙarin cin zarafin mu akan titi haka"

"zaka rufe mana baki ko semun fasa kanka da bindiga, dalla ku fizgota ta ƙarfin tsiya suna ɓata mana lokaci"

Ai Widad sekace Mayya ko ƙarfe ta riƙe Yusuf gam, wani gigitaccen mari ɗayan ya kwaɗawa Widad yana ƙoƙarin janyo ta, sedai ga mamakin Yusuf mutumin yana sauke hannun sa Widad ta rama marin, dukda a gigice take tace   "karka ƙara gangancin marina, wallahi ka kuma dukana sena rama"

"Ashar ya saki yace lallai wannan yarinyar akwai ƙarfin hali, yau zamuyi maganinki"

Hannu ya kai ze shaƙota, amma Yusuf ya riƙe hannun mutumin yace  "karka kuskura ka sake marinta"

"Idan aka sake marinta me zakayi? Dan Allah oga ka bani dama in fasa kan gayen nan da bindiga"

Shugabansu yace "babu kisan kai a wannan deal ɗin, ban sani ba ko zuwa gaba"

Suka cigaba da jan Widad, Yusuf yaƙi sakin ta, baya son ya zafafa suyi mata illa gashi babu makami a jikinsa.

Yace "idan kunga kun tafi da Widad to tabbas kun kasheni ne, amma ba inda zaku da ita"

Ganin Yusuf na ɓata musu lokaci ga Widad na nema tasa asrinsu ya tonu, bakinta yaƙi rufuwa sunan Yusuf kawai take kira, haka suka haɗa da Yusuf suka sasu a tasu motar.

Suka ƙulle hannayensu, sukayi daji dasu, ihu Widad ta cigaba dayi, gaba ɗaya ta manne a jikin Yusuf sosai tana cewa
"ni ku ƙyalemu, besan komai akai ba, direba nane kawai ku ƙyalemu mu tafi"

Yusuf yace  "kiyi shiru karsu illataki"

Ai be gama rufe bakinsa ba, suka sa ƙyalle suka rufe musu ido.

Widad tasa haƙoranta ta riƙe rigar Yusuf, duk dan kar su raba ta da Yusuf, se haki take tana jin yadda zuciyar Yusuf ke bugawa, Yusuf kam ya yabawa jarumtar Widad yau.

Shikansa Saleh da'aka haɗa baki dashi akayi aikin, ya rikice gaba ɗaya ya shiga damuwa mussman yadda yaga Alhaji Nasir na zubda Hawaye yana kaiwa yana komowa a harabar gidan, Alhaji Bulama nata rarrashinsa amma se kuka yake kamar ƙaramin yaro, zuwan 'yan sanda yayi dai dai da shigowar wani saƙon wayar Alhaji Nasir.

"A ZATONKA KA FIMU WAYO NE, MUN KAMA' YARKA DA DIREBANKA SUNA HANNUNMU, SHAWARA TA RAGE NAKA, ZAMU CIGABA DA AZABTAR DASU, DAN HAKA SEKA KA ZAƁA KO RANSU KOKUMA ABUNDA MUKA NEMA A HANNUNKA"

Yana gama karanta saƙon ya yanke jiki ya faɗi a gurin

In an karanta ayi share please
🙏 🙏 🙏

Gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

_*AƘIDATA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

PART1
Page 24_25

Gaba ɗaya ma'aikatan gidan su kayo kan Alhaji Nasir, sedai jikinsa kamar babu rai, 'yan sanda suka ƙaraso cikin gidan aka kwashi Alhaji Nasir a daren zuwa Asibiti.

Widad kam gajiya tayi da zaman motar, saboda tafiya suke bata wasa ba cikin wani irin azababben gudu, jin tafiyar taƙi ƙarewa ne yasa Widad fara mustu mutsu, tun tana mutsu mutsun har bacci ya kwashe ta, a firgice ta farka ta kurma wani uban ihu tana kiran
"wayyo Allah na Yoseef, karka tafi ka barni"

Yusuf yace "Widad ina nan, muna tare har yanzu Allah ze fitarmu insha Allah, ki dena shouting karsu miki wani abun"

Me tuƙa motar yace gara dai kaja mata kunnen.

Memakon tayi shiru ta cigaba da ihu tana "ku ƙyalemu mu tafi, yoseef na gaji da zaman nan hannuna igiyar nan ta dameni, bayana ciwo na gaji bayana ze karye"

Wata hoda su watsawa Widad, wanda hakan yasa ta baccin dole, ba Widad ba har Yusuf gaba ɗaya bacci ya kwashe su.

Ana kai Alhaji Nasir Asibiti, aka kwantar da shi aka dinga masa allurai da ƙarin ruwa, ga oxygen ansa masa domin temakawa numfashinsa dake barazanar ɗaukewa.

Likitoci suka duƙufa akansa, suna bashi dukkanin taimakon da zasu iya, ga jininsa ya hau fiye da kima suna ta ƙoƙari jininsa ya sauka.

Yusuf ne ya fara farkawa jin motar ta tsaya, aka buɗe motar suka kwance musu ido, mamakine ya kama Yusuf, tun cikin dare suke tafiyar nan amma da'aka kwance musu ido yaga yanayin garin kamar Azahar ta gota, daji ne sosai ciyayi sun lulluɓe ko ina, gaba ɗaya Yusuf baya gane inane gabas ko yamma ya kasa gane ta ina suka zo nan gurin.

Widad kam sam bata hayyacinta, ta farka amma se tangaɗi take haka suka sasu a gaba zuwa wani gini.

Yusuf yayi mamakin yadda aka shigo cikin wannan uban dajin akayi ginin gida, suka buɗe gidan suka shiga dasu Yusuf.

Gaba ɗaya gurin kango ne, kuma ga dukkanin alamu an samar dashi ne mussman saboda wannan aikin, saboda gurin sabon gini ne harda ragowar kayan aikin ginin.

Wani ɗaki suka kai su Widad suka ajiye, akan tsurar tabarma suka kawo musu ruwan pure water guda biyu suka ajiye musu suka maida ƙofa suka rufesu a ciki.

Yusuf ya ɗau ruwa ɗaya ya fasa ya bawa Widad, aikuwa nan da na ta zuƙeshi da alama tana jin ƙishirwar sosai, ga ko salla ba suyi ba haka ya zuba mata ruwa tayi alwala, ɗan ragowar shima yayi ba tare da sun san inane gabas ba haka suka gabatar da salla.

Shiru Widad tayi, gaba ɗaya jikinta ciwo yake ga wata uwar yunwa da take ji, gashi har yanzu jikinta babu ƙwari saboda hodar da suka watsa mata.

Ta kalli Yusuf da yayi shiru ya sunkuyar da kai, gaba ɗaya tausayinsa yakamata duk a dalilin ta wannan masifar ta faɗa masa.

Kifewa tayi a gurin, hakan yasa Yusuf ɗagowa da sauri yana kiran sunan ta, cikin kasala tace "Yunwa nake ji"

A hankali yace "kiyi haƙuri kinji, Insha Allah zamu bar gurin nan, kuma zaki ci Abinci"

Ba tace komai ba ta maida kanta ta kwanta, wani irin sanyi na ratsa ta, miƙewa Yusuf yayi yana zagaye ɗakin harda ban ɗaki sedai an rufe ko ina babu hanyar tsira.

Zagaye ɗakin ya shiga yi yana sake tunanin menene mafita, ya kalli inda Widad ke kwancw ta takure sosai gwanin ban tausayi.

Haka suka wanzu babu me cewa komai tsawon wasu awanni, suka riƙe alwalarsu in sun kintaci lokacin salla se suyi.

Alhaji Bulama ya samu ya koma gida, dan Alhaji Nasir ya farfaɗo ya samu bacci, yana zuwa Matarsa tace "kaikam ina ka tafi haka, na farka na nemeka na rasa na dinga kiran wayarka kaƙi ɗagawa, duk ka ɗaga mana hankali"

"Daula ne babu lafiya" ya bata amsa

Sekuma jikinta yayi sanyi tace "meya same shi?"

"An sace 'yarsa da direbanta, shi kuma ya yanke jiki ya faɗi"

Dafe ƙirji Hajiya Sarah tayi tace "Kamar ya an sace su sekace kaji? Yaza' ayi ace 'ya kamar ta Alhaji Nasir an saceta, suwaye suka sace ta?"

"Mutanen da suke bibiyar sa ne, ni nafi kyautata zaton harda haɗin bakin direban nata"

Sarah ta girgiza kai tace "Amma Alhaji wannan yaron sam neyi zubin Azzalumai ba"

"ke bari, duniyar nan babu gaskiya shi mugu ai bashi da kama"

"Hakane, Allah ya fidda su lafiya, amma an sanarwa jami'am tsaro?"

Bulama yace "eh na sanar musu an fara bincike ma"

Gaba ɗaya Hajiya Sarah ta shiga damuwa, dukda yadda take jin haushin Widad, su Ramadan ma da Iman sin shiga damuwa sosai da jin labarin.

Isa megadi ne ya shigo falon gidan a gigice yana kiran Hajiya.
A fusace Hajiya Halima tace "lafiya kake min wannan kiran kamar wata 'yarka"

"Hajiya babu lafiya fa, muna nan zaune gaho an sace Autar daula da direbanta, shi kuma Alhaji yana kwance a Asibiti"

"to shine me zaka zo kanamin wannan kiran, aita sace tan mana ai hakane ya dace da ita, Allah yasa daga na su kashe ta ma kowa ya huta, fita ka ban guri ka koma kan aikin ka"

Galala Isa ya bita da kallo, "bazaka fita ba sena zo na kwasheka da mari"

Jiki a sanyaye yayi waje yana tunanin, to idan ma bata tausayawa Widad ba saboda tana musu wulaƙanci to Alhajin fa, wanda duk wani gata da jin daɗi a dalilinsa suka same shi.
Yana wannan tunanin yayi karo da Anwar ba tare da ya sani ba.

Anwar yace " lafiya kuwa? Kana tafe baka ganin gabanka"

A firgice Isa ya labarta masa abunda ke faruwa, wata mummunar faɗuwar gabace ta kama Anwar yace "garin yaya Isa? Ina Alhajin yake?"

Isa yace "Ance yana Asibiti, amma bam san wane Asibitin bane, sedai a tambayi Alhaji Bulama"

Anwar yace "shikenan nagode"

Ya nufi cikin gida da hanzari, ya tarar mahaifiyarsa da Ramlah suna ta hirarsu.

Anwar hankali a tashe yace "Mummy kin san meke faruwa kuwa, Daddy yana kwance ba lafiya sannan an sace little"

Cike da salo da iya rainin hankali Hajiya Halima ta miƙe tayi gigicewar ƙarya tace "haba dai waye ya gaya maka, bana son wasa fa"

Anwar yace "ba wasa bane Mummy, ki kwantar da hankalinki, zanje gidan su Fahad inji komai, se inzo muje Asibitin".

"shikenan hanzarta Anwar, innalillahi wa inna ialaihi raji'un Allah yasa ba gaske bane"

Anwar yace "Mummy ki kwantar da hankalinki, ina dawowa" yayi waje da sauri ko ganin gabansa ba yayi saboda tashin hankali.

Duhu ya fara yi sosai, ba wanda yasa wani abu a cikinsa tsakanin Widad da Yusuf, can sukaji hayaniyar mutanen da suka sace su sun shigo, Widad tayi zumbur ta tashi zaune, suka saka mukulli suka kwance sarƙar da suka kulle ƙofar da ita da kuma kwaɗon sannan suka shigo.

Manyan torchlight suka kunna suna haske su Yusuf, suka shigo hannunsu ɗauke da mugayen makamai, da manyan bindigogi.

Babban ya haske Widad da fitila, ta sunkuyar da kai taƙi ɗagowa yace "shegiya kalleta kamar ta Allah, zamu kawo ƙarshen wannan izzar da gadarar taki uwar taurin kai"

Yai maganar tare da ajiye mata takeaway a gaban ta, wata bushashiyar shinkafa ce a ciki sekace ƙanzo gefen shinkafar duk ƙonanniya.

"ki tashi kici Abinci Malama, sedai ba irin na gidan shashsashan ubanki bane daya sangartaki"

Ƙafarta ta saka tayi Ball da takeaway ɗin shinkafar ta watse a gurin.

Aikuwa ya harzuƙa ya shaƙeta yana faɗin "nan ba gidan ubanki bane da zaki mana gadara, zakiga yadda zamu lallasa ki sekin sauke wannan izzar taki"

A gigice Yusuf yazo ya riƙe hannun sa yace "dan girman Allah kayi haƙuri ka ƙyaleta, a galabaice take zata iya mutuwa inka cigaba da shaƙeta"

Yayi jifa da ita ta faɗi jiki ba ƙwari tana kakari, ya kalli Yusuf yace "banza ɗan shishshigi ga abunda shishshigi yaja maka nan, aka dinga ja maka kunne akanta amma kaƙi ji, ga shi nan koba komai kaima ka shiga wahala"

Yusuf bece komai ba yayi kan Widad yana ɗagota, da ƙyar take numfashi.
Yusuf yace "Uwar ɗakina, ki dena musu gardama ko so kike su kashe ki a gurin nan?"

Lumshe ido kawai tayi tana sauke numfashi da ƙyar.

Hadda Saleh aka tafi Asibiti gurin Alhaji Nasir, an samu ya farfaɗo har ya zauna sedai yayi shiru baya magana.

Saleh yace "sannu ranka ya daɗe"

Daula ya jinjina kai, ya kamo hannun Saleh yana ta haki yace "Saleh 'yata, an sacemin Widad da Yusuf nayi dana sanin saka Yusuf a harkar tafiyar nan, gashi ya shiga matsala a dalilina"

Saleh yayi shiru sannan yace "kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka Alhajin Allah, babu yadda za' ayi akasa gano inda Widad take, a matsayinka na babban mutum a ƙasar nan, Insha Allah zasu kuɓuta"

Daula yace "ai ba wai kuɓutar tasu ba, yadda zasu tsira da rayuwar su bayan sun kuɓutan shi nake tunani"

Saleh yace "karka damu da wannan Yallaɓai, yanzu Addu'ar mu suke buƙata insha insha Allah zasu kuɓuta"

Bulama ne da matarsa suka shigo ɗakin shida Anwar da su Ramadan, Bulama yace "sannu ya jikin naka?"

"Alhamdilillah"

"Ubangiji Allah ya ƙara afuwa"

"Ameen" na suka shiga yi masa sannu, Anwar ya ƙarasa kusa dashi yace "Sannu Daddy Allah ya baka lafiya"

Kasa Amsawa yayi sema share ƙwalla da yayi yace "Anwar an sacemin Widad, an sace autar daula, ga yaron dabe ji ba be gani ba shima ta ritsa dashi"

Cikin damuwa Anwar yace "ka kwantar da hankalinka Daddy, Insha Allah zasu kuɓuta, za'a gansu, babansu Fahad yace min an kai report"

Alhaji Nasir yace "Allah yasa su kuɓuta gaba ɗaya yasa karsu cutarmin da su"

Alhaji Bulama yace "ka jika da wani zance, muji da 'yarmu da' aka sace kana wani kar'a cutar dasu"

Alhaji Daula yace "haba Bulama, ai gara su riƙe Widad su saki Yusuf, yana zamansa a dalilina da 'yata ya shiga hatsari, in gaya maka gaskiya tsakanin Widad da Yusuf ba wanda bana so, Allah ya samin ƙaunar yaron a zuciya ta, bazan so ya rasa ransa ba shima, Allah ya bayyana min su duka ba wanda bana so"

Kuka sosai Alhaji Nasir yake kamar ƙaramin yaro, Anwar ne ya rungume shi a jikinsa, yana faɗin "yi haƙuri Daddy, duk zasu kuɓuta cikin ƙoshin lafiya, kar lafiyar ka ta taɓu, kaima muna buƙatarka"

Hajiya Sarah tace "dole Baban Widad yayi kuka kuma gaskiya ya faɗa, yaron nan shima abun tausayi ne, beji ba be gani ba tsautsayi ya ritsa dashi abun da tausayi"

Alhaji Bulama yace "dama ku mata wani lokacin ba hankali kuka cika ba, dama Allah yayi haka zata faru dashi, amma mudai mu samu 'yarmu ta kuɓuta"

Hajiya Sarah tace "shi Yusuf ɗin ba uwace ta haife shi ba? Ya zataji idan ta samu labarin ɓatan ɗanta?"

Ramadan ne yai saurin cewa "Mummy kiyi haƙuri kiyi shiru, duk zasu bayyana insha Allah, Allah sarki Yusuf ɗin nan yana da kirki wallahi ga haƙuri da yawan murmushi"

Likita ne ya shigo ze duba Alhaji Nasir, dan haka duk aka basu umarnin su fita daga ɗakin domin a duba shi.

Anwar ya maida su Alhaji Nasir gida, ya shiga part ɗin Fahad, sedai ya tarar da shi da mace suna shan shisha, Anwar ya girgiza kai dan ya saba ganin Anwar a wannan halin, mussman da suna ƙasar waje, Anwar yace "Fahad baka san meya faru da Widad bane da direbanta, ina ta kiranka baka ɗaga ba?"

Fahad ya fesar da hayaƙi yace "Nasani mana"

"Amma ko Daddyn namu ai yakamata kaje ka duba"

Fahad ya kalle shi yace "Daddynku ku suwa? Baza'a dubo shi ɗin ba, ni burina duk inda ta shiga a nemo min mata ta, dan nasan wannan tsinannen direban ne ya gudu da ita, kuma sena nuna masa iyakarsa"

Karuwar dake tare da Fahad tace "Baby wai maganar wa kuke yi ne?"

Fahad yace "ba ruwan ki uwar shishshigi, jeki shirya inzo in maida ke gida"

Anwar yace "Fahad se yanzu na sake tabattar da Widad a kan gaskiya take na ƙin yadda da mutane, yanzu Fahad kasan nida kai iyayenmu basu da ƙarfin kaimu ƙasashen waje, amma ya ɗauke mu kamar yaransa, ya kaimu ƙasar waje mukayi karatu, dukkaninmu ba wanda be mallakawa motar hawa ba da gidan kansa, muba komai ba silarsa muka zama wani abu, kalli yadda muke fantamawa a cikin rigar arzikinsa, albarkacin sunansa duk inda muka shiga a faɗin ƙasar nan muna da Alfarma, yau shine Iftila'i ze faɗa masa amma ka nuna halin ko in kula, Anya Fahad kana gayawa kanka gaskiya kuwa "

Fahad yace " A'a sedai idan yanzu zaka fara gayamin gaskiyar "

Yai maganar tareda miƙewa ya shige bedroom ɗinsa, jiki a saɓule Anwar ya baro gidan Bulama ya koma Asibiti, ya bawa Alhaji Nasir Abinci ya canza masa kaya, sedai yaita mamakin rashin ganin mahaifiyarsa taje Asibitin gurin mijinta.

Gida ya koma yana tunanin butulci irin na Fahad, a falo ya tarar da Hajiya Halima tana cin Abinci suna kallon zee world, sedai kamar Amal ce a cikin damuwa.

Anwar yayi sallama suka amsa gaba ɗaya, Anwar yace "Mummy meyasa ba kije Asibiti ba?"

"bana jin daɗine, bana son inje inga abunda ze sake ɗagamin hankali"

"Amma Mummy ai jikin nasa da sauƙi, kuma yakamata ace ko su Ramla sunje duba shi"

A fusace tace "Ubansu ne da lallai se sunje duba shi, fita ka bani guri dalla"

Buɗe baki yayi yana kallon mahaifiyarsa yana ƙoƙarin tabattar da anya daga bakinta wannan maganar ke fitowa?

Duhu ya fara yi, sauro ya shiga ambaliya a gurin nan, Yusuf ya zauna se akin yi mata fifita yake da wani gutsararren kwali, A hankali Yusuf yace "Kidena musu taurin kai kinji, sannan idan an baki Abincin ki karɓa kici, baze yuwu ki zauna da yunwa ba"

"ba zanci ba" ta bashi amsa

"kin fi son su cigaba da azabtar dake?"

Shiru tayi masa ba tace komai ba, can ya kuma cewa

"dan Allah ki basu abunda suke nema, dan su ƙyale ki ko a yanzu kin galabaita"

"wallahi ko zasu kasheni bazan basu ba, shiyasa nace tun farko su sake ka ni su barni anan"

"tayaya zasu sakeni in tafi, alhalin kina gurinsu sedai kome ze faru ya faru muna tare"

Ajiyar zuciya ta shiga saukewa, tana jin yadda sauro ke shagali akanta, abunda bata saba ba, bata son yin kuka dan yanzu Yusuf ze ɗaga hankalinsa

Cikinsu babu wanda ya rintsa, har gari ya waye, taimama sukayi sukayi sallar Asuba.

Fuskar Widad duk ta kumbura saboda sanyi da cizon sauro, kuma har a lokacin jikinta babu ƙwari.

Yusuf yana zaune, yayin da Widad ke kwance akan tabarmar, buɗe ƙofar ɗakin akayi suka sake shigowa su huɗu.

Suka kalli inda Widad ke kwance, ɗayan ya buga mata tsawa yace

"tashi ko in taka ƙafarki in karya banza"

Gyara kwanciya tayi ta juya musu baya, alamar bata da niyyar tashin, yau Yusuf ya ƙara tabbatar da azababben taurin kai da Widad ke dashi.

Da sauri Yusuf yazo inda take ya ɗaga ta zaune yace "ya haka ne, so kike yauma su dake ki"

Wani banzan kallo tayiwa shugabn nasu ta ɗaunke kai tana hura hanci.

Ɗayan yace "shegiya se kyau kamar ita tayi kanta, amma zuciyar ta kamar dutse shegiya me kama da sadakar yalla"

Babban su yace "zamuyi maganinta kafin tabar gurin nan, da ganin idonta yunwa take ji, amma saboda taurin kai taƙi cin Abinci, ku ɗakko Abinci ku bata idan taga dama taci"

Shinkafa da wake ce irin garau garau ɗin nan takan 'yan talla, tayi sanyi ƙalau ga ba mai sosai, suka dire mata a gabanta, yunƙurawa tayi zata sake fatali da Abincin Yusuf ya riƙe ta yace "dan Allah ki daure kici, kinga tun shekaranjiya rabonki da Abinci"

Ta kalli idon Yusuf tace "bazan ci ba"

Ɗayan yace "kai dalla ka ƙyaleta mana, kar taci ubanwa tayiwa, Oga ka fara aiki kawai"

Rarrashin duniya Widad tayi mursisi taƙi cin Abinci.

Babban cikinsu ya ɗakko wayarsa zeyi kira.

"Nurat ki kaiwa Daddynki tea ɗin nan da baƙinsa, kafin yazo ya ishemu da faɗa"

Nurat ta miƙe ta ɗauki kayan tea ta nufi part ɗin mahaifinta.

Alhaji Munir ya shafa ƙaton cikinsa yace "nifa bakina yaƙi rufuwa ma, nasan dole abun nan yazo hannunmu a yau base gobe ba, nace a tura masa saƙo, kodai ya bayar ko mu cigaba da tsare ta"

Alhaji Musa yace "ba kai kaɗai ba ni kaina ina cikin murna, sun kwana a hannu, Daula yana gadon Asibiti yana ta sharɓar hawaye, mutum se taurin kan tsiya kamar arnen dutse"

Suka kwashe da dariya, Alhaji Haruna yace "dalla ƙyaleshi, gefe guda baze samu Halartar taron shekara na kasuwanci ba, da haka zamu sanar da cewa an samu gagarumar Asara kasuwancin da muke yi, zamu bada fake Account statement, zamu kwashi rabonmu kafin wancan yazo hannunmu, ai daula ya gama yawo wai shi me gaskiya"

Suka sake kwashewa da dariya, wayar Alhaji Haruna ce ta fara ringing, ya ɗaga ya sa musu a hands free, Alhaji Haruna yace "Ya me ake ciki ne?"

"Yallaɓai tunda nake aikin nan, ko a maza ban taɓa ganin mutum me baƙin taurin kai kamar yarinyar nan ba, kwana biyu kenan taƙi cin Abinci, ruwa kawai take sha, gashi kamar bata da lafiya kullum tana kwance ko magana seta ga dama take yi"

Alhaji Munir yayi tsaki yace "dalla ku rabu da ita, ku karɓo mana abunda muke buƙata, sannan ku turawa ubanta saƙo shima koya bamu ko kuma ku kashe ta"

Daga wayar akace "An gama Oga, yadda kukace"

Nurat da taje kai musu shayi jikinta ya shiga ɓari, dan tsaf taji hirar da mahaifinta suke yi, cikin sanɗa taje ta ajiye farantin kayan shayin, ta ruga da gudu ɗakinta ta saka hijjabi ta ɗau wayarta ta fice daga gidan.

Babban cikin mutanen wanda suke cewa me Adda ne ya ɗakko wata kujera ya zauna a gaban Widad ya kalle ta cikin tsawa yace

"ke kalleni nan, ina takaddun nan suke? Ki gayamin cikin ruwan sanyi ko kuma in kasheki in koma in kashe wancan daƙiƙin uban naki"

Sunkuyar da ka tayi tai shiru, Yusuf yace "Yana miki magana ki gaya masa, su ƙyaleki ki huta"

Kallon Yusuf tayi da jajayen idonta sannan tace "takaddun da suke nema, akwai masu shi nayiwa Daddy Alƙawarin miƙasu ga masu shi, kuma na bawa masu shi suna can suna yawon su a gari, me suke so kuma ince musu"

"ƙarya kike, duk binciken da'akayi sun tabattar da suna wajen ki dan haka ki gayamana inda suke"

A harzuƙe tace "bazan faɗa ba, nace bazan faɗa ba kayi abunda zaka yi!"

Kan bindiga ɗaya yasa ya buga mata a baki, take jini ya shiga zuba daga bakinta Yusuf ya gigice ze tashi, suka ɗora masa bindiga aka "kana motsawa zamu fasa kanka da harsashi"

Widad ta tattaro dukkan yawun bakinta, me ɗauke da jini ta tofawa shugabannin nasu tace "wallahi ko me zaki sedai kayi, bazan bayar ba ka koma ka gayawa Azsaluman da suka saku aiki cewar bazan bayar ba, kuma matsorata ne tunda suka gaza fitowa gaba da gaba su karɓi abunda suke so, kuma ko sun kasheni na kafa musu tarkon da ko bayan raina se Asirinsu ya tonu, saboda na sansu kuma na tattara duk wata hujja da yakamata a kansu san......

Bata ƙarasa ba ta kuma jin wani marin a fuskarta, a duk lokacin da suka daki Widad Yusuf ji yake kamar ƙirjinsa ya tsage dan baƙin ciki, sedai ba yadda ya iya muddin yayi wani yunƙuri dabe gamshesu ba zasu mata illa, dan ba imani ne dasu ba, ga Widad bakinta yaƙi mutuwa.

Nurat bata tsaya ko ina ba se gidan su Widad, a waje ta tarar da Anwar ya fito da mota ze fita, Anwar ne ya ganta dan sam bata lura dashi ba yace "Nurat"

Ɗaga kai tai ta kalle shi sannan tace "Yaya Anwar ashe ka dawo, babu Labari"

Anwar yace "Na dawo, ina zaki haka naga kamar bakya hayyacinki"

Nurat tace "gurin Widad nazo"

Anwar yace "baki san na sace ta ba ita da direbanta?"

Hannu ta ɗora a ka, ta durƙusa a gurin ta fashe da kuka, Anwar ya fito daga motar yace "Nurat lafiya kuwa?"

Nurat tace "lafiya ƙalau, dan Allah kasan wani ɗan uwanta wanda suke yawo tare?"

Anwar yace "Ai Widad bata da ɗan uwa"

Nurat tacs "Nasani, wannan zaka ga tare suke yawo, ban san sunashi ba ya cemin ɗan uwanta me shi, wani dogo kamar bafulatani, me yawan murmushi"

Anwar yace "ko Yusuf kike nufi?"

Nurat tace "ban san sunansa ba"

Anwar yace "indai Yusuf ne tare suke yawo kam, kuma tare aka sace su"

Zare ido waje tayi tace "tare aka sace su, na shiga uku ni Nurat, meyasa aka sace su?"

Anwar yace "shine abunda bamu sani ba, amma 'yan sanda na nan na bincike yanzu haka zanje Asibiti gurin daddynta ne, daga nan mu koma station"

Nurat tace "zan iya binka in duba shi?"

Anwar yace "meze hana? Muje"

Suka shiga motar suka tafi.

Me Adda ya jinjinawa wannan baƙi taurin kai na Widad, yasa bakin bindiga ya daki kanta dashi ta kurma wani uban ihu tace "wallahi ba zan faɗa ba, sedai kayi min duk abunda zakamin"

Ya kuma ɗaga bakin bindiga ze da keta, Yusuf ya miƙe ya riƙe shi gam yace 'Anya akwai imaniba zuciyar ka, kalli yadda take kururuwa amma ba zaka ƙyaleta ba"

Me adda yasa hannu ya hankaɗa Yusuf amma Yusuf ko gezau beba, ya kalli Yusuf ya kuma ƙoƙarin hankaɗeshi amma Yusuf ko gezau balle ya kai ƙasa dukda ya kwana biyu ba Abinci amma hakan besa ya faɗi ba.

Haɗuwa sukayi su huɗu suka kama dukan Yusuf, da manyan sanduna, suka masa jina jina sannan suka ɗaureshi, tun suna dukansa Widad na ihu harta suma a gurin.

Koda Anwar yaje a Asibiti seya tarar da mahaifiyarsa da su Ramlah a gurin, tayi masa ƙaryar wai da'aka gayamata abunda ya faru suma tayi seda aka kaita Asibiti shiyasa bata zoba, shi kuma Daddy ya yarda da abunda ta faɗa.

Anwar tun yana mamakin abubuwan da suke faruwa harya dena.

Nurat ta ƙarasa gaban Gadon Alhaji Nasir tace "Sannu Daddy ya jiki".

Ta faɗa tana sheshesheƙar kuka.

Alhaji Nasir yace "da sauƙi Nurat, ashe kin samu labarin ɓatan ƙawar ki?"

Ta jinjina masa kai alamar eh, yace "to ki cigaba da Addu'a Allah ya bayyana ta, sannan ki koma gida kar babanki yayi miki faɗa kinzo nan"

Ya kalli Anwar yace "ɗan beauty mayar min da ita gida kaji"

Yai maganar cikin ƙarfin hali cike da zolayar Anwar.
Anwar yayi murmushi, tare da wayancewa ya goge ƙwallar dake idonsa, kallo ɗaya zaka yiwa Alhaji Nasir kasan yana matuƙar jin jiki.

Tunawa yayi da abunda Widad ta gaya masa daren da abun ze faru, take yaji wasu hawayen na bin idonsa, duniya Kenan Abun tsoro.

Saleh ya kasa zama, ya kasa tsaye abun duniya ya dames hi, tabbas Alhaji Nasir mutumin kirki ne ya masa alkhairi daban daban a rayuwar sa, ga Yusuf dabe ji ba be gani ba shima an ritsa dashi, anya hakki ze barshi kuwa, wannan tunanin ne ya cika masa zuciya ko Abinci ya kasa ci.

Widad ta buɗe ido a hankali ta kalli inda Yusuf ke kwance, duk jikinsa jini, se sauke ajiyar zuciya yake, gashi an ɗaure shi tamau da sarƙa.

Ko tashi bata iyayi saboda dukan da take sha, jikin ta ko ina rauni ne, ta janyo jikinta a hankali tazo inda Yusuf ke kwance kawai ta faɗa kansa tana kuka.

"Yoseef dan Allah ka tashi, dan Allah kayi magana idan kana jina"

A hankali can ƙasan maƙoshinsa ido a lumshe yace "Insha Allah zamu kuɓuta, ki dena kuka, ina mana Addu'a nasan Daddynki ma yana yi, Ummana ma tana yi mana"

Haka ta cigaba da ƙoƙari ko zata iya kwance Yusuf, amma abu yaci tira.

"Ranka ya daɗe yarinyar nan fa baza tayi magana ba, mun daka mun daka amma kamar jinjirar jaka saboda taurin kai, mun mata jina jina amma taƙi faɗa se rashin kunya take yi, gashi kwana huɗun nan Ruwa kawai suke sha, ita muna bata Abinci amma taƙi ci duk ta galabaita "

Alhaji Haruna yace " A tauna tsakuwa, dan aya taji tsoro kuyi mata azaba wadda zataji a jikinta"

Me adda yace "An gama ranka ya daɗe"

Ya buɗe ƙofar ɗakin dasu Widad ke ciki, tana zaune a gaban Yusuf ta zuba masa ido idonta yayi jawur saboda yunwa da wahala, gashin kanta duk ƙasa da abun ciyay, saboda birgimar da take a gurin, ya sauka a kafaɗarta ya baje kamar mara hankali.

Suka ƙaraso suka kwance Yusuf, da shima yake a mugun galabaice, suna kwance shi Widad ta kama ƙasan rigarsa tana goge masa jinin jikinsa, me Adda ya fizgota ya zaunar da ita tana fuskantar sa yace "ke dan uwarki wannan shine karo na ƙarshe da zan tambayeki, dan mun gaji da wannan sintirn a wannan surƙumin dajin, ina takaddun nan suke?"

Cikin tsawa tace "ban sani ba! Kuma karka sake zagin uwata dan uwa bata fi uwa ba"

Yadda gashin kanta baƙi kamar na Larabawa ya baje, gaba ɗaya seta burgeshi danƙo gashin kanta yayi ya miƙar da ita tsaye, tsanani zafi yasa ta fasa ihu, Yusuf ya yunƙura ze miƙe suka sake buga masa sanda a ƙafa ya faɗi ƙasa.

Ya kai bakinsa na Widad da niyyar ya haɗe bakinsu, tayi masa gware da kanta, dukda yaji zafi hakan besa ya cikata ba, ya kuma danƙar gashin kanta ze haɗe bakinsu, ta tattaro ƙarfinta ta daki mararsa da ƙafarta, a gigice yayi jifa da ita, ya ɗakko ƙaramar pistol ya harbe ta a hannu, tare sukayi ƙara da Yusuf ta zube a gurin jini na zuba a dantsenta.

Me adda miƙewa tsaye ma kasawa yayi saboda bala'in azabar da yake ji, 'yan uwansa suka ɗauke shi, suka sake kulle su Widad.

Yusuf ya ƙarasa kan Widad ya ɗagota, a gigice yake magana "Widad sannu, kina ganina?"

Ta jinjina masa kai dukda idonta na ƙoƙarin lumshewa, jikinta se rawa yaje gumi na tsatstsafo mata ta ko' ina.

Yusuf ya ɗau ɗan siririn mayafint da tazo dashi ya ɗaure mata damtsen, ya rungomata jikinsa yana jijjigata yace

"Dan Allah karki tafi ki barni, zamu bar gurin nan insha Allah, zan maida ke gurin Daddy, dan Allah Widad karki tafi ki bar Yusuf"

Sosai hawaye ke zuba daga idon Yusuf, magana takeson tayi amma ta kasa, se rawa da bakinta yake yi kawai, ta ɗaga hannu da nufin ta kaishi fuskar Yusuf amma abu ya gagara hannun ya sauka tun tana ganin Yusuf dishi dishi harta dena ganinsa wuyanta ya langaɓe.

Rungume ta yayi a jikinsa yana ambaton Allah, yana sheshesheƙar kuma, yayin da mayafin da ya ɗaure mata hannu dashi ya jiƙe sharkaf da jini.

In an karanta ayi share please, masu neman recent pages dan Allah ku dinga dubawa a watpad, @ Ayshercool7724.

Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

                    _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

(GAMAYYAR MARUBUTA NA ELEGANT ONLINE WRITER'S, INA GODIYA DA KARRAMANI DA'AKAYI DA CERTIFICATE NIDA ƘUNGIYATA TA PERFECT WRITERS ASSOCIATION, INA GODIYA DA WANNAN KARAMCI UBANGIJI ALLAH YA ƘARA HAƊA KAN MARUBUTAN MU AMEEN, INAWA KOWA DA KOWA FATAN ALKHAIRI, TARE DA FATAN KOWA YAJE GIDA LAIFIN)


ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 26_27

Gaba ɗaya Widad ko motsi ba tayi, Yusuf ya rungumeta sosai a jikinsa kamar wani ze ƙwace masa ita, zuciyar ta na bugawa amma numfashinta baya fita sosai, ga cikinta se ƙara yake saboda yunwa.

Anwar ya kai Nurat gida, suka yi Sallama, ta shige gida jikin ta na rawa ta tafi ɗakin mahaifiyar ta.

"ke ina kika fita kikaje ban sani ba?"

"Mummy akwai matsala fa"

Cike da rashin fahimta mahaifiyar ta tace "matsalar me?"

"Widad ta ɓata an sace ta"

Dafe ƙirji tayi tace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, waye ya gaya miki?"

"Mummy can naje fa, Daddynta yana Asibiti ma naje na duba shi ma"

Zaro ido tayi tace  "ubanwa yace kije? Sekin jawa kanki faɗa a gurin mahaifinki ko? Tashi maza kije ki cire hijjabin nan ki huta"

Nurat ta kalli mahaifiyar ta tace  "Mummy, Daddy ne fa yasa aka sace Widad"

"inji ubanwa? Rufen baki shashasha, in kika sake maganar nan yaji kema zeyi maganin ki"

"Mummy a matsayinki na uwa, ya zakiji idan ni aka sace, yakamata ki cire tsoro a ranki ki gayawa babana gaskiya, ranar da hakki ya tashi bashi kaɗai ze kama ba harmu"
Ta ƙare maganar tare da ficewa daga ɗakin gaba ɗaya

Kwata kwata duk bidirin da'ake Fahad beje yaga jikin Alhaji Nasir ba shima kuma Alhaji Nasir be tambaya ba, yana fama da kansa.

Mussaman Abbas daga inda yake aiki ya kira Umman Yusuf ya sanar da ita ɓatan ɗanta, dama ta kira wayar Yusuf harta gaji bata shiga.
Aikuwa ta kiɗime sosai ta tashi hankalin ta, ta shirya ta tafi gurin aikin Yusuf.

Ma'aikatan su kansu a kiɗime suke tun bayan da suka samu labarin ɓatan Yusuf, Suleman yayi duk yadda zeyi a basu damar bincike akam al'amarin amma daga sama aka hanasu, akace an riga an danƙa case ɗin a hannun wasu jam'ian tsaron.

Sosai Umman Yusuf tasa Abbas a gaba tana zabga kuka
"dan Allah ranka ya daɗe ina ɗana yake? Ku kuka sashi aikin nan ina kuka turamin shi shi kaɗai nake kallo inji daɗi, Yusuf ne kaɗai dani, dan Allah ku temaka ku nemomin Yusuf ɗina"

Cikin ƙwarin gwiwa Sulaiman yace "ki kwantar da hankalinki Umma, Insha Allah indai Yusuf ne zamuyi duk me yuwuwa muga mun kuɓutar dashi, an baza jami'an tsaro kuma ins me tabbatar miki ba abunda zasuyi masa dan bashi suke hari ba, yarinyar da yakewa aiki suke hari, dan ba suce abasu komai ba, yanzu haka mahaifin yarinyar yana kwance a asibiti, kuma bashi da magana seta Yusuf"

Suleiman ya dinga kwantar mata da hankali, amma abunka da ɗa d uwa ta saurari kalaman Suleiman ne kawai, amma bata ga alamar ana neman ɗan nata ba.

Umman Yusuf bacci ya ga gareta, balle cin Abinci banda kuka da Addu'a babu abunda take yi wa ɗan nata, dan yanzu a duniya idan ta rasa Yusuf ba.

Jikin Alhaji Nasir ƙara rikicewa yake saboda damuwa, Anwar yace wa Mahaifiyarsa "Mummy ya kamata ayi wani abu akan rashin lafiyar daddy, inze yuwu ayi visa a fita da shi, kullum jikinsa ƙara rikicewa yake babu sauƙi"

Hajiya Halima tace  "ko bangon duniya za'a kai shi idan Allah yayi niyyar karɓar rayuwarsa ba yadda muka iya, anan ɗinma naga likitocin suna iya ƙoƙarin su, meye kuma se an kwashi jiki an tafi ƙasar waje dan ɓarnar kuɗi"

"Mummy ɓarnar kuɗi kuma? Koma ɓarnar kuɗin ne naga nasane ai, meye amfaninsu in baza'a nema masa lafiya ba"

"kaga Anwar ka kiyaye ni, kafini sanin abunda ya dace ne? Fita ka ban guri kafin in ɓata maka rai, sakarai kawai"

Fitowa yayi gwiwa a saɓule yana tunanin wannan halina Mummynsa.

Gidan Bulama ya tafi, yaje ya tarar yana shirin fita, suka gaisa da Anwar, Anwar yace "Daddy gurinka nazo"

Bulama yace "gashi ina shirin fita ne, Amma meya faru?"

Anwar yace  "Daddy dama cewa nayi meze hana a fita da Daddynmu waje a duba shi yadda ya kamata a can, naga kullum ciwon nasa gaba yake ba sauƙi"

Alhaji Bulama yace  "Anwar kazo da magana me kyau, amma ka sani ko an fitar da Daula waje in har baze cire damuwa dake ransa ba, babu yadda za'ayi magunguna suyi masa aiki, haka likitoci suke ta faɗa"

"Amma da dai an jarraba, amma jikinsa yana bani tsoro"

Alhaji Bulama yayi shiru sannan yace "shikenan Anwar, zamu yi maganar da mahaifiyarka, zanga abunda ya dace ayi"

Anwar yayi masa godiya sannan ya tafi.

Alhaji Haruna ne zaune akan kujera, fuskar nan tasa babu alamar imani ya kalli wani matashi dake zaune yace

"doctor Sufyan, mun yaba da ƙoƙarin da kuke yi a Asibitinka akan Shahararren Attajirin da'ake ji dashi a faɗin ƙasar nan wato Alhaji Nasir Daula"

Doctor Sufyan yayi murmushi yace  "Nagode ranka ya daɗe"

Alhaji Musa yace  "Kasan meyasa muka kiraka?"

Sufyan ya girgiza kai alamar aa'

Alhaji Haruna ya gyara zama yace "Abunda muke so da kai shine, bama son Daula ya tashi"

Zare ido Sufyan yayi yace "kamar yaya?"

Alhaji Musa yace "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ba muna nufin ka kasheshi ba, A'a bama so ya tashi ya warke ta hanyar dena bashi magungunan da ya dace, kayi duk abunda zakayi masa wanda ze ƙara kwantar dashi, idan kayi haka akwai lada me tsoka da zamu baka"

Saleh dake gurin gaba ɗaya ya rikice yace "Amma Yallaɓai ba muyi haka daku ba, idan kuma ya rasa ransa fa?"

Alhaji Haruna yace "Saleh ka rufewa mutane baki, karka ɓatamin rai"

Ya maida hankalinsa kan doctor Sufyan yace  "Yaya zakayi ko bazaka yi ba?"

Doctor Sufyan yace "Nifa na ɗau Alƙawarin bazan cutar da lafiyar kowa ba kafin in fara aiki, kuma Alhaji Nasir ya yadda dani, na daɗe ina duba shi lokaci ɗaya kuma se in....

" Kai dakata "  Alhaji Musa ya dakawa Sufyan tsawa yace " karka kawo mana maganar banza malam, idan baka yi ba zamu nemi wani, kwata kwata aikin wata uku muke so kayi mana, za mu baka Naira miliyan goma, idan yayi maka kaɗan zamu ƙara maka"

Zare ido Sufyan yayi yace "miliyan Goma"

"ƙwarai kuwa, miliyan goma idan kuma kaƙi zamu saka wani amma ka tabattar da kaima ba zamu ƙyaleka ba"

Cikin hanzari Sufyan yace "zanyi ma, na amince zanyi insha Allah karka damu Alhaji"

Shiru Saleh yayi yana tunani, wato akan kuɗi mutanen yanzu duk alkhairinka sesu manta, idan baze manta ba  dangin Sufyan ɗaiɗaiku ne Daula be kai aikin Hajji ba, Amma ya amince ze karɓi kuɗi ya cutar da Alhaji Nasir "

Da Sufyan ze tafi dubu ɗari biyar suka bashi wai ya zuba mai a mota.

Saleh yayi shiru abun duniya duk ya dameshi.
Su Alhaji Musa kuwa cigaba da ƙulle ƙullen sharrinsu suka yi.

Wayar Alhaji Haruna ce ta fara ringing, suka tsagaita da dariyar da suke Ya ɗaga wayar yace

"Yaya me Adda, ya ake ciki ta faɗa maka kuwa?"

"Ina fa ta faɗa se wahalar damu take, ga taurin kai da tsiwar tsiya, sannan ta bada saƙo a baku"

Alhaji Musa a gigice  yace  "Kamar ya ta bada saƙo abamu ta sanmu ne?"

Me adda yace "ina nasan mata, cewa tayi mu cewa wanda suka sa a sace ta, ta tattaar duk wata hujja akan su, ko bayan an kashe ta asirinku ze tonu"

Wani gumine ya shiga tsatsafowa Alhaji Haruna yace  "ƙarya take bata sanmu ba, a gidan uban wa ta sanmu balle ta tattara wata hujja a kanmu, yanzu kana ina ne?"

"ina cikin gari mana, naje Asibiti ne wani yarfi yarinyar nan ta min na kasa ko miƙewa tsaye, na ɗauka ma na tashi daga aiki"

Alhaji Musa yace  "wani sakarci ne zesa ku baro su acan, maza ka koma ku gana mata Azaba iya Azaba seta faɗi inda takaddun suke, idan ta faɗi inda suke ku kashe su kawai"

Saleh yace "What akan me za'a kashe ta?"

Alhaji Musa be saurari Saleh ba ya cigaba da wayar sa.

Me Adda yace "gaskiya Oga kisan Yarinya kamar wannan ba kamar kashe sauran mutane bane, tsaf wannan cinnakun zasuyi ram damu"

Alhji Haruna yace  "ba wanda ze kama ku, zancen nan da muke maka gaba ɗaya mun siye jami'an tsaro ba wani bincike da'ake akan ɓatan nata, dan haka ka gaggauta zuwa jibi idan bata faɗa ba ka tirsasa ta, ta gaya maka wasu hujjoji take dasu sannan ka kashe mana su"

Me Adda yace  "angama Oga"

Alhaji Haruna ya sharce gumi yace  "bala'i, Musa anya ba dagaske yarinyar nan ta gano mu ba, karfa muje dagaske take"

"Rabu da ita ƙarya take, da dagaske ta sanmu da tuni ta ɗau mataki akanmu, amma kasan bamu gayawa Munir da Bukar hukuncin da muka yanke ba?"

Alhaji Haruna yace  "Suma idan mun gaya musu hukuncin da za susa ayi mata kenan a kashe ta kawai, karta ja mana masifa"

Alhaji Musa ya kalli Saleh yace  "wai kai meye naka na saka baki dan munce  a kashe ta, kabi a sannu fa wallahi kar kasa musa a haɗa da kai, kabi umarnin mu kawai"

Saleh yayi murmushi yace "Tausayin Daula ne ya kamani wallahi, karka damu bazan baku kunya ba insha Allah dani za'a kammala komai nima in samu rabona"

"daka temaki kanka" cewar Alhaji Haruna, yayin da cikkunansu suka ɗuri ruwa.

Yusuf yana nan zaune rungume da Widad, har duhu yayi gari ya waye, sam be bacci ba gani yake da yayi bacci Widad zata mutu, dan bugun zuciyar ta da yake ji shike tabattar masa tana da rai, dan wani lokacin har motsawa take.

A hankali Yusuf ya kwantar da ita, yayi taimama yayi sallar Asuba, shima gaba ɗaya jikinsa a sake yake babu ƙwari saboda azabar wahala, ga yunwa ga duka ga cizon sauro ga azabar sanyi dake gurin, amma gaba ɗaya yafi tausayawa Widad, lokaci lokaci yakan kwance hannun nata, ya goge jinin ya sake ɗaure mata, ga wani irin zazzafan zazzabi da ko sauka bayayi a jikinta.

A hankali Widad ta buɗe ido, sedai dishi dishi take gani bata gane komai, tana yi tana lumshe ido haka take kallon Yusuf.
Yusuf ya girgiza ta yace "Alhamdilillah, you are alive"
Bata iya amsa masa ba, sedai idonta ya sake rufewa

Yana rungume da ita, yayi shiru yana ta ambaton Allah, babu zato ba tsammani yaji ana ta sukuwa a saman roofing ɗin ɗakin, Yusuf ya ɗaga kai yana son gane meke faruwa haka? Cigaba da sukuwa akayi a gurin anata ƙoƙarin ɓare kwanon, can kuma se'aka dena, yaji anata ƙoƙarin buɗe ƙofar da suke ciki, waze gani Saleh ne ya shigo cikin ɗakin.

A gigice Yusuf yace  "kaine? Da kai aka haɗa baki kenan aka mana haka?"

Saleh yace  "baka da lokacin wannan tambayoyin, zuwa nayi na tseratar da ku, ka adana tambayoyinka, idan kun tsira seka yi su"

Hankalinsa ya kai kan hannun Widad dake sume yama zubar da jini, da sauri ya ƙaraso yace  "meya sameta haka? Harbinta sukayi?"

Yusuf bece masa komai ba, sedai kallon tuhuma da yake ta binsa dashi.

Saleh yace "zaka iya tafiya kuwa?"

Yusuf ya jinjina masa kai alamar eh, "to taso maza"

Yusuf ya yunƙura ya miƙe, amma ƙafafunsa se rawa suke saboda dukan daya sha, ga uwa uba yunwar da yake ji.
Amma cikin jarumta, da sadaukarwa ya miƙe ya goya Widad a bayansa.

Suka fito daga gidan, Saleh ya maida gidan ya rufe, sannan ya ɓare saman roofing yayi hanya, sannan yayi musu jagora hannunsa ɗauke da compass dake nuna masa direction suka nausa cikin daji.

Yusuf ji yake kamar ze kifa, amma haka ya cigaba da tafiya, Saleh ya kalle shi yace "ko zaka sauketa in ta yaka?"

Yusuf ya girgiza kai yace "A'a karka damu"

Tafiya sukayi bata wasa ba, ƙafar Yusuf ko takalmi babu, ya dinga taka abubuwa danma ta cikin ciyayi suke kutsawa, haka suka dinga tafiyar cikin sauri, suna bi takan ciyayi dan kaucewa barin sawunsu yadda za'a gane hanyar da suka bi, daji ne har daji me sarƙaƙiyar tsiya, da manyan bishiyu.

Sunyi tafiya me nisan gaske sannan suka fito titi, sam Yusuf be san a ina suke bama, Saleh ya nunawa Yusuf mota yace  "ya shiga"

Yusuf yayi turus ya kalli Saleh, a wahalce yace "wannan taimakon ma da kayi mana mungode, amma bazan hauba, Insha Allah zamu bar gurin nan".

"Yusuf, wallahi suka kamaku kashe ku zasuyi, da inada niyyar cutar daku da bazan ceceku ba"

Da ƙyar Yusuf ya yadda, ya hau motar, da alama Saleh ya gama shirya komai.

Shima Saleh haka yayi doguwar tafiya dasu a motar, tafiya kamar za'a bar duniya dazuka kawai suke ratsawa, tituna bakowa se su kaɗai, Shiru ne ya wanzu tsakaninsu har suka fara fita gari.

Wani ɗan madaidaicin Asibiti suka tarar a hanya, Saleh yayi parking Yasa Yusuf ya ɗakko Widad suka shiga Asibitin.

Kuɗi Saleh ya ajiyewa likitan, dan haka ba wani dogon bincike suka karɓi Widad, Amma Yusuf yaƙi zuwa ko'ina, a gabansa aka cirewa Widad bullet, akace se an tafi neman jini za'a ƙara mata.

Yusuf yace a ɗibi nashi, Saleh yace "baze yuwu a ɗebi naka ba, kaima a galabaice kake akwai buƙatar a duba ka"

Yusuf ya dage sedai a gwada jininsa in zeyi a ɗiba a sa mata.

Aka duba aka ga Yusuf ze iya bawa Widad jini, saboda rukunin jininsa ake cewa universal donor wato O-, sedai an samu jinin Yusuf da malaria, likitan yace 

"baze yuwu asa mata jinin ba"

Shikuma Yusuf yace be yadda da kowa ba, jininsa za'a saka.

Saleh yace  "kaga doctor, koma menene a jinin nasa saka mata, can taƙarke musu dan zamanmu anan akwai hatsari"

Aka bawa Yusuf Abinci, amma ya kasa ci se ɗan kaɗan saboda hankalinsa na kan Widad, ana ɗibar Jinin Yusuf jiri ya ɗebe shi ya yanke jiki ya faɗi, haka aka ɗauke shi aka bashi gado.

Akayi treating ɗin raunkan jikin Yusuf, aka masa allaurai dan samun relief.

Aka sakawa Widad jinin Yusuf, tare da sauran Allurai, Yusuf na farfaɗowa ya fara tambayar ina Widad.

Likitan yace "wai dan Allah meye alaƙarsa da wannan yarinyar haka?"

Saleh yace "ƙanwarsa ce shiyasa ya damu da ita, 'yan fashi ne suka harbeta akan hanyar su ta tafiya, ita kaɗai yake da ita shiyasa"

Yusuf ya koma inda Widad take yasa ta a gaba, ya ƙura mata ido ko ƙyaftawa bayayi, tunda aka cire bullet ɗin nan har yanzu bata farka ba.

A hankali ta buɗe idonta, ta yunƙura zata miƙe Yusuf ya riƙeta yace "bi a hankali fa jikinki babu ƙwari"

Ta kalli Yusuf tace  "A ina muke nan?"

"I think we are save now insha Allah, yanzu zamu koma gida" ya bata amsa

Saleh ya shigo ɗakin yace  "waye yace maka zaku koma gida ne"?

Widad ta kalli Saleh ta ƙura masa ido, kamar taga baƙuwar halitta.

Yusuf yace "meyasa ba zamu koma gida ba yanzu?"

"saboda idan kuka koma, da kai da ita da mahafinta duk sesun kasheku"

Yusuf yace  "meyasa?"

"Zan gaya maka komai, Amma daga nan mafaka zan baku, inda zaku ɓuya ba zasu san inda kuke ba na gama shirya komai daga nan tafiya kawai zamuyi"

Saleh ya miƙowa Yusuf wata babbar jarkar youghurt yace "gashi nan kuci nasan ba wani Abincin kirki a cikinu, sannan ka canza riga ita kuma a sama ta hijjabi"

Yusuf ya karɓi youghurt ɗin ya buɗe ya miƙa mata, amma ta ɗauke kai, Yusuf ya girgiza youghurt ɗin ya ɗaga kai ya sha, sannan ya sake miƙa mata.

Se a lokacin ta karɓa, ta dinga sha saboda azabar yunwar da take ji, sedai tana gama sha ta dinga amai saboda kwanakin da tayi babu Abinci a cikinta.

Saleh yace  "Yusuf yakamata mu bar gurin nan da gaggawa in kaiku inda zaku fake, zamanmu anan hatsari ne na gaske"

Yusuf yace  "Amma jikinta har yanzu bata da lafiya, ya za'ayi mu tafi a haka?"

Saleh yace "zamu karɓi magungunan da zaku cigaba da Amfani da shi, amma dole mu bar gurin nan"

Haka likitan ya tattara magungunan Yusuf dana Widad ya basu, suka hau mota Saleh ya cigaba da nausawa dasu seda suka sake shafe wata tafiyar, Widad kam magungunan data sha basu saketa ba dan haka duka tafiyar nan bacci take, seda sukazo wata mararraba sannan Saleh yayi parking, wata tsohuwar motace akori kura ('yar ƙurƙura) gaba ɗaya ta sha jiki ta fatattake, hatta fentin jikinta ya koɗe duk ta mole, anyi parking ɗintabakin hanya.

Wani mutum ne ya fito daga a kori kurar, suka gaisa da Saleh, Saleh ya bashi mukullin motar da suka je da ita, suka kwance lambar motar dake jiki da wata.

Saleh Ya kalli Yusuf yace "Yusuf ku fito wannan motar zamu hau mu ƙarasa"

Yusuf yace "nifa Saleh ban gane wannan abubuwan ba, kodai kaima kana da wani ƙudurin ne akanmu"

"Yusuf wallahi ba wani abu da nake shiryawa don in cutar daku, sedai ƙoƙarin ceton rayuwar ku"

Yusuf ya fito hannun sa ɗauke da Widad suka shiga 'yar ƙurƙuran nan, Saleh yaja motar.
(Yau Widad ce a cikin irin wannan motar🙄)

Tashin hankali ba' a samasa rana, duk wannan uwar tafiyar da suka sha Nafila ce akan wadda suke yi yanzu, wata irin ruɓaɓɓiyar hanya suka bi, banda ƙura babu abunda yake tashi wata irin lalatacciyar hanyace, duk kwazazzabai da turɓaya ga uban ramuka, wani ramin in suka shiga da ƙyar suke fita ga ƙurƙuran nan se wani irin ƙugi injinta yake yi, gashi sun matsu a motar, duk yayin da suka shiga rami haka suke bige kafaɗu da ƙarfen motar.

Wannan kwaraf kwaraf ɗin ne yasa Widad ta farka, a hankali ta kalli Yusuf tace

"A ina muke?"

Yusuf yace "Sannu ya jikin naki?"

Bata bashi amsa ba ta kuma cewa  "A ina muke ne?"

"Mun kuɓuta ne, Saleh ze bamu mafaka"

Ɗan lumshe ido tayi sannan tace "Na gaji jikina ciwo yake, hannuna zafi kaina ze fashe, Wayyo Allah Daddy na"

Yusuf yace "kiyi haƙuri insha Allah komai ze daidaita, zakiji sauƙi mun taho da magunguna"

Shiru tayi ta sake kwantar da jikinta a ƙirjin Yusuf, hawaye na bin gefen idonta.

Tun Yusuf yana sa ran tafiyar ta ƙare har yayi shiru ya zubawa sarautar Allah ido.

A hankali Yusuf ya fara ganin gidaje  tsilla tsilla a gurin, gine gine na tsurar ƙasa haka Gidajen suke, wasuma ko katanga babu a haka suke, yayi mamakin wannan irin ƙasurgumin ƙauye haka da yadda mutane ke rayuwa a cikinsa, suka baro duk bakin hanya suka shigo wannan surƙuƙin guri sukayi ginin Gidaje.

A hankali suna cigaba da tafiya, yaga ƙauyene sosai me ɗauke da gidaje da mutane a ciki, sedai sunyi hannun riga da duk wani abun more rayuwa da jin daɗi, kama daga Makaranta, Asibiti, ko wani abu me kama da borehole tunda suka shiga ƙauyen Yusuf be ganshi ba.

A ƙofar wani babban gidan ƙasa, an shafawa ƙofar gidan farar ƙasa, alama dai mamallakin gidan yana riƙe da wata sarauta ne a ƙauyen.

Saleh yace "Yusuf ina zuwa"

Ya sauka daga motar ya shiga cikin gidan, Yusuf yana ta ƙarewa gurin kallo yana tunanin anya Widad zata iya rayuwa a cikin gurin nan?

A hankali yaji tace  "Ka yadda da Saleh, kana da tabbacin shima ba cutar damu zeba?"

"Ko ban yadda dashi ba, Allah baze bashi damae cutar damu ba, nidai fatana inga kinji sauƙi gaba ɗaya"

Ajiyar zuciya tayi, tai shiru ba tace komai ba can Saleh ya fito shida wani dattijon Mutum, kansa ɗauke sa rawani.

Suka ƙaraso gaban akori kurar, dattijon yace "sannu dai ɗan samari"

Yusuf yace yawwa Baba, barka da yamma

"Yawwa barka" mutumin ya kalli Saleh yace  "sune wannan?"

"Eh sune wanda na gaya maka, ina son su zauna a gidanka na wani lokaci, kafin komai ya lafa su koma"

"Amma kana ganin babu wata matsala Saleh, nifa bana son abunda zezo ya ɗagawa Al'ummar garina hankali, kasan ku mutan binni se a hankali"

Saleh yace "Haba dai, wane irin matsala taimako zakayi, baka ga yadda suke a galabaice ba, babu wata matsala insha Allah"

"Shikenan, shigo dasu se a kaisu ɗakin daka gyara musun"

Yanzu ma Widad ba zata iya tafiya ba, Yusuf ne ya ɗauke ta zuwa cikin gidan.

Duk da rabi tana hayyacin ta rabi bata hayyacin ta, tana mamakin mutane ne ke rayuwa a wannan gidan, roofing gidan kansa na Azarane, ta dinga kallon roofing tana tunanin menene wannan?
Yayin da wasu ɗakunan roofing danga ne.

Tunda suka shigo gidan, mutan gidan maza da mata suka fito suka yi cirko cirko kamar zakaru suna binsu Yusuf da kallo kamar sunga baƙin halitta.

Wani ɗakine a can ƙarshen gidan, Saleh yasa mukulli ya buɗe ƙofar katakon dake ɗakin ya shiga yacewa Yusuf "bismillah"

Ba lefi ɗakin yana da girma amma ba sosai ba, yana da taga guda ɗaya wadda akayi ta da katako da kuma langa langa, ɗakin ginin ƙasa ne tsura, sedai anyiwa ƙasan floor, aka shimfiɗa buhu a ƙasa sannan aka kawo tabarma duk aka shimfiɗa.

Akwai matsaikaciyar katifa a shimfiɗe a ƙasa, da bargo guda biyu se fula guda ɗaya duk sababbi.

Gefe ga tulu, da wani ƙaramin kwandon kwanuka da 'yan kwanuka a ciki, gefe ga sababbun bokitai guda biyu, da sabuwar buta.

Akan katifar Yusuf ya kwantar da Widad, da duk inda ya motsa ta ciwo yake mata.

Dattijon yace  "wannan bata da lafiya ne haka?"

Saleh yace "Eh bata da lafiya, a hannun masu garkuwa fa na karɓo su, na maka bayanin komai, dan Allah Baba a kula dasu, duk abunda suke buƙata ayi musu"

"Shikenan, indai nine baka da matsala, ko baka kawo kowa ya zauna a gidan nan ba, gidan nan na jama'a ne, Allah ya basu lafiya"

Ya juya ya fita, yana kora yaran da suka yi dandazo a ƙofar ɗakin suna leƙen su Widad.

Idon Yusuf ne ya sauka akan akwatunan Widad data shirya domin tafiyar da zasuyi, da traveling bag ɗinsa da suka bari a motar da'aka sace su.

Yusuf ya zare ido yace "Nifa Saleh ina buƙatar kamin bayanin abubuwa, ya akayi ka samu jakunkunan mu na tafiya? Ya akayi kasan idan muke kaje ka tseratar damu?"

Saleh yace  "Nasan zakayi mamaki, kuma dole ku tambaya, Amma yanzu ina sauri saboda zan koma kano kar su gane wani abu a ƙasa su fara zargina, duk yadda aka shirya sace ku dani akayi shi, Tun bayan sace ku ni kuma na fara shirin yadda zaku tsira, amma ka sani koda wasa karka kuskura kayi gangancin barin ƙauyen nan in bani na fita daku ba, dan wallahi suka ganku sekun kasheku"

Yusuf yace "wai tsaya, wai inane nan ma tukuna?"

"Nan wani ƙauye ne a cikin garin Bauchi, Zan dinga zuwa ina duba ku, a waccan jakar na ajiye muku abubuwan da ba'a rasa ba da zaku buƙata kafin ku saba da irin rayuwar da suke yi, ga kuma kayanku can dana kawo nan, nan gidan ƙanin kakana ne dan haka insha Allah baku da wata matsala, idan ma dawo za kaji komai "

Saleh ya fita tsakar gida ya kalli wata dattijuwa yace "Gwaggo dan Allah Amana nan, a kula da baƙin nan dan manyane duk abunda suke buƙata ayi musu"

Gwaggo tace  "Lallai kam, baƙin suna da girma a gurinka, tunda sanadinsu gashi kana leƙo mu"

Wata mata a tsakar gidan tace "Eh aimu da yake cinyesu zamuyi shiyasa ba'a bamu amanar baƙin ba se ita"

Saleh yace "Aifa kedai halinki yana nan bazaki canza ba" yayi gaba abunsa, ya tafi gurin me gari suka sake tattaunawa sannan ya tafi.

Haka Saleh ya tafi ya bar su Yusuf a cikin wannan ƙasurgumin ƙauye.

A hankali Widad tayi juyi, ta ƙarewa ɗakin da take ciki kallo, wai anan zata zauna ita da suka zo sam bata zaci wai nan mutane ne ke rayuwa a cikin gurin ba se yanzu.

Yusuf yaje yayo Alwala, yazo ya tada salla sedai duk inda yayi se mutanen gidan su bishi da kallo.

Widad ta cire hijjabin jikinta, jikinta se faman ƙaiƙayi yake mata, Yusuf ya idar da salla zeyi magana ta riga shi ta hanyar cewa "zanyi wanka"

Ɗan zare ido yayi yace "to shikenan, bari inwa mutan gidan magana"

Ya fito tsakar gidan, yaga wadda Saleh ya kira da Gwaggo ɗazu tana ta aiki a tsakar gida, yace mata  "dan Allah Mama ko zamu samu ruwan ɗumi, mara lafiyar zata yi wanka, nikuma ko na sanyi ne na samu se inyi Amfani da shi"

Tayi murmushi tace  "bakomai, na zuba ruwan tuwon dare dama, bari in ɗibar maka"

Yusuf yace  "to nagode"

Ya tafi ɗakin su, ya ɗakko sabon bokiti, aka zuba ruwa aka sirka Yusuf ya koma ɗakin yace  "An haɗa ruwan"

Ta tashi zaune ta fara kiciniyar cire rigar jikinta, sedai hannunta na hagu shine wanda aka harbeta, na dama kuma yana ciwo saboda duka da wahalar mota.

Yusuf ya juya mata baya da nufin ta kintsa ya kaita banɗakin.

"Zoka tayani cire wannan rigar na kasa cirewa....

(Akwa ƙura fa🚶 🚶 🚶 🚶 🚶)

Share, share and share please 🙏

Domin, gyara sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

     _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 28_29

Gaba ɗaya dirircewa Yusuf yayi, se yayi kamar beji me tace ba, ganin yaƙi magana yasa itama tai shiru ta nemi guri ta kashingiɗa.

Yusuf ya waigo yace  "Kin gama kintsawar ne?"

Kawai ya ganta a zaune.

"Ya haka kuma? Se ruwan ya huce?"

"Ban sani ba, ai kana jina ina magana kayi min shiru, nace kazo ka tayani in cire rigar nan, amma kayi kamar baka jiba"

Ikon Allah bata da lafiyar ma, an tsira da ƙyar bakinta be mutu ba, gashi da ƙyar take maganar.

Yusuf yace  "bari inyiwa mutanen gidan magana, se suzo su cire miki"

"Wallahi babu matar da zata taɓani" tai maganar tana kuka

Seda Yusuf yayi shiru, sannan ya tako a hankali kan katifar da take, ya zagaya bayanta hannunsa rawa yake ya zuge zip ɗin doguwar rigar tata ƙasa.

Farar fatarta ta bayyana cikin wata baƙar vest, shiru yayi yana kallonta, ta janyo hijjabi ta mayar ta yunƙura zata miƙe tsaye amma jiri ya kwashe ta.

Yusuf yace  "ki dena gaggawa, a halin da kike ciki ɗin nan, idan kika faɗi zaki ji ciwo fa"

Ya duba ya ɗakko soson wankanta dake cikin Akwatinta, sedai babu sabulu haka ya riƙota suka fito, Gwaggo na ganin haka ta taho da sauri da nufin ta taya Yusuf, Amma Widad ta maƙale hannunta, ta manne a jikin Yusuf tabi gwaggo da ido, gwaggo ta tsaya sororo tana kallonsu.

Yusuf yace "Mama karki damu, kiyi haƙuri haka halinta yake bata da yadda ne"

Matar dake gaban murhu ta juyo ta kallesu tace "yau nake ganin ikon Allah, wannan gwandamemiyar matar ce take ƙyuya se kace me shan Nono, taɓ amma lamari ya ɓaci, koda yake wannan kamar ma ba irin tamuce ta nan ƙasar ba"

Widad tabi matar gaban murhun da kallo, haƙoranta yellow shar ga haƙorannata wasu sunyi goyon kura, gata baƙa sosai ga fuskarta duk tsagu, gashi se ƙara baje hanci take.

Gwaggo tace "Haba Hari, ina ruwanki da ita irinku ne ke sawa adinga cewa Hausawa basu da kirki, yanzu da taji abunda kike faɗa ba"

Zatonsu duk Widad bata jin hausa, gwaggo ta kalli Yusuf tace "ga banɗakin can seka kaita"

Suna zuwa ƙofar banɗakin Widad tayi tiris taƙi gaba taƙi baya.
Yusuf yace "muje mana seki shiga kiyi wankan"

Girgiza masa kai tayi tace  "Ni wallahi tsoro nake ji bazan iya shiga ba" sam Widad gurin be mata kama da banɗaki ba, kamar wani gidan horo haka taga gurin.

"meye abun tsoron, zan jiraki anan gurin kiyi ki fito"

Riƙe shi tayi tsam tana girgiza kai tace  "Ni na fasa wankan, bazan shiga nan ba"

Gwaggo tace  "ɗan nan ya naga bata shiga ba, lafiya kuwa?"

Yusuf yace  "wai tsoro take ji ba zata iya shiga ba"

Gwaggo tace  "Allah sarki, ƙasashenku babu irin wannan banɗakin ko? Abun duk se haƙuri ai, akwai wani ɗaki da babu komai a ciki ta shiga tayi a ciki kawai"

Yusuf yace "mungode Mama"

"A'a bakomai"

Ta nuna musu ɗakin, duk yadda Yusuf ya tsani roƙo, haka ya karya billensa ya tambayi sabulun wanka, sedai Sabulun da suke wanka da shi irin sabulun nan ne kore na wanki me ƙarnin tsiya, Yusuf ya miƙawa Widad, tasa hannu ta karɓi sabulun ta kalli Yusuf kawai yaga Hawaye a idonta.

Tausayinta ya kama shi, amma ya basar kamar bega hawayen idonta ba, haka ta shiga ɗakin da siminti a ƙasan ɗakin, tayi wankan nan tsigar jikinta na tashi saboda yadda ruwan in ya zuba a ƙasa yake taɓata, ga tashin zuciya saboda ƙarnin sabulun, ba shiri ta ajiye sabulun tayi wankan a haja, sedai taji daɗin ruwan zafin sosai "

Ta fito tana kama bango, Yusuf ya riƙeta ya maida ita ɗaki, ya duba Akwatinta ya ɗakko kaya ya bata, ta saka itama tayi salla.

Saleh beje gida ba se bayan sha biyu na dare, yayi tunanin ko yaje yayi magana da doctor Safwan amma wata zuciyar ta hana shi, saboda yadda Safwan ya dinga rawar jiki da yaji batun kuɗi tsaf zeje ya gaya musu, yaje ya sameshi.
Gaba ɗaya tunaninsa ya koma kan yaze ƙwaci Alhaji Nasir a gurin wannan Azzaluman mutanen? Dan ba ƙaramin shiri suke dashi ba.

Me Adda suka koma inda suka ajiye su Widad, da niyyar ayita ta ƙare, suna zuwa suka buɗe gidan, suka shiga suka saka mukulli suka buɗe ɗakin suka ga wayam ba kowa a ciki, a kiɗime ɗayan yace  "Me Adda bafa kowa a ɗakin nan"

Ƙarasawa yayi da sauri ya shiga ɗakin shima amma ba kowa a ciki, nan da nan suka gigice suka shiga lalauben su Widad.

Me Adda yace "Mutanen da ko iya takawa basayi, ta yaya zasu gudu? Duk matakan tsaron dake gurin nan ina sukabi suka fita?"

Cam ɗaya daga cikinsu ya ɗaga kai ya kalli Roofing ɗakin yace  "me Adda kalli ta nan suka fice" yai maganar yana nuna musu saman roofing ɗakin

Me Adda a gigice yace "ya zama dole mu bazama neman su, amma ta yaya suka samu abu sukayi hanya har suka fita?"

Ɗaya daga cikinsu yace "Allah ne ya san yadda suka gudu"

Me Adda yace  "bamu da lokacin ɓatawa, maza maza mubi sahun su yadda suke a galabaice ba lallai su iya tafiya me nisa ba"
Haka kuwa akayi suka rarraba kansu a cikin daji.

Saleh yaje duba Alhaji Nasir a Asibiti, ya tarar da Anwar a gurinsa, suka gaisa yayi masa ya me jiki, ya ɗan dubi Anwar yace
"Amma meyasa baza'a fita da Alhaji waje a nema masa magani ba?"

Anwar yace  "Nayi duk me yuwuwa inga an fita da shi, amma Mummy da Alhaji Bulama sunce nan ma ana kula da shi"

Saleh yace "Abunda za'ayi yanzu shi ne, ka ɗauke shi ka canza masa Asibiti ba tare da ka sanar dasu ba, ko ba'a fita dashi waje ba a camza masa Asibiti, sedai kawai suga ka canza maaa Asibiti"

Anwar yace  "Amma zasuji babu daɗi idan nayi hakan, suna ganin nanma ana ƙoƙari akansa amma inyi haka kamar ban kyauta ba"

"Anwar zamanku a Asibitin nan yaci ace jikinsa yana karɓar treatment yadda yakamata, amma har yanzu babu wani cigaba, mu canza masa wani Asibitin kawai"

Anwar yace  "Kana ganin babu matsala idan muka yi hakan?"

"eh babu matsala, Amma karkace ni nace ka canza masa Asibiti"

Anwae yace  "shikenan, ka kawo shawara me kyau insha Allah gobe in Allah ya kaimu da Safe, sedai suzo su tarar na canza masa Asibiti ni kaina rashin samun sauƙin nan nasa yana bani mamaki"

Doctor Sufyan ne yake ta zagaye acikin Office ɗinsa, yana tunanin me yakamata yayi akan batun su Alhaji Haruna, yana tuno irin halacci da kirkin Alhaji Daula, idan aka haɗa kai dashi aka cutar dashi to tabbas mesa Adalci ba, Amma wani mataki Alhaji Musa zasu ɗauka akansa idan har be abunda sukace ba?.

Fitowa yayi da sauri daga office ɗin nasa ya nufi ɗakin da Alhaji Nasir yake, yana zuwa shiga suka haɗu da Saleh, suka yi kallon kallo babu wanda ya cewa kowa komai suka wuce.

Ya shiga ɗakin da Sallama, Anwar ya amsa masa, doctor Sufyan yace "Anwar yame jikin kuwa?"

"Jiki sedai muce Alhamdilillah, amma doctor na fara karaya da yanayin jikin sa, babu wani cigaba fa gashi nayiwa su Mummy magana a fita dashi amma sunƙi amincewa, na rasa dalili"

Sufyan yace  "ka kwantar da hankalinka Anwar, treatments ɗin dai da muke masa anan, shi za suyi masa a can, komai ze tafi dai dai ze warke in Allah ya yarda"

Anwar yace "Shikenan Allah yasa"

Haka Widad ta kwanta akan katifar, Yusuf ya ɗau bargo ɗaya ya koma bakin ƙofa ya shimfiɗa ya kwanta, shiru Widad ta kasa bacci, tana tunanin wai itace zata kwana a gurin nan, ga sauro se kururuwa yake mata a kunne, ga zafi ga jikinta da yake ciwo, ga rashin lafiya tana fama.

Ɓangaren Yusuf ma shiru Yayi yana saƙe saƙe, yana tunanin wani hali Ummansa take ciki, yasan duk inda take hankalin ta a tashe yake, dan tun tasowarsa be taɓa nesa da ita ba, wani ɓangare na zuciyar sa yana tunanin Alhaji Nasir yasan tabbas shima yana cikin damuwa, ko wani haki yake ciki Allah masani, ga zamansa da Widad a ɗaki ɗaya baze yuwu ba, tunda ba muharramarsa bace, gashi ba ta yadda da kowa se shi, ga wasu abubuwan se anyi mata saboda bata da lafiya, dole idan Saleh yazo yayi masa magana asama masa wani ɗakin, dan gudun afkawa tarkon sheɗan.

Yana nan kwancw sauro yana cizonsa, yana masa hada hada aka, ga cinnaka da yake ta gasa masa cizo a gurin nan, tunani yake Allah yasa kae cinnakan ya ciji Widad.

Katsam ya jiyo sheshsheƙar Widad tana kuka, da yayi kamar ya basar amma ya dinga jin kukan nata a zuciyar sa, tabbas yakamata a tausaya mata.

Ɗakin baƙiƙirin da duhu, ko tafin hannu ba'a iya gani saboda duhu, haka yaja jikinsa cikin lalube yaje gefen katifar ta yace "uwa ɗakina kukan me kike?"

Maimakon tayi magana seta sake fashewa da kuka, Yusuf yace "Am sorry, i feel your pain kiyi haƙuri ki karɓi hakan a matsayin ƙaddarar mu, yakamata ki gode Allah da yasa muka tsira daga hannun mutanen nan, kuma insha Allah zamu koma gida ki dena kuka, kiyi bacci zaki ji daɗin jikin ki"

"I can't sleep, sauro ya dameni zafi nake ji, kuma ina tunanin Daddy na"

Tai maganar tana sake fashewa da kuka.

"kiyi hakuri, Insha Allah Daddy yana nan lafiya, komai ze wuce kamar be faru ba, ki dena kuka kinga baki da lafiya"

Ajiyar zuciya kawai tayi, ta lumshe idinta tana jin yadda zuciyarta ke raɗaɗi.

Da Asuba yayi Alwala yazo ya tada Salla, bacci take dan sam bata samu bacci ba da daddare, seda ya idar sannan ya tashe ta ya kaita tayi alwala tazo ta tada salla.

Da gari ya fara haske me gari da kansa yayi sallama a ƙofar ɗakin su Yusuf, Yusuf ya fita ya durƙusa ya gaishe shi.

Ya amsa cikin mutuntawa yace "Ya me jikin kuwa?"

Yusuf yace  "Jikinta da sauƙi Alhamdilillah"

"Masha Allah, Allah ya ƙara afuwa ya bata lafiya, karkaji komai ku saki jikinku duk abunda kuke buƙata kuyi magana insha Allah baze gagara ba"

Yusuf yace  "Masha Allah, mungode sosai da wannan karamcin naku"

"Karka damu, ai shi ɗa na kowa ne"

Wajejen ƙarfe tara na Safe aka aiko yaro ya kawowa Su Yusuf Koko me zafi da ɗumamen tuwo, Yusuf ya karɓa yace sun gode.

Ya kalli Widad dake zaune tayi shiru, gwanin ban tausayi yace  "ga Abinci an kawo, ki daure kici se Kisha magani"

Kallon kwanon tuwon tayi, sannan ta kalli kwanon da'aka zubo kokon, har ɗan gara kwanon kokon, amma na tuwon dai se a hankali ga warin daddawar nan ji tayi kamar tayi amai, miyar nan baƙa wuluk ga uban tuwo a ido in ka kalli Tuwon nan kasan ze azabar tauri.

Ta kalli kokon tana tunanin ta ina zata sha abun sha a cikin kwano, ta kalli Yusuf tace "janye min wannan baƙin Abincin kar inyi amai"

Kallonta yayi da mamaki, tuwon ne bata sani ba ko kuma tsabar rainin hankali ne? Ta miƙa hannu ta ɗau kwanon kokon, ta dinga juya kwanon sannan ta kai bakin ta, karɓa ɗaya tayi ta dire kwanon ta yamutsa fuska kamar zata yi kuka.

Yusuf yace  "ya dai?"

"Ba daɗi" ta bashi amsa

"to ai badan daɗi zaki sha ba, kinga nan ba kamar gida bane da zakici abunda kike so, ki daure kisha"

Banza tayi masa taƙi kallonsa, ya ɗau kwanon ya zuƙi kokon, kokon dawane kuma gasarar tayi tsami dan ta ɗan fara wari ma, gashi babu ko ɗigon sugar a ciki.

Yusuf yace "kinga babu wani Abincin da zan baki, idan baki sha ba babu wani Abincin da zaki samu kici, ki daure ki ɗauke numfashi kawai kisha"

Da ƙyar ya lallaɓata ta sha kokon nan shima kaɗan ta sha tace ita ta ƙoshi, sannan ya bata magungunanta.

Yusuf yace  "Inaga yakamata inyi musu magana, idan da hali a bani ɗakin da zan dinga kwana, kinga be dace mudinga kwana a ɗaki ɗaya nida ke ba, sannan dole kiyi haƙuri su ɗan dinga temaka miki ko gurin wankan ne da canza kaya, nida nake miki be dace ba, tunda ba muharrama tace keba"

Da sauri ta kalle shi tace "Nikaɗai zan dinga kwana a ɗakin nan? Ni gaskiya bazan iya ba"

"to se a samu a yaran gidan wasu su dinga ta yaki kwana"

Ai tuni ta fara kuka tace  "Ni wallahi ba wanda nasani a gurin nan ba zaka tafi ka barni a ɗakin nan ba, kuma wallahi niba zasu dinga taɓani ba, wannan matar me haƙora tsoro take bani, in ba haka ba kawai ka maida ni gida"

Yusuf ya ƙara kwantar da murya yace "Widad mufa musulmi ne, mun san illar zaman mu a guri ɗaya, bekamata yadda nake kula dake ba bayan ga 'yan uwanki mata a gidan nan ba"

"to ni ka maida ni gida mana, kkme ze faru ya faru amma wallahi ba inda zaka tafi ka barni".

"so kike mu koma gida wani abu
ya sameki?

" Idan ba zamu koma gida ba, to bazaka bar ɗakin nan ba, in ba haka ba ni zan tafi gidan nikaɗai "

"Amma kin san zamana dake a ɗaki ɗaya ya saɓawa shari'ar musulunci?"

Shiru tayi bata ce komai ba, Yusuf yace "kiyi haƙuri, mutan gidan nan suna da kirki kuma duk mutane ne, babu wanda ze cutar dake, kiyi haƙuri zanje in samu me garin muyi magana"

Riƙo rigar Yusuf tayi ta fashe da kuka tace "Wallahi bazan dinga zama a ɗakin nan nikaɗai ba, sedai duk inda zaka in bika"

Shiru yayi yana Kallonta, kuka take sosai har cikin ranta, tabbas yasan halinta da ƙyanƙyami da rashin yadda, ba zata yadda ta zauna da kowa a ɗaki ɗaya ba in bashi ba, kuma gashi hakan ya haramta.

Jiki a sanyaye yace  "shikenan is ok kidena kuka, idan har kina son mu cigaba da zama tare a ɗakin nan inyi jinyarki bisa shari'a mafita ɗaya ce, kuma mafitar nasan me tsaurin gaske ce a gurinki ba lallai ki yadda ba"

Widad ta ɗago idonta tace "Meye mafitar?"

Yusuf yace " Sedai ki amince muyi Aure zuwa lokacin da zaki warke, mu koma gida semu rabu"

Gaban Widad ne ya faɗi ta tsaya tana masa wani irin kallo

Duk yadda me Adda yake tunanin lamarin ya wuce tunaninsa, dan babu wata alama ko sheda da zata nuna maka inda su Yusuf sukabi, suka yi sintiri da neman duniya a dajin nan basu sami su Yusuf ba, me Adda yace  "gaskiya ina mamakin guduwar mutanen nan, tabbas akwai munafiki a cikinmu, wanda ya kuɓutar dasu banda haka yaza'ayi mutanen da ko tashi basa iyawa ace sun gudu?"

"Oga nima dai nayi wannan tunanin, dan tabbas maganar ka haka take, da saka hannun wani a kuɓutar tasu"

Me Adda yace  "Ni yanzu tunanina yadda zanwa wannan mutanen bayanin sun ɓata, dan wallahi babu lallai su ƙyalemu"

"To Oga ko muma sanfewa za muyi muyi ta kanmu"

Me Adda yace  "ƙwarai kuwa, Amma zamu fara kiransu mu gaya musu su san meya dace suyi, sannan muma muyi ta kanmu da ba mutunci mutanen nan suka cika ba"

Suleiman shike zuwa ya rarrashi Maman Yusuf, dan ko Abinci bata iya ci, sedai wataran inzeje yayi mata Nasiha ya sai wani abun ya kai mata.

Yauma bayan Azahar da ya taso daga gurin aiki gidan su Yusuf yaje, yatarar da Umman Yusuf akan dadduma taci kuka ta ƙoshi, idanunta duk sunyi jawur.

Suka gaisa Suleiman yace "Umma har yanzu baki dena kukan ba? Ki sani wannan carbin da kike ja kina masa Addu'a yafi wannan kukan da kike yi, dan Allah ki kwantar da hankalinki, kar wani ciwon ya shige ki"

Umman Yusuf tace  "To Suleiman dangana ta zama dole, yau da gawar Yusuf na gani seta fiyemin kwanciyar hankali akan ɓatansa, ban san a ina yake ba, yaci Abinci? Yayi wanka? Me yake ciki? Yana samun Abincin da yake so duk ban sani ba, Allah ne kawai ya barwa kansa sani, dole in shiga damuwa inyi kuka"

Suleiman yace  "hakane Umma, amma ki kwantar da hankalinki, muna nan muna bincike akan mu gano inda Yusuf yake, very soon zakiji labari me daɗi, kuma kisawa zuciyarki addu'ar nan da kike tana isa ga Yusuf insha Allah muna sa ran jin labari me daɗi akan Yusuf"

Umman Yusuf tace "Nagode Suleiman, Allah ya saka da alkhairi tunda abun nan ya faru kai kaɗai kake zuwa inda nake ka rarrashenin, Nagode Allah yayi Albarka"

Suleiman yace "Ameen Umma, kin san mahaifin yarinyar ma yana can a gadon Asibiti, sedai fatan Allah ya bayyanasu"

Umma ta amsa da Ameen.

Nurat ta kuma satar jiki, mahaifiyarta bata sani ba ta tafi Asibiti duba jikin Baban Widad, koda taje Anwar kawai ta gani a gurinsa, sedai abun mamaki har yana zaune yana cin Abinci da kansa.

Nurat tace  "Alhamdilillah lafiya ta fara samuwa, ya ƙarfin jiki kuwa Daddy?"

Daula yayi murmushi yace "Alhamdilillah, yau gani a zaune ina cin Abinci ma"

Nurat tace "Alhamdilillah"
Ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar ina kwana"

Anwar yace  "lafiya ƙalau, ya mutan gidan?"

"duk suna lafiya Alhamdilillah, Amma ina su Anty Ramlah ne?"

Ɗan kame kame Anwar ya fara yace "kin san da yake tunda Daddy ya kwanta itama taƙi lafiya, tana can tana jinya su Amal ke kula da ita"

Nurat tace "Allah sarki, Allah ya sawwake naje in duba ta"

Saleh ne yayi sallama ya shigo, yana ganin Daula a zaune yace "Alhamdilillah Alhajin Allah, kaine a zaune haka kake cin Abinci?"

Daula yayi murmushi yace "Alhamdilillah, tambayi Anwar da kaina na tashi na zauna, sedai bana jin daɗin Abincin sam tunanin 'ya' yana nake, ban san a halinda suke ciki ba"

Saleh yace "Insha Allah suna lafiya, kuma da yardar Allah za'a gansu"

Nurat tayi shiru zuciyarta gaba ɗaya ta tsinke, tausayin Daddyn Widad ya kamata, ji take tamkar ta gaya masa abunda ke faruwa, Amma idan ta faɗa da wani suna za'a kirata, kuma meye hujjarta na cewa da hannun mahaifinta a sace Widad tunda ita kaɗai taji abunda suka faɗa, Mahaifinta yana zaune da nasa iyalin cikin kwanciyar hankali, amma ya jefa rayuwar wannan iyalan cikin fargaba da damuwa.

Tana cikin tunanin Daddy yace  "Nurat, ki koma gida kinji ko, nagode sosai Allah yayi miki Albarka"

Nurat tace "Ameen Daddy"

Ta miƙe tsaye ta fita, Anwar yabi bayanta suka fita, suna fita harabar ta tsaya ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar wai meyasa baza'a fita da Daddy waje ba, tunda yana da kuɗin nan ba babu ba? Kana kallon da yadda yake numfashi fa"

Anwar yace "Wallahi Nurat, nayi iya yina amma su Mummy sunƙi Amincewa, wai anan ma ana kula dashi, Jiya Saleh ya bani shawarar ko Asibiti in canza masa basu sani ba, sedai kawai suga an canza amma ina tunanin abunda ze biyo ba idan nayi hakan"

Nurat tayi ajiyar zuciya tace "ya batun taron kasuwanci da'ake yi duk ƙarshen shekara da ma'aikata da 'yan kasuwa kuwa?"

Anwar yace "Ana nan za' ayi jibi insha Allah"

Nurat tace  "babu wanda ze wakilci Daddyn Widad kenan?"

"Nurat ana ta lafiyarsa wake ta wani taron kasuwanci"

"Amma idan da kara, tunda shike jagorantar taron ayi wani abu akai, tunda yana kwance ba lafiya"

"Ayi wani abu kamar me kenan?"

Nurat tace "A ɗaga taron zuwa wani lokacin"

Anwar yace  "kina ganin su saura mahalarta taron zasu yarda da haka?"

"Yaya Anwar, ƙaddara bata wuce kan kowa ba, dan haka babu laifi idan munyi wani abu akai"

Anwar ya gyara tsaiwa yace "to gurin wa zamuje ayi mana wannan Alfarmar?"

Nurat tace "karka damu ina da hanya, duk yadda ake ciki zan kiraka amma wannan maganar da gani se kai, karka gayawa kowa"

"insha Allah babu wanda zan gayawa, Allah ya saka da alkhairi da wannan taimako da zakiyi"

"Babu komai yaya, yiwa kaine inda kara ai bekamata ayi taron nan Daddy na kwance ba"

A ranta kuwa cewa tayi "daka san Abunda ake shirya yi a gurin taron nan, da kaima ka nemawa Alhaji Daula mafita '

Saleh ya kalli Alhaji Daula yace
" Yanzu idan nace maka na san inda Widad take zaka yadda? "

Daula yayi murmushi yace " daka san inda Widad take da baka ƙyaleni ina fama haka ba"

Saleh yace  "Hakane, jikina yana bani Su Widad sun kuɓuta, sedai kasan su dawo cikin garin nan hatsari ne?"

Daula yayi shiru yace "Tabbas, dan mutanen nan basu da imani, Allah kaɗai yasan halin da suke ciki, ina cikin damuwa sosai Saleh"

Saleh yace "Insha Allah nan ba da daɗewa ba zanzo maka da Labari me daɗi a kansu"

"kamar yaya kenan?"

"Kai dai ka kwantar da hankinka Alhajin Allah, kasan retired solder neni, nasan techniques na abubuwa da dama, dan haka ina daf da gano su"

Riƙo hannun Saleh yayi yace "Dan Allah Saleh dagaske kake? Gaba ɗay....

Farinciki yasa Daula kasa cigaba da magana, sema tari daya sarƙeshi.

Saleh yace" ka kwantar da hankalinka, Amma wannan maganar iyani da kaine, ban yadda wani yaji ba, ko Bulama karka sake ka gayawa "

" Insha Allah bazan gayawa kowa ba, Nagode Saleh "

Yusuf ya cigaba da kallon Widad da take masa wani irin kallo, zame hannun ta yayi daga jikin rigarsa yace
" Shikenan tunda baki amince ba, na manta baki da babban maƙiyi kamar Aure, kuma Aure ma kamar Auren maƙasƙancin mutum irin direbanki, bani da wani zaɓi na zama dake inba Aure mukayi ba, kuma niba abunda ze haɗa ni dake har mu gama zamanmu anan mu koma gida, tunda baki amince ba shikenan "

Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya nufi hanyar fita, jiki a sanyaye Widad tace
"Na Amince!"

Share, share and Share please 🙏🙏🙏

Domin gyara sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

                    _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 30_31

Yusuf ya tsaya cak ya waigo ya kalle ta yace "are you serious kin amince?"

Shiru tayi, taƙi ce masa komai, har yanzu izzar tana nan, abune mawuyaci ta maimaita magana sau biyu, Yusuf yace "Shikenan, idan Saleh yazo zanyi masa magana, kokuma in samu maigari in masa bayanin komai"

Gyara kwanciyarta tayi tace "kuma ranar da zamu koma gida zaka sakeni,gara kasa wannan a ranka"

Yusuf yayi murmushi yace "karki damu, nidai fatana ki samu lafiya komai ya lafa mu koma gida"

Nurat ta koma gida, ta lallaɓa zata silale ta shiga ɓangarenta, "daga ina kike?"

Taji muryar mahaifinta, tsayawa tayi amma takasa cewa komai, cikin tsawa yace "Nace gidan ubanwa kikaje?"

"Amm.. Ammmm. Dama... Damanaje gidansu ƙawata ne shine....

" shine ubanki, yaushe kika fara fita ke kaɗai babu direba? Daga gidan ubanwa kike? Zaki gayamin ko sena kwantar dake na yankaki a gurin nan"

Nurat ta faɗa a Shagwaɓe "Nifa ba inda naje"

"Ubanwa ya kaiki duba Daula a Asibiti ubanki ne?"

A razane ta ɗago ta kalleshi, ta shiga rarraba ido.

"ba magana nake miki ba?"

"Daddy waye ya gaya maka naje duba shi?"

"Ubanki ne ya gayamin" Alhaji Musa ya bata amsa

"Kin san a duniya mutumin nan maƙiyinane, shine kika kwashi jiki kika tafi?"

Nurat tace "Daddy, 'yarsa ƙawatace kuma dukda abunda ke tsakaninku tazo gidan nan birthday na ta bani kyautar mota, yanzu kuma a sace ta mahaifinta a gadon Asibiti in kasa duba shi"

Kafin ta ƙarasa ya ɗauketa da mari, wanda seda ta dena gani na wani ɗan lokaci.

Da sauri Mahaifiyar Nurat ta fito tana cewa "lafiya kuwa? Me tayi maka ne?"

"dole ki tambayi me tayimin mana, munafuka daga ke har ita, wato da saninki ta fita taje Asibiti duba Daula, babban maƙiyina ko?"

Mahaifiyar Nurat tace "haba Alhaji kai waye ya gaya maka can taje"

Alhaji musa yace "Rufemin baki kafin in haɗa dake in muku duka, na wuce duk yadda kuke tunani, duk wani motsinku a waje ina da masu kawomin rahoto, kuma daga yau na saka doka, kada ki kuskura Nuratu ta sake fita daga cikin gidan nan, ban yadda ta sake zuwa ko'ina ba, idan kuwa ta sake sena saɓa muku daga ke har ita"

Maman Nurat taji zafin marin da yayiwa 'yarta, dan ba taga laifin da tayi wanda harta cancanci wannan marin ba.

Taja hannun Nurat zuwa ɗakinta, ta kalleta tace "kema Allah ya ƙara, gobe ma ki sake, gashi nan ya mareki a banza, kin fiye rawar kai Nurat"

Nurat ta share hawayenta tace  "Ni ban san wani tantirin munafikin ne ya gaya masa naje ba, Amma idan harna cika 'ya ta halak inason mahaifina ya dace da rahamar Ubangiji, dole in shiga rusa duk wani mummunan ƙudirinsa, ta haka ne kawai zan huce wannan marin da yayi min"

"kinga karki jawa kanki wani tashin hankalin, ki ɗakko mana magana kin san halinsa sarai"

"Mummy, wallahi zubawa Mahaifina ido yana abunda yaga dama, alhalin nida ke munsan ba dai dai yake ba bamu kyauta ba, babu ruwanki a ciki nikaɗai zanyi komai.

" Na sani, amma Nurat ina jiye miki matakin daze ɗauka akanki, idan ya gane abunda kikeyi "

Nurat tace "ba abunda ze gane, sedai inke zaki gaya masa"

Ta ɗau jakarta ta bar ɗakin, ta nufi nata ɗakin.

Amal ta zama kamar wata me jinya, ta rame sosai dan ko Abinci bata iya ci Sam, sedai abunda ba'a rasa ba, yanzu ma Mummy ce da Ramlah suke cin Abinci suna hirarsu, yayin da Amal juya cokali kawai take, ba ta kai ko loma ɗaya bakin ta ba.

Ramlah tace "wai Abincin ne bakyaci, kokuwa? naga se juya spoon kike"

Hajiya Halima tace "na lura da yarinyar nan, kwanakin nan sam bata walwala ta takure kanta da yawa"

Amal tace "Nifa wallahi ɓatan Yusuf ne ke ɗaga min hankali, wallahi na damu sosai beji ba be gani ba am sace shi, Allah kaɗai yasan wahalar da yake sha"

Ramlah tace "Ai kece 'yar wahalar, dama abunda yasa kike wannan damuwar kenan?"

Hajiya Halima tace " waini Yusuf ɗin nan ko tare mukayi Naƙudarki ne muka haifeki ban sani ba? Ubanki ne shi? Ko haifarki yayi idan baki kiyayeni da maganarsa ba sena fasa miki baki, kije ki kashe kanki saboda wani ɗan iska, Allah yasa su haɗa dashi su kashe"

Zare ido Amal tayi tace "Mummy a kasheshi kuma?"

"Eh a kashe shi, munafikin yaro na tsani yaron nan wallahi ba ƙaramin daɗi naji ba da aka sace dashi"

Ramlah tace "wallahi nima naji daɗin hakan, munafuki yaita sunkuyar da kai kamar na Allah, saboda shi ba irin wulaƙancin da wannan makirar ba tayi mana ba, yanzu da suka ƙara gaba se hutawarmu muke"

Amal ta dire cokalin ta miƙe ta bar musu dining ɗin.

Mummy tace "Allah ya kawo lokacin da burinmu ze cika, ita kuma tana wani shirme daban"

Ramlah tace  "kedai bari Mummy, nifa harna fara tunanin irin bushshar da zanyi, da yadda zan fantama in kece raini a cikin manyan yara, wayyo Allah daɗi"

Mummy tace "kedai bari yarinya, ai komai yana tafiya daidai"
Suka kwashe da wata uwar dariya, hakan yayi daidai da shigowar Anwar, hakan yasa suka ja baki sukayi tsit.

Ganin yadda sam halin da Daula ke ciki baya gaban mahaifiyarsa da 'yan uwansa yasa ya girgiza kai, tunda Daula ya kwanta a Asibiti bata taɓa kwana a gurinsa ba, se tafi kwana uku ma bata je ba.

Hajiya Halima tace  "Allah sarki yaron kirki, Anwar duk ka rame fa, anya baza' a nemi me kula da Alhaji a dinga biyansa ba, ba haƙƙinka bane yin jinyarsa, duk kayi wani iri jinya ba sauƙi fa"

Ya kalli mahaifiyarsa yace "Ciyar damu ɗaukae ɗawainiyar karatunmu da sauran buƙatunmu da yake haƙƙinsa ne? Me yasa lokacin da yakw ɗawainiyar damu baki ce masa ba haƙƙinsa bane, babanmu yayi mana ba tunda yana raye?"

Ya ajiye kayan hannunsa yayi waje zuciyar sa na ƙuna, da irin wannan hali na mahaifiyarsa.

Ramlah taja wani ɗan gajeren tsaki tace " Mummy ya kamata anemo wanda zasu ɓalle ƙofar ɗakin yarinyar nan, mu ɗibi abunda zamu ɗiba, kuma mu shiga ɗakin ubanta mu kwashi abunda muka samu kafin wancan manyan suzo"

Hajiya Halima tace  "hakane, amma dole muyi komai a hankali naga Anwar yana neman ya gane halin da'ake ciki nikuma bazan so hakan ba"

Ramlah tace "Ai Mummy ki rabu da Yaya Anwar ɗin nan kawai"

Saleh ne a hukumar 'yan Sanda na farin kaya, ya nemi ganawa da Sulaiman, ai kuwa be sha wata wahala ba saboda Kasancewar shima ma'aikacin tsarone.

Ya shiga Office ɗin Suleiman suka gaisa, Saleh ya gabatarwa Suleiman kansa sannan yace  "kamar yadda nima jami' in tsaro ne nazo maka da wata mahimmiyar maganane akan jami'inku da'aka sace tare da 'yar gidan Daula"

Suleiman yace  "ya akayi kasan jami' inmu ne? Ba kowa yasan Yusuf ɗan sanda bane"

Saleh yace "ba abun mamaki bane dan na san hakan, Amma yanzu ba wannan ne mafi a'ala ba, ka tsaya ka saurareni da kyau, na kuɓuttar da Jami'inku tare da 'yar gidan Daula"

Wani irin kallo Suleiman yayi masa yace "ya akayi kasan inda suke harka kuɓuttar dasu? Kenan dasa hannunka akan sacesun da' akayi"

Saleh yace "ka dena wannan muzuran, ka tsaya in maka bayani dan baka da ikon da zaka kamani ko gayawa duniya abunda ya faru, idan kayi haka kayi abakin ranka"

Nan Saleh ya warwarewa Suleiman komai sedai be faɗa masa ƙauyen daya bawa su Widad mafaka ba, Suleiman yayi matuƙar girgiza da jin labarin da Saleh ya gaya masa, Saleh yace "a yanzu haka babu wani bincike da akeyi akan ɓatansu, saboda sun siye jam'ian tsaro gaba ɗaya kuma suna harin rayuwar Daula duk saboda dukiyarsa, na fuskanci idan nayi wani kyakkyawan yunƙuri a gurin ceton Daula tabbas Asirina ze tonu, kuma zasu kasheni, kaima na gaya maka dan ka sani, ka samu iyayen Yusuf ka musu bayani, dan hankalinsu ya kwanta, sannan ka gargaɗesu akan suyi shiru da bakin su "

Suleiman ya jinjina kai yace ai abunda za'ayi yanzu shine, zan ɗaukeka muje gaban mahaifiyar Yusuf kayi mata bayani da bakinka dan ta samu nutsuwa"

Saleh yace   "kana ganin babu matsala?, bafa nason a ganeni"

Suleiman yace "babu wata matsala insha Allah, hankalin mahaifiyarsa ne yaƙi kwanciya, ta damu sosai"

Saleh yace "shikenan muje"

Suleiman yayi musu jagora har gidansu Yusuf, ba ƙaramin farinciki tayi ba da jin an kuɓuttar mata da Yusuf ɗinta, sedai jin an ɓoye shi a ƙauye, ga kuma bata san ranar dawowarsa ba yasa tace "Allah sarki Yusufa na, koze iya rayuwar ƙauye? Be saba ba nace ko zaku kaini in ganshi?"

Saleh yace "A'a hakan bame yuwuwa bane, akwai hatsari a cikin hakan, sedai zanyi recoding ɗin muryarki in kai masa, amma baze yuwu in kaiki inda yake ba"

Umma tace "ynzu dai dan Allah dagaske kake ya tsira baya hannun Azzaluman da suka sace shi?"

Saleh yace "tabbas basa nan, ya kuɓuta"

Umma tace "Allah kaine abun godiya, ubangiji Allah ya ƙara tsare su"

Widad kuwa wunin ranar nan ji take kamar ba ita ba, wai ita da bakinta ta Amince da Auren Yusuf, abun da tafi tsana a rayuwar ta yau da bakinta ta amince.
Amma da:ace wannan me korayen haƙoran me kama dana horo tazo ta dinga kwana da ita, ko wannan yaran nasu masu kallon jaraba, gara tayi maleji ta Auri Yusuf ɗin su dinga kwana guri ɗaya, tunda duk abu dai shi ta sani.

Widad sam bata iya cin Abincin da ake kawo musu, saboda gaba ɗaya kwanon da'ake kawo Abincin kansa idan ta kalla be mata ba ba zata ci ba, se taji kamar tayi amai, Yusuf yayi ta fama da ita ga larura tana fama, ga rashin cin Abinci.

Haka a daddafe suka kwana uku, kullum tana kan katifa, Yusuf yana bakin ƙofa a ƙasa, idan ta fito tsakar gidan nan to tare da Yusuf ne ze rakata banɗaki, shima bata shiga banɗakinsu, wannan ɗakin da ba kowa a ciki take wankanta, shima idan tayi abunda zata yi tun safe bata sake yadda ko fitsari ta sake yi.

Ko sannu bata taɓa haɗata da mutan gidan ba, shiyasa suke zaton ko bata jin hausa ma, haka suke wuni a ɗaki bata yadda Yusuf ya fita ya barta, tsakaninsa da ita sedai kallon kallo.

Babban abunda yake ƙara bata haushi be wuce yadda data fito, gaba ɗaya sesu koma kallonta ba, sekace sunga wasu halittu daban, ita tarasa meye abunda suke kallo.

Yanzu tana ɗan iyayiwa kanta wasu abubuwan, dukda bata gama warkewa ba, bata cin Abinci sosai, dukda a da ɗinma ba wani ci take ba, Yanzu kam cimar ƙauyen nan ta sha banban da irin wadda ta saba gani, gaba ɗaya kalar Abincinsu yasha banban da wanda ta saba gani ko ta saba ci.

Yusuf yana son yayiwa megari bayani, amma yana tsoron irin kallon daze masa kuma gashi besan me Saleh yace masa ba game dasu
A haka suka kwana uku, ranar kwana na ukun da yamma ba tsammani suka ji salamar Saleh, ba ƙaramin farinciki Yusuf yayi da zuwan Saleh ba, yayo musu siyayya cikin ledoji.

Saleh suka gaisa da Yusuf, yace "Yusuf ya zaman haƙuri ya me jiki kuma?"

Yusuf yace "Alhamdilillah, me jiki tana samun sauƙi"

Saleh yace "fatan dai komai lafiya, kuna lafiya kuda mutan gidan?"

Yusuf yace "Alhamdilillah komai lafiya ƙalau"

Saleh ya kalli Widad yace "Autar Daula ya jikin naki?"

Banza tayi masa ba tace komai ba, Saleh yace "hmm aike  in dan halinki ne ko kashe ki za'ayi mutum baze ceceki ba, sedai amiki dan Allah dan karamcin mahaifinki, mace se tsabar girman kai da izzar tsiya, yanzu dai dole ki sauke su ki rungumi ƙaddarar da tayi kutse cikin rayuwar ki ba tare da kin shirya mata ba, ki sani abunda kika gayawa wanda sukayi garkuwa da ku, sun Sanarwa da wanda suka sa a sace ku, dan haka idanma dagaske kin san wanda suka sa a saceku inama baki sani ba kikace kin sani, sun bada umarnin a kasheku, zuwa yanzu basu san kun kuɓuta ba, da zarar sun farga kun gudu zasu saka ɗambar nemanku, dan haka idan kin gadama ki haƙura ki zauna anan na wani ɗan lokaci domin ki tserar da rayuwar ki, in baki ga dama ba kuma kiyi yadda kike so "

Yadda Widad take a kashingiɗe ko motsi ba tayi ba, balle Saleh yasa ran jin wani abu daga gareta.

Yusuf ne yace " Ayi dai haƙuri, Insha Allah zata zauna ma, kuma mungode sosai da taimakon da kayi mana Allah ya saka da alkhairi, ya Yallaɓai kuwa? "

Saleh yace "Yana nan ƙalau, dan ina daf da sanar dashi cewar kun tsira, kasan komai nima se nayi lissafi nake yinshi, domin ɓadda sahu, jiya munje gidanku na gana da mahaifiyarka ma"

Da sauri Yusuf ya ɗago ya kalle shi zeyi magana, Amma Saleh ya girgiza masa kai.

Yusuf yace "Amma ya akayi kasan wanda suka sacemu, harka kuɓutar damu?"

Saleh yace "labarin dogone Malam Yusuf, uwa ɗakinka tasa an kama ɗan uwana an tsare shi tsawon shekaru goma, akan zargin dasa hannunsa akan kisan mahaifiyarta, na haɗa kai da maƙiyanta domin in rama abunda tayi min, sedai suma maƙiyan nata kansu kawai suka sani basu da adalci, gefe guda dukda zargin da yake kan ɗan uwana mahaifinta be fasa kyautatamin ba, yana matuƙar girmamani yana kyautatamin ga kuma kai Yusuf da babu ruwan ka, shiyasa na ceceku ba dan halinta ba Wallahi "

"I don't judge based on Assumptions, what happens ten years back is still dancing in my memory, abunda ya faru a wancan lokacin ina jinsa a raina kuma ina ganinsa a idona tamkar a yanzu yake faruwa, da sa hannun Bala akan abunda ya faru, kuma ko ka ceceni ko kar ka ceceni hakan baze taɓa canza ƙaddarata ba, nasan wanda suke bibiyar abun nan tsawon shekaru suna da Alaƙa da wanda suka kashe mahaifiyata, kallona kawai kuke but am beyond your expectations, idan kaje ka ƙara tabattar musu ko bayan raina se sun Wulaƙanta se Asirinsu ya tonu wulaƙanta mafi muni a duniya "

Tuni Hawaye ya wanke fuskarta, yadda take maganar zaka san abun yana taɓa mata zuciya sosai, Yusuf yace
"Amm inaga ku bar wannan maganar, it's hurt her feelings kuma kaga bata da lafiya, dama ina son muyi wata magana da kai ne"

Saleh yace "Ina jinka"

Yusuf yace "kaga zaman da muke da ita a ɗaki ɗaya be halarta ba, tunda ba muharrama ta bace, kuma kasan ba zata yadda matan gidan nan su kula da ita ba, ga yanayi na jinya tana ciki, da nace mu raba ɗaki taƙi yadda, amma munyi shawarar zamuyi Aure, yadda zan iya jinyarta lokacin da Allah ya ƙaddara zamu bar garin nan semu rabu, da naso in yiwa megari bayani, amma ban san yadda kuka yi da shi ba"

Saleh yace  "eh to ni namanta kam banyi tunanin raba muku ɗaki ba, taɓ amma wannan zaka aura? Allah ya baka haƙuri da juriya, tashi muje gurin me garin, dama Jibi in Allah ya kaimu Juma'a se'a ɗaura"

Widad dai bata tanka musu ba, suka tashi suka tafi turakar mai gari.

Mai gari na ganinsu tare yace "Masha Allah, Saleh fatan dai ba wata matsala ba suce, mun musu wani laifin bako?"

Saleh yace "Lafiya ƙalau babu wata matsala, munzo da wata 'yar magana ne"

Maigari yace "Masha Allah"

Saleh yace "Ina son in Allah ya kaimu jibi da rai da lafiya, ka ɗaurawa baƙinka Aure"

Buɗe baki Maigari yayi yace "dama ba matarsa bace?"

"Eh ba matarsa bace, ƙanwarsa ce hatsarin ya ritsa dasu tare kamar yadda nayi maka bayani, 'yar uwarsa ce amma da Aure a tsakanin su"

Maigari yace "Shikenan babu laifi, amma hakan baze kawo matsala ba idan suka koma gida?"

Saleh yace "kaikam Baffa ba dai tsoro ba,' yan uwane fa kuma ba lallai su koma gida nan kusa, se rigimar da'ake a garinsu ta lafa"

Maigari yace "Shikenan Allah ya kaimu, idan anyi sallar Juma'ar se' a ɗaura"

Saleh yace "yawwa Baffa godiya muke, nima ina nan bazan tafi ba se Allah ya kaimu juma'ar idan an ɗaura Auren"

Maigari yace "to madalla babu laifi"

Suka fito shida Yusuf, Yusuf yace "nikam me ka cewa Maigari ne a kanmu?"

Saleh yace "kasan mutumin ƙauye, kawai kifeshi nayi, nace masa faɗan ƙabilanci ake a garinku, kun samu kun tsira da ƙyara akan hanyarku ta guduwa kuma akayi garkuwa daku, har yanzu garinku babu lafiya"

Yusuf yayi murmushi yace "Allah sarki, yana da kirki da karamci kam,
Amma nifa bani da sadakin da zan bayar"

Saleh yace  "karka damu zan bayar, Allah yasa Auren ka yayi silar shiryuwarta daga wannan baƙin taurin kan da izzar, shegiya me kama da Aljanu"

Yusuf yace "dan Allah kadena zagin ta, bana jin daɗi idan ka zageta, ɗazuma ka sata kuka"

Saleh ya yamutsa fuska yace "Yusuf ina zaton kana son yarinyar nan ne, in bahaka ba tun a baya su Nura dama sunce baka ganin laifinta, da'an mata abu sekaji haushi"

Yusuf yayi murmushi yace  "Saleh, duk ɗan adam tara yake be cika goma ba, duk rashin kirkinta akwai halayenta masu kyau, su kansu su Nuran yanzu zasu gane Amfaninta"

Saleh yace "eh amma rashin kirkinta yafi kirkinta yawa ai"

Yusuf yayi murmushi yace  "koma dai yane ni nasan tana da kirki ai, amma dagaske kaje gidanmu? Ya akayi kasan gidanmu?"

Saleh yayi murmushi yace" Yusuf kenan, har gurin aikinka nasani kai jami'in tsarone na farin kaya"

Gaban Yusuf ne ya faɗi "ya akayi kasan hakan?"

"saboda ina tare da maƙiyan Daula, binciken da'aka saka ma duk cikin shirinsu ne, ni naje na shirya komai, ba lallai kasan komai yanzu ba, amma anaso ka gama ka tattara bayanai akan binciken se akai sama, su kuma su karɓa su basu, duk cikin ƙoƙarin su na goge duk wata sheda da zesa asan sunawa Daula da 'yarsa zagon ƙasa, sedai basu san cewar kai aka saka kayi binciken ba, sudai kawai zaman jiran sakamakon bincikenka suke, basu san kaike binciken ba shi kanaa me gidanka Suleiman be san hakan ba, sedai akwai wani abokin aikinka da nayi connecting dashi, da zimmar idan ka gama binciken ya dinga bani wasu bayanai daga abunda kake binciken, sedai bazan gaya maka waye ba"

Shiru Yusuf yayi gaba ɗaya kansa ya gama kullewa, kenan dama duk wannan wahalar da yake sha shirine, jiki a sanyaye yace "Widas tasan koni waye?"

Saleh yace "Yadda take shiri haka maƙiyanta sukeyi, sannan da ta san kai waye, wallahi da yanzu kana prison saboda bata yafewa wanda yayi mata ƙarya koya yaudare ta, kayi fatan Allah yasa ta fara sonka kafin lokacin da zata san ko waye, wataƙila ta sassauta maka"

Gaba ɗaya Yusuf yayi shiru ya rasa abunda yake masa daɗi.

Saleh yace "zomu je mu ɗan zazzaga, kaga yanayin yadda ƙauyen yake"

Haka akayi Yusuf yabi Saleh, garin yana da kyau sedai ƙauyen ƙayau ne, babu ababen more rayuwa sam.

Ramlah tasha kwalliya cikin wasu ƙananan kaya, tayi kyau sosai, tana zaune a falo tana kaɗa ƙafa, aka kirata a waya, tana ganin me kiran ta miƙe tsaye, ta ɗau ƙaramin gyalenta ta yafa tace  "Mummy yazo bari inje"

Hajiya Halima tace "shikenan sekin dawo"

Amal tace "wallahi Ramlah baki da aji, daga zuwansa harkin miƙe kina rawar ƙafa zaki fita da nice da yanzu kina nan kinamin surutu, wani banza dashi gwalagwaji se shegiyar ƙarya da iyayi"

Ramlah a fusace  "Mummy kinga kiyiwa Amal magana ba ruwanta dani"

Mummy tace "Amal kar in ƙara jin bakinki a gurin nan"

Amal ta kwaɓe fuska tace "eh ai tuni na gane, kin fi son Ramlah akaina, damuwar ta ce kawai damuwa ni kuma baki damu dani ba, shikenan"

Ta miƙe fuuuu ta bar falon, Ramlah tayi waje abunta, a harabar gidan taga Fahad sanye da ƙananan kaya da tabarau yana tsaye a jikin motarsa, ta ƙarasa gurinsa tana wani yauƙi, tana ƙarasawa inda yake ya rungume ta, ba kunya ba tsoron Allah suka fara kissing ɗin juna a gaban ma'aikatan dake gurin, Fahad ya zame bakinsa a hankali yace
"you look so cute Baby"

Ramlah tace  "Really, you look good too baka ga yadda kayi kyau ba"

Ya riƙo ƙugunta yace "mu tafi ko"

"Ke Ramlah!" muryar Anwar ce cikin fushi yace "meye haka? Baki da hankali ne? Malama wuce ki koma gida"

Fahad yace "kamar ya ta koma gida, meyasa kake hakane Anwar"

A tsawace Anwar yace "zaki koma ko sena ɓaɓallaki a gurin nan, ballagaza kawai"

Da sauri Ramlah ta jiya da gudu cikin gida.

Anwar ya kalli Fahad yace  "Fahad kayi Asara wallahi, ita waccan da kake iƙrarin zaka aura baka samu ba, shine ka dawo zaka lallaɓa ka lalata ƙanwata, meyasa baka da imani Fahad, kana da 'yar uwa mace fa, baka tsoron ayimata abunda kake wa' ya'yan wasu, ya zakaji idan wani yayiwa Iman abunda kake yi "

Be rufe baki ba ya jiyo muryar Hajiya Halima tana masifa
" Anwar meye haka, yaushe ka zama haka? Ya zasu fita da yarinya zaka ce ba zata ba, tunda wannan shashashar ta ɓata ai ita ze Aura, me zesa ka kore ta haka akeyi? "

Anwar kamar zeyi kuka yace
" Mummy ke uwace, kamata yayi kisa ido sosai akan Yaran nan, yanzu ya dace Ramlah tabi saurayi da yammacin nan, kalli suturar dake jikinta fa"

"rufemin baki ko in gaggaura maka mari, ke wuce ku tafi"

Anwar yana kallo Ramlah ta shige motar Fahad, yayin da Fahad ke masa wani irin kallo na ya kaga lamarin.

Anwar dama Asibiti zashi gurin Alhaji Nasir, dan haka be sake cewa komai ba ya juya ya tafi.

Nura yace  "Bala'i ana shegiya a gidan Nasir Daula, duk iskanci shigar banza da izzar Gimbiyar Daula ban taɓa ganin ta aikata makamancin abunda wannan kwazgwamar tayi a gaban mu ba"

Isa me gadi yace "kaidai bari Nura, ai iskanci guri yake samu, kai da Yarinyar nan tana nan waya isa ya shigo gidan nan ya aikata wannan baɗalar, kuma wallahi kayan basu yiwa wannan shegiyar Ramlan kyau ba, wanka ai se Gimbiyar gidan nan, kaga kaya cas a jikinta kamar ita tayi kanta"

Nura yace  "kai dai bari Malam Isa, ni se yanzu nake ganin Amfaninta a gidan nan, duk wulaƙancinta idan tana nan se an bamu Abinci sau uku a rana munci mun ƙoshi a gidan nan, amma kalli yanzu sau ɗaya ma ba'a bamu"

Isa yace  "kai ba wannan ba, nifa ban gane kan wannan matar ba, kofa Asibiti basa zuwa, Anwar ɗin nan ne kawai yake zuwa yana kula dashi su kuwa ko a jikinsu"

Nufa yace "Hmm kai dai bar kowane munafuki inda ka ganshi, kallon mutan gidan nan kawai nake yi"

A kayan da Saleh ya kawowa su Yusuf, hadda kayan sawa ya kawowa Yusuf, dan Widad Akwatinan ta akawai kayan sawa, ya kawo musu man shafawa da sabulun wanka, dasu Omo, ya siyo musu sabon risho, da fitila sekuma kwalin batir, saboda garin ba Wuta.

Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, Ranar Juma'a bayan an idar da sallar juma'a aka ɗaura Auren Yusuf da Widad akan sadaki naira dubu goma sha biyar, shi kansa inda masallacin juma'ar nasu yake se anyi wata uwar tafiya daga nan inda su Yusuf suke kafin aje, ga shi duk ya lalace ya fatattake.

Nurat ce zaune a ɗakinta da system akan cinyarta, a hankali ta zare earpiece ɗin kunnenta tace "Alhamdilillah, done with this chapter"

Ta ɗakko wayarta ta kira Anwar, tayi sa'a ya ɗaga, ko gaisawa ba suyi ba tace "Alhamdilillah Yaya Anwar, na turo maka lamabar wani Bature, abokin cinikayyar baban Widad ne sosai, tare dashi za'ayi zaman taron kasuwancin, dan sune kusan wanda suke shirya taron kasuwancin, na san shi lokacin da nayi makaranta a England, muna zuwa gidansa tare da Widad, nayi masa bayani, Amma dukda haka nace zan bashi lambarka kuyi magana "

Jiki a sanyaye, tunda acikin damuwa yake yace " Madalla, Allah yasaka miki da Alkhairi Nurat, abokan kasuwancinsa da yakamata suyi wannan ƙoƙarin babu wanda yayi tunanin yin hakan, kowa harkar gabansa kawai yake, kamar ba wanda ya damu da halin da yake ciki"

Nurat tace "Hakane dama Yaya Anwar, kasan wani ya gayawa mahaifina naje duba Baban Widad, yanzu ya hanani fita kwata2"

Anwar yace "haba dai? Waye ya gaya masa?"

"Nima ban sani ba, amma insha Allah karka damu, zamu cigaba da communicating ta waya, ya jikin nasa kuwa?"

Anwar yace "to Alhamdilillah za'ace, yau dai naga jikin nasa ya tashi, dan se NG tube aka samasa tanan na bashi Abinci yau"

Nurat tace "Allah yasaka maka da alheri Yaya Anwar"

Anwar yace "Nurat kome nayiwa Alhaji Nasir Daula ai kaina nayiwa, karki damu Allah yayi mana jagora"

Ta amsa da Ameen.
Sukayi sallama tace "Alhamdilillah, saura kuma kuɓutar da Yusuf, Allah ka bani ikon kuɓutar dashi"  tunani ta shigayi, ta yaya zata san inda su Yusuf suke balle ta kuɓutar dasu?

Yusuf, da Saleh se megari da samarin 'ya' yansa suka shigo gidan, hannunsu ɗauke da goro dabino da alawa, uwargidan megari wadda suke cewa gwaggo tace
"Malam ya dai na ganku da kayan ɗaurin Aure haka? Bikinwa akeyi?"

Megari yace "baƙin 'ya' yanmu aka ɗaurawa Aure yau, ga naku kayan Ɗaurin Auren nan ayi musu addu'a"

Harira wadda itace matarsa ta tsakiya tace "Taɓɗijan kwaɗo, auda ba matarsa bace suke kwana ɗaki ɗaya? Aikin gama ya gama ai, me kuma za'a ɗaurawa Aure?"

Megari yace "ina ruwanki? Meye naki a ciki? Ke bakinki baya taɓa faɗar alkhairi"

Saleh yace "ke Hari ki iya bakinki akan mutanen nan, bana son rigima fa kin san halina, uwar gulma kawai"
Dama sun saba faɗa basa jituwa da Saleh sam

Gwaggo tace "daka gayamana da wuri, aida mun ɗanyi girki mun gayawa maƙwabta"

Saleh yace "gwaggona 'yar Aljanna, karki damu hakanma mungode, Allah yasaka miki da alkhairinsa"

Daga nan Yusuf da Saleh suka wuce ɗakin Widad, tana sanye da hijjabi da alama salla ta idar, tana zaune a gefen katifa suka shigo ɗakin, Yusuf ya ƙaraso gabanta ya ajiye mata goro da alawar ɗaurin Auren, ya miƙa mata sadakinta yace "uwaɗakina ga Sadakinki nan, an ɗaura Auren"

Ta ɗaga kai ta ɗan tsurawa Yusuf ido, sekuma ta sunkuyar da kai tana zubda hawaye, Yusuf yace  "me kuma ya faru?"
Girgiza masa kai tayi alamar bakomai, yace "ga sadakinki nan, ki karɓa na kine"

"ka barsu a gurinka ni ba'abunda zanyi dashi"

"Ai haƙƙinki ne, mallakin kine"

"Nikuma nace ka riƙe" tai maganar a ɗan hasale

"Ai hakan baze yuwu bane, amma ki dena kuka kinji, bana son yawan kukan da kike, nidai tunda na sanki kusan kullum cikin kuka kike, dan Allah kiyi hakuri ki sassautawa zuciyarki, wallahi ba ƙaramin damuwa nake shiga ba idan naga kina kukan nan"

Saleh yace "dalla in bazata karɓa ba, ka sai mata ɗan Akuya da kuɗin, idan na tafi ka zauna kayi ta rarrashin nata, kazo muje zanyi magana dakai, ina son in tafi kafin mutanen nan su farga"

Alhaji Musa ne a tsaye, hannunsa ɗauke da waya yace "wai kaji abunda naji kuwa, wai an ɗaga taron kasuwanci na kamfanunnukan Daula saboda bashi da lafiya"

Wanda yake wayar dashi yace "Naji, ƙarewa ma ni message aka turomin"

Alhaji Musa yace "to wani matsiyacin ne ya shirya hakan? Waye da wannan aikin, ya'akayi ma turawan nan suka san da bashi da lafiya?"

"Nima ban sani ba, nayi iya bincike na ban gane wanda ya gaya musu ba, amma dole muyi wani abu akai, idan wannan damar ta wuce mu, kuma bamu samu abun hannun 'yarsa ba to tabbas zamu tafka gagarumar asara"

Alhaji Musa yace "Shikenan, dole muyi meeting yau ƙarfe biyu na dare, zan sanar dasu Alhaji Haruna"

Ya kashe wayar yana cigaba da masifa, wayar ta sace ta sake fara ringing, a fusace ya ɗaga yace "meye waye?"

"Me Adda ne"

"Yawwa me ake cikine me Adda? Ta faɗa ɗin ko kuwa? Kaga idan bata faɗa ba, kusa flier ku dinga cire mata yatsu ɗaya bayan ɗaya har seta faɗa"

Me Adda yace "ka tsaya ka saurareni da kyau, yau kwana biyar kenan sun gudu da inda muka ajiye su, mun zaga ko'ina a dajin nam bamu samesu ba shine ma yanke shawarar in sanar da kai"

"what!!!"


(Mutanen Zamfara masu an yanke mana Network, da masu Anty cool daga farko, dan Allah idan kuna da manhajar Wattpad, idan kukayi searching ɗin littafin AƘIDATA kokuma Ayshercool7724 zaku sameshi tun daga farko har inda na tsaya, kuna bani aiki yaseen 🙄🙄🙄 duba ga yadda ake ta yaɗa cewar what's app ze dena aiki dukda bani da tabbas, ga link ɗin group ɗina na telegram nan meso se yayi joining
https://t.me/joinchat/SYIfEaoQo_JlNDM0 ina godiya da ƙaunar ku masoya 😍😍😍)

Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

    _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 32_33

Alhaji Musa yace "Me Adda, ina irin wannan wasan da kaine? Wace irin maganar banza kake faɗa haka?"

Me Adda yace "ba maganar banza bace, roofing kwano suka buɗe suka gudu"

"Roofing kwanon ne ba kuyi da kyauba kokuwa?"

"wallahi munyi komai yadda yakamata, ni babban abunda ya bani mamaki be wuce yadda ko iya miƙewa tsaye ba sayi saboda wahala, amma suka iya tserewa, ni yanz....

Alhaji Musa ya katse shi ta hanyar cewa " kaga dalla rufemin baki, na yadda da ƙarewarka  a wannan fannin shiyasa na baka aikin nan, amma ka kunyatani, shekara nawa kayi kana aikata irin wannan Aikin? Miyagun ayyuka mawa ka aikata kana Nasara, amma se yanzu wannan ɗan ƙaramin aikin ka bari har suka gudu saboda hauka, wallahi tun wuri ka nemo su na gaya maka"

Ya ajiye wayar tare da yin jifa da ita yana dafe kai, jinjina kai yayi yace "Akwai babbar matsala"

Ramlah ce kwance akan gadon Hotel, se bacci take yi kamar matacciya, ta lulluɓe jikinta da blanket, Fahad na gefenta yana ta busa shisha.
Seda yasha me isarsa sannan ya duba agogon hannunsa, ya miƙe zaune dagashi se gajeren wando, yaye blanket ɗin da Ramlah ke ciki yayi ya ɗagota zaune, ko sutura babu a jikinta, busa mata hayaƙi yayi a fuska, a hankali ta motsa ta fara tari, buɗe idanunta tayi wanda sukayi mata matuƙar nauyi ta kalle shi.

Fahad yayi wani murmushi irin na 'yan bariki yace "baccin ya isa haka, yakamata mu koma gida, kafin yaynki ya fara masifa"

Miƙa tayi ta sake kwanciya a jikinsa tace "ƙarfe nawa ne?"

"Ƙarfe takwas na safe" ya bata amsa, ba shiri ta watsakke tare da zaro ido tace

"takwas na safe, na shiga uku Fahad, wacw irin ƙwaya ka bani haka? Me zan cewa Mummy?"

Murmushi yayi yace "matsoraciya kawai, ashe iskancin naki na ƙarya ne, karki damu baby zance mata a gidanmu kika kwana kawai"

Tayi ajiyar zuciya tace  "kuma kasan Mummy tana yarda da maganar ka sosai, har naji daɗi wallahi I love you Fahad"

"Love you too baby"

"Fahad tunda Widad ta ɓata zaka Aureni?"

Ya sake rungumeta yace  "idan ban Aureki ba wa zan aura? Itama na yadda da Aurenta ne dan in Aureta in Wulaƙanta ta, Allah ya temake ta wannan abu ya faru, amma a duniya in bake ba wace macece ta dace da Fahad?"

Murmushi tayi tama jin daɗin kalamansa ma yaudara suna ratsa ta.

Saleh ya kamo hannun Yusuf suka fito waje, Saleh yace

" Samun mutum managarci me Amana kamarka abune me matuƙar wahala Yusuf, ka cika mutum nagari abun a jinjina masa, iyakar sadaukarwa kayi ta, ina fatan wannan Auren anyi shi kenan har gaban Abada, duk macen da ta auri namiji irinka yakamata ta gode Allah, nasan kayi haƙuri a baya dan haka ina fatan ka ƙara haƙuri, Widad yarinya ce me tsiwa da girman kai amma zakaji daɗin zama da ita, saboda tana sa sauƙin kai ga wanda ya gane kanta, dan wani lokacin gane kanta se a hankali, nasan zata baka wahala kafin ta saba da zaman garin nan, amma kayi haƙuri a hankali zata saba, babu wanda ta sani a yanzu daga Allah se kai, ka riƙe Amana Yusuf babu tabbacin ku koma gida Widad ta tarar da mahaifinta a raye! "

Wata irin mummunar faɗuwar gaba Yusuf yaji, yace " Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, me kake Nufi? "

"tunda kuka ɓata Daula yake gadon Asibiti, kullum zancensa 'ya' yana wani hali suke ciki? An ɗaga taron da suke burin ayi suyi amfani da sunan Daula su damfari biliyoyin kuɗi, yanzu idan suka farga kun gudu akwai gagarumar matsala, maganar da nake maka matarsa ba ita take jinyarsa ba, tana can tana shagalinta, babban ɗanta Anwar shike ta sintirin jinyarsa, sannan an bawa likitansa maƙudan kuɗi sunce yayi duk me yuwuwa kar Daula ya warke, Nayi duk ƙoƙarin da zanyi a rabashi da Asibitin amma ba hali, muddin nayi wani babban yunƙuri komai ze lalace "

Yusuf ya dafe kai ya shiga jera salati,
"Rananar da'aka ɗaukeku ni naje na janye Motar da kuke ciki daga titi na maida ita, aka cire lamabr motar, shiyasa na samu wayoyinku da kuma wannan Akwatunan naku, amma bazan baku wayoyin ba, dan nasan tabbas za'a iya tracking ɗin inda kuke, zan kawo maka ƙaramar waya da sim wadda zamu dinga communicating da kai, mahaifiyarka na gaisheka tana ta samaka Albarka "

Yusuf kasa magana yayi se zuciyarsa daketa faman tafasa, suka nufi turakar megari Saleh yace  " Baffa zan koma yau, na bawa ila kuɗi da kayan aiki, zezo yayi musu banɗaki, wallahi nan da kwana uku idan beyi ba, yasan halina, na bashi isassun kuɗi wallahi na dawo beyi ba koya cinye kuɗin sena karya shi, kaja masa kunne"
Megari yace
"Subhanallah zeyima Insha Allah, ɗakin nan da bakomai shi za'a gyara ba wani abu, ai kaine ka sashi zeyi insha Allah"
Saleh yayiwa Megari sallama, Yusuf ya ɗanyiwa Saleh rakiya sannan ya koma.
Gaba ɗaya kamar an zarewa Yusuf laka jin maganganun da Saleh ya gaya masa, ji yake tamkar mahaifinsa ne a wannan haɗarin, wani irin tausayin Widad ya kama shi.

Ya shiga gidan yana takawa da ƙyar, gwaggo ce tace "Malam Yusufa Allah ya Sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya, yasa anyi kenan kasan lamarin Aure se anyi haƙuri Allah ya baku zaman lafiya"

Yusuf ya ƙaƙaro murmushi yace "Ameen ya Allah nagode sosai"

Gwaggo tace  "sedai akwai ɗan bikin Al'ada da mukeyi anan in akayi Aure, yakamata mu gayyaci mutane mu ɗanyi mu tayaku murna"

Yusuf yace "Allah sarki Mama, base kin wahal da kanki ba, kinga ita Amaryar ma bata cikakkiyar lafiya kuma har yanzu a tsorace take, baki ga ko magana bata sonyi ba, Addu'ar ku da kulawar da kuke bamuma mungode sosai"

Gwaggo tace "shikenan Allah ya bata lafiya"

Yusuf yace "Ameen"

Jiki babu ƙwari ya ƙarasa ɗakin nasu, kayan ɗaurin Auren suna nan a inda suke, da kuɗin sadakin nata, tana zaune ta haɗe kai da gwiwa se rusar uban kuka take.

Dole Widad tayi kuka, rayuwar ta cike take da ƙaddara daban daban, a hankali ya ƙaraso bakin katifar ya zauna, sam bataji zuwansa ba seji tayi ya taɓa ta, a ɗan razane ta ɗago ta kalleshi, ganin Yusuf ne yasa ta maida kanta kan gwiwarta ta cigaba da kukanta.

Yusuf yasa hannu ya ɗagota yana kallon yadda farar fatarta ta koma ja saboda kuka da wahala.
Girgiza mata kai yayi amma yakasa ce mata komai, dan bema san ta'ina ze fara ba, Widad ta cancanci tayi kuka.

A hankali tasa hannu ta ture nasa hannun ta kwanta, tare da ɗora hannunta akan fuskarta tana ci gaba da kukan, A hankali take furta
"Ya Allah, aslihli sha'ani kullahu, wala takilni ila Nafsi, ɗarfatu ainun"

(wuya koda magani ba daɗi, ashe Widad ta iya Addu'a haka 🙄)

Yusuf ya zauna ya zuba mata ido wai a hakama bata san halin da mahaifinta ke cikiba kenan, inaga inta sani.

Yarone yayi Sallama ɗakinsu Yusuf, Yusuf ya amsa, yaron yace "Wai gashi inji gwaggo"

Yusuf ya karɓi ƙwaryar da'aka rufeya da faifai, yace "Masha Allah, kace mata mungode"

Yaron yace to ya fita, Yusuf ya ajiye Ƙwaryar yayi shiru yana kallon Widad da jikinta har rawa yake saboda tsabar kuka.

Yusuf yayi shiru, abubuwa suka cinkushe masa kai, nan da nan kansa ya fara sarawa, ya jingina da jikin bango ya rasa abunda yake masa daɗi.

A hankali Widad ta buɗe idonta, ta kalli inda Yusuf ke zaune yayi shiru, jijiyoyin kansa duk sun tashi, ga idonsa yayi ja kallo ɗaya zaka masa kasan a cikin damuwa yake.

Ta miƙe zaune a hankali, yai saurin juyowa yana kallonta, ta goge hawayenta tace
"me'aka kawo? Yunwa nakeji"

Yusuf yace "ban san me'aka kawo ba bari im duba"

Ya ɗakko ƙwaryar ya duba, fura da Nono ne aka dama, tace "bani cokali a can gurin"

Ya duba ya ɗakko mata, ya bata. Sosai take jin yunwa ta ɗiba ta kai bakinta, ajiye cokalin tayi a gefe ta kafa kai ta dinga sha, tasha ya kai rabi sannan ta ajiye, ta koma gefe ta zauna tana lumshe ido.

Yusuf yace "kin ƙoshi ne?" ta jinjina masa kai ba tare da ta buɗe idonta ba, yasa hannu ya ɗau wadda ta rage ya fara sha, an zuba zuma a cikin furar shiyasa tasha da yawa.

Gaba ɗaya Yusuf tausayi yake bata, beji ba be gani ba ƙaddara ta haɗasj se wahala suke sha tare, duk abunda za'a kawo na Abinci indai zata iya ci, se taci ta rage sannan zeci, kuma seya tabattar ta ƙoshi sannan ko yaya ta rage shima yaci.

Kallonsa take yadda ya duƙa yana shan furar, wadda ba isarsa za tayi ba, ta lura shidai a rayuwarsa be ɗau komai da zafi ba, irin mutanen nan ne da duk yadda rayuwa tazo zasu karɓeta a haka.

Yusuf ji yayi kamar tana kallonsa, ya ɗago kai ba tayi zato ba suka haɗa ido, tao saurin ɗauke nata idon.

Jiki a sanyaye yace "har yanzu dai kukan baki dena ba? Yakamata ace zuwa yanzu kin sawa zuciyarki haƙuri, kukan nan bashi da amfani, kina ƙaramin damuwa akan wadda nake ciki ne"

"Ni nace ka damu dani ne? Don't try to comfort me when ever am crying, kaji da damuwarka kaima"

Yusuf yace "tun daga lokacin da kika fara kuka saboda damuwa zuwa yanzu, maganin me kuka yayi miki? Kuka baya maganin damuwa wasu lokutan sema dai ya ƙara maka ƙuncin zuciya, ina tare da ke a guri ɗaya ta yaya zan zuba miki ido kiyi ta kuka, kina wahalar da kanki da yawa "

" kowa yaji da kansa malam ka dena damun kanka akaina"

Yusuf yace "Ai bazan iya bane, in dai kina kuka nikuma zuciyata rauni take"

Tsaki tayi tace "Se kai tayi ai"

Yusuf murmushi yayi bece komai ba.

Can tace "yanzu kaga death contract ɗin da nake gaya maka muddin zakayi aiki dani ko? Meyasa baka yi tunani akai ba kasa hannu, dukda na gaya maka haka? "

Yusuf yace "saboda shi bawa baya taɓa tsallake ƙaddararsa, Allah ya ƙaddara se haka ta faru"

Shiru tayi ta shiga duniyar tunani, tana cikin tunanin ne bacci ya kwasheta daga nan inda take zaune, ta lanƙwashe wuyanta.

Yusuf ya miƙe yaje da nufin ya gyara mata kwanciya saboda wuyanta, ashe baccin nata ba nisa yayi ba, ta buɗe idonta ta kalle shi, haɗe rai tayi tace "meye haka?"

"yi haƙuri, gani nai kin lanƙwasa wuyanki, kar yayi miki ciwo kuma bana son in tasheki"

"to ina ruwanka inma yayi min ciwon? Dalla cikani kuma karka ƙara taɓani na gaya maka"

(Nikam nace Mamaki 😂 jimin mara kunya, sekace yau aka fara)

Murmushi yayi yace "shikenan Allah ya huci zuciyarki"

Ta kwanta tareda juya masa baya, Yusuf ya ƙura mata ido tare da yin murmushi a ransa yace 'insha Allah sena maye gurbin wannan damuwar taki da farinciki'

Yusuf ji yake kamar bashi ba, wai shine ya Auri Widad, yasan badan ƙaddara ta Ubangiji ba, kamar shi a yadda yake ya Auri mace irin Widad kyakkyawa 'yar me kuɗi haka, sedai wani iko na ubangiji.

Haka nan yake fatan Allah yasa su kasance tare har Abada, Allah yasa idan ta gano waye shi karta guje shi.

Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare, Nurat taji motsi a harabar gidansu, ta leƙa ta taga ta hango mahaifinta ya fita shida direbansa, tunani ta shiga yi ina mahaifinta zeje a wannan daren haka? Tashi tayi ta tafi ɗakinsa, ta murɗa ƙofar a hankali ta shiga, ƙarƙashin gadonsa taje ta ɗakko wayarta da ta ajiye ta kunna recording.

Tayi saving ta fito daga ɗakin ta koma nata ɗakin, anan taji wayar da yayi da batun kuɓutar su Widad, da sauri ta miƙe tsaye tana Alhamdilillah, ta dinga kunna recording ɗin tana sake saurara, hankalinta ya koma son sanin me zasu tattauna a meeting ɗin da zasuyi a wannan tsakiyar dare kamar wasu matsafa.

Babban falon Hotel ne suke zaune, sunyi jugum jugum kamar masu jiran tsammani kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin damuwa.
Alhaji Haruna yace  "jama'a ayi magana, abubuwa da sun taho kamar abun arziki, amma yanzu komai taɓarɓarwa yake, ta yaya za'ace sun gudu se kace a film, ko wata tatsuniya.

Alhaji Munir yace "nima abun ya ɗauremin kai, ga kuma wannan samu da rashi da muka gani, muna shirya abu amma wai an fasa taron, wannan shegun turawan ne suka ce a ɗaga, na rasa wani baƙin munafukin ne ya gaya musu ba, nifa kaina gaba ɗaya ya kulle"

Alhaji Musa yace  "babu yadda za'ayi ace su kasa jim rashin lafiyarsa ko kun manta shahararsa ne? Dole zasuji ai"

Wayar hannun Alhaji Musace ta fara ringing, ya fito da ita ya ɗaga .

"ban samu halartar zaman da kuke a daren yauba, hakanma duk yana cikin shirina ne, yakamata ku maida hankali gurin gane cewar wani yana muku zagon ƙasa, akwai na jikinku wanda yasan siriinku shine yake ta dagula muku lissafi, ku maida hankali gurin gano waye, sannan kusam duk yadda zakuyi ku kama wanda sukayi garkuwa da 'yar gidan Daula ku kashe su, in bahaka ba akwai gagarumar matsala, sannan ko a mace ko a raye ku tabattar an kama yaran nan an kashesu"  yana gama maganar ya kashe wayarsa.

Nan fa suka sake shiga wani ruɗanin, tabbas inba wanda yake cikinsu ba babu ta yadda za' ayi Su Widad su iya tsira daga inda aka ɓoyesu.

Alhaji Haruna yace "to kun daiji abunda Alhaji Bukar yace, yanzu abunda za'ayi shine, kusa a binciko mana wanda aka bawa bincike hukumar jam'ian tsaro, ayi karɓo mana sakamakon binciken, hakan ze ƙara haska mana wani abun"

Alhaji Munir yace "wannan kuma aikin Saleh ne, shi'aka ɗorawa wannan ragamar"

Alhaji Musa yace "Na kira shi sam labarsa bata shiga, inaga zan tura ɗan aike a kiramin shi da safe"

Haka suka gama tattaunawa suka tashi ba tare da cimma wata ƙwaƙwarar matsaya ba.

Da safe Hajiya Halima nata safa da marwa, layin Ramlah sam baya shiga, ƙarfe goma na safe sega Ramlah ta dawo, Hajiya Halima tace  "daga ina kike?"

Kafin tayi magana Fahad ya shigo, Yace  'Mummy barka da safiya, mun miki laifi ko? Wallahi bayan mun dawo daga cinema ne naga kwana biyu ba taje gidanmu ba, kawai muka zarce can, daga nan kuma mumsy tace seta kwana tunda bata zumunci "

Hajiya Halima tace " Aida ta kira ta gayamin, hankalina ya tashi ince kaddai kuma an sace mana ku"

Ramlah tace "haba Mummy wani irin sacewa kuma, ai an san wanda ake sata, ina tare da Fahad waye yavisa ya saceni"

Sukayi dariya gaba ɗaya, Fahad ya kashe mata ido, sukayi Sallama ya tafi.

Ramlah na zuwa ɗakinta ta jefar da jakarta ta kife akan gado ta cigaba da bacci, saboda har yanzu ƙwayar da ta sha bata saketa ba, kuma ga rashin sabo dama, dan bata taɓa shan kayan maye ba.

Yusuf bayan ya dawo daga sallar Asuba, har ya kwanta ya tashi, ya duba shimfiɗar Widad yaga bata nan, zumbur ya miƙe zaune a gigice yana waige waige, miƙewa yayi ya fito tsakar gidan bakowa, saboda yanayin garin da sanyi kuma gari be gama waye ba, leƙe leƙe ya shiga yi yana nemanta, can ya hangota daga wani ɗan lungu tana tsaye tana leƙa wata taga se murmushi take, hannunta riƙe da brush da toothpaste, kan nan ko ɗan kwali babu, gashinta ko taza babu ta naɗeshi da ribbon ya kwanta a bayanta.

A hankali ya ƙarasa inda take cike da son sanin me takewa wannan murmushi haka?

Jin mutum tayi a tsaye a bayanta, ta juyo a ɗan razane, Yusuf ta gani a tsaye a daf da ita.

"meye haka?"

Yusuf yace "gani nayi kina tsaye kina murmushi, shiyasa nace bari inga abunda ya saki nishaɗi haka? Sannan gari akwai sanyi fa, kalli kanki babu ɗan kwali kar mura ta kamaki, sannan kayan jikinki  maza na shiga na fita a gidan nan, kar gari yayi haske suzo su sameki a haka, su kansu matan gidan zasu ga hakan wani iri saboda ya saɓawa Al'adunsu"

"Wai kai meyasa ka fiye shishshigi da takura ne?"

"ba shishshigi da takura bane, kinga yanzu kina da Aure fa"

"kaga wannan Auren fa dashi da babu duk ɗaya, karka ƙara sawa ranka wani Aure mukayi"

Yusuf ya ɗanyi murmushi, cike da basar da zancen  yace   "kin tsorata nifa, harna kwanta na duba ban ganki ba, shiru shiru kuma naga baki shigo ɗaki ba"

"hmm kayi zaton zan gudune? In gudu inje ina? Ko kana zaton zan gudu da wannan Auren naka a kaina? Idan kaga na gudu ko na bar ƙauyen nan to tabbas ka sakeni ne"

Yusuf yace "idan kuma ban sake kin bafa?"

Juyowa tayi ta saka idonta a nasa tace "me kace?"

Girgiza mata kai yayi alamar bakomai, ta harareshi tace  "ban guri in wuce"

Seda ta tafi ya Leƙa me take kallo, ɗakin zomaye ne, an kunna musu aci balbal an rataye ta, se guje guje suke suna haƙa ƙasa, da wasanninsu shine abunda yasa ta nishaɗi ta tsaya take kallonsu.

Yusuf ya koma ya kwanta bacci ya ɗauke shi, ita kuwa Widad data gama brush ɗin komawa tayi ta cigaba da kallon zomaye, seda ta gaji sannan ta koma ɗaki.

Yusuf yayi juyi ya buɗe idonsa a hankali, ya sauke su akan Widad, ta gyara shimfiɗarta sa kanta, ta sauke Akwatunanta tana ta gyara kayan ciki, ta ware masu datti ta tattare Akwatunan ta canza musu guri, duk Yusuf yana kallonta, Widas sam bata son ƙazanta, tana da matuƙar son tsafta a rayuwarta.

Yusuf ya tashi ya kwashe kayan shimfiɗarasa ya ninke, bata kula shi ba sabgoginta kawai take, Yusuf yayi mamakin danganar da Widad tayi, dukda har yanzu bata saba da abubuwa da yawa ba.

"wai babu inda za'a samu inji wanki ne? Ina son a wanke min wannan kayan ne"

Yusuf yace "Ai baki da wani injin wankin daya wuceni, in kin haɗa se in ɗiba inje in wanko su"

Widad tace "kaine zaka wankemin kayan?"

Yusuf yace  "eh mana, ko kinga alamar injin wanki a garin nan, tunda muka zo kin taɓa ganin wuta?"

"to gasu nan na haɗa, kaje kace a bani ruwan wanka"

Yusuf ya girgiza kai yace "to"

Ya miƙe ya ɗau bokiti ya fita, Widad ta buɗe Akwatinta ta ɗakko towel ta ɗaura, ta saka hijjabi ta biyo bayansa yadda ana haɗa ruwan se ta shiga tayi wanka.

Mutan gidan sunata hada Hadar yadda za'a haɗa karin kumallo, ga dukkan alamu yau mutuniyar Widas ce da girki, wato Harira.

Yusuf ya durƙusa ya gaishesu, cikin jin nauyi kafin yayi magana Gwaggo tace  "Yusufa na ganka da bokiti, ruwan wankan za'a zuba mata?"

Yusuf yace  "eh Mama"

Tace  "kawo in zuba maka anan, ya jikin nata kuwa"

Yusuf yace "jiki Alhamdilillah"

Tace  "Madalla, nikam ya sunan nata ne? Bamu san sunanta ba"

Yusuf yayi murmushi yace "Sunanta Widad"

Hari dake gaban murhu ta juyo da sauri tace 

"Bala'i, wannan wane irin sunane? Hudas ko wudas sekace kayan citta da masoro wane irin sunane wannan"

Tsakin Widad ne yasa Yusuf juyawa, yadda ta tamke fuskane ya tabattar maaa sa taji abunda Hari tace, Yusuf kamar yayi dariya Amma ya basar kar suyi faɗa a gaban mutane.

Gwaggo tace "kaga 'yar halak, ana zancenta se gata, sedai ni wannan sunan nata na Larabawa bazan iya faɗa ba, Amarya ya jikin naki?"

Widad a ranta tace "wai Amarya Taɓɗijan"

Yusuf yace "Ana miki ya jiki?"

"Naji sauƙi"

Galala Hari ta bita da kallo tace "Ashe bahaushiya ce, wallahi ganinta nake kamar bata jin hausa, yo aini harna fara tunanin ko kurma ce, ashe tana magana sannu Amarya wudas, ashe kina magana Allah sarki, ya jiki?"

Sake yamutsa fuska Widad tayi, 'ita dai wannan matar bata gajiya da magana, kodai bata san yadda haƙoranta suke bane take buɗesu tana surutu haka, bar wani kore kore ne a jikinsu, ga maganar tsiya da take dashi"

Widad bata kulata ba, aka haɗa mata ruwanta, Yusuf ya kaimata inda take wanka.

Aka haɗa Yusuf da yaro ya rakashi rafin da matasan garin suke haɗuwa suyi wanki.

Amlace ta shiga ɗakin Ramlah, ta dinga bubbuga mata filo, da ƙyar Ramlah ta tashi a fusace tace  "Meye haka Amal?"

Amal tace  "Anya lafiyar ki kuwa? Ƙarfe biyi fa, amma har yanzu bacci kike, yakamata ki tashi haka ai"

Miƙewa tayi zaune tana miƙa tare da duba agogo, dagaske biyu na rana, haka ta miƙe ta tafi banɗaki tayi wanka sannan ta ɗanji ƙarfin jikinta.

Koda Saleh ya dawo kano, be biya ko'ima ba Asibiti ya fara zuwa duba jikin Alhaji Nasir, amma yanayin jikin nasa se godiyar Allah, Nurses suka gaya masa Anwar yaje masallaci.

Saleh ya zauna a kusa da Alhaji Nasir, wanda idanunsa ke lumshe yake numfashi da temakon Na'urar dakw bashi iskar Oxygen, ya riƙo hannunsa da suka yi sanyi ƙalau, cike da tausayawa ya kai bakinsa daidai kunnensa  yace
"Allah ya baka lafiya Yallaɓai, 'ya' yanka sun kuɓuta daga hannun miyagun nan, yanzu haka suna wasu ƙauye na basu mafaka, saboda tseratar da Rayuwarsu, Yusuf yayi ƙoƙari matuƙa ya kula da Amanarka, yana kula da gimbiyarka sosai, Amma munyi maka wani laifi da ban san ya zaka ɗauki abunba, Na wuce gaba Yusuf ya Auri 'yarka, dan kasan bata yadda da kowa seshi, kuma baze yuwu ya cigaba da kula da ita ba, tunda ba muharramarsa bace"

Dukda Alhaji Nasir ba iya magana zeba, da alama yana jin abunda Saleh yake faɗa, ƙara riƙe hannun Saleh yayi gam sannan yayi masa murmushi.

Saleh yace "Amma karka kuskura ka gayawa kowa, kayi shiru da bakinka"

Anwar ne ya shigo bakinsa ɗauke da Sallama, yana ganin Saleh yayi murmushi yace "Saleh sannu da zuwa, naje Sallane"

Saleh yace  "bakomai Anwar, ya me jiki?"

Shiru Anwar yayi, ƙwalla na taruwa a idonsa yace 

"Saleh na rasa wane irin abokai Allah ya bawa bawan Allah nan, sam hankalinsu baya kansa, amma lokacin da yake da lafiya sune kan gaba gurin nuna masa ƙauna, Amma dubi yanzu, look at how he's suffering alone, ba wanda ya bani mamaki kamar mahaifiyata"

Anwar ya ƙarasa maganar, jijiyoyin kansa na tashi idonsa yayi ja, Alhaji Nasir ne yayiwa Anwar Alamar yaje da hannunsa.

Anwar  ya ƙarasa gaban gadon Alhaji Nasir ya zauna.

Alhaji Nasir ya kamo hannun Anwar, sannan ya miƙa hannunsa ɗaya yana shafa kan Anwar tareda yi masa murmushi a hankali yace  "Nagode, Nagode"

Kawai Anwar ya rungume Daula ya fashe da kuka, shima Daula hawayene suka fara bin gefen idonsa, da ba ƙaramin mamaki ya shiga ba, ganin yadda gaba ɗaya mutanensa da suke tare dashi suka watse suka barshi, ciki harda matarsa da take morarsa.

Yusuf yaje ya tarar da matasa da magidanta a gurin wankin nan, wasu na wanki wasu na wanka a ruwan, in an koro dabbobi suma suzo su sha ruwan, amma a haka yaga wasu na ɗiba na tafiya dashi abun ya bashi mamaki, dama a gurin salla megari ya gabatar dashi, dan haka wasu daga cikinsu sun sanshi.
Duk rashin son mutane irin na Yusuf ya ɗan sake dasu, suka dinga hira suma bashi labari akan yanayin garin nasu.
Abun ya dinga bawa Yusuf mamaki, suna rayuwa cike da son juna mutanen ƙauyen, sedai abun mamaki ɗan majaillisar dake wakiltar yankin kakannisa 'yan garinne, amma abun mamaki sukace lokacin da yake campaign har falafalan wuta aka samu su, ya gina musu borehole guda ɗaya can wajen gidan kakaninsa shima se anyi tafiya me nisan gaske borehole ɗin yake, yace idan suka zaɓe shi yaci ze janyo musu wutar lantarki, tundaga wannan campaign da yazo tsawon shekara uku basu sake ganinsa ba, ko gidan kakannin nasa baya zuwa ziyara gaba ɗaya ya koma Abuja.
Haka Yusuf suka cigaba da hira shikuma yana wankinsa, seda ya gama suka bushe ya ninko kayan tsaf, sannan suka taho sa wani maƙocin gidan megari zuwa gida.

Yana zuwa gida ya tarar da Widad a ƙofar ɗakinsu a zaune, zaman dirshen a ƙasa fuskarta tayi jawur saboda kuka, Yusuf ya razana ko ciwonta ne ya tashi.
Gwaggo na ganinsa tace "yawwa Yusufa, wallahi muna tsakar gida muna aiki muka jiyo ihunta, ta fito da gudu mukaje kanta, juyin duniya taƙi magana tayi zamanta a nan gurin, munce ta bar ranar ta shiga ko ɗakina ta zauna taƙi.

Yusuf ya ƙarasa inda take ya ajiye bokitin hannunsa me ɗauke da ninkakkun kayansu  yace "lafiya kuwa? Meyasameki haka?"

Cikin harshen turanci tace masa, "wasu ƙwarine suka yi ta cizona, sekuma naga spider manya guda biyu a ɗakin, dana fito nan ma ƙwarin suka cigaba da cizona"

Girgiza kai yayi yace "shikenan tunda na dawo tashi mu shiga ɗaki, kalli a yadda kike kin zauna a tsakar gida kowa yana kallonki a haka, kuma kinga kin tayarwa da mutanen gidan hankali"

"wallahi bazan shiga ba se an cire wannan spider ni bana sonshi, bana son ganinsa it's irritating me, looks at my body"

Se yanzu ya lura da yadda kafofin gashinta suka buɗe, jikinta yayi wani irin burɗin_ burɗin, fuskarta ma tayi ja saboda cizon sauro.

Hari tace "Allah dai yasa ba wani abun mukayi mata ba, dan naga alamar makirace, tun ɗazu muke fama taƙi magana, Amma tana ganin mijinta ta fara magana hadda karairaya"

Widad ta ɗaga kai ta ƙurawa Hari ido, yayin da gwaggo taji haushin abunda Harin tayi.

Yusuf kam ba ƙaramin dariya Hari ke bashi ba idan ta kunna Widad, yasan Widad tana mata kawaici ne kafin ta ɗan sake.

Yace "ba wani abun kukayi mata ba, wai wani abune ya cijeta amma, bakomai yanzu zan shiga in duba"

Yusuf ya shiga ya duba bega gizo2 ba, sedai cinnaku dake yawo a ɗakin, da alama su suka cijeta.
Yasa tsintsiya ya shashsharesu tsaf, sannan yace ta dawo ɗakin.

Yusuf "Yace meye ya cijekin?"

Guri ta zauna ta janye rigar jikinta, ta nuna masa cinyarta, fara tas fiye da fuskarta, sedai tayi ja saboda cizon cinnaka, banda wanda ya gasa mata a hannu.

Yusuf yace  "Sannu bari in tambayi gwaggo inda zaitun ta bani ki shafa"
Zumɓura baki tayi tace  "ni banyi wanka ba"

Haka ya karɓo ruwa tayi wanka, sannan ta dawo ɗakin, ya bata guri ta sa kaya, ya ɗakko zaitun ta zauna ya shafa mata a na hannun, ya fara shafa mata a ƙafarta ne a hankali, haka kurum taji jikinta wani iri, kawai seji yayi ta doke hannunsa tace
"meye haka?"

"Me kuma nayi miki?"

"ban sani ba" ta bashi amsa tare da miƙewa, ɗan sunkuyar da kai yayi yana murmushi.

Daga Asibitin gurin Alhaji Musa Saleh ya wuce, yaje ya sames hi a office ɗinsa.
Saleh yace  "Ranka ya daɗe kwana biyu bani da lafiya, ko ƙofar ɗaki bana iya fitowa, shiyasa kwana biyu bana zuwa"

Alhaji Haruna yace "Akwai damuwa fa, ko Kasan me Adda ya cemin yarinyar nan sun gudu"

A razane Saleh yace "wace irin maganar banzace wannan? Kamarya sun gudu?"

"Nima dai abunda na gani kenan, gaba ɗaya sun mayar mana da aiki baya, yanzu Bukar yace ko a raye ko'a mace anemosu a kashesu kar Asirinmu ya tonu, sannan kaje ka bincika mana wa'aka bawa aikin binciken nan a cikin jam'ian tsaro?"

Saleh yace "Amma fa wani hanzari ba gudu ba, ina kyautata zaton me Adda yana sane ya sake su, wataƙila tace zata bashi kuɗine koma ta ninka masa abunda kuka bashi, shine ya sake su, in bahaka ba ta yaya zasu iya tserewa? Kokuma a cikinku ne wani ya zagaya ya haɗa baki dashi, idan an karɓo abun a gaya masa shikaɗai ba"

Shiru Alhaji Haruna yayi yace "Biri yayi kama da mutum, kuma fa Saleh kayi magana, tabbas dan nasan zata iya, kuma babu Abunda me Adda baze iya akan kuɗi ba"

Jinjina mara adadi ga ɗumbin masoya littafin AƘIDATA, niba abunda zance muku se godiya Allah ya bar ƙauna, ga dogon page nan, nima inga dogon sharhi, ga link ɗin telegram nan a ƙasa

https://t.me/joinchat/SYIfEaoQo_JlNDM0

Share, share and share please 🙏 🙏 🙏
Domin gyara sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680

                       _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 34_35

Saleh ya cigaba da ziga Alhaji Haruna, akan lallai yayi bincike, dan zata iya yuwuwa abokan harƙallaesa ne wani yasa a karɓo masa abun hannun Widad, shiyasa me Adda yace masa sun gudu.

Alhaji Haruna yace "Nagode sosai Saleh, Insha Allah zanyi tunani akai"

Saleh yace "bakomai yallaɓai, bari in ɗanje gida in huta, kasan bana jin daɗin jikin nan nawa"

Alhaji Haruna yace  "shikenan Allah ya sawwake"

Saleh ya tashi ya tafi

Sakina ce fuskarta ɗauke sa damuwa ta shiga ofishin Suleiman, Suleiman yace "Sakina lafiya kuwa?"

Sakina tace "Yallaɓai akwai damuwa, yau sati biyu sa sace Yusuf amma har yanzu babu wani kyakkyawan rahoto, da yake nuna ana bincike akan lamarin nan, anya anyi adalci kuwa duba da yadda Yusuf yake bada gudunmuwa akan harkar tsaro, amma ace shi wannan iftila'in ya faɗa masa amma babu wani yunƙuri da'ake gurin ceto shi, idan ya rasa ransa fa? "  ta ƙarasa maganar kamar zata yi kuka.

Suleiman yace "look Sakina, kiyi wani tunani kodan Albarkacin 'yar babban attajirin da' aka sace su tare, yaci ace an maida hankali akan nemansu, amma har yanzu shiru, shikansa Daulan yana gadon Asibiti a kwance, na kai ƙorafi akan abari muma mu gudanar da namu binciken, amma daga sama aka bani umarnin cewar ba'a samu ba, ana gudanar da bincike akan al'amarin, babu wani abu da zamu iya banda muyi musu Addu'a "

Sakina tace " shikenan Yallaɓai, ubangiji Allah ya kuɓutar dasu lafiya, bari in koma kan aikina"

"Shikenan Sakina, Allah ya taimaka"

Sakina na tafiya, telephone ɗin gaban Suleiman ta fara ringing, ya sa hannu ya ɗaga, jin muryar wanda ya kira shin yasa shi miƙewa tsaye cikin girmamawa yana amsa wayar.

"A cikin ma'aikatanka wa'aka saka akan binciken masu bibiyar Alhaji Nasir Daula?"

Suleiman yace  "Yallaɓai Yusuf ne, wanda aka ƙarawa matsayi kwanan nan"

"A gaggauta kammala binciken nan, a miƙo bayanan binciken nan headquarter"

Suleiman yace "Ok Sir"

Yusuf ya kalli Widad da tayi kicin kicin da fuska yace "ga kayan nan na wankesu, sun bushe ma gaba ɗaya"

Tasa hannu ta ciro kayan daga bokiti, taga kayan a haɗe dana Yusuf, kwashe nata tayi ta zube masa nasa a gurin, Yusuf yasa hannu ya kwashe ya zuba a jakarsa.

Ya kalleta yace "kinci Abinci kuwa?"

"ni banci wani Abinci ba, kaga fa abunda aka kawo"

Kwano ta miƙa masa, yasa hannu ya buɗe dafaffiyar masarace a ciki da ɓawonta da komai, Yusuf yace "to me yasa baki ciba?"

"ta ina zanci ? Kawai se in kama cin masara, ni ban taɓa ganin anci masara ba, nidai kawai nasan Abinci akeyi da ita, amma ba'aci"

Yusuf yace "ikon Allah, wannan wace irin hausa ce? Waye ya gaya miki ba'a cin masara"

Ya zauna ya ɓare masarar tsaf, ya ɗaurayeta, yace "nasan kece baki taɓa ciba, amma ana cin masara dafaffiya ko gasashiya, ci kiji"

Ɗauke kai tayi taƙi karɓa, Yusuf kuwa yasa masara a gaba ya fara ci, zuba masa ido tayi tana kallon ikon Allah, yana nufin itama haka zata ɗau masarar ta dinga wannan kokawar haka sekace wata saniya.

Plate ya ɗakko ya shiga ɓanɓarowa yana tara mata a plate yace "gashi na ciro miki ɗauki kici"

Ba kunya tasa hannu ta fara tsinta tana kaiwa bakinta, dan bilhaƙƙi ita bata taɓa ganin ana cin masara a haka ba, amma kuma tabbas da daɗi, ya dinga cirowa yana tara mata tana tsinta tana ci, kamar wata 'yar yaye, cikin ikon Allah a haka kuma ta ƙoshi.

Shiru tayi ta tuna lokacin da sukaje restaurant cin Abinci, Yusuf yake gayamata Naira ɗarin cin Abinci tana gagarar wasu, take ganin kamar ƙarya yake, se gashi yanzu ta gani da idonta, da wanine ya bata labarin ana dafa masara aci a matsayin Abinci zata ce ƙaryane dan bata taɓa gani ba.

Can Yusuf yace "inda ƙwaron ya cijeki ya dena zafin?"

Ta gyaɗa masa kai alamar eh, yace "hannun da'aka harbe ki fa?"

"yayi sauƙi, ina iya motsa hannun sosai, sedai idan ma bige ne nake jin zafin"

Yusuf yace "masha Allah, Allah ya ƙara miki ingantacciyar lafiya"

Shiru tayi kamar ba taji ba, Yusuf yace "Addu'ar ma bakya so?"

Shiru tayi masa tana sake ƙarewa roofing ɗin ɗakin kallo, tana son gane dame akayi shi.

Yusuf yace "me kike kallone?"

Widad tace  "kai subhanallah, wallahi ka dameni da surutu haba, sekace waccan matar me haƙora"

Yusuf yace "to shikenan na dena gimbiyata"

Ɗagowa tayi ta masa wani irin kallo, ba shiri ya miƙe yayi waje ya bar mata ɗakin yana murmushi.

Wasa2 Ramlah ta ganewa shaye2, bata salla se wajen ƙarfe takwas na safe, da ta idar zata ɗakko Coca-Cola tasha, seta kai ƙarfe biyun rana tana bacci.

Yanzuma Amal ce ta shiga ɗakin Ramlah, ta tarar da ita tana girgiza jarkar Coca-Cola.

Amal tace  "Ramlah, wai me yake damunki ne haka? Wane irin coc ne kike sha ba yau ba gobe ga shegen bacci kamae kin haɗiyi kasa"

Ramlah ta kalleta tace "kina da matsala da hakanne?"

"ba wai batun ina da matsala da hakan bane, sedai cewa kina ganganci da rayuwar ki, baccin da kike ya wuce ƙa'ida, kuma wannan coc da kike sha yayi yawa sosai, nifa na fara zargin wani abu kike sha a cikin coc ɗin nan"

"Ke Amal! Ki kiyayeni, dalla wuce ki barmin ɗaki, ina ruwanki dani idanma wani abun nake sha?"

Amal tace "shawara ce nake baki, amma

" wallahi Amal in baki barmin ɗaki ba sena miki rashin mutunci, Dalla ƙara gaba kije kiji da kanki"

Amal tace "shikenan Kije ki ƙarata" ta fito daga ɗakin.

Yanzu kusan kullum se Ramlah ta fita, ko tare da Fahad ko ita kaɗai, kuma Hajiya Halima bata taɓa yi mata magana akan hakan ba.

Anwar kam ya tattara yasa musu ido, ya maida hankali akan kula da Alhaji Nasir, kwata kwata ya dena shiga sabgarsu ma.

Abubuwa suka fara cakuɗewa su Alhaji Musa, suka kuma hayar wasu 'yan ta' addan domin a nemo musu  su Me Adda, yayin da Alhaji Haruna ya keta tunani akan maganar da Saleh ya gaya masa game da tserewar Su Yusuf.

Meeting suke akai akai akan yadda zasu ɓullowa al'amarin,
Alhaji Munir yace  "tabbas idan har yaran nan suka kuɓuta suka dawo Asirinmu ze iya tonuwa"

Alhaji Musa yace "yakamata ku kwantar da hankalinku, babu yadda za'ayi Asirinmu ya tonu, yanzu naga Likitan nan yana aikin da muka sashi,  dan yanzu baya gane waye akansa sam"

Alhaji Haruna yace "hakane Daula ya zama abun tausayi, talakawan da yake fafutuka akansu, an hana kowa zuwa inda yake, manyan ƙasar nan ma kowa yayi watsi da lamarinsa, yanzu haka nasa Jam'ian tsaro su hana kowa shiga inda yake, se ɗan matar nan tasa, shi kuma wannan soko ne, ba abunda yake ganewa, shekaranjiya wasu baƙin turawa sunzo duba shi, amma an hana su ganinsa ance yana ƙarƙashin kulawar likita baza'a ganshi ba"

Alhaji Musa yace "Good hakanma yayi, a hana kowa zuwa inda yake muyi yadda muke so, Amma Nifa har yanzu ina mamaki akan guduwar yaran nan, kuma da suka kuɓuta aida zasu dawo a gari a gansu, amma har yanzu babu wanda yaji ɗuriyarsu"

Alhaji Munir yace  "ni kaina abunda yake ɗauremin kai kenan, zuwa yanzu ai yaci ace anji labarin sun dawo, amma babu wanda yaji hakan"

Alhaji Musa yace "shiyasa nake tunanin akwai wata a ƙasa ruwa baya tsami banza, akwai munafiki a cikin mu"

Alhaji Haruna yace "kamarya? Kana nufin a tsakaninmu munafikin yake kokuwa?"

Alhaji Munir yace "kunga ya isa haka, nima nayi zargin haka amma babu lallai da munafuki a tsakaninmu, sedai a wanda suke mana aiki tabbas, kokuma akwai wani a gefe daya ke farautar abunda muke nema"

Alhj Haruna yace  "ba abunda baze iya faruwa ba, Amma kar mu ɗora komai akan zargi semun tabattar"

Kamar yadda Saleh ya bada umarni, aka ginawa Widad nata banɗakin, akwai wata ƙatuwar rijiya a gidan ruwan sam bashi da kyau, haka nan ake amfani dashi a gidan, ko kuma mutum yayi tafiyayyiya yaje rafi ya Ɗebo.

Yusuf kuwa tafiya yake me nisa, yaje ya ɗebo ruwa a wannan borehole guda ɗaya tal ta garin, yazo gida ya tafasa idan ya huce seya zuba a randarsu suke amfani da shi a matsayin na sha.

Har yanzu Widad bata saba da kowa a gidan ba, ba ruwanta dasu sedai in sun haɗu a tsakar gida suka mata sannu ta amsa, amma bata shiga sabgar Hari sam, saboda Hari baƙar magana take gaya mata.

Yanzu ma tana tsugune tana brush da yamma, yaran Hari suka kewaye Widad suna kallonta, mussman dogon gashinta dake ɗaukar ido, gata ba ma'abociyar saka kallabi ba, abun haushi hadda 'yan matan gidan da suka tasa, se kallonta suke ita ta rasa se yaushe zasu saba da ganinta su dena mata wannan kallon haka?.

Widad tace "kai me kuke kallone, haba bana son kallon nan da kuke min, did i look like a beast?"

Hari tace "yo sunga abunda basu saba gani ba, kin fito tiɓitiɓi da wasu irin kaya ai dole su kalleki ni wallahi da ban zaci ma musulma ce ke kina jin hausa ba"

Widad tace "eh ba musulma bace ni, gunki nake bautawa yana ɗaki idan kina so ki ganshi"

Sam hari bata zaci Widad tana da baki hadda baƙar magana ba.

Gwaggo tace "Amarya ƙyaleta kiyi haƙuri"

Sannan ta kalli Hari tace "haba Hari, kin fiye magana wallahi duk haƙurin yarinyar nan kinsa ta fara tanka miki"

Hari tace "yo Yaya yara sunga abunda basu saba gani ba ba dole su kalla ba"

Yusuf yana ta tunanin wace sana'ar ze ɗan fara, saboda ya saukewa mutan gidan ɗawainiyar da'ake dasu, ga Widad bakomai take ciba duk ta rame, ya dawo daga sallar Azahar ya tarar an kawowa Widad gujjiya, tanaci hadda ɓawon, Yusuf yace  "mekike ci ne?"

Ta ɗan taɓe baki tace "na manta sunanshi, amma inaga wake ne wannan maman ce ta bani"

Yusuf ya kwashe da dariya, ta haɗe rai tana kallonsa, yace "haba Madam, wannan ne waken? Kuma da ɓawo kike ci bari kiga"

Ya zauna yana ɓarewa yana bata, ita tunda take bata san wata gujjiya ba, da taci a baki se taji kamar wake, ta zata ma wake ne yazo a haka.

Tun Yusuf yana mamakin bata san abubuwa da yawa ba, har ya dena mussman duba da yanayin rayuwarta, ita ba sakewa take da mutane ba, kuma mafi yawa a waje tayi rayuwarta, dan haka yake mata uzuri a wasu abubuwan.

Yusuf yace "Ina son in fara zuwa kasuwar garin nan, inga me zan fara siyarwa saboda mu ragewa mutanen gidan nan ɗawainiyar da suke damu"

"dama akwai kasuwa a dajin nan?"

"daji kuma?"

"Eh mana" ta bashi amsa

Yusuf yace "eh akwai kasuwa amma se anyi tafiya me nisa sosai, nayi magana da megari ya haɗani da yaronsa tare zamuje kasuwar gobe in Allah ya kaimu inga yanayin abubuwan"

Tace "Shikenan" tana ci gaba da cin gujjiyarta, seda ta gama ta kalle shi tace "Wanka"

Yusuf yace "to"  ya haɗa mata ruwa sannan ya fita sallar la'asar

A gurin salla Yusuf yaga abun mamaki, akwai ƙaramin gurin da suke jam'in salla, akwai ƙarancin ilimi ga mutan ƙauyen, liman ya makara wani yaja salla a raka'ar ƙarshe liman yazo, raka'ar ƙarshe kawai ya samu, itama an ɗago daga ruku'u, da'aka idar Yusuf yana jira yaga liman ya tashi ya kawo wadda be samu ba amma yaga liman yayi ƙyam yaja gefe yana laziminsa.

Yusuf ya dinga kallonsa ko ze tashi ya canza sallane, amma yaga aka jima liman ya shafa addu'a ya miƙe ya gaisa da mutane ya ƙara gaba.

Yusuf yayi shiru a ransa yace "wannan mutumin dabe san hukuncin salla ba, shine kuma yake jan salla? Tabbas akwai matsala babba, mutanen garin nan suna buƙatar ilimin Addini, ya barwa ransa cewa zeyi wa megari magana, yaga ta inda ze iya basu gudunmuwa.

Ya shiga cikin gida ya shiga ɗakinsu da sallama, Widad ta fito daga wankan tana shafa mai, ba tare da ta kalle shi ba ta amsa ƙasa ƙasa, ta cigaba da abunda take.

Kusa da ita yaje ya zauna yana kallonta, duk cikin salon son yasa ta kula shi, dan idan har bashi yayi mata magana ba in zasu kwana idan ba wani abu take buƙata ba, ba zata kula shi ba.

Tana jin yadda ya zauna daf da ita ya ƙureta da ido, kamar tasan maganar yake so tayi, taƙi magana.

Cike da fargaba dan yasan ze sha masifa, amma ya maze ya kai hannunsa gashin kanta yace

"wannan gashin yaushe rabonsa da a taje shi? Insha Allah idan na fara zuwa kasuwa  indai naga comb zan siyo, in taje shi da kaina"

Bige hannunsa tayi tace "wai kai meye haka? Me yasa kake son taɓani ne? Na gaya maka bana son karka ƙara taɓani na gaya maka, in ba haka ba duk abunda nayi maka kai ka siya, haba sekace baka da zuciya, ko baka gane magana"

Shiru yayi kawai yana kallonta yadda take ta masa masifa, shi yaga tana magana ma se yaji daɗi a ransa, dan yaga ta rage yawan kukan da take yi.

Ga mamakinta murmushi yayi maimakon taga yaji haushi.

"kawo man in tayaki shafawa" yai maganar yana ɗaukar robar man, ƙwacewa tayi tace
"bana so na gama"

Yusuf yace"Shikenan bari in baki guri kisa kaya"

"inma baka bani gurin ba baze hanani sa kayana ba"

Yayi murmushi ya miƙe cike da jin daɗin yasa ta magana, bayansa tabi kallo yana fita ta ajiye abunda ke hannunta ta shiga goge hawayen da ita kaɗai tasan dalilinsu.

Doctor Sufyan yana Office ɗinsa, yana jiran lokaci yayi ze shiga tiyata, wayarsa yaji ta fara ringin, ya tsaya ya ɗaga tareda yin sallama.

"Sufyan ne?"

"Eh nine"

"ina son ka kasa kunne ka saurareni dakyau, dukda nasan baka san dawa kake magana ba, hakan ya faru ne sakamakon sanin wanda kake maganar dashi a gurinka bashi da amfani, ina son ka saurareni da kyau kaji abunda zan gaya maka, kana jina ko?"

Sufyan yace "ina jinka"

"kamar yadda aka baka kwangilar sake kwantar da Daula, aka baka miliyoyin kuɗi akan karya warke, kuma kayi dan tuni wani percentage ya shiga hannunka, to nima aiki nake son kayi min, niba kwantar da Daula nake so kayi ba, kawar da Daula nake son kayi!!!"

Miƙewa doctor Sufyan yayi tsaye ya shiga waige waige karya je wani yaji abunda ake faɗa masa a waya, cikin rawar murya yace "amm.. Ban gane me kake fada ba fa"

"ƙarya ka keyi ka gane, kuma kaji me nace tunda ka iya karɓar kuɗi kake bashi wrong treatment, to zaka iya karɓar kuɗi ka kasheshi, likita ne kai babu me zarginka, tunda kowa yasan condition ɗinsa yayi worse, bazance ga abunda zan bi yaka ba, sedai da kanka nakeso ka yanke abunda zan bi yaka "

Wani wahallalen gumine ya dinga ratsowa Sufyan, gumi yake ji har tsakanin cinyoyinsa, yace " Amma kisan Alhaji Daula hatsari ne, dole se anyi bincike akan gawar sa, don a tabattar da abunda ya kashe shi, idan aka ganoni fa, ina da iyali da ƙananan yara nasan kasheni za'ayi, Daula babban Attajiri ne"

"meye marabar abunda kake masa yanzu da wanda nace kayi masa, sanin kanka ne wrong treatment ɗinma ze iya kasheshi, baka da damar cewa ba zakayi ba, saboda na maka tarko ta ko'ina, ina da duk yadda akayi ka karɓi kuɗi kake bashi wrong treatment, duk wata hujja daza'a kamaka ina dashi, idan kuma naga dama zan saka ɗauke ɗaya daga
'ya' yan naka ko kayi ko kuma ransa ya salwanta, zaɓi ya rage naka, sannan idan kaga dama ka gayawa wani"

Ƙit aka katse kiran, gaba ɗaya doctor Sufyan yaji kamar an zare masa laka, jikinsa se rawa yake ya duba wayarsa yaga anyi hiding ɗin lambar, dan ko unknown number be fito ba,  duk sanyin Ac dake office ɗin shi gumi yake, kamar wanda ya tuƙa tuwon gidan biki a tsakae rana.

Yau da wuri Yusuf ya shirya, dan zebi ɗan megari kasuwa, ɗan megarin shima matashi ne be kai Yusuf ba, a bayan gidan megari nasa gidan yake, da matarsa da 'ya' yansa shida.

Har Yusuf ya gama shirinsa, aka kawo musu Abincin safe Widad bacci take, a hankali ya ƙarasa gaban katifarta ya janye bargon jikinta, bacci take hankalinta kwance, se yarintarta ta sake fitowa ta ƙara kyau a idon Yusuf, yayi shiru yana kallonta.

A hankali ya ɗan daki pillow ɗin da take kai, amma bata motsa ba, ya sake taɓa pillow amma still bata motsa ba, hannu yasa ya ɗan daddaki nata hannun, kamar me tashin ƙaramin yaro, juyi tayi amma taƙi buɗe ido.

"Widad" karo na farko a rayuwarta data ji ya kira sunanta, taji zuciyar ta ta buga da ƙarfi, ta buɗe ido ta kalle shi

Yace "ga breakfast an kawo karya huce, kuma inason zan fita ni"

"shine zaka wani durƙuso kaina haka? Kamar zaka shige cikina"

"ke komai nayi miki lefi ne? To sorry tashi karya huce kinji gimbiyar..

Kallonsa take taji meze ƙarasa, maimakon ya ƙarasa se yayi murmushi yace "tashi kije kiyi brush, muci Abinci "

Ta miƙe ta ɗau brush tayi waje, Yusuf ya gyara mata shimfiɗa, ya gyara ɗakin.

Widad ta fita tsakar gida, gwaggo tace "Amarya ina kwana"

Widad tace "lafiya ƙalau"

Gwaggo tace "Alhamdilillah ya ƙarfin jiki?"

"Naji sauƙi"

Gwaggo tace  "to madalla"

Hari ta ƙurowa Widad ido tana so tayi magana, Widad tace 

"idan baki dena kallona ba, sena saka butar hannuna na  ɓallo miki wannan haƙorin da yake leƙowa idan kina magana"

Hari tace "ke hudas kike ko wudas, yau dai ban kulaki ba balle ace na shiga harkarki"

Widad ta Harareta ta wuce banɗakinta.

Data fito ta manta da batun Yusuf dake jiranta, ta tsaya gurin da take leƙen zomaye.

Seda tayi me isarta, sannan ta koma ɗaki.
seda taga Yusuf sannan ta tuna ashe ita yake jira suci Abinci, yace  "naga kin daɗe?"

Kai tsaye tace "kallon zomaye nayi" , ta ajiye kayan brush ɗinta, tazo ta zauna ta buɗe kwanon farko, dakakken ƙuli ƙuli ne a ciki, ta rufe ta buɗe ɗayan dafaffen dankalin hausa ne a ciki da ɓawonsa da komai manya guda uku.

Ta kalli Yusuf tace "meye wannan?"

"Dankali" ya bata amsa

"kuma a haka? Ta yaya za'aci"

Yusuf yace "ga mahaɗin nan ƙuliƙuli a wannan kwanon"

Widad tace "ta yaya za'aci wannan abun ba tea?"

Yusuf yace  "seki kora da ruwa" yai maganar tare da fara ɓare dankalin.

ta zuba masa ido, ya ɓare tsaf ya yayyanka shi a kwano, ya ɗebo ruwa ya ajiye mata yace  "bismillah"

Tsayawa tayi tana kallonsa kamar wata sokuwa, ya ɗakko ɗaya ya dangwala da ƙuli ƙuli ya kai bakinta, ɗauke kanta tayi tasa hannu ta karɓa tasa a bakinta.

Ba zata ce babu daɗi ba, sedai gurin haɗiyewa ne daƙyar take yi, dan kasa haɗiyewa tayi seda ta haɗa da ruwa.

Dan haka shima ba taci dayawa ba tace ita bazata iya cin wannan abun ba, shaƙe mata wuya yake.

Yusuf ne yaci sauran, sannan yayi mata sallama ya tafi.

Sufyan abun duniya ya dameshi, ya rasa inda ze saka ransa, ba ƙaramin hatsari bane kashe shahararren mutum kamar Daula, amma kowa se saka rayuwarsa yake a hatsari saboda suna taƙamar suna da kuɗi, shiba abun ya kaisu gurin 'yan sanda ba, shi ze kwana a ciki.

Gaba ɗaya daren nan yakasa bacci, sedai juyi dafa da Asuba aka kuma sake kiransa, bashi da zaɓin daya wuce ya amsa wayar.

"baka da isasheshen lokacin ɓatawa gurin aiwatar sa wannan aikin, kana da yau zuwa gobe in Allah ya kaimu ne kawai, idan baka yi ba ni zan aikata maka abunda nace"

Aka katse layin, Doctor Sufyan yayi jifa da wayar ya dafe kai, matarsa ta lura da yana cikin damuwa ta tambaye shi ko lafiya, yace mata babu komai.

Widad bata taɓa shiga damuwa ba, tsawon lokacin data ɗauka tana rayuwar kaɗaici a rayuwarta se wannan karon, tunda Yusuf ya fita be dawo ba taji gaba ɗaya duniyar ta mata faɗi, gashi ita bata saba da kowa ba se shi, seta ji ta wani iri kamar ita kaɗaice a duniyar, koba komai ganin motsinsa yana rage mata damuwa.

Yau wuni guda tana ɗaki, ba wanda yake shigowa inda take, saboda bata da fuskar daza'ayi mata hakan, bayan tayi sallar la'asar yunwa ta isheta ta fito tsakar gida.

Gwaggo tace "Amarya lafiya dai ko?"

Widad tace "Naga har yanzu Yusuf be dawo ba kuma ni yunwa nakeji"

Gwaggo tace  "Allah sarki, yau Harice da girki bata aiko miki da Abinci ba kenan"

Widad tace  "kota aiko ba zanci ba, dan ƙazama ce"

Hari dake salla a tsakar gida ko sallamewa ba tayi ba tace "jar'uba kekam anyi mara albarka, nice ƙazamar?"

"Eh kece ƙazama, kalli zanin jikinki kalli faratanki, hijjabin jikinki ma me datti ne, sekiyi abu ki bani inci, an gaya miki komai nake ci?"

Wato Widad sam ta dena ragawa Hari, gwaggo tayi murmushi tace "Yanzu to me zakici?

Widad tayi shiru ba tace komai ba, gwaggo tace  "Akwai Furar megari dana dama, bari in ɗebar miki"

Widad tace "Nagode"

Hari tace "Furar malam ɗin zaki ɗiba ki bata? Lallai Yaya akwaiki da neman gindin zama"

Widad tace "Eh ita za'a ban, ba zanci Abincinki ba"

Gwaggo dai ba tace komai ba, ta ɗebowa Widad fura a kofin silba ta bata, ta samu guri ta zauna tana sha.

Furar tayi zaƙi zau da zumar da'aka zuba a ciki, tana cikin shan furar can seta miƙe tsaye, gwaggo tace  "kin ƙoshi ne?"

Widad tace  "A'a Yusuf na ragewa"

Hari tace "Ohh ni jikar Hama, ji wata fitsara take cewa ta ragewa mijinta abu"

Wasu matane suka shigo su Uku, ɗaya 'yar babba biyu kuma 'yan mata da sallama suka shigo, Hari tace
"Ahh marabanku da dawowa, wai an sha suna"

Ɗayace ta kalli Widad tace  "Hari wace wannan?"

Hari tace  "wasu baƙine mukayi"

Ɗayar tace  "kalleta kamar balarabiya"

Widad bata tanka musu ba ta koma ɗakinta.

Sukam bajewa sukayi a tsakar gida, ɗayar itama matar megari ce hansai, se 'yan matan Hindu da Hanne, suma' ya'yansa ne sunje wani ƙauyene, inda 'yar megari take Aure ta haihu.

Se bayan la'asar Yusuf ya dawo gida, kallo ɗaya zakayi masa kasan a gajiye yake, ya gaisa da mutanen gidan ya shiga ɗakinsu.

Ba sannu da zuwa bakomai Widad tace "Shine kaƙi dawowa se yanzu?"

Yusuf yace yanzun ma tun ɗazu na taho, akwai nisane sosai.

Ya ajiye kayan hannunsa, yaje yayi wanka, a ɗaki yayi salla saboda gajiya ya nemi guri ya kwanta yayi shiru.

Widad tace  "to ni dai gaskiya ka dinga dawowa da wuri, kawai seka tafi ka barni nikaɗai, gaba ɗaya nagaji"

Yusuf ya kalleta yace "Aikin me kikayi kika gaji?"

"Aikin zama ba abunda nake, ba kowa a ɗakin nan seni kaɗai"

"Amma ai da mutane a gidan, seki fita kuyi hira"

"Ni gaskiya dana fita wannan me haƙoran take min rashin mutunci, nikuma ramawa nake"

Yusuf yace  "Kidinga ƙyaleta, kinga babbace ba sa'arki bace ta girmeki"

"da alama ka manta Widad Nasir Daula ce ko?"

Yusuf yace "ya za'ayi na manta nina isa? Yau ba'a kawo komai bane yunwa nake ji"

Widad ta taɓe baki tace "wannan ƙazamarce tayi girki, ni kuma nace ba zamu ciba, shine Mama ta bani furar mijinta"

Buɗe baki Yusuf yayi yace "ba dai ce mata kikayi ƙazama a gabanta ba?"

"idan na gaya mata zata cinye nine?"

Yusuf ya dafe kai, ita Widad a rayuwar ta bata san kara ko alkunya ba sam.

Ta ɗakko kofin furar nan tace  "gashi nasha na rage maka"

Yusuf yace "dagaske ragemin kikayi?"

"is there anything special, dan na rage maka?"

Yusuf yace a"a a ransa kuma yace "lallai kin damu dani"

Yusuf yace  "Naje kasuwa, naga abubuwa ana saye da siyarwa ba laifi, ɗan megari ze aran kuɗi, inga me zan fara siyarwa, ranar daba kasuwa kuma naje wani gurin inga me zanyi"

"to duk meye na wannan wahalar?, naga dai barin gurin nan zamuyi"

"A'a yakamata in koma ciyar dake da kaina, da duk buƙatunki be kamata mucigaba da ɗora musu ɗawainiya ba, nauyinki a kaina yake yanzu"

Kallonsa tayi tace "don't bother yourself, wannan fa ba Aure neba"

"meye inba Aure ba?"

Tace "Shiri mana"

Yace "Ba ruwan Allah da shiri, kuma koda shirin ne aini yakamata in kula da Gimbiya ta"

"karka ƙara cemin gimbiyarka"

Yusuf yayi murmushi yace "Lokacin da muna gida gimbiyar Daddy ce, yanzu kuma da muke nan ba wanda kika sani seni, dan haka gimbiyata ce"

Tsaki tayi ta miƙe daga inda take zaune, Yusuf yace  "Komai naki me kyau ne Widad"

Ko Kallonsa ba tayi ba tayi masa shiru, yace  "ga Alƙawarin da nayi miki, na samo comb da ƙyar a kasuwa, yaushe zamu gyara gashin namu?"

Ficewa tayi daga ɗakin ta barshi, shi kuma ya dinga murmushi ganin takaici ya hana ta magana, Yusuf yace da haka da haka gimbiya"

Sufyan fa hankalinsa gaba ɗaya ya gama tashi, ya hanga yaga bashi da wata mafita data rage masa banda ya aikata abunda akace, ya haɗa allurai a cikin syringe ya zauna ya zuba musu ido, gabansa nata dukan biyar biyar, kiransa akayi a waya, hannun narawa ya ɗauka

"Ka shirya aiwatar da aikinne ko kuwa?"

Cikin jan numfashi Sufyan yace  "Eh na shirya"

"shikenan, ina jiran sakamako a yau, ka duba wayarka zakaga Alert ɗin kuɗi"
Sufyan bece komai ba ya ajiye wayar yana yakice gumi.

Zuwa yanzu Widad ta fara dangana, ta ɗan fara sabawa da halin data tsinci kanta a ciki, Cikin dare Widad tana bacci tayi juyi, hasken farin wata ya hasake ɗakin, ta hangi Yusuf a zaune akan shimfiɗarsa yayi tagumi,
Da alama tunani yake.

A ranta tace  'Ashe shima yana damuwa, amma ya dinga basarwa yace nize hanani kuka'

"wai tunanin mekake?"

Firgigit ya dawo hayyacinsa, yace "idonki biyune?"

"A'a mafarki nake na maka magana"

Yusuf yace "hmm ba tunani nake bafa, cinnaka ne ya cijeni na kasa bacci"

"yaushe ka fara ƙarya?"

"dagaske nake" yai maganar tare da miƙewa ya fita waje, Alwala yaje ya ɗauro yazo ya tada salla, Widad kam baccinta ta koma.

Yusuf yana cikin sallar ne yaji A gigice Widad tace  "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wayyo Allah Daddyna"

Ta miƙe da gudu tayi hanyar waje



(Up Up masoya littafin AƘIDATA, Comments ɗinku na matukar ƙayatar dani, shike bani ƙwarin gwiwa nayin posting, Allah ya bar ƙauna 😍 😍 😍)

Share, share and share please 🙏 🙏 🙏
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

         _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 36_37

Riƙeta gam Yusuf yayi, yayin da ta cigaba da fizge fizge tana kuka, a hankali Yusuf ya zame ya zauna da ita a jikinsa, ya toshe mata baki, saboda dare ne nan da nan sautinta ze iya cika ko'ina.

Yusuf yace "Widad, ki nutsu mana darene yanzu karkisa hankalin mutane ya dawo kanmu, mafarki kikayi fa"

Girgiza masa kai ta shiga yi, cikin kuka tace "is not just a dream, wani abu na shirin faruwa da Daddyna, ka ƙyaleni inje in ganshi, wani abu ze sameshi"

"yanzu idan kika tafi ina zaki? Daddy Addu'ar mu yake buƙata, tun ɗazu nan salla nake ina mana addu'a muda iyayen mu, Insha Allah babu wanda ze iya cutar dasu, kuma Saleh ya cemin ya gaya masa muna nan tare, kidena kuka"

Girgiza kai take tana kuka tace "Daddy na, shikaɗai ya ragemin bani da kowa, bana son in rasa Daddyna, idan na rasa Daddy babu sauran me ƙaunata sedai dukiyar daze bari, wayyo Allah Daddyna, ya Allah secure my Dad, Allah yasa in koma in tarad da kai a raye"

Gaban Yusuf ne ya faɗi, ya tuna abunda Saleh ya gaya masa game da mahaifin Widad.

Kuka take sosai jikinta har rawa yake, ga wani irin gumi daya rufe ta, ɗora hannunsa yayi a saman ƙirjinta, se bugawa zuciyarta take da ƙarfin gaske.

Yusuf ya shiga karanta mata dukkan Addu'ar da tazo bakinsa, a hankali zuciyarta ta rage bugawa da sauri da sauri, can kuma bacci ya ɗauketa, ta shiga sauke Ajiyar zuciya.

Yusuf ya miƙe a hankali da ita, ya kaita kan katifarta ya rufe ta da bargo, ya koma ya sake alwala ya cigaba da sallar sa.

Alhaji Musane keta sintiri a cikin ɗakinsa, se safa da marwa yake ya kai gwauro ya kai mari, ya rasa abunda yake masa daɗi, sosai maganganun Saleh sunyi tasiri a zuciyarsa, sosai zargi ya ɗarsu a ransa cewar a cikinsu akwai wanda ya zame yake shirin cin amanarsu, kamar yadda ya zame a baya yaso ya haɗa kai shida Alhaji Bukar.
A fili ya furta dole  "inyi wani abu akai"

Juyowa yayi yaga Nurat a tsaye a ƙofar ɗakinsa da tray ɗauke da kayan marmari a ciki, a fusace yace "dan uwarki laɓe kika koma Yimin ko?"

Cikin dakewa tace "meyasa zan maka laɓe kuma Daddy, tun ɗazu nake sallama amma baka amsa ba"

"Kuma shine seki tsaya ki laɓe?"

"Daddy bafa laɓewa nayi ba"

"zoki ajiye kayan nan ki fita ki ban guri"

Nurat taje ta ajiye masa tray ɗin ta fita, gaba ɗaya Nurat ta lura mahaifinta a kamar a ruɗe yake, akwai abunda yake damunsa, zata so sanin abunda yake damunsa, dan wataƙila yana da alaƙa da harƙallar da suke ƙullawa akan Alhaji Nasir da iyalansa.

Bayan sallar Asuba yau a masallaci, Yusuf ne ya tsaya ya ɗanyi wa mutanen ƙauyen Nasiha akan neman ilimin Addini, ta hanyar janyo musu ayoyi da hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam, be fito yace musu basu da ilimi ba, amma a cikin bayanin da yake musu ya kawo musu misalin yadda mutum ze kawo raka'oin daya rasa idan yazo bin jam'i, nan suka dinga gano irin tafka tafka da kwaɓar da suke yi.

Wani mutum yace "gaskiya Malam Yusufa munji daɗin wannan bayanin naka, danni harga Allah na ƙaru da abubuwa da dama, danni wallahi na zata idan mutum yayi alwala in yayi tusa indai ba tayi ƙara ba to bata karye ba"

Na kusa dashi yace "Nikuma wallahi na zata ko sujjada ka samu in ana salla shikenan ka samu salla, dan Allah yakamata ka cigaba da yi mana wannan bayanin idan anyi sallar Asuba ko kuma da daddare mudinga taruwa anan kana ƙara fahimtar damu abubuwa"

Megari yace  "hakane kam, Yusufa idan bamu takura maka ba, muna buƙatar hakan"

Yusuf yace "Ai babu batun takura ranka ya daɗe, mafi alkairin mutane shine wanda yasan ilimi kuma ya sanar dashi"

Seda gari yayi haske tukuna suka watse, suna mamakin kurakuran da suke aikatawa a sha'anin addininsu.

Yana shiga gidan yayi karo da wata budurwa tana koro dabbobi daga turke zasu fita kiwo, tana ganin Yusuf tayi turus tana kallonsa, har Yusuf ze wuce tace masa "Ina kwana"

Yusuf yace  "Yawwa lafiya ƙalau sannunki"

Yai gaba abunsa, ƙura masa ido tayi harya wuce ya shige ɗakinsu, anan ta tabattar da cewa shine mijin wannan farar matar me gashi.

Da sauri ta koma ɗakinsu, tana kiran "Hindu, Hindu"

Hindu dake sharar ɗaki tace  "lafiya kikemin wannan kiran?"

Hanne tace "kinga mijin wannan farar matar nan ta jiya kuwa?"

"me yayi?" hindu ta tambaya

"innalillahi, wallahi ban taɓa ganin namiji me kyau kamarsa ba"

Hindu tace "har Lamiɗon rigarsu gwaggo?"

Hanne tace  "wallahi harshi, taɓ bakiga kyau ba masha Allah, ban taɓa ganin namiji me kyansa ba"

Hindu tace "bakiga matarsa bama, fara me kyau"

Hanne tace "dalla wannan da gani bata da mutunci, kinga kallon da tayi mana jiya kamar taga kashi, da gani bata da mutunci"

Hindu tace  "ke Hanne karkice haka, aikinga bata sanmu ba"

Hanne tace  "ke dallacan Allah yasa in kuma ganinsa"

Yusuf ya shiga ɗaki ya tarar da Widad a zaune, ya kalleta yace  "ina kwana?"

Kallonsa tayi kawai ba tace komai ba, Yusuf yace "Munyi magana da ɗan megari na bashi kuɗi, zeje cikin gari ze siyo miki kayan tea da sauran abun buƙata"

Ita dai ba tace komai ba, sema lumshe idanunta da tayi.

"wai meke damunki ne kuma?"

"Bakomai"

"zakiyi wanka ne? Ina son zan fita"

Tace  "kaje kawai, zanyi komai da kaina"

Yusuf yace "Aini tsoron fitarma nakeji, jiya da daddare ki tsoratani sosai, kar in fitane kema kice zaki tafi"

Shiru tayi masa ta ƙara rufe idonta, "Widad" ya kira sunanta, a ɗan hasale tace  "meye ne?"

"Inaga bari in haƙura da fitar nan, bari inje inyiwa abokin tafiyar tawa magana se in dawo"

"Nifa ban hanaka tafiya ba, ba inda zani jiyanma na tsorata ne mafarkin da nayi"

Yusuf yace  "dagaske idan na fita bazaki tafi ki barni ba"?

Ɗagowa tayi tana kallon cikin ƙwayar idonsa, ta jinjina masa kai alamar eh, yayi murmushi yace 

"to bari inje in wanke mana kwanuka, in wanke miki banɗaki se in tafi, sena dawo, in a kawo abun karyawa kiyi breakfast ɗinki kawai, base kin ragemin ba"

Yai maganar tare da miƙewa ya fice, ya kwashi kwanukan ya zuba ruwa, Hanne ce ta hango Yusuf da kwanuka, ta taho da sauri tace
"kawo in wanke maka"

Yusuf yace "A'a bakomai nagode, yanzu zan wanke in gama"

"dan Allah ka kawo, ai be kamata kayi wanke wanke da kanka ba, idan Baffa ya gani ma ze iyayi mana faɗa"

Yusuf yace "kema 'yarsa ce ne?"

Hanne tace  "eh nima' yarsa ce nida Hindu, muje wani ƙauyene suna, se jiya muka dawo"

Yusuf yace "Allah sarki, Allah yayiwa rayuwar ku Albarka"

Cike da jin daɗi Hanne tace  "Ameen" ta karɓi kwanukan, yace  "in kin gama, seki kai mata ɗakin"

Hanne tace  "to" tana mamakin ace yana da mata amma shize wanke wanke, Yusuf ya janyo ruwa a rijiya ya wanke banɗakinsu, yayi wanka ya fice.

Hanne ta gama wanke wanke, ta tafi ƙofar ɗakinsu Widad, ta tsaya tana sallama, ƙasa ƙasa Hanne ta shiga ɗakin ta cewa Widad "ga kwanuka inji mijinki"

"Ajiye anan"
Hanne ta ajiye, ta juya ta fita tana mamakin wannan irin nuna isa na Widad.

Anwar ya gayarawa Daula jikinsa, ya canza masa kaya ya bashi Abinci da sirinji, ta cikin robar dake hancin Daula, ya gyara ɗakin ya tattara kayansa marasa kyau ya fita ze bayar akai gida su Nura su wanke.

Sufyan ne ya tinkari ɗakin da Alhaji Nasir yake, gaban sa se faɗuwa yake, ji yake kamar kowa kallonsa yake a baranda ya haɗu da Anwar, suka gaisa da Anwar, doctor Sufyan yace  "ina zaka haka Anwar? Kasan bama san ana barinsa shi kaɗai"

Anwar yace  "yanzu zan koma, kayan nan na fito dashi zan kaiwa direba ya kai gida a wanke"

Sufyan yace  "to masha Allah, ga wasu magunguna na rubuta, idan ka kai kayan wankin seka biya pharmacy ka siyo"

Suna nan tsaye aka fito da wani mutum ya mutu an turo shi a gado za'a fita dashi.

Anwar yace "doctor, dan Allah nasan lafiyar Alhaji ba a hannunka take ba tana hannun Allah, dan Allah ka ƙara ƙoƙari, bawan Allah nan kullum jikinsa ƙara rikicewa yake"

Sufyan ya dafa kafaɗar Anwar yace "karka damu Anwar, kamar yadda ka faɗa sauƙi na Allah ne, Amma muna fatan Allah ya bawa Daula lafiya"

Anwar yace "shikenan nagode, bari inje"

Anwar yayi gaba, Sufyan ya tsaya a gurin yayi shiru, sannan yayi gaba jikinsa gaba ɗaya babu ƙwari, a haka ya taka har yaje ƙofar ɗakin da Daula yake, yasa hannu ya murɗa ƙofar ya shiga, sedai me yana shiga yaga wayam ba kowa akan gadon, ya ƙarasa gaban gadon da sauri ya yaye bargon kai, ba Daula babu alamarsa, ya buɗe banɗaki ya duba nan ma kowa, ya duba bayan ƙofa zuwa ƙarƙashin gado, amma be ganshi ba ƙarewa har fridge ya buɗe amma bega alamar Daula ba.

Cire gilashin dake idonsa yayi yana zazzare ido, yana waige waige kamar Ɓarawo

Fitowa yayi da sauri daga ɗakin, aikuwa yayi karo da Anwar, Anwar yace "doctor Sufyan ya dai? Naganka a haka? Na kawo maganin"

Doctor Sufyan yace "Amm... Mmm.. Nace ina Mara lafiyar ne?"

Anwar yace  "kamarya? Yana ciki mana"

Sufyan yace  "Baya nan na duba ko ina ban ganshi ba"

Anwar yace  "kamar yaya? Ya za'ayi in fita barshi, daga zuwa siyo magani kace baka gasnhi ba? Sekace wata eiga, mutumin da komai sena masa ta yaya ze iya fita?"

Sufyan yace   "Nima abunda ya bani mamaki kenan, na duba ko'ina ban ganshi ba, har banɗaki na duba baya nan"

Kallon tuhuma Anwar yayiwa Sufyan yace "Amma gaskiya ni ina tantama, babu wanda ya shiga ɗakin bayan fita ta sekai"

Sufyan yace "Wallahi ban tarar dashi a ɗakin nan ba kaji na rantse"

Anwar ya ɗaga waya ya kira 'yan sanda, ya kira ya sanar da Bulama abunda ake ciki.



Widad ta gaji da zaman ɗaki, ta fito tsakar gida ƙarƙashin bishiya ta zauna, yaron gurin hansai ne da baze wuce shekaru uku ba, yake ta kallon Widad yana leƙa gashin kanta, murmushi Widad tayi tace "Naga kana son gashin nan, zo in baka ka taɓa"

Tsayawa yaron yayi yana murmushi, a hankali ya ƙaraso inda Widad take, ta riƙe hannunsa ta ɗora akan gashinta, nan yaron ya shiga wasa da gashin nata yana dariya.

Hansai data fito taga abunda yake faruwa, tunda suka dawo suka tarar dasu Widad, ko sannu bata taɓa haɗasu ba, ko murmurewa bata taɓa ganin tayi ba, Hausawa sukace me ɗa wawa se taji daɗin yadda Widad take wasa da ɗan nata.

Hindu data fito tsakar gidanma, tana ganin haka ta ƙaraso tace "kai Sani sakar mata gashi mana, ya takura miki ko?"

Widad tace  "A'a nibe takura min ba, naga yana son kamawa ne shiyasa nace yazo ya taɓa"

Hindu tace "Abunka daba'a saba ganiba shiyasa yazo ya saki gaba"

Widad tayi murmushi har haƙoranta suka fito tace  "gashin ne ba'a saba gani ba, bayan duk kanku ba'a aske yake ba"

Hindu tace "to ai ganin gashi me yawan naki dai basu saba gani ba, kuma dan Allah ke 'yar ƙasar nan ce?"

Hansai dake ƙoƙarin haɗa wuta tace "wallahi nima abunda ke bani mamaki kenan, dan Allah' yar ƙasar nan ce ke?"

Widad tace  "taɓ 'yar ƙasar nan ceni mana, banyi kama da Hausawa bane"

Hindu tace "gaskiya ko bahaushiya ce ke, to sedai ko ruwa biyu"

Widad tace "ruwa biyu kamar yaya?"

Hansai tace "kamar ace mamanki bahaushiya mahaifinki wani yaren, ko mahaifinki bahaushe mamanki wata yaren"

Widad ta ɗanyi jim sannan ta murmusa tace "dukkansu Hausawa ne, mazauna Kano"

Hindu tace  "kano, dan Allah a kano kike?"

Widad tace "kin taɓa zuwa ne?"

"Ni waze kaini kano? Muna dai jin labarin kano, ance garin yana da kyau sosai, kuma mutanen kano suna da kirki"

Widad tace "Insha Allah wataran zaki kano, ba laifi kam kano tana da kyau, nikam ya sunanki ne"

Hindu tace "sunana Hindu"

Widad tace "Masha Allah, Hindatu"

Gwaggo ce ta fito hannunta ɗauke da ƙwarya da rariya tace "Amarya yau hira ake haka? Badan da kaina naga kina surutu ba, da zance bake bace"

Widad tace "Wallahi gwaggo bani da surutu, amma ina magana sosai ai"

Hanne kuwa dake bakin rijiya tana wanke wanke ko kulasu ba tayi ba.

Itakuwa Hari fitowa tayi da gero, ta zuba a turmi ta fara daka tana habaice habaicenta, basu kulata ba suka cigaba da hira.

Gwaggo tace "Ai Amarya mutum rahama ne, ko yaya idan kina ɗan fitowa ana hira zaki rage kaɗaici, amma ace ke mijinki kawai kika sani"

Widad tace "Mama kenan, to ai shikaɗai ɗin kawai na sani, kawo in tayaki tankaɗawa"

Gwaggo tace  "A'a kar in takura miki"

Widad tace "ni baki takuramin ba"

Ta ɗaga kai ta kalli Hari tace "dan Allah malama kiyi ɗaya, ko dakan kokuma waƙe waƙen haba dan Allah, da wanne za muji ƙarar daka ko kuma na wannan hayaniyar da kike yi"

Hari tace "Allah ya haɗani da Baƙar Jaraba ni Hari jikar Hama, na kulaki ne ko tsabar jan bala'i ne? Wallahi ki fita a sabgata, tun kafin in miki wulaƙanci"

Widad ta sunkuyar da kai tana dariya, dama abunda take so kenan, ta zungurota taita masifa, dan ita yanzu ta maida Hari comedy.

Widad ta karɓi tankaɗe kamar abun Arziki, ta riƙe rariyar da hannu ɗaya, ta ɗaga hannun sama tana girgiza rariyar, garin kuwa se kama gabansa yake, dan haka iska ta dinga kwashe shi, gwaggo kuma takasa yi mata magana saboda kawaici.

Yusuf ne yayi sallama hannunsa ɗauke da ledar viva, hango Widad yayi tayi buɗu buɗu a cikin gari, gashi a ƙarƙashin bishiya take tankaɗen, iska duk ta kwashe garin.

Hanne na ganinsa ta wani fara mutsu mutsu da gyare2, tace "sannu da zuwa" Yusuf be kula da ita ba
Da sauri ya ƙarasa inda Widad take  yace 'Subhanallah Widad waye ya saki wannan aikin "

Gwaggo tace "seda nace base tayi ba, tace in bata tayi"

Yusuf yace "wa yace ki bata, Mama bata iya bafa, kalli yadda tayi miki Asarar gari"

Murmushi gwaggo tayi, ta ɗauke kai daga kallonsu.

Widad tace "Na iya, ba gashi inayi ba, kai komai nayi seka gwalemin"

Yusuf yace  "Ni na isa kiyi abu in gwale, amma kalli yadda kika ɓata gurin"

"Ni dai ka ƙyaleni in cigaba da aikina"

Yace "Naji, amma kawo in nuna miki yadda akeyi"

"A'a ni naga yadda akeyi ai, shine nima nake gwadawa"

Gwaggo kam gaba ɗaya kunya suka bata, dan haka ta miƙe ta bar musu gurin gaba ɗaya.

Yusuf yayi ƙasa da murya yace "dan Allah kiyi haƙuri ki kawo, wallahi baki iya ba kawaici kawai tayi miki, amma wannan aika aika kike mata"

Sakar masa rariyar tayi, ya shiga gwada mata yadda ake yi, kawai ta kwashe da dariya, ya kalle ta yace "lafiya kuwa?"

"A'a gani nayi ka iya sosai"

Ba ƙaramin kyau tayi ba dariyar da tayi, karon farko da tayi fara'a haka sosai ya gani.

Kawai ya shagala da kallonta, ya ɗanyi murmushi ya cigaba da nuna mata yadda akeyi.

Hanne kuwa ji tayi ta tsani Widad gaba ɗaya, ko ganinta bata son yi ganin Yadda Yusuf ke wani ƙure Widad da ido se taji kamar tayi kuka.

Megari ne yayi sallama ya shigo, yace "Malam Yusuf ka dawo kenan?"

Yusuf yace "eh Baba na dawo" Megari yana jin daɗin yadda Yusuf yake girmamashi

Yace "ya kasuwar kuwa?"

Yusuf yace "Alhamdilillah, naje harna dawo"

Megari yace "to masha Allah"

Widad kam ko kallon Megari ba tayi ba, balle tace masa wani abu, Megari ya ƙaraso inda take yace "wannan 'ya tawa akwai miskilanci, tunda ba zata kula baban nata ba, toga tsaraba na kawo mata, Allah ya ƙara ƙarfin jiki"

Ya ajiye mata dabino rabin kwano a gabanta, Yusuf yace "Mungode sosai Baba, Allah yasaka da alkhairi"

Megari yace "A' a bakomai Yusufa, Allah ne ya haɗa mu zama tare, kuma naji harga Allah kun kwantamin, Allah yayi muku Albarka"

Yusuf yace "Ameen"

Yusuf ya ɗau ledae daya shigo da ita, da wadda Megari ya bawa Widad, ya shige gaba Widad na binsa a baya, gwaggo tace
"Amarya karɓi kayan hannun nasa mana"

Widad tace "Ai ze iya ɗauka, ni yamin nauyi"

Gwaggo ta jinjinawa gaɓunta irinta Widad, akwai buƙatar a zaunar da ita ayi mata takara akan zama da miji.

Suna shiga ɗaki Yusuf yace "yanzu uwaɗakina abaki abu amma ki kasa cewa kin gode, baze ji daɗi ba fa"

Maimakon tayi magana, sema sosa kai data hauyi tana wasa da gashin kanta ta wuce inda katifarta take, Yusuf  ya bita da ido, wato se yanzu yake ganin tsabar yarintar Widad, wato a da ɗinma tsabar izzarta da jin kaine yake sa ka ganta kamar wata babba amma kwanan nan wautar da Widad keyi wasu lokutan, suke ƙara fito da yarintar ta, sedai har yanzu wannan izzar da jin kan basu barta ba.

Yusuf yace yakamata kidinga gaida Megari, kinga yana mana ƙoƙari shima kinji gimbiyata.
Aikuwa nan da nan ta haɗa rai , Yusuf yace "meye kuma na haɗe ran?"

"Ai kafini sanin abunda ka faɗa, kuma kasan bana so"

Hindu ce tayi sallama a ɗakin nasu Yusuf ya amsa, ta shigo da kwano ta durƙusa ta gaida Yusuf, Yusuf ya amsa mata, tace  "Amarya gashi inji Gwaggo"

Widad tace "to Nagode"

Hindu ta juya ta fita, Widad ta buɗe kaanon tace "yau kuma meye wannan?"

Yusuf ya karɓa ya duba yace "kwaɗon rama ne"

Ta kalle shi tace "meke nan?"

Yusuf yace  "kici kiji mana"

Tashi tayi taje ta wanke hannu tazo ta zauna, ta ɗiba takai bakinta, yatsine fuska tayi tana taunawa da ƙyar, kamar tayi kuka tace
"Wai su mutanen nan basa girka abunda akeci ne?"

Yusuf kamar ya tintsire da dariya yace "wannan me ake dashi in ba ciba"

"to naji tsami, ga gishiri da kamar sugar"

Yusuf yace "kyaji dashi, nidai bari inje inyi salla" ya miƙe ya fita.

Abu kamar wasa, sa 'yan sanda suka tashi suka kama Anwar da Doctor Sufyan, wai za' ayi bincike a kansu akan ɓatan Alhaji Nasir Daula, aka kama wasu daga ma'aikatan Asibitin sannan aka rufe Asibitin. Tun ana ɓoye ɓoye har abu ya fara bayyana cewar wai Alhaji Nasir Daula ya ɓata a Asibiti.

Hankalin Hajiya Halima ya tashi, jin an kama mata ɗa an kai shi police station, gidan Bulama ta shirya ta tafi bagazan bagazan ta ɗau mota ta fice.

Tana fita Isa yace "Matsiyaciyar mata, da yake ɗanta aka kama kalli yadda ta fita afujajan, amma mijinta na kwance a Asibiti ko a jikinta, ni ɗanne ma yake bani tausayi da nace Allah yasa baza'a sake shi ba"

Murtalah yace "ai Matsiyaciya ɗaya kenan, kalli yadda ta saida fiye da rabin motocin gidan nan, kalli Yadda tabi ta rage mana albashi dan Azzaluma ce, Allah sarki Yusuf da uwaɗakinsa, ko a wane hali suke oho?"

Nura yace "Ai wallahi se yanzu nake ganin ranar yarinyar nan, duk wulaƙancinta haƙƙinmu baya ciwo koda megida baya nan, ubangiji Allah ya bayyana Alhaji Daula"

Isa yace "Ameen dai abubuwa se faruwa suke kamar almara wai anemi mutum a gadon Asibiti a rasa, Allah ya kyauta"

Suka haɗa baki sukace  "Ameen"

Yusuf ya dawo daga salla, yaga kwanon rama a rufe, yace "kaddai baki ci ba"?

Dabinonta take ci tace "ni bazan iya cin wannan Abunba"

Yana duba kwanon yaga ta tattare ƙuli ƙulin, da tumatir da Albasar da gurjin dake kai ta cinye abunta, ta bar gayan ramar duk ta lashe ƙulin jiki.

Murmushi yayi bece komai ba, ya ci ramar nan a haka, se jikinta yayi sanyi taga bata kyauta ba.

"Gimbiyata, ga wake nan na siyo mana a kasuwa yau da yamma za'a kawo kayan tea harda bredi"

Da sauri ta kalle shi tace "dan Allah dagaske hadda bredi?"

"ya zan miki ƙarya, inje ki hukunta ni, dagaske nake"

"Yau zanci bredi"

Yusuf yace "hadda shayi makuwa, bari inje in watsa ruwa na gaji sosai"

Widad tace "to, ba zaka ci dabinon ba?"

"bari in wanka tukuna"

Ya tashi ya ɗau bokiti ya fita, seda taga ta kassara dabinon nan, ta masa cin ƙoshi sannan ta ajiyewa Yusuf sauran.

Ta miƙe ta tattare ƙwallyen ta tafi taje ta zubar, gwaggo na ganin Widad tace "Amarya zo kinji yarinyar kirki"

Widad ta ƙarasa inda take, gwaggo tace "Amarya, daga yanzu idan mijinki ya dawo in yazo da kaya duk abunda kike ki tashi ki karɓi kayan hannunsa kinji?"

Widad a ranta tace 'wai nan duk zatonsu wani Auren kirki mukayi?'

A fili tace "To Mama zan dinga yi, amma gaskiya banda kaya me nauyi"

Gwaggo tayi murmushi tace "dama bance dame nauyi ba, amma ki dinga kula dashi sosai, ko so kike yayi miki amarya?"

Widad dariya kawai tayi tace "Mama kenan, to in yayi meye a ciki, nidai fatana mu koma gida"

Gwaggo tace  "hakane amma yakamata kidinga nuna kishi akansa, zeji daɗi ko Auren dolene kukayi?"

Ganin kamar Widad bata son zancen ne, yasa Widad tace "jeki abunki ɗiyata"

Widad ta juya ta tafi ɗaki, tana zuwa ta tarar Yusuf ya fito daga wankan, yana tsaye da gajeren wando a jikinsa yana goge ruwan wankan jikinsa, wasu irin dogayen gashi ne a jikin Yusuf, taga yayi mata wani irin girma da kwarjini.

A ɗan gigice tace "Yoseef meye haka?"

Da sauri ya waigo ya kalleta yace "meyafaru?"

"meyasa zaka shigomin ɗaki a haka? Kalleka fa tsirara"

Yusuf ya kalli kansa yace "Niba tsirara nake ba"

"to meye haka, naga a can banɗakin kake sa kayanka"

Yusuf yace "Ramawa nakeyi, Allah ya bani haƙuri in dai a haka tsirara nake, toke ban san a ya kike yawo ba"

Tsaki tayi ta shige can lungun ɗaki, ta juya masa baya ya juyo ya kalleta, yayi murmushi ya gama tsane jikinsa, ya zura riga, ya ɗakko man shafawa yazo kusa da ita yace

"dan Allah ki tayani shafawa a bayana mana"

"Allah ya kiyaye, ni ka tashi daga kusa dani"  ƙememe taƙi kallonsa.

Yusuf yace "kalli kiga"

Rintse ido ta sake yi tace "ni bazan Kalleka ba, seka sa kaya wallahi ko inyi ihu da ƙarfi"

"Aina saka kayan"

A hankali ta buɗe idonta tana kallonsa, Wani irin kallo yake mata, wanda ta kasa gane ma'anar kallon da yake mata.

Zamewa yayi ya kwanta akan cinyarta, yace  "Wash na gaji bayana ciwo yake kamar zan ɓalle"

Itadai kamar Yusuf ya ɗaureta yau, ta kasa magana sam balle ta motsa, hannunta ya kama yana ta murzawa a hankali, har bacci ya ɗaukeshi.

Har yanzu hannunsa yana cikin nata, Ƙura masa ido Widad tayi, gaba ɗaya Yusuf tausayi yake bata mussman idan ta tuna beji ba be gani ba tsautsayi ya ritsa dashi, se wahala yake faman sha, kuma be taɓa nuna mata ya gaza ba.

Riƙe hannunsa ta sake yi, ta toshe bakinta tana kuka, hawayen tausayinsu ya kamata.

Yusuf da bacci ya ɗauke shi, ya buɗe idonsa jin saukar hawayenta a fuskarsa, a gigice ya miƙe zaune yace "subhanallah meyafaru? Nine me nayi miki"?

Bata iya bashi amsa ba se kuka data cigaba dayi, Yusuf yace

"yi haƙuri na ɗagaki, tunda bakyaso bazan sake kwanciya a jikinki ba, yi haƙuri"

Ta lura baya son yaga tana kuka, dan haka ta basar dan karya gane acikin damuwa take yasa tace  "Kuma idan muka koma gida sena gayawa Daddy taɓani ka dingayi"

Yusuf yace "Yi haƙuri bazan sake ba, goge hawayenki bazan sake ba insha Allah, bari in sauka ma daga kan katifar"

"A'a ka kwanta anan, amma idan ka sake taɓani se nayi kuka, kuma Daddy zan gayawa idan muka koma gida"

"To shikenan naji"

Ya kwanta ya juya mata baya, murmushi ta dingayi ta miƙe ta tsallake shi tayi waje.


Alhaji Munir yace "Impossible, ta yaya Alhaji Nasir ze ɓata a gadon Asibiti, sekace ɓatan rigar sawa"

Alhaji Haruna yace "Abun da mamaki, a yadda yake dai be isa ya gudu da ƙafafunsa ba akwai wata a ƙasa"

Alhaji Munir yace "tabbas akwai lauje cikin naɗi, inma dai akwai wanda yake gefe yake mana manaƙisa, amma kowaye idan muka tono shi abun baze masa da daɗi ba"

Babu ko sallama Hajiya Halima ta shiga Falon Hajiya Sarah, a fusace ta kalli Sarah tace "ina megidan nan yake?"

Hajiya Sarah tace "lafiya kuwa, maman Anwar?"

"bani da lokacin baki wannan amsar, kije ki gaya masa ina son ganinsa"

Bulama yace  "Ai gani nan ina kusa"

Hajiya Halima ta kalleshi tace "da sanin ka aka kama min ɗana?"

Bulama yace "haka labari yazomin an kama shi"

"to ba labari bane ba, an kama min ɗana, to wallahi baze yuwu ba, daga abun Arziki seya koma na tsiya, daga yayi jinyarsa an sace shi a Asibiti se'a kamamin yaro akanme?"

Bulama yace "yanzu sace mijin naki be dameki ba?"

"Dalla karka gayamin maganar banza ko ka rainamin hankali mana, kai sace shin damunka yayi?"

"Yaya za'a sacemin Aminina ɗan uwana, sannan kizo kina tayarmin da hankali akan an kama ɗanki? Ki bar doka tayi aikinta, in sunga bashi da laifi zasu sake shi"

"dokar banza dokar wofi, ni zaka gayawa doka, doka nawa kayi amfani da kuɗi kayi fatali da ita a ƙasar nan? Ina son kayi Amfani da wannan damar taka da ikon kayi fatali da wannan dokar kasa a sakarmin ɗana, in bahaka ba you know what am capable of doing"


Godiya me tarin yawa Fans ina godiya 😍 😍 😍 😍 😍 😍

Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

                      _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 38_39

Shi kansa Saleh abun ya ɗaure masa kai, ta yaya za'a je har Asibiti a sace mara lafiya, kuma bayan da jam'ian tsaro a cikin Asibitin da suke tsaron lafiyarsa, koda yake ba abun mamaki bane a haɗa baki dasu a sace shin, saboda da yawa mutanen yanzu suna iya yin komai saboda kuɗi.

Maman Nurat ce ta shigo ɗakinta, ta tarar da Nurat tana kan system tana danne danne, ta ɗago ta  kalli Mahaifiyarta tace "Mummy lafiya kuwa?"

Mummy tace "Mhmm, wani labari naji"

Nurat tace "labarin me?"

"wai an nemi Alhaji Daula an rasa a Asibiti, yanzu haka an kama Shugaban Asibitin doctor Sufyan da kuma Anwar"

Zare farin glashin idonta Nurat tayi tace "What are serious Mum?"

"did I ever lie to you?"

Cikin kaɗuwa Nurat ta girgiza kai tace "Na shiga uku da wannan masifa, daga wannan se wannan ana ƙoƙarin a kashe wannan amma se waccan ta faru, an sace masa 'ya har yanzu ba wanda yasan inda suke, yana kwance yana fama da jinya an bishi gadon Asibiti an sace shi, innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Mummy me Anwar yayi aka kama shi to? "

Mummy tace " ina zan sani, ance dai har dashi a cikin suspect "

Nurat tace" idan harda sa hannun Yaya Anwar a ɓatan baban Widad, to tabbas beyi hakan dan cutar dashi ba, akwai dalili yakamata in ganshi "

Zare ido  Mummy tayi tace  " kiga wa? Ba dani ba Wallahi idan kika sake kika fita duk abunda yayi miki ke kika siya, na gaya miki babu ruwanki ki koma gefe ki taya su da Addu'a yafi "

Shiru Nurat tayi bata kuma cewa komai ba, Mummy ta gama mitarta ta tashi ta fita, ita kuwa Nurat ta shiga tunanin yadda zata yi ta fita.

Yanzu duk lokacin da aka idar da sallar Asuba, se Yusuf ya tsaya sunyi karatu a masallaci, aikuwa gasu da son karatun babu girman kai a lamarin su, dan haka yake jin daɗin koyar dasu, kuma ya basu damar yi masa tambayoyi, wasu tambayoyin idan kajisu sam bazaka ce musulmi ne ba, saboda tsagwaron Jahilci, Yusuf baya kyararsu ko hantararsu, haka yake amsa musu.
Akwai wanda yake tambayar Yusuf bayan an watse daga gurin karatun, wai shi ya zata in mutum ya kwanta da iyalinsa ba'a wanka se ranar Juma'a, Yusuf yayi masa bayani dalla dalla, kuma ya ƙudurce babu batun kunya, shine maudu'in daze musu gobe in Allah ya kai rai a gurin karatu "

Ya koma gida ya tarar da hakimar tanata kwasar baccinta, ya nemi guri shima ya ɗan kwanta, nannauyan bacci ne ya ɗauke shi, can cikin baccin nasa ya jiyo ihun Widad a tsakar gida, aikuwa a gigice ya tashi ya fita, wata kazar harice Widad tazo wucewa ta zata 'ya' yanta zata taɓa mata, dan haka ta fara bin Widad tana kai baki zata cije ta, shine take ta wannan ihun tana zagaye, ita kuma kazar na cigaba da binta.
  Hari na kallonta, ta dinga tintsira dariya, a gigice  Yusuf  ya fito, yazo da sauri ya kori kazar ya kalli Widad  yace "haba my queen, gaskiya kin ban kunya kaza ce fa kawai "

Widad tace "to ba cizona take son tayi ba, kuma wlh idan ta sake bina sena kamata na tura ta a cikin wutar can ta ƙone kowa ya huta"

Hari tace "kan bala'i, kazar tawa zaki saka a murhu? Aikuwa dana miki rashin mutunci kuma wallahi da sekin biyani"

Yusuf yace "yi haƙuri bama iyawa zata yi ba, tana faɗane kawai yanzun ma tanawa kazar ihu, ta ina zata iya kamawa balle tasa a murhu?"

Widad tai farat tace "to sena buga mata wannan icen ta mutu, ko in Takata da ƙafata harta mutu, garama kija mata kunne"

"Kazar zan jawa kunne ko kuma wa?"

"Eh ita kazar"

"ta yaya zanjawa kaza kunne? Ko nima kazarce?"

Widad tace "to waya sani"

Gwaggo dake banɗaki kam dariyarta ta sha, dan yanzu sun saba kusan kullum da rigimar Widad da Hari suke karyawa.

Yusuf da wanine yace masa Widad ta iya neman magana cewa ze ƙaryane, amma yanzu yake ganin zahiri da ikon Allah, haka yaita bawa Hari haƙuri sannan yasa Widad a gaba zuwa ɗaki.

Ya ƙura mata ido sannan yace "da wanine ya cemin kin iya rikici haka cewa zanyi an miki ƙarya, amma gashi da idona ina ganin ikon Allah, kullum sekin nemi magana"

"da da bana yi ancemin mahaukaciya bana son mutane, yanzu kuma kace na fiye rigima"

Yusuf yace "yi haƙuri, amma adinga ragewa kinji queen, waini ya'akayi kika sake da mutan gidan nan, abun ya bani mamaki fa"

"Basu san ni wace ba, dan haka bana tunanin zasu cutar dani, dukda suma bawai yarda dasu nayi ba, amma inajin daɗin yadda suke kyautata min ne"

Yusuf yace "to nifa, an yarda dani?"

Kallon up and down Tayi masa tace "tukuna dai"

"shikenan ni na yadda dake ai, zoki zauna kusa dani muyi hira"

"Baza'ayi hirar ba, idan nazo kusa da kai taɓani zakayi"

Dariya Yusuf yayi, yace "taɓakinne bakya so inyi?"

"Eh bana so, kai kuma sekace dole seka taɓani"

"ba laifina bane, laifin zuciyata ne Gimbiyata"

"kai ka sani kai da zuciyar taka"

Tai maganar tare da kwanciya ta koma bacci, a hankali Yusuf ya dawo kusa da ita ya kwanta, tana yunƙurin juyi akan katifarta taji mutum, ta leƙo kanta daga bargo taga Yusuf.

"wai dan Allah meyasa kake min hakane, tasarmin daga kan katifa"

"Niba taɓaki zanyi ba, ina son inyi bacci ne zuwa ƙarfe goma in fita, Amma cinnaku se cizona suke wuyana ciwo yake saboda kwanciyar ƙasa, haba uwa ɗakina, atemaka a tausayamin mana"

Tura baki tayi tace "to matsa ni in fita tsakar gida in baka guri seka kwanta"

Zaro ido yayi yace "haka kawai inje ki fita ki jawomin magana, ki fita neman rigima, a'a yi zamanki anan"

"toni gaskiya bazan kwanta a kusa da kai ba"

Banza yayi mata ya gyara kwanciyarsa, tare da lumshe ido, yunƙurawa tayi zata fice ya fizgota ya zaunar da ita yace "yi haƙuri, bari in tashi in bar miki katifar, base kin fita kin janyomin magana ba, har mamaki nake yadda kika koyo rigima"

"nifa ba magana zan ɗakko ba, ni kawai zomaye zan kalla"

"Idan kika tsokani Baba Hari, ba zan baki bredin ba"

"aikuwa kuka zanyi in ka hanani" ta miƙe tayi waje abunta.

Hankalin Hajiya Halima ya kasa kwanciya sam, saboda rufe mata ɗa da'akayi, Amal ma duk abun ya dametta, suna ta zaryar station amma abu ya gagara, Yanzu ma Amal ce ta tafi ɗakin Ramlah, ta tarar da ita a zaune tana waya, da Fahad.
Amal ta samu guri ta zauna, ta jira ta kammala sannan ta kalli Amal tace "lafiya kuwa? Kin shigomin ɗaki kin sani a gaba kina ta kallona"

Amal tace "Ramlah waike baki damu bane dan Allah, kwanan Yayanmu Uku a hannun 'yan sanda, Mummy se zarya take anƙi sakinsa, amma kin shigo ɗaki wayarki kawai kike"

"to Amal haukacewa kike so kiga nayi ko yaya? Shima Allah ya ƙara masa waishi ga me mutunci ya zauna yana jiyyar uban da ya tsinta a rana, kinga hakan ze zamo masa darasi gobe baya ƙara taimakao ba"

Amal tace "bekamata ki faɗi haka ba Ramlah? Ta wani fannin in aka duba abunda Yaya yayi beyi laifi ba, ko so kike duniya ta farga da halin da'ake ciki? Ace bashi da lafiya amma babu wanda ya damu a cikinmu? Ni wallahi abun ya fara damuna koba komai Yaya Anwar ɗan uwanmu ne"

Ramlah tayi ajiyar zuciya tace  "kuma fa hakane, ni kaina ta wani fannin inajin ba daɗi rufe shin da'akayi, amma me zan iya akai wanda Mummy ta kasa"?

Amal tace  "Fahad zakiyiwa magana, dan Mummy taje har gidansu ta gayawa mahaifinsa amma yaƙi ɗaukar abun da mahimmanci, ke tunda kuna ɗasawa dashi kisa yayiwa mahaifinsa magana yasa baki a saki Yayanmu"

Ramlah tace "Anya kuwa? Fahad fa akwai lafiyar kafiya mussman yanzu da suke takun saƙa da yaya"

Amal ta taɓe baki tace "ashema ba son naki yake ba tsakani da Allah tunda ze iya barinki cikin damuwa, Allah wadaran wannan soyayyar"

"Amal ni kike cewa Allah wadaran?"

"Na faɗa Allah ya wadaranta, dama wannan banzan Fahad ɗin me fuskar jakai kansa kawai ya sani, in ba soyayyar ƙarya ba, yayiwa mahaifinsa magana yasa baki a saki ɗan uwanmu mana, naga shima dai ɗan uwansa ne"

Ramlah tace "Aikuwa Amal i will prove you wrong, zan nuna miki soyayyar mu ta gaskiya ce"

Amal tace "in gani ƙas, ancewa kare ana biki a gidansu, ƙaryar banza burodi a lefe, ina amfanin soyayyar da baka da alfarma a gun wanda kake so"

Ta tashi ta bar mata ɗakin, tana ci gaba da mita da tsaki.

Nurat ta shirya cikin doguwar riga, tayi rolling ta ɗau wayarta da jakarta ta fito, ta leƙa ɗakin mamanta taga tana bacci, ta taho cikim sanɗa ta fito harabar gidan, da sauri sauri ta tafi bakin gate tace "zoka buɗemin ƙofa zan fita"

Me gadi ya kalleta yace   "ina zaki?"

"ka aikeni ne? Ka buɗemin zan fita"

Ya ɗan sosa kai yace "Madam, me gidan nan yace kar in kuskura in sake bari ki fita, muddin bashi ya bada umarnin hakan ba"

A ɗan hasale tace "ka buɗemin ba nisa zanyi ba, yanzu zan dawo"

Girgiza mata kai yayi yace "dan Allah kiyi haƙuri, wallahi zan fuskanci fushinsa muddin na bari kika fita"

Juya tayi cikin gida, jiki ba ƙwari tana tunanin meye mafita, can wani abu ya faɗo mata, ta miƙe ta fito tace masa  "kazo Mummy na kiranka"

Ya miƙe ya biyo bayan Nurat, yana gaba tana binsa a baya, yana shiga falonsu cikin sanɗa ta dawo baya a hankali, tayi waje tana zuwa tasa mukulli ta buɗe gate ɗin tayi waje abunta.

Gidansu Widad ta tafi, tana zuwa tayi sa'a ta tarar da Amal a babban falo tana karyawa, Amal na ganinta ta buɗe baki tace "Nurat yau kece a gidanmu haka? Abun mamaki"

Nurat tayi murmushi tace "meye na mamakin kuma?"

Amal tace "ni dai nasan koda zaki zo gidan nan saboda Widad zaki zo, kuma duk garin nan ba wanda be san anyi kidnapping ɗinsu ba, kuma dai amma baban ku besan kinzo ba"

Nurat tayi murmushi tace "tabbas nasan an sace Widad da ɗan uwanta, sedai...

Amal tace " ɗan uwanta kuma? Direbanta dai"

Nurat tace "direba kuma kamar yaya direba?"

Amal tace "kamar yadda na gaya miki, ita da Yusuf ne aka ɗauke su, Yusuf kuma direbanta ne"

Nurat tayi shiru, sannan tace "Amma meye alaƙar dake tsakaninta da Yusuf?"

Amal tace "Allah kaɗai yasani, Wallahi Nurat ina cikin matuƙar damuwa ɓatn nan nasu, mussman Yusuf idan nace zan nuna damuwar da nake ciki ma babu me saurarata a gidan nan, Amma duk rashin yardar Widad ta yadda da Yusuf fiye da tunaninki"

"Amma Amal mezesa matashi kamar Yusuf ya ɓige da aikin direba a gidan masu kuɗi?"

Amal tace "bake ba ni kaina ina wannan tambayar, amma kin san da wani aikin gwamnatin gara aiki a gida kamar wannan, dan ba Widad ba hatta me gidan nan ya yadda dashi sosai, Amma a yadda Yusuf ya haɗu kam, bekamata ace aikin direba yake ba, nayi masa zancen ya nemi wani aikin, amma yaƙi yarda, yafi ƙaunar kasancewa a ƙarƙashin wannan uwar izzar, tana hantararsa tana komai amma baya ganin laifinta"

Shiru Nurat tayi kamar ba zata ce komai ba, can tayi ajiyar zuciya tace "Amal ya batun Yaya Anwar kuwa?"

Amal tace "hamm, yana can Mummy tana ta fama anƙi sakinsa, wai har yanzu bincike ake akai"

Nurat tace "wani station ɗinne?"

"Suna state CID shida Likitan"

Nurat tace "Allah ya fidda shi lafiya, Insha Allah zanje in ganshi"

Amal tace "kai amma kuwa mungode sosai Nurat"

Nurat tace "bakomai Amal, se anjima"

Yusuf yayi baccinsa ya tashi, ya buɗe jakarsa ya ɗakko kayan tea daya bada sautu aka kawo masa, ya ɗora tea Widad tana tsakar gida suna hira da Hindu, da hansai.

Yayinda Hanne se wani gyatsine fuska take yi, bata kallon ko inda Widad take, Widad data fita bata taɓa nuna tasan da halittar Hanne ba, abun da Hanne bata sani ba shine, mutanen da suka damu da itama ba kowa take iya shiga sabgarsa ba, balle wanda ya nuna be damu da ita ba.

Yusuf ne ya fito tsakar gida, yaje ɗakin megari suka sake gaisawa  ya zauna suka shiga hira.

Widad na zaune kusa da gwaggo, tana dama koko tana kallon yadda take yi, Widad tace "Mama haɗa kokon nan ma ashe ba wahala, na iya haɗa custard shima zan iya wannan"

Hansai tace "meye kuma kostan?"

Widad tace "wani abune shima sha ake, kamar haka ake dama shi amma suna da ɗan banbanci da wannan, Ai zaki ban watarna nima inyi ko?"

"taɓ za'a sha kwaɓa kuwa, yadda kike a sangarcen nan ba uwar da kika iya, mijinki na fama wallahi, ba uwar da kika iya se zance"

Widad ta ɗaga ido ta kalli Hari tace "Mijinki ne yake fama da ƙazantarki ba nawa ba, kuma karki ƙara cemin sangartacciya"

Gwaggo tace "yi haƙuri Amarya, ƙyaleta"

Gwaggo ta fara rabon koko, ana zuba na kofin megari Widad tasa hannu ta ɗauka tace "wannan nake so, wannan kofin yafi kyau"

Gwaggo ta ɗanyi shiru, Hansai tace "Amarya kofin megari nefa"

Widad ta tura baki tace "toni ina son kofin, wannan nake so"

Gwaggo tace "Hindu, jeki ki duba ƙasan gadona a cikin kwanukan Hanne ki ɗakkon sabon kofi irina Malam"

Hanne tace "kai gwaggo kofin Auren nawa za'a ɗakko?"

Gwaggo tace "eh kema ba Allah ne ya baki ba, a sai miki wani"

Haka aka ɗakko sabon kofin silva, se ƙyalli yake da murfinsa aka zubawa Widad koko a ciki, Hanne ta dinga mita tana kumbura baki, ai Widad bata nuna tasan da zaman Hanne a gurin ba.

Hanne na tsaka da masifar ne sega Yusuf ya fito daga ɗakin megari, ai nan da nan Hanne ta nutsu ta fara murmushi, Yusuf ya harari Widad dan yaji duk abunda ya faru, ita kuwa tayi kamar bata ganshi ba.

Hanne ta durƙusa ta gaida Yusuf, Yusuf ya ɗan saki fuska ya amsa mata, yazo ya durƙusa ya gaida su gwaggo, duk faɗan da Hari keyi da Widad, tana matuƙar girmama Yusuf, dan suna ɗasawa dashi.

Hanne tace "yau ba wanke wanke ne ka kawo ayi?"

Yusuf ya kalli inda Widad take, yaga ko a jikin ta, jujjuya kofin kokonta kawai take.

Yusuf yace "A'a babu na wanke tun Asuba.

Gwaggo tace "kaine kake wanke wanken? "

Yusuf yayi murmushi yace "A'a Mama, wani lokacin ina rage mata aikine kawai"

Gwaggo ta kalli Widad tace "Anya Ɗiyata?"

Widad tace  "Mena yi? Shine yake cewa zeyi fa, kuma idan nace zanyi se yace ban iya ba"

Hanne tace "ka dinga barinsu, da safe se in haɗa in wanke, tunda bata iya ba"

Hansai tace "ikon Allah, toke Hanne dole ne sekin wanke musu kwanukan?"

Widad tace "Yoseef kaga sabon kofinmu, Mama ta bamu"

Yusuf yace "Ahh mama mungode sosai Allah yasaka da alkhairi"

Ya kalli Widad yace "let's go and have a breakfast"

Ta miƙe tayi gaba, suna zuwa ɗaki yace "sannu kinji"

Cikin rashin fahimta tace "aikin me nayi kakemin sannu?"

"yanzu memakon kice in sai miki kofin kina so, kawai seki sa rigima ke se'an baki?"

"ko zaka Ƙwace ka mayar ne?"

Yusuf yace "A'a ni bance ba, na dafa shayi ne kuma gashi kin karɓo koko"

Da sauri tace "dan Allah dagaske?"

Bece mata komai ba, ya wuce ya sauke tukunyar tea ɗin, ya buɗe jakarsa ya ɗakko kayan tea ɗin ya haɗa mata shayi yasa mata madara, tana zaune tana kallonsa, ya ɗauka ya kai ya ɗanɗana yaji in beyi zafi da yawa ba sannan ya bata.

Ta kalle shi tace  "meye kuma seka sha zaka bani?"

"Na duba ne inji in beyi zafi da yawa ba karki ƙone baki"

"to shine zaka sa baki a jikin kofin, toni gaskiya da cokali zan sha tunda kasa baki, ko in canza kofi"

Tsayawa yayi yana kallonta, taje ta ɗakko wani kofin ta juye a ciki, ta ɗau bredin ta gutsura ta koma gefe.

Karon farko da taga fuskar Yusuf ta canza saboda abunda tayi, ta nuna ƙarara tana ƙyamarsa kenan.

Tana kallon yadda ya ɗan ɓata fuska, ya kasa sakin jiki yaci Abincin ma, amma ta basar ta cigaba da cin bredinta, da a gidane ba yadda za'ayi taci bredi babu mahaɗi, amma yanzu se tura shi take kuma tana jin daɗinsa  a haka.

Ƙarshe Yusuf miƙewa yayi yaje yayo wanka, yazo ya fara shirin fita sedai yaƙi cewa uffan, be sake kula ta ba shirinsa kawai yake.

Widad ta matsa inda yake tace "wai naga ka wani yi shiru, lafiya dai?"

Girgiza mata kai yayi, ya cigaba da shirinsa "Amma naji kayi shiru haka? Nasan baka saba zama haka kayi tsit ba"

Still shiru ya kuma yi mata, yana gyara kayansa dake cikin jakar matafiya.

Ɗagowar da zeyi taga idonsa yayi jawur, gaba ɗaya se jikin ta yayi sanyi.

"dan Allah meye ya same ka?"

Raɓata yayi ze wuce ta sha gabansa tana kallonsa.

Ze kuma kaucewa ta kuma shan gabansa, ba tayi tsammani ba Yusuf ya janyota ya haɗe bakinsa da nata.

Mutsu Mutsu ta dingayi tana ƙoƙarin ƙwacewa, amma ta kasa ko ƙwaƙwaran motsi, saboda yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba.

A hankali ya cika ta, tayi baya da sauri tana rarraba ido, tare da sauke numfashi.

Tofar da yawun bakin ta ta dingayi, tana goge bakinta tana kuka.

Yusuf ya ƙaraso inda take, amma ta shiga ja da baya, riƙota yayi ya ƙura mata ido, take yayi mata wani irin kwarjini.

Cikin sanyin jiki Yusuf yace "Widad da zuciya zatamin adalci to da ban iya jure duk wulaƙancin da kikemin a baya ba, saboda Yusuf baya Jura wulaƙanci dan shima mutum ne kamar kowa, sedai kash zuciya ta ta fara son abunda tasan yayi mata nisa har abada, wanda be dace da ita ba, zuciyata ta saɓa Alƙawarin da mukayi da ita nayin ban kwana da soyayya har Abada, hakan shine kawai mafita ga irin rayuwar da Yusuf ya tsinci kansa a ciki, Amma ko warkewa banba daga cikin zugi da raɗaɗin da zuciyata ke ciki ba, ƙaddara ta haɗani dake, kuma zuciyata ta shiga begen ki, Auren nan da mukayi har cikin zuciyata nake som Auren nan, sedai nasan dole wataran zamu rabu saboda bamu gina Auren akan tirbar soyayya ba, dan Allah Widad ni bance sekin soni ba, saboda nasan hakan baya cikin tsarin rayuwar ki, kuma tamkar ƙasƙancine a gareki Auren mutumin dabe kaiki a komai ba, nasan yanzu ma kutsen ƙaddara ne ya haɗamu zama inuwa ɗaya dake, ko baki soni ba dan Allah kidena nunamin ƙyama kinji Gimbiya, yi haƙuri na saki kuka" yai maganar yana ƙoƙarin goge mata hawaye

Fizgewa tayi tace "Dalla ni cikani in wuce, the must useless word i hate in my life Love, kaima ka shiga sahun imagination da shirme kenan, ban guri ni zan wuce"

Ta ture shi tayi gaba abunta, ta ɗakko brush da toothpaste ta tafi sake wanke baki, duk dan Yusuf yayi kissing ɗinta.

Jiki a sanyaye ya ƙarasa shiryawa, ya fito ze fita ko kallon inda yake ba tayi ba, ganin ba kowa  a tsakar gidan se Hanne yasa yazo gabanta yace "Zan tafi"

"Jirani inzo in zama mota seka hau ka tafi"

Ya girgiza kai yace  "nasan kina jin haushina, kiyi haƙuri"

Banza tayi masa ta cigaba da abunda take, Hanne tace  "Adawo lafiya Allah ya tsare"

Yusuf yayi murmushi yace "Allah yasa nagode"

Har yayi gaba ya waigo ya kalle ta, suka haɗa ido ya ɗan lumshe ido yace "I love you My queen"

Wata uwar harara tayi masa ta miƙe ta bar tsakar gidan.

Nurat tana zaune a reception, da ƙyar aka bari taga Anwar, fuskarsa duk ta ɗaga yayi wani iri, a gigice tace "Yaya Anwar me kayi aka kama ka haka?"

Anwar yace "wallahi Nurat ban saniba, wai ana tuhumata da haɗin bakina akan sace Daddy, kuma wallahi ban san komai ba, na gyara masa jiki na bashi abinci, likita yace inje in karɓo wani magani, ina komawa se cemin yayi wai ya shiga ɗakin amma be ganshi ba"

Nurat tace "kamar yaya, ta yaya za'a sace mutum a Asibiti mutumin dako motsin kirki baya iyayi"

Anwar yace  "wallahi bam sani ba Nurat, ni yanzu ba kamanin da'akayine damuwa ta ba, sanin inda Alhaji Nasir yake shine babbar damuwa ta, ba shi da lafiya waye ya sace shi? Waze kula dashi? Waze bashi magani na rasa wacce irin masifa ce tasa ake bibiyarsa haka"

Shiru Nurat tayi tana zancen zuci  'Anya kuwa babu sa hannun mahaifina a sace Alhaji Nasir?'

Ta ɗago ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar baka yi laifi ba dan baka banga dalilin da zesa a kama ka ba, dan haka ka kwantar da hankalinka, akwai wani cousin brother ɗina, barrister Abdallah zan masa magana ya shiga cikin case ɗin"

Anwar yace "bakya ganin akwai matsala? Kar a sashi a matsala fa, sunce in suka gama bincike za'a sakeni"

"babu wata matsala insha Allah, ka kwantar da hankalinka, Insha Allah zak bar gurin nan"

Anwar yace "Nagode sosai Ƙanwata, Allah yasaka miki da alkhairi"

Nurat tace  "you deserve it dear" ta ɗau jakarta tayi waje.

Ramlah ce zaune a motar Fahad, ta murtuke fuska yana ta surutu amma tayi shiru, kallonta yayi yace "beb, ya inata magana amma kinyi shiru, lafiya kuwa?"

"Fahad yanzu ace brother na yana ɗaure, amma koka jajantamin talk less of kace zaka kai masa ziyara"

Fahad yace "ni inje state CID no i can't tarnish my image"

"Amma fa kaima ɗan uwanka nae"

"Yeah really, you are right dear but zuwa gurin nan se masu manyan crimes da manyan terrors, kuma kinga daddy na sanannen mutum ne, ace anga mutum kamar ni a irin wannan gurin is not fair at all, it will tarnish our family image"

Ramlah tace 'but your dad can bale him out, so you don't care about my feelings, ɗan uwana yana rufe kaikuma abunda ya dameka daban ko? "

"Ai na miki bayani, ban san me kike so ayi ba kuma"

"ina son ka saka baki, Daddynka yayi magana a sake shi"

"Amma Ramlah kin san ba abune me sauƙi yin hakan ba ko, yaynki an haɗa baki dashi an sace Daula, me zesa Daddy yasa baki"

A fusace  Ramlah tace "shut up Fahad, ta yaya Anwar ze hakan, tare kukayi school room ɗinku ɗaya, you know what he can do and what he cannot do, dan haka ina jiran kaje kayi magana da mahaifinka a fito da shi, that's the only way you can prove to me that you loves me"

Tana gama maganar tayi waje ta bar motar, ɗan taɓe baki yayi ya kunna motarsa yayi tafiyarsa.

Yau da Yusuf ya dawo a ɗaki ya tarar da widad, kamar tana cikin damuwa ya kalle ta yace "Na dawo"

Jinjina masa kai kawai tayi, amma ta kasa magana, se ya zata tun abunda ya faru da safe ne yasa take jin haushinsa.

"Meke damun kine? Ko har yanzu fushin kike dani?"

A kasale tace "Bakomai fa"

Haka ya fita yaje yayi wanka ya dawo ya sameta a inda ya barta, yau dambun tsaki Hansai ta girka ta aiko musu, amma taƙi sakin jiki taci, ya kaɗa ya raya amma tace lafiyarta ƙalau, sedai ya lura buni buni seta tafi toilet ta dawo.

"Gimbiya ko cikin kine ya ɓaci?"

Girgiza masa kai tayi tare da kwanciya, haka taita yi har washegari gaba ɗaya kamar bata da sukuni, kuma taƙi gaya masa abunda yake damun ta, haka ya fita ya barta ya ɗauka dai fushi kawai take, Da Azahar ya dawo sedai ya tarar da tun Abincin safe bata kuma cin komai ba.

Yaje gabanta ya durƙusa yana ƙare mata kallo yace "dan Allah idan fushi kike dani kiyi haƙuri, kin sani a damuwa fa"

"Nifa ba fushi nake ba, ka ƙyaleni kawai"

"baki da lafiya ne?"

"lafiya ta ƙalau"

"but you look so much restless"

Shiru tayi bata ce uffan ba, ya miƙe yana duba kwanuka yaga abunda aka kawao, se yaga tana ta dube duben abun shimfiɗar dake kan katifarta.

Yana zuwa ya ɗagata cak daga kan katifar, meze gani jini ne a jikin ta, ya ɓata mata jiki da katifar.

A gigice yace "Subhanallah, Widad meya same ki haka?"

Take ta fashe da kuka tace "Period yazo min tun jiya bani da pad"

Cike da damuwa yace "shikenan is ok, kwantar da hankalinki"

Yasa hannu ya naɗe bedsheets ɗin, ya ɗora ruwa yayi ɗumi ya haɗa mata ruwa, ya rakata banɗaki, ya dawo ya haɗa abun shimfiɗar da kayan data cire ya zubasu a bokiti.

Tayi wankan ta fito ta dawo ɗakin, har yanzu bata dena kuka ba, Yusuf yace "jeki zauna bari inje gurin Mama inga inda wani taimako da zata bamu"

"Idan na zauna ɓata gurin zanyi"

Yusuf yace "bakomai zauna, idan ya ɓaci zan gyara"

Ya zaunar da ita ya fita da sauri.

Yana fita tsakar gida Hanne ta kalle shi tayi murmushi tace   "kana buƙatar wani abune?"

Yusuf yace "gwaggo zaki kira min dan Allah"

Tace "to"

Ta tashi ta shiga ɗakin gwaggo, gwaggo ta fito ta kalli Yusuf tace "lafiya dai malam Yusuf?"

Cike da kunya, Yusuf yayi mata bayani, Gwaggo tace "to mudai yaranmu da tsimmane suke amfani, ban sani ba ko zata iya amfani da shi"

Yusuf yace "bakomai Gwaggo, zata iya insha Allah"

Gwaggo ta shiga ɗaki ta ɗakko sabon turmin Atamfa, da sabuwar reza, da ƙyar Gwaggo ta iya shiga ɗakin nasu saboda kunya.

Widad na zaune da towel se vest a jikinta, Gwaggo tace "Sannu Amarya ya jiki?"

Widad tace "lafiya ƙalau"

Tasa reza ta yanka Sabuwar Atamfa ta gwadawa Widad yadda zata yi.

Widad tayi shiru taƙi cewa uffan, Yusuf yace "Mama nagode sosai da taimakonki, Allah ya saka da alkhairi"

Gwaggo tace "bakomai Malam Yusufa"

Gwaggo ta fita, tana fita Hari tace "Yaya wai Wudas ɗince bata da lafiya?"

Gwaggo tace "Eh"

"meya same ta?"

Gwaggo bata amsa mata ba, Hanne tace "waini Gwaggo meye na yanka sabuwar Atamfarki, wallahi kin fiye zaƙewa akan wannan fitsararriyar"

Gwaggo a fusace tace "wallahi kika kuma magana sena kwaɗa miki mari, ina kallon ki duk abunda kike yi, ɗa na kowa ne, meye dan na yanka Atamfa? Abum duniya fararre ƙararre"

Haushi Hanne taji, dan da wuya kaga Gwaggo tana faɗa se an ɓata mata rai sosai, Amma yau akan wannan koɗaɗɗiyar tana ta mata masifa.

Yusuf ya kalli Widad yace "gimbiyata nasan baki saba amfani da irin wannan ba, amma kiyi haƙuri gidanmu babu mata nikaɗai ne shiyasa nima ban san kan wannan abubuwan ba, da tuntuni nasa an nemo miki abunda zaki yi amfani dashi"

Da ƙyar Yusuf ya lallaɓata ta saka ƙyallen nan, sam she's not comfortable with this thing, gaba ɗaya ta takure kanta, Yusuf yana kallonta ta kwanta ta zauna gaba ɗaya ta kasa zama.

Ya kwashi kayan data ɓata yaje ya wanke su tsaf, taga ya dawo ɗaki yana goge hannu ta kalleshi tace "wai me kayi?"

"kayanki na wanke"

"Kayan jinin?"

"Eh mana, nasan idan na bar miki ba zaki iya wankewa ba"

Shiru tayi ta bishi da kallo, tuno abunda ya faru da safe tayi, yadda tay masa wulaƙanci amma har ya manta yana tarairayarta, yasa hannu a kayanta na jini ya wanke.

Ganin da yayi ta kasa zaune ta kasa tsaye yace  "Gimbiyata meya ke damunki yanzu?"

"ƙafafuna ne kamar ba nawa ba, babu daɗi marata ma ciwo takemin"

Yazo ya zauna a kusa da ita, ya kamo ƙafafunta ya ɗora akan cinyarsa yana matsa mata a hankali, lumshe ido ta dinga yi.

Ta ɗauke ƙafafunta daga kan cinyarsa, ta ɗora kanta sannan ta miƙa masa hannunta, tana masa nuni daya ja mata yatsun, haka Yusuf ya riƙe yatsun ta yana matsawa a hankali, babu daɗewa kuwa bacci yayi gaba da ita.

Seda Nurat ta tinkaro komawa gida sannan gabanta ya shiga faɗuwa, dan se yanzu ma ta tuna taɓargazar da tayi.

Kanta tsaye tana ta Addu'a ta fara buga gate ɗin, me gadi yazo ya buɗe mata bece mata uffan ba, ta shiga cikin gidan, sedai me a harabar gidan idonta ya sauka a cikin na mahaifinta yana zaune yana kallonta.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

(Ina ma'abota karatun littafin AƘIDATA, a fari nace zan bada littafin kyauta ba tare da ko sisi ba, amin Afuwa wani dalili zesa zan saida book2 and 3,dukda nima ba hakan naso ba, gaba ɗaya kyauta nayi niyya bada littafina, Amma dalilin me ƙarfi zesa in saida ƙarashen in na gama book1 ina fatan zaku fahimceni)



Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
                  _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 40_41

Gaban Nurat ne ya shiga bugawa da sauri da sauri, ta shiga zazzare ido be kula ta ba bece mata komai ba, tazo ta tsaya tana kallon sa, taga harta wuce bece mata uffan ba.

Ta shiga ɗaki ta nemi guri ta zauna, tayi shiru tana tunanin yadda zata samu Anwar ya kuɓuta, babu zato  taji an murɗa ƙofar ɗakin nata.

Mahaifinta ne ya shigo yana rarraba ido, gadan gadan yayo kanta yana faɗin "gidan ubanwa kika je?"

Miƙewa tayi a gigice ta shiga ja da baya tana faɗin "babu inda naje Daddy"

"ƙarya kike munafuka, harni zan saka doka ki sa ƙafa kiyi fatali da ita? Uwarki ta ɗaure miki gindin kiyi rashin mutunci ko? Ni da Daula waye ya haifeki?"

"Daddy niba gurinsa na je ba, Ai an ɗauke shi daga Asibiti"

Sekuma yayi sak, "Ubanwa waye ya gaya miki?"

"wallahi Daddy a gari naji"

"to gidan ubanwa kikaje? Zaki gayamin ko sena yanka ki a gidan nan?"

Girgiza kai take, takasa magana ya cakumo wuyanta yana zazzare ido, kakari ta dinga yi tana kuka tace "Wallahi Daddy ba inda naje, kawai gajiya nayi da zaman gidan na fita, dan Allah kayi haƙuri"

"se naci ubanki yadda idan na sake saka doka ba zaki takamin ba"

Cikin kuka Nurat tace "Wayyo Allah Mummy, ki temakeni karya kasheni"

Maimakon ya saketa sake shaƙeta yayi, yana kuma zaro mata ido kamar tsohon maye.

Kakarin Nurat ne yasa mahaifiyar ta, ta sallame salar da take, a guje ta rugo ɗakin Nurat, ta tarar ya shaƙe Nurat kamar ya kama sa'ansa ko kuma wani shahararren Ɓarawo.

"Kayi haukane, ka cikamin 'yata ita kaɗai ce dani, kana gani duk yaranmu mutuwa suke, ita kaɗai Allah ya barmin ka ƙyalemin' yata"

Juyowa yayi a fusace ya mangare mahaifiyar Nurat yace "itama ɗin gara in aikata inda waɗancn suka tafi, muddin zata dinga takemin doka, tasan a duniya bani da maƙiyi sama da Daula, danme zata dinga zuwa inda yake, akan me?"

Yai maganar tare da wurgi da Nurat, wadda tuni ta fara fita a hayyacinta, dan daya jefar da ita ko motsi ba tayi, se kokawa take da numfashi.

Da sauri Maman Nurat ta nufi kan Nurat, yayin da Alhaji Musa ya cigaba da banbami, ta ɗago Nurat sedai bata numfashi.

Cikin kuka tace "wallahi idan ka kashe min 'ya se nayi shari'a da kai, Kai kanka kawai ka sani, buƙata in ba ta kaba baka damu da kowa ba"

A fusace yace "Maza karki fasa yin shari'a dani, idan na kashe ta na kashe banza, duk son da nakewa mutum muddin ze bujiremin to zega ba dai dai ba tabbas"

Banza tayi masa, Taje ta buɗe fridge ta ɗakko ruwa me sanyi ta shiga shafawa Nurat, a hankali ta dinga sauke Numfashi, tana buɗe ido ta fashe da kuka tace "Mummy anya Daddy ne ya haife ni? Kalli yadda yayi yunƙurin kasheni me nayi masa haka?"

"kema da halinki Nurat, kin fiye taurin kai, na hana ki wannan abun da kike amma kin kasa ganewa, gashi ze kashe ki a banza"

Shiru Nurat tayi, tabbas tunda mahaifinta yake yunƙurin kashe ta akan taje inda Daula yake, to tabbas wani mummunan abu yake aikatawa, kuma na abunda baze iya aikatawa akan kowa ba.
Lumshe idon ta tayi tana jin yadda ƙirjinta yayi nauyi, wani irin baƙinciki ya mamaye zuciyarta.

Shikuwa Alhaji Musa yana komawa ɗaki ya shiga sintiri, kamar yadda ya zame masa jiki a 'yan kwanakin nan, ba shi da nutsuwa sam, musamman da' aka ce su Widad sun gudu daga inda aka sace su, gashi sunsa a nemo su a ko'ina suke amma abu ya gagara.

Gashi yanzu wata maganar rainin hankali da ta taso, wai an sace Daula akan gadon Asibiti, 'Anya ba wani rainin hankalim su Alhaji Haruna suke shiryawa ba?'

A hankali Widad ta buɗe ido daga baccin da yayi awon gaba da ita, taga Yusuf ya jingina da jikin bango ya lumshe idanunsa, hannunsa ɗaya yana wasa da gashin kanta, a hankali tayi miƙa tare da hamma, da sauri ya buɗe ido yana jera mata sannu.

Ba tace komai ba se jinjina masa kai da take.

Miƙewa tayi zaune, se kuma yaga ta yamutsa fuska.

Kallon ta yayi da sauri yace "lafiya dai?"

Ɗan tura baki tayi tace "am not confortable at all, ji nake kaman am stain"

Yusuf yace "kiyi haƙuri insha Allah, zan san yadda zanyi a samo miki wancan da kike amfani da shi"

Widad tace "baza a samu wanda nake amfani da shi ba, sedai a siyomin kowanne ne, bana son wannan abun da nake using dashi yanzu, is so much irritating"

Yusuf yace "Shikenan, Insha Allah zan san abunyi"

"Sannan kuma..." se kuma tayi shiru

"sannan kuma me?" Yusuf ya tambaya

"Nasan baza'a samu shaving cream ko powder ba, a siyomin shaver please"

Cike da son ya kunnata Yusuf yace "shaver kuma, me zakiyi da shaver?"

"Abunda kake yi da ita" ta bashi amsa cike da tsiwa

Yayi murmushi yace "Aini gemuna nake askewa da ita"

Ta kalle shi ta ɗan tsuke baki tace "Nima nawa gemun zan aske"

Aikuwa Yusuf ya kwashe da dariya, sosai yadda tayi magana da abunda ta faɗa ɗin ya bashi dariya, kallonsa take yi yadda dariyar tayi masa kyau.

"wallahi idan ka ƙware ba ruwana"

Tai maganar tana shirin Miƙewa, ya kalleta yace "Ina zaki?"

"tsakar gida nake son fita"

"Amma kin manta halin da kike ciki ne?"

"To zama zan tayi ina kallonka, ni na gaji da kwanciyar ma, zan kula sosai"

Yusuf yace "Aini bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskar nan taki, muyi zamanmu a ɗaki nima na iya hirar se in miki, kuma baki ci Abinci ba, ko kin manta?"

'ƙyale Abincin nan, ni idan ina period bana son Abinci sosai "

Yusuf yace " dama can haka kike, ina lura dake tarkace kawai kike ci ba Abinci ba, so nake ki ƙara Ƙiba ki daure kici ko kaɗan ne mana"

"Ni gaskiya, ba irin wannan nake so ba"

"wanne kike so" ya faɗa cike da kulawa.

Ɗan tsura masa ido tayi, sannan tace
"Bari dai inci kaɗan"

Ya ɗakko kwanon dambun ya ajiye mata, tasa cokali ta fara ci, dambun tsaki ne amma yaji gyaɗa da zogale yayi daɗi Sosai.

Widad tace "tunda nazo ƙauyen nan, ban taɓa cin Abinci me daɗin wannan ba"

Yusuf yayi murmushi yace  "harda bredin jiya?"

Widad tace "hmm dan dai kar kaji haushi ne, amma gaskiya bredin nan ya daɗe a ajiye, se marmashewa yake ba daɗi"

Yusuf yace "dagaske ba kya son inji haushi?"

Ɗan kallonsa tayi tace "No i mean banyi niyyar magana ba lokacin shine kawai, ka ɗakko spoon muci Abinci mana"

Yusuf ya girgiza kai yace "A'a kici kawai, idan kin rage se inci"

Widad tace "meyasa? Ai ze ishemu"

Yusuf yace "bana son in samiki yawuna a jiki, naga bakya son hakan"

Ɗan tura baki tayi, cikin ƙunƙuni tace "na nawa kuma, ƙarewa ma ai Yawun naka ka samun a bakina jiya"

Yusuf yace "ai bazan manta wannan moment ɗinba, nayi kissing ɗin gimbiyata the most memorable moment in my life"

Widad tace "tabbas kam, ka kafa tarihi, kayi abunda wani mahaluki be taɓa gangancin gwadawa ba, kayi min abunda ban taɓa zaton wani zemin in ƙyaleshi ba, hmm ban san meyasa kake min abubuwa son ranka ba, ƙyaleka kawai nake"

"Are you sure babu wanda ya taɓa kissing ɗinki seni?"

Watsa dambu tayi a bakinta, ta ja wasu seconds sannan tace "Idan an taɓayi kana tunanin zanji tsoron ka ne? Ban taɓa shan yawun Ƙato ba se a kanka, kuma bashi ka ɗauka, tunda kasa na haɗiye yawunka"

Murmushi Yusuf yayi yace "Yaushe ne ranar biyan bashin?"

Banza tayi masa taƙi ko kallon inda yake, can Yusuf yace "Amma meyasa kike zuwa Clubs da kuma Hotel?"

Jin tambayar tayi a bazata, take taji tana kokawa da dambun dake bakinta, gaba ɗaya Mood ɗinta ya canza a hankali tace

"ai tun a lokacin na gaya maka me nake zuwa yi, na gaya maka ni karuwa ce kamar yadda matan gurin suke"

Haɗe rai Yusuf yayi yace "Kamar yadda bakya son ƙarya, na tabbata kema bakya aikata ta se bisa kuskure, meyasa zaki gayamin haka? Ko kina son zuciya ta ta buga ne?".

"Tunda baka yarda ba shikenan, amma kasan dai bazan zauna ina rantse maka dan ka yarda dani bako?"

Ta ajiye spoon ɗin Abincin ta je ta sha ruwa, tayi waje abunta ta bar Yusuf a gurin a zaune.

Roƙon Allah ya shiga yi akan Allah yasa abunda Widad ta faɗa ƙaryane, dan ba ƙaramin kishi yaji ba, kuma yasan halin ta ko meye zata yi ƙoƙarin gaya maka gaskiya, ko ta maka daɗi ko akasin hakan'

Tana fitowa Gwaggo tace "Amarya kin ware kenan?"

Widad tace "eh Alhamdilillah"

"Masha Allah, haka nake son ji"

Hari tace "Wai meya same ki ne?"

Widad tace "Kaji Baba Harin nan, sekace kin damu dani, bayan ko gani kika yi zan mutu murna zaki yi, to ciwon yara nake bana tsofaffi ba dan haka base kinji ba"

Aikuwa a fusace Hari tace "karki ƙara cemin tsohuwa, ta ina nayi miki kama da tsohuwa? Da ƙuruciyata dudu shekarun nawa ba zasu gaza Ashirin da shida ba, amma kike kiramin tsufa"

Ai gaba ɗaya wanda ke tsakar gidan ba wanda be dariya ba, Widad tace "A'a kin manta a zanin goyo kike ma ƙarewar yarinta, harfa jikokine dake amma kice shekarar ki Ashirin da shida, shekarar ki biyar akamiki Aure kenan"

Hari tace "koma yane dai, niba tsohuwa bace ba ehee, dan jina nake garas kamar 'yar shekara goma sha shida"

Widad tayi dariya tace "dama zaki dinga gayune, za kiga yadda zaki koma yarinya sharaf, amma indai baki dena ƙazanta ba, to tabbas wataran za' a kalle ki ace shekararki sittin da 'yan kai"

Hari tayi kicin kicin da Fuska, dan Widad ta fara kaita bango, idan ta cigaba da biye mata to tabbas za suyi ba daɗi, dan haka tayiwa Widad banza.

Widad ta ƙarasa inda Hindu ke tsinke zogale ta zauna tace "Hindatu, ya ki keyi? bari in tayaki"

Hindu Ta gwadawa Widad yadda ake tsintar zogale, ta zauna suna yi tare.

Can Widad tace "Hindu, wai kuma idan kuna period bakwa amfani da pad ne? Se tsimma"

Hindu tace "meye kuma firiyios?"

Widad tace "A'a ba kije makaranta bane? Me yasa Common things idan na faɗa, seki ce baki sani ba?"

Hindu tace "bari Amarya wallahi muna son karatun nan, amma ba yadda muka iya ne, kinga inda muke zuwa makarantar furamarai can wani ƙauye ne, kusan ƙauyuka biyar duk ita muke zuwa, to guri ba kusa ba nisa kafin kaje duk anyi wani abu baka nan, lokacin damuna kuwa bama samun zuwa, sannan akayi ruwan Sama me ƙarfi ya kwashe kwanon da'aka rufa azuzuwa, ai kuwa akace mu dena zuwa se an gyara, dan haka tun aji huɗu furamarai nidai na dena zuwa har yanzu "

Widad tayi shiru, ita ko a tatsuniya bata taɓa jin wannan al'amarin ba, ace a Nigeria akwai 'yan ƙasa wanda basa samun ilimi, ina wakilansu? Meye amfanin shugabannin da suka zaɓa suka wakilta dan suyi musu aiki? Ace ƙauyuka huɗu su dogara da primary ɗaya, kuma shima se sun sha baƙar wahala kafin suje, dole abun ya fita daga ransu'

Widad tace "gaskiya banji daɗi ba Hindu, ai Ilimi shine mutum, tabbas da'a bakin wani naji cewa zanyi ƙarya ne labarine kawai"

Hindu tace "aikuwa gashi a zahiri kinji, shiyasa duk muka haƙura wasu suka kama talla har zuwa lokacin da mace zata samu miji tayi Aure, dama idan kana karatun wasu kallon ɗan iska suke maka, muka koma zuwa ta Allo ta Allonma gata nan dai nidai na samu nayi izu biyar na haddace itama munyi yawa, babu wata kulawa yadda yakamata, dan anan wajejenmu makarantar Allo ɗaya ce"

Widad ta jinjina kai tace" to sauran litattaafai fa, kamar Ahlari, fiqhu hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam, suma ana koya muku? "

Hindu tace" Taɓɗijan, Al'qur'ani kawai ake koya mana a makarantar Allo, kuma shima mun dena zuwa, se Baffanmu ne dai da yana koya mana Alhadisin Auwwalu, shima yace mana Babansa ne ya koya masa, kuma ma yanzu duk mun manta tunda shekarun da yawa "

Widad kawai tayi tagumi tana sauraren Hindu, tana jin kwamacalar da ko a Film bata taɓa ganin irinta ba, yanzu dama da irin wannan mutanen suna rayuwa a haka, amma ake samun mutanen da suke wawashe dukiyar al'umma, a 'ya' yan sanatoci akwai wanda tasan ana biya musu ku&in makaranta na secondary naira milyan uku, duk term miliyan ɗaya, iya 'yan tsirarin' ya'yansa, amma ga dubunnai zaune a gida babu arabi babu boko, irin wannan ne idan suka faɗa harkar ta'addanci basa imani sam.

Hindu ta kalli Widad tace "ya naga kinyi shiru ne?"

Widad tace "Mhmm bakomai"

Hindu tace "Yawwa, dan Allah meye Firiyas ɗin da kika ce?"

Widad tace "Period nace, ina nufin jinin Al'ada"

Hindu tace "Auho ai ban gane ba, seki cemin baƙon wata, ai mu da tsumma mukeyi, mu yayyanka tsumma semu dinga amfani dashi, duk wanda muka cire se mu wanke mu ninke"

Widad ta kalleta da sauri tace "ku wanke me?"

"tsimmar mana, idan ɗan kamfan mutum ɗaya ma haka ze haɗa duk ya wanke, ya ɗan jira ya bushe seya sake mayarwa"

Dafe kai Widad tayi, tayi shiru ta shiga duniyar tunani, ta tuna yadda take fantamawa a cikin kuɗi, babu abunda ta nema ta rasa a rayuwar ta, Kama daga Abinci, sutura abun hawa gurin kwana, har wasu kuɗi ne da ita na musamman wanda take kula da dabbobinta kawai, tayi kyautar mota, tayi kyautar gida ta bada kuɗi kamar aikin banza, ashe akwai bayin Allahn da sun fidda rai da samun wani jin daɗi.

Hindu tace "Amarya, Allah yasa ba wani abun na miki ba, naga kin ɓata rai?"

Widad tace "bakomai Hindu, mu cigaba da aikin kawai"

Widad bata iya tsinkar zogalen ba, dan haka wani yanayi wani kuma harda kararen jiki take zubawa, Hindu bata damu idan Widad ta zuba a haka se tabi tana gyarawa.

Hanne ce ta taho a fusace tasa hannu ta ɗauke robar da suke tara zogalen tace "Aikin banza, ke Hindu kin san ba abunda ta iya kawai kin ɗauki abu kin bata kinsa se ɓatawa mutane take, tana mayar mana da aiki baya kin zauna se surutan shirme ki keyi, da yanzu an wanke an ɗora amma duk ta ɓata mana"

Hindu tace "Haba Hanne, to ba a hankali zata iya ba, kuma ai tayani take tana yi ina gyarawa, meye a ciki dan munyi tare"

Tsaki Hanne Tayi, tai gaba da robar zogalen, Widad ko ɗaga kai ba tayi ba balle ta kalli Hanne, tayi shiru ba tace komai ba.

Cikin damuwa Hindu tace "dan Allah Amarya kiyi haƙuri, ni ban san meyasa take wannan abubuwan ba"

Widad tayi murmushi tace "Ni banyi fushi ba ai, bakomai"

Saleh ya ɗau waya ya kira Abbas, sedai har tayi ringing ta katse be ɗaga ba, tana katsewar ne Abbas ya biyo kiran, Saleh ya ɗaga tare da yin Sallama Abbas ya amsa, Saleh yace
"Malam Abbas, kayi gaba ko waiwaye baka yi, kana da labarin an sace amininka kuwa tare da 'yar gidan Daula?"

Abbas yace "ƙwarai kuwa na sani, dan nine ma na gayawa mahaifiyarsa"

Saleh yace "Wani tunani kayi akai kuwa?"

"wani tunani zanyi kuwa, maganinsa kenan ai, shegen shishshiginsa da rawar kai yaja masa, ni Allah ne ya dube ni, dani naso in maye gurbinsa da dani za'a ɗauke, Amma kuwa an karɓi files ɗin daga hannunsa?"

Shiru Saleh yayi sannan yace "basu karɓa ba tukuna, ni suke jira, har yanzu basu san cewar Yusuf ne jami'in tsaron ba, zancen da nake maka yanzu haka Yusuf sun tsere daga inda aka ɓoye su"

Abbas yace "haba dai, garin yaya akayi suka tsere? Kai Yusuf fa ba ƙaramin hatsabibi bane ba"

Saleh yace "babu wanda ya sani, kuma har suka gudu ba'a samu karɓar abun nan daga hannun yarinyar ba, yanzu maganar da nake maka, shi kansa Daulan an ɗauke shi a gadon Asibiti, babu wanda yasan inda yake"

"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, garin yaya, yanzu shikenan munyi biyu babu, nifa ba wanda yake tuntuɓata yanzu tunda akamin transfer"

Saleh yace "karka damu, ina son ka saurareni da kyau, duk abunda ake ciki zan dinga sanar da kai, karka kusakura wani daga cikin su yayi yunƙurin haɗa kai da kai, dan yanzu gaba ɗaya kawunansu a rarrabe yake, duk wanda ya tuntuɓeka koya tambayeka wani abu game da wanda aka bawa binciken nan kace baka sani ba"

Abbas yace "to aini basu sanni ba, kai suka sani me zesa su nemeni?"

"Abbas mutane ne masu wayo matuƙa, yanzu haka a manyanka na gurin aiki wani ze iya bugun cikinka ya tambayeka wani abu, karka kuskura ka gaya wani, wani abu akan harkar nan, na gaya maka kansu ya rarrabu, wasu zasu iya zamewa suyi harkar nan babu mu, bayan wahalar da mukayi "

Abbas yace " bakomai na fahimce ka, Insha Allah babu wanda zeji wata magana daga bakina, dama kai ka jawoni cikin harkar "

Saleh yace " Good nagode "

Sukayi Sallama, Saleh ya jinjina kai yanzu ya sake jinjinawa Widad, lallai bata da laifi naƙin yadda da mutane, ƙir ƙiri Abbas na jikin Yusuf ne, amma saboda kuɗi yake masa zagon ƙasa, tabbas mutum abun tsoro ne, kuma da alama Abbas Soko ne, dan haka yi masa wayo ba wani abu bane me wahala.

Saleh yana son sake komawa gurinsu Widad, dan haka yana ta ɗanyi musu siyayya.
Alhaji Musa ne ya kira shi a waya yace 'lallai yana son ganinsa a guest house ɗinsa'

Haka Saleh ya bar abunda yake yi ya tafi gidan Alhaji Musa.

Yaje ya tarar dashi a lambun dake gidan, suka gaisa Alhaji Musa yace "Saleh ina cikin damuwa fa"

"wace irin damuwa kuma ranka ya daɗe?"

"Na fuskanci Nurat tana ƙoƙarin fara yin shisshigi ga al'amuran Daula, gashi yanzu ina ɗari ɗari da su Haruna, ina tsoron Ayi Amfani da ita a cutar da ita koni, yanzu babban abunda ya sake bani mamaki be wuce yadda Daula yayi ɓatan dabo ba, ko kusa ko alama an rasa inda yake, zargina yana ƙara tabatta akan ana min maƙarƙashiya, kodai su Alhaji Haruna suke cuta ta suke al'amuran su suka ɗai, kokuma akwai wani a gefe daya ke harin abunda muke hari, ko kuma yasan siriinmu yake son temakawa Daula"

Saleh yayi ajiyar zuciya yace "banƙi ta taka ba, Amma ko waye wannan tabbas na jikin ku ne, amma abun da mamaki ace an nemi Daula ko sama ko ƙasa an rasa sekace wata takadda"

"Shine abunda ya ɗauremin kai ai, ni yanzu gefe zan koma in nemawa kaina mafita, idan abun nan ya samu shikenan, in be samu ba shikenan, suma har yanzu da suka gudu babu wanda ya sake jin ɗuriyarsu, dan haka ni inaga tunda babu wanda yasan inda Daula yake, zan fito takarar Senate ne kawai "

Da sauri Saleh ya kalle shi yace " Amma ta yaya kake tunanin mutane zasu yarda su zaɓeka? Bayan Daula ya riga ya ɓata siyasarka a idon duniya? "

Alhaji Musa yace " shiyasa nima na ƙuduri aniyar kota wane hali, sena Wulaƙanta Daula a idon duniya, sannan malamai zan shiga a rufemin bakin jama'a, akwai yarana da suke aiki a wasu daga kamfanunukan Daula, zamu haɗa kai dasu mu karkatar da wasu kuɗaɗe inyi amfani da su, niba kuɗin Daula ne sjka dameni ba, yadda zan Wulaƙanta shi in ɗaiɗaita shine ya dameni, amma ko yanzu na rage raɗaɗin dake zuciyata, kuma zan cigaba da bibiyarsa se naga babu inda ya rage wanda ze jingina yaji daɗi, sannan in dawo kan su Alhaji Munir"

Yadda Alhaji Musa ke maganar babu alamun tausayi ko imani a tare da shi, har zuciyarsa yake faɗar wannan maganganun.
Saleh ya ɓoye duk mamakinsa, ya dinga ziga Alhaji Musa, Alhaji Musa ya kawo kuɗi ya bawa Saleh, Saleh a ransa yace "ka bada kuɗin da zanyiwa maƙiyan ka siyayya, kuma nima zancigaba da bibiyarku, ɗaya bayan ɗaya sena ɗau fansar cin amanata da kuka yi, da saɓa Yarjejeniyar da muka yi daku"

Widad gaba ɗaya hirar da suka yi da Hindu ta tsaye mata a zuciya, ta tuna yadda haka siddan se ɗan kasuwa yayiwa ɗan siyasa kyauta motar miliyoyi, ko biliyoyin nairori, Amma al'ummar su suna tagayyara, da yunwa da rashin kyakkyawan mahalli.

Yusuf yaga gaba ɗaya Widad tayi wani iri, seta zauna tayi shiru tana tunani, dukda shima zuciyarsa ba daɗi, Amma sam baya son ganinta a damuwa dan haka yace  "Ran gimbiyata ya daɗe meke damunki ne?"

Jiki a sanyaye tace "Abubuwa da yawa"

Yusuf yace "Kamar me? Ko har yanzu fushin kike dani"?

Jiki a matukar sanyaye ta bashi labarin hirar da suka yi da Hindu, daga ƙarshe tace "tabbas ƙaddarar data sameni na zuwa ƙauyen nan, ishara ce Allah ya nunamin, na rayu cikin gata wanda nake ganin babu wani abu da zan iya nema in rasa a rayuwata, ranar da kace min akwai mutanen da Naira ɗari take gagararsu, gani nake kawai ka faɗane dan ka rainamin hankali saboda a lokacin, abun da ke cikin asusun bankina ya ninka ɗari sau ɗari, bani da wata damuwa ko matsala, Amma ace a rayuwa akwai tarin 'ya' ya mata da suke zaune ba ilimi? Akwai tarin mutanen da suke rayuwa da gurɓataccen ruwan sha? Akwai tarin yara manyan gobe da rayuwarsu ta lalace saboda rashin gurin samun ilimi, Yoseef yaran masu kuɗi na Almubazzaranci da dukiya, da yawanmu bamu san yadda aka tara kuɗin ba...  Kasa ƙarasawa tayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, wani irin ɓacin rai ke taso mata, yadda ake ɓarnar kuɗi gurin bukukuwan birthday dana Aure, da makamantan su.

Yusuf ya taso daga inda yake, yazo ya samu guri ya zauna kusa da ita yace "Widad baki ga komai ba, a yanzu haka a cikin ni'ima muke, a gidan megari muke a zaune, kuma gidansa da rufin Asiri, ya kike tunanin gidajen sauran talakawa da suke garin nan? Wanima abunda zasu cin ma babu, Widad talauci gaskiya ne, shiyasa Wulaƙanta mutane bashi da kyau "

Widad tace" tabbas wulaƙanta mutane bashi da kyau, nasan mutane dayawa sunamin kallon mace me izza da Wulaƙanta mutane, sedai...

Se kuma tayi shiru, Yusuf yace "sedai me?"

"Bakomai" ta bashi amsa tare da basar da zancen.

Da Asuba bayan Yusuf ya dawo daga sallar Asuba yazo ya tattara kwanuka zeje ya wanke, Widad tace  "ka bari zan wanke"

Yusuf yace "No ki huta kawai, bari in wanke ai ba yawa kwanukan"

Widad tace "ce maka akayi ban iya wanke wanken bane?"

"Ni na isa ince gimbiya bata iya wanke wanke ba?"

Widad tace "gashi nan kuwa ka faɗa"

"A'a ni ban faɗa ba, taso muje muyi tare"

Widad ta tashi tabi Yusuf suka je suka wanke kwanukan tare, ta tattare duk kwanukan wanke wanken da'akayi fatali dasu na Abincin dare a tsakar gidan, ta haɗesu a guri ɗaya, Yusuf yasa tsintsiya duk girman tsakar gidan yana sharewa, Widad ta dinga kallon ikon Allah, yadda Yusuf yake sarrafa tsintsiya kamar mace.

Widad tace "dan Allah dagaske kai ka ɗaine a gidanku?"

Yusuf yace "Eh nikaɗai ne Mamana ta haifa, ni nake mata aikin gida, shara, wanke_wanke hadda girki duk ta koyamin ni nake yi, idan ta tafi unguwa kafin ta dawo nayi komai"

Widad tace "shiyasa ka iya aiki sosai, nima nasan da tare na girma da Ammi na da duk na iya aiki, da baza'a dinga kallon ban iya komaiba"

Yusuf yazo kusa da ita ya tsaya, ya kalleta yace "karki damu gimbiyata, Insha Allah muna tare zaki iya komai kafin mu koma gida"

Widad ta kalle shi tace "dagaske har girki zaka koyamin? Nafa iya girki amma ba sosai ba"

Hannu yasa ya ɗago haɓarta yace "zaki iya komai insha Allah, duk zan koya miki, amma bana son taurin kai, dan nasan halinki"

"Nice me taurin kai?"

Yusuf yace "eh kina dashi amma kaɗan"

Murmushi Widad tayi tace "Ni dai in zaka koyamin zanyi duk abunda kake so"

Yusuf yace "dagaske?"

Widad ta jinjina masa kai, ya matso daf da ita yace "to shikenan, Yimin kiss a goshina ma ba'a baki ba, se in koya miki kunna risho yau"

Tureshi tayi tace "Baza'ai wannan ɗinba"

Matseta yayi a jikin bishiyar ya riƙota, cikin sigar magiya yace "please Gimbiyata, ko sau ɗaya ki nuna kin damu dani please"

Cikin tsiwa tace "to Jaririne kai? Ko goya ka zanyi?"

Kwantar da kansa yayi a kafaɗarta yace "to goyanin mana, ko daga nan zuwa ɗakine"

"Eh ba shakka, ba kunya wai in goya ka, sakeni ko in cijeka yanzun nan"

Hanne ce ta fito daga ɗakinsu, tana fitowa idonta ya sauka akan Yusuf da Widad dake tsaye a jikin bishiyar ceɗiya dake tsakar gidan, kamar zasu shige jikin juna.

Da ƙyar ta haɗiye wani irin mugun yawu a wuyan ta, ta koma cikin ɗakinsu tana fesar da numfashin baƙin ciki.

Hindu ce ta Kalle ta tace "Hanne lafiya kuwa?"

Hanne tace "wallahi Hindu na tsani matar Yusuf, ji nake kamar in shaƙeta"

Cike da mamaki Hindu ta kalle ta tace "kamar yaya kin tsane ta?"

Hanne tace "Hindu dan Allah kina ganin Yusuf ze iya Aurena?"

Wani mugun kallo Hindu tayi mata tace "Anya kina kallon kanki a mudubi kuwa? Kina ganin mace jawur, kalle ki kice kina son mijinta, matar nan fa tana miki kawaici akan Mijinta, kiyi ta mata wulaƙanci amma tana ƙyale ki, karki kuskura Gwaggo taji wannan maganar da kike"

Hanne tace "ba zaki gane ba Hindu, wallahi Yusuf ɗin nan yana da kirki sosai, ita ba abunda ta iya se rashin kunya, gata bata da tarbiyya sam gata a wani taɓare, ga tsbar iskanci da rainin hankali, komai se tace bata sani ba"

Hindu tace "A'a wallahi tana da kirki, niba abunda tamin da zan zageta, kije kiyi ke kaɗai, Allah ya yaye miki wahala, dan tabbas yana da wannan matar babu abunda ze dake"

Yau kam Widad ta ɗan rage yiwa Widad rashin kunya, dan tare suka ci Abinci saboda tana son ya dinga koya mata aikin gida, dan tana jin zafin gorin da'ake mata, wai bata iya komai ba.

Bayan sallar la'asar Widad ta fito daga ɗakinsu, dama gyara ɗakin baya mata wahala da gyara gado duk wannan ta iya.

Hari ta hanga a inuwar bishiya tana saƙa mafici, Widad ta ɗakko kujera ta zauna a kusa da ita tace  "Uwata ta kaina"

Hari ta harareta tace "Allah ya kiyaye in haifi 'ya irin ki, na haifi fitinanniya kamarki ai se ince ko sa kamun hannu akayi"

Murmushi Widad tayi tace "ba wannan ba, ɗan koyamin wannan abun da kike yi mana, idan na iya se in dinga ta yaki"

"Lallai nasan ba iyawa zakiyi ba"

Widad tace "Allah zan iya"

Hari tace "Keɗin ce zaki iya, taɓ"

Widad tace "ni zaki wulaƙanta dan zaki koyamin abu? Shikenan"

Hansai tace "Amarya ba wahala, nima na iya zan koya miki"

Widad tace "Yawwa ummu Sani, thank you very much, May Allah subhanahu wata'ala bless and unite your Family"

Hari tace "kekam wudas akwaiki da tsirfa, meye hakan kuma kika faɗa? Ke ba zaki iya magana ba sekinyi yaren Yahudawa, kiyi ta zagin mutane"

Widad tace "aini kona rasa abun zagi, bazan zageki ba"

Hindu tace "Nidai dan Allah amarya ki koyamin turanci, ina son inga na iya"

Widad tace "Shikenan, zan koya miki insha Allah, amma nima zaki dinga koyamin abunda ban iya ba"

Hindu tace "duk abunda kika ce zan koya miki"

Gwaggo na gefe tana jinsu, tana murmushi, sam Widad bata da girman kai idan bata iya abuba, zata yi ta magiya a koya mata.

Da Yamma aka kawo manyan Ayaba daga gonar megari, aka raba aka bawa kowa, Widad se murna take dan tana son Ayaba, ajiyewa taje tayi a ɗaki tace, se Yusuf yazo zasu raba.

Yau Yusuf se gefin magariba ya dawo gidan, ya gaji sosai.
Tunda ya samu ya watsa ruwa ya dawo ɗaki ya kwanta, salla ma a gida yayi.

Widad tace "Yoseef ga Banana, an bamu daga gonar megari aka cirota, nace in ka dawo semu raba dan idan na fara ci, bazan iya rage maka ba"

Murmushi yayi yace "bani guda ɗaya kawai ta isa, kici Abunki"

Ta ɗan ɓata fuska tace "saboda me bakaci? In ajiye maka abu kace ba zaka ci ba"

"i don't have appetite, that's why"

Ta kalle shi tace "kamar yaya?"

Rungume ta yayi a jikinsa, ya kwantar da kansa a kafaɗarta yayi shiru.

Widad ta kalle shi da sauri tace "Subhanallah, ai baka da lafiya jikinka yayi zafi sosai fa"

Yusuf yace "karki damu zan warke insha Allah"

Yana nan rungume da ita, yana ta juya kansa a jikin ta, tana jin yadda jikinsa yake tsuma jikinsa na ƙara ɗaukar zafi.

Widad cike da damuwa tace "Yoseef jikinka zafi yake sake ɗauka fa"

Kasa magana yayi, sosai jikinsa yake rawa, da sauri ta miƙe ta ɗakko bargo ta rufa masa.

Haƙoransa se karkarwa sukeyi, ta ɗebo ruwa ta duba kayan ta, ta ɗakko wata vest ɗinta, ta shiga shafa masa ruwa a jikinsa, amma kamar tana ƙara rura masa wuta, jifa tayi da abunda take jiƙa masa jikin ta rungume shi ta fashe da kuka.

Share, share and share please 🙏 🙏

(insha Allah ranar 20th ga wata zan fara posting ɗin book 2&3, befi saura page biyu ba in kammala book 1, nagode ga wanda suka fahimceni, wanda suka zageni ma nagode, wanda suka shirya siya zasu iya tuntuɓata ta wannan lambar 07063065680 nagode ƙwarai dagaske, a nunamin ƙauna ta hanyar siyan littafin akan farashi me rahusa, Akwai garaɓasa ga mutum biyar ɗin farko da suka fara siya, cakwakiya da warwara suna book 2&3 don't missed it guys sena jiku"

Domin gyara sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680

                      _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED  (BANYI EDITING BA)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 42_43

Sosai Widad ke rusa kuka, Yusuf kasa magana yayi sedai ya ƙanƙameta a jikimsa, yana dukan bayanta da sigar rarrashi.

Can ta miƙe cikin hanzari ta fito waje, tana ta goge Hawaye ta samu Gwaggo tace "Mama Yoseef bashi da lafiya"

A gigice Gwaggo tace "Subhanallah, meya sameshi?"

Maimakon Widad tayi magana seta fashe da kuka, Hanne da take wanke wanke take ta dire kwanukan ta miƙe tsaye.

Gwaggo tace "Yi shiru, muje muga jikin nasa"

Hansai ma da Hari gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi, ɗaki gwaggo tabi Widad ta tarar da Yusuf yana ta karkarwa a cikin bargo.

Gwaggo tace "Subhanallah, sannu Yusufa Allah ya baka lafiya"

Be iya magana ba se jinjina mata kai da yayi, Hari tace "Yaya meya abunyi yanzu, ga  Malam baya nan yaje taronsu na masu sarauta"

Hansai tace "ina sauran saiwoyin nan, a jiƙa a bashi mana, kan malam yazo asan abunda yakamata ayi"

Widad ta koma kusa da Yusuf, tana ci gaba da share Hawaye, Hansai tace "Kidena kuka in Allah ya yadda ze samu lafiya"

Hanne ce ta shigo ɗakin itama, ta leƙa taga yadda Yusuf ke rawar jiki, gaba ɗaya se taji jikin ta yayi sanyi, a ranta tace 'dama wannan kinibabbiyar zazzaɓim ya kama'

Suka dinga rarrashin Widad, yayin da Yusuf ko iya ɗaga kansa ba yayi, Hansai ce ta kawo wasu jiƙe jiƙe wai a bawa Yusuf, Widad ta kalli kwanon ta girgiza kai, cikin kuka tace  "A'a wannan abubuwan suna da hatsari ga lafiya, nidai a kai shi Asibiti kawai"

Hari tace "Asibiti, ai kuwa ya mutu ba'a jeba, dan daga nan kafin aje Asibiti har mutum ya mutu akai gawarsa ba'a isa ba"

Sake rushewa Widad tayi da kuka tace "In Allah ya yadda baze mutu ba, semun koma gida tare, dan Allah Yoseef kaji sauƙi"

Gwaggo tace  "Hari kina da matsala wallahi, wace irin magana ce haka ba tsari, kalli yadda kika sake tayar mata da hankali fa"

Hari tace "Wallahi Yaya ni bada wani abu na faɗa ba, misali dai na bata, amma Wudas kiyi haƙuri, Insha Allah ze warke amma Asibiti kam kafin aje shi sedai idan amalanke za'a samo a ɗorashi, a fita can wajen gari sannan...

Hansai tace" haba Hari, ana rarrashin ta kina ƙara Sakata kuka, Amarya karki damu insha Allah za'a kai shi Asibiti bari Malam yazo "

Widad ta riƙe hannun Yusuf tana ci gaba da kuka, Hanne tace " Sannu Allah ya baka lafiya "

Har magariba sannan megari ya dawo, ya tarar da zancen rashin lafiyar Yusuf, megari yace  " me aka bashi na magani? "

Hansai tace " Na jiƙo tazargade nace a bashi, matarsa tace baza'a bashi ba sedai akai shi Asibiti"

Megari yace "Kin san mutan birni, basu fiye amfani da irin wannan magunguna namu ba, Amma yadda za'a kai Yusuf Asibiti nake ji, kafin Aje ya ƙara galabaita, dan miƙaƙiyar tafiya ce ta gaske"

Widad tace "Yanzu duk garin nan babu Asibiti, ko chemist babu?"

Hindu tace "kamis ɗayane a garin nan, shima a cikin kasuwar yamma da gari yaje, ba'a buɗeshi se ranar kasuwa"

Dafe kai Widad tayi tana faɗin "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wane irin abune haka, gari kamar wannan me ɗauke da al'umma suna rayuwa a ciki, ace babu gurin shan magani, Yasalam sannu Yoseef Allah ya baka lafiya"

Bece komai ba, se riƙe hannayenta da yayi, da hannu yayi mata nuni da zeyi alwala, Gwaggo ta bada ruwan ɗumi, Widad ta sirka masa, se a ɗaki yayi alwalar dan ko tsakar gida baya iya fita, saboda azabar sanyin da yake ji.

A zaune Yusuf yayi salla, Widad idanunta har sunyi jawur saboda kukan da tayi, ta kalle shi tace "me zaka ci? Kaga tun safe baka ci Abinci ba"

Girgiza mata kai yayi, alamar baya son komai "

Ya nemi guri ze sake kwanciya, Widad tace " kwanciyar nan zata ƙara kashe maka jikine, ka bari gobe in Allah ya kaimu duk yadda za'ayi za'a san yadda za'a kaika Asibiti kaji, sannu Allah ya baka lafiya "

Ta ƙarasa maganar idonta fal hawaye.

Murmushi Yusuf yayi, ya kai hannunsa dake rawa fuskarta ya goge mata hawaye tare da girgiza mata kai, alamar ta dena kuka.

Haka Widad ta raba dare ba tare da tayi bacci ba, data motsa sedai tayi ta shafa masa ruwa, amma jikinsa kamar wuta.

Tun tana yi da ƙarfinta, har bacci ya mamaye idonta ta kife a gurin tana bacci, a haka ya janyo ta jikinsa, yana kaɗe mata sauro yayin da ya kasa bacci saboda azabar ciwon gaɓoɓi da zafin zazzabi.

Da Asuba Widad ta farka, tana buɗe ido tace "Yoseef"

Da Mm ya amsa mata.

"baka yi bacci bane?"

"Nayi ya faɗa a hankali"

"ya jikin naka?"

"Naji sauƙi, samomin ruwan Alwala"

Ta miƙe ta fita waje, ta kawo masa ruwa yayi alwala yayi sallar Asuba.

Gwaggo tayo kunu ta aikowa da Yusuf, kasa sha yayi saboda yana jin jiki, amma saboda kukan da Widad take, ya karɓa ya sha kaɗan, haka nan ya amayar da shi gaba ɗaya, nan fa abun duniya ya ishi Widad, ta kasa cin Abinci se kuka.

Megari ya tashi ɗansa, yace "yaje can gaban su, ya aro babur azo a tafi da Yusuf Asibiti"

Har wajen ƙarfe sha ɗaya Widad tana tare da Yusuf, ko tsakar gidan ta kasa fita, ta kama yatsunsa tana ja masa a hankali kamar yadda yake mata, sam taƙi cin komai.

Wajen sha biyu na rana Saleh yazo gidan, zuwan Saleh ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, Megari yace "Alhamdilillah, kazo a dai dai, dama Yusuf yana kwance babu lafiya na aika azo ds babur a kai shi Asibiti, tun jiya ko magana baya iyayi"

A gigice Saleh ya tafi ɗakin su Widad,  Hindu da Hanne dasu Gwaggo suka bishi dan a yanke shawarar ƙarshe game da rashin lafiyar nasa, Saleh yayi Sallama Widad ta amsa, ya shiga ɗakin ya tarar da Yusuf ya ɗora kansa akan cinyar Widad, idanunta sunyi ja har sun fara kumbura.

Seda Saleh ya ɗanyi turus dan tabattar da abunda yake gani, wanda ko a wasan kwaikwayo akace Widad zata yi hakan baze yadda ba.

Ya ƙarasa cikin ɗakin, ya kalli Widad yace "meyasa me shi haka?"

Tsuke Fuska tayi sannan tace "zazzabi yake"

Ya kalli Yusuf yace "Sannu Yusuf, bari inje wannan sedai ko mota a samu, ba zaka iya hawan babur ba, se inzo akaika Asibiti"

Yusuf be iya cewa komai ba, se jinjina masa kai da yayi, tun a hannun wanda suka sace su Widad ta jinjinawa jarumta irin ta Yusuf, tunda harta kai ga baya magana to tabbas ta tabbatar yana jin jiki ƙwarai.

Saleh yace "Ranki ya daɗe bari inje a duba motar ko, se a zo a tafi dashi"

Cikin isa da take nunawa ma'aikatanta tace "ina fatan kaga halin da yake ciki, dan haka bana buƙatar ɓata lokaci, duk inda abun hawa yake a nemo azo a kai shi Asibiti, kar ya sake galabaita"

Mamaki ne ya kama su, Yadda Widad take wa Saleh magana cikin isa da gadara, dukda irin taimakon da yayi musu, ga kuma tarin tazarar shekaru da ya bata, amma take masa wannan isar haka, se suka ga ta canza kamar ba Widad ɗin dake magana sanyi sanyi ba.

Saleh ya ɗago ya ɗan ƙurawa Widad ido na wani ɗan lokaci.

Cikin tsawa tace "Kamar na gaya maka bana son ɓata lokaci, ka tsaya kana kallona, he's condition is getting worse, ko nawa za'a kashe ayi a nema masa lafiya" tai maganar tana wani sauke wahalallen numfashi.

Cikin harshen turanci Saleh yace "You are under my care now, why are you still shouting at me like this, so you are still rude up to now"

"My name remains Widad Nasir, Nothing will make me change, No matter what you did to help me, my policies remains constant, nothing has change"

Cikin rawar sanyi Yusuf ya shiga girgizawa Widad kai alamar tayi shiru.

Sudai mutan gida se binsu su kayi da ido.

Hanne ce taja wani uban tsaki tace "Aikin banza, ace mutum baya ganin girman kowa, se tsabar wulaƙanci da rashin ta ido"

Da sauri Saleh yace "Ke dawa kike? Idan kika kuma gangancin yin wannan mummunan furicin akanta duk abunda ya biyo baya ke kika siya, ko dan kin ganta zaune a gidanku, kin sam wace ita?"

Gwaggo tace "ayi haƙuri dai, naji tsayuwar Babur a waje, ina ga Ila ne ya dawo, maza jeka ku samo akori kura a kai shi Asibiti"

Haka akayi, Saleh yaje suka hau babur suka tafi nemo akori kura.

Sosai Fahad ya fara missing ɗin Ramlah, dan ba ƙaramin hutawa yake da ita ba, itama a ɓangarenta tana missing ɗinsa, amma tana so ta tabattar da idan dagaske yana sonta, kamar yadda Amal ta goranta mata.

Fahad ya ɗau waya ya kira Ramlah, tana ganin kiransa babu ko jan aji ta ɗauka da rawar jiki
"Hello Baby, shine kika watsar dani ko?"

"ba watsar da kai nayi ba, kaine ka watsar dani ka kasa Yimin abunda na tambayeka"

"Ramlah ki gane, baƙi nayi ba fa, kin san halin Daddy, ko zancen baya so na ɗakko masa, yaƙi saurarata sam gashi bani da lafiya se tunaninki nake, kuma nasan damuwa ce tamin yawa"

"dan Allah dagaske baka da lafiya? Ai ban sani ba, ohhh Sorry please i understand you, nasan kana son za kayi iya ƙoƙarin ka, bakomai hakanma nagode sosai my love"

Yayi ajiyar zuciya yace "Never mind baby, yanzu ya za'ayi ne? Inzo mu ɗan fitane yau ɗin?"

"Ni gaskiya a'a"

Ya ƙara marairaicewa yace "please na, ko so kike ace kizo ga gawata?"

"No bazata kaimu ga haka ba, kazo anjima mu fita, kasan bana son dsmuwarka my one"

"wow that's my only Ramlah, na ɗauka nikaɗai nake sonki na damu dake ai, shikenan dan Allah ki ƙure a daka, kiyi kwalliyar nan wadda ke narkamin zuciya"

"shikenan karka damu, sekazo"

Sukayi Sallama Fahad yace "akanme zanso a sako wani Anwar, yazo ya hanani rawar gaban hantsi, ai gara ayi ta tsare shi a can kowa ma ya huta.

Wasa2 labari ya karaɗe gari, an nemi Daula an rasa, abu kamar wasa kusan sati biyu amma babu ko wanda yaji ɗuriyarsa, Alhaji Munir ne da Alhaji Haruna zaune a office, sunyi jugum jugum.

Alhaji Munir yace "Nifa gaba ɗaya abubuwan nan suna nema su kwaɓe, wai kamar almara har yanzu babu ɗuriyar Daula, babu ta wannan shegiyar 'yar tasa me baƙin taurin kai kamar ubanta, kuma gashi an ɗaga taron kasuwanci komai ya watse, nifa gaba ɗaya na fara karaya"

Alhaji Haruna yace "wace irin karaya kuma? Ai ba gudu ba ja da baya a wannan harkar, mun ɓata shekaru da dama akan wannan sabgar, kawai kuma semu sare yanzu, a'a baze yuwu ba, ni yanzu na fara tunanin anya ba wanine yake mana maƙarƙashiya ba?"

"Hmm bari kawai, ni kaina nayi tunanin hakan, an tuhumi doctor Sufyan har yanzu yace be san komai akan ɓatan Daula ba, ga ɗan gidan Hajiya Halima shima da yake kula da Daula, an tsare shi amma yace besan komai ba, wannan wane irin lamarine haka?"

Alhaji Haruna yace " Wani abun haushin ma, Halima se shiga take tana fita a sakar mata ɗanta, tana neman ta tona mana Asiri "

Alhaji Munir yace " Ai duk wata sabga daza'a saka mata a ciki, to tabbas za'a sha takaici, tun farko nace kar a saka matar nan amma aka ƙi bin shawarata, gashi nan komai se kwaɓewa yake"

"Haba Munir, kai badan da temakonta ba ai da wata nasarar bamu sameta ba, ta bamu gudunmuwa sosai, sedai yanzu tana neman ta ɓata rawarta da tsalle"

Alhaji Munir yace "Kai ba wannan bama, kasan se siyar da manyan motocin Daula, tana ta holansuba ɓoye tana siyarwa, da wasu ƙananan kadarorinsa a ɓoye"

Zaro ido Alhaji Haruna yayi yace "bangane ba, kai waye ya gaya maka?"

"Al'amarin duniya baya ɓuya fa, nima labari naji kuma kana ganin mun fita wayo ne, kar take kallonmu matar nan mugun wayo ne da ita fa, tsohuwar  'yar duniya ce"

Shiru Alhaji Haruna yayi yace "Amma wannan ta cika muguwa, rabu da ita in tasan wata ai bata san wata ba, zamuyi magana da Musa, su tattauna da Bukar, muga yadda zamuyi maganinta"

Se wajen la' asar sannan Saleh suka zo da Mota, sedai akori kuran ta ɗanfi wadda aka kawo su ƙauyen a ciki, da ƙyar Yusuf ya miƙe Saleh ya riƙe shi, yana takawa a hankali.

Widad ta zuro Hijjabi tace binsu zata yi, Aikuwa Seleh yace "A'a base kinje ba, nida Ila da Megari za muje mu kai shi"

Ai nan da nan tasha gabansu ta tsaya ta kalli Seleh tace "wai kai a tunaninka har nayi yaddar da zaka ɗauke shi ka tafi da shi, bayan ban san inda zaka kai shi ba, baze yuwu ba duk inda za'aje sedai aje dani"

Saleh yace "look, idan ina da nufin cutar daku, to da yanzu ba wannan zancen ake ba, ni bani da niyyar cutar ku, Asibiti zamu kai shi"

Megari yace "ki kwantar da hankalinki, Insha Allah babu abunda ze sameshi"

Kunyar Megari da Gwaggo ne yasa Widad fasa binsu, ta kalli Yusuf tace "Allah ya baka lafiya Yoseef, Allah ya kula da kai kamar yadda kake kula dani"

Ɗagowa Yusuf yayi ya kalle ta, ya sakar mata murmushi suka yi waje.

Wajen ƙarfe Biyar na yamma, Anwar yazo gidansu Ramlah, ya kirata a waya ta fifo, har tazo falo suka haɗu da Amal, Amal ta kalli Ramlah tace "se ina?"

"zan fita ne" Ramlah ta bata amsa.

Amal ta jinjina kai tace "A dai dinga kula Ramlah, a dinga abunda ƙuda zebi, wannan gabtalin da kike ba yau ba gobe, ze ɓata miki suna ne"

"Ke dalla sauraramin, bana son shisshigi na gaya miki, ina ruwanki dsni ne? Kinfa fara isata na gaya miki"

Ta sa kai ta fice daga falon cike ɓacin rai.

Kai tsaye taje ta shige motar Fahad suka fita, Nura yace  "Allah wadaran wannan shegiyar Ramlah me kama da balbela"

Isa yace "bari, iskancin da take mana a gidan nan ko Gimbiyar Daula ba tayi shiba, kullum suna titi ita da wannan me kai kamar tumatir ɗin"

Murtalah yace "Ai har gara ma Amal da Anwar, Amma da matar gidan nan da Ramlah Allah ya tsine musu Albarka"

Isa yace "Ameen ya Allah, kalli duk manyan motocin dake gidan nan tabi ta siyar, kamar dasu tazo se facaka suke da kuɗi, Kai ta wani fannin yanzu bana ganin laifin 'yar masu gida da take musu rashin mutunci"

Murtalah yace "dama Hausawa sunce,' kada Allah ya kawo ranar yabo' duk rashin mutuncin da take Yusuf se yayi ta kare ta, se yanzu nake ganin gaskiyar zancensa da yace bata yiwa mutum wulaƙanci seya yi mata laifi"

Nura yace "Mhmm Ai kawai Allah yasaka mana, amma gidan nan ana abubuwa sedai fatan Allah ya kyauta"

Duk inda Hajiya Sarah tasan zata buga ta buga, amma anƙi sakin Anwar, gaba ɗaya ta rasa inda zata tsoma ranta, Anbi an toshe duk wata hanya da zata saka a samu belin Anwar.

Yanzu ma haka ta dawo fakan fakan kamar korarriya, a mugun guje ta shigo da mota gidan.

Tana shiga ta fara kiran "Ramlah! Ramlah! Ke Amal kuna inane?"

Amal ta fito tace "Mummy Ramlah fa bata nan"

"gidan ubanwa taje?"

Amal tace "sun fita ita da Fahad"

"zanci ubanta ita da Fahad ɗin kuwa, ai tunda ubansa ya watsa min ƙasa a ido, to tabbas zan masa rashin mutunci, zan nuna masa wacece Halima idan ya manta"

Amal tace "Mummy ɗan uwan naki?"

"Eh shi ɗin, tunda bani da kima a idon sa, nima zan nuna masa bashi da ita a nawa idon"

Amal tace "Mummy a bi dai komai a hankali, kar azo ayi aika aika"

Hajiya Halima tace "dalla rabu dani, ze gane ni ya taɓa, ai ɗa befi ɗa ba, yasani yaron nan besan inda aka kaai mutumin nan ba, amma se cemin yake wai in ƙyale doka tayi aikinta, na zagi dokar shi doka nawa yayi fatali da a rayuwar sa, zega tsiya"

Tai part ɗinta tana cigaba da banbami, kamar wadda ke shirin Zarewa.

Saleh da Yusuf da ɗan megari suka tafi kai Yusuf Asibiti, aka bar Widad da mutan gida tana ta faman yi musu kuka.

Gwaggo da Hindu ne suka iya zaman rarrashin Widad.

Hari tace wai ke Wudas daga miji na zazzaɓi seki zauna kita mana kuka, memakon ki masa Addu'a "

Ko kallon Hari ba tayi ba, ta miƙe ta tafi ɗakinsu tayi kwanciyarta tana cigaba da kuka.

Nurat suka dinga communicatinga da cousin ɗinta akan yadda za'ayi belin Anwar.
Yanzu ma tana kwance akan gadonta hannunta ɗauke da waya, tace" Brother ya ake ciki ne? Yakamata a gaggauta fitar da Anwar bashi da laifin komai fa"

"Nurat, kince bakyason asan muna ƙoƙarin belinsa, dan haka nake taka tsantsan, sedai abunda na gano shine tsare Anwar da akayi da manufa akayi shi, idan muka matsa tabbas za'a gano ke kikasa ayi belinamsa, tunda an san alaƙar dake tsakanin mu"

Cikin karaya Nurat tace "yanzu Brother babu abunda zaka iyayimin, Anwar be cancanci ya zauna a gurin nan ba"

Yace  "Nurat, lawyan mahaifiyarsa ma yana ta ƙoƙari, amma har yanzu sun hana belinshi bansan meye abunyi ba, amma meyasa kika damu ya fita bayan kin san munin Alaƙar dake tsakanin mahaifinki da Daula?"

"Brother, idan akazo batun gaskiya da adalci ba'a kawo maganar alaƙa, an cutar da Anwar fiye da yadda kake zato, shikaɗai ne akan lamarin rashin lafiyar Alhaji Nasir, amma kalli abunda ya biyo baya, kodai an masa hakane dan a tozarta shi, ko kuma wanda ya sace shine yake son wanke kansa ta hanyar sawa a kama Anwar "

Barrister yace "Amma abun da mamaki ta yaya za'a iya sace mutum Attajiri kamar wannan a gadon Asibiti, kuma babu wani ƙwaƙwaran bayani, abun da mamaki fa"

Nurat tace "Brother, dan Allah idan kana da dama ina son kazo in ganka, ina son mu tattauna wani zance da kai dan Allah"

Barrister yace  "Fara gayamin mana"

"A'a Brother, nidai so nake ina ganka, akwai magana ne a bakina"

"shikenan karki damu, Insha Allah idan ma samu lokaci zanzo insha Allah"

"Yawwa brother nagode sosai"

Ta kashe wayarta ta ajiye, shiru tayi abubuwa da dama suna damun zuciyarta, har yanzu bata ji alamar labarin inda su Yusuf suke ba, har yanzu bata sake jin wani magana game dasu ba, ta shiga tuna hirar da suka yi da Amal akan alaƙar Widad da Yusuf, ji tayi tana gumi dukda sanyin AC dake ɗakin nata, amma ta shiga haɗa gumi, miƙewa tayi ta tafi toilet da niyyar ta watsa ruwa ta rage damuwa.

Har bayan magariba babu labarin dawowar su Yusuf, nan fa Widad ta sake gigicewa, ta shiga sintir a gidan nan tana   "Allah ka duba Yoseef ka bashi lafiya, Allah ka bashi lafiya ba danni ba"

Gaba ɗaya tausayin ta ya hana Gwaggo nutsuwa, se aikin rarrashin Widad take, ita kuwa Hari harta ƙule saboda ganin abun na Widad take kama harda shagwaɓa dan taga ana lallaɓata, kawai dan mutum yana zazzaɓi ta cikawa mutane gida da ihu.

Dukda Hanne itama tana cikin damuwar rashin lafiyar Yusuf, amma ji take kamar ta make Widad, gaba ɗaya ta hana mutane sukuni, se wani kuka take se kace wadda akace ya mutu.

Gwaggo ta zauna tasa Widad a gaba taci Abinci, amma ta gagara ci, Gwaggo tace "Amarya kiyi haƙuri, kici Abinci kinji, ki cigaba dayi masa Addu'a"

Cikin kuka Widad tace "Mama idan wani abu ya samu Yoseef sanadina ne, ba danni ba ba dan yasanni ba da duk baze shiga wannan halin ba"

Gwaggo tace "A'a kiyi haƙuri, Allah ne ya ɗora masa, kuma ze yaye masa"

Har dare basu dawo ba, ba Saleh ba dalilinsa, hankalin Widad ya sake tashi, yanzu take sake ganin Amfanin Yusuf a tare da ita, dare yayi tace bazata iya zama a ɗakin ita kaɗai ba, Gwaggo tace taje ɗakinta ta kwana, amma Widad fafur taƙi, ƙarshe Hindu ce tabi Widad ɗakinsu ta tayata kwana.


Har yanzu hankalin Umman Yusuf yaƙi kwanciya, rashin Yusuf a tare da ita ba ƙaramin abu bane a gurinta, sam rayuwa kawai take ba dan tana jin daɗin rayuwar ba, Yusuf shine ɗanta ɗaya tilo, yau a sanadin aikinsa yayi nesa da ita, bata san inda yake ba, gashi a hukumance babu wanda yace mata komai, se Suleiman da yake sintirin zuwa ganinta yana kwantar mata da hankali.

Wataran a ɗakin Yusuf ɗin take kwana, taita kuka gwanin ban tausayi, tana matuƙar ɗan nata rabuwarta da shi ji take kamar ta rasa komai na rayuwarta.

Bacci kam Widad ba tayi shi ba, Hindu tun tana rarrashin ta harta gaji tayi bacci, Widad kam kwana tayi tana Addu'a, Allah ya bawa Yusuf lafiya.

Se washegari sannan Ila da suka tafi kai Yusuf Asibiti tare yazo gidan, Widad na ganin shi a gigice tace "Ina Yoseef ɗin? Yana ina?"

Ila yace "ki kwantar da hankalinki, kwantar dashi akai, can cikin garin Bauchi muka kai shi, ya ɗan samu sauƙi Amma yaji jiki fa, kafin muje har Suma ya dinga yi a mota, amma ya farfaɗo, baza'a sallameshi yau ba"

Hanne dake gefe tace  "Alhamdilillah"
Gaba ɗaya suka juya suna kallonta, banda Widad da tace "dan Allah dagaske kake ya tashi?"

Ila yace  "kwarankwatsa dagaske nake, dan yace in gaidaki, Saleh na baro a gurinsa"

Se a lokacin Widad ta ɗanji hankalin ta ya ɗan kwanta, harta samu tayi wanka, megari ma yayi ta mata Nasiha akan wannan kukan data dingayi.

Ramla kam a kusan buge ta dawo gidan nan, Hajiya Halima bata ga dawowarta ba, Amal ce taga wucewarta kamar tana tangaɗi, binta tayi da sauri ɗakinta, ta tarar tayi cilli da jakarta da takalmanta ta zube akan carfet tana bacci, Amal tace

"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Ramla me zan gani haka, meya same ki?"

Ramla kasa magana tayi se ɗaga hannu da take, cikin maye tace "ke.. Keee.. Nace ina ruwank.... Ki dani neeeee.. Ki fita nace"

"Ramla, shaye2 kika fara ne?"

Shiru Ramla tayi mata, ta cigaba da baccinta.

Gaba ɗaya hantar cikin Amal ya kaɗa, tabbas Ramla shaye2 take, dan maye take yi, ta tuna yadda take bacci ba ƙaƙƙautawa, da tayi kamar taje ta gayawa mahaifiyarsu, se kuma ta tuna dama a ƙule take da Fahad da mahaifinsa, muddin ta gayamata za'ayi ɓatacciya ne.

Kwanan Yusuf uku a Asibiti, gaba ɗaya Widad ta rame, idanunta duk sun kumbura, jama'ar ƙauyen duk sun san rashin lafiyar Yusuf, dan shike jansu Sallar Asuba da magariba zuwa isha'iyanzu, kuma ga karatu da yake koya musu suna jin daɗinsa.

Widad ta zuba ido, taga ta ina Za'a dawo mata da Yusuf, dan Ila ya gaya musu ranar za'a sallameshi.

Gwaggo tasa akayi Abinci, aka dama Fura saboda Yusuf.

Ila ya shigo gidan da Sallama yace "ku kintsa, mun dawo maƙota sun baibaye mota zasu shigo da shi"

Da ƙyar Gwaggo ta janye Widad zuwa ɗakinta, saboda maza zasu shigo, dukda damuwar da Widad ke ciki be hana Widad kallon Ɗakin Gwaggo ba, yasha jeren samiru da fanteku, ga gadonta na ƙarfe me rumfa da mudubi, ginin tsurar ƙasane ɗakin amma yayiwa Widad kyau nesa ba kusa ba, ga ƙwarya da'akayi wa itama nata jeren, ƙwaryar ta sha zane mekyau, ga wasu a cikin ragaya, Widad bata taɓa ganin irinsu ba"

Idan ba gizo kunnuwanta suka yi mata ba, to tabbas a cikin muryar mazan da suka yi Sallama hadda Yusuf.
Zumbur ta miƙe tsaye, Gwaggo tace "aikuwa ga muryar ɗana nan, Alhamdilillah lafiya ta samu"

Kasa jurewa Widad tayi, kawai se gani Gwaggo tayi Widad tayi waje, kai tsaye ta nufi ɗakinsu, ga mutane maza a ciki, wasu na ƙoƙarin fitowa, haka ta kutsa ta shiga, ta hango Yusuf yana zaune yana murmushi, sedai yayi rama sosai, yayi haske.

Da gudu ta ƙarasa ta rungume shi, ta kasa magana kawai ta fashe da kuka.

Ɗaya bayan ɗaya suka zame suka bar ɗakin, yau suka ga taɓara, ba kunya bakomai ba kara tazo ta rungume Yusuf a gabansu.

Suna fita Yusuf ya ha&a hannayensa ya rungumeta shima yace "Queen kin rame, duk kinyi wani iri"

Maimakon ta bashi amsa se sake kwanciya da tayi a jikinsa tace  "Ya jiki ka warke?"

" Na warke amma ina ganin yadda kika rame naji zata dawo"

Hanne ce tayi sallama da kayan Abinci a hannunta, sedai me taga Yusuf da Widad rungume da juna, take taji jikinta ya hau rawa, bata taɓa ganin hakan a zahiri ba, sannan ga wani kishi daya taso mata, take ta saki kwanon dake hannunta.

(Gobe insha Allah, zan kammala book 1,Ashirin ga wata insha Allah zan fara book 2&3,  tuni an fara biyan kuɗin, kuma zaku iya hanzarta biya ta wannan hanyar dake ƙasa "

Normal group duka littafi biyun  ₦300
Idan kuma ɗaya zaki siya  ₦200

VIP ₦ 500

Inkuma sena gama zaki sai complete document ₦700

Account Number
Aisha Adam
0009450228
Ja'iz Bank

Ko katin MTN banda VTU please
A turo evidence of payment ta 07063065680

Duk Wanda ya biya yayi min magana ta what's app number ɗina inyi adding ɗinsa a group ɗin Nagode

Domin gyara sharhi ko shawara
Ayshercool

  _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED  (BANYI EDITING BA)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 44_45

Yusuf ne yayi saurin ɗagowa ya kalli Hanne, Yusuf yace "Subhanallah, garin yaya kika ɓarar da Abinci?"

Widad kam ko motsawa ba tayi ba balle ta tashi daga jikin Yusuf.
  Cikin rawar jiki Hanne tace  "Tuntuɓe nayi shine ya zube, bari in samo in kwashe"
Ta juya ta fita da sauri, tana fita tsakar gida Gwaggo ta kalleta tace "ke meye haka, ba dai Abincin da nace ki kaiwa mara lafiyan kika zubar ba?"

Cikin inda inda tace "Amm.. Mm... Tuntuɓe nayi shine ya zube"

A fusace Gwaggo tace "kekam kamar mara hankali wani lokacin, kije ki kai Abinci kawai seki zubar dan shirme"

Hanne ba tace komai ba ta tafi ta ɗau tsintsiya da abun kwashe shara ta tafi gyara inda ta ɓata musu, cike da zullumin me zata je ta sake tararwa.

Gwaggo tace "Hindu tashi ki duba sauran kunu a ɗakina ki kai musu ba'a bar mara lafiya da Yunwa ba"

Sukam Maƙota da suka rako Yusuf ne suka dinga jinjina rashin ta ido irin na Widad, a gabansu ba kunya taje ta rungume mijinta.

Wani da'ake kira da Lado me Jakai yace "to ai kunsan su ba namu ne na nan ba, jama'ar birni ne baku ga matar tasa bama kamar balarabiya, su sun saba irin wannan bakomai ne ba"

Ɗayan da'ake cewa Liti yace "Aradu amma ai kunya wani abuce, tunda nasan duk abu Hausawa ne"

Lado yace "ku kuga haka, su a gurinsu ba wani abun bane ba"

Liti yace "Sumi sumi dashi haka, Amma ta rungume shi ya wani basar abunsa, memakon ma ya ɗanyi mata tsawa ya hanata"

Wani me shekaru a cikin su yace "Kai waye ya gaya maka suna hantarar matansu, lallaɓasu suke yi, ni wallahi birgeni ma suka yi"

Kwashewa sukayi da Dariya gaba ɗayansu, harda ƙyaƙyacewa.

Hindu tayi Sallama, da kofin kunu tace "gashi inji Gwaggo, tace dan Allah kuyi haƙuri Hanne ta zubar da Abincin"

Yusuf yace "bakomai Hindatu hakanma mungode"

Hindu tace  "Amarya yau za'a ci Abinci, tunda me gidan ya dawo"

Yusuf yace "Ai naga alama bata cin Abinci ta rame sosai"

Hindu tace  "bata ci, Gwaggo taita fama da ita sedai tayi ta kuka, ko bacci bata iyayi"

Widad ta yatsine baki tace "Akanme zanƙi bacci, in kasa cin Abinci toni ƙiba ma nayi, ci nake in ƙoshi"

Hindu tayi dariya tace "bari a kirawo Gwaggo a tambaye ta"

Sukayi dariya, Hindu tayi waje, Yusuf ya kalli Widad yace "bani kunun insha dan inajin Yunwa"

Widad ta miƙe ta ɗakko kofin kunu, tazo ta zauna tana bawa Yusuf, Saleh ne yayi Sallama ya shigo ɗakinsu.

Kallon Widad yayi yai murmushi yace "Allah me iko, Allah ba yadda be iyaba, wai Gimbiyar Daula ce ke bawa direbanta Abinci a baki, abun da mamaki"

Banza tayi masa ta cigaba da bawa Yusuf kunu, Yusuf yace "Saleh ƙaraso ka zauna mana"

Saleh yace "to bari in ƙaraso, ina fatan hankalinki ya kwanta ban gudu dashi ba, gashi na dawo miki da shi, kuma Alhamdilillah jikinsa yayi kyau"

Shiru ta kuma yi bata ce komai ba, Yusuf yace "Ana magana fa"

Widad tace "me zance?"

Saleh yace "base kince komai ba kam, Malaria me ƙarfi da typhoid ne suka kama Yusuf, sannan ulcer na damunsa, ga rashin sabo da wasu abubuwa da yake yi, wanda be saba ba, dan haka shine damuwa gajiya da pressure ga kuma zazzaɓi gaba ɗaya suka dameshi, amma Alhamdilillah mun samu an ceto miki shi, yasamu sauƙi Alhamdilillah, na samo Net guda ɗaya, yace min ba guri ɗaya muke kwana ba, dan haka ga guda biyu nan ke ɗaya shi ɗaya, likita yace 'ya dena zama da yunwa, ya dena barin sauro yana cizonsa, sannan a kula ya shanye magungunansa"

Widad tace "Aishi zaka gayawa bani ba, tunda ze iya kula da kansa ko"

Mamkine ya kama Saleh, ya tuna yadda ta dinga kuka ranar da zasu tafi da Yusuf, amma yanzu tana faɗar wata magana daban, shi kansa Yusuf beji daɗin hakan ba, amma ya basar.

Saleh yace "koma dai menene, Zan zauna zuwa jibi in Allah ya kaimu zan koma, nayi muku siyayya wajen gobe in Allah ya kaimu za'a kawo muku"

Yusuf yace "Mungode sosai da ɗawainiyar da kake mana, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya ka"

Saleh yace  "Ameen"

Ita kuwa madigar, miƙewa tayi tai waje abunta, ba tare da ta sake tanka musu ba.

Amal na kwance akan gadonta tayi shiru sosai take tunani, tayi zurfi sosai a tunani, Mummy ta shigo ɗaki Amal ta tarar a kwance tayi shiru tana ta tunani"

Mummy tace "ke meye haka? Tunanin me kike yi? "

Amal ta ɗan tura baki tace "lafiya ƙalau Mummy"

"Amma kika zauna kika yi shiru haka? Kina ƙarama dake kike tunani haka"

"Mummy ina ɗan zancen zuci ne kawai"

"to idan waccan uwar baccin ta tashi ki gaya mata zan fita, ni na rasa gane kan wannan baccin banzan dat take yi sekace wata kasa"

Ita dai Amal bata gayawa Mummy abunda Ramlan keyi ba.

Bayan fitar Mummy kwanciya Amal ta sake yi tana cigaba da tunani, kuma ba tunanin kowa take ba face Yusuf, tun tana dannewa yanzu abu yavfara gagara, bata iya ɓoyewa sam, Bata iya cin Abinci ba tayi zaton ƙaunar Yusuf haka tayi mat wannan mugun kamun ba, gaba ɗaya yanzu haushin samarin ta take ji, gani take duk cikinsu Yusuf yafi su komai dukda Kasancewarsa talaka, amma ya haɗu gashi nutsatse babu Hayaniya a tare da shi, ji tagi inama a sako Yusuf a riƙe Widad, dama itake hana ta rawar gaban hantsi, dan ta rasa wace irin Alaƙace ke tsakanin su, Widad bata da yadda kamar me, bata yadda kowa ya raɓe ta ba, amma ta yadda da Yusuf ya shiga jikinta sosai da sosai, Yusuf yasan abubuwan dasu da suke zaune da ita basu sani ba.

"Ke Amal! Tun ɗazu nake miki magana amma se kace wata kurma, kinmin shiru"

Firgigit Amal ta kalli Ramlah, tayi ajiyar zuciya tace "Meye nayi min ihu kuma?"

"na dole inyi miki ihu ba, tun ɗazu nake kanki ina magana amma kinyi shiru"

Amal ta miƙe zaune ta kalli Ramlah tace   "ban san kin shigo abane, dana san kin shigo ai zanyi responding"

"Wai nikam wane irin tunani haka kike yi?"

"Ramlah tunanin komai ma inayi, Abubuwa da yawa sun dameni, Amma Ramlah jiya fa maye kike kika dawo"

"Maye kuma?"

"Eh mana, wallahi jiya a buge kika dawo gidan nan, Mummy kuma a ƙule take dake, fitar da kikayi da Fahad"

Ramlah ta ɗan ɓata rai tace "ba wani maye da nake, na gaji ne kawai, sannan me Fahad ɗin kuma yayi?"

Amal tace "Eh to, kin san sunyi faɗa da ɗan uwanta akan belin Yaya Anwar, shiyasa"

"to kuma shine seya shafi Fahad, laifin meyayi? Kuma shima bakiga yadda yake ƙoƙari akan lamarin ba, amma kin san halin babansu da kafiya"

Amal tace "wani tabacci kike da shi na yana ƙoƙarin nan, nifa kallon Fahad ɗin nan kawai nake, bakin maƙaryata ne dashi"

Ramlah tace "zaki fara ko? Karki kusakura kici masa mutunci"

Amal tace  "ke niba wannan ba, nifa naji tana cewa za'ayi uwar watsi idan ba'a fito mata da Yaya Anwar ba, karta yi wani abu daza'a zo ana da nasani daga baya"

Ramlah tace "kuma fa hakane, kin san bata iya fushi ba, bari inje ɗakinta in sameta"

Amal tace "to ai ta fita"

"ta tafi ina?"

"Nima ban sani ba, ni dai tacemin zata fita"

Ramlah tace "Shikenan, bari inje kitchen in samu ɗan abunda zanci, da yamma zanje gurin wani birthday na 'yar gidan IG na ƙasa, na tura a ɗakkomin wata sabuwar motar megidan nan daga kamfani, da ita zanje, kin san gurine na manyan yara fa"

Amal tace "Mhmm yakamata kam"

"waini meke damunki ne Amal, bakya walwala fa"

"Ramlah wace walwala zanyi? Yaya Anwar a rufe, hankalin Mummy yaƙi kwanciya, ga uwa uba wallahi Ramlah Ji nake kamar inyi me saboda rashin Yusuf, na shiga damuwa wallahi ko bacci na kwanta yanzu mafarkinsa nake yi, na rasa inda zan saka raina, tun ina iya dannewa yanzu na kasa "

Wani uban dogon tsaki Ramlah taja tace " Aikin banza, shine zaki kashe kanki saboda wannan jakin"

"Karki sake kiransa da Jaki, Inda wanda za'a kira Jaki to tabbas Fahad ne, dan kunnuwansa ma irin na jakaine ga ƙaryar tsiya".

Haka abun nasa ya koma faɗa, ƙarshe sukayi baran Baran.

Widad ta fita tsakar gida, ta ƙarasa inda Gwaggo take tana murmushi, Hari tace "ohh ni Harira, se wangale baki kike miji ya dawo, kin ware"

Widad tace "Toke ya kika gani? A garin nan banda Allah se shi na sani, idan lafiyarsa ta taɓu akwai damuwa sosai"

Gwaggo tace "ƙyaleta Amarya, zolayarki take"

Widad tace "Mama, dan Allah abun nan na ɗakinki sunmin kyau sosai"

Gwaggo tace  "me fa?"

Widad tace "kwanukan nan da kika shirya a ɗakinki, sunyi kyau sosai fa"

Gwaggo tayi murmushi tace "Widad kenan, kayan Su Samira da fanteka kenan, mu dasu mukeyin adon ɗaki"

Widad tace "Masha Allah, gaskiya sunmin kyau sosai Mama"

Can ta hango bulugari, a gefen Gwaggo zata kaɗa miya.

Widad tace "ya sunan wannan Mama? Wanda kike juya miya dashi"

Gwaggo tace "Bulugari kenan, dashi muke kaɗa miya"

"Mama wannan tunkunyar naganta baƙa sosai"

Gwaggo tayi murmushi tace "wannan itace Talle Amarya, tukunya ce ta ƙasa, muna girki a cikinta, miya tafi zaƙi da daɗi Sosai"

Widad tayi murmushi tace "taɓ Mama duk ban san wannan abubuwan ba, ban taɓa ganinsu ba"

Gwaggo tace "hakane dama, tunda ba kuyi rayuwar karkara ba ba lallai ki sansu ba, bari inje ɗaki in ɗakko abun kaɗi"

Gwaggo ta tashi ta tafi, tana tafiya
Hanne  tayi tsaki tace "Aikin banza mutum ya zauna yaita ƙarya, mtseww aikin banza dana wofi, wai bata san bulugari da fanteka ba"

Widad ko waigawa ba tayi ba, tai shiru abunta, Hari tace "wato Wudas kinfi jin tsoron Hanne, ta gayamiki duk abunda data ga dama, kiyi ƙus amma da nice da tuni kim hayayyaƙomin"

Wani irin kallo Widad tayi wa Hari, nan take cikin Hari ya kaɗa, ganin wani irin kallo da Widad tayi mata, se taga kamar ta canza gaba ɗaya daga kamaninta, ba shiri Hari taja bakinta ta tsuke.

Saleh ya kalli Yusuf yace "Sannu Yusuf, gaskiya kana fama, yanzu haka kuke zaune? Tana maka wannan gadarar da jin kan, bayan taimakonta kake"

Yusuf yayi murmushi yace "lafiya ƙalau muke zaune da ita, duk wannan abubuwan bata Yimin, ƙalau muke zaune Alhamdilillah"

Saleh yace "kaga nifa bana son wannan kawaicin naka, kalli yadda take wani bintsire bintsire, tana cin magani, na zata tuni ta dena wannan halin nata?"

Yusuf yace "Kai da ita ta baka amsar wannan tambayar, Amma nan ma shigo ka tarar tana bani Abinci ai"

Saleh yace "kuma fa hakane, lallai kai ɗan baiwa ne kuma na musamman Yusuf, wannan yarinyar me Azabar taurin kai, amma take kula da kai haka, ta yadda ka shiga jikimta gaskiya abun da mamaki, kayi namijin ƙoƙari fa"

Yusuf yayi murmushi yace  "Haka lamarin ubangiji yake, yanzu ya jikin mahaifinta?"

Saleh yayi shiru da alama jikinsa yayi sanyi yace  "labari mara daɗi Yusuf, yanzu ma badan ka tambaya ba bazan gaya maka ba"

A rikice  Yusuf yace "Subhanallah, meyafaru kuma?"

Saleh ya gyara zama ya waiga yaji babu motsin kowa sannan ya waigo ya kalli Yusuf yace "An sace Daula akan gadon Asibiti"

Dafe ƙirji Yusuf yayi yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, kamar yaya?"

Saleh yace "kaima dai ka tambaya, abun kamar almara, Kasan tunda yake rashin lafiya Anwar ne kawai yake sintirin jinyarsa, matarsa da sauran yaran ba ruwansu dashi, daga ya ɗan fito daga ɗakin, ya koma aka nemi Daula aka rasa, yanzu haka an kama Anwar da me Asibitin ana tuhumarsu, yau sati uku kenan sun tsare "

Dafe kai Yusuf yayi ya shiga murza goshi, wannan wane irin bala'i ne? Duk yadda yake zaton lamarin ya wuce tunaninsa, wane irin tashin hankali ne haka?

Saleh yace " ka kwantar da hankslinka fa, ban gaya maka dan ka ɗaga hankalinka ba, sedai ka tayata da Addu'a, sannan karka bari ta sani"

Yusuf yace "kuma ana bincike akan lamarin, ba'a gano inda yake ba?"

Saleh yace "kai dai ayi sha'ani, har yanzu babu Labari"

"Amma naji kamar kace kasan suwaye ke wannan abubuwan"

Saleh yayi murmushi yace "kaifa jami'in tsarone, kuma kai aka bawa wannan aikin na binciken, zuwa yanzu ai nasan ka samu haske akan binciken da kayi"

Yusuf yace "kamar yaya kenan?"

"Kana nufin baka gane me nake nufi ba? Ai shikenan mu bar zancen, kar tazo ta same mu muna maganar"

Yusuf yace "Ya Ummana kuwa Saleh?"

"tana nan lafiya, Suleiman yana kula maka da ita"

"Amma Saleh, Akwai wani abokin aikina Abbas, babban Abokina nane, yana Ibadan akan aiki, ko Suleiman yayi maka maganrsa, nasan idan yasan ina nan Abbas ze shiga damuwa ina da tabbacim se yazo nan"

Ƙura masa ido Saleh yayi, ya ɗanyi shiru sannan yace "gaskiya ba muyi maganar wani da shi ba, kai dai kunci gaba da haƙuri, komai ze wuce kamar ba'ayi ba Insha Allah"

Yusuf yace "Allah yasa"

Saleh yace  "bari in ɗan fita waje, in zaga gari"

Yusuf yace "bari in bika bana son zaman gidan ne, gara in fita in ɗan tattaka"

Saleh yace "kar kasa matarka tamin tijara fa"

Yusuf yai murmushi yace "bakomai"

Suka fito shida Yusuf, Can Saleh ya hango Widad a kusa da Gwaggo suna hira, Widad ta maida hankalinta sosai akan Abunda Gwaggon take yi.

Saleh yace "iko se Allah, da a mafarki aka haskomin wannan abun ze faru, zance sharrin mafarki ne"

Widad ta ɗaga ido ta hango Yusuf, ya fito da alama fita za suyi, Widad tace "ya dai, naga ka fito, ina zaka haka?"

"You leave alone in the room, am so boring, Saleh is going out, so i feel like to follow him"

Widad tace "gaskiya ban yadda ba, ka koma ka huta in kuma ka faɗi fa?".

"Bazan faɗi ba insha Allah, ina son in ga gari ne kawai"

Widad tace "Shikenan, kar kayi nisa dai"

"As you wish your majesty"

Saleh jinjina kai kawai yayi, yayin da Yusuf yake jin wani irin matsanancin tausayinta, ko ya zataji idan taji labarin mahaifinta ya ɓata shima?.

Haka yabi Saleh suka fice.

A harabar gidan su Nurat kuwa, Nurat ce zaune a ɗaya daga fararen kujerun dake harabar gidan, ita da Barrister Khalil cousin ɗinta, teburin gabansu ɗauke da lemu ka da kuma kofunan glass.

Barrister Khalil yace "kince kina son ganina, gashi nazo amma kin kasa cemin komai"

"Brother, aini sam ban san ta ina zan fara maka bama, na rasa me ya kamata ince maka"

"Ki nutsu, ki gayamin komai a hankali, an fahimceki Insha Allah"

Ta ɗanyi ajiyar zuciya sannan tace  "brother, game da maganar da mukayi da kaine na belin Anwar" Se kuma tayi shiru.

Khalil yace "Mhmm ina jinki, gayamin ke nake sauraro"

"Barrister, kai ɗan uwana ne, kona ɓoyewa kowa wani abun, kai bazan ɓoye maka ba, amma ina son maganar ta tsaya iya nida kai, ko Kasan akwai hannun mahaifina a cikin abubuwan da suke faruwa da Alhaji Daula?"

A hankali Khalil ya zare glashin fuskarsa, ya kalle ta yace  " kamar yaya? Ban gane me kike nufi ba"

'Nasan abun ze baka mamaki, amma kasan Alhaji Daula me silar ɓacin siyasar Mahaifina? "

"Eh na sani, nasan da wannan"

"Mahaifina yayi alwashin ko ze mutu se ya rama abunda Alhaji Daula yayi masa, ya haɗa kai da wasu manyan abokan kasuwancin Alhaji Daula, suna ƙoƙarin ganin bayansa, zancen da nake maka, da saninsa aka sace 'yar gidan Daula da direbanta"

Hankici ya ɗakko a aljihunsa ya share gumin fuskarsa yace "wani tabbaci kike dashi, akan wannan maganar da kike yi"

"Brother, nikaɗai ce sheda, se Mummy amma kasan halin Mummy da tsoro, ba zata taɓa bamu goyon baya ba, yanzun kaima ma gaya maka ne, saboda yadda abun ke cin zuciyata, na rasa wa zan gayawa inji daɗi a raina"

Khalil yayi shiru sannan yace "am sorry to say, Nurat mahaifinki gaba ɗayansa zuciyarsa babu Allah a cikinta, yanzu muddin ya gano mum sam me yake yi to tabbas ze ɗau mataki a kanmj, nasan shi ba tun yanzu ba"

"Nasani brother, nikaina tunda naje na duba Daula a Asibiti ya samun takunkumi, ya hanani fita, rannan dana fita baka ga yadda ya shaƙeni ba kamar ze kasheni"

Khalil ya jinjina kai yace "yanzu Addu'a zamu ci gaba dayi, mahaifinki yana da goyon bayan manya sosai, dan haka babu wanda ze tsaya ya ɗau mataki, sedai muyi ta addu'a"

Nurat tace "hakane Brother, but am so much disturbed wallahi"

"Kakri damu, ki kwantar da hankalinki, Dukda haka zan duba inga me zan iyayi akai"

"Shikenan nagode sosai brother, Allah ya ƙara ɗaukaka"

"Ameen ya Allah karki damu kinji, ki  kwantar da hankalinki, komai zezo da sauƙi"

Haka sukka cigaba da tattaunawa.



"Alhaji Musa wai yanzu duk kuna kallo haka ɗana ze cigaba da zama a prison? Ba zakuyi komai akai ba? Na gaji da yawon da kukemin da hankali fa"

Alhaji Musa yace "Ni yanzu me kike son inyine? Nifa bani na sa aka kama ɗanki ba, me kike so inyi?"

"Idan ba ku kuka sa aka kamashi ba, amma kuna da ƙarfin da zaku sa a sakarmin shi aiko? Wane irin abune haka, se zarya nake a tsakanin ku, amma kowa da kalar rainin hankalin daze mun"

"Kinga saurara, ni babu abunda zan iyayi akan wannan al'amarin, wannan babban case ne da yake buƙatar bincike, idan bashi da laifi zasu sake shi fa"

Hajiya Halima tace "Shikenan nagode sosai da abunda kukayi min, wato na gama yi muku amfani, zaku watsamin ƙasa a ido, zaku ga abunda zanyi"

Ta juya fuuu tayi waje kamar zata tashi sama, tana tafe tana banbami, ofishin Bulama ta tafi, ta tarar yana shirin fita, ya kalle ta yace "Halima lafiya kuwa?"

"karka ƙara tambaya ta ko lafiya, lafiyar kenan kana nan hankalinka kwance, ni kuma nawa a tashe ko baccin kirki bana samu, na zama kamar mahaukaciya, ɗana yana can a tsare, kun nunamin halin ko in kula, kun nuna baku damu da halin da nake ciki ba"

Bulama yace "Nikam Halima kina bani mamaki, ɗanki fa ɗana ne, nima nawa hankalin ba'a kwance yake ba, muna iya ƙoƙarin mu, amma abunda ake gayamana shine, ana zargin da sa hannun Anwar a wannan abu daya faru, kuma duniya ta kasa kunne taji wani mataki za'a ɗauka, me kike tsammani idan aka ji da sa hannuna aka saki Anwar? "

" Kaga sauraramin dan Allah, bana son maganar banza data wofi, na sani ka sani Anwar baze iya aikata laifin da ake tuhumarsa ba"

"A'a karki  shedeshi, ba'a shedar ɗa a zamanin nan"

"Bulama, na gama magana da kai, zanje inyi abunda ya dace kawai"

Bulama yace "abunda ya dace kamar yaya?"

"Ka zuba ido zaka gani, bar ganin kai ɗan uwanane zan iya yin komai akan ɗana, na gaya maka"

Bulama yace "hmm kibi a sannu dai, kin san ido ya fara dawowa kanki yadda kike wadaƙa da wasu daga cikin kadarorin mijinki? Mutane sun san me kike aikatawa, ki sani tsalle ɗaya ke kai mutum rijiya, amma se yayi dubu be fito ba"

Tsaki tayi, ta ɗau mukullin motarta tace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, nasan abunda nakeyi"

Tai waje abunta, tana fita Bulama ya ɗau waya, ya danna yasa a kunnensa yayi shiru, can kuma yace "Yawwa kana jina da kyau, ina son ku ƙara tsananta tsaro da sa ido akan yaron nan Anwar, under no circumstances zaku bada belinsa, ku matsa se ya faɗi inda Daula yake, dan uwarsa ba abunda ba zata iya ba"

Daga cam ɓangaren yace "Ok sir an gama Insha Allah"

Bayan barin Hajiya Halima Office ɗin Alhaji Musa, su Alhaji Haruna suka dira, dukda haushinsu da Musa yake ji, amma ya maze ya sakar musu fuska yace "kun san yanzun nan wannan mahaukaciyar ta bar gurin nan"

Alhaji Haruna yace "wa kenan?"

"Hajiya Halima mana, tazo nan tana ta banbami, wai munƙi saka baki a sakar mata ɗa"

Alhaji Munir yace "ƙyale wannan mahaukaciyar, ni wata shawara nazo mana da ita"

Suka tattara masa hankalinsu, suna saurarensa  "Abunda nake gani shine, mu samu lauyoyin Daula, mu siye su, su saka hannu su fitar mana da wasu daga kadororinsa, a sasu a kasuwa a karya su, sannan ayi takaddun ƙarya, muce muna binsa zunzurtun bashi"

Alhaji Haruna yace "kayi magana mekyau, sedai abunda ka manta shine, lawayoyinsa basu san kan dukiyarsa kamar yadda wannan koɗaɗiyar 'yar ta sani ba, ta san komai tasan inda komai yake"

Alhaji Munir yace "to tunda yanzu ba ita babu ubanta aise muyi yadda zamuyi mu kwashi rabonmu, ko so kuke se wannan mahaukaciyar matar tasa ta ƙarar da komai ita da' ya'yanta? A ɓoye fa se saida kadarorinsa sukeyi, haka zamu zauna mu zuba ido."

Alhaji Musa ya nisa yace "duk naji ta bakin ku, kuma kowa yazo da magana me kyau, zamu jarraba lawyoyin suma, danni yanzu kuɗin tsayawa takara nake nema"

Kallonsa sukayi gaba ɗaya sukace "kamar ya tsayawa takara?"

"kamar yadda na gaya muku, bazan zauna bani ga tsuntsu bani da tarko ba"

Alhaji Haruna yace "hala ka manta da baƙin fentin da kake da shi, a dalilin Daula?"

"ina fa na manta, sedai a ƙasar nan indai kana da kuɗi ba abunda baze yuwu ba"

"Amma baka ganin hakan, ya saɓa da Yarjejeniyar mu, idan kayi haka kamar ka zame daga cikinmu ne, kuma me zaka cewa Bukar?"

"Bukar ubanane, ko haifata yayi? Ba gudu ba ja da baya, ina tare da ku amma tabbas zanyi takara"


Gaba ɗaya Yusuf ya fara jin kunyar mutanen da yake ja salla, musamman idan ya tuna abunda Widad tayi a gaban su, tunda su hakan kamar baƙon al'amarine a gare su, haka nan ya ɗan dinga basarwa, sukayi sallar magariba da isha'i suna ta sake duba shi.

Widad jin shiru Yusuf be shigo ba, yasa ta fito tsakar gida ta samu wani ɗan gidan Hansai tace masa  "kaga ɗan jeka waje ka cewa Yoseef in jini nace, baze dawo ba se sauron ya sake cizonsa yazo ya kwantamin?"

Gwaggo dake alwala tace "A'a kul kaje ka faɗi haka, kace tace  'dan Allah ya shigo gida, kar sauro ya kuma cizonsa'"

Widad tace "to ai kusan abunda na faɗa kika maimaita"

Gwaggo tace "A'a ke naki umarni da kashedi kika yi, aishi miji abun lallaɓawane da tattalawa, ki kalli yadda kika damu da bashi da lafiya, ki dinga masa magana da girmamawa kinji Amarya, yana da kirki mijinki, kema ki dinga tausasa harshen ki a kansa"

Widad tace "To Hajiya Mama"

Gwaggo tace "ni  a Hajiya, to me rai baya fidda rai da rahama, amma abun da wuya"

"Insha Allah indai da rai da rabo, zaki je saudi Arabia in dai Allah be ɗau rayuwar wani daga cikin mu ba, idan muka koma gida lafiya zaki je ƙasa me tsarki"

Tsaki Hanne tayi tace "san a sani, ji wata ƙarya kuma da son nuna iyawa, karma kisa rai ana gayamiki gaibu"

"Ke! Ki kiyayeni, dake muke taɗin, ina ruwan ki Hanne ki kiyayeni fa"

Widad ta juya kawai ta koma ɗaki, ta ɗakko ƙaramar fitilarsu ta kunna, batirin ma ya fara sanyi.

Ta zauna tayi shiru tana tunani, sallamar Yusuf ce tasa ta ɗago ta amsa masa, yaje kusa da ita ya zauna, daya kalleta se tausayinta ya kama shi yace "gani naji ance kina nemana"

"shine tun la'asar kaƙi dawowa, se sauro ya kuma cizonka ko?"

"Ai na warke, Alhamdilillah"
"dan ka warke shine se kaje, ka kuma kwaso wani zazzaɓin, kazo ka ɗagamin hankali"

"Insha Allah na warware ai, ance jinina ma yayi ƙasa, dole in dinga cin ganyayyaki"

"Sannu kaji jiki ai"

"Gaskiya muje ki dawomin da jinina dana baki"

"wai jininsa, jinin naka ma duk malaria ya ƙara samun zazzaɓi, zan biya ka jinin ka harda riba ma"

Dariya Yusuf yayi yace "ni iya nawa nake so, bana son naki danni bana son jinin me taurin kai"

"kai kai, nice me taurin kai? Zaka ga taurin kai'

Kwanciya yayi a kafaɗarta yace " dan Allah a sake rungumeni mana, i need your body warm "

Ture shi tayi tace  'kaje kaji ɗumin bargo mana"

Cikin kwantar da kai yace "A' a ni gaskiya naki nake so, ai naga yau ke kika rungumeni, idan muka koma gida sena gayawa Ummana, nima ince kina rungumeni"

Widad tace "ai kai ka fara bani ba, ka koyamin abunda ban iya ba"

Dariya Yusuf yayi yace "nayi mamakin yadda kika damu da rashin lafiya ta My queen"

"A cikin AƘIDATA babu butulci, bana manta alkhairi, bazan taɓa manta wahalar daka sha saboda rayuwa ta ba, idan na nuna halin ko in kula ga kafiyarka to tabbas banwa kaina adalci ba, dukda ana faɗin bani da kirki, banj da mutunci amma bana manta alkhairi"

Yusuf yace "waye yace miki baki da kirki, kina da kirki uwaɗakina"

"Hmm yoseef kenan, ka dena kareni danka burgeni, amma nasan bani da kirki kamar yadda da yawa mutane ke faɗa"

"ba kareki nake dan na burgeki ba, ina faɗa miki gaskiya ne kawai, amma kince bakya manta alkhairi, amma meyasa bakwa jituwa da Saleh, dukda irin taimakonmi da yayi?"

"saboda bana yafiya ga mutane ma'abota fuska biyu, da fari mahaifina ya yarda da shi da ɗam uwansa, amma ya koma ɓangaren maƙiyanmu, yanzu ya kuma dawowa ɓangaren mu, wani tabbaci muke dashi na muma baze sake juya mana baya ba? Duk yardar da nayiwa mutum, duk girman Alkhairin da yayumin, muddin yaci amanata koya min ƙarya to tabbas ze shafe dukkan alkhairansa a idona, bana yafewa mayaudari da maƙaryaci ko me fuska biyu, wannan itace AƘIDATA!!!


TOFA! Alhamdilillah nan na kawo ƙarshen kashi na ɗaya a littafin AƘIDATA,

Ɗanɗano daga Littafi na biyu

(idanunta sunyi jawur, kamar wadda aka zubawa barkono saboda kuka, ta sunkuyaf da kanta ta shafi ciknta, cikin zubda hawaye tace "wace amsa zan bawa abunda yake cikina, idan har ya girma ya samu labarin mahaifiyarsa taje kotu ta bada sheda akan mahaifinsa an kai shi prison, kaicona haɗuwa ta da Yusuf ta zame masa babbar ƙaddara a rayuwarsa, ya sadaukar da rayuwarsa don in ganta tawa, amma maƙiyana sun na ƙoƙarin cin galaba akanmu, abun da basu sani ba shine...............)

Karku bari a baku labari, saƙar labarin mukayi a na farko, tufaka da warwarar gami da cakwakiyar suna littafi na biyu dana uku, anan gwaramar take

SHINE MEYE LABARIN YUSUF?
MEYE LABARIN WIDAD?
WAYE MAMALLAKIN ABUNDA AKE NEMA A HANNUN WIDAD?
MEYE ABUNDA AKE NEMAN?
WAYE YA SACE DAULA?
SHIN ZASU BARO ƘAUYEN NAN?
ZASU KOMA GIDA DA WANNAN AUREN?
YA ZATA KAYA TSAKANIN WANNAN MANYAN ALHAZAI?
YA WIDAD ZATA YI IDAN TA GANE YUSUF JAMI'IN TSARO NE YA MATA ƘARYA?

Akwai cakwakiya me tarin yawa karku bari a baku labari, ga masu buƙatar siya

Normal group duka littafi biyun  ₦300
Idan kuma ɗaya zaki siya  ₦200

VIP ₦ 500

Inkuma sena gama zaki sai complete document ₦700

Account Number
Aisha Adam
0009450228
Ja'iz Bank

Ko katin MTN banda VTU please
A turo evidence of payment ta 07063065680

Zan fara posting ɗin littafi na biyu dana uku, ranar 20 ga watan October

Masu neman complete zasu sameshi ranar biyar ga watan November insha Allah

Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool. 07063065680

Nagode da ƙaunar da kuka nunamin

No comments