Ailimah Complete Hausa Novel
�Aalimah*
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870*
FREE PAGES 1
Jirgin ‘American Airways’ ya sauke AALIMAH MANSOUR a birnin Massachusetts na kasar Amurka a ranar ashirin da biyar ga watan Mayu, na shekara ta dubu biyu da goma sha shidda(2016). A sannu ta bi jerin gwanon masu saukowa daga jirgin rataye da
matsakaiciyar jakar hannu ta mata. Sanye ta ke da doguwar riga da veil dinta kirarTahran (maroon colour) ta zagaye fuskarta da veil din rigar. Takalmin kafarta baki ne mahadin jakar hannunta marar tsayin dunduniya. Taku ta ke cikin nutsuwa har ta taka kwaltar filin jirgin (Boston Logan International Airport) ta shiga van din da sauran fasinjoji ke shigawadda za ta karasa da su zuwa ainahin ginin cikin filin jirgin, inda aka yi mata duk wasu immigration checks, daga karshe ta dauko jakar kayanta ta fito.Hasken sassanyar ranar da ya soma ketowa ya dallare mata ido, ta sanya tafin hannunta ta kare saman idanunta daidai lokacin da masu taxi suka soma isowa gare ta.
Tambayarta suke inda za a kai ta. Ta diregajiyayyun dara-daran idanunta a kansu kamar mai kiyasi, kamar kuma mai tantance wanda ya kamata ta zaba,da ganinta ka ga bakoa kasar da bai taba zuwa ba, kafin ta tsaida idonta a kan wani dan tsamurmurin bature ta nuna mishi adireshin inda zai kai ta, wanda ke rubuce cikin jotter dinta, wadda ta fiddo daga jakar hannunta. Daukar jakar tata ya yi ya sanya a bayan motarsa ya bude mata kofar baya, ta shiga ta zauna. Ya zagaya ya shiga mazauninsa, ya tada motar.
Tafiya suke sannu kan hankali a kan kwaltar manyan titunan birnin Massachusetts tana karewa kyawawan titunan kallo.
Birnin Massachusetts na daya daga cikin manyan biranen da kasar Amurka ke tinkaho da su. Ya kuma kunshi al’ummatai daban-daban, daga yarekala-kala na duniya. An kiyasta population din birnin Massachusetts a shekarar (2017) da adadin (685, 094 population).
Yana kusa da Cambridge daga gabas, tana iyaka da Hampshire da Vermot daga Arewa, daga yamma zagaye yake da babban birniNew York, daga Kudu da birnin Connecticut da Rhode Island. Daga gabas kuma zagaye ta ke da Atlantic Ocean. Birni ne daga Arewa maso gabashin USA.
Mai taxi ya tsayar da motar a cikin estate din (Martha’s Vineyard) a kofar wani kyakkywan lodge cikin birnin BOSTON (Capital of Massachusetts).
Aalimah Mansour, ta yi ajiyar zuciya, ta lalubo adadin kudin da ya bukata ta ba shi, ya ba ta canjinta, ya kuma fitar mata da jakarta daga bayan motarsa. Sannu a hankali ta karasa kofar gidan tana nazarin kayatacciyar unguwar. Tana daga cikin manyan estate (kebantattun unguwanni) a birnin Boston. A saman kofar gidan an rubuta lambar gidan da kuma sunan mamallakin sa ‘ISHAQ RAAZEE’.
Kararrarwar kofar gidan ta shiga dannawa, sai da ta danna sau uku kafin ta jiyo muryar mace na fadin tana zuwa cikin harshen Nasara. Gabanta ya ci gaba da lugude kamar zuciyarta za ta fado daga cikin kirjinta. Ba ta da idea na irin karbar da za ta samu daga Kawun nata, haka ba ta da sanin irin karbar da za ta samu daga matarsa Mummy Zulaiha da ‘ya’yanta, matar da kowa a family dinsu ya kwana da sanin ba ta son kowa ya rabe ta, daga mijintasai ‘ya’yanta. Kada a rabi inuwar arzikin da suke ciki. Balle kuma su, da nata mahaifin duk cikin zuri’arsu shi ne mai karamin karfi. Banda Mamada ta dage ba za ta yi zaman hostel ba, alhalin ga Kawunta da iyalinsa a kasar da ba abin da zai kawo ta gidan Kawun nata.
Ta tabbata sai ta fi samun nutsuwa a zaman hostel din, amma ya ya za ta yi da umarnin iyayenta? Ta riga ta dora zuciyarta a kan son karatun nan, kamar yadda ta ke son rayuwarta. Sannan ba ta san kowa ba a kasar bayan su. Asstrict as her Mum is, (sabida tsantseni irin na mahaifiyarta) a kan tarbiyyah, ta tabbatar mata ko dai ta zauna gidan Kawunta ta yi karatun a gabansa, ta fuskanci kowannne irin kalubale na matarsa da ‘ya’yansa, ko ta hakura ta yi aure. Hankalinta zai fi kwantawa ita ta hakura da nata burin akan karatun nata.
Mahmoud, saurayi daya data ke da shi a rayuwarta, ko ta ce wanda ya taba cewa yana son ta da kalmar aure, dalibi ne shibai shirya ba, yanzu ne yake shekarar karshe a jami’a, sun kulla soyayyarsu ita da Mahmud Kaita ba tare da sanin iyayenta ba, karewa ma boye tarayyarta da Mahmud ta ke don muddin Mama ta san tana da tsayayye, duk sonta da karatun ga ‘yar tata, za ta hakura ne ta yi mata aure. Banda babban Yayanta Aboubacar (Abubakar)babu wanda ya san da maganagr Mahmud a gidansu, shi ma ya sani ne a dalilin Mahmud din abokinsa ne, kuma ta dalilinsa suka san juna.
Duk wannan tunanin Aalimah na yin shi ne a tsaye a kofar gidan Kawunta kafin a zo a bude mata kofar, cikin mintunan da ba su gaza biyar ba. A daidai lokacin ne kuma Easther (‘yar aikin) Mummy Zulaiha ta bude mata kofa. Kallon juna suka tsaya yi na rashin sani ita da Easther din na ‘yan sakanni, kafin ta ba ta hanya tare da yi mata alamun ta wuce ciki ba tareda ta tambayeta wanda ta zo nema ba. Ba kuma komai ya sanya Easther bai wa Aaalimah hanya babu tambaya ba, sai kamanninta da ta gani mai dimbin yawa da yaran gidan, musamman matan.
Aalimah ta wuce ciki tana jan jakarta cikin nutsuwa. Easther ta mayar da kofar ta rufe. Daidai lokacin da Mummy Zulaiha ta bullo daga upstairs a shirye tsaf, tana taku kwaf-kwaf akan tsanin takalmin ta irinna matan da duniya ke yi da su, suka kuma sameta dai-dai da ra’ayinsu, makale da jakar hannu da mukullin mota alamar fita za ta yi.
Sakin baki ta yi cikin madaukakin mamaki tana kallon ba’abziniyar budurwar da ke shigowa. Doguwa, sambaleliya, fara tas! Mai dogon hanci da manyan fararen idanu, labbanta sirara jazur da su, ma’abociyar yalwar sumar kai, wadda ta fallasa kasantuwarta daga ruwa biyu, wato kallo daya za ka yi mata ka fahimci ba cikakkiyar bahaushiya ba ce, jinin su maigidanta Ishaq Razee ce. Yarinya ta karshe da ta yi tsammanin gani a kasar America, kuma cikin gidanta, a dai cikin family din maigidanta.
Aalimah ta saki murmushin yake, wani lallausan murmushi mai ban sha’awa na nuna ladabi, ta russuna tana gaida matar Kawunta, wadda mamaki ya hana ta ce mata kanzil. Sai da ta gaishe ta har sau biyu, Zulaiha ba ta farfado daga suman mamakin wucin-gadin da ta yi ba, har sai da karamar ‘yarta Yasmin ta taba ta, tana fadin,
“Mummy ana gaishe ki�.
Firgigit ta yi, ta dubi Aalimah tana ayyana abubuwa da yawa a cikin ranta, me ya kawota? Wato Ishaq wuyansa ya yi kaurin da zai soma kwaso abzinawan danginsa yana kawo mata gida ba tare da shawara da ita ba? Abin da ba za ta taba dauka ba kenan. Amsa gaisuwar ta yi kadaran-kadahankafin cikin shaqaqqiyar murya ta ce,
“Ke da wa ku ka zo?�
Aalimah ta sunkuyar da kai cikin muryarta mai sanyi, ta ce,
“Ni kadai ce Aunty�.
“Ke kadai tun daga Nigeria?�
Ta daga mata kai alamar “Eh�.
Kamar za ta ce wani abu, sai kuma ta fasa ta ci gaba da saukowa daga stairs din. Ta dubi Easther cikin rashin walwala ta ce,
“Ki ba ta abinci ki nuna mata dakin kwana, ni fita zan yi�.
Easther ta amsa, “Yes, Ma!�
Ta dubi Aalimah cikin hadiye fushi ta ce, “Ki wuce ku je. Sai na dawo. Zan kai Yasmin makaranta ne, daga can zan koma office�.
Cike da ladabi Aalimah ta amsa, ta bi bayan Easther, Mummy Zulaiha da ‘yarta Yasmin suka fita.
Gidan Ishaq Raazee karamin ‘American lodge’ ne, ginin sama da kasa. A saman, dakin maigidan da na matar gidan har ma da na yaransu mata guda uku yake. A kasa kicin ne da babban English parlour wanda a cikinsa dakin manyan ‘ya’yansu maza yake. Mai aikin gidan, wato Easther ba ta kwana, zuwa ta ke da safe ta tafi da yamma in ta kare girkin dare. Don haka Easther ta rasa dakin da za ta kai bakuwa Aalimah, gidan ba a gina shi da niyyar karbar baki ba, tana ganin bai kamata ta kai ta sama ba, tunda maigidan a sama yake, bai kuma kamata ta ajiye ta a kasa ba babu kowa sai ita kadai. A falon kasan, akwai wani daki bayan na Yayansu dake makaranta, amma a rufe yake ba ta taba ganin an bude shi ba, balle tayi tunanin ajiye ta anan, don haka sai ta kai ta dakin su Yasmin kawai, wanda ke daura da na mahaifiyarsu. Cike da zullumin ko ta yi ba daidai ba. Ta koma kicin ta hado mata abinci a kan ‘tray’ ta ajiye mata a gefen gado. Ta yi mata sallama ta koma bakin aikinta.
Kafin Aalimah ta yi komai, wanka ta shiga don ji ta ke jikinta har wani danko-danko yake mata. Ga ta da son wanka dama kamar agwagwa komai sanyi, balle kuma a lokacin zafi. Hatta gashin kanta ji ta yi yana mata kaikayi – kaikayi, duk da yau kwananta uku da wanke shi. Ta sunce ta dauko kayan wankanta daga jakarta ta shiga toilet din da ke cikin dakin.
Ta tsaya na dan lokaci tana nazarin bandakin. Ba ta taba zuwa kasar waje ba, amma kuma hakan bai maida ita bakauyiya ba. Nazarin bandakin ta shiga yi wanda ke dauke da bathtube na jacuzzi, kalarsa light blue komai da ke cikin bandakin kalarsa kenan. Ta mika hannu ta zare ribbon din da ta daure tulin gashinta ya wargaje a kafadunta, baki sidik mai tsayi da salki, na abzinawan usli.
A cikin toilet din har da hand dryer makale a gefe. Ba karamin jin dadin hakan ta yi ba. Ga shampoos nan kala-kala masu tsada a jere, wannan na da nasaba da kasancewar su ma yaran gidan mata guda uku, gashin gare su kamar ita. A lokacin ta manta da komai ta tara ruwan dumi cikin jacuzzi ta shiga ta soma abin da ta fi so a rayuwarta, wato ‘wanka’. Ta jima tana kalkale sassalkar fatar jikinta kafin ta soma wanke sumar kanta tana cudawa da kumfar(head& shoulder). Ta gama ta busar da shi da hand dryer, ta dauro alwala ta fito. Doguwar rigar atamfa (fitted-gown) ta sanya ta dauko hijabin sallarta ta tada sallah.
Sai da ta rama sallolin da ake binta sannan ta samu nutsuwa tazauna ta soma cin abincin.
Faten dankalin Turawa ne da aka yi da Mushroom da zallar tsokar naman kaza. A gefe kuma gasasshiyar hanta ce a cikin bowl na tangaran ta sanya fork tana cin hantar a hankali bayan ta gama da faten dankalin. Da ta gama, ta kora da lemun kwali na Apple mai sanyi, sannan ta kishingida a sofa tana hutawa.
Mamanta, Daddynsu, kannenta da masoyinta Mahmud suka fado mata a rai. Ta san suna can suna sauraron kiran wayarta. Da sauri ta sauko daga gadon ta lalubo wayar a jakarta. Tana kunnawa ta tuno ba ta da internet connection, kuma ba ta da credit na kasar. A rashin saninta da cewa gidan (WiFi) suke amfani dashi. Ta maida wayar gefe ta ajiye ta dauki kayan da ta ci abinci da su ta sauko kasa.
Kofofin falon ta shiga nazari tana son gano wacce ce ta kicin?Sai ta jiyo karar kwanuka kamar ana wanke-wanke da karar zubar ruwa daga famfo. Nan ta gane kofar da ke can karshe ita ce kicin. Ta karasa ta tadda Easther suka yi wa juna murmushi na rashin sabo, Easther ta karbi ‘tray’ din ta hada da wadanda take wankewa, sai ta kasa komawa daki ta jingina da cabinet din kicin suka soma hira.
Aalimah ta ce tana so ta taimaka mata su ci gaba da aikin tare. Easther ta ce ta rufa mata asiri ta koma daki kada ta yi laifi wajen uwar dakinta, tunda ba ta ce ta sa ta aiki ba. Amma ta kasa komawar, sai ta samu daya daga kujerun karamin dining da ke cikin kicin din ta zauna, Easther na aikin suna hira jefi-jefi da turancinta mai rauni.
Easther ‘yar Africa ce, wato bakar fata wadda aka haifa ta kuma girma a kasar Amurka, wadanda ake kira black- American. Ta ke gaya wa Aalimah su ‘yan asalin kasar Ghana ne daga Kumasi, iyayenta da kakanninta duk a nan aka haife su sun rayu tsayin rayuwarsu suna yi wa Turawa bauta. Ta tambayi Aalimah amma ita ‘yar uwar Daddy ce ko? Don ta ga tana kama da shi da ‘ya’yansa. Aalimah ta gaya mata cewa; “Wan babanta ne Ishaq Razee�.
Daidai lokacin da suka ji shigowar motoci har guda biyu, daya ta maigidan, daya ta Mummy. Yaransu ne suka fara shigowa daya bayan daya suna ta hayaniya, Aalimah ta dawo kofar kicin tana kallonsu. Basma ce a gaba, sai Khalisat sai auta Yasmin. Rabonta da su shekara shidda kenan zuwansu Nigeria na karshe. Lokacin Aunty Zulaiha na da cikin Yasmin. Duk sun yi wani irin girma mai ban mamaki da ban sha’awa, irin girman ‘ya’yan Turawa. Ba mai cewa Basma sa’arta ce domin ta yi biyunta a girman jiki. Mai bi mata Khalisat, Aalimah ta girme ta da shekaru biyu, shekarunta goma sha hudu. Ita da Basma za su yi sha shidda da ‘yan watanni. Bayan haihuwar Khalisat Mummy Zulaiha ta dade ba ta haihu ba,sai da Khalisat ta yi shekaru takwas,sannan ta haifi autarta Yasmin.
Haihuwarta ta farko da ta biyu ‘ya’ya maza ne. Su ma tsakaninsu ratar shekaru biyar ne, haihuwa irin ta turawa Mummy Zulaiha ke yi, haihuwar Khaleesat data yi shekaru biyu bayan ta Basma (unwanted pregnancy) ne wanda ba yadda zata yi da shi.Data haife tan kuma, sai tafi sonta fiye da dukkan ‘ya’yanta mata. Itama Khalisan bata aje Mummy kusa da kowa na gidan ba a kauna da shakuwa. Idan ka dubi Mummy Zulaiha ba za ka ce ta haifi wadannan zaratan ‘ya’yan ba saboda hutu da kula da jiki. Shekarunta sun kusa hamsin, amma tsammani za ka yi talatin da biyar gare ta.
Daga ita har maigidanta Ishaq sun yi auren wuri, aure na soyayya, irin makauniyar soyayyar da iyayenta suka gwammace su cire ta daga makaranta tun tana aji biyar na sakandire su aura wa Ishaq. A lokacin yana shekara ta uku a jami’ar Ahmadu Bello. Ko abin da zai rike ta ba shi da shi, ga hidimar karatu, don haka ya dauke ta ya tafi da ita kasarsu Niger Republic ya ajiye ta a family house dinsu, inda aka ba su daki a babban gidan na zuri’ar Mal. Ibrahim Raazi. Ya maida ita makarantar sakandire a nan garinsu, Yamai, duk da ba ta jin faransanci har a hankali ta koya, in ya samu hutun semester ne yake zuwa gida shi din ma ba kowanne ba.
Tun yana yaro yake son kasar Nigeria da son zama a cikinta, ko da ya gama sakandire ya ce da mahaifinsu Malam Ibrahim Razee shi a Nigeria zai yi jami’a yana sha’awar harshen turanci, bai hana shi ba, amma ya ce ya tafi tare da kaninsa ‘Mansour’ wanda ya samu double promotion sabida hazakarsa suka gama sakandire a shekara guda, shi ma ya yi karatun a can zai fi jinsa kamar a gida in suna tare.
3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:30 AM - Buhainat: **🌹 *Aalimah**🌹
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870
FREE PAGES 2
Ba su sha wahalar samun gurbi a jami’ar Ahmadu Bello ba, kasancewar a wancan lokacin neman masu yin karatun gwamnati ke yi ido rufe, ga kuma takardunsu sun yi kyau, wadanda aka yi wa fassarar takardun Nigeria, suka kuma shiga wani tsari na koyon harshen turanci da jami’ar ke yi a wancan lokacin, kasancewar sun yi karatunsu ne da harshen faransa. Komai tare suke yinsa a A.B.U kasantuwar baki da basu da kowa sai junansu, sannan kuma uwarsu daya ubansu daya.
A gida ba sa jituwa kasancewarsu sakonnin juna, kowanne kamar yana ganin hanjin dan uwansa. Amma da suka zo Nigeria ba su da kowa, dole suka rungume junansu. Wannan kuma wata hikima ce irin ta iyaye, mahaifinsu ya yi musu ba tare da saninsu ba.
Daga Mansour har Ishaq dukkansu gifted ne a karatu. Ba fanni daya suke karanta ba, Ishaq na nazarin International Relation, yayin da Mansour ke karantar Mass Communication. A hostel suke rayuwa, duk abin da suke bukata mahaifinsu na aiko musu ta banki.
Mahaifinsu babban malami ne ta daya bangaren kuma babban dan kasuwa a babban birni Yamai, yana sana’ar kasuwancin kayan abinci yana kuma taba kasuwancin rakuma da kiwonsu, wanda ya gada iyaye da kakanni. Matansa na aure guda biyu, wadanda ke haifa masa ‘ya’ya kusan a tare, don in wannan ta haihu yau, bayan sati daya ko wata daya za ka ji dayar ma ta haihu.
Inna Bintou da Inna Kasisi, sune matan Malam Raazee. Ishaq da Mansour ‘ya’yan Kasisi ne, wato uwargida. Haihuwa suke kusan duk shekara, don haka ‘ya’yan Malam Ibrahim ashirin da biyar a duniya kafin haihuwar ta tsaya wa matan nasa. Ishaq ba shi ne babba ba a ‘ya’yan Kasisi, yana da yayye har biyu, sannan shi, sai Mansour.
Ba duka ‘ya’yan Malam Razee ke son karatun boko ba, hasalima mazan duka ba sa so, sun fi son sana’ar mahaifinsu in ka cire Ishaq da Mansour, matan kuwa suna gama sakandire yake yi musu aure. Dalili kenan da sanda Ishaq ya zo masa da maganar ya samu matar aure a Nigeria yana so ya yi aure bai ja zancen da nisa ba, shi ya ma fi son hakan. Sai ya tuntubi Mansour ko shi ma yana da wadda yake so a hada? Ya ce shi kam ba yanzu ba, sai ya gama karatu.
Ishaq da Zulaiha sun hadu a jami’ar Ahmad Bello, kanwar wani course mate dinsa ce Ahmad Madobi, ‘yan asalin jihar Kano ne. Lokacin yana aji biyu a jami’,Zulaiha da ‘yan gidansu suka zo wajen Yayanta Ahmad, a lokacin yana tare da Ishaq Ba’abzine (kamar yadda suke kiransa). Abin nan da Turawa ke kira ‘love at first sight shi ya afku tsakanin Ishaq da Zulaiha.
Zulaiha baka ce (black beauty), yarinya danya sharaf ‘yar saandire. Iyayenta ba ‘yan boko ba ne, ‘yan kasuwa ne. Har Kano Ishaq ke zuwa daga Zaria wajen Zulaiha. Wata irin zazzafar soyayya ce ta shiga tsakaninsu, wadda ta sa iyayenta gwammacewa su cire ta daga makaranta su yi mata auren, don kuwa ta yi watsi da karatun ta kama Ishaq. Sai aka yi sa’a shi ma nashi iyayen ba masu tsattsauran ra’ayi ba ne a kan karatun, suka yi musu aure.
Hankalin iyayeyn Zulaiha bai tashi tashi ba sai da iyayen Ishaq suka ce Nijar za su tafi da ita can main house din su. Sun dauka tunda yana Nigeria bbai gama karatun ba haya zai kama su zauna. Daga karshe ba su da yadda za su yi, sun aminceAURE ba inda ba ya kai ‘ya mace, suka amince Ishaq ya tafi da matarsa kasarsa ta haihuwa, ya baro ta tare da iyayensa ya dawo makaranta ya ci gaba da karatunsa cikin kwanciyar hankali, tunda ya mallaki abin da zuciyarsa ke so.
A irin zaman amincin da ake yi tsakanin Inna Kasisi da Inna Bintou, ‘ya’yan wannan sune na waccan, sai ya zama cewa, Zulaiha surukar Bintou ce ba surukar Kasisi ba. Ita ke kula da al’amarinta tunda mijinta ba ya nan. Malam Razee bai ragi Zulaiha da komai ba ta fannin bukatunta tamkar mijinta na kusa da ita, makarantar da ta ke yi ma ta kudi ce, wadda shi ya sanya ta a can Yamai, har ta gama sakandire.
Sai dai sam Inna Bintou ba ta jin dadin surukuta da Zulaiha, sabida baudaddun halayenta;Yarinya ce mara godiyar Allah da fadin rai. Duk abin da suke mata a raine ta ke kallonsa ba ta godewa, ba ta jan jikokinsu a jiki, ba yaron da ya isa ya shigar mata daki. Ba ta taimaka musu da komai na hidimomin gida, ga ta da girman kai da raini ga kowa. Inna Kasisi kawai ta ke shakka a gidan, don ita kam ko kusa ba ta daukar raini, tana da zafi. Hatta ga ‘ya’yanta, mijinta ma lallaba ta yakeyi. Ita da kanta ta fahimci wasu daga halayen Zulaiha ba tare da Inna Bintou ta ankarar da ita ba. Don haka ta kara jan girmanta ta rike tamau a idanun Zulaiha. Ba ta shiga duk wata sabgarta, in taro suke yi a gidan na abin da ya shafi ‘ya’ya da jikokinsu, Zulaiha ba ta shiga sam, kullum tana killace kanta tana yi wa kowa kallon bai isa ba.
Malam Ibrahim bai san ko daya daga halayen Zulaiha ba, sosai yake kyautata mata iyakar iyawarsa, tunda yana ganin an rabo ta da iyayenta da kowa nata. Matan kuma babu wadda ta taba dosarsa da irin wannan zancen, don bai raine su da tsegumi da gutsiri tsoma ba.
Haka Inna Bintou ta yi ta hakuri da Zulaiha. A shekarar ne Ishaq da Mansour suka kammala karatunsu suka dawo gida. Kwarai Mansour ya ji dadin zaman Nigeria, ya ji yana son ci gaba da zama a can, musamman da yake ya yi nasa kamun shi ma a Nigeria. Don haka ya yi hidimar kasa a can kafin ya koma Nijar, yana gamawa jami’ar Ahmadu Bello ta dauke shi aiki a tsangayar Mass Communication a matsayin assistant lecturer, sabida kyawun takardunsa. Ishaq shi kadai ya koma Nijar da zama wajen iyaye da iyalinsa.
A ‘ya’yan Inna Bintou mata sun fi yawa, na Kasisi maza sun fi yawa, izuwa wannan lokacin manyan ‘ya’yan Inna Kasisi Edrissa da Oussama sun zama manyan attajirai a Yamai (Niamey) daga sana’ar da suka gada daga wajen mahaifinsu, wato shigo da shinkafa da sauran kayan abinci daga kasar Faransa zuwa Niger. Sun buge gidan mahaifinsu sun gina katon gida na zamani, ginin attajiran Nijar. Gidan ya zama mai sassa daban-daban, sassan iyayensu mata, sassan Malam, sassan matansa, na ‘ya’ya maza da sassan ‘ya’ya mata (jikoki), kasancewar yawancin jikokin gidan a gidan Malam Razee suke rayuwarsu. Gida mai cike da kyawawan ‘yammata da kyawawan samari kamar kana cikin birnin Punjabta kasar Hindu.
Gidan Ibrahimu Sarhamu Razee kenan.
*****
ASALIN SU
Asalin kakansu Malam Ibrahim Razee ba dan kasar Nijar ba ne, iyayensa larabawa ne na sahara, wadanda suka fito usul daga saharar TOMBOUCTOU. Ita Tombouctou karkashin kasar Mali ta ke, larabawan ta ma’abota sanin addini ne masu yawo a kan rakumansu cikin kasashen Africa suna neman ilmin addinin musulunci a duk kasar da suka ji labarin ta shahara wajen yada musulunci. Ba su da wata sana’a sama da kiwon dabbobinsu.
A irin yawon neman ilmi da suke yi sun shiga manyan kasashen Africa masu yawa, irin su Mouritania, Sudan, Ethiopia (Habasha), Somalia, Algeria, Libya, Senegal da Malawi. Daga karshe suka shigo Chadi, suka gangaro kasar Niger. A daidai wannan lokacin Niger ta samu ‘yancin kanta daga hannun Faransa a shekara ta (1960). Lokacin da suka samu kansu a Niger sun yada zango a Tessoua inda mahaifin Malam Razee ya tabbatar musu da ya ga gurin zama sabida albarkar wajen da habakar dabbobinsu. A lokacin ita kanta Tessoua kauye ce kayau, ba ta kai ga zama jiha ba.
Mahaifin nasa ya zama babban malami mai bada karatun buzu a Tessoua, a hannunsa duka ‘ya’yansa suka yi karatu, wadanda dukkansu maza ne. Ibrahimu shi ne babban dansa. Yahayya ke binsa, sai Lamin, Hassan da Hussain. Wadanda ya haifa da matarsa daya tilo ‘Zainabou’ wadda ya aura a nan. Buzuwar Tessoua ce ta asali iyaye da kakanninta.
Barkowar ‘yancin kai Nijar, da yaduwar sabbin sana’o’i bayan kiwo a tsakanin matasa cikin manyan biranen Nijar da makobtansu, irin Mali da Chadi, ya sanya wa Ibrahim Sarhamukwadayin barin gida domin neman na kai. Ya kuma roki mahaifinsa da ya ba shi dabbobinsa ya yi jari cikin tarin dabbobinsa, ya ce ba zai taba raba shi da kiwo ba, amma zai ba shi wani abu daga ciki, sannan zai ci gaba da yi masa kiwon rabi kafin ya dawo. Kiwon dabbobi da rakuma shi ne abin da suka gada daga iyaye da kakanninsu, ko bayan ransa bai yarda su watsar ba. Ko ba ya nan kannensa za su yi masa a Tessoua.
Ibrahim Razee ya shiga Yamai (Niamey) da kafar dama. A lokacin da matasa daga kowanne sassa na Africa ke silalowa cikinta, sakamakon (territoire de la capitale) wato capital territory da aka yi mata bayan Faransa ta ba su ‘yancin kai ranar 3 ga watan Agusta 1960.
Kasuwanci iri-iri ya gwada a kasuwar Nouhou market, inda daga karshe na hatsi wato kayan abinci shi ya fi karbarsa. Ya je garin Zinder duk kan sana’arsa ya ga Kasisi ya aure ta, ya tafi da ita Yamai. Sai da Kasisi ta yi haihuwa biyar ya auri Bintou, ita kuma daga Arlit. A lokacin mahaifinsa ya jima da rasuwa, lokaci-lokaci yana zuwa gida ya ga ‘yan uwansa da mahaifiyarsu, wadanda duka sun yi aure sun hayayyafa a can su ma, Yahayya shi ne ya gaji mahaifinsu wajen bada karatun buzu, shi ne kuma yake rike da ragamar gidan da sana’arsa ta kiwo. Duk da a lokacin Ibrahim bai yi wani karfi ba a hakan yana taimaka wa ‘yan uwansa sosai.
Wani zuwa da ya yi da iyalinsa bayan auren Bintou da haihuwarta ta fari, ya tarar da rasuwar mahaifiyarsa.
Wannan karon tunda ya bar gida ya dukufa neman na kai, ya mallaki karamin gida a unguwar (Liberte), unguwar talakawa ce a Yamai. Zamani na kara habaka, masu sana’ar kayan abinci suka gane wa sabuwar hanyar shigo da shinkafa da sauran kayan abinci na alkama irin su macaroni, taliya daga kasar Faransa zuwa manyan biranen Nijar ba Niamey kadai ba. Sai dai ita din ta zame musu cibiyar kasuwancin. Wannan shi ne silar arzikin Malam Ibrahim Sarhamu Razee da tarihin zamansa a babban birni (Niamey), kuma asalin su Aalimah, iyaye da kakanninsu.
*****
A Yamai Zulaiha ta haifi danta na fari, wanda Ishaq ya radawa sunan mahaifinsa ‘IBRAHEEM MU’AZZAM’, shekarar Mu’azzam daya Ishaq ya samu aikin da ya kai shi kasar Amurka a Niger Consulate America. Suka tattara suka koma kasar Amurka shi da iyalinsa.
Ya jima yana aiki a consulate na kasarsu kafin hanyoyi su bude masa sosai, ya koma karkashin siyasar gwamnatin kasar mai tabbataccen aikin gwamnati a hannunsa, ya ajiye aikin consulate a gefe ya zama dan kasa mai zaune da cikakken lasisi. A can ya haife sauran yaransa hudu daya bayan daya; Abulkhairi, Basma, Khalisat da Yasmin. In ka hada harYayansu haifaffen Yamaisun zama su biyar kenan.
Bayan dawowarsu Amurka Mummy Zulaiha ta ci gaba da karatu, inda ta yi digirinta a fannin tsimi da tanadi (Economics). Yanzu haka MummyZulaiha Raazee ma’aikaciyar banki ce da (JPMorgan Chase). Girman kai da fadin raisai abin da ya karu cikin halayenta. Al’adunta duk sun juye sun zama na al’ummar da ta ke zaune da su.
A hakan kuma ta raini ‘ya’yanta mata guda uku, mazan kam Babansu na matukar kokari a kansu, a halin yanzu yana jan su a jikinsa yadda ya kamata.He’sspending most of his leisure time with them yana dora su a kan tafarki mai kyau tun bayan mummunar kaddarar data shigo rayuwarsu. Da ma an ce ‘ya mace ta Uwarta, Da namiji na Ubansa.
Suna daukar lokaci ba su je Yamai ba, amma in suka je din suna jimawa. Suna kuma zuwa Kano wajen dangin Mummy, saboda mugun hali irin na Zulaiha ko nata dangin ba ta ja a jikinta, ba ta taba daukar wani nata ta kai inda ta ke ba. A haihuwar Basma ne shi Ishaq ya biya wa mahaifiyarta da Yayarta da Inna Bintou suka je, Inna Kasisi ta ki zuwa, don ba ta son duk wani sha’ani da zai hada ta inuwa daya da Zulaiha, zuciyarta ba za ta dauka ba.
*****
3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM - Buhainat: 🌹 *Aalimah**🌹
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI**
07030137870
FREE PAGES 3
MANSOUR RAAZEE
Sanda Yayansa Ishaq ya koma gida Yamai, shi kuma jami’ar ta rike shi don ya yi mata aiki bayan kammala hidimar kasarshi. Ya je ya ga iyayensa, ya kuma gaya musu samun aikinsa a inda ya yi karatu, atafau Inna Kasisi ta ce ita ba ta yarda ba, tunda babu Ishaq ya dawo gida ya nemi aikin ya yi aure. A nan yake gaya musu ya samu mata a Zaria abokiyar karatunsa. Nan ma Inna Kasisi ta yi tsalle ta dire ta ce ba ta yarda su kara yo mata wannan auren ba, ga Zulaiha nan da aka auro ba dadinta suke ji ba.
Mansour, ba shi da abin da zai ce da mahaiafinsu a duniya sai Allah ya ji kansa, ba don ya mutu ba. Yadda yake din bai yi karatun zamani ba, amma wayewarsa da rayuwa da yadda yake tafiyar da tsarin rayuwarsa babu matsi babu takura ga ‘ya’yansa, in har ba addini suka kauce wa ba, wane wani Farfesan. He is very soft on them (shi mai tausasawa ne a garesu). Shi ya tsaya masa ya auri ‘Aseeya’ diya ga shugaban jami’ar na wancan lokacin.
Aseeya ‘yar ajinsu e wadda ta fi duk ‘yan ajin kankantar shekaru. Babanta V.C, uwarta Dr. duk a jami’ar Ahmadu Bello. Asalinsu ‘yan Maiduguri ne daga kabilar Margi, aiki ya kawo mahaifinta A.B.U Zaria inda mamanta ta yi doctorate dinta a Microbiology, ta fara lecturing a nan itama, shi kuma yana matsayin V.C.
A nan cikin A.B.U aka haife su ita da Yayanta Suraj, ajinsu daya ita da Mansour Raazee a tsangayar aikin jarida.
Da fari haduwar jini ce tsakaninsu da aron note da yin tutorial in jarrabawa ta matso wanda ya rikide ya koma soyayya tsantsa. Tun abin bai yi nisa ba iyayenta suka so su dakatar kasancewar Mansour bakon haure. Suna tunanin watarana zai dauke musu ‘ya, ya mayar kasarsu.
Amma da Malam Ibrahim Sarhamu Razee ya tako da kansa tun daga Niamey shi da manyan ‘ya’yansa Oussama da Edrissa suka zo har Maiduguri nema wa dansu auren Aseeya, Prof. Kashim, kasa badawawannan farin ba’abzinen dattijon mai kama da Larabawan Hijaz kasa a ido ya yi, sabida haiba da kamalarsa. Ya kuma yi duk iya binciken da zai yi a kan Mansour, inda ya tarar asali kam sai dai ya gaya wa Aseeya, tun kafin zuwan Malam Ibrahim.
Ba da jimawa ba aka yi auren Aseeya da Mansour, suka tare a gidansa da jami’ar ta bashi, shekara na zagayowa ta haifi Da namiji, ya sa masa suna Aboubacar.
Sai da Aboubacar ya shekara bakwai aka haifi ‘AALIMAH’, ita ma sai da ta shekara biyar aka fara yi mata kanne; Sultana, Suhaima da Sabrina.
Har inda yau ke motsi Baban Aalimah Malamin jami’a ne mai matsayin Dr., Amma sun bar Zaria sun koma jami’ar Bayerota Kano bayan rasuwar mahaifin Aseeya, wato Prof. Kashim, mahaifiyarta ta koma Maiduguri cikin danginta.
Wannan ya tayar da hankalin Aseeya ta ce ba za ta iya ci gaba da zama cikin A.B.U ba, tana kallon kofar gidan da iyayenta suka rayu, hakan yana dawo mata da memories na rayuwarta tare da su. Har sai da ta samu matsala a kwakwalwarta (anxiety). Duk son da Mansour ke wa A.B.U haka ya barta ya koma Bayero don kwanciyar hankalin maidakinsa.
A sannan ne suka fahimci wani babban jigo nasu a Nigeria ya fadi (Prof. Kashim), ta ajiye aikinta da ta ke yi a gidan talbijin, sai abin da Mansour ya kawo, kusan komai da ta saba na rayuwarta dainawa ta yi. Da aka raba musu gado ta yi wa nata adani sosai a banki da wani kuduri a zuciyarta.
Yana kai ta Maiduguri akai-akai wajen mahaifiyarta da danginta, kuma suna zuwa Yamaiwajen nashi iyayen a duk sanda suka samu hutu.
A sannu Inna Kasisi ta fahimci Aseeya ba halinta daya da Zulaiha ba, they are totally opposite in every aspect.
Sonsu ta ke da zuciya daya, tare da girmama ko da kare ne in dai daga Nijar ya fito, sabida son da ta ke wa mijinta,. Yayanta Suraj ya bar kasar tun mahaifinsu na raye, tun daga zuwa karatu a kasar Canada ya yi zamansa a can musamman da mahaifinsu ya rasu, mahaifiyarsu ta koma Maiduguri, bai kara sha’awar dawowa Nigeria ba.
*****
Aalimah tun suna kanana suka taso da fahimtar cewa, mamansu is a mental patient, sannan suka fahimci Babansu na tsananin sonta. Tana daukar lokaci lafiya kalau don tana kan shan magani, amma in abin ya tashi ba Babansu kadai ba su kansu suna jin jiki. Babu duka babu zagi sai kuka. Za ta kwana ta wuni tana kuka kamar ranta zai fita babu gaira babu dalili. Ta bar shiga komai nasu, ta bar yi musu girki. A irin wannan lokacin Babansu ke yi musu komai; wanka, girki, shirin makaranta, wankin uniform da dukkan hidimar da uwa ke yi wa ‘ya’yanta.
Da Aboubacar ya soma hankali shi yake kula da Maman. Baban ya kula da su ita da su Sultana. A haka suka taso da wata irin shakuwa matsananciya tsakaninsu da Babansu, Mamansu tana da tsauri a kan tarbiyyarsu, hakan ba ya nufin ba ta sonsu, amma tana da zafi. Ba su nemi komai sun rasa ba, amma ba su da wadatar da sauran ‘yan uwansu na Yamai ke da shi.
Babansu bai dogara da komai ba sai albashinsa, sannan ba shi da halin rokon ‘yan uwa wai don sun fi shi wadata. Ya dogara da kansa ya tsare wa iyalinsa komai na bukatun rayuwa daidai misali, irin na kowanne cikakken dan boko. A halin yanzu Dr. ne shi a jami’ar Bayero a tsangayar kimiyyar sadarwa.
Aalimah na matukar son zuwa Yamai, ta iya harshen mahaifinta sosai don kusan duk wani hutu mai tsawo a can ta ke yinsa. Inda za ta hadu da ‘yammatan family sa’anninta su Balkissa ‘ya’yan Kawu Oussama su yi ta dabdalarsu tun suna yara. Ko a cikin jikoki Aalimah ta daban ce a wajen Kakansu. Sakamakon ita kadai ya sanyawa sunan mahaifiyarsa.
Yana sonta son da ba ya iya boyewa, kowa ya kwana da sanin hakan a familyn, Aalimah ce ta gaban goshin Mallam. Kuma shi ya zaba mata wannan suna na Innarsa (Aalimah) wato mai ilmi.
‘Margi’ da ‘Abzin’su suka hadu suka haife Aalimah, don haka na bar wa mai karatu ya siffanta kamannin Aalimah Mansour yadda yake so. Babu wanda ya damu da yin wani abu wai shi auren zumunci a wannan family kowa yana kawo wanda yake so ne ya aura, don haka babu rikici babu rashin fahimta, kansu a hade yake kamar tsintsiya. Sai dan abin da ba a rasa ba, wanda ba ka rasa shi a kowanne extended family, shi ma ya fi yawa a tsakanin faccaloli (matan ‘ya’yansu), amma jikokin gidan da ‘ya’yan gidan kam kaf dinsu kansu a hade yake.
Haduwar Aalimah da Mahmoud ta faru ne tana ajin karshe a sakandire ta staff school inda ta yi sakandire. Mahmoud abokin Yaya Aboubacar ne, tare suka yi karatu a nan B.U.K. Mahmoud bakatsine ne, wanda ya fito daga karamar hukumar Kaita ta jihar Katsina.Da suka zo yin hidimar kasa aka kai shi wata makaranta da ke daura da sabuwar jami’ar Bayero.
Daddyn su Aalimah ya san irin abotar da ke tsakanin Aboubacar da Mahmoud, don haka da Aboubacar ya zo yana nemawa Mahmoud alfarmar zama tare da shi a nan boys quartersdinsu wajen mahaifinsu, Daddyn ya amince, amma kuma ya ce masa ya gaya wa Mahmoud dokarsa ita ce; karfe tara na dare yake rufe gida, in ya amince ya zo ya zauna babu laifi.
Zaman Mahmoud Kaita a gidan Dr. Mansur Razee zama ne na aminci. Ya samu iyalin Dr. mutane masu karamci, tarbiyya, tsantsar ilmi da son junansu. Dole duk wanda ke gaba da kai a haihuwa ka ce masa ‘Yaaya’, ka dinga respecting dinsa. Wannan ne babba abinda ya ja hankalin Mahmud ga son hada jini da iyalin Dr. Mansour Raazi. Tsakanin Daddy da yaransa auzinanci suke yi ko yaren Temachekwato harshen Inna Kasisi, Mama ce kadai ke musu Hausa da Turanci. Wani lokacin ma tana musu Margiduka ba wanda ba sa ji. Duka yaran gidan sun saba da shi, suna kula shi kamar Yayansu Aboubacar, banda Yayarsu Aalimah.
Wata mutum guda daya a gidan Dr. Mansur Razee mai wani irin halina seriousness irin na Babanta. Ba ta da hayaniya, ba ta da sakin jiki da mutane. She’s very authoritative ga kannenta, kuma sosai suke jin tsoronta. Shi kansa Yaya Aboubacar wani lokacin sai ya ji tana commanding dinsa. Abin yana ba shi dariya sosai. Kafin ya ankara, ya zama infatuateda kan Aalimah,so much so that, in ya wuni bai ga giftawarta ba, sai ya yi ta zarya kamar zararre a cikin gidan ko ya tambayi Sultana cikin hikima. Sau tari yarinyar kan ce masa, ‘karatu ta ke yi’, kuma ‘ba’a yi mata magana in tana karatu’. Ta hakan ya gano cewa; karatu is the best hobby for Aalimah, kuma da shi zai yi amfani ya jawo hankalinta gare shi.
Aka yi sa’a Aboubacar ya tafi Yamai a safiyar wata litinin zai halarci daurin auren daya daga cikin cousins dinsa dan Kawu Saddam wato jikan Inna Bintou. A ka’ida kuma Aboubacar ke yi musu extra lesson kullum bayan sun dawo daga islamiyya wadda ita ma a nan cikin New Site ta ke, don haka Daddy ya dora alhakin koyarwar a wuyan Mahmoud kafin dawowar Aboubacar.
Wannan shi ne mafari, mafarin soyayyar Aalimah da Mahmoud Sulaiman Kaita.
Ta samu Mahmoud irin mazan da ta ke burin aura, wato yaro dan boko mai kwakwalwa da nunawa macen da suke so soyayyah a fili kamar duk duniya ba wata macen sai ita. Kafin dawowar Aboubacar sun shaku fiye da zato, sai daga baya ya fahimci ko me suke ciki.
A zuciyarsa ya yi musu fatan alkhairi, amma a fili ya dora wa mu’amalarsu ido, har ya fahimci tsaftacciyar soyayya ce suke yi wa juna, Mahmoud ba yaudarar kanwarsa yake da niyyar yi ba, har ya gama hidimar kasarshi ya koma garinsu Katsina, shi da Aalimah remains in contact ta wayar Yaya Aboubacar ba tare da sanin Mama da Daddy ba wadanda ya san ba za su taba amincewa aurar da Aalimah a daidai wannan lokacin da ko sakandire ba ta gama ba, shi kuma yana son abokinsa da Aalimah don ya san in har ta aure shi to ta yi miji, wanda zai rike masa ita da daraja da mutunci har karshen rayuwarta.
Dalilinsa kenan na kyale su suka ci gaba da contacting juna ta wayarsa. Don Aalimah a lokacin Iyayensu basu bata damar mallakar waya ba. Bayan komawar Mahmoud garinsu, ba da jimawa ba ya samu aiki da hukumar zabe ta kasa a can Katsina, ita kuma Aalimah ta gama jarrabawar fita sakandire a shekarar. Ba jimawa sakamakonsu ya fito, tana daga cikin zakarun gwajin dafin da (BUK staff school) ta yaye a shekara ta 2015.
A wannan lokacin ne Maman su Aalimah wato Aseeya ta samu mijinta da takardun banki,mai dauke da sunanta na fixed deposit account da ta bude da gadon mahaifinta. Kudi ne zunzurutu da a iyakacin rayuwarsa bai taba mallakar ko da rabinsu ba. Ta gaya masa kudurin da ta ke da shi, wato tana son kai Aboubacar karatu jami’ar da mahaifinta marigayi V.C ya yi a kasar America. Tana so Aboubacar ya gaji Babanta. Watarana ya zama kamarsa....as the only male child she have (a matsayin sa na Da namiji daya kwal data mallaka).
Murmushi Daddy ya yi ya dube ta sosai cikin idanunta, sannan ya soma magana.
“Aboubacar bai da sha’awar hakan, bai da sha’awar ilmi mai zurfi,abinda yake mafarki kawai(is to become a banker), amma kina da wani dan, da zai iya cika miki wannan burin. Amma fa in za ki kauda kowanne irin tunani ki bada kwarin gwiwa�.
Da mamaki ta ke kallonsa,
“Duk ‘ya’yana mata ne Daddy, he’s the only male one....�.
“… Mace ma mutum ce!�
Ya yi hanzarin katse ta.
“…Amma me rauni�. Ta ba shi amsa.
“Idan za a yi ta kallon rauninta ba za’a ba ta damar bada gudunmawarta ga al’umma ba. Musamman in aka fahimci cewa tana da motive a kan neman ilmin. Don haka in har amincewa ta da shawara ta ki ke nema, to Aalimah ce za ta tafi karatu ba Aboubacar ba. Shi ya ci karfin duk wani karatu da zai yi a gaba, tunda yana da kwalin degree. Duk wani abu da zai kara karantawa a gaba ado ne kawai ga na baya�.
Mama ta yi shiru tana tunani, kafin cikin sanyin jiki ta ce,
“Daddy ka fahimce ni, ba kasancewar Aalimah mace wajen karatu ne abin dubawa ba. Yadda tafiyar mace wani waje bata halatta ba tare da muharrami ba. Aalimah ba mu yi mata aure ba, mu dauke ta mu kai ta kasa irin America mu ajiye mu ce ta yi karatu babu idon kowa a kanta babban kuskure ne duk irin tarbiyyarta.
Ubangiji ma sai ya tambaye mu. Na sani bokonka mai zurfi ne, irin wanda ke hana ku daukar hakan da muhimmanci, amma hakan zai zama mana damuwa a gaba, kada garin neman gira a rasa ido�.
Ta karasa cikin karyewar murya.
Murmushi Dr. Mansur ya yi ya ce,
“Na fahimce ki, na kuma fahimci abinda kike so na fahimta, ni ma ba zan amince ta zauna a hostel ba, hannun Yaya Ishaq zan damka ta. Ta zauna cikin iyalinsa.
Fadamiki ne ban taba yi ba, ya sha cewa in ba shi ita ya hada da yaransa su Basma ya rike ina cewa, sai ta gama makaranta. Ni ma kuma akwai nawa tanadin da na dade ina yi don haka kudin nan naki ki yi tunanin business din da za ki fara da su, ni zan dauki nauyin makarantar Aalimah�.
Nan Mama ta nuna ba ta yarda ba, ta san ba shi da wannan halin, amma ya ce ta kyale shi.
Abinda Mama bata sani ba shine;Federal Scholarship ne ya samo mata ta hanyar wani abokinsa shugaban scholarship board na kasa, tare suka yi karatu, wato Dr. Obi Olayinka. Da mama ta dage tana so ta bada tata gudummawar sai ya ce, to ta saya mata ticket, amma duk sauran shirye-shiryen Babanta ne ya yi mata.
Sai da komai ya kammala, admission da komai, sannan ya kira dan uwan nasa ya sanar da shi komai. Ishaq din ya ce da bai yi wahalar neman scholarship din ba ma ya yanke shawarar sanya su ita da Basma daga aljihunsa a wannan shekarar, amma tunda ta riga ta samu shi kenan ya sako ta a jirgi ta taho.
Ranar da Aalimah za ta taso kuma tafiya ta kama shi daga office dinsu zuwa California zai kwana daya, don haka ya tura wa Dr. Mansour adireshin gidan nasa, ya ce ta dauki drop har gida.
Zulaiha tana wajen aiki sanda za ta iso, yaransa maza kuma duk ba sa gari. Wannan shi ne tarihin su Aalimah da asalin tahowarta kasar America. Kafin ta taho ta je Maiduguri da Yamai ta yi sallama da kakanninta da ‘yan uwanta. Inna Kasisi kam abin bai yi mata dadi ba ko kusa, yadda ba ta son rabar Zulaiha, haka ba ta son kowa nata ya rabe ta, balle Aalimah wadda ko a cikin jikokinsu ita ta daban ce, mai kyakkyawar tarbiyyah da sanin ya-kamata. Suna ji da ita fiyeda sauran jikokinsu. Tsoronta Allah tsoronta kada ta koyo dabi’un ‘ya’yan Zulaiha da kullum ke sanya ta cikin takaicin wai cikin zuri’arta suke.
*****
Aalimah, ta ja dogon numfashi a yayin da tunaninta ya zo nan, tana kallon su Basma na shigowa falon, babu kamannin ‘ya’yan Auzinawa ko na Malam Bahaushe ko kadan a tare da su, sun fi kama da ‘ya’yan kasar Somalia. Fatar Babansu da ta mamansu bahaushiya ta cakude ta ba su wata irin colour da complexion mai ban sha’awa. Ga su da tsayi da mulmulallen jiki tubarkallah. Sunshades a idanun Basma da Khaleesat, dogayen wandunan jeans na mata da rigunan Armani collection a jikin kowaccensu. Khaleesa ta kusa kamo Basma a tsayi, babu dankwali a kansu gashin Abzin din ya kwanta a kafadunsu.
Basma a gaba, sai Yesmin biye da ita, sannan Khaleesa, Aunty Zulaiha da Daddy suka biyo bayansu.
Tsayawa ta yi a kofar kicin din ta harde hannayenta a kirjinta tana kallonsu da murmushi irin na ‘yan uwantaka. Khaleesat ce ta fara ganinta, ta zare sun shade dinta ta mutstsika idanunta ta ce,
“Daddy, am I dreaming? She looks so much like Aalimah�. (Daddy Mafarki nake yi? Ta yi kama sosai da Aalimah). Sannan ne hankalin kowa ya kai gare ta.
Aunty Zulaiha kam shaf! Ta manta da zuwanta, sai yanzu ta tuna. Take fuskarta ta sauya, ta wuce upstairs kai tsaye.
Basma ta yi cilli da jakarta ta yi kanta da dan banzan gudu, saura kadan su sha kasa su duka biyun, tana kakabin murna. Daddy ya wuce kujerun falon ya ajiye suitcasedinshi, yana rike da falmaran din suit din jikinshi. Gogaggen dan boko wanda ya ga jiya a Amurka yake kuma ganin yau, ga furfura nan tsilli-tsilli a kanshi, amma tsammani za ka yi Balarabe ne ba ba’abzine ba. Dogon hancin nan zur! Kamar na Babanta.
Kujera ya samu ya zauna a gajiye yana kallon Aalimah da ke tahowa, Basma da Khaleesa sun sako ta a tsakiya har gabansa, sun bi sun rirrike hannunta, bakinsu kamar zai tsage don farin ciki, kan kujerar suke kokarin zaunar da ita kusa da Daddyn, amma sai ta zame ta zauna a kasa daura da kafafunsa ta soma gaishe shi cikin harshen Hausa.
Cewa yake, “Tashi-tashi ‘yata ki zauna a kujera, kin sha hanya. Ki yi hakuri I couldn’t make it taking you from airport, I went to California for a meeting, dawowata kenan. Ina fatan kin ci abinci kin huta?�
Murmushi ta yi, ta ce,
“Babu damuwa Daddy, kuma na ci abinci�.
Ya kalli Basma ya ce, “ Basma bani jakar can�.
Ta dauko jakar ta kawo masa babu ko russunawa kamar ta mikawa sa’anta, Aalimah ta ji wani iri a ranta. Budewa ya yi ya fiddo wasu takardu ya mika wa Basma, ya kuma mika wa Aalimahn wasu irinsu. Ya bawa kowaccensu biro ya ce ta sanya hannu karkashin dokokin jami’ar da za su je. Sai a lokacin ne Aalimah ta ga admission letter dinta da kwas din da Babanta ya zaba mata.
Zukar numfashi ta yi ta fesar, tana rokon Allah ya fidda ita kunyar iyayen ta, ta sha ji a bakin Yayanta Aboubacar how complicated pharmacy is (tsaurin kwas din harhada magunguna) lokacin da Daddy ya ce ya karanta shi don shine abinda Kakansa Prof. Kashim ya karanta ya kuma zauna akan (proffessorial chair) dinsa har mutuwar sa, ko don ya farantawa Mama, Aboubacar ya fitittike ya ce shi ba zai iya ba, Accounting yake so.
Nasiha sosai Daddyn ya yi musu a kan su tsare mutuncinsu, su maida hankali kan abin da ya kai su. Bai yarda da yin saurayi ko friendship da maza ba, duk kuma ranar da ya ga hakan zai cire kowaccensu ne ya yi mata aure. A karshe ya yi musu addu’a, ya gaya musu jibi za su fara registration.
3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM - Buhainat: 🌹 *Aalimah* 🌹
*
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
FREE PAGES 6
Ta jima a jikinsa tana ba shi hakuri, sannan ya ce ya hakura, amma in tana son zaman lafiya ta daina kawo masa wadannan sababbin halayen da ta billo da su, kuma ta zauna lafiya da Aalimah don zamanta daram a gidansa, tunda ba tare suka hada kudi suka sayi gidan ba. Duk ta ce ta yarda, sannan suka yi dan gajeren romancing dinsu suka fito, suka tadda yaran duk sun sha wanka sun shirya gwanin sha’awa. Daga Basma har Khaleesat kayan Aalimah ne a jikinsu. Sun dan matse su sabida duk sun fita garin jiki. Don ma dai manyan riguna ne dinkin Nijar. Ta hadiye wani abu da ya tokare ta a wuya, ta kama hannun Yesmin suka fita. Ta dauka motarsa zai nufa ya shiga ya tafi inda za shi, sai ta ga ya ce duk su shigo tashi motar.
Mummy kamar ta yi kuka don ya rushe duk wani plan da ta shirya. Ta shirya a ranta ba wani traditional wears da za ta saya musu, kuma ba za ta sai wa Aalimah wani abin kirki ba, kwancen su Basma za ta dawo ta tattara mata. Ta san ba shi da sanya ido, ba abin da zai fahimta. Amma yanzu ta san ya ruguza komai.
Chevrolet din Daddy suka shige dukkansu. Ya zauna a mazauninsa ya sanya belt, sannan ya tsaya yana dan duba abu a wayarsa,da alama adireshin inda zai je yake dubawa a yanar gizo. Sannan a tsanake ya dauki hanya. Aalimah sakin ido da baki da hanci ta yi sosai tana shan kallon birnin Boston, don tunda ta zo ban da makaranta, babu inda ta ke zuwa.
Su Khaleesa na ta hira a tsakaninsu ba ta sa musu baki ba, wani lokacin ma ba sosai ta ke fahimtar maganganunsu ba, sabida yanayin accent dinsu. Sun iya Hausa, amma ba sa janta da nisa, wato jefi-jefi suke yinta. Ta lura Mummy ba ta da walwala sosai tunda suka taho duk da Daddy na yi mata hira. Tafiya suke sosai kamar za su bar cikin gari, kafin Aalimah ta ga sun hau wani titi da aka rubuta Newbury street Boston. Sun yi tafiya sosai a cikinsa kafin su karkata ya yi parking a kofar wani katafaren shago a samansa an rubuta Riccardi. Tunda Mummy ta fahimci shagon African Germents ne na maza da mata ta sake gyara zamanta cikin motar tana duba Ipad dinta.
Daddy ya dan dube ta ya ga ba ta da alamar fita sai ya mika mata hannu ya ce,
“Give me the credit card�.
Ba musu ta dauko a jakarta ta ba shi abinsa.
“Ba kya bukatar komai?� Ya sake tambaya cikin kwantar da murya.
Ba tare da ta dube shi ba, ta ce,
“A nan dai babu, su shiga su fito�.
Ya kada kai ya bi bayan yaransa wadanda har sun shige shagon sun hau elavator. Abubuwa kadan suka tsitstsinta a Riccardi don kayan maza na Africa sun fi yawa. Basma ta ce, Daddy ya kai su wani shagon again. A cikin mota ya zauna ya kira waya ya yi magana da wani abokinsa dan Nigeria, mutumin ya hada shi da matarsa suka yi magana, sai ya ja motar. Wannan karon kan titin Harrison Ave Daddy ya shiga.
Tun daga nesa Aalimah ta hango dogon ginin da ya tabbatar mata wannan karon su Basma za su samu har ma fiye da irin kayan da suke so. Daddy ya yi parking a parking lot suka firfito, wannan karon ma banda Mummy, Aalimah, ta daga kai tana karanta sunan shagon, ‘ZAINAB SUMU PRIMITIVE MODERN’. A cikin shagon nan su Basma sun yi siyayyar kaya da jewelleries har da na banza. Da ta ga Aalimah ta ki daukan komai ita da kanta ta dinga daukar mata duk abin da ta daukar wa kanta. Sai dai tana bambanta colour. Ta fahimci Aalimah na son ‘dark colours’ sabida kalar fatarta don haka komai ta daukar wa Aalimah mai turuwa ne sosai, sai ta daukar wa kanta lighter one. Hatta Yesmin sun gwangwajeta da kayayyaki daidai jikinta, sun samu kaya iri-iri, na Nijar, na Najeriya, na Senegal, na Arab da na D’jbouti. Daddy shi yake nuna musu wasu ma ya ce su kara. Sai da Khaleesat ta ji tausayin creditcard dinsa, ta ce su barshi haka, amma shi ko a jikinsa. Ya basu suka zare kudin komai, za su fito kenan wani Bature ya biyo su da gudu ya ba su wani littafi yana tallata musu malldin The Germent District, ya tabbatar musu za su samu shagon beyond their expection, za su ji shi kamar suna cikin Africa in dai batun tufafi ne. Basma ta ce a je, Khaleesat ta ce, sai dai wani lokacin, Aalimah ta ce su tausaya wa Daddy su barshi haka. Hannu ya dora a kan kafadunta ya bubbuga.
“If you like atamfa, lets go Aalimah, kada ki ji tausayin wannan Daddyn he loves you more than his money�.
Dariya suka yi suka shiga mota suka tafi. Aalimah dai ta kafe a barshi haka sai wani lokacin. Ganin ta dage suka yarda.
Sai da suka yi nisa Mummy Zulaiha ta yi gyaran murya, su kam har sun manta Mamansu na cikin motar saboda rashin motsinta. Daddy ya dan dube ta ya maida idonsa kan titi. Duk kokarinsa na fahimtar matarsa ya kasa. Ta zame masa ‘alqibla-less’. Ta dan motsa dan kyakkyawan bakinta tana magana, “Mu shiga kasuwa daBURLINGTON MALL zan yi cefane da tawa siyayyar�.
Bai ce komai ba ya karkata kan motar ya nufi kasuwar da ta fada, su suka taya Mummy da tura sayayyar da ta ke yi a shopping bag, har ta gama cefanen kayan abinci kala-kala nau’i-nau’i suka sa a bayan mota. Daga nan sai suka wuce Burlington Mall din ta yi ta sayayyar kayan gayunta, su ma ba a barsu a baya ba duk wani abin amfani na mata na tsaftar jiki da kayan shafa da kamshi sun saya, Daddy na ta biya, sannan suka taho gida.
Kafin su iso gida Mummy ta saki rai sosai tana ta jan mijinta da hira, su ma yaran tana kula su har Aalimah. Shi dai kallonta yake yana mamakinta. Ta zame masa kamar wata mai ‘Multi personality disorder’ yanzu ta ke daidai anjima za ta koma wata majanuniya. He loves his wife as such! Wato yana son matarsa a duk yadda ta ke. Take-away suka yi na KFC kafin su shiga gida don already dare ya yi, kuma duk yunwa suke ji mai girkawar ma Mummy ta gaji tibis. Tun a lokacin ta soma regrettingkorar Easther da yanzu kafin su dawo sun tadda komai yana jiransu a kan dining. To wai ma da ta yi gaggawar korar Easther how sure is she (wane tabbaci ta ke da shi na cewa) Aalimah ta iya girkin da za su iya ci har mijinta? Damuwa karara ta bayyana a kan fuskarta har suka shiga gida.
Kafin su kwanta, suna zaune a falo tare da yaran, Daddy ya ce, “Zulaiha ina tunanin daukar wa yaran nan driver, Basma ba ta kai shekaru sha takwas baballe ta dinga tuka su. Duk da Aboulkhair is coming for his holiday next month bana jin zai juri jigilar kai su da dauko su da wannan baccin safen nasa. Hanya ta da tasu are parallel (sun baude) ina makara most often (sau-tari)�.
Da sauri Mummy ta ce, “Ka san bana son strangers Daddy, ka bar zancen daukar driver din nan don Allah. Ni zan dauki nauyin kai su da dauko su dukkaninsu. Na gama course din da office suka sanya ni yi a Worcesterkarfe hudu zan dinga dawowa, kuma zan zauna wata guda a gida kafin na koma office so I will take care of their transportation�.
Cike da gamsuwa ya gyada kai sannan ya dago ya dube ta yana murmushi.
“Promotion in progress… Ummu Mu’az, wannan karon ya kamata a cire min parcentage, kudi sun yi miki yawa matar nan kuma ba mai ci, ke kanki ban ga kina ci ba�.
Dariya ta yi cikin nishadi ta kada masa kyawawan idanunta,
“Kai ma ka san wa nake tarawa.
I want him to own a lodge in one of the America’s most expensive luxury condos. Be it in San Francisco, Miami, Los Angels, Dallas, Seattle, New York, Oahu, Ohio, Chicago, nan Massachusetts, or wherever he like. A penthouse; irin wanda ko a garuruwan nan dana ambata sai dan gata zai iya mallaka. Ka san Allah Daddy ba don kaina nake wahalar aikin nan ba. I’m doing it for “MU’AZZAM� da lafiyarsa, tunda na lura shi in don ta shi bai damu ya tara komai ba.
Abin da ya sani kawai shi ne, ya yi ta bautawa wannan aikin nasa, yana karar da kudin a gidan haya, bayan wannan ban san me Mu’azzam ke yi da kudin da yake samu ba. I’m sometimes wondering he belongs to CHEVRON (wani lokacin ina tababar kasancewarsa ma’aikacin CHEVRON)�.
Murmushi sosai Daddy yake yi yana sauraronta da mamaki. Ba tun yau ba ya sani, Mu’azzam is her favourite childcikin ‘ya’yanta, amma bai taba sanin abin ya kai haka ba. Ta ci buri mai girma a kansa.
Wato duk tsayin shekaru goman nan da ta dauka tana aiki da JP Morgan Chase yana mamakin me ta ke yi da kudinta, tunda duk bukatunta babu wanda ta taba dauke mishi, sannan ya san ba iyayenta ta ke kaiwa ba, don shi ne ya gaji da ganinsu cikin tsohon gidan da suke ciki ya sauya musu, hatta petir din da za ta zuba a mota yana wuyansa, ashe this is her dream! Gyara zama ya yi sosai ya fuskance ta, ya kira ta da sunanta na yanka,
“Zulaihatu!�
Wannan ya tabbatar mata maganar da zai yin is highly sensitive. Bai damu da amsawarta ba, ya ce, “Ki fidda ZAKKAH, ki yi sadaka, ki kai iyayenki Hajj da duk wanda ya kamata cikin ‘yan uwanki. Sannan ki ninka kyautatawarki gare su.
Ba’a san gawar fari ba, amma use your opportunity when it is in your hands (wani lokaci na zuwa da za ki so ganinsu ko sau daya, amma zai zamo ba sa raye, ki yi amfani da damarki a lokacin da ta ke hannunki). Mu’azzam baya neman agajin ki a halin yanzu, domin ya riga ya tsaya a kan duga-dugansa. Abinda yake bukata daga gareki shine kawai ADDU’A da sanya albarka. And thank Allah the exalted for making you two alive together,which is his foremost success in life(kuma ki godewa Ubangiji Mabuwayi da ya raya ku tare, wannan shine babbar nasarar sa a rayuwa). Wannanita ce shawara ta gare ki a matsayina na mijinki, uban ‘ya’yanki,wanda ya fi kowa kaunarki in an cire iyayenki. Besides, this boy is making a lot of money beyond your expection (ta wani gefen, wannan yaron yana samun kudi fiye da tsammaninki). Yarage naki ki dauka ko kada ki dauka. Ina kara maimaita miki cewa(Mu’azzam ba ya bukatar kudinki don ya tsaya da kafafunsa, abin da yake bukata shi ne, KE din kanki a raye, da addu’o’inki.
Yana gama fadin hakan ya tashi ya hau sama ya barta a nan tana ta karanta wasikar jiki. Tana analysing kalamansa filla-filla.
*****
Kamar kullum washegari suka yi wanka suka shisshirya. Mummy Zulaiha ta zo har dakinsu ta yi kiran Aalimah. Tare suka fita ta nuna mata duk yadda ake amfani da injinan cleaning din gidan, da yadda ake tsaftace shi. Sannan ta tambaye ta ko ta iya girki? Ta ce ba abin da ba ta iya girkawa ba. Sai ta ce, har English meals? Ta ce, ta iya wasu a wurin Mamanta. Sai ta ce, to shi kenan daga yau ita za ta dinga girki da cleaning, mai aikinta ta yi tafiya. Tana kuma son kullum ta gama abincin dare kafin dawowar Daddy. Tana kuma son wannan zancen ya tsaya a tsakaninsu. Incase su Basma za su tambaye ta wani abu a kan hakan, ta ce, ita ta sa kanta.
Aalimah ta yi motsi da bakinta tana so ta tambaye ta makarantarta kuma fa? Amma ganin ba fuska dole ta hadiye. Tun a lokacin ta fara girkin rana bayan MummyZulaiha din ta nuna mata yadda ake amfani da komai.
Ta yi cleaning, ta yi girkin rana, ta yi na dare. Ko na minti biyu ba ta huta ba. Da suka tambaye ta ko me ta ke yi haka tun safe? Ta gaya musu yadda uwarsu ta gaya mata. Ta kara da cewa, Easther ta yi tafiya shi ya sa ta ke taimaka wa Mummyn. Allah ya so tun farko Mamansu ta hore su da komai, ba ta da son jiki ko kankani.
Ranar litinin, wato washegarin ranar,Mummy Zulaiha ta kwashe ‘ya’yanta ta kai makaranta, ta bar Aalimah a kitchen. Mamaki ya kama su har hada baki suke wajen tambayarta,
“Aal, will not go to school Mum?�
Ta lailayo ashariyar da ba su san ta iya ba ta antaya musu, ta kuma ce duk wanda ya kara yi mata zancen wata “Aal� ubansa za ta ci ciki da waje. Ta cire ta daga makarantar don ubansu, su je su gaya wa ubansu su ga yadda za ta ci mutuncinsu. Duk suka yi lakwas. Zaginta da balbalin bala’inta ya fi karfi a kan Basma, ta ce ta san ta fi kowa firirita a kan wata Aal, to in ta isa ta je ta gaya wa ubanta RAAZEE ISHAQ ta cire Aalimah daga makaranta.
Hatta abokan karatun Basma sun fahimci yau ba ta cikin walwala. Wadanda suka damu har tambayarta suke yi, me ke damunta? A gajarce ta ke cewa, “Headache�.
Da yamma motar makaranta ta bi ta koma gida, Mummy ta ce su Khaleesat kawai za ta dinga maidawa gida, she’s old enough ta kula da kanta (Basman).
Ko da suka dawo a kitchen suka tadda Aalimah ko wanka ba ta samu ta yi ba saboda aiki. Har wanki Mummy ta jibga mata don ma dai da inji ne. A ranta ta ce, in kin ji wuya za ki koma inda ki ka fito.
Idanu narai-narai da hawaye Basma da ke tsaye a bakin kofa ta ke kallon Aalimah, wadda duk ta yi gumi ta yi maiko, ta takarkare sai kankarar tukunya ta ke da cokali tana ci, abinci cokali daya wannan Mummy ba ta bata ba, duk da ita ta yi girkin. Tazo ta kwashe shi tsaf ta kai ‘dining’ kuma ta kasa-ta-tsare a falon tana ta ayyukan ta cikin system dinta, bata bari Aalimah ta ganta ba ta bar wurin da sauri ta yi sama da gudu, ta fada gadonta tana hawaye. Me za ta iya a kai banda fada wa Daddy? Babu!
Haka suka wuni dukkansu sukuku da su cikin damuwa da mamakin Mummy. Su dai sun san ko a cikin iyaye tasu uwar is exceptional wajen kyautata wa ‘ya’yanta. Yaushe ta canzazuwa maketaciya?
Rayuwar da suka yi ta yi kenan har tsayin wata guda, sai Daddy zai dawo ta ke cewa ta je ta yi wanka, sai za a zauna cin abincin dare za ta samu ta ci. Amma ba ta da breakfast ba ta da lunch. Sai karshen mako kuma, shi ma don Daddy na gida tana da freedom duk da haka komai ita ta ke yi, bai taba lura ba. Yanayin abincin gidan ne kawai ya lura ya canza, kuma ya fi jin dadinshi a kan na baya. Kuma da yake Allah ya yi shi mutum mara sa ido ko bin kwakkwafi, bai taba tankawa ba. Sakin ciki yake ya ci iyakar cinsa.
Karatu fal! Ya yi wa Aalimah fintinkau, ya wuce ta, an bada assingments har ba adadi ba ta yi ko daya ba. Absentness dinta da ya yi yawa shi ya sa coordinator dinsu da wasu daga cikin course tutors suka ankara. Makarantar ta yi tracingguardian phone number dinta a file dinta suka yi mishi phone call officially.
Ina kwalin digiri da masters din Mummy Zulaiha ya je ta manta da hakan zai faru? Oho! She’s blindly chasing a way to push poor Aalimah from her house. Ta manta an ce rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya.
Karfe biyu na rana Aalimah tana kwashe abincin da ta gama girkawa a warmers, Mummy Zulaiha tana sama bedroom dinta tana barci abinta hankali a kwance. Kuka ta ke yi mara sauti tana share hawaye da hanci da gefen mayafin da ke kanta. Ba tana kuka ne don aikin da Mummy ke jibga mata ba wanda ko makaho ya shafa ya san ya fi karfinta ita kadai, ko kukan yadda ta kasa treating dinta kamar ‘ya’yan da ta haifa ba, tana kuka ne na tausayin kanta da iyayenta. Sun hana idonsu barci, sun yi fafutuka sun kawo ta don ta yi karatu an raba ta da shi a banza a daidai lokacin da ta fara fahimtarsa, kwakwalwarta ta bude ya soma shiga kanta, an maida ta boyi-boyin gida on no reason. Ba ta son zama sanadin kawo commution tsakanin ma’auratan, amma da ta ce da kawunta ya maida ita hostel tunda ita ta fahimci Mummy Zulaiha zamanta a gidan ne kawai ba ta so.
Ba zato ba tsammani sai ganin Daddy ta yi a tsaye a bakin kofa, ya dogara hannunsa na dama da kofar kicin din. Ta yi nisa a kukanta, shi ya sa ko motsin motarsa ba ta ji ba.
Daddy ya jima a tsaye a bakin kofa yana kallon Aalimah ba tare da saninta ba, ba kuma tare da sanin shi kansa mintuna nawa ya ba ta a wurin yana nazarin abubuwan ba. An ce four weeks rabonta da school, ya zo ya same ta tana girki a kitchen. Wannan na nufin duk abincin da suke ci tsawon sati hudun da ya fahimci canzawarsa ita ce ke girka shi? Wannan ne dalilin Zulaiha na korar mai aikinta, ta kuma hana shi daukar driver da ya ce zai daukar musu? Ba ya so ya yardar wa zuciyarsa Zulaiha ta aikata hakan da gan-gan, kuma za ta iya cin amanarsa har haka.
Ba zai yi saurin yanke hukunci ba sai ya ji daga bakin kowaccensu. Shigowa kicin din ya yi ya kama hannunta ya ja ta suka fice daga gidan, kafarta ko takalmi babu. Da fari ta tsorata, amma da ta ga Daddy ne sai ta yi shiru. Kukan ma bakidaya ya dauke. Ta san yau dubun Mummy ce ta cika tunda yanzun ba lokacin dawowarsa ba ne. Za ta yi amfani da wannan damar ta roke shi ya maida ita hostelno matter what. Yau da a ce zama ne ya kawo ta gidan ba karatu ba, she’s willing to do beyond what Mummy wants from her… ita ma uwa ce a gare ta kuma uwarta ma tana sa ta aiki, amma ba ta hora ta da yunwa. Daddy murfin chevrolet dinsa ya bude ya sanya ta a gaban motar, ya zagayo ya shiga mazauninsa a nitse ya fita daga compound din gidan nasa suka hau titi.
Sun yi tafiya mai nisa ba tare da ya ce komai ba, ita kuma ta yi kokari ta daina kukan da ta ke yi ta tsane hawayen idanunta tsaf! Amma kallo daya za ka yi mata ka fahimci ta ci kuka ta koshi, abinka da farar mace, fuskar nan ta yi jazur kamar jini zai fito. Sai daya yi nisa da unguwar su ‘Martha’s Vineyard Real Estate’ sosai sannan ya gangara ya sauka a gefen titi.
Yadda fuskarta ta yi jajawur saboda kuka haka tashi ma ta yi, duk da shi ba kukan ya yi ba. Tsananin bacin rai ne ya maida shi hakan. Ba Zulaiha kadai ya ji matukar haushi ba, har ita Aalimahn. Cikin fada ya soma yi mata magana cikin harshen su Temachek. Ga abinda yake cewa.
“Me yasa baki gaya min ba ta kai ki makaranta ba?�
Shiru ta yi, don ba ta san amsar da za ta ba shi ba. Mummy ba ta bata damar hakan ba, ‘ya’yanta ma sun kasa gaya masa balle ita? Idan ya dawo Mummy kasawa ta ke ta tsare har sai ta tabbatar ya shiga dakin barcinsa ya kwanta. Ko ba don wannan ba baza ta iya hada shi fada da matarshi da ta zo ta same su suna zaune happily da ‘ya’yansu, sannan tun washegarin ranar da Mummy ta ce zata dinga driving dinsu ta karbe wayarta data bata daga cewa za ta debi wasu muhimman contacts dinta da ke ciki, ba ta dawo mata da ita ba, and she lacks the courage to ask her again (bata da karfin gwiwar sake tambayar ta) tunda ta san wayarta ce.
Ko iyayenta da Yaya Aboubacar ba ta kira ba a tsayin kwanakin nan kusan talatin. He trust his wifeso much(ya yarda da matarsa sosai) ta yadda har ya daura mata alhakin kai su da dauko su.Howcould she told him that his wife is a green snake? (Ta yaya zata iya gaya masa cewa matar tasa macijin sari-ka-noke ce?�.
Jin ta yi shiru,sai ajiyar zuciya kawai take yi, sai kuma ya sassauta daga fadan da ya ke yi mata.
“Gaya min kin ji ‘yata Aalimah, me ke faruwa a gidan da ban sani ba? Ya ya aka yi kowa yana zuwa makaranta banda ke? Kada ki ji tsoro ki gaya min ba abin da zai same ki. Sai na ji gaskiya daga bakinki ne zan san matakin da zan dauka�.
Sosai ya ke lallashinta, yadda Daddynta ke yi in yana so ya ji cikinta. Kuka ne ya kufce mata, ta soma yinsa sosai.
“Na roke ka da Allah Daddy ka maida ni hostel, Daddy da Mama zuciyarsu za ta karye, in na kasa yin karatun nan. I’m not here to stay at home. I’m here to study, don Allah Daddy �.
Shiru ya yi zuciyarsa har barbawa ta ke yi sabida bacin rai. Daga bisani ya ce,
“Ina wayarki? Me ya sa ko text ne ba ki yi min ba in kin kasa kira na?�
Cike da fargabata ce,
“Ta karbi wayarta�.
Wuta ta dauke masa na dan lokaci, kafin ya ce cikin sanyin murya.
“I’m sorry my daughter, I failed to fulfill my responsibilities as a father. But that doesn’t mean negligence, it’s because I trust my wife so much on everything, (ki yi hakuri ‘ya ta, na gaza wajen cikasa hakkokina na Uba a gareki cikin gidana, saidai hakan baya nufin ‘sakaci’, a’ah, na yi ne sabida na yarda da mata ta akan komai. Ban taba zaton za ta iya yi min haka ba.
Na san ba ta son mutane, amma ban zaci har haka ba tunda ba yau muke tare ba. Kada ki kara zancen hostel din nan while I’m alive, living in America. In mutane ba su zage ni ba, Allah zai tambaye ni hakkin zumunci. Sai ka kyautata shi za ka shiga aljannah. Give me one last chance...(ki bani dama ta karshe)zan gyara komai�.
3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM - Buhainat: 🌹 *Aalimah* 🌹
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870*
FREE PAGES 5
Tsakaninsa da Aunty Zulaiha babu mu’amala mai dadi, duk wannan soyayyar da ake masa an yi wurgi da ita. Yana tambayar kansa da ma haka ta ke? Ita shin meye matsalarta da zaman ‘yar dan uwansa ciki daya a gidan? Shi ya sha nono ya sakarwa ubanta! Inda hankali da tunani Zulaiha ba za ta yi masa abin da ta ke yi ba don ya kawo ‘yar Mansour gidansa. Wacce irin kulawa ce ba ya bawa nata dangin? Yana son Zulaiha matukar so ta yadda har ake ganin ta fi karfinsa. Amma wannan karon ya sha alwashin motsa kwanjinsa ba zai bari ta juya shi ba when it comes to Mansour. A kan komai ta yi ta yi, amma ban da wannan dan uwan.
Ita da kanta Aunty Zulaiha ta fara gajiya da irin zaman da ta ke yi da mijinta da ‘ya’yanta a kan wata banza Aalimah. Walwalar gidan completely reduced. Ga shi duk yadda ta so ya kwantar da kai ya lallashe ta ya soma ba ta excuses a kan zaman yarinyar tare da su ya ki yin hakan. Ta fahimci ma makarantar da zai kai Basma tare ya kai su wanda ke nuna babu ranar barin ‘yar Mansour gidan.
Dole ta sauke makaman yakinta ta nemi sulhu da shi, maimakon ya ba ta excuses ita ce ta dawo tana bayarwa. Tana gaya masa ita ba danginsa ne ba ta so ba, she don’t want the house to be bulky (bata so gidan ya cika) sannan yaranta za su matsu, dakin ya yi musu kadan, sannan a budget dinsu na abin da suke spendingmonthly babu karin komai, in karatu ta zo yi America ya maida ta hostel za ta fi maida hankali ta yi karatu sosai.
Wannan karon ma banza ya baiwa ajiyarta, yana tauna silly(wawayen) maganganunta a ransa, ko daya babu gamsasshe. Halinta ne dai da ya sani na rashin son mutane ba danginshi kadai ba har nata ma ba su ishe ta kallo ba, yadda shi yake zumunci da ‘yan gidansu da iyayenta ita ba ta yi.
Aunty Zulaiha dai ta ga babu mafita, wankin hula zai kai ta dare dole ta dawo ta lallaba abinta, ta ce ta yarda Aalimah ta zauna, amma a bude mata rufaffen dakin Mu’azzam da ke kasa ta koma, akalla dai su Basma ba su matsu ba.
Wannan karon ne ya dago manyan idanunsa na IYALAN RAAZEE da suka gigitata, ya dube ta da su da kakkausan kallo. Sun kada sun yi jazir. Sosai ta razana, don bai taba yi mata irin wannan kallon ba, in ba ta yi kuskure ba sai ta ce har tsana-tsana (hatred) ta hango a cikin kyawawan idanun da suka rudeta ta fada a makauniyar soyayyarsa.
Ya dade yana mata kallon har sai da ta ja baya don tsoron kada ya kai hannunsa gare ta.
“Da abin da na haifa, da wanda Mansour ya haifa daya ne a wajena, babu bambanci. You can book an apartment for rent in wannan ya muku kadan ke da ‘ya’yan naki�.
Duk inda Aunty Zulaiha ta ke tsammanin Ishaq Razee a kan zaman Aalimah a gidansa, sai ta same shi ya wuce nan. He’s no longer the Ishaq she know, father of her children, apple of her eyes…! Mene ne abin yi a gare ta? Surrender! Zuciyarta ta ba ta amsa, wato sallamawa ga zaman ‘yar Mansour a tare da su. Ta yi amfani da wata hikimar daban ban da tursasawa.
A sati na biyu, kwana goma sha hudu da zuwan Aalimah America ta fahimci wani abu, Aunty Zulaiha ta canza mata sosai, tana janta a jiki in har Daddy na gida ko yana zaune a waje. In ba ya nan kuwa kashi ma ya fi ta daraja.
Maganar da ya gaya mata ta cewa;she can book a rent with her children (zata iya kama haya itada ‘ya’yanta idan gidan ya musu kadan) a kan Aalimah ta tsaya mata a zuciya, ta kuma sanya mata TSANARTA. A da, ba tsanarta ta yi ba, apparentlybako ne ba ta so a cikin gidanta. Amma reactions dinsa da amsoshinsa gare ta sun nuna yana son ‘yar dan uwansa kamar, ko ma fiye da yadda yake son ‘ya’yansa. Wani abu da zuciyarta ta gaza dauka, ba kuma za ta iya dauka din ba.
Duk kokarin Aalimah na kin sanya damuwa a rai don tana da masaniyar yadda ta illata kwakwalwar mahaifiyarta dole ta fara damuwa da halayen Mummy Zulaiha. Tana riga kowa fita a gidan saboda banki, amma duk suna riga ta dawowa. Duk walwalar da ta ke ciki da ta jiyo horn din motar Mummy, gabanta zai yanke ya fadi, ta soma neman inda za ta adana kanta.
Basma da Khaleesat suna da hankali, kuma zuwa yanzu sun lura Mummy is not happy any more da zaman Aalimah tare da su. Musamman suka same ta a daki suna lallashinta kan ta karbi Aalimah, she’s nice, she’ll come to like her too(tana da kirki, itama zata so ta) idan ta saki zuciyarta da ita. Ba tare da sanin Aalimah ba.
Ce musu ta yi su tashi su ba ta wuri, ita ina ruwanta da wata sister dinsu? Ko a kanta ta ke zaune?
Sosai ta saki rai da Aalimah, har da tsokana in Daddy na zaune. Rannan ta ce masa ma ya ba ta kudi za ta yo mata shopping ta lura akwai abubuwan da Aalimah bata da su. Dadi ya ji har ransa ganin ta fara son farin cikinsa.
A hankali yake nuna mata Aalimah yarinyar kirki ce ta ba ta dama ta fahimce ta, ba zai kawo wadda za ta cutar da su ba, above all jini ba wasa ba ne, jinin da ke yawo a jikin Aalimah, shi yake yawo a jikin ‘ya’yanta. Ta bude zuciyarta ta so mutane, mutum rahma ne, kuma falala gare shi. Duk da cewa zama da shi da wuya. Amma in kayi katari dana kirki rahma ne a gareka. Ya gaya mata irin canjin da yaransu ke samu tun zuwan Aalimah, yanzu har Yesmin ba ta bari sallah ta wuce ta.
Maimakon zuciyarta ta yi sanyi, sai ta kara zafafa ta fusata fiye da kima. Is she here to study, or to distort her children? (Ta zo karatu ne ko ta zo canza rayuwar ‘ya’yanta?) Amma ta hadiye ta kuma ba shi hakurin rashin fahimtar ta. Credit card dinsa ya bata ma gabadaya na bankin (Well Fargo) ya ce ta ciri duk abin da zai isa ta yi musu siyayyar dukkaninsu har ita.
A daren ranar bayan an yi dinner suka koma kan kujerun falon suka zazzauna. Mummyn aiki ta fara yi cikin system dinta ba ta kallonsu. Daddy news yake kallo a tashar Aljazeerah, ya canza ya mayar CNN. Basma na danne-danne cikin Ipad dinta, Khaleesat alqur’ani ne a hannunta tana manne da Aalimah wadda ita kuma text book ne a hannunta tana duba course din da suka yi yau, littafin introductory ne ga fanninta na harhada magunguna, in Khaleesat ta karanto aya cikin suratul Yasin, sai ta ci gyaranta ba tare da ta duba Qur’anin ba ita. Idonta na kan littafin hannunta.
Yesmin ta ce, “Aunty Aalimah, yaya ma ki ka ce addu’ar shiga toilet? Zanje nayi fitsari�.
Ta ce, “Allahumma inni a’uzu bika minal khubsi wal khaba’is. In an fito kuma a fito da kafar dama a ce, Gufranakallahummallazee azhab anniyal azaa�.
Yesmin ta maimaita, sannan ta nufi bandaki da gudu. Bayan ta dawo kowa ya ci gaba da abin da yake yi, kamar daga sama Yesmin ta sake cewa,
“Mummy ina dankwalinki? Ba kyau zama ba dankwali. Dubi yadda Shaitaan duk ya bi ya yi miki fitsari a ka�.
Ai kuwa kowa ya cira ido ya dubi Mummyn, har Daddy, sai a lokacin ya lura duk cikinsu babu wadda ba ta daure kanta ba sai Mummyn, kuma ya san da ba haka suke ba. Dariya ce ta kama shi, yadda Mummy ta yi wani kicin-kicin da fuska tana kallon Yesmin kamar ta kai mata mangara. Wai ita ce kanta da fitsarin Shaitaan? Tabbas a bakin Aalimah ta ji wannan nassin. This is not her words, beside(wadannan ba kalaman ta bane, tukunnama) yaushe ma dukkaninsu suka koyi daura kallabi? Oho! Ko silin gashinsu daya babu a waje, sun bi sun dukunkune abinsu cikin hula. Ba ta ce mata komai ba ta ci gaba da abin da ta ke yi, zuciyarta a cunkushe. So she want to change her chindren to total ‘yan kauye as she is ko me? Ba ta son shisshigi da katsalandan cikin al’amarin ‘ya’yanta, ina dalili? Aalimah must go! She cannot take it.
Tun zuwanta sau daya ta yi magana da gida, shi din ma da wayar Daddy. Ta nemi wayarta ta rasa sama ko kasa, ba ta sani ba can wani loko a cikin kayanta ta shige. Cike da kauna Daddy ke dubansu tana ma Khaleesat kari da ka, ba tare da ta duba Qur’an ba har suka gama. Khaleesat ta karanta Fatiha suka shafa. Cewa ta ke gobe za ta bai wa Shaikh (Malaminsu na islamiyya) mamaki, ta iya inda zai dora musu tun kafin kowa a ajin ya iya. Wata islamiyya Daddy ya kai su ta mutanen Libya in sun taso daga boko. Khaleesat ta haye sama tana fadin bacci ta ke ji, bayan ta sumbaci iyayen daya bayan daya.
Ya ce, “Aalimah kina kiran su Aboubacar kuwa kuna gaisawa? Dazu Mansour ya kira ni ina office ya ce in ba ki, ni kuma lokacin bana gida, na ce masa in na dawo I will check on you, me ya sa ba kya kiransu?�
An tabo mata babbar damuwarta a dan tsukin. Ta sunkuyar da kanta, ta ce, “Daddy, tunda na zo ban ga waya ta ba�.
Fada ya hau ta da shi, ya ce, he’s no longer her Dad kenan, tunda har ba ta da waya tsayin wannan lokacin ba ta bude baki ta gaya masa ba. Hakuri ta shiga ba shi tana fada masa ta san wayar ba bata ta yi ba, wani wajen ta jefa ta ta manta.
Ya dubi Aunty Zulaiha ya ce, “Yaushe za ku je shopping din ki sama mata waya?�
Ta ce, babu damuwa za ta ba ta daya daga cikin nata kafin su je, sai weekend za su fita.
A gaban Daddy ta cire layin daya daga cikin kan wayoyinta guda uku, ta bai wa Aalimah. Hannu bibbiyu ta karba ta yi godiya.
Ya ce da Basma gobe kafin su fita ta kunna mata WiFi dinsu, ta kuma saya mata credit in sun fita gobe.
Sallama suka yi wa iyayen suka wuce dakinsu har Yesmin don su kwanta. Babu mai yin latti a cikinsu. Ta lura duk al’ummar kasar ma babu lateness cikin dictionary dinsu.
A washegari Basma ta sayi layin ta sanya mata, ta loda mata kudi. Yau ba su yi lecture da yawa ba suka koma gida. Ko abinci ba ta ci ba sai da ta kira kowa nata da sabon layinta. Duk ta haddace lambobinsu a kanta. A karshe ta kira Mahmoud, yana zaune a office dinsa cikin ma’aikatar hukumar zabe ta Katsina a lokacin, aiki ya dan ragu masa, ya dafe kai a kan tebirinsa. Ba tunanin komai yake ba sai na Aalimah. Tunda ta tsallaka Amurka bai kara jin duriyarta ba, she didn’t give him a call as she promised (bata kira shi ba kamar yadda tayi alkawari). Ko ta samu dadin duniya ne ta manta da shi? Ya sani tun tafiyar Aalimah, wata zuciyar na gaya masa ya yi wauta, babbar wauta kuwa da ya bari ta tafi ba tare da gamsasshiyar magana a tsakanin iyayensu ba.
Aalimah a Nigeria ma zubinta na ‘ya’yan manya ne, balle ta haura Amurka. Ko kadan ransa bai son wannan tafiyar, don dai ba yadda zai yi ne, tunda bai isa ya hana iyayenta iko da ita ba, tunda ba aurenta yake ba. Sai dai wani saqo can na zuciyarsa na gaya masa… this is the deadly mistake(kuskure mafi muni) da ya taba yi a rayuwarsa, babu wanda ya san da zancensa da Aalimah daga nasa iyayen har nata. A hakan kuma wai yana jira ta dawo ya aure ta. Yaushe? Ta wacce hanya?Kuma a ina? Sanda zata dawo ta kara shekaru da sanin ciwon kanta. Za ta iya haduwa da wani ya karkatar da zuciyarta daga gare shi… ‘NO!!!� Ya fada da karfi, tare da naushin tebirin da ke gabansa. Yana da kyakkyawan zato a kan, Aalimah, duniya ba ta gabanta. Za ta rike soyayyarsu da amana no matter what ya yarda da wannan!
Wayar da ke gefensa ce ta hau ruri, ta yi har ta katse, ta sake ci gaba kafin ya dauka. Lambobi ne rututu irin na kasar waje. Wani sanyi ne ya tsirga a zuciyarsa, ya amsa da sauri.
“Aalimah!�
Ya fada in exclamation.
Bai ba ta damar cewa komai ba ya dora, “You keep me anxiously waiting(kin barni inata jira cike da taraddadi) kwana ashirin da daya, Na dauka ma kin manta da ni�. Ya fada da karyewar sauti.
Sosai ta ji tausayinsa ya kama ta, ta san yadda Mahmoud ya damu da ita, yake kuma sonta ita ko rabin hakan ba ta masa. Tunda ta zo ba za ta ce ga lokacin da ta ware ta zauna don ta yi tunaninsa ba. She justadmires him, she likes him,because he has brain.(Kawai tana son shi sabida hazakarshi). Haka nan tana jinsa a ranta sakamakon shakuwar da suka yi da shi na shekara guda a gidansu. He is good and well-mannered (yanada kyawawan dabi’u).
Sanda za ta taho a waya suka yi sallama, ya tada hankalinsa sosai, kiris ya rage ya yi mata kuka. Ya ce, tsoro yake ji, tsoron rasa ta. He’s afraid, and he don’t know WHY?.
Murmushi ta yi, murmushin nan nata mai nutsar da zuciya, duk da Mahmoud ba ya ganinta ya ji sautin murmushinta. Shekarunta goma sha shidda, amma ma’abociyar tsinkaye ce, amma tsinkayenta bai taba tsinkayo mata akwai abin da zai sa ta ki Mahmoud ba, ko ta juya masa baya. Cewa ta yi da shi,
“We cannot run-away from our destinies, but I’m hoping that destiny tied us together�.
(Bazamu iya gujewa kaddarorin mu ba, amma ina fatan kaddarar ta bar mu tare).
Wadannan sune kalaman Aalimah da yake kwana ya tashi da su tun tafiyarta, zuciyarsa na yi musu fassara kala daban-daban, mai dadi da mara dadi. Wannan ne yanayin da yake ciki har zuwa yau da ya samu kiran Aalimah. Ya lumshe ido ita kuma ta yi ajiyar zuciya. A hankali ta shiga warware masa dalilin da ya sa ba ta kira shi ba tun zuwanta, she lost her phone, she has been busy with school, (ta rasa wayar ta, tana cikin hidimar makaranta) ko su Mama ba ta kira ba sai yau.
Ajiyar zuciya ya yi, ransa ya yi masa dadi. At least Aalimah ba ta manta shi ba bayan shigarta USA. Suka shiga hira ya gaya mata har Aboubacar ya kira don ya samu lambarta ya gaya masa su ma da lambar kawunta suke magana da ita, ya san in ta nutsu za ta kira shi. Ya kara da yi mata nasiha kan ta kama kanta a kan wanda ya santa da shi, shi in son samu ne ma ta dinga sa hijabi da niqabi he’s always afraid bai san dalili ba.
Dariya Aalimah ta yi a ranta tana tunanin ta ya ya wani zai ce yana sonta a nan? Duk abin da yake hange ba haka yake ba, ga ‘yammata nan birjik masu mugun kyau da ya dame nata ya shanye, abin da ta lura ma kowa is busy with himself a nan ba ruwan wani da harkar wani in ba wani naka ba. Hijab kuma ai ba sai ya sa ta ba tana sa abinta (a lokuta da dama) duk da kanana ne, amma ta san shigarta is fully Islamic.
Sai da Khaleesat ta shigo tana kiranta, sannan suka yi sallama da Mahmoud ta kashe wayar gabadaya. Ba ta da ra’ayin shiga kowanne‘social media’ don yanayin karatunta, sannan kuma, ba ta son hayaniya, ba ta da ra’ayinta.
Ranar asabar da safe Aunty zulaiha ta gaya musu su shirya za su je shopping da yamma kuma za su shiga kasuwa. Daddy na gefe yana ta ‘making calls’, amma ya ji ta. Bayan ya gama ya dube ta da murmushi ya ce,
“Umm Mu’az, ki kai su inda za a samu ready-madeAfrican wears ki saya wa kowa yadda ta ke so, sun gaya min sun daina saka wando, sai ki hada musu da Arabian gowns�.
Cikin mamaki Mummy Zulaiha ta dago ta dubi Khaleesat, sannan Basma da Yesmin ta ce, “Dalili? Are we in Africa or what?�
Duk suka yi shiru suka sunkuyar da kai ganin yadda ta fusata ainun. Gab ta ke da ta kai musu duka. A nitse Daddy ya bi ta da ido yana son karanto matsalar matarsa a dan tsukin nan,she becomes pepper-tempared. Shin ita wace irin uwa ce da ba za ta iya bambance abu mai kyau da mara kyau ga ‘ya’yanta ba? Al’amarin Mu’azzam bai isa ya zama iznah a gareta ba? Me suka yi abin bacin rai a nan?She’sgetting angry easily a dan tsukin nan duk da yadda yake kokarin kyautata mata don ta kara sakin ranta da Aalimah.
A nutse ya ce da ita“I think you are supposed to be happy, they are trying to adopt their native culture (Na yi tsammanin farin ciki zakiyi, suna kokarin daukar al’adun su na gado) su ajiye wannan mara tushen?�
Tashi ta yi fuuu! Ta bar falon ba tare da ta ce da shi komai ba ganin yadda yaran gabadaya suka zuba mata ido har Aalimah.
Safah da marwah Mummy ta shiga yi a dakinta. Tunanin hanyoyin da za ta bi ta kori Aalimah daga gidanta ta ke yi from every direction ta rasa. A karshe ta samu guda daya, duk da ba ta da tabbacin dorewarta da sahihancinta..
Kafin yamma ta yi kokari ta saki ranta. Yau ita da kanta ta shirya musu abincin rana. Aalimah ta zo tana so ta taimaka mata don ta aiki Easther ta ce ta wuce ta ba ta guri, ba ta son karambani. Su Basma da ma ba abin da suka tsana irin aiki, don haka ko kusa ba sa dosar kichin in ba wani abu za su dauka ba.
Easther na dawowa ta kira ta gefe, ta sallame ta da kudi masu yawa, ta ce da ita daga yau ba ta bukatarta, ta je ta nemi wani aikin, amma duk sanda ta ke bukatarta za ta yi mata waya ta dawo. Easther har da kukanta, domin ba karamin sabawa ta yi da gidan aikinta ba da iyalin gidan bakidaya. Su din masu karamci da kyautatawa ne a gare ta. Amma tunda Mummy ta ce za ta dawo da ita wani lokaci she will go home, and wait. Amma ba za ta iya neman wani aikin ba. Kudin da Mummy ta ba ta za su iya rike ta da mahaifiyarta har tsawon shekara daya.
Asabar da lahadi Daddy ba ya zuwa ko’ina. Haka kawai ya yideciding ya bi su kasuwar kan a barshi shi kadai a gida. Ba tare da ya gaya wa Mummy ba. Sanda ta ke shiryawa sai ta ga shi ma yana shirin fita. Ta tambaye shi zai je wani wuri ne, ya yi mata shiru don ya ji haushin abin da ta yi masa dazun a gaban ‘ya’yansa, amma dubi kamar ba ita ba, yanzu wai har ta manta. Kananan kaya ya saka wadanda suka zaftare shekaru ashirin daga hamsin din da yake da su kai ka ce balaraben kasar Misra ne. Zulaiha kasa jurewa ta yi, ta yi azama ta rungume shi ta baya yana dab da ficewa daga dakin. Hakuri ta shiga ba shi ta ce tana bisa umarninsa, za ta yi duk abin da ya ce ta yi. Kwace jikinsa ya yi, ta sake kamo shi.
“Daddy please…� Ta marairaice masa yadda ta san ba ya iya jurewa. Ya ce,
“Na nawa kuma Zulaiha? Sau nawa za ki yi min laifi ki ce in yi hakuri in hakura, amma gobe ki sake? Wait, I want know your problem(ina son sanin menene matsalarki) cikin kwanakin nan. Da fari kin ce zaman Aalimah ne da yaranki, you then come and said you regretted hurting me with this, you accepted her. And now, what’s bothering you? I failed to get you right, please make it clear to me (kika dawo kika ce kinyi nadamar bata min rai akan hakan, kin karbe ta cikin ‘ya’yanki, yanzu kuma, me ke damun ki? Na kasa fahimtar ki daidai, don Allah ki fahimtar dani abinda ke ran ki)�.
Hakurin dai ta ci gaba da ba shi kwando-kwando. Bayan shi ba ta san da wacce kalma za ta yi masa bayani ya fahimta ba. Ya fahimci she doesn’t want a STRANGER close to her family (bata son BAKO cikin iyalin ta). Cewa zai yi Aalimah is not a stranger she’s part of him. Ita kuma ‘Da’ in ba ita ta haife shi ba, to ba Da ba ne a gurinta, tunaninta daban, ra’ayinta daban da na kowa. Kai ka ce haifaffiyar Amurka ce iyaye da kakanninta sabida dabi’u da akidojinta.
3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price 1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM - Buhainat: 🌹 *Aalimah* 🌹
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
LAST FREE PAGE
Kai ta daga, cike da tausayinsa. Babban mutum kamarshi haka, mai manyan ‘ya’ya da furfurarsa da komai yana ta kwantar da murya, yana lallashinta kan dan abin da bai kai ya kawo ba. Ko bai roke ta ba, ba ta yi niyyar gaya wa Daddynta komai ba balle Mama, da ba’a gaya mata abin da zai daga mata hankali.
Ta ce, “Daddy na yi maka alkawarin zancen nan ya wuce. Amma ina rokonka ni ma don Allah kada ka yi wa Mummy fada. It’s human nature (halittar dan adam ne).
Ko ka yi fadan ba abin da zai canza ta. Akwai mutane irinta da yawa da ba sa son kowa ya rabe su, they will act absent mindedly, su rasa tsinkayensu da tunaninsu.
Yanzu kamar Mummy she’s very well educated, amma ka ga ta kasa hangen cewa, abinda take shukawa a kaina ba inda zai je musamman a kasar nan, you’ll soon come to know it.
A lokacin da za ta aikata ba ta yi tunanin hakan ba. Abinda take so kawai shine in matsa in bata gidan ta. Don haka ko me za ka zo mata da shi yanzu ta riga ta shirya maka. Daddy act smart, sai a zauna lafiya. Ni kuma ba zan sake cewa zan koma hostel ba har sai na gama karatuna, zan zauna da Mummy yadda ta ke Daddy, it’s a promise�.
Hannayensa biyu ya ware mata,
“Give me a hug my daughter�.
Kunya ta ji sosai ta soma dariya, kafin ta karasa ya rungume ta. Sannan ya sake ta ya dan bubbuga kafadunta.
“What do you like to eat?�
Ta ce, “Na yi girki Daddy, mu je gida mu jira su Basma su dawo mu ci abinci tare yadda muka saba�.
Ya ce, “No, it will take time, mu je in sama miki abin da za ki ci, ki ci a gabana ki koshi, sannan mu je mu dauko su Basman mu koma gida�.
Wani gidan cin abinci ya kai ta, ya tula mata kayan dadi a gabanta, irin wanda ba ta taba ci ba. A gefe ga Pizza, Shawarma da kazar Kentucky fried chicken. Ta ci iya cinta, ta kora da sassanyan Pepsi, ta yi gyatsa, ta yi hamdala. Ya yi wa su Khaleesat guzurin nasu suka tafi, Khaleesat aka fara dauka a makarantarsu ta islamiyya da yake in ta tashi daga boko islamiyya ta ke shiga wadda ta ke daura da makarantar bokon nasu, ita da Yesmin, ta wasu larabawan Libya. Sannan suka dau hanyar Boston University bayan Daddy ya kira Basma yace kada ta biyo Vangasu nan zuwa daukarta. Khaleesat cike da murna da ganin yau Aalimah ta fito, wannan ya tabbatar mata Daddy came to know Mummy’s mischiviousness (Daddy ya ganeketar Mami).
A kalla dai ba su sabawa uwarsu ba tunda ba su suka gaya masa ba. Abin da ya sa Basma ma ba ta damu sosai ba kenan a kai, ta san jami’ar Boston wil not take that any longer they will trace for Aalimah (bazasu dau wannan ba, zasu bi bayan Aalimah). Ta yi mamaki ma da aka dauki tsawon wannan lokacin. Tana ganin Aalimah a motar sai Ehoo! Ta rungume ta tana ta faman sambatu.
“Aal, are you alright? We are sorry Aal, we can’t do anything for you�.
Harararta Daddy ya yi sosai, mai dauke da maganar da ba sai ya furta ba.
Da sauri ta ce, “I’m sorry Dad, she’ll throw a tantrum (zata yi balbalin bala’i) (tana nufin Mamanta)�. Ya girgiza kai kafin ya ce.
“Wannan na nufin kun fi jin tsoron Mamanku a kaina�.
“Of course, Dad�. In ji su duka su biyun har suna hada baki.
Dariya ya yi, a ransa yana fadin, ni kaina wani lokacin tsoron nata nake ji, amma this time around za ta gane kurenta. Yesmin ba ta san bikin da ake ba, tana ta kokawa da robar ice-cream dinta. Aalimah ta baiwa kowacce ledar takeaway dinta. A cikin motar suka hau ci don duka yunwa suke ji.
“Kada ki so ki tona yadda nayi kewarki a makarantar nan Aalimah�. In ji Basma.
“I can estimate (zan iya kintatawa)�. In ji Aalimah ba tareda ta dago ba tana kokarin hudawa Yesmin lemo.
Daddy yana jinsu yana jin dadi a ransa, zumuncin Basma da Aalimah yana yi masa dadi, ‘yarsa Basma haka ta ke, zuciyarta a bude ta ke, kuma ba ta boye duk abin da ke zuciyarta,whilstKhaleesa ‘yarI don’t carece, though she’s nice too (yayin da Khaleesat mai halin ko’in kula ce, duk da haka tana da kirki).
“Bazan ba ki hakuri kan abinda ba ni da laifinsa ba Aal, Mummy tana da kirki, amma wani lokacin ba ka gane kanta. Na tabbata za ta zo ta so ki idan ta gane kyawawan dabi’unki. Ban taba ce miki komai ba, tunda Mummy ta fara abinnan, ina jira ne sai Daddy ya sani. I’m sorry Aal�.
“Zan iya rokon alfarmar ki bar maganar nan haka Basma?Mum is my mother, meye a ciki don uwa ta yi wa danta wani abu da bai ji dadin sa ba?�
“Ai haka ta ke da mita kaman tsohuwa�. In ji Khaleesat.
Dariya suka yi ita da Khaleesat, Basma ta harare ta. Daddy uffan bai ce musu ba, shi kadai yake sakawa yana warwarewa a ransa na matakin da zai dauka a kan Mummy, yana kuma tunanin maganganun da suka yi shi da Aalimah. yarinya karama na koyar da shi ‘psychology’. Na yadda zai tafiyar da matarsa mai baudadden hali. Ya san duk maganganun da Basma ke yi wa Aalimah borin kunya ne na halin uwarsu. Ya jinjina wa Mansour da Aseeya na irin tarbiyyar da suka bai wa Aalimah.
Daya bayan daya suke shigowa gidan, Aalimah, ita ce karshen shigowa. Tsoron Mummy ta ke ji, tsoro mai yawa. Sanda suka shigo ita kadai suka hango zaune a dining tana shan wani damammen abu cikin kofi kaman oat, Yesmin ta yi wajenta tana kai mata ledar takeaway da suka taho mata da shi. Ido ta daga tana kallonsu one-by-one bayan ta hambare Yesmin ita da ledar tata.
Ta kan Basma ta fara don me ta kashe wayarta tana so ta tambaye ta karfe nawa za ta gama lectures ta dauko ta, shi ne ta sa ta yi wahalar banza? Sai ta koma kan Khaleesat, uban wa ya ce su taho ba su jira ta ba bayan sun san za ta zo daukansu kamar kullum? Sannan ta dawo kan Aalimah, har huci ta ke yi.
“Wato don ba ni na haife ki ba ban isa in sa ki aiki ba, tunda mai aikina ba ta nan aiki ya yi min yawa, shi ne ki ka kira ubanki? To don Allah in kin isa ki sa ya yi min duka ko ya sake ni, in bar miki kasar ki yi abin da za ki yi a cikinta�.
Ko tari babu wadda ta yi a cikinsu, ‘ya’yanta sun zuba mata ido, Aalimah ta sunkuyar da kai kasa sai hawaye ta ke yi. Ba ta saba da fada ba, ko Mamansu duk zafinta hadawa ta ke da nasiha. Mummy fada ta ke kamar ta ari baki ba wanda ta bari a cikinsu. She’s doing it fiercely kamar babu mijinta uban ‘ya’yanta a tsaye a cikinsu.
Wata tsawa da Ishaq Razee ya daka mata sai da ta sa Aalimah karasa fashewa da kuka, Yesmin kuma ta yi tsalle a sittin ta kankame Basma. Shi ma ya bude nasa famfon yi yake kamar zai doke ta. Duk yadda suka yi da Aalimah na cewa, he will act smart ya kasa. Da ma an ce mai hakuri bai iya fushi ba.
Bai zo da wannan niyyar ba ya zo ne da intention na hukuntata cikin ruwan sanyi. Amma ya lura zuwa wannan lokacin Zulaiha ta dade tana amfani da sanyinsa tana yin yadda ta ga dama da rayuwarsu. Ta yi masa laifi, sannan ta nuna ta fi kowa daukar zafi. Har da yi wa Aalimah kazafi wai ta kira shi. Ya tabbata Tabarmar kunya ta ke nannadewa da hauka. Gaskiya ne da ake cewa, mace komai shekarunta wani lokacin ba ka raba ta da dabba. Yanzu kamar Zulaiha mai manyan samari da ‘yammata ta tsaya tana wannan haukan just because ya kawo ‘yar dan uwansa gidansa?
Tun yana yi da turanci har ya saki ya koma da buzanci, ya koma harshensa Temachek, ya saki ya koma Francaise. A karshe ya ce,
“Please kindly get out of my mansion, go to the one who has no relatives, but I belong to IBRAHEEM RAAZI’S. I couldn’t scratch them from me for your selfish interest and your personal satisfaction. Is that clear? (Don Allah ki bar min gidana, ki tafi ga wanda bashi da dangi, amma ni jinin Razee ne, bazan iya ciresu daga jikina ba sabida son kai irin naki da biyan bukatar ranki)Ko sai na sake maimaitawa?�
A kidime ta dago ta dube shi, he’s no longer her silent Ishaq. Wannan sassanyan mutumin mai kama da ko cokali aka sa masa a baka bazai ciza ba.Gabadaya ya hautsine mata ya koma cikakken buzunsa. Abin takaicin a gaban ‘ya’yanta, a kan wata ba’abziniyar ‘yarsa mai kama da danyen nama. Kafa ta sa ta hambare tebirin cin abincin tangarayen dakekai suka rikito suka kwankwatse nan take. Ba ta bi ta kansu ba ta wuce da gudu ta yi sama. Shi kuma Daddy juyawa ya yi ya fita daga gidan.
Kafin a jima Mummy ta sauko jaye da trolley. Dogon bakin wando na mata ne a jikinta da farar shirt an yi rubutu da bakin fenti ‘calvin klien, ta nade kanta da veil wanda ya sauka kan kirjinta, ta kuma ratayo jakar hannu mai dan girma Gucci. Ta rufe kwayar idanunta da black shades mai fadi don kada a gane halin da kwayar idanunta ke ciki. Suna tsaye cirko-cirko ta wuce su fuuu! Kamar guguwa ta fice. Sai karar reverseda mota da ficewarta gidan aguje suka ji. Yesmin ta sa kuka tana kiran, “Mummy…!�
Za ta fice Aalimah ta kamo ta. Ta fi kowa shiga tashin hankali, kuka ta ke tun daga karkashin zuciyarta. She must leave this family for them to live in peace… ko Daddy na so ko ba ya so za ta koma hostel ko ta koma Nigeria.
Kama hannunta Basma ta yi suka hau sama, Khaleesat da Yesmin suka biyo bayansu. Ba wadda ta iya ce da ‘yar uwarta komai. Alwallah suka yi kowacce ta tada sallah. Ko da suka idar, Basma ta lura Aalimah ta kasa barin kan sallayarta kamar yadda ta kasa tsaida hawayen idanunta.
Ta raba aure! Ta raba ‘ya’ya da uwarsu!! Shi ne damuwarta!!!.
Kunna fitilar dakin Basma ta yi ta dubi Aalimah, “Malama, ba za ki zo ki kwanta ba? It’s past tenfa!�
Kuka na sosai Aalimah ta fashe da shi.
“Ku yi hakuri Basma, gobe zan koma hostel, I’m not here to bring ‘anarchy’ between your parents. I’m sorry, very sorry…� Kukanta ya kara karfi sosai.
Basma ta sauko daga gadon ta zo ta zauna a gabanta. Kama ta ta yi ta rungume a jikinta, ta ce, “Aal, stop crying, kwantar da hankalinki. Ba nisa ta yi ba, za ta dawo. Kada ki damu kanki. Ba nisa zata yi ba. Our Mum will not go out of America because of you, she don’t even have friends. She’s going to that ANNOYING son of her’s. She mightbe in LAS VEGAS!�.
(Maman mu bazata bar kasar Amurka saboda ke ba, ko kawaye bata da su, ta tafi wajen wannan Dan nata mai ban haushi. Yanzu haka tana birnin LAS VEGAS!�
Aalimah ta maimaita kalmar LAS VEGAS!Akan halshenta har sau uku. Ta kuma karanta kalmar a zuciyarta sau ba adadi a wannan ‘yan dakikan da basu gaza biyar ba. She has been hearing things about Las vegas… Nan da can, daga bakin su Basma, and her fellow Boston students. Haka kawai sunan garin ke mata dadi da kwarjini a zuciyarta. Yake sanya mata wata irin nutsuwa, a duk lokacin da taji an ambace shi. Jikinta da zuciyarta kuma ke yawan bata wani irin feeling; there’s something STRANGE associated with her life and this city........Wato haka kawai jikinta da zuciyarta ke ba ta akwai wani BAKON al’amari mai karfi dake da alaqa da rayuwarta da wannan birni,wanda a wannan lokacin ba za ta iya cewa mene ne shi ba.
3094856450
Sumayyah Kabara
Firstbank
Price1&2 N400
6/28/21, 7:31 AM - Buhainat: Aalimah
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI
07030137870
Aalimah ta maimaita kalmar LAS VEGAS!Akan halshenta har sau uku. Ta kuma karanta kalmar a zuciyarta sau ba adadi a wannan ‘yan dakikan da basu gaza biyar ba. She has been hearing things about Las vegas… Nan da can, daga bakin su Basma, and her fellow Boston students. Haka kawai sunan garin ke mata dadi da kwarjini a zuciyarta. Yake sanya mata wata irin nutsuwa, a duk lokacin da taji an ambace shi. Jikinta da zuciyarta kuma ke yawan bata wani irin feeling; there’s something STRANGE associated with her life and this city, which so far... she don’t know.Wato haka kawai jikinta da zuciyarta ke ba ta akwai wani sabon al’amari mai karfi dake da alaqa da rayuwarta da wannan birni,wanda a wannan lokacin ba za ta iya cewa mene ne shi ba. In aka ce strange ana nufin bakon abu. A kalla hankalinta ya dan kwanta da kalaman Basma. Tunda ta tabbatar mata Mamansu bazata bar su saboda ita ba. Khaleesat is busy with her I don’t care attitude, ta dade tana sharbar barcinta, Yesmin ce dai sai da dabara suka samu ta yi barci, don sun ce mata gobe za su kai ta wajen Mummy.
Duk da ba ta kwanta da wuri ba, hakan bai sa ta makara sallar asubah ba. Ta yi sallah ta tashe su dukkaninsu suka yi, har Yesmin. Barci suka koma, ita kuma kitchen ta nufa ta soma kici-kicin hada musu breakfast. Simple breakfast ta yi musu don zuciyarta ba dadi, plaintain (Agada), chips, da liver souce ta hada, sai ruwan shayi da ya ji kaninfari da cinnamon, wato (kirfa). Ta shirya komai a dining sannan ta koma sama. Tashinsu ta yi duka kowacce ta soma shirin wanka, daga nan sai shirin tafiya makaranta. Aalimah ji ta yi wani farin ciki ya zagaye ta, yau za ta je makaranta bayan zaman ukuba na sati hudu.
Suna karyawa Daddy ya aje fork din hannunsa ya dube su duka, “Daga yau Basma da Khaleesat ku dinga shiga kitchen tare da Aalimah, ku dinga koyon girki you are no more a kids now, ba wadda ba ta isa aure ba da a Nijar ko Nigeria ku ke, kuna jina?�
Dariya suka hau yi kasa-kasa, wai aure.
Basma is 16+, Khaleesat is fourteen, amma Daddy na kira musu aure. Su a gurinsu they are babies, nono ne kawai ba sa sha.
Khaleesat ta ce, “Yaushe za ka bi bayan Mummy?�
Hade rai ya yi sosai, ya ce, “She’s in Las Vegas. He called me yesterday�.
Daga haka ya mike, ya ce su wuce kada su makara.
Har department dinsu Aalimah ya kai ta, ya ga malaman tsangayar da level-coordinator dinsu. Shi kadai ya san uzurin da ya ba su suka yarda za su yi mata covering abinda ya wuce ta. Allah ya so ta ba a fara jarrabawar karshen zango ba, amma ana gab da farawa, don haka a karshe sun gargade ta da ta maida hankali sosai ta kamo darussan da suka wuce ta.A yau har aboki ta yi wai shi Alex, baturen Poland don ta lura kwakwalwarsa is sharpduk a kokarin ta na cimma ‘yan ajinsu abinda ya wuce ta, kuma a yinin ranar kadai data zauna da Alex ta amince mutum ba zai iya rayuwa mai kyau shi kadai ba. Yana bukatar tarayya da mutum dan uwansa cikin kowanne al’amari na rayuwa, ba kamar yadda ta dauka a baya ba.
Yau kwanan Mummy uku da tafiya, kuma karatun Aalimah ya farfado. Don Daddy ya dawo da Easther babu nauyin komai a kanta, sai na karatun. Kusan kullum tana waya da Daddy da Mama, Yaya Aboubacar, Mahmoud, kannenta da mutanen Nijar. Ba kudi kadan Daddy ya loda mata a wayar ba. Haka Daddy ya takura kansa yake squeezing time dinsa wajen kai su da dauko su. Amma ya ce yana cigiyar direba.
Yau Aunty Zulaiha ta cika sati daya da barin garin. Gidan ba kowa daga ita sai Easther, yau din da ta kama juma’ah ba ta da lecture. Daddy ya ce ta maida hankali ta yi bitar littattafanta, kuma ta yi masa pounded yam and egusi soup yana so ya ci in ya dawo. Ba abin da ba su da shi a store da freezers don Mummy Zulaiha ba daga nan ba wajen iya cefane, ba ta wasa da cikin iyalinta.
A satin kadai saboda nutsuwar da ta samu ta yi fresh da ita, fatarta har wani sulbi da sheki ta ke yi sabida kyawun muhalli da weather din Massachusetts da ya karbe ta. Karfi da yaji jikinta da fatarta so suke su zama irin na su Basma.
Ta wuni tana karatu, sannan ta je ta yi wa Daddy girkin da ya sanya ta, daga bisani ta yi freshen up ta sanya daga cikin kayan da suka sayo a Zainab Sumu Primitive Modern. Bubu ne na swiss lacedark green mai stones. Ta kame gashin kanta a tsakiyar kanta, ta fesa turarenta (Nude by Rihanna). Ta sauko falo ta zauna da tintimemen text book dinta (Concepts in Pharmacogenomics) tana ci gaba da nazari. Easther ta fito ta yi mata sallama ta tafi gida.
Mintuna kadan da fitar Easther aka shiga danna bell ta ajiye littafin a zatonta su Basma ne suka dawo. Ta bude da sauri, amma maimakon su Basma wani handsomesaurayi ta gani a tsaye goye da jakar baya.Bazata iya kintata shekarunsa ba. Wani kyakkyawan murmushi ya sakar mata, tutsiysr karen fararen hakoransa ta fito, ya ce,
“Hi Pretty, I’m ABOULKHAIR!�
Murmushin sanayya itama ta mayar masa, duk da bata san shin ba, amma jini ya bayyana kansa.
“....And I’m Aalimah�.
Hannu ya miko mata da nufin su yi musabaha. Maida hannayenta biyu bayanta ta yi ta sarke su.Sannan ta ba shi hanya tare da janyo trolley dinsa ciki. Ya karasa shigowa ciki yana kare wa gidan kallo, sannan ya dawo da kallonsa ga Aalimah wadda ta ja gefe tana ta kallonsa. He’s very handsome, elegant and energetic.
“Aalimah, ‘yar Kawu Mansour, kanwar Aboubacar na Kano Nigeria, right?�
Daga masa kanta ta yi, har yanzu murmushin ta ke yi. Farat daya ta ji ya zauna mata a zuciya, irin mutanen nan ne da psychologist ke kira cheerful and passionate,masu shiga ran mutum ba tare da ya shirya ba, ko kuma zuciyarsa ta tsaya yin shawara da shi kafin ta karbe su ba.
Wannan saurayi shi ne Abulkhair Ishaq Raazi, dalibin medicine a jami’ar Louisiana. Da na biyu ga Ishaq Raazi. Sanye yake da farar T.shirt samfurin Balenciaga da dogon wando monclear. Ya tara suma mai yawa a kansa. Aalimah, ta samu kanta da kasa dauke ido daga Abulkhair, sosai ta ke kallonsa wani abu na dan sukarta a kirji. Kallo ta ke yi masa wanda ba ta taba yi wa kowanne Da namiji ba.
Ya gama yi wa gidan da falon kallon kurillar da yake masa, ya juyo sai karaf! Suka hada ido da Aalimah, ya kamata tana yi masa kallon kurillah, kallon da ya wuce kima.
Da sauri ta sunkuyar da kanta. Dariya ya yiya matso gabanta ya tsaya. Tana iya jiyo tashin sassanyan kamshinturarensa, wanda ya danne duk wata ni’ima na dukka turaren da ta fesa. Ya sanya hannu ya dago habarta, ga mamakinta ta kasa hanawa. Karewa ma lumshe idanunta ta yi tana karbar wani bakon yanayi a zuciya da gangar jikinta. Muryarsa (kamar ta rowa).
“Ba kya shan hannu da maza, amma kin fi kowa iya kare musu kallo ko?�
“By the way, you are beautiful my sister. One of the prettiest creatures I came across. Enjoy your stay in Boston�.
Daga haka ya cika ta, ya yi mata wink, sannan ya nufi daya daga cikin dakunan da ke falon kasa, wanda tunda ta zo ta ke ganinsu a rufe. Ya bude ya shige ya rufe, ya barta nan tsaye kamar mutum-mutuma. Yo mutum-mutuma mana? Tunda mutum ce amma bata motsi?Ta tabbata da za a tsaga jikinta a daidai wannan lokacin za’a tarar gudun jini, ya katse a cikin dukkan jijiyoyinta, na adadin wasu mintuna da bata kididdige ba. Zata iya rantsuwa bata taba katari da namijin da ya dau hankalinta irin shi ba. Da ta tuna ya ce ita kyakkyawa ce, daya daga cikin kyawawan halittun da ya taba cin karo da su a rayuwarsa, sai ta ji kamar zaginta ya yi. However, statement din ya yi mata dadi. Ya sanya ta murmushi.
Ba shi ne mutum na farko da ya fara gaya mata tana da kyau ba,Mahmoud ya fada a baya. Sai dai shi ne wanda ya fada ta ji kalmar ta tsirga har cikin bargo da ruhinta. Duk da ta tabbata ba gaskiya ba ne abinda ya fada din. Ya fada ne don ta ji dadi, ko don wani dalili nasa na daban. Amma how could a hunk like him could notice the beauty of another person? (Ta yaya kyakkyawa kamarsa zai iya gane kyan wani dan adam? A nata ganin nasa kyawun ya isa ya disashe duk wani kyawu da zai gani. Wannan tunaninta ne amma.
Ta daga kafa da niyyar komawa sama ta ji dirin motar Daddy. Da sauri ta bude kofar suka soma shigowa daya bayan daya. Duk wadda ta shigo sai ta ba ta runguma da sumba sannan ta wuce. Daddy ne karshen shigowa, abin da ya fara tambayarta shi ne,
“Dan uwanki ya iso?�
“Yes, he’s here atleast ten minutes ago Daddy�. ( Eh, yana nan, akalla mintuna goma da suka wuce Daddy).
Karasa shigowa ya yi yana mai dafa kafadunta da murmushi a kan fuskarsa.
“Hope you study your pharmaceutical books very-very much?� (Dafatan kin karanta littattafan harhada magunguna ki sosai sosai?�
Dariya ta yi,
“I do Daddy, and also, your pouded yam and egusi soup is ready on the table�. (Na yi Daddy, kuma sakwararka da miyar agushi sun kammala akan tebir).
Murmushi ya yi,
“Wato ‘yar tana son Babanta irin sosai-sosai ko?�
Murmushi tayi. Kafin tace.
“Yes, she do Daddy,sosai-sosai take matukar son sa�.
Yadda suke maganar tactically with nodding head sai da suka baiwa su Basma dariya. Ya barsu a nan ya wuce upstairs yana dariya shima yana cewa,
“Let me bath and pray. I will then hurriedly come and eat my sakwara. God bless you my child with amazing husband. Basma tell Abulkhair that we are having dinner together by 8pm.(Bari in yi wanka inyi sallah, sannan inyi sauri inzo in ci sakwara ta, Allah ya albarkaceki ‘ya ta da miji na ban mamaki. Basma gayawa Abulkhair zamu ci abincin dare gabadayanmu karfe takwas na dare)�.
Shi ne farkon halartar table din. Ya yi wanka ya sake kayan jikinsa, gashin nan ya sha gyara ya kwanta luf sai sheki yake yi na abzinawan usli. Daddy shi ne na biyun saukowa shi ma ya cire kayan office ya yi wanka ya sanya na zaman gida. Suna daki suna sallah kafin su fito kusan a tare.
Idanun Aboulkhair kur! A kan steps din benen cikin falon, wanda yake fuskanta. Hira Daddy yake masa, amma da alama ba ya fahimtarsa, kunnuwa kam ya zuba yana sauraronsa. Abinda ya sani bayan wannan shine, zuciyarsa na neman yin tsalle ta fito daga allon kirjinsa. A lokacin da ta ke saukowa daga matattakalar benen rike da hannun Yesmin. Bai san ya kafa idanunsa a wurin ba sai da ya daina ganin reflection dinta a kan benen.
Kusa da Daddy Basma ta zauna, Khaleesat a gefenta. Kujerar Yesmin a dining din da ma karama ce, sai kujerar Mummy wadda ba wanda yake zama a kai ko da ba ta nan, sannan wata kujera guda daya a kusa da ta Abulkhair wadda Aalimah bata taba ganin wani cikinsu ya zauna a kai ba.It’s a seven-chaired dining table. Don haka empty kujerar da ke kusa da Abulkhair ta nufa ta zauna. Murmushi ta sakar masa kusa da fuskarsa tana kokarin zama.
“Ina fatan ban takura ka ba?�
“Ta ina zan takura don kin zauna a kujerar Mu’azzam? Daddy, another one chair is needed on this table (ana bukatar karin kujera a tebirin nan) for Aal…alimah�. Ya fada muryarsa na sarkewa da ya zo fadar sunan.
Daidai lokacin da Khaleesat ta soma serving kowa curin pounded yam a kan platedinsa. Tana diban hadaddiyar miyar da ta ji ganyen alayyahu da na ugu da zallar tsokar kaza tana zuba wa kowa. Ba tare da Daddy ya dago ba yana kokarin kai lomar farko bakinsaya ce.
“She replaces him in us, he don’t want to stay in his family, So no need of another chair. (Ta maye mana gurbinsa, ba ya son zama cikin iyalinsa, abin da ya sani, yake so kadai shi ne sana’arsa. Saboda haka babu bukatar karin kujera)�.
Ya yi murmushi bai amsawa Baban nasa ba, ba’a fadin laifin Mu’azzam akan idonsa, Yayan da baya taba yin laifi ne,kuma dan uwanda babu kamarsa. Ya soma cin abincin, “Tastes good�. Inji Aboulkhair yana duban tsakiyar idanun Aalimah. Wadda tayi murmushi ta sunkuyar da kanta.
Daga haka bai kara magana ba. Sai dai lokaci zuwa lokaci idonsa na satar kallon Aalimah. Ita ma duk dagowar da za ta yi sai ta tsinci idanuwan Abulkhair cikin nata. Gabanta ya ci gaba da tsananta faduwa. Wani al’amari da bai taba faruwa da ita ba a kan Da namiji shi ke faruwa da ita akan Aboulkhair. Gabanta bai taba faduwa ba da kasantuwar Mahmoud a wuri, kallon idanunsa ko wani abu makamancin hakan.
Can tsakar kanta ta tsinkayi muryar Abulkhair yana tambayar Babansa ina Mummy? Ba ta ji amsar da ya ba shi ba, saboda ta yi nisa cikin wata duniya mai hasaso mata abubuwa kala-kala masu tsauri a kan Abulkhair. Wadanda ita kanta ta kasa sanin abin da ya janyo su ko dalilin afkowarsu cikin tunaninta. Shi ne Da namiji na farko da ya fara kai hannunshi jikin ta a shekarun balagarta.Habarta kawai ya taba, ba da wata manufa ba, amma ta samu zuciyarta cikin wani sabon yanayi. And she don’t want the feeling to grow higher! Runtse idanunta ta yi da karfi tana kiran sunan Allah. Cikin zuciyarta ta ke rokonSa Ya kawar mata da wannan bakon yanayin da ta samu kanta a ciki akan dan uwanta.
A haka aka gama cin abincin ba tare da ta ci wani abin kirki ba. Plate dinta fal sakwara ta barshi ta mike ta soma tattare plates din. Abulkhair ya dago idonsa daga kan Yesmin da yake yi wa fadan yadda ta bata jikinta da miya. Kallonta ya yi ido cikin ido, sannan ya ce,
“Give it a good six mosels, (kiyi ma sakwarar nan kyawawan loma guda shidda) sannan ki bar wurin nan�.
Da sauri ta dube shi, jin yadda ya yi maganar authoritatively, irin yadda ta ke yi wa nata kannen. Sannan fuskarshi babu wasa. Sosai ta nutsu, ta saita kanta a gabansa. Abin da bai sani ba, kasancewarsa a wurin ne yasa ta kasa cin abincin. Gabadaya a takure take, wani yanayi ne da bata taba samun kanta a ciki ba.
Marairaice fuska ta yi kamar za ta yi kuka, kuma da gaske gab ta ke da ta yi kukan...
“Wallahi na koshi…� ta furta da iyakar gaskiyarta.
Inda Allah ya ceceta kafin ya ce komai Daddy ya yi kiransa. Ya mike ya bar dining area din, ita kuma ta karasa tattare kayan da suka ci abincin, ta yi kicin da su. Ta dawo ta gyara komai, ba ta zauna a cikinsu ba ta ce musu da abin da za ta yi, ta haye sama.
Aalimah ta dauko daya daga cikin text books dinta na makaranta ‘Basic and clinical pharmacology’ ta soma budewa wai don ya kawar mata da nacin tunanin Abulkhair da ya daura aure da zuciyarta cikin dan lokaci kalilan. Amma kowanne shafin littafin wanda (Bartram G. Katzung) ya rubuta, fuskar ABOULKHAIR ke appearing maimakon rubutun littafin. Babu shiri ta rufe ta soma kuka. Kuka sosai na tunanin wata cutar kwakwalwar ta same ta. Yo in ba hallucination ba wanda ta san ana ganin mutane a cikinsa mene ne wannan? Hayaniyar su Basma ta ji suna hawowa benen. Da gudu ta yi toilet ta shige ta rufe kanta.
Tsaida kukan ta yi, ta wanke fuskarta da sabulu, sannan ta fito. Canza kaya suke zuwa na barci, sai ita ma ta bi layinsu. Suna ta karadinsu irin wanda suka saba kafin su kwanta barci. Babu wadda hankalinta ya kai ga idanunta balle su yi noticing canjin yanayi a tare da ita. Kuma dama sun sani; ba ta cika surutu ba, sannan ba duka hirarrakinsu ta ke ganewa ba.
Wani sabon dare ga Aalimah Mansour Raazee, mai cike da rudani, wanda ya kawo sauyi cikin kyakkyawar rayuwarta. She fall madly in LOVE ba tare da saninta ba, kuma ba tare da ta shirya wa hakan ba. Barcin daren yau ya zamo ragagge a gare ta. Ga shi ita kanta ba ta san hakikanin abin da ya faru da itan ba. Abin da ta sani kawai shi ne, zuwan Abulkhair ya yi affecting kwakwalwarta da jin dadinta da walwalar ta.
Tana hasashen yadda za ta iya ci gaba da rayuwa a haka, cikin gidan Ishaq Raazi, muddin dansa Abulkhair na cikinsa. Sai asuba wani wahalallen bacci ya sure ta, wanda a cikinsa ta ga mutum biyu; Mahmoud da Abulkhair cikin yanayi mabanbanci.
Aboulkhair cikin farin ciki, Mahmoud cikin tsaka mai wuya, kuma wai duk a kanta. Sai da ta makara sallar asuba. Ita da ta ke tashin su Basma sallah, yau su suka tashe ta. Idonta ya yi jajawur ya yi luhu-luhu da kyar ta ke iya bude shi. Khaleesat ce ta fara lura da idanunta.
“Aal, kin tashi da ciwon ido?�
Basma ta juyo, “Ai kuwa. In mun shiga makaranta sai mu je hospital a sa miki magani�.
Duk damuwa ta bayyana a fuskokinsu. Murmushin kwantar da hankali ta yi musu.
“Ba fa ciwo yake yi ba, laifina ne, ni ce ban yi barci yadda ya kamata ba�.
“But why?� Har suna hada baki wurin tambaya.
Sai ta rasa abin da za ta ce musu. Su kuma sun ki dauke idonsu a kanta har da kama kugu suna kalonta cikin tuhuma kamar su din ta yi wa laifin rashin barcin. Kafadunsu ta dafa duk su biyu a tsanake, ta ce, “calculus! I’m finding it difficult to understand�.
Kuma da gaske din ne, darasin yana ba ta matukar wahala wajen fahimta duk da kwarewarta a fannin lissafi. Basma ta yi dariya kafin ta yi dan juyi a tsakiyar dakin, ta ce, “Hey! Daina damuwa Aal, we have a calculus-gem in this house. Just tell him your problem and consider it solved! Na rantse sai kin ci abin da ya fi ‘A’ a calculus�.
Har ta je kitchen ta hada breakfast ta dawo ta fara shiryawa surutun da suke yi kenan. Na irin kwarewar Yayan nasu a fannonin lissafi da dama.
“Yo Allah na tuba ‘calculus’ ai shan ruwa ya fi shi sauki a wajen Monsieur Abulkhair, da har wani cikin gidan nan zai hana kansa barci a kansa. Sannan he is doing his teaching patiently. Unlike this ANNOYING son of Mum…!� (yana yin koyarwar sa a tsanake, ba kamar wannan dan Mummyn mai ban haushi ba).
Suka kyalkyale da dariya har da tafawa. Bude kofar aka yi ba zatonsu ba tsammani, wanda suke zunden nasa ne ya shigo. Kayan barci ne a jikinsa wadanda suka nuna manyan damatsansa (muscles) da halittar kasaitaccen kirjinsa wanda ke lullube cikin shara-sharan pajamas ruwan madara ‘yan gidan Ralph Lauren. Wannan kwantaccen gashin na jiya it’s no more like it was before. Ya cukurkude ya hargitse. Yana shigowa fada ya rufe su da shi.
6/28/21, 7:32 AM - Buhainat: Aalimah
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI
07030137870
“…You goddam talkatives!Kuna duba agogo kuwa? Har downstairs nake jiyo karadinku tun asuba. Kun hana ni barci, kun hana kunnena zaman lafiya. Kun san cewa doguwar tafiya na yi, ina bukatar hutu, kuma ba abin da na tsana irin a hana ni barci da safe… za ku wuce ku karya ku tafi, ko shi ma Daddyn sai kun makarar da shi ya hana ni barci saboda ku?�
Turanci yake zubawa kamar Charles Dickens ya sauka a Massachusetts. Tuni jikin Aalimah ya hau bari an fara abin da ta ki jini, wato (fada). Sum-sum-sum suka shiga wucewa, Allah ya so duk sun gama shiryawa. Basma har da zumburo baki, Aalimah ce karshen wucewa ta gabansa duk ta gigice. Babban abin da ke maida ita upset shi ne hargagi. Ai kuwa ta ci uban tuntube da kafarsa ta dama, ta tafi za ta ci da baka. Da wani irin zafin nama ya taro ta da dukkan hannayensa. Ido ya bude yana kallon cikin idanunta sosai da dukkan nasa idanun, kamar mai son karanto al’amarin da ke cikinsu. Ba ya so ya yarda da abin da kyawawan idanun ke gaya masa, cewa al’amarin da ke cikinsu, daya yake da wanda ya hana shi runtsawa a tsayin daren bakidayansa.
Yadda nasa idon ya tasa ya yi jajawur yayi luhu - luhu haka idanun nan da ke kallonsa suke. Sai dai kuma a nassi mai kyau na zuciyarsa na gaya masa, kada ya bari ta gane, dukkaninsu are too young da soyayya! Yanzu ne suke kokarin gina future dinsu. Kafin haka, soyayya da duk abin da ya shafe ta ba nasa ba ne. Infact, it’s out of his vocab bank (vocabulary bank).
Zuciya ce dai da ba ka da iko da linzaminta. He has a mission that he want to fulfill(yanada uzrin da yake son gabatarwa) kafin soyayyah. Yanzu ne yake shekara ta uku a jami’a, sannan yana da mashahuriyar damuwa da ke danne duk wani situation da ka iya samun zuciyarsa, na farin ciki ko na bakin ciki.
He will help his sister to concentrate on what she’s here for (zai taimakawa ‘yar uwarsa ta maida hankali kan abindaya kawota) ta manta da shi da duk abin da ya shafe shi.
A hankali ya lumshe idonsa na tsawon lokaci ba tareda ya san lokacin da yayi hakan ba, sannan ya bude su a kan Aalimah, wadda ta yi suman wucin-gadi a hannunsa. Dago ta ya yi ta tsaya da kafafunta, sannan ya sake ta, amma bai iya ci gaba da fadan ba, kamar wanda aka daurewa bakin. Ita ce karshen fita, da sassarfa ya biyo stairs ya sauko daga benen. Bai kalle su a dining ba ya wuce dakinsa.
Cikin quilt dinsa ya shige da sauri ya dukunkune kansa, zuciyarsa na racing wajen bugawa. Numfashin da yake shaka ya ji yana sauyawa da wani irin mayataccen kamshi, kuma kamshin (is feminine) wato na mace ne mai tada hankalin duk wani lafiyayyen Da namiji. Ya fahimci ma kamshin daga jikinsa yake, in fact shi yake kamshin sexy perfume din (‘Nude’ by Rihanna) wanda babu tantama a jikin Aalimah ya kwaso. Abulkhair ya ji komai nasa yana canzawa har numfashinsa. Wani situation ne da bai taba tsintar kansa a ciki ba.
Ya dauki lokaci cikin yanayin da yake ciki din yana kuma neman hanyar samun sauki. First, he have to get rid out of these clothes.(Gara ya cire kayan nan). Mikewa ya yi zaune ya soma zare su daya bayan daya, sannan ya shige toilet ya sakar wa kanshi shower.
Saukar ruwan a tsakar kansa zuwa jikinsa na tafiya tare da kawo sassauci a bugun zuciyarsa. Duka wannan ya faru cikin mintunan da ba su wuce goma sha biyar ba. Al’amarin ya zamo tamkar wani majigi da ya gifta a idanunsa. Har mamakin kansa yake yi, tunda dai ba yau ya fara ganin mata da yin alaqa da su ba. Matan ma ajin farko da suka amsa sunan mata a duk inda ya yi rayuwarsa cikin kasar America, daga sakandire har jami’a.
Sunyi dukkan rayuwarsu a Washington D.C ainahinaikin da ya yi sanadin kawo mahaifinsu kasar Amurka(consulate officer ne a baya). A Washington din duk suka yi sakandire shi da Yayansa MU’AZZAM, shi Aboulkhair bai ma karasa a can din ba.Abubuwa da yawa suka raba Daddynsu da Niger consulate America.Amma ba don dukkaninsu suna so ba.
Na farko rashin lafiyar Mu’azzam, wanda likitoci suka bada shawarar inda hali a sauya masa inda yake rayuwa zai fi jin dadin canza rayuwarsa, kuma a barshi a inda ya fi so. Sannan kuma Daddyn ya samu hanyoyin budi daban-daban wadanda samunsu ya fi na consulatedin kasarshi nesa ba kusa ba. Sannan lafiyar Mu’az tafi musu komai. Wannan ne mafarin komawarsu Massachusetts ba don suna son garin ba.
Kamar wanda ya saba zama a Abuja ne a ce ya koma Adamawa ko Yobe. Sai dai Alhamdu lillahi lafiyar Mu’az ta inganta.
Ya zabi Jami’ar Louisiana don ya yi nisa da Mu’azzam, saboda wasu dalilai da dama, muhimmi shi ne; ba ya iya jure ganin Mu’azzam cikin halin da ya kan samu kansa.
Bai taba sanya al’amarin mata a gabansa ba balle ya dame shi. Burinsa kadai ya zama ‘psychiatric doctor’ don ya san mene ne matsalar Mu’azzam ciki da bai dinta, ya yi masa maganinta. In haka ne, kenan abin da zuciyarsa ke darsa masa daga jiya zuwa yau akan... Aalimah ba nasa ba ne! He has to be cautious in his relationship with her(dole ya zama mai taka-tsan—tsan a mu’amalar shi da ita). Daga shi har ita, sunadafocus fiye da wannan da zuciyarsu ke son kai su.
Kwankwasa kofar dakinsa ake yi, tun ana yi a hankali har aka soma yi da dan karfi. ‘shower’ din ya kashe ya janyo tawul ya goge kansa da jikinsa a gaggauce. A gurguje ya saka kaya yana jiyo muryar Basma a kofar dakin nasa tana ambaton sunansa a tausashe“Monsieur Aboulkhair�. (Kalmar‘Monsieur’ da suke kiran shi da ita is a French-speaking word da ake amfani da ita don nuna girmamawa ga namiji kamar a ce Mr, ko makamancin haka)�.
Bude kofar ya yi kafin ya ce komai ta mika masa mukullin mota, “Daddy latti, ya ce ka yi ajiye mu, in mun tashi ka dauko mu. Ya fasa neman direban tunda ga ka�. Ta fada tana dan ja da baya koda zai kawo mata mari.
Harararta ya yi, sannan ya karbi mukullin. Ya san daddy ya yi haka ne don ya hana shi barcin safensa. Ai shikenan, shi ma dama ya fara tunanin guduwa ya bar musu gidansu zuwa inda zai samu hutun jiki da na zuciya sosai, ya yi huta daga tunanin bakuwar gidan su Aalimah mai kokarin raba shi da numfashinsa da burikansa.
Haka ya sanya su a mota ya kai su makaranta daya bayan daya, Aalimah na jin Khaleesat da Basma suna rada a kunnen junansu,
“What’s wrong with this man ne?� (Me ke damun wannan mutumin ne?) In ji Khaleesat.
“He come with strange behaviours, I’m praying not he becomes ANNOYING like the other person� (ya zo da sababbin dabi’u, ina addu’ar Allah yasa kada ya zamo mai ban haushi kamar daya mutumin)�. Ta fada cike da damuwa.
Abulkhair na da kyakkyawan ji at times, sosai ya ji abin da suka ce. Ya dafe sitiyarinsa ya ci gaba da sarrafa shi cikin gwaninta yana murmushi. Can kasan zuciyarshi kuma ya ji ba dadi for calling Mu’azzam da ANNOYING da suke yi tunda suka fara wayo. Wane bayani zai yi musu su fahimci. Yayansu is not annoying, but rather; he’s fighting with his destiny?(Yayan su ba mai ban haushi bane, a’ah, yana gwagwarmaya ne da kaddarorinsa). Shekarunsu da iliminsu sun yi kadan su san mece ce matsalar Yayan nasu?
Ya fara sauke Yesmin da Khaleesat, sannan ya kawo Basma da Aalimah har gaban block din da za su shiga lacca, ya sauke Basma, ya kara gaba kadan zai sauke Aalimah ba tare da ya ce da su komai ba. Da ta zo fita kasa jurewa ta yi sai da ta saci kallonsa, shi ma satar kallon nata yake yi ta gefen idanunsa, har ta fice rungume da folder dinta a kirjinta. Tafiya ta ke yi cikin nutsuwa babu waiwaye. Wani numfashi ya ja ya kuma sauke shi sharply, sannan ya ja motar.
Daga university of Boston kai tsaye ma’aikatar su Daddy ya nufa. Akwai abubuwa da yawa da yake so su tattauna, wadanda suke bukatar nutsuwa, kuma wadannan yaran da hayaniyarsu ba za su barsu su tattauna su a gida ba, sannan ba zai iya komawa gida ya yi ta jira har sai Daddyn ya dawo ba, hypertension sai ya kama shi in tunanin Aalimah bai zauta shi ba.
Yana nukatar karin bayani akan ta daga bakin Babansa. Yana kuma son jin me ya hada iyayensa fada duk da ba yau suka soma ba, kuma kullum Mummy ce da laifi sabida anti-social nature dinta. Ya kira ta jiya ya gaya mata ya zo gida zai yi four weeks winter holiday dinsa bai ganta ba, ya kuma tambayi Daddy tana ina? Ya ce masa tana Las Vegas, ba tareda wani karin bayani ba, ya tambaye ta yaushe za ta dawo?
Ce masa ta yi Daddyn ya kore ta, kuma ita ba za ta dawo ba sai Aalimah ta koma Nigeria. Ya tambaye ta abin da ya faru ta ce ya tambayi wanda ya kore ta. Ko kadan bai sa damuwar komai a ransa ba ya ci gaba da sabgoginsa don ya riga ya fahimci abin da ya faru. Mummy and her anti-social nature and the existence of stranger. Maybe this time around Daddyya motsa kwanjinsa, ita kuma tunda tun farko ba haka ya sabar mata ba ta kasa dauka.
Haka ya yi ta kiyasce-kiyasce har ya iso ofishin Daddy.
Sai da sakatariyar Daddy ta yi masa iso, ya kuma bi layin mutum uku da ke kan layin ganin Daddyn, daga bisani ya samu ya shiga. Fridge ya fara budewa ya sha ruwa sosai. Kansa ya dau zafi da yawa, Daddyn na kallonsa yana ci gaba da aiki cikin na’ura mai kwakwalwa. Sannan ya zo ya zauna a kan kujerar da ke fuskantar makeken tebirin Ishaq Raazee. Dan Nijar din da ya rikide ya zama gawurtaccen Ba’amurke cikin shekaru ashirin da bakwai tsayin zamansa a Amurka. Ishaq Raazee ya raini ‘ya’yansa da rainon Bature ta hanyar maida su manyan abokansa, daga matan har mazan. Ba sa iya boye masa komai na rayuwarsu. Shi ya sansu fiye da sanin da mahaifiyarsu ta yi musu. Shi tashi soyayyar ba ta hana shi ba su tarbiyyah ba, amma ita ba ta san komai ba sai son ‘ya’ya da kokarin ganin sun fi ‘ya’yan kowa gata da jin dadi.
Duk amincin Abulkhair da Babansa yau ya samu kansa da kasa bude mishi cikinsa da amayar masa da damuwarsa. Sabon al’amarin da ya hana shi bacci daren jiya bakidayansa, ya hana shi nutsuwa tun wayewar gari.
Ya zo gaban mahaifinsa don ya gaya masa ko ya samu sassauci, amma ga shi ya kasa. Kallonsa Daddy ya ci gaba da yi yana murmushi, bai ce komai ba shi kadai ya san me ya fahimta tun jiya a tare da Dan nasa. Amma tunda bai furta ba bari ya bi shi da yadda ya zo masa.
“Mummy, na yi magana da ita ta ce kai ne ka kore ta�.
Aboulkhair ya katse shirun nasu ganin Daddy bai da niyyar tankawa.
“Ni ban kore ta ba, zabi na bata�.
Ya fada ba tare da ya dauke kai daga aikin da yake yi cikin na’ura mai kwakwalwa ba. Abulkhair ya yi dan jim! Kafin ya ce,
“Is that related to Aal… I mean Aalimah?�. Ya fada kansa a kasa, muryarsa na sarkewa da ya zo furta sunan. Tun jiya in zai furta sunan sai harshensa ya sarke ya rasa dalili.
Murmushi Daddy ya yi, ya kashe system din gabadaya ya juya kujerarsa mai tayoyi baya ya fuskance shi da murmushi bisa lebbansa, “Pronounce the name properly (furta sunan yadda yake daidai)�.
Kunya ta rufe Abulkhair, ya kasa dago ido ya kalli Babansa.
Ji yake yana dagowa Daddy zai karance abin da ke cikin idanunsa tsaf! Tunda ga shi yana kokarin karanto rudanin da ke tattare da muryarsa akan furta sunanta. Shi kuma ba zai so hakan ba, saboda shi kansa bai yarda da kansa ba. Bai yarda da feelings dinsa are morethan emotion ba. Bai yarda zuciyarsa ta kamu da son Aalimah ba, don a ganinsa babu dalilin hakan.
Abin da ya yarda da shi shine there are certain characteristics about her da za su rikita kowanne Da namiji mai cikakken hankali ba shi kadai ba. Her well-structured body, her pointed nose… these thick eye-lashes… this red soft lips are all breadth taking! (Wannan ginannen jikin nata, wannan tsayayyen hancin nata, wadannan jajayen tausasan lebban, wannan cikakken gashin idon da gashin girar, duka masudauke numfashin mutum ne!) Kowanne namiji zai yi mafarkin samunta matsayin matar aurensa!!!
Shirun Abulkhair ya yi yawa, sannan ya ki dago kansa. Daddy ya ba shi mintoci masu kyau don ya gama duk tunanin da zai yi, amma ganin ba shi da niyyar magana kuma ya kasa dubansa, sannan yana cinye masa lokaci, sai ya kira sunansa cikin nutsuar murya. For all he know, Abulkhair dinsa ba miskili ba ne, Allah ya sa kada Aalimah ta sauya shi. In hakan ta faru ya ya zai yi da miskilai biyu? A Aboulkhair yake samun duk abin da yake so daga aboki, he is cheerful as well as passionate. Dayan, da shi da babu, duk daya. Ba rashin lafiya kadai ke aiki a jikinsa ba, har da hali. Tunda yana samun sound-medical treatment.
A wannan din yake jin dadi, yake samun duk abin da yake so daga aboki, ba zai so abin da zai yi spoiling farin cikin Aboulkhair ba, zai yi duk wani kokari ya samar da shi gare shi, ko da hakan na nufin… hadiye sauran tunanin ya yi, don yana ganin nan din ba filin yinsa ba ne ba.
Dago kansa ya yi ya dubi mahaifinsabut he is still lowering his gaze (har yanzu yana yin kasa da ganinsa) duk a kokarinsa na kada mahaifin nasa ya karanto idanunsa.
“Wouldn’t you speak out abin da ya kawo ka? Kana ganin ayyukan da ke gabana, sannan dube ka ko wanka ba ka yi ba, dubi kayan jikinka, dubi gashin kanka. Dubi idanunka, bana jin duk son ka da barci yau ka yi shi yadda ya kamata, ka koma gida za mu yi maganar Mummyn in na dawo, amma nan office ne�.
Yana so ya gaya masa ba maganar Mummy ce kadai ta kawo shi ba, in da sabo ai sun saba da cases din Mummy da yin yajinta zuwa wajen Danta. Gara ya yi ta zama a gaban Daddyn har ya gama aikin su koma gidan tare, a kan ya koma ya zauna shi kadai a gidan. Bai san me zai faru da shi ba, he’s afraid of going back to Boston University.
Tunda can din ma in ya je bai san me zai aikata ba. Gara nan din sau dubu a kan ya koma gida.
“Zan jira ka Daddy har ka gama, sai mu koma tare�.
Ya samu kansa da furta kalaman daki-daki ko Daddyn ya fi fahimtarsa. Amma Daddyn ya nuna shi bai fahimci komai ba.
“Ni kuma bazan iya ci gaba da aiki na kazo ka sani a gaba ba sai ka ce wani uwata. In dai uwarka ce na ce ban kore ta ba zabi na bata. In za ta iya sona da duk wanda ya shafe ni ta zauna, in ba za ta iya ba she could go to someone who has no relatives, but Ishaq Raazee is a family Man. Wannan shi ne kawai sakona gare ta. Abin da ta zaba determines ci gaba da zamanta gaban ‘ya’yanta or not�.
Sosai ya fahimci Daddyn, amma har yanzu bai yi magana a kan gabar da yake son ji ba. Kuma da alama ba shi da niyya. Ya ci gaba da zama, ya ci gaba da yin shirun.
Daddy dai kallonsa yake yana cewa a ransa, ‘I wouldn’t, untill you did (ba zan yi ba har sai ka yi)’.
Mikewa ya yi ya dauki mukullin motar da ya aje a kan tebirin Daddy ya nufi kofa. Sai da ya kai bakin kofa ya kama handle din kofar sannan Daddy ya kira sunansa. Bai amsa ba, kuma bai juyo ba, amma ya dakata.
“Drive with care (ka yi tuki da kula)�. Abin da ya ce da shi kawai kenan. Ya karasa ficewa daga office din.
Maimakon ya dauki hanyar gida, sai ya samu hannunsa da ke kan sitiyari da juya kan motar ya dauki hanyar Boston University. Jin kansa yake kamar wanda ake directing ya kasacontrolling kansa. A hankali yake tukin motar har ya tsaya a inda aka tanada don adana motoci (parking lot) da ke dab da ‘school of medical sciences’ na jami’ar. Kwantar da kansa ya yi a kan sityari yana tunanin me ya kawo shi? Don me zai zo? Sai ya ji kamar ana yi masa amsa-kuwwa cikin kwanyar kansa da cewa, kada ya koma, atleast ya samu ya ganta.
Bai zo don ya hana ta karatu ba sai don kawai ya ganta. Ganin nata shi ne kadai zai samar masa da nutsuwa ya koma cikin hayyacinsa.
Luckly for him, sai ya hango ta ita da wani saurayi bature zaune kasan wata farar lema da fararen kujeru da tebiri a tsakiyarsu. Daga gani karatu suke yi, amma shi sai idanunsa suka zarce suka soma ba shi delusion na abin da ba haka yake ba. Wani irin bacin rai da bai taba ji a rayuwarsa ba.
Yana can zuciyarsa na neman raba shi da numfashinsa saboda ita, tana nan happily accompanied with someone. Wanin ma wani banzan arne mai kama da skeleton. Tana nufin ta ce; duk wannan azabar shi kadai yake kwankwadarta ko me? Wata zuciyar ta ce, ya ja motar ya yi tafiyarsa ya bar garin ya bi Mamansa, ya ga sanyin idaniyarsa (Mu’azzam) ya manta da Aalimah tunda dama bai bari Daddy ya gane ba. Amma bangare mafi rinjaye ya ce ya dan faffallawa yaron mari ko hudu ne ya huce. Da sauri kuma ya tuna me yin hakan ke nufi a kasar bature. A kan Aalimahr ya kamata ya huce haushinsa, tunda ita har dukan nata zai iya yi ya zauna lafiya.
Aalimah da Alex, sun dukufa karatu, yana koya mata calculus. A wurinta sau dubu gara Alex ya koya mata a kan Monsieur din su Basma. She can’t even look into his eyes balle ya koyar da karatu. Akwai wani abu mai kama da sihiri cikin kwayar idon sa dake fizgarta wanda tun shigowarsa gidansu ya hana zuciya da kwakwalwarta zama lafiya. Sannan shi kansa tunda ya zo bai zauna lafiya ba, daga fada sai masifa wanda hakan ya sanya mata matsanancin tsoronsa bayan unexpressable emotions and feelings din da ta kwana da su a kansa.
A karshe kuma ta yi wa kanta fada, ta gaya wa zuciyarta wannan al’amarin da a yanzu ta gama fahimtar ‘soyayyah’ ne irin wanda ke kasancewa tsakanin mace da namijin da suka kai munzalin balaga comes at a very wrong time for her! ( ya zo a lokacin da bai dace ba). Sannan it could destory her parents dream on her… it can also destroy her future ( zai lalata mafarkin iyayenta akanta, sannan ya rusa future dinta) idan ba ta sanya taka-tsan-tsan ba da jajircewa a cikinsa. Ta sha jin yadda maza suke yaudarar ‘yammata su hana su karatu, su yi musu cikin shege, iyayensu kuma su tsine musu su shiga karuwanci ko su haife shege. Zuciyarta ba ta taba kawo mata tunanin aure nan kusa ba.
Da wannan dalilin dama wasu da dama ya sanya tun safe ta ke yaki da zuciyarta a kan Aboulkhair duk da cewa dan uwanta ne, ta san ba zai cutar da ita ba. Amma ba a shaidar maza a wannan fannin, Mahmoud kadai zata iya shaida a cikin maza. Sannan shi da kansa (Aboulkhair ) ya tilastawa zuciyarta ta ji tsoronsa daga yadda yake behaving ga kannensa tun jiya. Sosai ta himmatu wajen yakice shi daga zuciyarta ta ke ta karatu tun safe. Sun yi lacca biyu suna da hutun awa daya kafin su koma wata, shi ne ta roki Alex ya yi highlighting dinta abin da ya shige mata duhu.
6/28/21, 7:32 AM - Buhainat: Aalimah
SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI
07030137870
“…You goddam talkatives!Kuna duba agogo kuwa? Har downstairs nake jiyo karadinku tun asuba. Kun hana ni barci, kun hana kunnena zaman lafiya. Kun san cewa doguwar tafiya na yi, ina bukatar hutu, kuma ba abin da na tsana irin a hana ni barci da safe… za ku wuce ku karya ku tafi, ko shi ma Daddyn sai kun makarar da shi ya hana ni barci saboda ku?�
Turanci yake zubawa kamar Charles Dickens ya sauka a Massachusetts. Tuni jikin Aalimah ya hau bari an fara abin da ta ki jini, wato (fada). Sum-sum-sum suka shiga wucewa, Allah ya so duk sun gama shiryawa. Basma har da zumburo baki, Aalimah ce karshen wucewa ta gabansa duk ta gigice. Babban abin da ke maida ita upset shi ne hargagi. Ai kuwa ta ci uban tuntube da kafarsa ta dama, ta tafi za ta ci da baka. Da wani irin zafin nama ya taro ta da dukkan hannayensa. Ido ya bude yana kallon cikin idanunta sosai da dukkan nasa idanun, kamar mai son karanto al’amarin da ke cikinsu. Ba ya so ya yarda da abin da kyawawan idanun ke gaya masa, cewa al’amarin da ke cikinsu, daya yake da wanda ya hana shi runtsawa a tsayin daren bakidayansa.
Yadda nasa idon ya tasa ya yi jajawur yayi luhu - luhu haka idanun nan da ke kallonsa suke. Sai dai kuma a nassi mai kyau na zuciyarsa na gaya masa, kada ya bari ta gane, dukkaninsu are too young da soyayya! Yanzu ne suke kokarin gina future dinsu. Kafin haka, soyayya da duk abin da ya shafe ta ba nasa ba ne. Infact, it’s out of his vocab bank (vocabulary bank).
Zuciya ce dai da ba ka da iko da linzaminta. He has a mission that he want to fulfill(yanada uzrin da yake son gabatarwa) kafin soyayyah. Yanzu ne yake shekara ta uku a jami’a, sannan yana da mashahuriyar damuwa da ke danne duk wani situation da ka iya samun zuciyarsa, na farin ciki ko na bakin ciki.
He will help his sister to concentrate on what she’s here for (zai taimakawa ‘yar uwarsa ta maida hankali kan abindaya kawota) ta manta da shi da duk abin da ya shafe shi.
A hankali ya lumshe idonsa na tsawon lokaci ba tareda ya san lokacin da yayi hakan ba, sannan ya bude su a kan Aalimah, wadda ta yi suman wucin-gadi a hannunsa. Dago ta ya yi ta tsaya da kafafunta, sannan ya sake ta, amma bai iya ci gaba da fadan ba, kamar wanda aka daurewa bakin. Ita ce karshen fita, da sassarfa ya biyo stairs ya sauko daga benen. Bai kalle su a dining ba ya wuce dakinsa.
Cikin quilt dinsa ya shige da sauri ya dukunkune kansa, zuciyarsa na racing wajen bugawa. Numfashin da yake shaka ya ji yana sauyawa da wani irin mayataccen kamshi, kuma kamshin (is feminine) wato na mace ne mai tada hankalin duk wani lafiyayyen Da namiji. Ya fahimci ma kamshin daga jikinsa yake, in fact shi yake kamshin sexy perfume din (‘Nude’ by Rihanna) wanda babu tantama a jikin Aalimah ya kwaso. Abulkhair ya ji komai nasa yana canzawa har numfashinsa. Wani situation ne da bai taba tsintar kansa a ciki ba.
Ya dauki lokaci cikin yanayin da yake ciki din yana kuma neman hanyar samun sauki. First, he have to get rid out of these clothes.(Gara ya cire kayan nan). Mikewa ya yi zaune ya soma zare su daya bayan daya, sannan ya shige toilet ya sakar wa kanshi shower.
Saukar ruwan a tsakar kansa zuwa jikinsa na tafiya tare da kawo sassauci a bugun zuciyarsa. Duka wannan ya faru cikin mintunan da ba su wuce goma sha biyar ba. Al’amarin ya zamo tamkar wani majigi da ya gifta a idanunsa. Har mamakin kansa yake yi, tunda dai ba yau ya fara ganin mata da yin alaqa da su ba. Matan ma ajin farko da suka amsa sunan mata a duk inda ya yi rayuwarsa cikin kasar America, daga sakandire har jami’a.
Sunyi dukkan rayuwarsu a Washington D.C ainahinaikin da ya yi sanadin kawo mahaifinsu kasar Amurka(consulate officer ne a baya). A Washington din duk suka yi sakandire shi da Yayansa MU’AZZAM, shi Aboulkhair bai ma karasa a can din ba.Abubuwa da yawa suka raba Daddynsu da Niger consulate America.Amma ba don dukkaninsu suna so ba.
Na farko rashin lafiyar Mu’azzam, wanda likitoci suka bada shawarar inda hali a sauya masa inda yake rayuwa zai fi jin dadin canza rayuwarsa, kuma a barshi a inda ya fi so. Sannan kuma Daddyn ya samu hanyoyin budi daban-daban wadanda samunsu ya fi na consulatedin kasarshi nesa ba kusa ba. Sannan lafiyar Mu’az tafi musu komai. Wannan ne mafarin komawarsu Massachusetts ba don suna son garin ba.
Kamar wanda ya saba zama a Abuja ne a ce ya koma Adamawa ko Yobe. Sai dai Alhamdu lillahi lafiyar Mu’az ta inganta.
Ya zabi Jami’ar Louisiana don ya yi nisa da Mu’azzam, saboda wasu dalilai da dama, muhimmi shi ne; ba ya iya jure ganin Mu’azzam cikin halin da ya kan samu kansa.
Bai taba sanya al’amarin mata a gabansa ba balle ya dame shi. Burinsa kadai ya zama ‘psychiatric doctor’ don ya san mene ne matsalar Mu’azzam ciki da bai dinta, ya yi masa maganinta. In haka ne, kenan abin da zuciyarsa ke darsa masa daga jiya zuwa yau akan... Aalimah ba nasa ba ne! He has to be cautious in his relationship with her(dole ya zama mai taka-tsan—tsan a mu’amalar shi da ita). Daga shi har ita, sunadafocus fiye da wannan da zuciyarsu ke son kai su.
Kwankwasa kofar dakinsa ake yi, tun ana yi a hankali har aka soma yi da dan karfi. ‘shower’ din ya kashe ya janyo tawul ya goge kansa da jikinsa a gaggauce. A gurguje ya saka kaya yana jiyo muryar Basma a kofar dakin nasa tana ambaton sunansa a tausashe“Monsieur Aboulkhair�. (Kalmar‘Monsieur’ da suke kiran shi da ita is a French-speaking word da ake amfani da ita don nuna girmamawa ga namiji kamar a ce Mr, ko makamancin haka)�.
Bude kofar ya yi kafin ya ce komai ta mika masa mukullin mota, “Daddy latti, ya ce ka yi ajiye mu, in mun tashi ka dauko mu. Ya fasa neman direban tunda ga ka�. Ta fada tana dan ja da baya koda zai kawo mata mari.
Harararta ya yi, sannan ya karbi mukullin. Ya san daddy ya yi haka ne don ya hana shi barcin safensa. Ai shikenan, shi ma dama ya fara tunanin guduwa ya bar musu gidansu zuwa inda zai samu hutun jiki da na zuciya sosai, ya yi huta daga tunanin bakuwar gidan su Aalimah mai kokarin raba shi da numfashinsa da burikansa.
Haka ya sanya su a mota ya kai su makaranta daya bayan daya, Aalimah na jin Khaleesat da Basma suna rada a kunnen junansu,
“What’s wrong with this man ne?� (Me ke damun wannan mutumin ne?) In ji Khaleesat.
“He come with strange behaviours, I’m praying not he becomes ANNOYING like the other person� (ya zo da sababbin dabi’u, ina addu’ar Allah yasa kada ya zamo mai ban haushi kamar daya mutumin)�. Ta fada cike da damuwa.
Abulkhair na da kyakkyawan ji at times, sosai ya ji abin da suka ce. Ya dafe sitiyarinsa ya ci gaba da sarrafa shi cikin gwaninta yana murmushi. Can kasan zuciyarshi kuma ya ji ba dadi for calling Mu’azzam da ANNOYING da suke yi tunda suka fara wayo. Wane bayani zai yi musu su fahimci. Yayansu is not annoying, but rather; he’s fighting with his destiny?(Yayan su ba mai ban haushi bane, a’ah, yana gwagwarmaya ne da kaddarorinsa). Shekarunsu da iliminsu sun yi kadan su san mece ce matsalar Yayan nasu?
Ya fara sauke Yesmin da Khaleesat, sannan ya kawo Basma da Aalimah har gaban block din da za su shiga lacca, ya sauke Basma, ya kara gaba kadan zai sauke Aalimah ba tare da ya ce da su komai ba. Da ta zo fita kasa jurewa ta yi sai da ta saci kallonsa, shi ma satar kallon nata yake yi ta gefen idanunsa, har ta fice rungume da folder dinta a kirjinta. Tafiya ta ke yi cikin nutsuwa babu waiwaye. Wani numfashi ya ja ya kuma sauke shi sharply, sannan ya ja motar.
Daga university of Boston kai tsaye ma’aikatar su Daddy ya nufa. Akwai abubuwa da yawa da yake so su tattauna, wadanda suke bukatar nutsuwa, kuma wadannan yaran da hayaniyarsu ba za su barsu su tattauna su a gida ba, sannan ba zai iya komawa gida ya yi ta jira har sai Daddyn ya dawo ba, hypertension sai ya kama shi in tunanin Aalimah bai zauta shi ba.
Yana nukatar karin bayani akan ta daga bakin Babansa. Yana kuma son jin me ya hada iyayensa fada duk da ba yau suka soma ba, kuma kullum Mummy ce da laifi sabida anti-social nature dinta. Ya kira ta jiya ya gaya mata ya zo gida zai yi four weeks winter holiday dinsa bai ganta ba, ya kuma tambayi Daddy tana ina? Ya ce masa tana Las Vegas, ba tareda wani karin bayani ba, ya tambaye ta yaushe za ta dawo?
Ce masa ta yi Daddyn ya kore ta, kuma ita ba za ta dawo ba sai Aalimah ta koma Nigeria. Ya tambaye ta abin da ya faru ta ce ya tambayi wanda ya kore ta. Ko kadan bai sa damuwar komai a ransa ba ya ci gaba da sabgoginsa don ya riga ya fahimci abin da ya faru. Mummy and her anti-social nature and the existence of stranger. Maybe this time around Daddyya motsa kwanjinsa, ita kuma tunda tun farko ba haka ya sabar mata ba ta kasa dauka.
Haka ya yi ta kiyasce-kiyasce har ya iso ofishin Daddy.
Sai da sakatariyar Daddy ta yi masa iso, ya kuma bi layin mutum uku da ke kan layin ganin Daddyn, daga bisani ya samu ya shiga. Fridge ya fara budewa ya sha ruwa sosai. Kansa ya dau zafi da yawa, Daddyn na kallonsa yana ci gaba da aiki cikin na’ura mai kwakwalwa. Sannan ya zo ya zauna a kan kujerar da ke fuskantar makeken tebirin Ishaq Raazee. Dan Nijar din da ya rikide ya zama gawurtaccen Ba’amurke cikin shekaru ashirin da bakwai tsayin zamansa a Amurka. Ishaq Raazee ya raini ‘ya’yansa da rainon Bature ta hanyar maida su manyan abokansa, daga matan har mazan. Ba sa iya boye masa komai na rayuwarsu. Shi ya sansu fiye da sanin da mahaifiyarsu ta yi musu. Shi tashi soyayyar ba ta hana shi ba su tarbiyyah ba, amma ita ba ta san komai ba sai son ‘ya’ya da kokarin ganin sun fi ‘ya’yan kowa gata da jin dadi.
Duk amincin Abulkhair da Babansa yau ya samu kansa da kasa bude mishi cikinsa da amayar masa da damuwarsa. Sabon al’amarin da ya hana shi bacci daren jiya bakidayansa, ya hana shi nutsuwa tun wayewar gari.
Ya zo gaban mahaifinsa don ya gaya masa ko ya samu sassauci, amma ga shi ya kasa. Kallonsa Daddy ya ci gaba da yi yana murmushi, bai ce komai ba shi kadai ya san me ya fahimta tun jiya a tare da Dan nasa. Amma tunda bai furta ba bari ya bi shi da yadda ya zo masa.
“Mummy, na yi magana da ita ta ce kai ne ka kore ta�.
Aboulkhair ya katse shirun nasu ganin Daddy bai da niyyar tankawa.
“Ni ban kore ta ba, zabi na bata�.
Ya fada ba tare da ya dauke kai daga aikin da yake yi cikin na’ura mai kwakwalwa ba. Abulkhair ya yi dan jim! Kafin ya ce,
“Is that related to Aal… I mean Aalimah?�. Ya fada kansa a kasa, muryarsa na sarkewa da ya zo furta sunan. Tun jiya in zai furta sunan sai harshensa ya sarke ya rasa dalili.
Murmushi Daddy ya yi, ya kashe system din gabadaya ya juya kujerarsa mai tayoyi baya ya fuskance shi da murmushi bisa lebbansa, “Pronounce the name properly (furta sunan yadda yake daidai)�.
Kunya ta rufe Abulkhair, ya kasa dago ido ya kalli Babansa.
Ji yake yana dagowa Daddy zai karance abin da ke cikin idanunsa tsaf! Tunda ga shi yana kokarin karanto rudanin da ke tattare da muryarsa akan furta sunanta. Shi kuma ba zai so hakan ba, saboda shi kansa bai yarda da kansa ba. Bai yarda da feelings dinsa are morethan emotion ba. Bai yarda zuciyarsa ta kamu da son Aalimah ba, don a ganinsa babu dalilin hakan.
Abin da ya yarda da shi shine there are certain characteristics about her da za su rikita kowanne Da namiji mai cikakken hankali ba shi kadai ba. Her well-structured body, her pointed nose… these thick eye-lashes… this red soft lips are all breadth taking! (Wannan ginannen jikin nata, wannan tsayayyen hancin nata, wadannan jajayen tausasan lebban, wannan cikakken gashin idon da gashin girar, duka masudauke numfashin mutum ne!) Kowanne namiji zai yi mafarkin samunta matsayin matar aurensa!!!
Shirun Abulkhair ya yi yawa, sannan ya ki dago kansa. Daddy ya ba shi mintoci masu kyau don ya gama duk tunanin da zai yi, amma ganin ba shi da niyyar magana kuma ya kasa dubansa, sannan yana cinye masa lokaci, sai ya kira sunansa cikin nutsuar murya. For all he know, Abulkhair dinsa ba miskili ba ne, Allah ya sa kada Aalimah ta sauya shi. In hakan ta faru ya ya zai yi da miskilai biyu? A Aboulkhair yake samun duk abin da yake so daga aboki, he is cheerful as well as passionate. Dayan, da shi da babu, duk daya. Ba rashin lafiya kadai ke aiki a jikinsa ba, har da hali. Tunda yana samun sound-medical treatment.
A wannan din yake jin dadi, yake samun duk abin da yake so daga aboki, ba zai so abin da zai yi spoiling farin cikin Aboulkhair ba, zai yi duk wani kokari ya samar da shi gare shi, ko da hakan na nufin… hadiye sauran tunanin ya yi, don yana ganin nan din ba filin yinsa ba ne ba.
Dago kansa ya yi ya dubi mahaifinsabut he is still lowering his gaze (har yanzu yana yin kasa da ganinsa) duk a kokarinsa na kada mahaifin nasa ya karanto idanunsa.
“Wouldn’t you speak out abin da ya kawo ka? Kana ganin ayyukan da ke gabana, sannan dube ka ko wanka ba ka yi ba, dubi kayan jikinka, dubi gashin kanka. Dubi idanunka, bana jin duk son ka da barci yau ka yi shi yadda ya kamata, ka koma gida za mu yi maganar Mummyn in na dawo, amma nan office ne�.
Yana so ya gaya masa ba maganar Mummy ce kadai ta kawo shi ba, in da sabo ai sun saba da cases din Mummy da yin yajinta zuwa wajen Danta. Gara ya yi ta zama a gaban Daddyn har ya gama aikin su koma gidan tare, a kan ya koma ya zauna shi kadai a gidan. Bai san me zai faru da shi ba, he’s afraid of going back to Boston University.
Tunda can din ma in ya je bai san me zai aikata ba. Gara nan din sau dubu a kan ya koma gida.
“Zan jira ka Daddy har ka gama, sai mu koma tare�.
Ya samu kansa da furta kalaman daki-daki ko Daddyn ya fi fahimtarsa. Amma Daddyn ya nuna shi bai fahimci komai ba.
“Ni kuma bazan iya ci gaba da aiki na kazo ka sani a gaba ba sai ka ce wani uwata. In dai uwarka ce na ce ban kore ta ba zabi na bata. In za ta iya sona da duk wanda ya shafe ni ta zauna, in ba za ta iya ba she could go to someone who has no relatives, but Ishaq Raazee is a family Man. Wannan shi ne kawai sakona gare ta. Abin da ta zaba determines ci gaba da zamanta gaban ‘ya’yanta or not�.
Sosai ya fahimci Daddyn, amma har yanzu bai yi magana a kan gabar da yake son ji ba. Kuma da alama ba shi da niyya. Ya ci gaba da zama, ya ci gaba da yin shirun.
Daddy dai kallonsa yake yana cewa a ransa, ‘I wouldn’t, untill you did (ba zan yi ba har sai ka yi)’.
Mikewa ya yi ya dauki mukullin motar da ya aje a kan tebirin Daddy ya nufi kofa. Sai da ya kai bakin kofa ya kama handle din kofar sannan Daddy ya kira sunansa. Bai amsa ba, kuma bai juyo ba, amma ya dakata.
“Drive with care (ka yi tuki da kula)�. Abin da ya ce da shi kawai kenan. Ya karasa ficewa daga office din.
Maimakon ya dauki hanyar gida, sai ya samu hannunsa da ke kan sitiyari da juya kan motar ya dauki hanyar Boston University. Jin kansa yake kamar wanda ake directing ya kasacontrolling kansa. A hankali yake tukin motar har ya tsaya a inda aka tanada don adana motoci (parking lot) da ke dab da ‘school of medical sciences’ na jami’ar. Kwantar da kansa ya yi a kan sityari yana tunanin me ya kawo shi? Don me zai zo? Sai ya ji kamar ana yi masa amsa-kuwwa cikin kwanyar kansa da cewa, kada ya koma, atleast ya samu ya ganta.
Bai zo don ya hana ta karatu ba sai don kawai ya ganta. Ganin nata shi ne kadai zai samar masa da nutsuwa ya koma cikin hayyacinsa.
Luckly for him, sai ya hango ta ita da wani saurayi bature zaune kasan wata farar lema da fararen kujeru da tebiri a tsakiyarsu. Daga gani karatu suke yi, amma shi sai idanunsa suka zarce suka soma ba shi delusion na abin da ba haka yake ba. Wani irin bacin rai da bai taba ji a rayuwarsa ba.
Yana can zuciyarsa na neman raba shi da numfashinsa saboda ita, tana nan happily accompanied with someone. Wanin ma wani banzan arne mai kama da skeleton. Tana nufin ta ce; duk wannan azabar shi kadai yake kwankwadarta ko me? Wata zuciyar ta ce, ya ja motar ya yi tafiyarsa ya bar garin ya bi Mamansa, ya ga sanyin idaniyarsa (Mu’azzam) ya manta da Aalimah tunda dama bai bari Daddy ya gane ba. Amma bangare mafi rinjaye ya ce ya dan faffallawa yaron mari ko hudu ne ya huce. Da sauri kuma ya tuna me yin hakan ke nufi a kasar bature. A kan Aalimahr ya kamata ya huce haushinsa, tunda ita har dukan nata zai iya yi ya zauna lafiya.
Aalimah da Alex, sun dukufa karatu, yana koya mata calculus. A wurinta sau dubu gara Alex ya koya mata a kan Monsieur din su Basma. She can’t even look into his eyes balle ya koyar da karatu. Akwai wani abu mai kama da sihiri cikin kwayar idon sa dake fizgarta wanda tun shigowarsa gidansu ya hana zuciya da kwakwalwarta zama lafiya. Sannan shi kansa tunda ya zo bai zauna lafiya ba, daga fada sai masifa wanda hakan ya sanya mata matsanancin tsoronsa bayan unexpressable emotions and feelings din da ta kwana da su a kansa.
A karshe kuma ta yi wa kanta fada, ta gaya wa zuciyarta wannan al’amarin da a yanzu ta gama fahimtar ‘soyayyah’ ne irin wanda ke kasancewa tsakanin mace da namijin da suka kai munzalin balaga comes at a very wrong time for her! ( ya zo a lokacin da bai dace ba). Sannan it could destory her parents dream on her… it can also destroy her future ( zai lalata mafarkin iyayenta akanta, sannan ya rusa future dinta) idan ba ta sanya taka-tsan-tsan ba da jajircewa a cikinsa. Ta sha jin yadda maza suke yaudarar ‘yammata su hana su karatu, su yi musu cikin shege, iyayensu kuma su tsine musu su shiga karuwanci ko su haife shege. Zuciyarta ba ta taba kawo mata tunanin aure nan kusa ba.
Da wannan dalilin dama wasu da dama ya sanya tun safe ta ke yaki da zuciyarta a kan Aboulkhair duk da cewa dan uwanta ne, ta san ba zai cutar da ita ba. Amma ba a shaidar maza a wannan fannin, Mahmoud kadai zata iya shaida a cikin maza. Sannan shi da kansa (Aboulkhair ) ya tilastawa zuciyarta ta ji tsoronsa daga yadda yake behaving ga kannensa tun jiya. Sosai ta himmatu wajen yakice shi daga zuciyarta ta ke ta karatu tun safe. Sun yi lacca biyu suna da hutun awa daya kafin su koma wata, shi ne ta roki Alex ya yi highlighting dinta abin da ya shige mata duhu.
6/28/21, 7:32 AM - Buhainat: 07030137870
45
#####################################################
Mummy ta manta ba ita za ta kai Daddy aljannah ba, wannan buzuwar dai da ta raina wadda ba ta je makarantar boko ba, ko Abuja ba ta taba takawa ba, bayan danta ya share sama da shekaru ashirin da bakwai a kasar Amurka. Daidai da rana daya kuma hakan bai taba damunta ba, ba ta taba daga ido ta dubi wani abu da Ishaq ya mallaka ba. Wadanda ba su yi karatun bokon ba, Eedrissa da Oussama sun share mata hawaye, sun gama mata komai. Dole Kasisi ta ce me ake da boko?
Ita dai kam bai amfana ta da komai ba daga nata ‘ya’yan. Daya ya tsallake ‘boarder’ ya je ya kafa iyali a inda ba shi da kowa, saboda ya auri ‘yar Nigeria, sai shekara-shekara ta ke ganinsa. A hakan ma nashi da kyau shi, tunda mace ba ta hana shi kyautata ma iyayensa ba. Sannan yana matukar kokari wajen lika ‘ya’yansa jikin iyayensa da ‘yan uwansu. Dayan kuma tun da ya tsallake kasar da sunan aiki ya fidda kansa daga sahun ‘ya’yan da ta haifa, ya koma dan Zulaiha mijin Zulaiha. Kowa banza ne tunda bai yi rayuwa a America ba, har wadanda suka samar da kwan haihuwarsa a duniya.
Kuka Aboulkhair ya soma yi a hankali yana fidda shessheka, kukan tausayin mahaifinsa da yin Allah wadai da wannan hali da mahaifiyarsa ta rika a matsayin dabi’a. Wutar Allah yake hango masa karara. Yana kyautata zaton ko a waya Daddy ba ya kiran Inna Kasisi ya gaishe ta yadda ya kamata, kullum he is busy bautar iyalinsa da nemo musu kudi. Sau da yawa yana ganin mahaifinsa (Malam Raazee) yakira shi in ya ji shirunsa ya yi yawa, in suka gaisa sai ya ce,
“Na yi mafarkinka ne kai da takwara da Aboulkhairi, to nesa ba ta maganin kusa balle in ganku. Ina fatan dai lafiya ku ke?�
Wadannan sune kalaman Kakansu duk sanda ya kira wayar Daddy, har ya haddace su. Sai ya kira shi sau goma bai kira shi sau uku ba. In ya ba su wayar kullum nasiha yake musu kan su ji tsoron Allah a duk inda suka samu kansu, su tsaida sallah, su bi iyayensu, su rike ZUMUNCI, in sun yi hakan za su shiga aljannah. Shi ma ya san halin ko’inkulan na Daddy ga iyaye da danginsa ya shafe shi, Mu’az ne kawai mai kula da lamarinsu duk da halin rashin lafiyar da yake ciki he’s doing well with Daddy’s parents and family. Rabin albashin Mu’az ya san inda yake kai su duk da Mu’az din bai so ya sani ba.
Kwantar da kai ya yi a kan cinyar Daddy ya yi ta kuka, gwiwoyinsa suna durkushe a kan carpet kansa a kan kafafun Daddy. Gani yake yanzu in ya zo neman auren Aalimah babu mai ba shi, tunda daga shi har Daddy halinsu daya. Shi ma Daddyn could not help yin kuka, kukan yake amma na hawaye ba mai sauti ba. Ya sanya hannunsa cikin sumar Abulkhair yana shafawa a hankali, yana mai tuno dukkan kura-kuransa yana yarda da su, tare da yin nadamarsu daya bayan daya.
Ko da halin Zulaiha a kan tabarbarewar zumuncinsa da kowa nasa da kokarin fin karfinsa da ta ke yi, most at times shi ma da sakacinsa. Ya yi mata riko irin na mijin bature da macen baturiya; wadanda ba su san kowa ba a rayuwa sai kansu da ‘ya’yansu.
“It’s ok Aboulkhair, stop crying like that, Allah zai gyara mana komai. Sannan yanzu na sa damba a rikon Aalimah sai inda karfina ya kare. Wannan sakona ne ga mahaifiyar ku ku gaya mata. Zan ci gaba da dakon igiyoyin aurenta saboda ta bani the most expensive gift of life. Wannan kuma ba komai ba ne sai ku din nan ku biyar. Duk abin da nake nema a ‘ya’ya na same shi daga gare ku. Kun zame min abokai a lokacin da ta raba ni da su. Kun zame min DANGI a lokacin da ta raba ni da su. You brought all the happiness that children brings to the parents. (Kun bani duk wani farin ciki da ‘ya’ya ke baiwa iyaye).
Amma yanzu ina ji a jikina akwai wani babban gibi da na rasa, duk wannan rayuwar farin cikin da nake tsammanin ina ciki, my life is incomplete. Ina jin wani wawakeken rami a wani gefen na zuciyata Abulkhairi. Bayan kowacce soyayyah dan Adam yana bukatarta fiye da soyayyar kowa. Wannan ba wata soyayya ba ce face ta UWA! I missed MOTHER’S LOVE which is like no other. I’m lucky she is alive (nayi kewar soyayyar Uwa, wadda babu kamarta, nayi sa’a tana raye) yau da ban san inda zan sanya kaina ba�.
Aboulkhair ya share hawayensa, sannan ya kara dukar da kansa cikin cinyoyin Daddy, as if kansa zai kutsa cikin rigarsa ya shige cikinsa, shi kuma ya sake haifo shi.
“Daddy, ku ba ni auren Aalimah, I mean Aal… Daddy zai dinke komai. Zai faranta ran Inna Kasisi. Above all, I LOVE HER SO MUCH DADDY, I mean it, from the bottom of my heart…!�.
Dariya Daddy ya kama yi, kafin ya ce,
“I know�.
Da sauri ya dago ido yana yi wa Daddyn kallon mamaki, ya san dazu a office bai furta masa ba, sabida kunya yake ji, kuma ya san Daddy sai ya yi masa dariya, saboda ya sha cewa sai Mu’az ya haifi ‘ya’ya biyu zai yi aure. Sai ya zama cikakken medical doctor. He is now in year 4. Akwai kwararan shekaru biyu a gabansa kafin ya gama MBBS, sannan ya zo ya yi Specializing. Wannan na nufin; sai ya kwashe shekaru kusan hudu zuwa biyar kwarara nan gaba kafin ya mallaki Aalimah???
Ina ruwansa da auren Mu’az?Mutumin da aure baya cikin vocabulary dinsa. He can’t even develop emotion!Duk da lalurar da Allah ya jarrabce shi da ita, ya gwammace ya yi ta daureb kansa da kwayoyi, shi zai zauna ya yi ta jira ya yi aure ya haihu? Tunanin da yake ta yi kenan idonsa a kan mahaifinsa, wanda ke ta binsa da murmushin kauna kamar ya hadiye shi, saboda farin cikin da kalamansa suka jefa shi. Sun wanke duk wasu damuwoyi da suka lullube shi a ranar.
Wannan ne babban abin da zai yi ya gyara komai din, har Khaleesat da Basma ya yi musu nasu tanadin wanda ya san hakan ne kadai zai wanke dattinsa daga idanun ‘yan uwa da iyayensa, wanda ya yi shekaru ashirin da bakwai yana barbada musu a idanunsu.
“Kana mamakin ya aka yi na sani? Na sani tun daga lokacin da ka tasa ta a gaba sai ta cinye sakwara, bayan kai ne ka sa ta kasa ci�.
Zuru ya yi yana kallon Daddy, wato iyaye sun fi kowa karantar ‘ya’yansu.
“Amma Aboulkhairi…� Daddy ya ci gaba da magana, sannan ya dakata. Tattaro dukkan attention dinsa ya yi ya mika wa Daddyn, burinsa ya ce gobe zai nema masa auren AALIMAH.
Daddy ya ci gaba da magana, “Cire gaggawa daga cikin lamarin nan, domin ita gaggawa daga shaidan ta ke. A yanzu haka in na nema maka auren Aalimah da kyar za su ba ni. Musamman Yaya Oussama wanda shi ke ba da aure a family dinmu. I have wronged them so much. I’ve to cover my mistakes first, make-up my short comings, eradicate the inconveniences.(Na bata musu da yawa, dole in fara wanke kurakurai na tukunna, in wanke laifi na). Idan na je musu da nadama ta da kuma nema maka auren Aalimah concurrently (a lokaci guda) cewa za su yi abin da ya kawo ni kenan.
Don haka mu bi abin a hankali, mu fara gyara girgidadden zumuncin. Ina ji a jikina komai zai zama daidai ba da jimawa ba. But I want you to exercise patience, concentrate on your studies, make me proud with flying colours kamar dan uwanka. Shi ne babban abin da zai ba ni karfin gwiwar nema maka auren Aalimah. Amma yanzu ba ni da guts na yin hakan tunda baka da halin rike iyali�.
Da sauri Aboulkhair ya dubi Babansa, damuwa kwance baro-baro a kan kyakkyawar fuskarsa, “Daddy, allowee dina ya ishe mu, ko aikin karfi zan hada da shi in ciyar da ita. Daddy don Allah…!�
6/28/21, 7:32 AM - Buhainat: 07030137870
103
####################
Wani matsanancin tausayi irin na iyaye ga ‘ya’yansu ya kama Ishaq Razee. Ya san Aboulkhair fiye da kowa cikin ‘ya’yansa. Ya amince yana nufin kalamansa. Karatun likita kuma ba wasa ba, kada hidimar iyali ta dauke masa hankali, ya hana shi kuma rashin nutsuwa da soy ayyah su hana shi karatun. Gara ya kasa karatun a kan ya zama Mu’azzam, shi ga karatun, ga kwalayen masu karshen kima da daraja, ga kuma career mai matukar daraja, amma ba ya zancen auren. Nan da shekaru goma a gaba ma ba shi da niyya, shi kuma ba zai taba takura masa ya yi ba, uzurinsa ya kai uzuri, kwanciyar hankalinsa a hakan da yake rayuwa ya fi musu komai.
Idanunsa suka cicciko da kwalla, gab yake da ya zubar da hawaye sabida tausayin dan sa Mu’azzam.
Ga wannan mai lafiyar shi ma yana kokarin zame masa wani abin tausayin. Hannu biyu ya sa ya dago shi daga durkuson da ya yi a gabansa kamar mai neman gafara, nan kuwa Aalimah yake nema.
Zaunar da shi ya yi a barin jikinsa ya rike hannayensa, “Aboulkhairi, ni ta bangarena ba ni da matsala da zarar na dinke barakar da ke tsakanina da ‘yan uwana zan iya yi maka aure daga yanzu zuwa kowanne lokaci, in ciyar da kai, in ciyar da matarka, in suturta ku, in ba ku muhalli ku haifa min jikoki su ma in ciyar da su. In dauki nauyin kula da lafiyarku da karatunku har zuwa sanda za ku iya rike kanku. Matsalar daga iyayen Aalimah ne.
Sun dauki duk wani buri da suke da shi a kan babban dan su Aboubacar sun dora a kanta, they wanted her to be very well educated, kamar kakanta na wajen uwa Prof. Kashim.Mutuwarsa ta taba mahaifiyarta tun daga zuciya har kwakwalwa, she dropped her career and became a mental patient too, ta tsaya da burin danta Aboubacar ya zame mata magaji ga mahaifinta. Su biyu rak! Ya haifa,dan uwan nata Suraj yayi mata nisa.
Aboubacar ya ki yarda ya karanta pharmaceutical science, ainahin kwas din marigayi Prof. Kashim, sai mijinta ya shwarce ta da ta ba wa Aalimah damar da ta ke son bai wa Aboubacar. Yana so kada ta zama discouraged don ta haifi ‘ya’ya mata da yawa fiye da maza, yana so ta yarda mata ma ‘ya’ya ne kuma ta yi farin ciki da haihuwarsu.
Alhamdu lillah Aalimah ta fara kokari sosai a karatunta. Ka ga ya kamata yanzu in ce su cire ta daga makaranta su aura wa Dana? Shi kadai ya san yadda ya yi fafutukar da ya yi ya samo mata scholarship din nan babu ko sisina, ko kudin jirgi uwarta ta biya mata ba su karbi nawa ba. Hakan ya kamata Aboulkhair?�
Da matukar sanyin jikin Aboulkhair ya girgiza kai, da zai iya, da zai so ya ce da Daddy “aurena ba zai hana burin iyayenta cika a kanta ba, zai zamo ne a step toward her achievements… zan zamo tsanin cikar burinta… zan taimaka mata ta duk hanyar da zan iya……�. Maganar zuci yake bai san a fili yake yi ba. Saboda ya zama very infatuatedakanAalimah, ya kasa controlling emotions dinsa da damuwar zuciyarsa.
“Be strong my son, ina tabbatar maka za ka iya JIRA, musamman idan ba ka ganinta. I’m not against early marriage(bana kin auren wuri)sabida ni ma sanda mahaifina ya yi min na ji dadi, na tabbata ni dan gata ne, kuma iyaye irinshi kadan ne. Da kuma za’a samu yawaitar irinsa a duniya, da zina ta ragu a cikin al’ummah.
Mahaifiyarku ajinta biyar a sakandire na aure ta, yau ga ta da degree har da masters . So ni ta fannina na yarda aure da hidimar iyali ba sa hana goal attainment. Daga iyayenta ne, and their convenience. Ni ko gobe Mansour ya ba ka Aalimah zan biya sadaki. Amma na rokeka ka daga min kafa in gyara nawa ruguzajjen ginin tukunna. Kada ka dagula min al’amura. In kuma za ka yi min abin da na fi so shi neWAIT FOR HER!(Ka jira ta). Jikina yana ba ni matarka ce, kuma uwar ‘ya’yanka�.
Wani numfashi Aboulkhair ya zuka ya kuma dawo da shi da sauri. Dariya ta kama Daddy, amma ya gintse. Yana mamakin wane irin so ne haka ya kama Aboulkhairinsa cikin kwana daya rak? Tarihi ne ke maimaita kansa. Ya sani duk ‘ya’yansa maza shi suke gadowa a halayya dabi’a. Shi ma haka ce ta faru da shi a kan mahaifiyarsu the very first time he saw her, bai kuma nutsu ba sai da ya aure ta. Baya fatan hakan ta faru da Aboulkhair, tunda ba shi da ikon ba shi Aalimah a yanzu, rashin nutsuwarsa kuma daidai yake da tabarbarewar karatunsa, wanda ba ya fata…
“Would you keep encouraging me to wait? (zaka cigaba da karfafa min gwiwa wajen jiran?�) Ya tambayi baban kamar zai yi kuka. Abin nasa har da shagwaba-shagwaba.
Gyada kai Daddy ya yi yana masa murmushin bada karfin gwiwa da son karfafa gwiwa.
“Yes, I will keep encouraging�.
“Would it take long?�
Aboulkhair ya kara tambaya.
“No, five years is like a blink of an eye (kamar kiftawar ido shekaru hudun suke). Especially when a person makes himself busy with studies. Make frequent phone calls when he is far, but he should make sure the phone calls doesn’t distract or affect his study times, once in a day or twice in a week. And it shouldn’t contain deep emotional talks that would inturn arouse his fantasies. It ought to stick on “how are you� and “how is studies?�
Dariya Aboulkhair ya shiga kyalkyalawa kamar babu gobe. Shi kansa Daddyn dariya yake yi, zukatansu suka yi dadi tamkar babu sauran damuwa a cikinsu.
Yana komawa dakinsa ya rufe kofa ya dauki wayarsa da niyyar ya kira Yayansa, amma sai ya duba lokaci, lokacin shan magungunan Mu’az ne yanzu, yana sha kuma zai yi bacci. Kamar ya kyale shi, amma sai ya ga ba zai iya ba, ya kamata yasan komai da ke faruwa tsakanin Mummy da Daddy daga bangaren kowannensu don yayi sulhu. Ya manta da situation din Mu’az da tunanin zai shiga lokacin barcin sa ya danna masa kira. Sai da ta kusa katsewa kafin ya daga.
“I’ve been expecting your call since yesterday, where have you been?� (nayi ta tsammanin kiranka tun jiya, ina ka shiga?�
A cikin muryar akwai maturity, akwai nutsuwa da haiba, akwai gentleness, akwai kwarjini da kamala, akwai wani abu wai shi ‘class’ da sanin ciwon kai. Sannan it is so caring as well as affectionate ga wanda ake magana da shi. Shi ma wanda ya yi kiran respect ne da affection zallah a tashi muryar. Ya tattaro dukkan nutsuwarsa ya daidaita tone din muryarsa yadda ba zai zama boring ga mai saurare ba, sannan ya zauna a gefen gadonsa ya yi wa wayar rikon aminci, yadda ba za ta zame ba.
“Is Mummy beside you? Mummy na kusa da kai?�
“No, ta shiga barci tun dazu. Ni ma I’m about to take medicines(gab nake da shan maganina) in kwanta, wani aiki ne ya dan tsare ni da ba za ka same ni ido biyu ba�.
“Kayi hakuri da rashin kiranka tunda na iso, bana cikin nutsuwa, I metatedious threshold inthe house…� Ya warware masa komai; tun daga farko har karshe da nasa observation din na halin Momy tun suna kanana. Da irin kukan da suka yi dazu shi da mahaifinsu. Amma bai gaya masa he is in love da Aalimah ba, komai da lokacinsa.
Shiru Mu’azzam din ya yi, kamar ruwa ya cinye shi. He didn’t cry. Ba abu kankani ke sa Mu’azzam kuka ba, sannan ba ya jan magana da nisa, his words are specified, he is very selective and picky before he utter a word. Amma duk sanda ya furta magana zata kasance ta kunshi ma’anoni masu yawa a dunkule. Aboulkhair ya yi zaton sam ba zai yi magana ba har sai shi din ya gaji ya ajiye wayar, bai damu ba, sabida ya san dan uwansa fiyeda kowa a duniya. Ya san bynowzuwa yanzu ya gama tunanin yadda zai shawo kan matsalar iyayen nasu gaba daya cikin dan wannan lokacin da ya dauka shiru.
Daga baya Mu’azzam din ya kira shi.
“This is totally opposite with what she told me…�. (Abinda ka fadamin kwatakwata bai yi dai-dai da wanda ta fada min ba). Mu’azzam ya fada cike da tausayin mahaifinsa.
Suka yi maganganu na maza masu hankali na dan gajeran lokaci, kafin Mu’azzam ya ce,
“Is the girl still in the house? (Har yanzu yarinyar na gidan?)�
“Yes, she is, the nicest sister I ever met (eh tana nan, ‘yar uwa mafi dadin mu’amala dana taba haduwa da ita a rayuwa�.
“Greet her for me�.
(Ka gaishe min da ita)
“Za ta ji insha Allah�.
“As for Mummy (Game da Mummy, ofishin su sun kirata jiya, kyale ta kada ka kirata don ka rarrasheta, da kanta zaka ga ta dawo. Ka yi kokari ka gina kyakkyawar mu’amala a tsakaninta da yarinyar kafin ka koma makaranta. Ka nunawa yarinyar yadda zata yi hakuri da ita.Sukuma ka rabu da su za su shirya kansu a junansu�. (Yana nufin ita da Daddy)
Da haka suka yi sallama.
******
ABOULKHAIR DA WAYAR AALIMAH!
Sai da ya gama komai da ya saba yi kafin ya kwanta, kama daga wanka, brush, shan black tea, ya daura pajamas sannan ya shige cikin quiltdinsa da wayar Aalimah a hannunsa. ‘Yar kankanuwar waya Daddy ya saya mata kirar Iphone. Contact list shi ne abin da ya fara shiga, contacts din ba su da yawa, ba su fi ashirin ba. Ya ci gaba da scrolling contactsdin, akwai mamere, watau Mamanta kenan, mon pere (Babanta), sai Bhaiyya, wato Yayanta Aboubacar da harshen India. Sai ta Daddy, ta Basma, ta Khaleesat, Malam Raazii, Kawu Oussama, Kawu Edrissa, Balkissa Eedrissa, Grandma Kasisi, Grandma Bintou. Sai lambobin maza guda biyar wadanda ya ga ba zai jurewa zamansu ba.
Alex ya fara gogewa, ya goge Harrison, ya goge Mr. Edward Proffessor. Bai san cewa course tutor dinsu ne ba ma. Harrison kuma course mate dinta ne. Lambar da ta rage guda daya ce ta tsaya masa a makoshi, kuma ya kasa goge ta. Akwai bukatar ya dauke ta a tasa wayar, sannan ya goge. ‘MAHMOUD’. Ba don komai ba sai don ya kawo karshen alakarsu ko ma wane ne. Har wani heart ta makala masa bayan ta rubuta sunansa. Bai yi mamaki ba, don yarinya kamar Aalimah ba yadda za a yi a ce ba ta da mashinshini har zuwa wannan lokacin. But he’s jealous, in ya ce jealous to guda daya kenan. He is very-very jealous! Don ya lura ko ma wane ne wannan Mahmoud din ba yau ya fara son Aalimah ba, kuma bai fara don watarana ya daina ba.
Zuciyarsa ba ta gama tsinkewa ba sai da ya shiga message inbox. Sakonnin Mahmoud din ne rututu masu barazanar tarwatsa kwanyarsa. Bai iya ci gaba da karantawa ba ya hada su duka ya goge su daga doron kasa. Abu daya ya dan kwantar da hankalinsa, ba reply mai zafi daga Aalimah, ga dukkan alamu ba ta damu da yin rubutu cikin waya ba, babu wani social media da ta bude, she only text Mahmoud twice, saying that she saw his messages, she’s doing morethan fine. She will call him when she is opportune, he know how tedious her studies is. (Sau biyu ta yi ma Mahmoud sako, inda tace ta ga sakonsa, tana nan lafiya, zata kira shi in ta samu dama, ya san yadda karatunta yake da tsauri). Wannan ne kadai ya dan sanyaya ransa. Amma ya rantse gobe sai ya raba Aalimah da Mahmoud yadda zuciyarsa za ta buga ya mutu ya huta.
Ya dauki lambar Daddynta, mamanta da ta Yaya Aboubacar. Lambobinsa ya zuba cikin wayar tata, ya yi saving da Mon Amour (MY LOVE da harshen faransa), sannan ya yi mata downloading din whatsapp application. Da niyyar cewa shi kadai zai dinga mata magana ta cikinsa, not even Daddy karshenta kenan. Sannan ya koma cikin gallery na wayar, duka yawanci selfie ne ita da Basma a makaranta, wani a mota, he can guess that she adores Basma a lot (tasu ta fi zuwa daya).
Murmushi ya yi da ya tuna Khaleesat ko Daddy bai cika shiri da ita ba sabida I don’t care attitude dinta. Tafi shiri da Mummy. Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskar da ta zame masa madubin zuciya daga jiya zuwa yau. Ta rusa duk wasu plans da ya yi wa rayuwarsa, ta kuma zamo babban kalubalensa na rayuwa a yanzu. Mallakarta is the greatest challenge of his life now. Ban da barci ya fi kowa iya sata da Aboulkhair yau ma bai runtsa ba kamar yadda ya ga dare da rana jiya.
Amma yau ya yi barci yadda ya kamata da wata irin nutsuwa da ya dade bai samu ba a rayuwarsa.
Washegari, Aboulkhair ya yi wanka ya shirya cikin shirt da wando ‘yan gidan Nordstrom, rigar orange ce da ratsin baki, wandon fari tas. Sumar nan ta sha taza ta kwanta luf a kansa. Samun kansa ya yi da zakulo turaren da ya fi kowanne kamshi mai sanyi cikin tarin turarukansa masu ban sha’awa, sannan ya fesa. Ya fi son shi fiye da dukkan turarukansa, saboda Mu’az ke ba shi (SAUVAGE Dior). Duk wani abu kuma da ya fito hannun Mu’azzam is preciousa gun Aboulkhair. Ya san dai ba yau ya fara fesa turare ba, amma shi kansa ya san wanda ya fesa yau bai fesa shi don radin kansa ba.Is meant for AALIMAH ta ji yana kamshi.
Wani murmushi yake saki shi kadai yana yi wa kansa dariya. Sanda ya fito su ma duk sun yi shirin makaranta suna dining suna karyawa har Daddy, sai Aalimah da ke ta shige da fice daga kitchen zuwa dinning area din tana miqo musu abubuwan da suke bukata.
Sosai ya ji haushi, amma bai ce komai ba har ya zauna. Shi ma ita ta yi serving dinshi ba tare da ta yarda sun hada ido ba.
Ya dubi Basma, “Ina mai aikin Mummy?�
“Aal, ta hana ta zuwa by 6am ta ce ita za ta dinga yin breakfast, Easther ta yi lunch and dinner�.
Ya dubi Daddy ko zai ce wani abu? Ya ga bai ce komai ba, sai shi ma ya yi shiru. After all ita mace ce kuma rainon Nigeria, she might be willing to do so. Shi kansa ya fi son cin nata abincin a kan na Easther, tunda ya ci pounded yam sau daya. Amma anya hakan ba zai zamo takura a gare ta ba?
Muryar Daddy ya ji yana yi wa su Basma fada kan su dinga shiga kitchen din da safe tare da ita za su fi sauri, kuma su ma su koya. Ajiyar zuciya ya yi cikin jin dadi.
Fara cin abincin ya yi, su kuma suka koma sama don dauko jakunkunansu da mayafansu. Khaleesat da Yesmin da ma uniform ne a jikinsu. Daddy ya riga su ficewa, su ma mota suka wuce don su jira shi, bai dade ba ya gama ya fito. Kofar direba ya shiga ya rufe, sannan ya mika hannu ya bude kujerar gefensa. Basma za ta shiga, ya ce, “No, koma baya, daga yau seat dinta ne�.
Ta ce, “Who?�
Harara ya galla mata ba shiri ta shige bayan don ta lura daga zuwansa zuwa yau he’s a changed person. Aalimah ba da son ranta ba ta zauna a gaban, ba ta so ko kadan su Basma su fahimci tsakaninta da Yayansu akwai wani abu, kunya ta ke ji sosai balle ta san Basma da digimi da maida allura garma. Sai da suka hau titi sosai ya dan juyo ya dube ta. Ta yi masa kyau sosai cikin doguwar riga ruwan kasa da veil dinta sakar kasar Kuwait. Takardun hannunta ta ke dubawa tana da gwaji yau (test). A duk lokacin da ya dube ta his feelings for her heightened bai san dalili ba. Cikin tattausar murya ya ce, “Babu gaisuwa Aalimah?�
Ko su Basma da ke baya ba su ji abin da ya ce ba, sabida raunin muryarsa. Ba tare da ta dago ba ta ce,
“Bonjour?�
Ya amsa, sannan ya ce, “What time is your interval (lokaci na hutu tsakanin wata lakcar da wata). Ta gaya masa.
Daidai lokacin da suka shigo Boston campus ya ajiye su ya juya. Ko da ya koma gida kasa hassala komai ya yi, sai tunanin Aalimah. Tashi zaune ya yi daga kan resting chair ta falon da yake kwance a kai, ya hau saman gidansu. Akwai wani balcony da galiban daddy ke zama da yamma ya yi karatun jarida a weekends can ya je ya zauna. Wayarsa ya lalubo ya nemo lambobin da ya yi saving jiya daga wayar Aalimah ya kira ‘UNCLE MONSOUR’. Gara ya fara yi wa kansa yakin neman auren Aalimah kafin Daddy ya gama yangarsa ya fara nasa.
Dr. Monsour Raazee, na zaune cikin ofishinsa da ke cikin sabuwar jami’ar Bayero yana marking takardun dalibai ya ga shigowar kiran mai dauke da lambobin kasar Amurka cikin wayarsa. Amma kuma ba Aalimah ba ce ba, kuma ba yayansa Ishaq ba, sannan it is not his darling son MU’AZZAM ISHAQ RAAZII, wanda sati ba ya shigowa ya shude ba tare da ya kira shi ya gaishe shi ba, musamman a ranakun karshen mako. To ko Aalimah ce ta canza layi? Haka ya mika hannu ya sanya ta a handsfree yana ci gaba da marking din da yake yi saboda tsabar kwarewa da aikinsa.
“Assalamu alaikum Uncle�. Ya jiyo muryar saurayin mai wani irin accent shi ba bature ba, shi ba balarabe ba, ba ma kuma za ka sanya accent dinsa a jerin na Hausawa ba duk da uwarsa cikakkiyar bakanuwa ce.
“Ameenwa’alaikumus-salam warahmatullah, da wa nake magana?�
Kunya da jin nauyi da nadama baki daya sukayi rubdugu a kan Aboulkhair, a girmansa ba zai iya tuna rana ta karshe da ya kira wani cikin dangin mahaifinsa ya gaishe shi ba, tun suna yara Mummy ke gaya musu they don’t love them, they are always saying ‘baku da tarbiyyah’ don kawai ba sa sona!’
Ya runtse idonsa yana jin wata irin nadama tana ratsa shi. A shekarun girmansa kuma he is very busy with schools musamman da ya fara karatun jami’a ya bar iyayensa ma bakidaya ya tare a jami’a, sannan ga yanayin karatunsa, he hardly find time for himself ma balle ya tuna mutanen da suka shafe shi. Ko askin kansa ba ya samun damar yi sai gashin na neman rufe masa ido. Ko kadan bai dauko Mummy ba, sai idanunta da duhun fatarta, he is a perfect photocopy of his father. Mu’azzam ne mai kama da ita, sai dai shi kuma ya yi hasken fatar Daddy, bai yo yawan sumar kai ba, sannan he shaves regularly (yana yawan yin aski).
Ya yi nisa a tunani, wanda ya mantar da shi cewa ya kira waya har kawun ya amsa. Muryar Kawun nasa ya ji yana tambaya cikin sanyin murya,
“Ko ABOULKHAIR ne?�
Ya cije labbansa cikin mamaki mai cakude da jin kunya da jin dadi duk a lokaci daya, ya ce,
“Ni ne Uncle�.
“I guessed�. Inji Dr. Mansour, “Ya ya ku ke, ya Babanka da ‘yan uwanka da mahaifiyarku?�
“Suna lafiya Uncle, I’m sorry for not calling you. Nayi nadama uncle.Uncle na ji kunyarka, amma ka yarda da niban taba mantawa da ku ba. Bana tare da iyaye na, ina karatu a Louisiana shekaru hudu kenan. Yanzu ma hutu na zo, kuma nanda sati hudu zan koma.I need your blessing!�.
Hausa yake iyakar iyawarsa tana subuce masa yana cakudo ta da turanci.
Dr. Monsour ya yi murmushi kamar yaron na kallonsa. Hamdala yake yi cikin zuciyarsa, addu’ar mahaifinsu da kalaman mahaifiyarsu ba su fadi a banza ba. Inna Kasisi ta sha cewa kowa ya daina damuwa da rayuwar Ishaq da ‘ya’yansa, idan ‘ya’yan na halal ne da kansu za su neme su. Malam kuwa ya sha cewa, “Da izinin Allah kan ‘ya’yansa da jikokinsa ba zai rabu ba ko bayan ransa. Ishaq da ‘ya’yansa da suka zama saniyar ware, yana rokon Allah ya karkato da hankalinsu gida, su rungumi ‘yan uwansu da iyayensu.
Kiran sunan yaron ya yi wanda ya fada cikin damuwa da shirun Kawun nasa.
Ya ce, “Aboulkhair, Aboulkhair! Kana jina?�
“Eh Uncle, I’m still online�.
Ya ce, “Ka daina damuwa, I’m your father, an halicci iyaye da dabi’ar zama masu karbar uzurin ‘ya’yansu. Na ji uzurinka, kuma in gaya maka ban taba damuwa da hakan ba, tunda na san lafiya ku ke. Amma ka dinga koyi da dan uwanka wajen kula da zumunci. Ya fi ka yawan hidimomi tunda shi babban ma’aikaci ne, still ya rike danginsa kam-kam. He is not with us, but we are feeling him beside us. (Baya tareda mu, amma jinsa muke kamar a gefen mu). Sallar bara da ta wuce tare da shi muka yi sallar idi a Nijar, ya je Zinder (garin su Inna Kasisi), ya je Tessaoua (garin su Malam Ibrahim Razee), har Arlit (garin su Inna Bintou) ba inda bai je ya ga dangi su ma sun ganshi ba. Ga albarkar kakanninsa da iyayensa yana sha ta ko’ina, ba ka yi wa kanka kwadayin hakan?�
Ya ci gaba da kawo masa ayoyi da hadisai da Allah ya yi umarni da zumunci, da kyautata shi, musamman ga maza kuma manyan jikoki a family. A karshe ya saka masa albarka, shi kuma ya yi alkawarin zai ci gaba da kiran kowa. Ya ce yana son kiran Maman Aalimah da yaya Aboubacar, amma bai sani ba ko sun manta shi?
Dr. Mansur ya ce, “You are welcome to call everybody within your family, babu wanda ya manta da ku ko don Mu’azzam. Allah ya yi muku albarka bakidaya�.
Bayan sun gama waya da Daddyn Aalimah ya dade a wurin, ya jingina da karfen balcony din zuciyarsa ta yi masa dadi. Sai kuma ya fada wani tunanin. Wato duk yadda yake da tabbacin ya fi kowa sanin Yayansa Mu’az har gobe bai zo rabi a sanin nasa ba! Abubuwan mamakinsa yawa gare su, kuma ba wanda ya isa ya san cikinsa hatta da iyayensu idan aka zo maganar abin alkhairin da yake yi a rayuwa. Sai dai ya tsinta nan da can kuma bai isa ya yi masa zancen ba, yanzu zai ce bai san maganar ba, ko ya ce ya kyale shi da unnecessary magana, ba ya son yin magana mai tsawo.
Ajiye tunanin Mu’azzam ya yi a gefe, don abubuwan mamakinsa ba masu karewa ba ne. He is just far beyond everyone’s assumption (ya wuce da sanin kowa). He is a patient, amma abubuwan da yake yi da yadda yake gudanar da rayuwarsa masu lafiya dari bisa dari ba za su iya ba.
Maman Aalimah Hajiya Aseeyaita ce mutum ta biyu da ya kira. Ita kam ba ta gane shi ba, sai da ya kara da bayanin kansa sannan ta gane. Sosai ta shiga janshi da hira, tana tambayar kannensa da mamanshi. Abin da ya ba shi mamaki, ba ta tambayi Aalimah ba, sai su Basma. Abin ya burge shi kwarai da gaske. Kawaici wani abu ne mai kyau cikin al’adun malam bahaushe, wanda Mamansa ba ta sanshi ba. A gaban kowa, kiri-kiri ta ke nuna son ‘ya’yanta da nuna babu ya su a duniya. Su ne kadai ‘ya’ya. Sannan ya kira Yaya Aboubacar.
Aboubacar sa’an Aboulkhair ne, bai fi watanni biyu Aboulkhair ya ba shi ba. Don haka hira sosai suka yi, irin ta ‘yan uwa. Ya ce ya gaida Aalimah duk da ba a fi kwana biyu ba sun yi magana shi da ita.
Yau dai Aboulkhair ya yi wa kamfanin wayarsa na VERIZON ciniki mai dumbin yawa, don bayan gama wayarshi da ‘yan gidan su Aalimah ‘yan Nijar ya hau kira, duk wasu manya a dangin ba wanda bai kira ya wanke kansa ba.
Inna Kasisi na yi masa tirjiya da hutsancinta, haka ya yi ta lallashinta har ta ware suka yi hira. Ya yi mata alkawarin he will keep calling kuma zai zo Nijar next hutunsa. Albarka kuma ya sha ta wajen malam da manyan Uncles dinsa. Ba su da riko ko kadan sai kaunar junansu. Ya kuma yi mamakin matsayin da Mu’azzam ke da shi a family dinsu. Ya raina kansa, don ba wanda zai yi magana da shi har ya kare bai tambayi Mu’az ba, bai fada mishi alherin da yake masa ba. A karshe da ya gama wayar Mu’azzam din ya kira. Yana dagawa cikin sauri ya ce da shi,
“At office, call later�.
Murmushi ya yi yana jin kaunar Yayan nasa na kara ratsa shi.
A fili ya ce,
“Ni ma ba wani abu zan ce maka ba. I just want to hear your voice, (kawai ina son jin muryar ka ne) kuma na ji�.
6/28/21, 7:32 AM - Buhainat: 185
Zuwa lokacin azahar ta yi, dakinsa ya koma ya yi sallah, ba ya bukatar abinci don haka ya je ya yi sabgoginsa a cikin gari zuwa lokacin da Aalimah ta gaya masa tana da sarari. Yana yin parking kuwa ya gansu suna fitowa, daga dakin laccar tana rungume da folder.
Tsura mata ido ya yi tana nufo motarshi. A zuciyarsa tambayar kansa yake yi, me ya fi so a Aalimah? A gaggauce amsar ta halarto zuciyarsa… Yana son komai nata… komai ta yi abin burgewa ne a idonsa. He loves her dearly.
Har ta shigo ta zauna a gefensa bai sani ba. Sai da ta hada yatsunta biyu suka yi kas! A kunnensa. Kallonta ya yi, sannan ya dauko wayarta daga inda ya ajiye ta ya lalubo lamba ya danna kira. Ba ta ankara ba ta ji muryar Mahmoud na amsawa da sallamarsa, yana tambayar ina ta shiga kwana biyu? Kafin ta kwace wayar ya bada amsa,
“Ba ita ba ce, mijinta ne, kuma Yayanta, wanda ya bada sadakinta ga iyayenta. This is for your information not to call or text my wife again�. Ya datse kiran.
Aalimah ta ji ba dadi har fuskarta ta nuna.Mahmoud yana da mutunci a idonta ko don Yaya Aboubacar. Ko rabuwa za ta yi da shi ba za ta so su yi irin wannan rabuwar ba.
Kallonta yake kai tsaye cikin idanunta don ganin reaction dinta, amma ya kasa fahimtar komai ban da rashin jin dadin da idanunta suka nuna. Magana ta yi a hankali cikin rarrashi don fahimtar cewa so yake su yi rigima.
“Haba Yayan Basma? Abokin Yaya Aboubacar ne kuma…..� Ta yi shiru ta kasa ci gaba.
“…... Kuma saurayin ki�, yayi maza ya karasa mata. “Kawai ki fashe da kuka na raba ki da saurayinki…�.
Turo baki ta yi cikin shagwaba, “…Ni ba saurayina ba ne, cewa zan yi muna mutunci ni da shi fa… Ni ba ni da saurayi…�.
Ganin yadda yake kallon bakin nata admiringly ya sanya ta maida bakin nata ta kintse, ta kuma sunkuyar da kanta. Murmushi ta shiga saki kasa-kasa a sanda ya sanyaya murya ya ce da ita,
“Har NI?�
Tafukanta ta kai ta rufe fuskarta tana murmushi,
“Kai ma Yayana ne�.
“Ko?� Ya tambaye ta.
Bai jira amsarta ba ya ci gaba, “Za mu bambance hakan ranar da aka daura mana aure�.
Ta kara tusa fuskar tata cikin tafukan nata, cikin matsananciyar jin kunya.
Wayarta ya jefa mata kan cinyarta ya tada motar, “Na bude miki Whatsapp, Daddy ya amince min in dinga magana da ke ta waya, daga yau har zuwa ranar da zai karbi sadakinki. Idan ki ka yi chatting da wannan mutumin Allah ya isa�.
Dariya ta soma yi tana fita daga motar. Ganin yadda yake maganar with confidence kamar ta furta masa tana sonshi ita ma. Tana son mutum mai courage, wanda ya iya yarda da kansa.
Ko da ta koma class ta bude littafin da ta ke rubutu, samun hannunta ta yi da rubuta haruffan guda tara, ‘A…B…U…L…K…H…A…I…R, ta zagaye su da zanen zuciya (heart). Kafin ta ankara cewa a cikin littafin daukar laccarta ta ke yi. Hannu ta kai ta dafe goshinta tana ambaton sunan Allah, me ke damuna ni Aalimah? Me ya shiga kaina? Me zuciyata ke nufi da ni a kan Yayan Basma? Ina zan kai Mahmoud wanda ke can wata duniya yana jirana? To amma me? The feelings are entirely not equal! Ko kusa da juna ba su zo ba, infact, abin da ta ke ji a kan Aboulkhair ba ta taba jin irinsa a kan kowa a duniya ba.
******
Shi ya dawo ya dauke su. A kofar gida bayan su Basma sun fito daga mota ya dakatar da ita. Tsare gida ya yi sosai, sannan ya jefo mata tambaya.
“Will you call him (Za ki kira shi)?�
Da lumsassun idanunta masu gazar-gazar eye-lashes ta dago ta dube shi. Ita ma ta jefa masa tambayar, “Who?�
Don ita shaf! Ta manta sun yi zancen Mahmoud dazu.
Runtse idanunsa ya yi ya kasa budewa, shi kadai ya san kishin Mahmoud da ke cinsa a zuci. Bai sani ba ko bayan lambarsa da ya goge daga cikin wayarta ko ta haddace lambar a cikin kanta. He don’t know how intimate they are. Daga yadda Mahmoud ke magana da kuma sakonninsa da ya karanta ya fahimci sun jima tare, kuma ta saba kiransa. Wannan tunanin ya tsaye masa a zuciya ya hana shi sukuni. Wani zazzafan so yake wa Aalimah, wanda shi kanshi yake ba shi tsoro.
Sai da fuskarsa ta yi jajawur sannan ya ce da ita,
“Saurayinki!�
Murmushi ta yi ta dauke idonta a kansa, sannan ta ce, “Ba zan iya sanin cewa zan kira shi ko ba zan kira shi ba, sai ka gaya min sunan budurwarka�.
Bata fuska ya yi ya yamutse ta abin dariya kamar wanda aka nunawa kashi.
“But, I don’t have, I have only friends�.
Murguda masa baki ta yi ta fice daga motar, sai kuma ta dawo ta zura kanta ta tagar murfin motar a hankali ta ce,
“Ni ma Mahmoud abokina ne!�.
Da gudu-gudu ta bi bayan su Basma ganin yadda yanayin fuskarsa ya canza bakidaya. Tana tsoron ya kife ta da mari, duk da ta san ba zai yi hakan ba.
Ficewa ya yi da motar ya fasa shiga gidan. Yana fitowa mota kirar Rolls Royce ta sanyo hancinta harabar gidan, wadda ke cike da korran shuke-shuken grass carpet. Tun daga nesa ya gane ko motar waye, “Mummy�. Fasa zuwa inda ya yi niyya ya yi, ya yi reverseya dawo da baya. A tare suka yi parking a harabar adana motocinsu, suka kuma fito a tare. Da sassarfa ya karasa gare ta ita ma ta taho suka hade, ta rungume shi. Sun dade ba su ga juna ba, kewar mai yawa ce. Duk da yana kallon mahaifiyarsa matsayin mai laifi ga rayuwar mahaifinsu, hakan ba ya nufin matsayinta ya canza a zuciyarsa ko wani abu makamancin hakan. A mother is always a mother!
Tana rike da hannunsa suka shiga gidan, su dai su Basma, Aalimah, Khaleesat da Yesmin sai ganin Mummynsu suka yi a tsakiyar falonsu. Wani ihun murna da kowaccensu ta saka ta yo kan Mummyn ta rungume ta, ba ka jin komai sai kalaman kewar juna da soyayyar junansu.
Aalimah ta koma gefe tana kallon soyayyar UWA da ‘ya’yanta, wata irin kewar iyayenta ta kama ta. Ta koma gefe ta rakube kamar marainiya.
Sam ba ta ga tahowar Abulkhair gare ta ba. Hannunta ya kamo ya soma janyo ta har gaban Mummy. Ta gintse farin cikin da ke kan fuskarta lokaci guda. Duk wata fara’a da ke kan fuskarta sai ta dauke. Girgiza mata kai Abulkhair ya shiga yi, sannan cikin nutsuwa ya soma magana.
“Mummy, Aalimah is saying welcome back to you�.
Aalimah ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na son zubowa. Kamar Anty Zulaiha ba za ta yi magana ba, sai kuma kwarjinin dan nata da ya kafe ta da kyawawan idanunshi ya cika mata ido.
Ta sassauta grinning din fuskarta, ta ce, “Ita ba ta da baki? Ko kai ne bakinta?�
Aalimah ta zube a kan gwiwoyinta a gaban Mummy Zulaiha cikin sanyin murya ta ce, “Welcome Mummy. And I’m sorry if I hurt you. I’m very sorry!�.
Aunty Zulaiha ta dan rufe idanunta, sannan ta bude ta dubi yarinyar. She’s innocent, tana da innocence looks. She’s looking just like her husband kamar shi ya haife ta. Yanayin su na sanyin hali iri daya ne. Wannan ya sa ta ke kama da su Basma. Tunda ta zo ba za ta ce ga wani abu da ta yi da ya bata mata rai ba. Tana shaping tarbiyyar su Basma ne kawai, ba lalata su ta ke yi ba. Sunkuyar da kanta ta yi kasa.
Basma ta ce, “PleaseMum talk to Aal, she’s our sister�.
Khaleesat ta ce, “She is nice Mummy, she cooks for us, she’s taking care of us very well in your absence (ki yi mata magana Mummy ‘yar uwarmu ce)�. In ji Basma (tana da kirki Mummy, tana dafa mana abinci, tana kula da mu da ba kya nan sosai)�. In ji Khaleesat.
“And she bought for me sweets also�. In ji Yesmin.
Duk sun daure ta da jijiyoyinta. Ko ita ce tafi kowa rashin adalci a duniya. Sai ta mika hannu ta kama hannun Aalimah. A hankali ta ce,
“Thank you�.
Dadi ya kama sudukkansu, kar dai Abulkhair ya ji labari. A haka Daddy ya shigo ya cimmasu. Tsaye ya yi a tsakiyar falon ya kama kugu yana kare mata kallo. Ga hannunta cikin na Aalimah shi ne abin da ya dan sanyaya zuciyarsa. Sama ya wuce rike da suitcase dinsa ba tare da ya ce da kowa komai ba.
Mikewa Mummy ta yi ta bi bayanshi, yaran kuma kowacce ta kama sabgar gabanta cike da farin ciki. Aalimah ta mike za ta shiga kitchen suka hada ido da Abulkhair da ke zaune a kan daya daga cikin kujerun dining table ya zuba mata ido. Wani irin sonshi da kaunarshi ya kara mamaye ta.
Murmushi ta hau yi masa ba ta san tana yi ba, ya wani dauke kai ya juya mata baya. Sai a lokacin ta tuna ashe fa fushi yake yi da ita ta yi masa laifi. Karasawa ta yi kicin don yin abin da ta nufa, amma sai ta ji duk ta damu, zuciyarta ta yi mata babu dadi da fushin nasa.
Da ta fito daga kicin din kuma ba ta same shi a falon ba ya fice ya bar gidan. Tana jiyo hucin motarsa don ba za ta ce kara ba. Motocin Daddy are not making sounds wato (ba sa kara).
A can dakin iyayen suna can suna tafka ta a tsakaninsu, Daddy ya ce, don me ta dawo masa gida bai neme ta ba? Ta ce, saboda gidan mijina ne, gidan ‘ya’yana, kuma mijina ba sakina ya yi ba. Nan kuma ta kwantar da kai ta shiga ba shi haquri har da kukanta.
Mikewa ya yi zai bar mata dakin ta kamo shi ta kankame, ta shiga rantsuwa tana daukar masa alkawarin wannan karon ta dau laifinta, za ta canza ya ba ta dama, she has no business ( ba ruwanta) da kowa nasa da duk wanda zai kawo gidansa. Cewa ya yi I’m tired(na gaji) da tuban muzurinki.You will never change Zulaihatu, (bazaki taba canzawa ba) mai hali ba ya fasa halinsa, I’m tired of all these, ya kamata mu bai wa juna sarari, har kowannenmu ya je ya yi kwas a kan halin dan uwansa. Na kasa saninki fully har gobe, in na ci gaba da biye miki halaka ni za ki yi…!�
Yadda ta rungume shi cikin jikinta da runguma mai tsananin karfi, jikinta yana rawa da karkarwa da jin kalamansa, shi ya hana shi karasa magana. They missed each other to such an extent… don haka duk wani mai korafi ma a tsakaninsu ya adana korafin nasa a gefe zuwa gaba. Amma ko daga yanayin Zulaiha a yau da yanayin bugun numfashinta ya san ta yi nadama wannan karon, wadda yake fatan Allah ya sa ta dore. In kuma hakan bai yiwu ba, duk son da yake mata wannan karon zai ba ta mamaki ta inda ba ta zata ba. Al’amarin mace da miji sai Allah, cikin daren suka shirya kansu.
A can dakin su Aalimah kuma, kowa ya yi barci ya barta. Wayarta ce a hannunta tana jira ko Abulkhair zai kirata? Ta kasa barci ko kankani. Ganin har karfe sha daya na dare bai kiratan ba bai kuma yi mata sako ba ya tabbatar mata fushin nasa na gaske ne. Ji ta yi duk ta tsani kanta, don me zata batawa mutum mai kyakkyawar zuciya irin Abulkhair? Mai sonka shi yake KISHIN KA, shi ya damu da al’amarinka. To amma don me zai damu kansa da zancen Mahmoud? Ya sa pressure sosai a kan zancensa. Ita ba ta dauki al’amarin Mahmoud da zafi ba, ba ta yi masa alkawarin za ta aure shi ba amma yafi karfin wulakanci a idanunta.
Abin da ta san ta ce da shi shi ne, “We can not runaway from our destinies but she is hoping that destiny tied them together (ba za mu iya gujewa kaddarorinmu ba, amma tana fatan kaddarar ta barsu tare). To kuma ga kaddarar ta yi gardama. Kamata yayi Aboulkhair ya dubi present dinta ba past dinta ba. Damuwa ta yi damuwa a zuciyar Aalimah, ta jefa zuciyarta cikin wani yanayi mara dadi. Ba ta san ta kamu da son Abulkhair har haka ba sai yanzu da ta ke ganin yana kokarin barinta kan abin da bai kai ya kawo ba a ganinta.
Da gaske Mahmoud ya fi kama da aboki fiye da saurayi a zuciyarta. Akwai sabo a tsakaninsu, duk da shi ba hakan ba ne a tashi zuciyar. Amma a halin yanzu ji ta ke zata iya komai don ta samu Abulkhair, farin cikinsa da kwanciyar hankalinsa ya fiye mata komai, hada da wannan karatun da ta ke yi kuwa, za ta iya barinshi in har barin nasa na nufin mallakar Aboulkhair a matsayin miji.
Ba ta da masaniyar cewar Abulkhair ya sanya lambar wayarsa a ciki ya adana, sai ganin wani lafiyayyen french word ta yi yana yawo a fuskar wayarta, mai nuna shigowar kira; Ma cherie, wato My love da harshen faransa. Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki ta yunkura ta mike zaune. Sannan ta hau juyawa damanta da hagunta kamar munafuka tana kallon su Basma don tabbatar da barci suke ko idonsu biyu? Ta tabbatar sun yi nisa a barcinsu sai ta lallaba ta shige toilet da wayar a hannunta.
Zuwa lokacin kiran ya katse wani ya kara shigowa. Zama ta yi a gefen bath tube, sannan ta yi sliding wajen amsa kiran.
“Not asleep like me?�
Ta ji muryarsa cikin damuwa tana tambayarta.
“Ta ya ya zan iya barci kana fushi da ni Yayan Basma?� Muryar da ta yi amfani da ita wajen yin maganar ta nuna zahirin damuwar da ta ke ciki.
Tana jin yadda Abulkhair ya sauke ajiyar zuciya, “Ban san kin damu da ni har haka ba, da ban sa kaina cikin damuwa haka ba. I thought you love him, since you cannot erase him from your memories, you want your relationship to continue…� ( na zaci kina sonsa, tunda bazaki iya goge shi daga tunanin ki ba, kina son alaqarku ta cigaba).
Dan runtse ido ta yi, tone din muryarsa na kassara duk wani sauran kwarin gwiwar da ta ke da shi na yi masa bayanin da zai kwantar da hankalinsa. Da kyar ta iya yafito sauti daga makogaronta.
“He is not in my memories, he is where he is (ba ya cikin tunanina, yana dai inda yake). I feel nothing for him� (bana jin komai akansa).
Abulkhair ya kara nitsewa cikin duvet dinsa. Murmushi yake yi wannan karon, duk wata damuwar da ya sanya kansa ya neme ta ya rasa. Murmushin da ake kira daga kunne zuwa kunne don fadinsa.
“Ni kuma fa? A wane bangare aka sanya nawa feeling din? Tunda na shigo gidan nan na rasa kaina, na zama ba ni ba Aal, duk bugun da zuciyata za ta yi ke ce a cikinsa. Aalimah, I want to say it loud I love you… ba zan taba komawa yadda na zo ba sai na samu amsar bakinki. Ki gaya min komai kankantar kalmar da zan amince ba ni kadai nake wahala ba. Amma in kin fi son wancan mutumin don Allah kada ki gaya min, it will go away with my last breath (zai tafi da numfashina na karshe)�.
Tun da ya fara magana Aalimah ke jin wasu bululluka da suka danne zuciyarta na rugurguzowa suna kara dasa shi a zuciyarta. Zuciyar ta zama ‘yar shafal babu sauran damuwa a cikinta. Lumshe idonta ta yi ita kadai ta ke blushing tana rufe ido tana budewa. Ci gaba ya yi da gaya mata duk abubuwan da yake fama da su cikin zuciyarsa a kanta yana kuma rokon mafi kankantar kalma daga gareta mai nuna kauna ko yaya a gareshi. Kwalla ta ji ta taru a idonta, ta so da kaunar Abulkhair da kuma tausayinsa duka a lokaci daya.
Ta samu kanta a mai tambayar kanta me ta ke da shi da har dan gata irin Abulkhair zai mace a soyayyarta haka? Yaya Aboubacar ya sha cewa she’s the ugliest of their house (itace mafi muni a gidansu). Hancinta kamar an dosana mata shi, idonta kamar kwan zabo, bakinta kamar gidan tsutsa. Ta tuno suffa da kira mai zati irin na Aboulkhair, amma duk bai duba wannan ba a haka yake sonta.
Abulkhair ya fidda ran samun raddi daga Aalimah, yana shirin kashewa ya san yadda zai yi ya yi jinyar zuciyarsa ya jiyo ta tana cewa.
“Ina jin fiyeda abinda kake ji, na fara son ka daga lokacin da na dora idona a kanka. Na kasa barci sabida tunanin kana fushi da ni. Ban taba soyayyya ba sai a kan ka. I love you ABOULKHAIR!�. .
This is the beginning,kuma farkon kaddarorin rayuwar Aalimah.
******
Washegari Mummy ta koma aiki, tsakaninta da Aalimah kadaran-kadahan, babu tsana babu hantara, amma babu soyayyah. Duk hidimominta da ‘ya’yanta ta ke yi ba ta sanya ta. Ba ta sanya ta a shirginta balle ta dame ta, sabgogin gabanta kawai ta ke yi. Aalimah, ba ta sanya hakan a ranta ba balle ya dame ta, sai ma wani ladabi na musamman da ta ke yi wa Mummyn kamar uwar da ta haife ta, ko da Mummyn ba za ta nuna appreciation ba.
Ta dora wa kanta gyaran komai na Mummyn wanda Easther ke yi kamar gyaran kayan sanyawarta, shirya mata takardun office in ta hargitse, rike mata jaka zuwa mota, gaisuwa da tsugunno har kasa. Taya ta hidimar gida, da kula da Yesmin saboda ita kanta Easther ayyukan gidan wani lokacin suna fin karfinta kasancewar ita kadai ta ke komai da komai, Mummy ba ta son yawan ‘yan aiki kada su cika mata gida, don haka Aalimah ta karbi rabin hidimar gidan in dai tana gida ko ba ta da lacca ko a karshen sati dan abin da su Basma ke yi a gidan bai taka kara ba balle ya karya. A ganin Aalimah, a yanzu kam she can do anything for Mummy in dai za ta barta ta rayu da danta. Wanda ranshi ne kawai ba ya cirowa ya bata saboda so da kauna.
Ya ci gaba da kai su makaranta da dauko su da komawa wajen Aalimah su sha hirar soyayyarsu a dukkan intervals dinta, in dare ya yi kuwa lokacin bude ofishin soyayyarsu kenan a waya, yadda suke son junansu ba sa son karatun da suke yi. Tun Basma ba ta ba su hankalinta don ta dauka haduwar jini ce, har ta soma disa wa alakarsu dindimemiyar ayar tambaya.
Mummy kam ba ta fahimci komai ba, har gobe. Don hasashenta da hankalinta bai taba hasaso mata hakan za ta iya kasancewa ba. Khaleesat kam babu harkar kowa a gabanta balle ta damu da sanin me wani nata yake ciki. She’s always busy with her text books and islamic lesson. Basma ta sha kama Aalimah na yin night call a toilet, sai dai ba ta san da wa ta ke yi ba, ta ma fi zaton wannan nataccen saurayin nata na Nigeria ne. Abin da ya fara cika mata idanu shi ne kusan kullum, Monsieur Abulkhair dinsu na makarantarsu, kuma duk sanda ta zo neman Aalimah za ta gansu tare. Mafiyawan lokuta karatu suke yi yana koyar da Aalimah lissafi da sauran abin da ya shige mata duhu, sai dai idanunsu kadai za ka kalla ka hango wani kwantaccen al’amari da suke dauke da shi ga junansu. Kasa boye tambayoyinta ta yi rannan ta tambayi Aalimah a kan hanyarsu ta isa ga inda Abulkhair ya yi parking domin su tafi gida.
“Is Monsieur Abulkhair in love with you?� Ta yi tambayar ne don shakuwar da ta ke gani a tsakaninsu ta wuce hankalinta, amma ba wai don akwai wani abu a ranta game da hakan ba, so ta ke ta tabbatar da abin da zuciyarta ke gaya mata.
Hararar da Aalimah ke jifanta da shi, ta kuma ki ba ta amsa ya tabbatar mata da zarginta. Dariya ta yi, sannan ta kai wa Aalimah dundu a baya.
“Ke da shi din kun dace, saboda dukkaninku halinku daya, charming, cheerfuland compossionate personality. Sai dai zan so in tuna miki rules din Daddy kafin shigowarmu makaranta, duk wadda ta sake ta yi saurayi, AURE!�.
A yadda Aalimah ke jin Abulkhair a ranta, she can give him the life itself(zata iya bashi rayuwarta dungurungum) idan za ta iya, ba karatu kadai ba. Abulkhair, ba ya son tunowa cewa hutunsa ya zo karshe, zai koma Baton Rouge (Louisiana) kwanaki biyu masu zuwa.
Sosai Aalimah ke rokon Basma kada ta gaya wa Mummy komai a kansu. Da Basma ta tambayi dalili, sai ta ce, “Mummy ta fara sona Basma, mun fara samun fahimtar juna, I don’t want to lose this love from her, (bana son rasa wannan soyayyar daga gareta) tunda ban san yadda za ta karbi al’amarin ba�.
Basma ta yarda da uzurinta, amma zuwa can sai ta ce, “But she must know (dole ta sani) tunda karewa ma jikoki za ki kawo mata!�.
“Sai ki bari in jikokin sun zo sai su fada mata da kansu�.
******
Yau asabar, ta kama da yammacin yau din Abulkhair zai bi jirgin kasa zuwa inda ya fito. Tun safe yake dacin rai, Aalimah ta shirya masa breakfast amma yana fitowa daga wanka da ya zo ya gani sai ya hau fada, wai shi bai ce mata chips zai ci ba, ta kwashe ta maida kitchen tun bai kifar ba. Gefe ta koma ta langabe kai abin tausayi, sai dai fa duk fadan nan da yake yi ya ki yarda ya kalli kwayar idanunta.
Mummy da ke kan dining din tana cin nata ta dube shi cikin jin haushi, “Amma me ye laifinta, ta bata lokacinta ta shirya maka ba tare da kowa ya sanya ta ba? Besides, the cooking is good, as far as I know, you love chips so much�.
“To yau na daina sonshi. Ni ban ce muku ma zan ci abinci ba, I’m not hungry�.
Aalimah na gefe tana kallon sakarci, uwar ta bi duk ta damu, sai lallaba shi ta ke kan ya ci, yana dada botsarewa.
Daddy ya shigo falon daga jogging din da ya je waje, ya tadda su a haka. Yana shigowa Mummy cikin damuwa ta soma gaya masa yadda aka yi.
“Idan aka kyale shi haka zai kama hanya ya tafi ciki ba komai�.
Ya ce, “Wa ya yi girkin?�
Ta ce, “Aalimah ce�.
“Kuma ya ce ba zai ci ba?�
Abulkhair ya sunkuyar da kai sai cika yake shi kadai. Daddy kwafa ya yi ya iso har gabansa ya ce, “Gara ma ka ci, ka ci na bankwana sai bayan wata ukku. Idan kuma ka sake ka kara ko kwana daya kan hutun nan I know how to deal with you. I will cancel even the phone calls�.
Da sauri ya dago ya dubi mahaifinsa, with shock in his eyes.
Ya ce, “Yes, I mean it�.
Aalimah ta sunkuyar da kai kamar ta ce, kasar ta tsage ta shige. Wato maganar da ya taba gaya mata na cewa, Daddy ya san da zancensu da gaske yake yi? Yau ina za ta sa kanta da kunyar kawunta? Mummy ta ce,
“Wane phone-call za a yi cancelling?�
Daddy bai ba ta amsa ba ya yi wucewarsa.
Basma ta shiga boye bakinta tana dariya, ganin yadda Monsieur ya kwalalo ido an ce za a hana shi waya da Aalimahrsa. Mummy dai ta kasa gane me suke ciki, ta tashi ta bar wajen.
Aalimah ta daga kafa za ta bi bayanta, ya sha gabanta. Ta dago idanunta da suka yi rauni ta dube shi, ta fi shi shiga damuwa a kan tafiyarsa. Ta fi shi shiga taraddadin yadda za ta iya ci gaba da rayuwa cikin Massachusetts babu shi, kanta ya bude da calculus da sauran danginsa, yanzun ba ta shayinsu. He made all her courses very clear and simple to her ta yadda ba ta bukatar taimakon kowanne namiji a Boston yanzu. Ya taka rawar mutane guda hudu a dan zaman da suka yi tare; dan uwa, aboki, malami kuma masoyi. Ya koyar da ita karatu ya koyar da ita yadda za ta so shi. Ba ta son ta soma tunanin ta yadda za ta fara kewarsa…!!!
“Is that the kind of adios we are going to do? (wannan ce irin sallamar da za mu yi?)� Cikin zuciyarta ta ce, “Kai zan tambaya. Ka zo kana ta dagawa iyayenka hankali for no reason (babu dalili) don kawai sun ce ka koma makaranta�.
Zancen zuci ta ke, ba ta san cewa a fili ta ke yi ba.
Yatsun hannunsa ya tura cikin tarin sumar kansa, yanayin fuskarsa kadai ya nuna tsantsar damuwar da yake ciki. “na rasa hanyar da zan nuna musu bana son komawashi ya sa na ce bari in ki cin abinci, watakila su gane zuciya ta, ba ta da lafiya su barni in zauna, amma ki ji abin da ya ce he will cancel even the phone call�.
Ya fada yana bata fuska kamar mai fadar wani mummunan abu.
Dariya Aalimah ta yi, ya bata rai sosai, “Au dariya ma ki ke mini? Ba komai, it’s all a matter of time. I will wait, as he insist, I know it is not easy to possessed a diamond, but when one have it, he will do what he wants with it (Zan jira, kamar yada ya dage sai na jira. Nasan ba abu ne mai sauki ba mallakar lu’u’lu’u(dutsen yakutu), amma idan mutum ya mallake shi zai yi abinda ya ga dama da shi�.
Wannan ita ce sallamar Aalimah da Abulkhair. Da yamma ya bi motar haya zuwa birnin Baton Rouge daga Boston inda Louisiana State University ta ke. Tafiya ce ta one hour kacal a tsakaninsu.
Yana zaune a seat dinsa yana ta juya wayar hannunsa. Daddy ya ce bai yarda ya kira Aalimah ba ko ya yi mata sako, sai a karshen mako kadai. Idan kuma ya ketare zai zare hannunsa ya barshi da dabararsa. Hukuncin is so painful so much unbearable… To amma ya zai yi? Yana son mallakar Aalimah kuma Daddy ya yi na’am, alfarma daya yake so ya yi masa kada ya hana ta karatu da soyayyah, don ya fita kunyar iyayenta. Shi kuma zai yi duk iya kokarinsa na samar da ita gare shi. Ya san jiran zai zamanto kamar jiran zuwan ranar tashin kiyama (seem like endless), amma ya amince with time and Allah’s will da kuma tsawon numfashi komai mai tabbatuwane. .
Da tunani ya cika masa kwanya sai ya kira Yayansa Mu’az, shi kadai ne zai iya mantar da shi duk wani hali da yake ciki da salon tashi kaunar ta dan uwa which is exceptional. Mu’az na dagawa abin da ya fara cewa shi ne.
“Something or someone snatched away my brother from me. What is it? Or who is she?(Wani abu ko wani mutum ya janye min dan uwana daga gareni, menene wannan abun ko wacece ita?)�
Ajiyar zuciya Aboulkhair ya yi, wasu lokutan Mu’azzam kamar yana karantar shafukan zuciyarsa. Duk abin da yake ciki kafin ya gaya masa yake ganewa. Shi ne dai har gobe ya kasa gama sanin Mu’azzam. He is like a magician when it comes to reading minds (kamar wani mai sihiri yake in aka zo batun karantar zuciyar mutane, musamman shi Abulkhair). He care for him too much fiye da sauran kannensa. Tare suka yi duk wata dabdala ta kuruciya a birnin Washington kafin kaddara ta dawo da su zama a Boston (Massachusetts). Haka duk kaddarorin rayuwar Mu’az sun faru ne a kan idonsa. Wani abu da ya dasa wata irin kauna da jin kai a zuciyarsa. Ba don Mu’az ya fi son rayuwa shi kadai a inda yake ba, da zai iya hakura da karatu a Baton Rouge ya zauna tare da shi, ya ba shi dukkanin farin cikin da dan uwa zai iya bai wa dan uwansa duk da ya san hakan ba zai fidda shi daga halin da yake ciki ba.
‘Kwalla’ abu ce mai sauki daga idanun Abulkhair when it comes to MU’AZZAM. A yanzun ma kwallar ce ta cicciko idanunsa. Ya canza position din rikon wayar daga kunnen dama zuwa na hagu, amma bai yi magana ba. Mu’az a tausashe ya ce, “Na ce mene ne ya dauke hankalinka daga gare ni, ko WACE CE?�
With a very low tone ya ce, “AALIMAH�.
Dariya Mu’azzam ya yi irin dariyarshi mai tafe da gentleness tune.Wai yau Abulkhair ne da soyayyah! Abulkhair din da ya sha cewa, tunda ba zai yi aure ba, shi ma ba zai yi ba, yau shi ne da dakon soyayyah tun kan a kai ga zama Doctor din kula da shi da aka ci wa alwashi. Lallai ko wace ce wannan Aalimah ta ciri tuta, kuma zai so ya ganta. Dariyar Mu’az ta sanya Abulkhair rufe fuskarsa da tafin hannunsa, kamar Mu’az din na ganinsa. Wai shi ya ji kunya.
Mu’az ya ce,
“Then where will I find my psychiatric Doctor?�
Cikin tsokana ya yi maganar, kamar yana magana da karamin yaro.
Dariyar da Abulkhair yake yi ta mantar da shi duk wasu damuwoyinsa,
“The boy will keep striving to be what he promised to be. This is a promise!�.
(Yaron zai cigaba da kokari har sai ya zama abinda yayi alkawarin zama. Wannan alkawari ne)�.
Da wannan suka yi sallama.
******
Wani dare mai wuyar barci ga Aalimah. Ji ta ke kamar wani sashe na jikinta ba ya tare da ita. Abulkhair ya shigo rayuwarta da karfi, ya zauna da muhimmanci. Ta kasa barci sai juyi a kan gadonsu. Duk kuma juyin da ta yi sai ta ji amsa kuwwar dadadan kalamansa cikin kunnuwanta. Sai ta ga gilmawar kyakkyawar fuskarsa a idanunta. Idan wannan ita ce soyayyah, to ba ta yi mata kamun sauki ba, sannan aba ce mai wahala cikin zuciya da kwakwalwar dan Adam.
Da safe ta sha tsokana a wajen Basma, ganin yadda ta yi cooling ta rasa duk wani karsashinta, Basma ta ce, “Ko Baton Rouge za mu koma da karatu ne?�
Harararta ta yi ta sauka kasa, don taimaka wa Mummy a kitchen kafin zuwan Easther.
6/28/21, 7:32 AM - Buhainat: $$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$
64
Daddy shi ya kai su makaranta ranar litinin, kamun Laraba kuma ya samar musu direba. Bakar fata ne dan kasar Cameroon. Sunansa Joseph, suka ci gaba da karatunsu cikin kwanciyar hankali. Tsakaninta da Mummy yana nan yadda yake, babu soyayya, amma babu kiyayyah. Kowa yana zaman kansa, zaman wanda ya ajiye shi. Sai dai ita kanta Mummy tana yabawa da dabi’un Aalimah a zuciyarta, furtawa ne ba za ta yi ba. Tana yabawa da kulawarta a kan yaranta da yadda suke canza dabi’u gradually ta hanyar koyi da ‘yar uwar tasu. Khaleesat har koyon daurin zani ta ke, tana kuma daukan karatun alkur’ani daga Aalimah da sauran al’adunmu na gargajiya, al’adun da ta ke wa kallon kauyanci, amma can a karkashin zuciyarta ta san wannan shi ne daidai, kuma ita ma ba sonta ba ne yaranta su lalace ba, tun a kan Mu’azzam ta yi sanyi da daukan dabi’un Turawa da tsanani, duk da cewa sun yi babban tasiri cikin rayuwarta. Ta manta da yawa daga nata al’adun da hukunce-hukuncen addini.
Zamanta da Aalimah da kasancewarta cikin ‘ya’yanta sai ya zamanto kamar ana tuna mata wasu abubuwa da ta manta. Ta kuma fara sassauta wa kanta kin yarinyar, ta yarda mutum rahma ne, amma jure zama da shi shi ne abin da yake mata wuya. Sai dai in ka yi katari da na kirki irin Aalimah ya fi ruwan sha saukin sha.
Babban abin da ke burge ta da Aalimah rashin kiwa, ba ta da son jikinta ko kankani, ga nutsuwa da rashin rawar kai, ga tsafta da kula da tsaftar jikinta. Ko fensir Yesmin ta yasar Aalimah ba za ta barshi ba sai ta dauke ta adana mata shi cikin jakar makarantarta. Sannan ba ta da rayuwa mai zafi irin ta Basma, ita kam Basma komai nata tana so ya zama na musamman. Kayayyakinta, abubuwan amfaninta sai ta tabbatar fitacce ne (designer) ne ko latest fashion. Zamanta da Basma da shakuwar da ke tsakaninsu bai sa ta yi adopting nata dabi’un ba, ita Basman ce ke tsintar nata tana hadawa da nata.
Abulkhair ya yi kokari sosai wajen maida hankali a kan karatunsa kamar yadda mahaifinsa da Yayansa ke so. Sun yi masa alkawarin tsaya masa a kan komai idan ya jajirce ya fiddo kwalin likitancinsa. Ba Aalimah kadai ba, har da karin guda uku bayan ita in yana so. Dakatar da su yake in sun fadi hakan, “She’s okey for me till eternity (ta ishe ni har abada)�.
Asabar na zagayowa ba ya iya hakurin yamma ko dare zai fara kiran waya kamar Allah ya aiko shi. Tana zama unease idan kiranshi ya shigo tana tare da kannensa ko iyayensa ba ta iya amsawa. Don haka duk sabar ta ke maida wayarta a vibrating ta soke ta a jikinta, da ta ji shigowar kiran Abulkhair za ta tsallake ko mene ne ta fita compound na lodge dinsu su sha hirarsu kamar sun hadiye juna, duk rabin hirar Abulkhair yana gaya mata yadda yake kewarta ne da yadda zuciyarsa ta makance a kaunarta. Yadda yake managing kafin zagayowar sati ya yi magana da ita. Hakuri ta ke ba shi ta karfafa masa gwiwa kan bin maganar Daddy. Tana tunatar da shi cewa abu mai kyau yake nufinsu da shi (good future). Ya ci gaba da rokon Allah ya barsu da rai da lafiya, shekaru hudu kamar yau ne. Sun fi yin magana a vedio call, yadda za su dinga ganin zahirin abin da ke zuciyar junansu cikin kwayan idanunsu. Ba ya kiranta da daddare, yana barinta ta yi barci isasshe. Wannan ya kara kauda hankalin kowa a kansu cikin gidan, ban da Basma da Daddy ba wanda ya san me suke ciki.
Sun yi jarrabawar karshen zangonsu lafiya, suka samu hutu na sati biyu. Ba da sanin kowannensu ba daddy ya gama yi musu shirin tafiya Nijar. Bai gaya musu ba, sai ana saura kwana biyu tashinsu. Yaran sai murna suke yi, don sun dade ba su je Nijar ba. Sai dai daddy ya ce da Aalimah ta rage murnarta, ba za su karasa Nigeria ba, sai a hutun karshen shekara zai shirya mata zuwan ita kadai. Murmushi kawai ta yi, daga Nijar har Kano duk gida ne a wurinta.
Mummy dai ta bada uzuri da office dinta. Kuma da gaske hakan ne, ba za su barta ba. Sai dai fa gaskiyar magana ko babu office ba za ta yarda ta bi su ba. Ta riga ta sa wa ranta dangin Ishaq ba sa sonta, don haka babu wata alaka tsakaninta da su. Ta yi kokari kwarai wajen dauke hankalinsa daga kansu da nuna wa ‘ya’yanta su manta da wanzuwarsu a doron kasa ba masoyansu ba ne.
Yau rana daya ya zo ya ce zai tafi Nijar da ‘ya’yansa bayan ‘yarsu da ya dauko ya kawo mata, har ya kore ta daga gidan a kanta! Ba ta san me yake ta canza mata Ishaq haka ba, ga shi duk wani karfi da ta ke da shi a idonsa ya yi sanyi, yanzu ba ta isa ya yi abu wanda bai gamshe ta ba ta ce da shi don me? Wani sabon Ishaq ne wannan ba wanda ta sani tun kuruciyarsu ba.
******
Jirgin Ethiopian Air ya sauke iyalin Ishaq Raazee a filin jiragen saman Diori Hamani International Airport da misalin karfe goma na safiyar lahadi agogonsu na can. Sun samu Hamoud babban dan Uncle Oussama yana jiran saukarsu, shi da Balkisa ‘yar Uncle Edrissa babbar kawa ga Aalimah kenan kaf dangi. Iyalin Ishaq sun zamo kamar wasu taurari sha kallo a cikin gidan Malam Ibrahim Raazee a yau saboda murjewa da kyan fatarsu, duk da cewa kowa a gidan fari ne kal! Amma nasu ya sha bamban da na kowa. Kan ka ce meye wannan? Gida da makwabta ya kacame da murnar zuwansu, aka shiga aiko da akussan abinci daga kowanne bangare. Inna Kasisi kam ko a launin fuska babu wani alamu da zai nuna maka ta yi farin ciki da zuwan nasu, sabgogin gabanta kawai ta ke na dora sanwar abincin rana na gidan bakidaya, kasancewar abincin gandu ake yi a gidan.
Inna Bintou ce ke ta hidima da su tun shigowarsu da ‘yammatan gidan (jikoki) sa’anninsu. Daddy Ishaq kasa yi wa Inna Bintou alkunya ya yi irin wadda ya saba, wato fara shiga sassanta, dakin mahaifiyarsa ya shiga kansa a duke yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Ta kara tsufa mai nuna alamun girma a tare da ita tsayin shekaru shidda da ya kwashe bai sako kafarsa a gidan iyayensa ba. Zama ya yi a kan kilishi ya tankwashe kafafunsa, zuciyarsa ta yi nauyi mai cakude da matsananciyar nadama. Sam ta ki yarda ta zauna a dakin, sai dai ta shigo ta dauki abu ta fita ba tare da ta dubi bigiren da yake ba.
Ko da ta gama girkinta ba ta zubo masa ba, amma ta zuba wa su Aalimah. Shinkafa fara tas! Da miyar dage-dage wadda ta ji fala-falan ganyen kabeji da naman rakumi zuku-zuku. Abincin ya yi masa kyau a ido, ya kuma ba shi sha’awa. Ya shiga tunano yadda suke santin abincin Innar shi da yayyensa Oussama, Edrissa da kaninsa Mansour da sauran kannensu ‘ya’yan Inna Bintou. Da yake a faranti guda ake zuba musu, in an cinye a yi kari, kafin a zo karshe a yi wawa a rikice da kokawa. Kwalla ta ciko idanunsa, amma bai bari ta gangaro ba.
Reaction din Inna ya nuna masa Inna tana fushi da shi, duka tsayin wannan lokacin tana kullace da shi a kan banzatar da ita din da ya yi, ya shiga tambayar kansa me ya shiga kansa? All these while da ya manta da iyayensa, ya manta da girman hakkinsu a kanshi da kulawar da Allah ya ce ya ba su.
A lokacin ne Malam ya dawo daga rangadin da ya tafi wajen rakumansa a can wani kebantaccen muhalli. Tsufa ya bayyana sosai a tare da shi. Inna Bintou ce ta je ta sanar da shi zuwansu. Ko abinci kasa ci ya yi sai da aka kira mishi jikokin nashi, tare suka ci abinci a kwano guda yana tambayar Aalimah yanayin karatunta. Ta gaya masa komai lafiya, sannan ya ce da Basma, “Ina Mu’azzam? Ina kuma Abulkhair?� Cikin harshen buzanci.
Daddy yana yi musu sosai don haka suna ji sama-sama, sai ta juya nata harshen ta soma ba shi amsa cikin yaren Faransa.
“Monsiuer Abulkhair ya koma makaranta, bai ma san za mu zo nan ba, na tabbatar maka da sai ya ajiye jarrabawar da yake yi ya zo. Mu’az kuma yana nan yadda yake, annoying kamar koyaushe. Ya fi son rayuwa a LAS VEGAS fiye da ko’ina a duniya. Ba ya zuwa gidanmu don wai muna yi masa hayaniya. Mum and Dad, su suke zuwa wajen Mu’azzam. Grand-pere (kakanmu) Mu’az ba ya son mu ko kadan, Monsiuer Abulkhair kadai yake so a cikinmu. Ba dama mu yi magana in yana zaune he will throw a tantrum (zai yi masifa). He is the most annoying person in the world (ya fi kowa ban haushi a duniya), watakila shi ya sa ya kasa samun mata�. Ta karasa cikin dariya.
Tunda ta fara kakan yake sauraronta, yana duba maganganunta filla-filla. Shi kuma a wurinsa Mu’azzam is a nice person fiye da dukkan jikokinsa. Duk sanda ya tambaye shi me ya hana shi aure, sai dukkan walwalar fuskarsa ta canza, idan ya takura da tambayar sai ya ce,
“Idan ba ka daina yi min zancen aure ba Mallam zan daina kiranka a waya, ba kun yi min auren ba? Me na tsinta a cikinsa?�
“Mu’azzam, ba mu muka yi maka aure ba, Babarka ce ta yi maka, babu saninmu, babu hannunmu. Babanka ya zo bagatatan ya ce za a daura maka aure don a ceci rayuwarka ba ka da lafiya, shi ya sa na amince wa Oussama ya je aka daura, amma ba mu san komai a kai ba�.
Dattijo Ibrahim Raazee ya yi ajiyar zuciya. Ya dubi jikokinsa biyar da ke zaune a wajen ciki har da Aalimah. Sannan ya kai dubansa ga Basma wadda ta fi kowa kaifin baki cikin jikokinsa. Ya ce da ita cikin auzinanci,
“He is not annoying, he is compassionate�.
Ta daga manyan idanunta irin nasa da suka gado, ta dube shi, “Non Grand pere (a’ah Kaka), he’s annoying, and he don’t like us�.
Sai ya yi murmushi ya kyale ta suka shiga wata hirar. Ya fahimci babu wanda zai kankare wannan belief din daga zuciyar Basma, na cewa, Yayanta mutum ne mai ban haushi, mara dadin mu’amala, sannan ba ya sonsu.
A can dakin Inna kasisi ta gama duk sabgoginta ba abin da ya rage mata a tsakar gidan, dole ta koma dakinta ta yi alwala ta tada sallah. Duk Daddyn Basma yana zaune sunkuye da kai ya kasa cin nau’ikan abincin da aka tara masa a gaba. Sai da ta idar ta yi addu’a ta shafa, sai ta ci gaba da zama a kan sallayarta. Ya ga cewa wannan ita ce damarsa ta karshe, kada ta sake ficewa a dakin.
Ya shiga rarrafawa a kan gwiwoyinsa har ya tadda ita. Hannayenta biyu ya kama ya rike cikin nashi, sai kuma ya kwantar da kai a cinyoyinta ya fashe da kuka.
Cikin kukan yake rokonta ta yafe masa, ya gane dukkan kurakuran da ya tafka da kansa, ya yi nadama ya dauki niyyar gyarawa, in ma cewa ta yi ya baro kasar Amurka ya dawo gida zai yi mata wannan biyayyar. Tun zuciyarta na tururi har ta soma karyewa. Shi din ba karamin yaro ba ne ya ba wa hamsin baya, har da furfurarsa. Amma ga shi yana kuka cikin tsananin nadama, ta gode wa Allah da hakan ta faru da sauran numfashinta. Ta san kaidi irin Jai mazajensu jahannama a dalilin fushin iyaye.
Lokaci ya yi da ita ma za ta nuna wa Zulaiha matsayinta na UWA mai cikakken iko a kan danta, ba ita da ba ta da ikon komai a kansa ba, shi ne ma yake da shi a kanta.
“Mon pils�. Ya ji ta ambata ayayin da ta kai hannunta cikin tarin sumar kansa. Mon pils na nufin DANA.
“Na yafe maka duniya da lahira. Ka je wajen mahaifinka ya dawo tun dazun�.
Dagowa ya yi idanunsa sharkaf da hawaye yana yi mata godiya. A yadda ya san taurin rai irin na Innarsa bai zaci wannan yafiyar ta gaggawa ba. Allah kadai ya san shekarun da ta kwashe tana kwankwadar damuwa da bacin rai a kansa.
Dakin Malam ya nufa, nan ya tadda su Aalimah suna ta shan hira da kakansu. Kana jin tashin muryar kowaccensu tun daga bakin kofa ana ta auzinanci mai cakude da faransanci, amma ban da ta Aalimah. Da ya yi sallama ya shigo duk suka yo kansa da magana, Aalimah tana daga gefen daman kakan tana danna wayar hannunta, nutsuwar yarinyar da rashin hayaniyarta na burge shi. Sai ta tuna masa da dansa Mu’azzam, haka yake shi ma, in za ka ji muryar mutum goma a wuri ba za ka ji tashi ba. Wani tsananin tausayin Mu’azzam ya kara lullube shi.
To shi Mu’az haka zai karasa rayuwarshi babu farin ciki babu future kawai don Allah ya dora masa lalura? Hawaye ya ji sun ciko idonsa, ya yi sauri ya dauke su da yatsun hannunshi, duk a kan idon mahaifinsa. Duban yaran ya yi, ya ce duk su je su yi sallar la’asar lokaci ya yi. Ya rage daga shi sai Babansa.
Sun gaisa sosai, da tambayar iyali da hidimomin rayuwa. Ya ba wa Malam hakurin tsawon lokacin da ya dauka bai zo gida ba. Ya roke shi ya taya shi kara bai wa Inna hakuri. Ya yi alkawarin canza tsarin rayuwarsa. Ya gane mutum komin matsayinsa a duniya shi ba komai ba ne in babu albarkar iyaye a tare da shi. Duk tsayin shekarun nan ba wai dadi ne ya boye shi ba, ko kwanciyar hankali. Sam ma zai iya cewa tun shekarunsa biyu a American rabonsa da kwanciyar hankali, wato tun haihuwar Abulkhair. Matsalar rashin lafiyar Mu’azzam bai taba barinsa cikin kwanciyar hankali ba, bai barshi ya tara komai ba, kawai dai ya fi karfin abin da iyalinsa za su ci da bukatocinsu, sai gidan da ya mallaka da abin hawa. Shi ma wani babban mai mulki a siyasar kasar da yake aiki a karkashinsa ne ya mallaka masa su.
Komai na rayuwarsa a American da iyalinsa ya fede wa mahaifinsa, amma ya zaftare duk wani abu da ya shafi rayuwar Mu’azzam, saboda shi kansa ba ya son tunawa, kuma ba zai iya tattauna wannan al’amarin da kowa ba ban da Abulkhair, Zulaiha kuwa ba don rashin yafiyarsa gare ta da yin Allah ya isa gare ta a kansa zai kare ba, da sai ya yi mata.
Hira ce aka yi tsakanin uba da Da irin wacce ba a taba yi ba. Malam ya fahimci rayuwar dan nasa sosai, ba wai daular duniya ta boye shi ba, shi ma a can inda yaken matsaloli ne dankare tare da shi. Ba za a sanya Ishaq Raazee matsayin attajirai a Amurka ba, amma yana da rufin asirinsa irin na diaspora.
Kyakkyawan lodge da rantsattsun motocin hawa guda uku. Ga parmanent aikinsa a hannu. Sannan matarsa da ke aiki da babban bankin kasar Amurka ta fi shi tara abin duniya. Aikin Mu’azzam da kamfanin man fetur na CHEVRON CORPORATION ya kara taimakawa wajen rufuwar asirinsu. Kasancewar Mu’az din wani mutum da bai san dadin abun hannunsa ba, saboda ba shi da buri, ba shi da future planning a kan komai. Aikin ma yana yinsa ne don kar ya zauna ba ya komai, yana kuma biyan kudin hayar mansion din da yake ciki.
Shi yake biyan kudin makarantar Abulkhair baki daya, duk da cewa abin da yake biya din babu yawa kasancewar Abulkhair dan kasa ne, a can aka haife shi, duk cikinsu shi kadai ne mai nationality din Nijar, ba zai iya manta wahalar da Daddy ya ci a kan nasa karatun ba lokacin yana consulate officer karkashin ofishin jakadanci na kasar Nijar a kasar Amurka, lokacin Daddyn ba shi da hanyar samu mai yawa. Don haka zai iya cewa yana da buri a kan DADDY, ya kasance cikin wadata shi da wadanda suka shafe shi da kannenshi. Bayan wannan ba shi da wani solemn buri a rayuwarsa. Daga sanda ya fara aiki da Chevronya dauke wa Daddy hidimar lafiyarsa.
Sai da suka gama hirar suka soma labarin ‘yan uwa na nan kasar da Mansour da ke Nigeria. Mahaifin nasu ya tambaye shi ko shi ne ya sanya Mansour ya ba shi rikon Aalimah? Nan ya yi masa bayanin yadda komai ya kasance. Cewa, Mansour din a kan-kansa shi da maidakinsa suna da burin Aalimah ta yi karatun a Boston jami’ar da mahaifin maidakinsa ya yi ce. Ya gaya masa tun kafin hakan ya sha rokon Mansour ya ba shi yaran guda biyu (Aalimah da Aboubacar), amma ya ki. Sai kuma ga shi shi da kansa ya neme shi ya gaya masa ya samo mata scholarship a garin da yake. Malam ya jinjina son boko irin na Mansour a wasu lokutan har ya fi Ishaq muhimmanta ilimin boko. Kamar daga sama mahaifin nasa ya jefo masa tambayar da ta birkita shi.
“Me ke damun takwarana Mu’azzamu? Kun dade kuna ce da ni ba shi da lafiya, amma daidai da rana daya daga kai har shi ba wanda ya taba bude baki ya gaya min hakikanin me ke damunsa. Ban taba ganinsa da wasu kamanni ko alamomi na mara lafiya ba. Karewa ma duk ya fi ku kyakkyawan tunani da tsinkaye. Ya fi ku son zumunci da muhimmanta shi. Rashin lafiyar me ku ke cewa yana yi da har ya sanya ku yi masa wani irin aure da har gobe ba mu ji karshensa ba? Sannan me ya hana shi yin aure a halin yanzu a wannan gabar ta rayuwarsa?�
Gumi (zufa) Daddy Ishaq ya shiga tsattsafarwa daga kowanne sashe na jikinsa, ya kuma kasa amsa tambayoyin mahaifinsa. Malam din ya tsura masa ido, ya kuma fahimci halin rudanin da maganganunsa suka jefa dan nasa. Take wasu tunaninnika marasa dadi suka shiga darsuwa a ransa. Ya kaurara murya ya ce, “ISHAQA!�
Ya dago a hankali ya dubi mahaifinsa.
“Mu’azzamu kanjamau gare shi ko (yana nufin acquired immune deficiency syndrom)?�
A firgice Ishaq Raazee ya ce,
“A’ah, non, quite non, pere�.
Yana ganin yadda mahaifin nasa ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciya, ya lumshe idonsa irin na samun kubuta daga tunanin da ya dade yana wahalar da mutum. Sannan ya ce,
“Gaya min gaskiya, shi ba namiji ba ne to?�
Cikin yamutsa fuska da rashin fahimtar hausar ya ce, “Malam, kamar ya ya shi ba namiji ba ne?�
Sai Malam din ya sauya harshe, ya yi masa bayani yadda zai gane da abzinanci. Yana nufin wanda ba zai iya biyan bukatar auratayya ba. Ya fada masa gaskiya, in wannan ce matsalar Mu’azzam ba wani abu ba ne, babu irin maganin da bai sani ba a rayuwarsa, in ma shi bai sani ba, to ya san inda zai kai shi a yi masa maganin lalurar a Tessoua. Daddy ya rasa yadda zai yi. Bai san wane bayani zai masa ya fahimta ba. Lalura ce irin wadda bai taba sani ba a duniyarsa, kuma za ta yi masa wuyar fahimta. Nan dai ya tabbatar masa wannan ba ita ce matsalar Mu’azzam ba, sannan ya yi ta kame-kame. A karshe ya ce, likitoci suna kan bincike da sun fadi sakamako zai gaya amsa. Amma ya tabbatar masa ya kwantar da hankalinsa, Mu’azzam ba ya tare da ko daya daga cututtukan da ya ambata a sama.
Suna haka sauran ‘ya’yan Malam suka soma shigowa shigifar daya-bayan-daya daga gidajensu, daga unguwanni daban-daban da suke zaune a nan Niamey (Yamai). Daga ‘yan cikin Innarshi zuwa na Inna Bintou abokiyar zamanta. Kai ka ce Larabawan Kuwait ke shigowa suna zazzaunawa. Musabiha ce ta rika gudana tsakanin Ishaq da ‘yan uwansa, sai tambaye-tambayen lafiya da iyalin juna. Su goma sha tara cif! Sauran shidan mata ne a gidajen aurensu. Mansour da ke Nigeria ne kawai babu a cikinsu yau.
Cikin su mutum biyu ne suka girmi Ishaq, Uncle Edrissa da Uncle Oussama, wadanda suka kasance sun fito ne daga ciki daya, ragowar duka kannensu ne. a mazan akwai wadanda ba su kai ga yin auren fari ba suna karatu, sun biyo Ishaq da Mansour. Amma a nan jami’ar Abdou-moumoun babbar jami’ar kasar Nijar.
Ranar ta zamo wata ranar reunion ta iyalin RAAZEE. Matan ma da ke gidan aure duk sun zo wajen Yayan nasu da suka dade ba su gani ba, da kyawawan ‘ya’yansa wadanda suka dauko gida a kamanninsa.
Da daddare bayan kowa ya koma gidansa dakin Inna Kasisi ya koma. Ya ce, shi ba abincin wanda zai ci sai nata. Murmushi ta yi da ta tuna wani abu, ya fi kowa son girkinta. Har satar dumame yake mata tana barci, in kuma Mansour ya cinye masa abinci kafin ya dawo yana cin uban duka. Bai sani ba tun tafiyarsa dakin Malam ta shiga kicin ta shirya masa lafiyayyen abincin abzinawa na asali. Ya ci ya yi hani’an kamar mai yin cin biyan bashi.
Washegari ya gaya wa Yayansa Uncle Oussama yana so zai je Tessoua da Zinder son samu har Arlit ya kai yara su ga asalinsa da dangin Inna da ke can, da na Malam. Uncle Oussama ya bada mota Hilux da suke shiga sahara da ita, da kuma dansa Hamoud ya tuka su, ya fi kowa iya tukin mota a gidan, kuma ya saba shiga garuruwa da sahara tare da Malam.
Tun suna tafe kan kwalta har ta soma bacewa ganinsu. Tafiya ce suke ta yi cikin rairayin sahara. Aalimah na kallon yanki da bigire na tsatson mahaifinta tana jin wani shauki a zuciyarta. Tafiya ce mai dadi da ta sanya nishadi a zukatansu. Ga guzurin abinciccika kala-kala a warmers da ababen sha masu sanyi a coolers Inna Kasisi ta yo musu. Duk wanda ya ji yunwa zai bude ya diba ya ci ya sha. Tafiya aka ce yankin azaba, kuma mabudin ilmi. Tsananin ranar kasar Nijar da zafin rairayin sahara ya sanya ita kanta A.C din motar ta daina bada wani sanyi mai karfi. Ba abin da Aalimah ke so a wannan tafiya irin kallon rakuma da makiyayansu, Daddy na ba su labarin kuruciyarsu da yadda suke taya mahaifinsu kiwon nashi rakuman a Tessoua, garin da za su je.
Tafiyar awanni masu yawa ta kawo su birnin Tessoua.Tessoua na daya daga cikin manyan birane goma da kasar Niger ke ji da su. Hamoud ya dauke kan motar ya shiga unguwar da za su, har kofar wani gidan laka mai cike da yawan dabbobi da almajirai fal! A kofar gidan Mazaje ne suna daukar karatu tare da wani dattijo. Wannan shi ne ainahin gidan kakannin su Daddy, wato gidan iyayen Malam Raazee. Dattijon da ke bada karatun shi ke amsa sunan Malam Yahyya, kani yake ga Malam, shi ke zaune a gidan yanzu da iyalansa, sai sauran ‘yan uwan Malam da iyalansu duk a gidan suke kasancewarsa babban gida na gado.
Sun samu kyakkyawar tarba daga jama’ar gidan, abinci kala-kala na abzin, rago guda aka gashe musu don Malam Yahya ya san da zuwansu. Har gonar kiwon kakansu an raka su. Su Basma ‘yan Massachusetts yau an yi kwanan gadon alawayyo. Sauro ya ci rabonsa ya more. Sun ga dangi-dangi sun gansu. Washegari da safe Hamoud ya cika tankin motarsu da mai tatul suka kama hanyar Zinder.
Tafiyar sai ta zame musu tamkar ta yawon bude ido, ga Hamoud da ke yi musu bayanin ko’ina. Basma da Khaleesat, sai suka bude wayoyinsu suka shiga recording abubuwan da suka burge su. Zinder babban gari ne, kuma jiha mai tarin al’umma masu ethnic group daban-daban.
A gidan iyayen Inna Kasisi suka sauka, nan ma an musu tarba ta musamman duk da ba su san da zuwansu ba. Daddy ya bi ‘yan uwa lungu-lungu ya yi musu alheri mai yawa, kamar yadda ya yi a Tessoua. Kwana biyu suka yi harama suka dauki hanyar Arlit. Awanni masu yawa a tsakani suka isa. Arlit nan ne tushen su Inna Bintou kishiyar uwa, wadda ta zame musu babu maraba da uwa mahaifiya. Ta ba su kulawar da ba su samu daga mahaifiyarsu ba, don haka tana da matsayi sosai a wurin ‘ya’yan Inna kasisi. Nan ma Daddy ya yi alheri sosai, don duka dangin nasu tun daga na Tessoua, na Zinder har nan na Arlit suna cikin yanayin rayuwa, abin sai godiyar Allah. Daddy yana shan mamaki in yana jin sunan Mu’azzam a bakin danginshi sosai, ba wanda bai sanshi ba, ba wanda ba ya yi masa addu’ar alheri saboda taimakon da yake musu, wanda Daddyn ba shi da masaniya sam. Jinjina kai yake yana sanya mishi albarka cikin zuciyarsa.
Sun baro garuruwan bayan Hilux dinsu cike da tsarabobi kala-kala na abubuwan amfani, irin nasu. Da suka dawo Niamey ma ba su huta ba, zagaye suke na gidajen ‘yan uwa.
A can kasar America kuma Abulkhair ya kira wayar Aalimah a karshen satin kamar yadda ya saba, inda gidan wayar Verizon wareless suka tabbatar masa ba’a amfani da layin, ya kira na Basma shi ma haka, sannan na Khaleesat, shi din ma dai babu. Tsoro da fargaba har ma da mamaki suka kama shi, musamman da ya gwada na Daddy shi ma haka. Wuninsa guda yana abu daya, amma ya kasa samun kowannensu. A karshe ya gwada na Mummy. Cikin sa’a sai ya same ta. Ya tambaye ta ko me ya samu wayoyin Daddy da na su Basma ya kasa samunsu? Nan take gaya masa ai suna Nijar yau satinsu daya. Ya ce ta ba sh lambar da ta ke magana da su.
Tsaki ta yi, ta ce, ita tunda suka tafi ba su yi waya ba, ba ta da lokacinsu. Ya san halin Mamanshi sarai in ya ci gaba da damunta, za su yi ta ba dadi, dole ya hakura, a kalla hankalinsa ya kwanta tunda lafiyarsu kalau. Ya ci gaba da rubuta jarrabawarsa cikin nutsuwa. Sai dai fa Aalimah na ciki kowanne bugun numfashinsa, tafiyar tasu ta tabbatar masa Daddy (takes the first step) ga gyaran rayuwarsa da iyaye da ‘yan uwansa.
Ana saura kwana uku su tafi Inna Kasisi ta kira manyan ‘ya’yanta da na Bintou maza, da shi Daddyn a babban falon Malam Raazee, shi ma Malam din yana zaune. Cewa ta yi Malam ya bude taron da addu’a, akwai damuwa a fuskar Daddy Ishaq don har zuwa lokacin Innar ba ta gama sake masa sosai ba. Kuka Inna Kasisi ta saka wani abu da ta dade ba ta yi shi ba, mace ce mai taurin zuciya kwarai da nuna ba ta da damuwa a kan komai, ko da tana da damuwar. Hankalin manyan ‘ya’yanta ciki har da Daddy ya yi matukar tashi. Lallashinta suka shiga yi suna rokon ta fada musu damuwarta, sun yi alkawarin magance mata ita muddin ba ta fi karfinsu ba. Sai da ta yi mai isarta, sannan ta ce, ba ta yarda Ishaq ya koma Amurka ba, ko dai ya kara aure ya bar matar a nan tare da su, shi ya koma din inyaso ya dinga zuwa in ya samu sarari, ko ya baro Amurka bakidaya ya zo ya zauna cikin ‘yan uwansa tare da iyalinsa.
Zufa ce kawai ta lullube Daddy, saboda cikin zabin nata duka babu mai sauki. He has a life where he live, a career, a family and everything. Ko zai baro Amurka ba lokaci daya ba. Zabinta na biyu kuma karin aure wani karin nauyi ne a gare shi da bai san yadda zai yi ya dinga sauke shi ba.
Bai ma taba hasaso wa kanshi irin wannan rayuwar ba (polygamy), duk da ita ya taso ya tarar a gidansu. Shirunsa ya sanya kowa da ke dakin ma ya yi shiru, ita kuma Inna ta ci gaba da sharbe. Malam ya yi gyaran murya don katse shirun, ya ce,
“To Ishaqu ka ji bukatar mahaifiyarka a kanka, wannan karon ina bayanta, kullum na kasance cikin bin ra’ayinku in dai bai saba wa addini ba, ina hana ta nata hakkin na uwa. Ka kara aure matar ta zauna da mu, ko ka dawo gida�.
Da kyar Daddy ya iya hadiyar miyau, sannan ya muskuta, “Malam da Inna na ji batunku. Da man kowanne bakon haure a kasashen ketare dole watarana zai dawo gida. Ina da wannan niyyar ko Inna ba ta furta ba, amma ba zai yiwu a lokaci daya ba. Duka yaran karatu suke yi ba su gama ba, Mu’azzam ne kadai ya tsaya da kafafunsa.
Ni kuma sai ya kasance ina da abin yi a nan din kafin in dawo, don ba zai yiwu in zo in zame muku lalura ba. Magana ce ta WATARANA da babu wanda ya san wace rana ce. Maganar karin aure kuma Inna ni yanzu tsofai-tsofai da ni wane aure zan kara?
Gidana babu ko dakin ajiye mace, in kuma na ce a nan zan ajiye ta yanayin aikina ba zai bari in dinga zuwa akai-akai ba, zai zama akwai zalunci a ciki ta fannin matar. Inna ko za ki fadi wata alfarmar in yi miki bayan wannan?� Ya fada cikin taushin murya mai cike da ladabi da kwantar da kai, hadi da lallashi.
Amma budar bakin Inna kasisi sai cewa ta yi, ita ta riga ta gama magana, har ta tanadar masa matar, ta ji ta yarda ba zai iya dawowa Niamey yanzu ba, amma dole ya auri GUMSU!
Wata sabuwa inji ‘yan caca, shuka tsakiyar rani!
6/28/21, 7:33 AM - Buhainat: &&&&&&&&&&
****************************************************************************
17
Gumsu kanwa ce ga Inna Bintou, ba’abziniyar Arlit ce, mijinta sojan sama ne, ya rasu a wani hadarin jirgin sama da ya faru a kasar Kenya a shekarar da ta gabata. Ya barta da yara biyu. A hannunshi ta samu ta yi karatun boko mai zurfi a France inda aka tura shi yin wani course na tsawon shekaru uku, inda ta samu ta hada digiri na farko a fannin pastry art. Sun yi aure da uban ‘ya’yanta bayan kammala sakandirenta. Zamansu a birnin Paris ya sanya mata sha’awar shiga makaranta. Ashe da rabon zai amfane ta a gaba. (Aah toh zama da Mummy ai sai wanda ya je makaranta)
Cikin ‘yan uwansa kaf! Wadanda ya girma da wadanda suka girme shi babu wanda ya goyi bayansa kan kin bin umarnin Inna, ashe cikinsu babu wanda ba shi da cikin Zulaiha kan yadda ta raba su da dan uwansu. Ganin ba shi da zabi in dai yana so ya yi rabuwar lafiya da Inna ban da amince wa bukatarta ya ce ya amince da maganar auren, amma zai je ya shirya sai ya dawo a yi maganar auren. Inna ta yi tsalle gefe ta ce sam! Ba ta amince ba. Kafin ya tsallake boarder din Nijar zuwa wata, za a yi auren nan.
Daddy ba shi da zabi ban da amincewa don son gamawa da iyaye lafiya. Amma fa yana hango kanshi da mata biyu, ko ya ya zai yi da su? Ya tuno kishi irin na Mummy Zulaiha da ko kyakkyawar gaisuwa ba ta bari yayi da mata, yau ita za a yi wa kishiya? Sai kuma yaji wani murmushi ya subuce mishi. Watakila sanadiyyar hakan ya yi silar daidaituwar halayenta masu ci masa tuwo a kwarya, musamman aikin bankinta wanda ya sanya kwata-kwata ba ta da lokacinshi balle na ‘ya’yanta, sai ko a karshen mako kadai.
Sai da ya daga booking dinsu zuwa wani satin, saboda maganar auren.
Inna ta so ya fara zuwa su daidaita da juna kafin daurin auren, ya ce shi ba shi da bukatar hakan, ba sai ya ganta ba, in dai ta yi mata (Innar) ta kuma yarda da tarbiyyarta, to a yi. Murmushi Inna ta yi tana fadi cikin ranta, za ka zo da bayani yaro. Matan abzinawa ka ke jin labari.
Su Uncle Oussama sun tafi har Arlit sun karba wa dan uwansu Ishaq auren Gumsu. Da sadakin manyan rakuma goma, sun kuma dauko ta sun taho da ita Niamey.
Duk abin nan da ake, Aalimah da su Basma ba su san wainar da ake toyawa ba. Sai zuwan amarya Gumsu dakin Inna Kasisi tare da matan Uncle Edrissa, Fatsume da Fattu. Gidan ya soma cika da matan ‘ya’yan gidan sun zo karbar amarya. Abinci na musamman Inna Bintou da Inna Kasisi suka shirya wa amarya da ‘yan uwanta da suka rako ta, kodayake abin nasu duk na gida ne, dangin Inna Bintou ne wadanda duk familyn an sansu.
Aalimah da Basma na dakin ‘yammatan gidan, Rumana kanwar Balkisa na yi musu kalba kanana ta tafiya, ba su san an daga tafiyar ba sam. Balkissa ta shigo da gudu kamar an jefo ta, tana fadin, ‘Amaryar Oncle Ishaq ta zo�. Cikin harshen Faransa.
“Amarya?� Su duka biyun suka tambaya a tare with astonishing tone. Balkissa da Rumana ma har suna hada baki wajen ba su amsa, “Au? Ba ku san Baban Basma ya yi amarya ba? Gumsu kanwar Inna Bintou?�
A tare Basma da Aalimah suka mike tsaye, Basma cike da tsoro, mamaki da firgita amma ita Aalimah ba ta san a wane yanayi ta karbi labarin ba. Khaleesat ta fado dakin daga yawon da ta tafi tana fadin,
“Gidan nan yau a cike yake da mata kamar gidan biki�.
“Bikin Babanki ake�. In ji Rumana.
“Wanne Baban nawa? Kin san Babannin gidan nan yawa gare su�.
“Wanda ya haife ki�. In ji Balkissa.
Khaleesat ta zame ta zauna a kan kafafunta bakinta na marmar yana fadin,
“In wasa ki ke ina rokonki ki bari�.
Rantsuwa Balkissa ta hau yi tana gaya musu, ai an kwana biyu da yin maganar, ta ji Babanta yana gaya wa Mamanta ta dauka ma sun sani.
Kwasa suka yi dukkansu da gudu suka yi sassan matan gidan don ganewa idanunsu. Ya kuma tabbata gare su; Daddy ya kara aure, sun kuma yi nasarar ganin fuskar amaryar, wata tsaleliyar sambaleliyar ba’abziniya, gashinta har duwawunta. Ya sha ado ko ta ina. Tana nannade cikin laffaya.
Jikin Basma ya yi sanyi, ta rasa me ta ke ji a ranta game da al’amarin. Tausayin Mummynta ko taya Daddynta murnar samun wannan hadaddiyar mace? Khaleesat muraran ta nuna kishi tun daga kwayar idanunta har furucinta,
“Da ma Daddy ya kawo mu gidansu ne don mu halacci bikin aurensa shi ya sa bai damu ba da Mummy ta ce ba za ta zo ba?�
Dakin da Daddy Ishaq ya sauka a cikin gidan wanda ciki da falo ne, an yi shi ne don saukar baki, can aka kai amarya Gumsu, bayan ta huta ta yi sallah ta ci abinci.
Khaleesat kayanta ta hau kwasa babu ko ninki tana dannawa a jaka, ita gobe za ta koma America ba zuwa ta yi ta taya Daddy honey moon ba. Basma ta fidda hannu ta kwashe ta da mari, sannan ta ce, “Ki san irin kalaman da za ki dinga furtawa a gare shi, ba sa’anki ba ne, ba abokin wasanki ba ne. Ubanki ne! Yana da damar auren mata uku bayan Mummy, Ubangiji ya lamunce masa�.
Sosai Khaleesat ta saki kuka ta fada jikin Aalimah, yayin da Aalimahn ta rungume ta tana lallashinta. Ita ma nasiha ta shiga yi mata kan ta fidda kanta daga cikin al’amarin kada ta bi bayan kowannensu. Tare ta taso ta gansu, kuma kowannensu yana da hakki a kanta, ta yi masa adalci.
Daddy Ishaq ya shiga dakin amaryarsa Gumsu (Moiram) ya karbi kyakkyawar kyautar da ta yo mishi guzurinta, irin wadda bai taba zaton akwai a diya mace ba. Wayewar garin kuma ya sha albarka daga iyayensa.
Sai da suka kara sati daya a kan sati biyunsu, kwananshi uku tare da amarya, ko sallar jam’i da kyar ka ke ganinshi, ta asubah kuwa bai kara samun ko daya ba, a daki yake yinta tare da matarsa.
Ana i-gobe za su tafi ya tadda Malam da Inna a gefensa a turakarsa suna cin abincin dare ya zauna ya dukar da kai. Malam ya yi ta tsokanarsa, wai sai kyallin goshi yake yi, ga kamshin jikinsa ya karu. Shi dai murmushi yake yi, sannan ya fadi abin da ya kawo shi. Yana so zai tafi da Gumsu tunda ba a kammala gyaran sashin da za ta zauna ba. In ya samu hutun wata shekarar zai dawo da ita, ko ya hado ta ita da Aalimah don ya yi mata alkawarin zuwa Nigeria in ta gama shekararta ta farko.
Hamdala Inna ta rinka yi a zuciyarta, ko banza ta samu ta dinga ganin danta akai-akai, ko wani bangare da ya shafe shi. Ya gaya musu ya yi processing din visa dinta, yana jira ta fito, don haka zai sanya yaran a jirgi su tafi gobe saboda makarantunsu, shi kuma zai jira visar Gumsu su koma tare. Inna ta kara jin dadi a cikin ranta.
Washegari shi da Hamoud suka kai yaran filin jirgin saman Diori Hamani. A kujerar gaba yake Hamoud na tuki. Yana lura da yadda yanayin kowaccensu yake, Khaleesat fuska ba rahma sai cin fushi ta ke. Basma ta zama mara karsashi, wannan surutu da karadin duk babu shi. Yesmin nata fama da choculates da biscuits dinta. Aalimah, tana cikin yanayin da ba za a iya fassarawa ba, sai dai ga duk wanda ya santa da yaran zai fahimci canzawar walwalar yaran ne ya yi affecting mood dinta. Gyaran murya ya yi lokacin da suka shiga receptionna filin jirginsuka zazzauna a kan kujerun jiran saukar jirgi, ya dube su dukkaninsu.
A nitse ya kira sunayensu, kowacce ta amsa. Sannan ya ce Yesmin ta je wajen Hamoud. Ya dawo da hankalinsa gare su, ya soma magana irin ta uba mai cikakken iko a kan ‘ya’yansa.
“Iyayena sun min aure saboda su tabbatar da suna da amfani cikin rayuwata, kuma suna da iko a kaina, kamar yadda na san ina da iko a kanku. Aure sunna ce ta ma’aikin Allah sallallahu alaihi wasallam. Abu ne da ake yinshi ba don son zuciya ba. Na karbi auren da iyayena suka umarce ni da shi da hannu bibbiyu don bin umarnin Allah da ya yi umarni da a yi musu biyayya don samun rabauta duniya da lahira ba don bana son Babarku ba, ko don in tozartata. Don haka bana fatan hakan ya kawo sauyi cikin mu’amalata da ku, har ma da mahaifiyarku. Ruwanku ne ku je ku gaya mata kafin zuwana in yi mata bayani yadda za ta fahimta. Ruwanku ne kuma ku fidda kanku daga ciki tunda da ni da ita kowanne mai hakki ne a kanku. Ruwanku ne ku sauya akalar rayuwarmu zuwa mai kyau ko mara kyau sabida na yi aure don cika sunnar Ma’aiki da son gamawa da iyaye lafiya. Ku tashi ku shiga jirgi, Allah ya yi muku albarka�.
A salube kowacce ta mike ta dau jakarta, don fasinjoji na ta wuce su tun dazu suna shiga jirgi. Aalimah ta kamo Yesmin suka yi sallama da Hamoud. Daddy na tsaye a inda yake hannayenshi zube cikin aljihu, idonsa kyar a kansu. Har sun bi sahun masu shiga jirgin, Basma ta juyo suka hada ido. Murmushi ya yi mata, sai ta saki trolley dinta ta dawo da gudu ta rungume shi, ta sumbaci goshinsa. Ganin haka Khaleesat ma ta dawo ta rungume shi tana hawaye. Tausayinsa ta ji sosai da nadamar abin da ta ke yi da farko. Ta kuma yardar wa zuciyarta Daddy bai zo Niamey don ya yi aure ba, Allah ya rubuto masa auren ne cikin kaddararsa. Babu kuma wanda ya isa ya tsallake kaddararsa, amma ba don ya daina son mahaifiyarsu ba.
******
Jirgin Ethiopian Air ya sauke su a Boston Logan International Airport da misalin karfe goma na dare agogon Massachusetts. Mummy ba ta san da dawowarsu ba a ranar don tsayin lokacin nan babu wanda ya yi magana da ita, daga su har Daddy. Su kansu ba su san dalili ba, don rashin sayen layi na kasar bai isa ya zama dalili ba, abubuwa da yawa sun janye hankalinsu a Nijar, kama daga tafiye-tafiyen da suka yi ta yi, da yadda suke zama busy cikin ‘yan uwa. Ga shi Mummy ba ta yin social media, hada layin ne ya zame musu wahala. Don haka cab suka dauka tun daga airport har kofar gidansu da ke cikin rukunin gidajen Martha’s Vineyard Estate, Mummy ta jima da kwanciya sai jin kararrawar gidan ta yi tana ta faman ruri ba kakkautawa.
Barci fal idanunta ta zo ta bude kofar, sai kawai ta gansu kamar daga sama, sai murmushi suke dukanta da shi. Sai dai wannan hargagin nasu duk babu, Yesmin ce kawai ke mata karadi, ta kuma hahhanga bayansu ba ta hango sanyin idaniyarta ba, ba ta hango tauraron zuciyarta ba, ba ta hango Ishaq dinta ba.
‘Where’s your Dad (ina Babanku)?� Shi ne abin da ta fara tambayarsu, kafin ta bi su da runguma da sumba daya bayan daya. Amma da ta zo kan Aalimah hannunta kawai ta kama, sannan ta ce mata, “Welcome back (sannu da zuwa)�.
Zubewa ta yi a kan gwiwoyinta ta ce, “Mummy ina wuni, ya ya gida, mun same ku lafiya?�
Sosai ta ji zuciyarta ta motsa, ta kai hannu ta daga yarinyar tsaye sannan ta rungume ta. (kyautatawa da ladabi suna canza kiyayya daga zuciyar ma’abocinta, zuwa akasinta- Takori).
Aalimah ta lumshe idonta na lokaci mai tsawo da ta ji ta yau a jikin Mummy Zulaiha. Ji ta yi kamar ABULKHAIR ne ya rungume ta. Kafin ta farfado daga duniyar shaukin Abulkhair da ta tafi a jikin Mamansa, Mummy ta sake ta, sannan ta kama hannunta tare da taya ta da daukan jakarta daya suka shige cikin gidan.
Mummy ta tambaye ta, ya ya ta samu mutanen gida? Nan ta ke gaya mata, “All our stay was in Niamey (Niamey kawai muka je)�.
Ta jinjina kai. Suka ci gaba da hira da sauran ‘ya’yanta. Labarin zuwansu Zinder, Arlit da Tessoua suke ba ta da irin wahalar da suka sha a sahara. Dukkansu kamar an sa zare da allura an dinke musu baki, babu wadda ta yi gangancin faxa mata maganar auren Daddy, ko da da subutar baki ne. Ta tambaye su ina yake? Suka ce akwai abin da ya zaunar da shi, zai taho in ya gama.
Yau Aunty Zulaiha cike ta ke da farin ciki wanda dawowar ‘ya’yanta gare ta shi ne sila. Ba su taba daukar irin tsayin wannan lokacin ba sa tare ba. Kowa ya kasa barci, raba dare akai ana hira. Ta yi musu alkawarin kai su MIAMI RESORT shakatawa sati mai zuwa idan yayansu Abulkhair ya zo hutu.
“Wouldn’t you take us to Las Vegas?� Yesmin ta tambaya tana mai kwanciya a jikinta. Duk da baya sake musu, ba ya shiga sha’aninsu kamar Abulkhair, zuciyar Yesmin tana son Mu’azzam. Duk da suna daukar lokaci mai tsawo ba su ganshi ba ba ta manta shi. Duka Khaleesat ta kai mata, Mummy ta janye ta da sauri,
“Mu je mu yi kaniyarki a Las Vegas?�
Rungume Yesmin Mummy ta yi tana murmushi, “He is not at Las Vegas Yesmin, he went to Bahamas. I promised taking you to him as soon as he is back (ba ya Las Vegas yanzu, ya je Bahamas. Na yi miki alkawarin kai ki wurinsa da zarar ya dawo) in ba ku koma makaranta ba�.
Aalimah upstairs ta haye ta barsu, ta shige dakinsu. Nemo layin wayarta ta yi na gidan wayar Verizon jikinta har rawa yake ta sanya cikin wayarta, she cannot even express how much she missed him, (bazata iya fadin yadda tayi kewarsa ba) kawai ka sanya wa zuciyarka mai karatu cewa, Aalimah ta yi kewar Abulkhair yadda hasashenka ba zai iya bayyanawa ba. Duk da ta yi farin cikin ji daga bakin Mummy cewa, yana nan zuwa sati mai zuwa. Unfortunately, alkawarin da suka daukar wa Daddy ya fado mata, na haramta musu kiran juna a ranakun mako. In ta yi hakan ta ci amanar Daddy…
Da sauri ta yi jifa da wayar a kan gadonsu ta fada bisa lallausan gadon ta nitse cikin (water mattress) dinsa tana maida numfashi dai-dai. Su Basma na shigowa ta rufe idonta kamar mai barci. Barcin ta ke so ya dauke ta don ta huta daga azabtuwa da zuciyarta ke yi da tunanin Abulkhair. Basma ta hango wayarta tsakiyar gado ta dauka ta sanya mata a charging.
Washegari tun asubah da ta yi sallah ta kira Mamanta, Daddynta da Yaya Aboubacarsuka sha hira. Ta ba su labarin zuwansu Niger. A karshen wayarsu kowannensu sai ya ce da ita ta gaida Abulkhair. Kunya ta ji tana kamata, ko dai Abulkhair ya ce musu wani abu ne? Sai kuma ta ce, “Kai ba zai fadi komai ba, tunda Daddy ya ce ya bar masa komai na maganarsu a hannunsa, ba zai yi wannan azarbabin ba�.
Ita kadai ta yi breakfast a gidan don rashin kwanciya da wuri ya sa duk ba su tashi da wuri ba. Kafin ta bar kitchen Easther ta zo suka gaisa ta bar kicin din bayan ta shirya musu karin kumallon a dining. Basma ta tayar don ta shirya, ta ce mata ba za ta iya shiga makaranta ba yau, akwai gajiya mai yawa tattare da ita. Wanka ta shiga ta fito ta shirya tsaf! Ta kira Joseph a waya ya kai ta makaranta. Sun yi karin sati daya a kan hutunsu, don haka ta tadda note mai yawa a wurin Alex da abubuwa masu yawa da suka soma tsere mata. Sai dai tana tunawa da Abulkhair da alkawarin da ta yi masa ba ta kara kebewa da Alex ba. A cikin aji suke magana gaban kowa, Khaleesat da Yesmin su da ma nasu hutun na sati hudu ne. Islamiyya kawai suke zuwa.
6/28/21, 7:33 AM - Buhainat: HAULATU 66
%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%%
A haka satin ya kare musu, tana lissafe da kwanakin. Ranar juma’a wadda ta kama ranar zuwan Abulkhair kasa zaune ta yi ta kasa tsaye. Kwalliya ta yi ta har sau uku tana canzawa. Ba ta da lecture ranar, don haka ta makale a kicin da sunan taya Easther aiki. Nan kuwa masoyinta ta ke son yi wa girkin da zai yi farin ciki da shi. Waina (massa) ta soya masa wadda ta jika shinkafar tun daren jiya, ta markada da safe. Sai miyar ganye wadda ta ji tsokar naman talo-talo (Turkey). Ta dade da sanin Abulkhair na son chips wato soyayyan dankalin Turawa, ta zauna ta fere ta yi masa kyakkyawar suya. Mummy na office, Basma na school, Khaleesat da Yesmin suna Tahfiz dinsu. Gidan daga ita sai Easther, ta yi light make up kamar yadda ta saba, sannan ta zabo wani lallausan swiss lacelemon green mai stones da aka yi wa dinkin gown ta sanya.
Ita da Easther suna shirya abincin a diningaka danna kararrawar kofar gidan. Cewa Easther ta yi ta je ta bude, ita kuma da gaggawa ta gudu upstairs dakinsu. Ba ta san me ya sa ba, kunyarsa ta ke ji yau, kunya sosai, it has been long…har wata uku da rabi without them seeing each other (ba tareda sun ga juna ba)Ba ta san da fuskar da za ta kalle shi ba, ko wace tarba za ta yi masa. Fuskarta ta sanya cikin tafukanta ta zauna a bakin luntsumemen gadonsu.
“Yaa Allah! Grant me the courage�. Shi ne abin da ta furta a hankali.
Ya tambayi Easther da ta shigo masa da jakarsa, “Duk ina mutanen gidan?�
Ta ce da shi babu kowa sai Aalimah. Cikin mamaki ya ce, “Sun dawo? Yaushe? Tana ina?�
Bai kuma tsaya ta ba shi amsar ko guda daya ba, ya shiga hada steps biyu-uku, yana hawa sama.
Sai da ya murdo kofar dakin nasu ya shigo ya yi daidai da dago kanta da ta yi ta dubi saitin kofar. Kirjinta na harbawa.
Yana nan yadda yake, handsome Abulkhair. Well dressed in a Nordstromshirt and jeans trouser, masu kalar baki da fari, mai yawan gargasa a jiki, da sumar kai irin na buzayen usul. Ko bakar jakar da yake goye da ita a bayansa bai sauke ba. Sai dai kuma ya yi rama sosai. Kallo daya za ka yi masa ka san cewa ya rame din, duk da physique chest din yana nan ba abin da ya girgiza shi.
Idanunsa suka sauka cikin nata, sun dade suna kallon juna kowannensu yana sakin murmushi kafin ya saki jakar da ke bayansa kasa, ya bude mata hannayensa. Girgiza masa kai ta shiga yi alamar a’ah, ba ta san sanda ya iso gabanta ba har inda ta ke zaune ya zube gwiwoyinsa ya zauna a gabanta, ya zuba mata ido ba ya ko kiftawa. Daga bisani lumshe idanu kowannensu ya yi cikin jin wata irin nutsuwa na sauka a zuciya da gangar jikinsa.
“Kallon ya yi yawa. Babu aure a tsakaninku�. Tunanin da ya shiga kan Aalimah kenan, ta mike tsaye da sauri. Shi ma mikewar ya yi ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallonta a tsanake, ta kara kyau ta cicciko sosai, wanda ke nuna ita kam cikin kwanciyar hankalinta ta ke. Duk wahalar nan da ya yi tsayin sati hudu bai ji ko da muryarta ba, ita ba haka ba ne a tare da ita ba.
Murmushi Aalimah ta yi, “Monsieur…�
“... Don’t dare call me Monsieur again�.Yakatseta. “Na ga abubuwa sabanin yadda na zace su, ni kadai na yi kewarki. Ni kadai na damu da ke…!�
Ya karasa maganar in subdued wato cikin muryar da ke nuna how dissappointed he was. Tare da juya mata baya.
Takowa ta yi a hankali har ta zo dab da shi, sannan ta tsaya. Cikin sanyin murya ta ce,
“Ba haka ba ne. tunda muka je ban…�
“...Ba ki sake tunawa da ni ba, balle halin da rashin ji daga gare ki zai sanya ni. Quite four weeks�. Ya fada yana daga yatsun hannunsa guda hudu, akwai fushi sosai cikin muryarsa.
“Daddy bai ba mu layi ba…�. Ta fada cikin son kare zarginsa na cewa ba ta damu da shi ba.
“In ba ku da layi ba za ki iya siya ba? Ko ba za ki iya roaming naki layin ki yi amfani da shi ba a ko’ina? In duk hakan ba mai yiwuwa ba ce, ba za ki iya aron wayar wani ki kira ni ba?� Wannan karon da fada sosai yake magana.
Abin da Aalimah ta ki jini kenan, tuni idonta ya cicciko da kwallah.
Hakan ya sa Abulkhair sassauta fushinsa, ya juyo yana kallonta. Fahimtar hakan ya ba ta damar iya yin magana cikin kwantaccen sauti.
“Na ji Basma na fada wa Malam Razee cewa jarrabawa ka ke yi, kuma ka yarda da ni ko su Mamanmu ban kira ba har muka je muka dawo. The house is always full and very busy… Mun kuma yi tafiye-tafiye na garuruwa masu nisa cikin sahara inda babu network har mutum sai ya manta ma yana da waya, amma ba don na manta da kai ba, ko ba ka zuciyata. Ina dawowa na yi niyyar kiranka na tuna ba weekend ba ne kada in ha’inci Daddy. Ina tabbatar maka tunaninka na tafiya ne tare da bugun zuciyata. Babu inda zan shiga, ko wani yanayi da zan shiga da zai sa in manta ka ko na kasa tunaka…�
Ba karamin sanyi kalamanta suka yi masa a zuciya ba. Ya manta duk wani bacin rai da ya samu kansa a ciki.
“Then give me a hug… don in tabbatar ba dadin baki kika yimin don in yarda da ke ba�. Ya fada yana cin magani.
Dariya ta yi, ta ce, “Not now�.
Kwafa ya yi ya fice daga dakin jin shigowar motar Mummy, yana ce da ita,
“Jira ba ya kisa. Da yana kisa da ban kawo yau ba!�.
******
Kamar yadda Mummy ta yi alkawari washegari ta shirya musu tafiya picnic zuwa ‘Miami’.
Ko a kwanaki uku da suka karar tare a Miami Resort, Mummy ba ta fahimci komai tsakanin Abulkhair da Aalimah ba. Suna zaune a gabanta suna chatting da juna da wayoyinsu bata san me suke yi ba. Sannan daki daya ta kama musu dukkansu ita da yaran, Abulkhair na dakinsa shi kadai, sai sun fito bakin beach suke haduwa. Watakila kuma don ba ta da kurillah ne da ta gano yadda suke magana da juna cikin halittar idanunsu. Da ta hango matsananciyar soyayyar da ke kwance cikin idanun kowannensu.Sun shakata yadda suke so. A jirgin Alaska Airlines suka je Miami daga Boston a cikinsa suka dawo.
Da suka sauka a filin jirgin saman Boston Logan, Mummy ta fiddo waya ta kira Joseph. Shi ya zo ya kwashe su zuwa gida.
Tun daga harabar gidan suka ga alamun an canza wa motar Daddy matsugunni. Motar da shi kadai yake hawanta, wato Chevrolet volt. Har suna hada baki yaran da Mamansu wajen tambayar Joseph, “
Daddy ya dawo ne?�
A nan yake gaya musu ai tun washegarin tafiyarsu suka dawo shi da second madam dinsa.
Mummy ba ta wani fahimce shi ba. Cike ta ke da dokin ganin mijin nata abin kaunarta. Amma su sun gane me Joseph ke nufi da second madam, ban da Abulkhair. Jikinsu gabadaya ya yi sanyi, don haka ba su wani fita da sauri ba, Mummy ta riga su isa kofar shiga gidan da kanta ta danna kararrawa kafin su karaso.
Wata kyakkyawar ba’abziniya kamar balarabiya, ita ta bude kofar. Idanunta cikin na Zulaiha. Ba ta fice age mate (sa’ar) Abulkhair, wato ba za ta wuce shekarunsa ba. Mai yawan fara’a da hasken idanu da na hakora. Kallon-kallo suka shiga yi, sai dai kowacce nau’in kallon da ta ke yi wa ‘yar uwarta daban yake da na ‘yar uwarta. Zulaiha kallon ya tashi daga na mamaki ya koma na tsoro, da tunanin aljana ce ta shigo mata gida, don wannan ba ta yi kama da turawa ba. Yayin da Gumsu Moiram, ke kare wa uwargidan Ishaq kallo da son tantance rukunin matan da ta ke ciki don ta san da fuskar da za ta rayu da ita.
Daddy ne ya iso kofar ya katse kallon kudan matan nasa biyu. Shi ma kansa a darare yake, amma ya karfafi kansa ko don ya zama cikakken miji a gidansa ya ce, “Sun dawo ne? Gumsu shige ciki su shigo, ina zuwa�.
Ta wuce ta koma ciki.
Mummy Zulaiha ta kalli Daddy cikin ido, yawu ya kafe a cikin bakinta. Kin shiga ta yi kamar yadda yaran ma suka ja tunga a bayanta. Ta ce, “First, tell me who is she?�
Da sassauci a kan fuskarsa ya ce, “A bakin kofa, a gaban yara ki ke so mu yi magana irin wannan? Ki shigo ciki tukunna�.
“Magana irin wacce?� Ta tambaya cikin danne ko ma wane irin tunani ke son shiga zuciyarta a lokacin. Hannunta kawai ya kamo ya janyo ta cikin falon su Aalimah suka biyo bayansu.
Bai cika hannun Mummy ba (upstair) ya haye da ita don su kauce ma idanun yaransu. Yayin da amarya Gumsu ta wuce dakin da Daddy ya ba ta tun zuwansu, dakin Mu’az na da, kafin ya sama mata matsugunni.
Duk wani bayani irin na nuna concern, wanke kai da kawo dalilai Ishaq Raazee ya yi ga Mummy Zulaiha don ta karbi kaddarar aurensa kamar yadda ya karbe ta, ta yarda bai yi da niyya ba, bai yi don ya tozartata ba, bai yi don ya daina sonta ba. Zulaiha ta ki fahimtar ko guda daya. Wani dan karamin hauka ne ya same ta a wannan lokacin. Ta gaya masa ta bar gidansa kenan, har abada ba zai burge ta ba sai ya auro matan Niger Republic bakidaya sannan za ta amince danginsa ba sa sonta. Ga gidansa nan, ga ‘ya’yansa nan, ya manta ya taba saninta a rayuwarsa.
Su dai su Aalimah suna zaune jigum-jigum kowacce da jakar matafiyanta a gabanta a falon kasa, tun bayan da suka shigo Abulkhair bai zauna gidan ba, ya shiga cikin gari ne tun bayan ya gaisa da amarya Gumsu da bai wan wace ce ba. Ya dai fahimci Daddy ya zo da ita ne daga Niger, sai ganin saukowar Mummy suka yi a sukwane tana hada steps biyu-uku, ta ja jakarta da suka dawo da ita ta yi waje, sai ga Daddy ya biyo bayanta da sauri shi ma. Yesmin ta bi ta da gudu, ya ce Khaleesat kada ta barta ta fita. Ta je ta riko ta tana kuka tana kiran Mummy. Wayarsa ya fiddo ya kira Abulkhair ya ce, “Kana ina?�
Abulkhair ya amsa da cewa, ya dan fita ne amma ga shi nan ma ya shigo kwanar gidan.
Ya ce, “Ka kula da Mamanka, ga ta nan za ta dau mota ta fita. Kada ka barta ta yi tuki. Take care of her�.
Abulkhair ya amsa, “Don’t worry Daddy�.
A take kuma ya shiga hasashen abin da yake faruwa da matar da ya gani daga Nijar.
“This cannot be possible�. Ya fada a fili.
Karawa motar gudu ya yi ya karaso gida, daidai Mummy na sanya jakarta a but din motarta tana rufewa. Ko daidaita parking bai yi ba ya kashe motar ya fito har da gudu ya hada ya bude mazaunin direba ya shige ya rufe. Kofar kusa da shi ta bude ta zauna tana fadin.
“Please go out, tafiya zan yi�.
“Ina so in raka ki ne Mummy�.
“Wannan karon tafiyar ba ta dawowa ba ce, please go to your Dad�. Sai a lokacin ne ta samu hawaye suka zubo mata.
Abulkhair ya ji wani iri a zuciyarsa, tissue din motar ya zara ya shiga tsane mata hawayen fuskarta.
“Mummy kun wuce wannan level din ke da Daddy, don Allah ki koma ku sulhunta kanku albarkacinmu�.
Girgiza kai ta shiga yi tare da fadin, “Ni da Babanku har abada! Kishiya ya yi min a shekarun girmana da furfurarsa da komai. Me zan yi da danginku? Tsakanina da su sai Allah ya isa!�
“Hasashena ya tabbata gaskiya kenan?� Abulkhairi ya fadi a zuciyarsa, “Na fahimta Mummy. Amma yanzu komai zan gaya miki ba za ki fahimce ni ba. Kina bukatar nutsuwa. Yanzu ina zan kai ki?�
Da sauri ta ce, “Las Vegas�.
Murmushi ya yi. A ransa yana fadin, “Wurin sanyin idaniyarta, mai share mata hawaye, mai fada mata ta ji kamar iyayenta. Kai ka ce shi ne uban ita ce ‘yarsa�.
A fili kuma ya ce, “Mummy, ni ma ki so ni yadda ki ke sonsa!�.
Duk halin da Mummy Zulaiha ke ciki sai da maganar Abulkhair ta sa ta murmushi. Anya za ta so wani Da cikin ‘ya’yanta irin son da ta ke yi wa MU’AZZAM?
******
Bayan fitarta da kamo Yesmin da Khaleesat ta yi, Daddy dakin da Gumsu ta ke ya shiga. Kiranta ya yi suka fito tare. ‘Ya’yan na nan zaune yadda suke tun shigowarsu. Cikin yanayi na zugum-zugum sai Yesmin da ke ta kukan an hana ta bin Mummy.
Zama ya yi a kujerar da ke fuskantarsu, Gumsu za ta zauna kusa da Aalimah ya ce, ta dawo kusa da shi ta zauna. A nutse ta bi umarninsa cikin tsananin ladabi. Ya dube su bakidaya, ya ce, “Ga Antinku Moiram na taho da ita. Ina ganin hakan zai fi min sauki a kan na baro ta a can na dinga zarya. Inyaso duk karshen shekara sai mu je hutu. Basma, Aalimah da Khaleesat dukkanku na san masu hankali ne, kuma masu adalci a tsakanin iyayenku. Ban auro Gumsu-Moiram don bana son mahaifiyarku ba, sai don cika sunnar manzo sallallahu alaihi wasallam, da biyayya ga iyayena. Moiram uwarku ce, kuma gaba ta ke da ku, don haka na hore ku da da’a da biyayya a gare ta. Ku bi ta yadda za ku bi mahaifiyarku. Ke kuma Moiram ga amanar ‘ya’yana nan ki zauna da su yadda za ki zauna da wadanda ki ka haifa. Wanda ya yi miki ba daidai ba, ki sanar da ni, balle kuma dai na shaide su dukkansu masu kaunar Daddy ne ba za su taba kin abin da ya kawo ya ce nashi ne ba. Haka ne ko ba haka ne ba?� Ya maida maganar cikin sigar tambaya, ta wani bangaren lallashi.
Basma ce ta fara amsawa da, “Haka ne Daddy. Aunty Gumsu muna miki barka da zuwa cikin family dinmu. Insha Allahu za ki same mu yadda Daddy ya shaide mu�.
Khaleesat ta dan ja fasali kafin ta ce, “Welcome Aunty Moiram�.
Kallo daya za ka yi mata ka san cewa tafiyar mahaifiyarta ta taba ranta. Gab ta ke da fashewa da kuka tana dai daurewa ne.
Aalimah Daddy yake kallo, yana so ita ma ta yi magana. Da farko ba ta yi niyyar cewa komai ba don a ganinta wannan abu ne da ya shafe su su kadai, ita ai ba ‘yar gidan ba ce. Amma ganin kowa ita yake kallo da saurare, sai ta ce,
“Sannu da zuwa Aunty Gumsu. I’m Aalimah�.
Daga nan kowacce ta fadi sunanta. Yesmin ma ta share hawaye jin kowa na fadin suna, ta ce, “Aunty I’m Yesmin, Mummy’s love�.
Sosai ta ba wa kowa dariya. Gumsu ta matso ta janyo ta jikinta ta dora ta a cinyarta, cikin faransanci ta ce, “Ni kuma sunana Aunty Gumsu. Yesmin’s Aunt�.
Yesmin ta girgiza kai cikin rashin yarda, “I’ve my Aunty, her name is Aunty Aalimah�. Ta fada tana nuna mata Aalimah.
Daddy ya ce, “Sun zama su biyu Yesmin, Aunty Aalimah da Aunty Gumsu�.
Cikin hikima Gumsu ke jansu da hira cike da kulawa da nuna kauna. Ba ta iya Hausa ba sai faransanci, abzinanci da turanci, don haka da turancin kadai suke magana da ita. Suna jin faransancin amma sama-sama amma. Tun suna dan jan jiki har suka ware musamman da ta ce kowacce ta je ta canza kaya ta zo ta daura apron su shiga kitchen tare. Abin da kowacce ta ke so shi za ta dafa mata, daga yau sun daina cin abincin mai aiki sai nata, tsakaninsu da mai aiki yanzu share-share da wanke-wanke ne kadai. She has a degree in Pastry-Art (tana da digiri kan girke-girke) kuma a gidansu za ta bude ofis dinta (tana nufin a kicin dinsu). Duk kinsu da shiga kicin kasa musa mata suka yi.
Aalimah ta ji dadin hakan sosai, don ita duk yadda za ta yi da su ba sa yarda. A ganinta da a gida Nigeria suke, duk sun isa aure. In aka aurar da su me za su tabuka a gidan miji?
******
Washegari suka koma makaranta dukkansu, Aunty Moiram kawai ake bari a gida, sai ko Easther in ta zo aiki, da ta gama ta ke tafiya. Abulkhair tunda ya kai Mummy gidan Mu’azzam bai dawo ba. A kwanaki uku da suka biyo baya sabo ne mai tsanani ya shiga tsakaninsu da Auntynsu Gumsu, wadda ke kula da komai nasu tsakani da Allah. Shi kansa Daddy yanzu da wuri yake dawowa gida don ya san in ya dawo zai tadda mai jiransa, abinci lafiyayye sai wanda ya zaba. Tun Gumsu na jin kunyar hawa upstairs turakan Daddy sabida idanun su Basma, har ta gaji ta zubar, inda ta fahimci yaran daban suke da irin wadanda ta sani a Nijar, wadannan masu budadden ido ne, kowa rayuwar ‘yanci yake yi babu takura. Sannan ginin benen ya fi na kasan girma da fadi sosai, a can dakin Mummy Zulaiha yake, na Daddyn da na su Basma. Inda aka batan karami ne, Mu’az ne ya zauna a dakin farkon dawowarsu gidan, kafin ya tafi jami’a a Las Vegas. Daddy ya ce zai kama mata apartment na haya a nan kusa da su, amma ta ce in dai hakan ba zai zama matsala ga Maman su Basma ba ita ta fi so ta zauna tare da su, dakin ya ishe ta, don hade yake da bayan gida, ba ta iya rayuwar kadaici ba, sai dai in zai ba ta yaran bakidaya. Shi ma zai fi son hakan, sai dai ya san Mummy ba za ta taba amincewa da kowanne a ciki ba (ba ta ‘ya’yanta ko zama tare da ita).
Ranar kwana na hudu ya yi musu sallama, ya ce zai bi bayan Mamansu. Abulkhair ne ya yi masa waya kan ya daure ya zo, don sun kasa tankwara ta shi da Mu’azzam, tana shirin barin America.
6/28/21, 7:33 AM - Buhainat: HARUNA TANKO
@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@
Al’amari in dai tsakanin Zulaiha da Ishaq Raazee ne, to dan Adam ka koma gefe kawai ka yi kallo. Ba karamar soyayya ce a tsakaninsu ba, wadda aka gina tun tali-talin kuruciya.
Kwanan Daddy biyu a gidan Mu’az asabar da lahadi ya ya aka yi, ya ya aka yi? Ko su Abulkhair ba su sani ba, sai ga su sun dawo tare su ukun. Shi dai Abulkhair dan kallo ya zama in ya tuna duk irin lallashin duniya da suka kwana uku suna yi wa Mummyn shi da Yayansa Mu’azzam, kan ta yi hakuri ta koma dakinta, ta kau da ido daga auren Daddy. Amma ta ki sauraronsu ta bude wa Mu’azzam wuta ya nema mata visa zuwa kasar da Ishaq ba zai kara sanin tana (existing) ba. Dalilin Abulkhair na kiran Daddyn kenan, wanda da farko ya yi niyyar ba ta sarari har sai ta gaji da zaman gidan Mu’azzam din ta dawo don kanta.
Amma darajar ‘ya’yanta da tunanin da ya yi, kada su ga ya wulakanta musu uwa don ya yi aure ya sa ya sauya niyya ya je din. Shi kadai ya san irin lallashin da ya yi mata har ta sauko. Abin har dariya yake bai wa Abulkhair, yana tuki yana jinsu suna ta muhawara kan ita ba ta yarda Gumsu ta zauna mata a gida ba, shi kuma yana nuna mata tarin alfanun da zaman nata tare da su ke da shi, in kuma ba ta amince ba, to ta ba ta yaran bakidaya tunda ita da ma ba wani zaman gidan ta ke yi ba. Nan ma ta yi tsalle ta dire ta ce ba ta yarda ba. Gumsu ta koma Nijar kawai ta yarda duk shekara ya je. Shi kuma ya ce, wannan rashin adalci ne.
Ya gaji da lallashinta, zai yi abin da ya ga dama. Zai kama wa Gumsu gida kusa da su, amma zai raba yaran biyu ya ba ta rabi, tunda ita ba ta san abin da zai taimake ta ba sabida kishin banza.
Ba tarbiyya ba ce iyaye na magana ‘ya’ya su sa musu baki ba tare da sun yi umarni a gare su da hakan ba, amma da ya ba wa Mummynsu shawarar ta kyale Gumsu ta zauna tare da su, amfani ne mai yawa a gare ta.
*****
Sanda suka iso, yaran ba su dawo daga makaranta ba. Sai Gumsu kadai a kitchen gida ya turnike, ya hautsine da kamshin girkin abzinawa, ga shi ta bi ko’ina na gidan ta turare da turaren wuta mai dadin kamshi a burner. Ta yi musu sannu da zuwa, ta gaida Mummy, amma ko kallonta ba ta yi ba ta haye sama. Abulkhair sai ya ji ba dadi, yanzu ne ya kalli matar sosai, mace mai tarin nutsuwa da kamala. Kyau kuwa ba a magana, ga ta nan irin Aalimahrsa, in Aalimah ta yi shekarunta she will look exactly like her. Ya tambayi kansa kenan duka matan kasar su Daddy za su kasance ababen so? Wani murmushi ya subuce masa, ya ce,
“Aunty Gumsu, I’m Abulkhair. Your second son. Wannan girkin naki mai kamshi za ki zubo min yanzu. I’m very-very hungry�.
Dariya ta yi har fararen hakoranta suka bayyana, haka kawai ta ji saurayin ya shiga ranta. He is very smart and jovial. Ta ce, “Mon pils (Dana) ba za ka jira in shirya tebur mu ci bakidayanmu ba? Kannenka na hanyar dawowa yanzu�.
Ya girgiza kai, “Minti biyar nan gaba in na kara girkin nan naki bai shiga bakina ba, ulcer za ta kama ni�.
Ta yi dariya ta wuce kitchen tana fadin, “Ina kuwa zan so ulcer ta kama min Da? Bani minti biyu Mon pils�.
Kan ya shiga dakinsa ya fito ta shirya masa abincin a tebir. Ya zauna ya nada yana ta santi. A haka su Aalimah suka shigo suka same shi bai kai ga tashi daga tebir din ba.
“Welcome Monsieur Abulkhair�.
Basma da Khaleesa suka hada baki wajen fadi cikin bayyanannen farin ciki.
Yesmin na mai rugawa gare shi, Basma kansa ta tsaya, Khaleesat na gabanshi, Aalimah kuma sai ta shige dakin Gumsu da sauri tun kafin su yi ido biyu.
“Ina ka tafi ne daga dawowarmu Miami muka neme ka muka rasa?�
A gurguje ya yi musu bayanin tafiyarsa Las Vegas, kuma Mummy ta dawo tana sama. Ai ba su gama ji ba suka runtuma saman benen har ana hankade Yesmin a kafar bene. Da ma haka yake so ya mike ya bi bayan Aunty Gumsu a kitchen.
“Aunty, don Allah zan iya shiga dakinki?� Ya fada yana sosa sumar kansa nannadaddiya irin ta Babanshi.
Moiram cikin son fahimtar me zai yi a dakin nata ta ke dubansa, sannan ta ce,
“Mu je in raka ka. Kai da dakin uwarka?� Ta wuce gaba yana binta a baya.
Tana shiga Aalimah na fitowa daga bayi, ta dauro alwalar sallar magriba, kanta babu kallabi ba ta lura da wanda ke bayanta ba ta shiga yi mata magana.
“Aunty Gumsu kin sa min wayar a caji?�
Kalaman bakinta suka makale yayin da ta yi ido biyu da Abulkhair. Wani kallo ya yi mata wanda ya sanya ta komawa bayin. Ta rufo kofa.
Gumsu ta ce, “A’ah? Ya ki ka koma?�
Ta juyo ga Abulkhair, sai ta ga shi ma ya juya zai fita. Ya shigo ne kawai da ma don ya ganta ko ya samu nutsuwa daga kewar ganinta na kwanaki hudun, kuma ya ganta;kanwa ta kar tsami, kwannafi ya kwanta.
“Kai ma ka koma?�
Cikinsu ba wanda ya ba ta amsa ta dai neme su ta rasa. A shekarunta da zurfin iliminta nan da nan ta yi murmushi, ta kuma gano su. Ta kama kugu ta ce, “Inye? To tsakanin ita ko shi wane ne ba dan cikin Daddyn ba? Don in dai don ta kamanni ne dukkaninsu suna kama da juna�.
Ba ta da wanda za ta yi wa wannan tambayar sai Daddyn nasu. Kunyarta da suka ji ya ba ta dariya. Ta tura kofar bandakin tana ce da Aalimah, “To fito ya tafi�.
Hannayenta duka biyu ta sa ta rufe fuskarta. Ba ta so Aunty Moiram ta dago al’amarin nan ba,. Ta so ya yi ta zama lullubabbe kamar yadda yake a idon mafi yawan al’ummar gidan. Ga Moiram da tsokana, tun daga ranar kuwa ta sa su gaba, ba dama su kalli juna sai ta yi musu gyaran murya, don Daddy ya tabbatar mata Aalimah ‘yar dan uwansa ce. Babban burinsa a nan gaba shi ne, hada wannan aure.
Haka a daddafe Abulkhair ya karasa hutunsa ya koma Baton Rouge, babu wani sakewa da ya samu da Aalimah, kullum tana makaranta, kuma Daddy ya hana shi binta makaranta. Duk ya bi ya tsani karatun nasa da nata. Amma kullum Mu’azzam karfafa shi yake yana cewa, ya yi for his sake, ya yi don ya samu abin da zai rike Aalimah, shi ba zai ciyar masa da mata ba.
Mummy Zulaiha ta yi duk iyaka tunaninta, hange iya hange ta rasa yadda za ta yi da auren mijinta da Gumsu. In ma wani tarko ne Kasisi ta dana don maida Danta jikinta, to hakika ya yi babban kamu. Rana dai-daya ne da ba za ta ji Daddy na waya da mahaifansa da ‘yan uwansa ba. Sannan a duk yadda ta dauki Gumsun ta wuce nan, ta dauka irin illiteratematan kasarsu ne ta taka ta yadda ta ga dama, sai ta samu Moiram beyond her imagination. Cikin dan lokaci ta siye zuciyar mijin da ‘ya’yansa da kyawawan dabi’unta da cikin cin abincinsu. Hatta Yesmin yanzu tsakaninsu sai oyoyo in ta dawo daga ofis daga nan za ta sauka kasa wajen Gumsu, ba ta kara ganinta sai ta neme ta.
Ta duba ta ga cewa in ta raba Gumsu da gidan, mijin mada kyar za ta dinga ganinshi kullum, sannan yaran ba za su fasa binta inda ta ke ba, tunda idata hana su Basma ba za ta iya hana shi bata Aalimah ba. Basma kuwa ba mai iya raba ta da Aalimah a halin yanzu sai aure, sai mutuwa.
Don haka dole ta zubar da makaman yakinta na hana Gumsu zaman gidan, ta ce da Daddy ya saki gidan da ya kama za ta zauna da ita. Shi kuma da ma ya fi son hakan. Ta shiga daki ta rufe kanta kamar ta yi hauka. Ta yi kuka, ta yi kuka a karshe ta dangana, ta sallama, ta yi saranda cewa Ishaq ba nata ba ne ita kadai yanzu. Sun mallake shi ne su biyu, ba ta da dukkan karfin iko a kansa. Uwarsa ta murza kambun nata ikon, wanda ta dade tana danne mata. Da ma wai Hausawa suka ce, rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya. Ya kamata ta canza hali tun wankin hula bai kai ta dare ba. Tunda tarin ‘ya’yan da ta haifa da tsayin girman kafadunsu bai hana iyayensa yi mata kishiya ba, babu abin da ba zai iya hanawa a gaba ba. Wani abu na karshe da ta tabbatar zuciyarta da rayuwarta ba za su iya dauka ba (rabuwa da Ishaq Raazee).
To amma ta wacce hanya? Ta wacce hanya za ta bi ta gyara halin nata wanda ita a kan karan-kanta ta san ba mai kyau ba ne? Halin dan Adam yana iya canzawa ne? An halicce mu ne da halinmu; the good, the bad and the ugly. Ita ta san nata halin is not good, neither bad, but ugly mace mai raba mutum da iyayensa da ‘yan uwansa wadanda aljannarsa ke karkashin duga-dugansu ya ya sunanta? Ta kasance mai son kanta da yawa. Ta rayu tana gaya wa ‘ya’yanta dangin ubansu ba sa sonta, idan har za ta yi adalci me suka yi mata na rashin so? Ta zauna da su na lokaci mai tsawo ba su taba yi mata wani abu na nuna kiyayya ba, ita ce ma ta ke musu mugun hali.
Sosai Mummy Zulaiha ta soma kuka mai cakude da nadama da ta tuna tsayin zamanta a America ba ta taba kiran Inna Kasisi ta gaishe ta ba, ko da a waya, matsayinta na wadda ta haifa mata mijin da ta ke tinkaho da shi. Ta shiga lalube cikin zuciyarta, iyayen Ishaq da ‘yan uwansa ne suke kinta, ko dai ita ke kinsu?
Kukanta ya tsananta ne da ta tuna cewa ba ta da wata hanya da za ta gyara wannan gingimemen kuskuren nata a yanzu ba tare da an fassara shi da auren Gumsu ba, ba tare da an yi tunanin wata makarkashiya ce a zuciyarta ba sabida Gumsu-Moiram.
Yau ta yi nadamar rashin amini, kin mutanenta bai tsaya a kan iyayen Ishaq kawai ba har nata dangin babu wanda ta ja a jiki. Ba ta da kawa ko aminiya tunda mahaifiyarta ta rasu a shekarar baya.
Shi ne kadai amini, abokin shawara, mai ba ta kyakkyawar shawara duk da yana da masaniyar ba za ta dauka ba, abin da ranta ya kwanta da shi, to shi ta ke yi. Amma har kwanan gobe bai bar gaya mata gaskiya a kan yadda ta ke mu’amala da kowa ba, musamman dangin mahaifinsa. Ya taba gaya mata, Inna Kasisi ta taba ce da shi; Ban san me na yi uwarka ta ke gaba da niba. “Mummy why?�
Wayarta ta janyo hannunta na rawa ta kira shi. Shigarsa ofishinsa kenan da sanyin safiyar litinin. Kiran nasa a daidai wannan lokaci ba daidai bane. Don haka ya rufe kansa a tankareren ofishin sa wanda ke cikin kamfanin man fetur na ChevronCorporationreshen jihar Las Vegas ya amsa kiran mahaifiyarsa with utmost respect.
“Mu’az, ina cikin wani hali. Ta kare min. Komai ya kare mini, ga kishiya ga mugun hali. Ka yi hakuri na san ba ka da lafiya, amma kullum cikin kara maka damuwa nake da matsalolina wadanda kullum ni nake janyo wa kaina su…�. Ta saka kuka.
Zama ya yi a lallausar kujerarsa baka wuluk! Ya yi loosing tie din wuyansa. Fahimta yake tattarowa ya sanya wa kalaman Mummy, don ya gane inda matsalar yau kuma ta sa gaba,she is always in trouble with her husband, kuma in ya ba ta shawarar ba ta dauka. Wannan baya hana gobe ta sake neman ya bata shawarar. Wannan ba ya hanawa gobe ta kwaso sabuwar matsalarta ta kawo masa. Yana jin dadin yadda ta maida shi aminin ba ta kama gurbatattun kawayen zamani ba.
Duk da in an dubi amintar tasu ta tsakanin Da da mahaifi ce, tana gaya masa ne don ta ji saukin damuwarta ba don ta yi amfani da abin da zai shawarce ta ba. Amma yau ji ta ke ko me Mu’azzam ya ce ta yi, za ta yi ko ba ta so, don ta zauna lafiya ta dawo da martabarta a idanun mijinta.
“Mummy me ya faru?�
Ya tambaya da kwantacciyar murya cikin tattausan turanci, wanda ya kama harshensa fiye da kowanne yare, sabida rashin abokin yin wani yaren bayan shi. In ka ji yana Hausa ko French, to ya je Nijar ne, ko yana magana da Monsour Razee, kanin mahaifinsa mai matsayin uba da aboki.
Ta sassauta kukanta, ta gaya masa duk halin da ta ke ciki bayan sun dawo. Halayen Gumsu da yadda Daddy yake martaba ta. Ta ce, ba wai ya sauya mata ba ne, amma ta lura ba ta da martaba da tasiri mai sosai a zuciyarsa, yanzu ya fi muhimmanta ‘ya’yansa da Gumsu. Ta gaya masa ta gane dukkan halayenta ba masu kyau ba ne a al’adar Malam Bahaushe.
Tana so ta gyara ta rasa hanya. Ba ta so a alakanta canzawarta da wanzuwar Gumsu. Tana so ta gyara tsakaninta da Inna Kasisi da Malam Raazee. Tana matukar nadamar watsar da su din da ta yi da rashin daukarsu da daraja. Ko ba a fada mata ba ta san halinta ne ya sanya Inna Kasisi tursasa wa Daddy yin aure. Ya ya za ta yi ta dawo da kyakkyawar alaka ta mutuntawa da girmamawa a tsakaninsu???�
Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee, komawa ya yi da bayansa ya jingina cikin kujerarsa yana jero hamdala a zuciyarsa.. At last, ta dawo kan kyakkyawar turba irin wadda yake mata addu’a kullum. Ta fahimci ita ce at fault ba kakanninsa ba. They hold nothing bad against her(ba su da wani mummunan kudiri a kanta).
“It’s o.k Mum, ki kwantar da hankalinki, na fahimce ki. Ba sai kin yi wani reaction da zai sa su gane kina so ki canza din ba, zuciyarki kawai za ki canza ki warware duk wani kullaci da ke cikinta, da tunanin ba sa kaunarki. Wadannan mutanen are very busy with their family life babu kowa a gabansu sai yadda za su kula da ‘ya’ya da jikokinsu. Ki mu’amalanci Daddy da kyakkyawar mu’amala irin wadda ki ka ga matar tasa na yi. Ki daina daukan kanki sama da shi. Ki ba shi cikakken iko a gidansa irin wanda addininmu ya ba shi. Idan ya yi umarni ki daina ketarewa, ki nuna masa ke abin ikonsa ce, sai yadda ya yi da ke. Ki saki zuciyarki da matar idan ba mai fitina ba ce, ki dauke ta kanwarki.
Malam Raazee da Inna ki bar lamarinsu a hannuna, ba su dauke ki yadda ke ki ka dauke su ba. Nan da sati biyu ma zan dauki annual leave zan je Nijar. Mummy zan gyara komai a tsakaninku�.
Mummy Zulaiha ta share hawayenta. Tambayar kanta ta shiga yi, me ta yi wa Ubangiji da ta cancanci samun ‘ya’ya irin Mu’azzam da Abulkhairi? Ko sallar farillarta ba ta ba ta hakkokinta yadda ya kamata sabida aikin banki, sai ta hada uku lokaci daya. Wani kukan ne ya zo mata da ta tuno halin da Mu’azzam ke ciki duk a kan sakaci da addininta. Babu ranar aure! Ba za ta dauki ‘ya’yansa ba? Kukanta ya karu har ya bai wa Mu’azzam tsoro. Bai ga abin kuka ba cikin kalamansa.
“Mu’azzam, ka yafe min…� Kawai ta ke cewa, ta fada ya kai sau uku.
Ya ce, “Mummy, laifin da ki ka yi min tun kafin ki haife ni, da wanda ki ka yi min daga sanda ki ka haife ni zuwa yau, da wanda za ki yi min shekaru dari masu zuwa in muna raye na yafe miki. Rokona gareki ki sa min albarka!�.
Mummy Zulaiha kasa ci gaba da rike wayar ta yi, ta sake ta a kasa ta rushe da kuka.
Ko dai irin auren baya za ta kara yi wa Mu’azzam, in ya so komai ta fanjama-fanjam???
******
Cikin sati guda kowa a gidan ya lura Mummy ta canza, ta zama saliha, ta aje izza, ta zama wata irin nutsattsiya, kullum sallah za ka taddata tana yi, ko alkur’ani a hannunta tana tilawa. Da ta dawo ofis ta ci abincin da Gumsu ce ke dafawa yanzu, za ta yi alwala ta shige daki. Ba ta son hayaniya sam, in a weekend ne ita ta ke yin girki gabadaya, tun daga daren Friday har daren Sunday. Ta daina kyarar Gumsu, ko kallon banza ba ta mata kamar farkon zuwanta.
Gane hakan da Gumsu ta yi sai ta kara zage damtse wajen girmamata. Ta ce ta bar mata breakfast din ranar litinin da ta ke takura kanta ta yi, ganin tana makara. Girkin kwana uku-uku suke yi. Canzawar Mummy Zulaiha ba ita kadai ya shafa ba, ya shafi walwalar gidan bakidaya, yaran sun sake sosai maimakon da ko magana za su yi da Gumsu suna kauce wa idon Mummy, yanzu kuwa ita da kanta tana kula Gumsun, har dakinta tana shiga, wanda Daddy ya yi furnishing dinsa ya yi kyau sosai. Ita ma Mummyn ya ce zai canza mata ta ce ba ta bukata, ba abin da dakinta ya yi. Shi da kansa ya lura Zulaiha ta canja, wata sabuwar Zulaiha ce wannan ba wadda ya dade da sani ba.
Ba karamin jin dadi da kwanciyar hankali hakan ya haifar masa ba. Har wata ‘yar kiba ya yi a dan tsukin. Gidan Ishaq Raazee a garin Boston ya koma wani sansani na zaman lafiya da fahimtar juna. A gefe soyayyar Aalimah da Abulkhair na kara gawurta. Duk da a waya kawai suke tare da juna.
A wannan satin su Aalimah suka samu hutun karshen shekara, maimakon yadda Daddy ya tsara da farko, cewa ita da Gumsu za su zo, sai ya hado har da Basma. Za su yi sati biyu a Nijar su wuce Nigeria gidan su Aalimah su karasa hutunsu.
Murnar zuwansu a wurin al’ummar gidan ba a magana, kada Inna Kasisi ta ji labari. A dakinta Gumsu ta sauka maimakon na yayarta Bintou.
Inna Bintou na ta mata tsiya wai ta zabi suruka ta barta. Kan ka ce me ye wannan? Gidan ya cika da ‘yammatan family din. Su Balkissa da Roumana mutanen Aalimah. Aka shiga yawo gida-gida gaida dangi. Kwanansu uku a Niamey suka wayi gari cikin shirin tafiya Arlit, za su raka Gumsu ganin gida. Wannan karon ma Hamoud ne ya kai su, sun kwana biyu a can suka wuce birnin Agadez gidan su tsohon mijin Gumsu, ganin ‘ya’yanta, wadanda ke hannun kakanninsu.
Aalimah sai da ta yi hawaye lokacin da ‘ya’yan Gumsu, Adizatou da Jamilatou suka rungume mahaifiyarsu suna kukan ba za su kara yarda ta tafi ta barsu ba. Da ‘yar shekara takwas da ‘yar shekara shidda. Duk kayan da ta sayo musu sun ce ba sa so ita suke so su bi, Basma kasa jurewa ta yi sai da ta gaya wa Daddy a waya. A daren ranar ya kira Gumsu ya ce, idan kakannin yaran za su yarda su taho tare da su, zai yi musu visa. Kememe dattijan sun ki, sun ce su kadai gare su da za su dinga tuna musu dansu Jibreel suna yi masa addu’a, Gumsu ta yi hakuri.
Yaran na kuka su Aalimah na yi suka bar Agadez a washegari. Gumsu ta yi dauriya sosai.
Soyayyar Gumsu da ‘ya’yanta ita ta sa Aalimah kasa cika sati biyu a Nijar. Kwanansu goma hankalinta ya yi gun nata iyayen, da yau shekara daya da kwana goma rabonta da su. Yayansu Hamoud ya sako su a jirgi mai tasowa daga Niamey zuwa Kano, Nigeria.
6/28/21, 7:33 AM - Buhainat: ADAMU DANKOLI
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
£££££££££££££££££££
******
Garin Kanon-Dabo, bai canza wa Aalimah da komai ba. Sai karin tsayin gine-gine kawai. Sun tadda Aboubacar ya zo daukansu don tun tasowarsu Hamoud ya gaya masa. karon farko wani miracle ne ya afku tun a filin jirgin saman Malam Aminu Kano. Basma ta kalli Aboubacar Yayan Aalimah, ma’aikacin bankin GT a halin yanzu, ta kara kallonsa ba ta iya kara yi masa kallo na uku ba, sabida tsanantar bugun zuciya a gare ta.
Suna tafe a sabuwar motar Aboubacar kirar Honda Accord da bai fi watanni biyu da sayenta ba a hanyarsu ta zuwa gida, Aalimah nata yi masa karadi, amma hankalinsa ba ya kanta. Basma yake satar kallo ta madubi, wadda duk kaudi irin nata ta ji yau ta kama kanta. Maimakon Aboubacar ya dauki hanyar B.U.K Road don isa ga gidansu wanda ke cikin rukunin gidajen malamai na sabuwar jami’ar Bayero sai ta ga ya dauke kan motar ya yi Nassarawa, billa can, billa nan sai ga su a kebantacciyar unguwar Sultan Road.
Aalimah ta ce, “Yaya Aboubacar ina za mu je ne?�
Bai juyo ya kalle ta ba ya amsa, “Gida�.
Daidai lokacin da ya sanya hancin motar a gate din wani kyakkyawan gida, wanda da ganinsa ka san sabon gini ne. Ba ta gama wannan mamakin ba ta hango fitowar kannenta a guje. Sultana a gaba, Suhaima biye da ita, Sabrina a bayansu. Mama ma ta kasa hakurin shigowar Aalimah, fitowa ta yi kofar shiga falon sai murmushi ta ke yi. Kasa jiran Aboubacar ya gama parking, Aalimah ta yi ta balle murfin motar ta fice saura kadan ta fadi. Tun daga nesa ta bude dukkan hannuwanta su Sultana suka shiga bakidayansu ta rungume su. Daga bayan wuyansu ta hango Mama sai kallonta ta ke tana murmushi. A kokarin mikewa ta kusa faduwa, sai da Basma ta rike ta ta mikar da ita. Ta karasa da gudu ta rungume Mamanta. Maman ta rike ta sosai a jikinta tana fadin, “Aalimah ta! Sannu da zuwa�.
Aboubacar ya karaso dauke da jakunkunansu, sai fada yake yi wa Aalimah, wai sai ka ce yau ta taba ganinsu. Shi ai ba ta yi masa irin wannan tarbar ba. Ga bakuwa ta kyale kamar ta manta da ita. Wannan karon ne Basma ta yi magana tana satar kallonsa komai da yake yi burge ta yake, very gentle da shi.
“Ni ba bakuwa ba ce�.
Ya juyo ya dan kalle ta ta saman idonsa, ya ce, “Ke da ki ka zo kasa ya kasa zuwa na farko ya kamata a karrama ki, duk da gidanku ne�.
Murmushi ta yi, Aboubacar ya yi saurin dauke kansa sabida wasu abu masu kama da electrical shocking da suka fito daga cikin murmushinta zuwa idanunsa.
Mama ta saki Aalimah ta kamo hannun Basma ta ja ta suka shige har bedroom dinta su Sultana suka shiga hidimar shirya abinci a dining. Aalimah sai bin gidan ta ke da kallon tsoro da mamaki, don kuwa ta san mahaifinta malamin jami’a ne, bayan wannan ba shi da wata sana’a. A cikinta suke ci suke sha, suke zaune cikin rufin asiri. Ko wata sana’ar ya samu bayan barinta gida bai isa a ce ya tara abin da zai mallaki wannan gidan cikin shekara daya ba. Mama sai ina-ta-ka-saka-ina-ta-ka-aje ta ke yi da Basma, ita kuma babu bakunta sai zuba hira suke da su Sultana, kannen Aalimah sun ba ta sha’awa, ga su nan kusan kai daya sabida bai fi shekaru bibbiyu ne a tsakaninsu ba. Sultana ce babba, shekarunta goma sha biyu, Suhaima goma, Sabrina takwas.
Mama ta tambayi Basma abinci za ta fara ci ko wanka? Ta ce, “Wankan dai Mama. Jikina fa har ya fara bashi�.
Aboubacar ya dago kansa daga kan wayarsa dariya ta kama shi. Ko a jikinta, ta ce, “Mama kada ki so in matso kusa da ke, tun a Nijar ya fara bashi�.
Dariya Mama ta yi ta nuna mata Aboubacar da ya zuba mata ido zaune a kan stool din madubi ta ce,
“Basma Yayanku yana jin ki fa!�
Ta juya da sauri suka yi ido hudu, da gudu ta kwasa ta yi toilet. Ya girgiza kai ya fita yana dariyarta.
A ransa ya ce, “Yar gayu da ke Basma! I’m sure in na matso kamshi zan ji�.
Mama ta kama hannun Aalimah cike da farin ciki, ta ce, “Come and see�.
Gidan suka zagaye tana nuna mata ko’ina. Self content family house wanda da ma mamakinsa ke damun Aalimah. A karshe suka dire a dakin da ke kallon na su Sabrina. Mama ta sa mukulli ta bude, Aalimah ko Mama ba ta fada ba, ta gane dakinta ne. Chinese bed madaidaici, wardrove din dakin ta jikin bango ce, sai madubin gadon da stool na kwalliya. An shimfide dakin da carpet ruwan bula mai duhu, kalar labulen dakin. A gefe teburin karatu ne da na’urar kan tebur (desktop), na’urar sanyaya daki na ta aiki gwanin dadi, kai ka ce iyayen Aalimah ko kuma wanda ya shirya dakin bai da niyyar aurar da ita watarana. RungumeMama ta yi don murna, sannan ta ce, “Shin don Allah Mama wa ya saya wa Daddy gidan nan?�
Mama ta ce, “Abin sirri ne Aalimah, kawai ki yi godiya ga Allah, ki kuma yi wa kowaye addu’ar Allah ya ba shi duk abin da yake so duniya da lahira�.
Basma ta shigo tana fadin, “Mama dakin Aalimah ai ya fi naki kyau�.
Dariya ta yi ta ce, “Kin santa da son blue shi ne Aboubacar ya sa komai blue ba mu dade da dawowa gidan ba�.
Ta ce, “Shi kenan in aka yi mata aure ni sai in dawo. I love the house da mutanen cikinsa�.
“Mutanen gidan ma bakidayansu suna sonki Basma, suna maraba da ke�. In ji Mama.
Aalimah ta harare ta, “Ni ba auren da zan yi, ke dai za a yi wa sai a kawo ki gidan nan din�.
Mama ta fice ta barsu tana fadin, “Duk tare za mu aurar da ku mu huta. Kun zama wasu gandama-gandaman ‘yammata in a nan ne ina za a bari ku kara shekara guda?�
Dariya suka yi dukkansu don a wajen Mummy Zulaiha Basma har gobe ba ta wuce goyo ba, in har za ta iya goya tan.
Sai dare Daddynsu ya dawo su Aalimah suka tadda shi a falonsa. Ya kasa boye jin dadinsa na ganin yadda ‘yarsa Aalimah ta koma. Ya yi maraba da zuwan Basma har fiye da Aalimah. Wannan ya nuna da gaske dan uwan nasa yake da ya ce zai gyara kuskurensa na baya. Nan suka zauna hira bayan sun ci abincin dare tare har Yaya Aboubacar, Basma ce ta fara tashi ta barsu sabida barci da ya soma dibanta.
Aalimah da iyayenta sun raba dare suna hira, labarin zamanta gidan kawunta a America ta ke ba su, wanda duk ciki babu wanda ba alkhairi ba, ko da kuskure da tuntuben harshe ba ta ce Mummy ta taba yi mata rashin kyautawa ba. Sai labarin yanayin karatunta da yadda ta tsinci kanta a matsayin dalibar jami’ar Boston wanda har gobe ta ke gani kamar mafarki. A cikin maganganunta tana ambaton Abulkhair da kyawawan halayensa da yawan kyautayinshi gare ta. Idan ka kalli kwayar idanunta kauna ce zallah. Daddy bai gane komai ba, amma Mama ta sanya wa maganganun Aalimah masu yawa a kan Abulkhair ayar tambaya.
Tambayar da Daddy ya yi wa Aalimah ta dan jefa ta a tunani.
“You praises Abulkhair so much,(kin yabi Aboulkhair da yawa) amma ko sau daya ban ji kin ambaci Dana ba, bayan ya fi shi kirki, ya fi shi son zumunci. Shi Abulkhair bature ne irin Babansa�.
“Wa kenan ka ke nufi Daddy?� Ta tambaya cikin dan yamutsa fuska na rashin fahimta.
“Dana MU’AZZAM!�.
“A ina yake? Ni ban sanshi ba�.
Cikin mamaki Mama da Daddy suka hada baki, “Mu’azzam fa Yayan su Basma, wanda Abulkhair ke bi a haihuwa�.
Tunani Aalimah ta fada don son gano wanda suke nufi, amma iyaka tunaninta bai ba ta ba. Girgiza kai ta yi, “I’ve never saw him (ban taba ganinsa ba)�.
Daddy ya ce, “Mu’azzam din?� A cikin muryarsa akwai mamaki.
Aalimah ta ce, “Ni ko sunansa ban taba ji ba, ban da yanzu a bakinku. To ko shi ne wanda su Basma ke yawan fadin yana wani gari Las Vegas?�.
“An yi haka! A can yake. To amma ko a can yake aiki ya za ki ce ba ya zuwa gidansu?�
“Wallahi Daddy bai taba zuwa ina nan ba, su Mummy din ne ke zuwa inda yake. Mummy tana zuwa sosai. Shi ma Daddyn kwanaki na ji ya je duba shi�.
Da haka suka bar zancen, Mama na fadi cikin ranta,
“Wani abu sai bature. Iyaye ne ke zuwa gaida dansu ba dan ne ke zuwa gaida su ba!�.
Sabanin Mama shi ‘yar hirar nan da ta fito daga bakin Aalimah a kan Mu’azzam a zurfin tunani ta jefa shi. Ishaq ya dade yana boye masa abubuwan da suka shafi Mu’azzam tun daga kan auren katsahan din da suka yi masa shekarun baya, dawowar matar daga America da karewar auren. Tun daga lokacin yake cewa ba shi da lafiya ya dinga sa shi a addu’a bayan shi bai ga wani alamun rashin lafiya tare da shi ba, ko a watanni uku baya ya zo Nigeria. Ya siya masa wannan gidan da yake ciki, ya ce ya bar New site gidan gwamnati ne in ya yi retire zai bukaci gidan kansa gara ya kama gidan tun yanzu shekaru turawa suke yi, me ya hana Mu’azzam aure har yau?
In rabuwa ce ta shiga tsakaninsa da wadda ya aura, me ya hana shi sake aure? Tukunna ma wane rashin lafiya ke damunsa da Baban nasa ke dauka da muhimmanci haka? Har da zai goyi bayansa ya ki yin aure? Ya sa a ransa gobe zai yi wa Yayansa Ishaq Raazee wadannan tambayoyin ko da ba zai amsa masa ba.
Washegari Yaya Aboubacar ya ba su layin wayar Mtn dukkansu. Godiya sosai suka yi, musamman Aalimah, Basma na daga gefensa zaune, Aalimah da Sabrina na gefe tana mata kalba a dogon gashin kanta. Ya sassauta murya yadda su Aalimah ba za su ji ba, ya ce da Basma,
“Sai ki ji dadin kiran saurayinki�.
Da sauri ta dago suka hada ido, ba shiri ta dauke idonta. “Ya Allah!� Basma ta ce a hankali idonta a kasa, “Believe me, I don’t have (ka yarda da ni, ba ni da shi)�.
Aboubacar wani irin sanyi ya ji a ransa, amma nan take zuciyarsa ta shiga cautioning din shi, tana gaya masa ya danne ko ma mene ne yake cin ransa a kan Basma, ta fi karfinshi. An haife ta a U.S, ta girma a can, rayuwarta gaba daya tana can. Shi ba kowa ba ne face karamin ma’aikacin banki. Gidan da suke ciki a yanzu ma Yayanta ne ya saya musu. Ya aure ta ya kai ta ina? Ban da giggiwa irin ta zuciya?
A sanyaye ya tashi ya bar falon. Basma ta bi shi da kallon mamaki da wata irin ragaita cikin kwayar idanunta.
Sosai ya janye jikinsa da zama cikin gidan. A ganinsa ganinta da yake yi ne yake jaza masa komai. Basma kuma rashin ganinsa a cikin gidan sai ya sabbaba mata rashin walwala, duk ta zama wata irin sukuku. Har Aalimah ta soma zargin ko zaman gidansu ne ba ta so. Ko ta kasa jure irin tasu rayuwar? Ko kuma tunanin gida ne ya addabe ta? Da ta ishe ta da tambaya ta ce kome ta ke tuhumarta ta je ta yi ta tuhuma, ta yi abin da za ta yi, amma ta daina damunta da magana. Haushi ya kama Aalimah ta ce, “To ko in dawo da booking dinki jibi ki koma ni na taho daga baya?�
Saura kadan ta mare ta, Aalimah na iya ganin hakan cikin idanunta.
Dariya ta yi, ta ce, “To Basma na kasa gane miki. Kin zo da walwala kwana biyu kin koma min haka�.
A fusace Basma ta ce, “Lokacin da ki ka fara son Monsieur Aboulkhair, na takura miki da tambaya? Ba idanu na sa miki har na gano da kaina ba? Amma ni kin sa ni gaba kin sa min ido, har da sharri da kazafi. Wai na gaji da Najeriya. To in gajiyar na yi kunyarki nake ji da zan kasa gaya miki?�
Aalimah ta kama baki tana kallonta, “Me ya kawo wannan tambayar?�
“You want to know?� Basma ta fada a raunane.
“Yes, I do�. Aalimah ta amsa.
Sunkuyar da kai ta yi.
“Yaya Aboubacar ya daina shigowa gidan nan saboda ba ya son ganina�. Sai hawaye.
Aalimah ta karasa kusa da ita sosai, tuni ta fahimci matsalar ‘yar uwarta. Hannayenta biyu ta kama, “Kina nufin damuwarki kenan?�
Basma ta daga kai, “Mu kuma kaddararmu kenan, son ‘yan uwanmu?�
Da sauri Basma ta cira kai ta dube ta,
“Sonsa nake yi?�
Murmushi Aalimah ta yi, “Ask yourself, not me. It’s your heart, not mine (tambayi kanki ba ni ba, zuciyarki ce ba tawa ba)�.
A hankali Basma ta zare hannayenta daga na Aalimah ta juya mata baya, “Idan dai yadda na damu da lamarinsa din nan da rashin ganinsa shi ne so, Aalimah ina son Yayanki…�. Kalaman da suka shiga kunnen Mama kenan, ta juya ta fasa shigowa kada Basma ta gane ta ji zancenta.
Aalimah ta dafa kafadunta, ta ce, “Basma!�
Ta juyo ta dube ta cikin damuwa, “Idan har za ki iya zaman Nigeria auren Yaya Aboubacar ya fi komai sauki a gare ki. In ba za ki iya ba ne da matsala. Amma kada ki bari ya gane kin damu haka. Ki dawo cikin walwalarki, tun zuwanmu ina lura da shi shi ma ya damu da lamarinki. Ki bi shi da duk ta inda ya billo, insha Allahu tsakaninku alheri ne�.
Da sauri Basma ta rungume Aalimah.
“Ni ko a jeji ne zan iya zama da shi Aal. Ba Nigeria ba, ko cikin bukka ne�.
******
Ya aka yi-ya-aka-yi? Cikin hira Aboubacar ya gaya wa Mahmoud zuwan Aalimah. Kwanansu bakwai sai ga shi a Kano. Gidansu na New site ya fara zuwa, inda aka gaya masa sun tashi. Ya kira Aboubacar a waya, shi ya kwatanta masa sabon gidansu da ke Sultan Road.
‘Yammatan biyu na zaune a falo sun dau wanka, kowacce da abin da ta ke yi. Basma tashar Arewa 24 ta ke kallo ana diramar Dadin Kowa, sosai abin ya dauki hankalinta yadda ake nuna typical Nigerian life da ba ta sani ba. Aalimah chatting suke yi da Abulkhair, wani abu da ya zame musu jiki tun zuwanta saboda ta roke shi kada ya kira ta ko sau daya, ba ta so Mama ta san akwai wani abu a tsakaninsu, za ta shiga damuwa a kan karatunta. Za ta yi tunanin ko ma ba karatu ta ke ba, tunda a gidansu ta ke.
Abulkhair ya fahimce ta, kuma shi ma yanzu ta kansa yake yi, ya shiga shekara ta biyun karshe a karatunsa, ko lokacin da yake chatting din da ita ma squeezing dinsa yake yi, saboda yana so ko me ta ke ciki ya sani, kada nisa ya nesanta shi da ita.
Aboubacar ya shigo, Mahmoud a bayansa, bayan sun yi sallama. Aalimah ta amsa ba tare da ta dago ba, komin canjin da rayuwa za ta kawo Mahmoud ba zai kasa gane Aalimah ba. Jikinta ne ya ba ta ana kallonta, kuma kamar yaya Aboubacar ba shi kadai ba ne ya shigo. Da sauri ta cira kai, suka yi ido hudu da Mahmoud. Sai da gabanta ya fadi, yana nan a yadda ta sanshi sai dan gogewa da ya yi. Yana sanye da shudiyar shadda kansa babu hula. Ajiyar zuciya ta yi ta janyo mayafinta a gefe ta lulluba, ya samu waje kusa da Aboubacar ya zauna, jikinsa a sanyaye. Yanzu ya kara tabbatarwa ya rasa Aalimah a bisa dalilai da dama.
Aboubacar da Basma sai kallon-kallo, kwana uku kenan bai shigo gidan ba sai yau a dalilin abokinsa ta ganshi. Aalimah ta rusuna ta gaida Mahmoud cike da jin wani irin nauyi domin har gobe Mahmoud mai kima ne a idanunta. Ba ta ji dadin abin da Abulkhair ya yi masa ba, wanda shine ya raba tsakaninsu, sannan bayan ya goge lambarsa daga wayarta ya yi masa kashedin sake kiranta ita din ba ta kara bi ta kansa ba, ko wajen Yaya Aboubacar ba ta karbi lambarsa ba. Idanunta sun rufe sun makance da soyayyar dan uwanta, wanda ya shigo cikin rayuwarta da wani irin karfin mulki, ya hana ta mallakar kowanne tunani sai nasa.
Hawaye ne suka ciko idanunta, “Ni mai laifi ce Mahmoud, ka yi hakuri�. Abin da ta iya furtawa gare shi kenan.
Murmushi Mahmoud ya yi, “I understand. Na dade da sanin haka za ta faru Aalimah. Shi ya sa na ce miki I’m scared da tafiyarki America. Da ni da ke duka babu mai iko da kansa ko zuciyarsa, sannan shi mijin aure rubutacce ne ga mace tun halittarta. Da ma ba ki yi min alkawarin ba za ki so kowa ba. Cewa ki ka yi you are hoping that destiny tied us together… to fatan bai karbu a wajen Ubangiji ba. Dan uwanki ya kira ni daga baya…�
Da sauri Aalimah ta dago ta dube shi. Abulkhair wane irin mutum ne? Tsoronta Allah, tsoronta kada ya kasance zaginsa ya yi.
Mahmoud ya yi murmushi ganin yadda ta tsorata. Ya ce, “Abin da ki ke tunani ba shi ne ba. Rokona ya yi in sonki nake na yi masa alfarma na bar masa ke, don ya fi ni sonki. Sannan yana mai tabbatar min babu sauran muhallina a zuciyarki�.
Aalimah ta dafe kai. Mahmoud ya ci gaba, fuskarsa dauke da murmushi.
“The guy is smart! Na kuma yi rantsuwa ni da kaina yana sonki. Na kuma yarda ya fi ni sonki. Na jinjina wa karfin zuciyarsa. Ina son mutum mai nuna kwanjinsa a kan macen da yake so. Ina yi muku fatan alheri�.
Aalimah sai ta ji hawaye sun sake ciko idonta. Mahmoud ya sanya hannu cikin aljihunsa ya fiddo abu cikin ambulan ya matsa ya mika wa Aalimah. Ta goge idonta ta karba, ta bude. Da sauri ta dube shi. Murmushi ya yi, “ni ma ‘yar uwata na nema. Na ga abin ya fi danko idan da alakar jini, kada in je wani waje in sake shan kaye a karo na biyu�.
Duk halin da ya sanya ta na tsananin tausayinsa, sai da ta yi murmushi. Katin daurin aurensa ne, sati biyu masu zuwa da cousin dinsa.
“Allah ya sanya alkhairi Mahmoud. Na gode, na gode. Ina kuma fatan hakan ba zai shafi tsakaninka da Yaya Aboubacar ba, ni kadai ce mai laifi�. Ta fada cikin sanyin murya.
Murmushi ya yi, ya ce, “Aboubacar ai ba ke ki ka hada mu ba, balle ki raba. Ki je ki ji da rigimammen saurayinki. Wannan in ya aure ki ki shirya shan kulle. Yana sonki fiye da kima, yana kishinki fiye da zatonki. Ni ma sakona gare shi ya gaggauta ya killace ki, in ba haka ba shi ma zai sha kaye, zai samu mai sonki fiye da shi. Saboda ke Aalimah daban ki ke. Soyayyarki ba ta yi wa maza sassaukan kamu�. Ya mike.
A zuciyar Aalimah ta ce, ‘ba amin ba, Abulkhair kawai nake so, daga nan har gaban abada!
Juyawar nan da za ta yi, Yaya Aboubacar ne da Basma, yana zaune a gabanta a kan kilishi, ita kuma tana kan kujera kamar dalibi gaban malaminsa. Maganganu suke yi kasa-kasa, wadanda daga su sai Ubangijinsu suka san me suke cewa. Mama ba ta gidan da ma, ta je asibitin Malam wanda ta ke zuwa duk karshen wata, su Sultana na makaranta.
“To kai yayan kwabo sai ka zo ka raka ni, zan tafi�. Mahmoud ya ce da Aboubacar yana kallon Basma cikin mamaki, sabida yadda idonsa ya rufe da ganin Aalimah bai ma lura da ko wace ce ba. Aalimah na da twin sister ne? Kai! That cannot be possible. Wannan ta fi ta aji, ta fi ta wankakken ido, me yiwuwa ‘yan uwan nasu ne na can�. Ya bai wa kansa amsa.
Aboubacar ya mike suka fita yana ce da Basma, “Ba doguwar rakiya zan yi masa ba, tasha zan kai shi ya hau motar Katsina�.
Dariya Aalimah ta yi tana kallon Basma, wadda annuri kadai ke fita a fuskarta, da gani sun daidaita abin da suke ganin matsala ne a gare su. In wani ya gaya mata Aboubacar Mansour ne wannan a gaban mace ba za ta taba yarda ba. Hakika soyayya abu ce mai girma, mai birkita rayuwar ‘ya’ya maza fiye da mata.
Kafin hutunsu ya kare su koma U.S, hatta Daddyn su Aalimah ya san da soyayyar Aboubacar da Basma, ba Mama kadai ba. Sai dai cikin su duka babu wanda ya zura jiki cikin al’amarin a bisa dalilai kwarara da dama. Ido kawai suka zuba musu, suna ganin da ta koma shi kenan za su manta da juna.
Sun dawo Massachusetts ranar asabar, litinin suka koma makaranta.
6/28/21, 7:36 AM - Buhainat: ₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩₩
💙💙💙💙💙����������💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💓💓💓💓💓
******
Haka Aalimah ta ci gaba da karatu a gidan Kawunta a Boston (Massachusetts) duk shekara suna zuwa gida su yi hutu su koma. Duk kuma zuwan da za su yi da Basma suke zuwa, inda suka girka wata irin soyayya ita da Yaya Aboubacar, yayan Aalimah. Wadda labarinta har Niger, har kunnen Malam Raazee. Da fari bai ce komai ba, don shi ba irin kakannin nan ba ne masu katsalandan cikin maganar auren ‘ya’yansu ko jikokinsu. Aalimah tana shekarar karshe, ita kuma Basma ta gama saboda karatun Aalimah na shekaru biyar ne, Aboulkhair ya kammala shekarar da ta gabata ya fito a cikakken likita mai kwalin MBBS. Ya tafi speciality a kan kwakwalwa a shahararriyar jami’ar da ta yi fice a duniya a kan ilimin psychiatry (wato John Hopkins University), wadda ke garin (Baltimore, Maryland).
Duk kawaicin Malam Raazee wannan lokacin ya yanke shawarar tsawatarwa ga ‘ya’yansa biyu kan wannan zuzzurfan ilmin boko da suka dora ‘ya’yansu akai, daga mazan har matan babu mai tunanin yi musu aure a cikinsu. An gaya masa batun Aboubacar da Basma, amma har gobe bai taba jin komai a kan Aalimah da Khaleesat ba, wadda ke aji biyu a jami’a yanzu haka. Idan sun ce karatu, to shi wannan karatun ba shi da iyaka ne, ko ko ba shi da madakata? Kada dauke idonsa ya sa a shiga keta haddin Allah.
Aunty Gumsu ta haihu shekaru biyu baya, ta haifi ‘ya mace Nurat. Don haka wannan zuwan da suka yi Niger har Mummy Zulaiha, ya ce a kira masa Mansour yana son ganinsa, ya zo su hadu da sauran ‘yan uwansu a yi ta ta kare kan ‘ya’yansu, ya gaji da ganinsu babu aure bakidaya. Cikin shekarar nan yake son ganinsu a dakin aure bakidaya, daga matan har mazan. Mu’azzam kuma sai sun gaya masa abin da ya hana shi aure.
Mu’azzam ya dade da sulhunta Mummynsa da dangin mahaifinsa bakidaya. Har nata ‘yan uwan. Tare da ita suke zuwa duk karshen shekara. Tsakaninta da Inna Kasisi yanzu sai sam-barka, da ma matsalar daga gare ta ne, kuma da ta nutsu ta bude zuciyarta kamar yadda dan nata ya shawarce ta, ta tadda abubuwan yadda ya gaya mata su. Ita kadai ta dauka da zafi, su mutane ne masu son junansu da kaunar duk wanda ya shafe su ba tare da nuna bambanci ba. Sai dai in ka nuna musu su ba wata tsiya ba ne cikin rayuwarka za su nuna maka ka yi kadan ka keta alfarmarsu, ko mene ne takamarka.
Don haka wannan zuwan har da Mummy aka zo Niamey. Kwanansu biyu kawu Mansour da Maman Aalimah da kannenta suka iso. Aboubacar bai biyo su ba, sabida aiki. Ba su samu zama da Malam ba sai da daddare. Ya sallami matan ya zauna da manyan ‘ya’yansa maza bakidayansu.
“Oussama kai ne babba, kai ne kuma za ka zame min shaida kan cewa tunda ka fara haihuwa ka ke aurar da ‘ya’yanka ban taba shiga ba, ban taba cewa da kai ga abin da ya kamata ba, saboda kai ka san ya-kamatan, ‘ya’ya mata ba sa wuce shekara sha shidda a gabanka. Kaninka Edrissa ya biyo bayanka da wannan kyakkyawan koyi. Amma wadannan (ya nuna Ishaq da Mansour) guguwar zamani ta debe su tana neman kai su ta baro.
Babu Allah a ransu sai ilmin nasara wanda iyakarsa duniya babu amfanin da zai yi musu a lahira. Sun aje balagaggun ‘ya’ya maza da mata ba sa ko tunanin yi musu aure. Bayan cikinsu babu wanda ban yi wa auren gata ba, tun kafin ya kama kwalin ilmin bokon don dai in fita hakkin Allah. Nauyin auren bai hana ku zama abin da ku ke son zama ba, don haka ku zama shaida, ko yau na fadi na mutu Ishaq da Mansour su suka yi ajalina.
Sun ki aurar da ‘ya’yansu, sun ki gaya min matsalar Mu’azzam, kullum abin nan na damuna a zuciya, da shi nake kwana nake tashi. Shi ma Mu’azzam din ba ya son na yi masa zancen aure, daga shi har Abulkhair ba su da niyyar yi musu aure, balle kannensu mata. Ga Aboubacar shi ma ya dade yana aiki, amma babu abin da suka yi a kan zancensa da Basma, wanda na dade da ji yana yawo a bakin su Bintou.
Yau ga su a gabanku su gaya mana gaskiyar lamarinsu. Me suka dauki rayuwar duniya? Wallahi ba inda za ta kai ku idan ba ku bi dokokin Allah ba�.
Ya soma matsar kwallah, duk kuma maganar cikin harshensa Temachek yake yinta.
Shiru ta ratsa a falon Malam Raazee. Daddy Ishaq idanunsa sun kada sun yi jazir. Jijiyoyin kansa sun fito rada-rada. Baban Aalimah bai ce komi ba, ko shi yana son jin mene ne matsalar Mu’azzam. Tambaya ta karshe da ya yi masa shekarun baya zuwan Aalimah na farko hutu, da ya tambaye shi cewa ya yi da shi, Mu’azzam addu’arsu kawai yake so, amma ba abinda yamadidi da lalurar tasa zai amfana masa.
Don haka yau shi ma ya zuba masa ido a qagare da son jin amsar bakinsa. Maganar Aboubacar da Basma ya santa ba tun yau ba, bai taba daukanta da muhimmanci ba ne saboda a ganinsa Aboubacar ba shi da abin da zai rike Basma, kuma ba za ta iya adopting tashi rayuwar ba.
“Kai muke saurare Ishaqa�. Uncle Edrissa ya katse masa dogon shirun da ya yi. Ajiyar zuciya ya yi, yau kam ya san ba shi da mafita ban da gaya wa mahaifi da ‘yan uwansa ko wane ne Mu’azzam. In ba haka ba za su yi zaton bai dauke su a bakin komai ba, kuma yana nufin ‘ya’yansa ba nasu ba ne. Mutuncin Mummy Zulaiha a idanunsu yake tattali wanda Mu’azzam din ya samu ya farfado da shi ba da jimawa ba.
Ina ga in sun ji ita ce ta illata wa wannan dan da suke matukar so rayuwa bakidaya? Duk da shi ma da nasa laifin, amma tarbiyya a hannun mace ta ke, ita kuma ba ta zauna a gida ba balle ta zama ginshikin samar da ita. Ta debi al’adun al’ummar da ta samu kanta a cikinsu ta yafa gabadaya babu gaira babu dalili.
Shirunsa ya kular da Uncle Oussama ya soma fada, da ma shi masifaffe ne. Ya fadi kalamai wadanda ba su yi wa Daddy Ishaq dadi ba. Ya ce don su ba su yi ilmin boko ba ne shi ya sa yake daukarsu ba a bakin komai ba; a wadanda ba su da kwakwalwar fahimtar abubuwa. Daddy Ishaq ya rasa inda zai sa kansa, sai ya soma hawaye.
Zuciyar Mansour ta tabu saboda ba ya hada Ishaq da kowa cikin rayuwarsa. Hakuri ya soma ba wa babban Yayansu ya ce Ishaq ba haka yake nufi ba. Zancen ne yake yi masa nauyin fada da alama, ya barshi ya hada zaren maganar da ke bakinsa a hankali.
Daddy Ishaq ya ji dadin abin da kaninsa ya ce, ya ce su yi masa alfarma ya kirawo Zulaiha a yi zancen nan a gabanta, amma yana rokon alfarmar abubuwa guda biyu kafin ya fada musu komai. Na daya, su yi wa Zulaiha uzuri su yafe mata kamar yadda ya yi mata uzuri, ya kuma yafe mata. Kowa rai ya yi wa dadi baran mai shi ne. Ta fi kowa kasancewa cikin damuwa da yanayin rayuwar Mu’azzam, kuma da tana da yadda za ta yi da tuni ta fitar da shi daga halin da yake ciki. Na biyu ba ya so zancen nan ya je kunnen mata har Inna Kasisi da Inna Bintou. Malam ya ce yana sauraronsa, kuma ya amince zancen zai tsaya a tsakaninsu su kadai.
Mikewa ya yi ya fita, ya tura yaro cikin gidan ya kira Mummy Zulaiha.
A nutse Mummy ta shigo falon, ta ratsa ta tsakiyarsu ta wuce ta nemi wuri can nesa da su ta zauna. Malam ya maimaita mata makasudin taron da bukatarsa na aurar da ‘ya’yansu bakidaya a lokaci guda, har Mu’azzam. Idan kuma sun ce rashin lafiya ya hana shi aure, to yau yana bukatar su fayyace masa wace irin rashin lafiya ce da abin da ya raba auren da ta yi masa shekarun baya.
Mummy kuka ta saki, a hankali ta rufe fuska da mayafinta. Daddy Ishaq ya ce, “Zulaiha yau zan gaya musu, don ba ni da wanda ya fi su. Dukkaninmu ni da ke masu sakaci ne, amma naki ya fi nawa yawa. Idan Allah ya ce haka Mu’azzam zai kare rayuwarsa babu tsimi babu dabara�.
Tiryan-tiryan ya soma ba su labari tun barinsa Nijar zuwa Amurka tare da maidakinsa da dansu guda daya da suka haifa a nan Niamey, wato Ibrahim-Mu’azzam, wanda sunan Malam Raazee na gaskiya ya ci. Shekaru talatin da uku a baya, da duka abin da ya wakana cikin shekarun har zuwa yau shekarar da muke ciki.
Falon ya dauki shiru, sai shesshekar kukan Mummy Zulaiha kadai. Jikin Uncle Oussama ya yi sanyi da fassarar da ya yi wa dan uwansa a baya.
Uncle Edrissa ya nisa ya ce, “To ku ne kun gama yin amanna da maganar bature da maganinsa, ban da haka ai babu cutar da ba ta da magani sai mutuwa da tsufa. Kuma ni ban yarda wannan cuta ba ce a nahiyarmu, can a kasashenku kadai ake wannan ciwace-ciwacen a ce ba su da magani. Mu a addinin musulunci mun yarda cewa babu maganin da babu a cikin Alkur’ani. Shi din (Alkur’ani) waraka ne, kuma magani ne na kowacce irin cuta.
Mu’azzam ya dawo gida, ya rabu da wannan maganin da yake sha, mu yi wanda muka gada iyaye da kakanni�.
Uncle Oussama da ke kallon Mummy a hasale babu ko digon tausayinta a ransa sabanin sauran kannensa ya ce, “To kukan me za ki damu mutane da shi yanzu? Wanda ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka. Ni ban taba ganin mace irinki ba, kawai don kin je kasar turawa sai ki dauki kanki jinsinku daya, ki kasa bambance mai kyau da mara kyau, ki saki koyarwar addininki ki kama ta wadanda tun a duniya Ubangiji subhanahu wata’ala ya gaya mana makamashin wutar jahannama ne su (yahudu da nasara).
An yarda babu inda neman abinci da yanayin rayuwa ba ya kai mutum, amma musulmi ya dinga tunawa shi musulmi ne a duk inda ya tsinci kansa, ya kiyaye martabar addininsa da koyarwarsa. Rayuwa cikinsu da cudanya da su (ahlil kitabi) ba laifi ba ne a musulunce, amma ‘ya’ya amana ne a hannun iyaye da ya zama dole a dora ido a kan mu’amalarsu da rayuwarsu, a tsawatar a inda yake bukatar tsawatarwa.
Makauniyar soyayya ga ‘ya’ya ba gata ba ne a gare su, don haka za ki yi ta kuka fiye da Mu’azzam tunda ke uwa ce, kin fi shi son kansa da kansa, babbar banza kawai! Ashe matan ma Aalimah ce ta gyara su inji Balkissa amma ai da dan wando da ‘yar riga suke yawo, kai ba kallabi kamar akuyoyi�.
Haka Uncle Oussama ya karewa Mummy tanadi tas ko dagowa ba ta yi ba. Malam dai ya kasa magana, tausayin Mu’az ya kashe bakinsa da zuciyarsa. Sai da Oussama ya yi shiru sannan Baban Aalimah Dr. Mansour ya yi gyaran murya, ya dubi Uncle Edrissa, ya ce,
“Ban musanta batunka ba Yaya Oussama. Kuma ban hana a nema wa Mu’azzam magani namu na gida ba. Amma zancen ya bar treatment dinsa ya daina shan maganin likitocinsa bai taso ba. Da gaske wannan cuta ce mai zaman kanta na taba cin karo da ita a wani bincike da muka gudanarwa world health organization (WHO) a kan hanyoyin da za a bi a rage cututtukan kwakwalwa a cikin al’umma. Kuma ba bugun aljannu ba ne, sannan ba a America kadai ake samun masu fama da ita ba, wallahi har nan Nigeria inda nake, kawai dai Society dinmu ba su dauke shi mental health deficiency ba ne, sun fi daukarsa a DABI’A. Don haka ni shawara ta ita ce a jefi tsuntsu biyu da dutse daya, wato Mu’azzam ya ci gaba da shan maganin asibiti, sannan ku ma ku yi irin naku kokarin, a taru a roki Allah ya yaye masa bakidaya�.
Kowa ya yi na’am da shawarar Dr. Mansour, ko da ma can duk ya fi kowa a gidan kaifin hikima.
“Don haka mun ajiye batun Mu’azzam a gefe, za mu dawo kansa daga baya in mun samu nutsuwa. Yanzu muna kan na masu lafiyar. Ishaq, me kake ciki maganar auren ‘ya’yanka? Kai ma Mansour me ka ke ciki kan Aalimah da Aboubacar?� In ji Uncle Oussama.
Daddy Ishaq ya muskuta ya ce, “Ba kin aurar da su na yi ba. In don ta ni ne da tuni na dade da aurar da su. Sun dade da hada kansu shekaru biyar a baya. Bana so ne in shiga gonar Mansour, ina so ya samu cikar burinsa shi da Aseeya a kan Aalimah, kada ya ga kamar na so kaina�.
Ido sosai Dr. Mansour ya bude yana kallon Yayansa cikin rashin fahimta. Edrissa ya ce, “Kamar ya ya? Su waye suka hada kan nasu?�
“Aboulkhair da Aalimah�.
Fuskokinsu suka bayyana dadin da zancen ya yi a zukatansu. Malam ya ce, “Da ma aure yana hana wani buri cika ne, ko dai ya taimaka masa ya kai ga ci? Tukunna ma wane buri ne Mansour din da maidakinsa suke da shi a kan Aalimah? Da ma ana ci wa ‘ya mace alwashi a hana ta aure ne?�
Nan Daddy Ishaq ya warware musu komai kan ba shi ya dauki nauyin karatun Aalimah ba. Ya gaya musu duk abin da ya wakana.
Dr. Mansour Raazee ya dubi yayansa kamar zai yi kuka, “Ba ka kyauta min ba Yaya! Shekaru biyar Aboulkhair na dakon soyayyar Aalimah bayan kai kanka mai daura mata aure ne. Aseeya ke son karatun nan ba ni ba, kuma ita ma in ta san Aboulkhair ne zai auri Aalimah ba za ta hana ba. Shekara biyar Yaya? Ban ji dadi ba ko kadan. A kalla da ka gaya mini ko shawara ce mu yi,. Idan har yanzu Aboulkhair na son Aalimah bai canja shawara ba sabida nisan shekarun da aka sanya shi jira, na ba shi ita duniya da lahira, kuma ban da sadaki ban dora masa komai ba. Sadakin ma in an amince min, zan biya masa�.
Uncle Oussama ya ce, “To ba a amince maka din ba. Shi zai biya ni daga aljihunsa. Aboubacar da Basma fa? Me suke ciki? Shin zancen da Inna Bintou ke fadi cewa sun hada kansu gaskiya ne?�
Shiru Dr. Mansour ya yi, sannan a sanyaye ya ce, “Na san zancen, sai dai ban taba ba shi muhimmanci ba, a bisa hujjojina kwarara�.
“Wane Aboubacar din da wace Basman?� Daddy Ishaq ya tambaya cikin mamaki da kuma dokantuwa da a fidda shi cikin duhu.
Nan Malam ya gaya masa shi ya dade da sanin zancen a bakin iyayensu mata. Ya yi zaton ya sani shi ya sa ya yi ta zuba ido yana jira su zo masa da zancen. Da ya ga suna nufin sai bayan ransa shi ya sa yake so a yi ta ta kare a yau. Ko bai ga ‘ya’yansu ba, ya shaida aurensu ya gode wa Allah.
Daddy ya dubi kaninsa zuciyarsa na ninkaya cikin farin cikin da ya gaza boyuwa a kan fuskarsa.
“Ba ka bai wa zancen muhimmanci ba sabida wadanne hujjoji naka? Da ni da kai wa ya fi rashin kyauta wa dan uwansa?�
Murmushi ya yi ya sunkuyar da kansa, “Ku fahimce ni bakidaya, dukkaninsu ba mai iya zama a kasar da dan uwansa ke zaune. Kowanne yana da tsararriyar rayuwa a inda yake. Sannan abu ne mai wahala Basma ta iya baro iyaye da ‘yan uwanta ta zauna da mu a Nigeria. Sannan ina tunanin kamar karfin samunsa bai isa ya rike ta ba in aka yi duba da irin rayuwar da ta taso a ciki�.
Murmushi Daddy Ishaq ya yi, kanin nasa na kara shiga ransa. Idan zai yi abu sai ya duba shi (from every sphere, he leave no stone unturned),
“To ai ni kaina na kusa barin Americar�.
Ba Mummy Zulaiha kadai ba, kowa a falon sai da ya juyo ya dube shi. Gyada kai ya yi don tabbatar musu da furucinsa, sannan ya ci gaba da bayani yana kallon matarsa.
“Saboda Mu’azzam na kai wannan lokacin a America, saboda yana karbar proper medical treatment, kuma bana so mu taho gabadaya mu barshi shi kadai, ga aikinsa ga yanayin da yake ciki, a ce ba shi da kowa a kasar da yake zaune. Amma ni tun farkon faruwar matsalolin nasa kasar Amurka ta fice min a rai. Ina ta dakon damuwar Mu’azzam. Yau da na fayyace muku sai na ji kamar an dauke min wani nannauyen dutse daga kirjina. A kalla nasan ba ni kadai nake jigilar damuwar ba, ina da masu taya ni ko da da addu’a ne. Target dina na yanzu shi ne, Aboulkhair ya kama aiki, ya yi aure ya zauna kusa da shi, ni kuma in nemi aiki a nan Niamey in dawo�.
“Allah ya yi maka albarka�. Inji Malam Raazee, “Shi kuma Allah ya ba shi lafiya�. In ji Uncle Oussama da Uncle Edrissa.
Ba su tashi daga wannan zaman ba sai da suka yanke lokacin auren yaran nasu hudu. Daddy ya gaya musu ita Khaleesat yana da buri a kanta, ya dade da gane shirin da ke tsakaninta da Hamoud kafin ya tafi Japan, inda yake kwas din aikin sojan ruwa, shekara mai zuwa zai kammala. Uncle Oussama rasa me zai ce ya yi, danshi yake wa tanadinta, amma ya gaya masa maganganu marasa dadi dazu. Matsar kwalla ya shiga yi yana cewa, “Pardonne-mon frere�. Wato (ka yafe min dan uwa da harshen faransanci).
“Ni ba ka yi min komai ba Yaya. Kauna ce ta saka damuwa da lamarin Mu’azzam�.
Addu’a mahaifin nasu ya daga hannu ya yi musu bakidayansu. Ya sa musu albarka, ya roki Allah ya sa su gama da duniya lafiya, ya kara musu kaunar junansu.
*****
Watanni uku aka sanya auren Aboulkhair da Aalimah, Aboubacar da Basma. A wannan lokacin Aboulkhair ya haye jarrabawarsa ta specialty da suke kira primaries a Psychiatry, ya zama junior registrar. Shekaru biyu baya ya sake yin jarrabawa part 1 ya haye cike da dumbin nasara ya zama senior registrar in Psychiatry. Asibitin Desert Parkway dake garin Las Vegas nan ya tura takardunsa neman aiki, don kawai ya zauna kusa da dan uwansa ya kula da shi, shi ya sa bai nema a garin da iyayensa suke zaune ba.
A ganinsa Mu’azzam ya fi su bukatarsa kusa da shi duk da ya san Mu’az ba zai yarda su zauna gida guda ba sabida rashin son hayaniyarsa, amma a kalla suna gari daya, koyaushe yake son ganinsa zai je, zai maido da kulawarsa bakidaya wuyansa, tunda dama saboda shi ya karanci wannan bangaren.
Idan ya yi shekaru biyu ko uku yana practicing kuma zai koma John Hopkins ya sake yin wata jarrabawar part 2 suke kiranshi, idan har ya ci shi kenan ya zama cikakken consultant (neuro psychiatrist). Duka wannan wahala da jajircewa ba don kowa Aboulkhair ke yi ba, ba don kansa ba, ba don shiryawa kai future ba, sai don ya kula da lafiyar Yayansa Mu’azzam.
6/29/21, 9:00 AM - Buhainat: 6
Sanda ya shigo gidan, Aalimah na kwance a three seater, idanunta a lumshe kamar mai barci da carbi a hannunta. Ko kusa ba ta ji shigowarsa ba sai zamansa bayan ya kwashe kafafunta ya zauna a muhallinsu, ya maida su bisa cinyoyinsa. Yatsun kafar ya shiga kallo kamar yau ya fara ganinsu. A hankali ya shiga ja mata yatsun daya bayan daya, uffan bai ce ba, gabadaya tafukan kafar nata masu tsananin taushi da suka sha adon jan lalle suna cikin hannayensa. Aalimah ta dada runtse idonta, wani abu ne da bai taba faruwa da ita batun tashin ta. Wato jikinta ya kusanci na wani da namiji, balle wannan ba wani ba ne face mutumin da zuciya da ruhinta suka dade suna mafarkin mallaka, Aboulkhair ne, dan uwanta da a yanzu yake amsa sunan mijinta, mahadin rayuwarta.
Katon mayafin ya shiga zarewa a hankali yana kiran sunanta. Dagota ya yi bakidaya ya aza a jikinsa, bayan ya yi nasarar zare mayafin, ya saura daga Aalimah sai rigar barcin da Gumsu ta zaba mata, wadda a cewarta ita ce ta dace da wannan ranar a gare ta, kuma irinta ta zaba wa Basma. Sunanta kawai yake kira, yana so ta bude ido ya kalli kwayar idanunta da ya dade bai samu alfarmar gani ba.Yayin da hannayensa biyu ke karadewa suna rungume ta a dukkan jikinshi.
Wata irin ajiyar zuciya Aboulkhair da ita kanta Aalimah ke saukewa akai-akai, zuciyoyinsu na tuno musu tsawon lokacin da suka dauka suna dakon zuwan wannan ranar, shekaru biyar cif! Ashe komai in aka yi hakuri aka bi dokar Ubangiji, aka yi biyayya ga iyaye komai nisansa watarana za a kai ga cimmasa ta tsaftacciyar hanya.
A wannan rana mai dumbin tarihi cikin rayuwarta, Aboulkhair Ishaq Raazee ya tabbatar mata ya wahala ba kadan ba, cikin dakon kaunarta da jiran wannan muhimmiyar rana a gare shi, wadda ranakunta suka shude a daddafe tamkar ba za ta taba zuwa ba. Kaunar ya nuna mata filla-filla da wani irin salo mai tsayawa a zuciyar diya mace. Aalimah, ta yarda ta amince; a daren yau son da Aboulkhair ke mata ya rinjayi nata, duk da yadda a baya ta ke zaton zuciyarta mai kankanba ce a kansa. Tun tana sanya wa ranta juriya da ganin cewa, lamarin mai iyaka ne tunda dai Aboulkhair mai sonta ne, mai tausayinta ne, har ta amince wannan ita ce ranar rashin tausayi ta duniya a rayuwar Aboulkhair. Ba ta kuma da wani yunkuri da za ta iya na kwatar kai, ko ceton kai, sai yadda Aboulkhair ya ga dama da rayuwarta.
A tsayin daren bakidaya Aboulkhair bai dawo Aboulkhairinsa ba sai da ya fahimci Aalimah duk juriya da dauriyarta da ta ke yi domin ya samu nutsuwa, domin ya tabbatar ba shi kadai ya yi wahalar shekaru biyar ba, ita din kuma ya cutar da lafiyarta ba dan kadan ba.
Shi likita, ita mai bada magani, don haka taruwa suka yi suka taimaki kansu ba tare da taimakon kowa ba, ba tare da wani ya ji ya gani ba. Ko Gumsu da suka biyo yi musu sallama washegari ta yi tsokanar duniyar nan, Aalimah ba ta tanka ba, sai murmushi da rufe ido. Shi kuma suna zuwa ya bar gidan ko gaisawa ba su yi ba. Rana ta farko da ya ji yana jin kunyar Mummy a rayuwarsa. Ya gode wa Allah da Mu’az ba ya nan, kallon cikin idanunsa a yau ya tambaye shi ya amarya ta kwana babban tashin hankali ne a gare shi. Saboda Mu’az ya san komai nasa tamkar a tafin hannunshi, ko da kuwa bai furta masa ba.
Ba su dade ba suka yi sallama da ita suka tafi, direban Mu’az har Massachusetts zai kai su, ya hana su bi motar kasuwa, kuma ya ce kada su sa Aboulkhair tuki ya bar matarsa a garin ita kadai bata saba ba.
******
“Sun tafi?� Aboulkhair ya tambayi Aalimah daga bakin kofa, yana mai leko kansa dakin kamar mara gaskiya.
Murmushi ta yi ba tare da ta juyo ba ta ci gaba da shafa manta a lallausar fatar jikinta. Alamu sun nuna daga wanka ta fito.
Ya karasa shigowa dakin ya isa gare ta, ya rungume ta ta baya yana sunsunar bathrobbs din da ta yi amfani da shi, suka kama fatar jikinta da karfin gaske, yana wani lumshe idanu. A karshe ya juyo ta bakidaya suka fuskanci juna. Kallonta ya yi, kamar ya hadiye ta don so, hannayensa na bisa kafadunta, goshinsa hade da nata, karan hancinsu na zungurar na juna.
Ya ce, “Kwanta ‘yar Gumsu in duba stitches din�.
Hannayenta biyu ta sa ta rufe fuskarta tare da yin baya da sauri za ta gudu. Da azama ya cafko ta.
“Mun wuce wannan stage din Aalimah, ki kwanta in duba�.
Yadda ya yi maganar cikin seriousness ya sa ta bi umarninsa.
Rungume ta ya yi sosai, yana fadin, “I’m sorry Aal, really sorry. Ba Aboulkhair ba ne ya aikata wannan laifin sabon mijin Aalimah ne. Shi Aboulkhair ai kin san shi mai tausayi ne ko?�.
Ya hau sumbatarta kusfa-kusfa yana rokonta ta yafe masa. Toshe masa baki ta yi da tausasan yatsunta.
“Aalimahr is nothing but his wife wadda Allah ya yi masa izinin ya zo mata sanda ya so, duk ta inda ya yi umarni, ita din gona ce a gare shi. In dai Aboulkhair ne yanzu ma ya maimaita goman laifin nan a shirye Aalimah take da karbarsa cikin kowanne hali Monsieur Aboulkhair. Na san ba rashin so ba ne, kauna ce. Kaunar ma ta Aboulkhair ga Aalimah, ‘yar asali, mai dogon tarihi, wadda ta cancanci bugawa a littafi da na iya rubutu�.
Murmushi Aboulkhair yake ta yi, wanda ke fitowa kai tsaye daga zuciyarsa, a lokaci guda yana mai cakuda yatsunsa cikin lallausar gashin kanta, ya ce,
“Gara da ba ki iya ba. haka kawai! Masu karantawar su ce… su ce…�
Dariya Aalimah ta saki, ta ce, “Su ce me?�
Karan hancinta ya kama ya ja da karfi, ya ce, “Na ki fada din, balle ki fara rubutun a kaina. Ki dai fara a kan wannan Gumsun uwar taki mai budurwar zuciya�.
Dukkansu dariya suka saki suna kewarta.
Ya ce, “A duniya ina son Aunty Gumsu, amma kwanan nan tana shigar min hanci, she’sannoying�.
Aalimah ta ce, “Ba ka ga abin da ta yi wa Basma ba, namu nafila ne. Har daga zanin gadon ta ke tana shiga da shi daki-daki wai wadanda ba su gani ba su zo su gani�.
Ya girgiza kai, ya ce, “Shi ya sa na zage na wanke abuna kada ta dauki hoto ta tura Niger�.
******
Kwanaki uku da suka biyo baya wata irin rayuwa ce mai cike da soyayyah, Aboulkhair da Aalimah ke gudanarwa a gidansu. Su yi girki tare, su ci abinci tare, su yi wasa su yi dariya, su sanya juna nishadi. Tarairayarta yake da jinya har ta warware. In ba wani abu da ya kama dole zai sayo musu ba, ba ya fita. Sallah kuwa jam’inta suke su biyu sau biyar a rana. Nata dakin sun kulle shi da nashi suke amfani. Sun yi wata irin shakuwa mai ban mamaki fiye da shekaru biyar din baya.
Yau suna zaune a dan karamin dining dinsu mai kujeru biyu kacal, wanda ke cikin kitchen dinsu suna cin abincin rana. Wayarsa ta yi kara, ya kalle ta da gefen ido, bai yi niyyar amsawa ba don a kwanakin nan ma amsa waya wahala yake masa, ta fi zama a kashe a yawancin lokuta kafin ya karasa cinye kwanakin hutunsa da suka rage. Amma ganin mai kiran da sauri ya dauka.
Aalimah na ganin yadda ya tattara bakidaya hankalinsa a kan wayar, ya kuma mike tsaye. Hatta muryarsa canzawa ta yi, magana yake with utmost respect.
“Ban san ka shigo gari ba, da tuni na zo na kwance jaka. A yi min izini na kawo Aalimah ta kwashi gaisuwa wajen babban Yaya, ba ta taba ganinka ba�.
Ba ta ji amsar da Mu’azzam din ya bayar ba, ta dai ga Aboulkhair ya kara nutsuwa yana rokonsa ya barsu su zo. Har yana fadin, ya fadi iya mintunan da zai iya ba su da bakinsa in suka haura gobe kada ya barsu su sake zuwa. Takaici ya kashe Aalimah daga zaune, sarkin ina ne wannan? Dole ne zuwa wajen nasa? Me yake rabawa da sai an roke shi za a je inda yake?
Ba ta gama wannan tunanin ba ta ga Aboulkhair ya cillar da wayar tasa gefe ya rarume ta ya mikar. Cike da zumudi ya ce, “kiyi girki, wanda ya fi kowanne dadi mu kai wa Mu’azzam, ki hanzarta mintuna talatin kawai ya ba mu in mun je, yana da wata seminar gobe da (Concophillips oil Gass) yana shiri, kada ki bata lokaci�.
Aalimah ta rausayar da kai, ta ce,
“Me zan dafa? Ban san me yake so ba?�
Ya koma ya zauna ya hau lissafi.
“Girkin da ya fi kowanne dadi with aroma and maggi�.
Ba ta san sanda ta saki dariya ba, ta tabbata Aboulkhair yana matukar son Yayansa, ba ta taba ganin ya dau lamarin wani da muhimmanci irin haka ba.
“Kowanne girki ai dole a sa masa aroma da maggi, I mean irin abincin da yake so�.
“Tashin hankali�. In ji Aboulkhair, “Ai wato menu ake ba shi daga WALDORF ASTORIA (mafi shaharar restaurant a Las Vegas) ya zabi abin da yake so, ni kaina ban sani ba. amma ke me ki ka ga ya dace?�
Aalimah kamar ta yi kuka, a ranta ta ce, ‘Haka kawai ina zaman-zamana za ka taro min aradu da ka, wannan basaraken naka ai sai kai�. A fili kuma ta ce, “Burabisko da miyar taushe�.
Ya zaro ido, ya ce, “You are not serious. Gero zaki dafa masa ya shaqe shi? Tukunna ma kin san wai wajen wa nake magana ne?�
“Ka ce sunansa Mu’azzam�.
Ya ce, “Ba ki san Yayanmu ba ne?�
Ganin kamar ya soma harzuka ta shiga nutsuwarta sosai, ita haka kawai ranta bai son Mu’azzam din nan tun daga lokacin da ta fahimci irin life style dinsa, da maganganun da kannensa ke yi a kansa na irin rashin kirkinsa da ginshirarsa, sannan shekaru biyar ta kwashe a gidan Ishaq Raazee daidai da rana daya ba ta taba ganin sawun wannan Mu’azzam din a gidan ba, da sunan ya zo gaida iyayensa. Sai dai kullum ta ji Mummy a hanyar zuwa gidansa, what a life! Sannan yanzu ta kara fahimtar wani abu, Aboulkhair ba ya hada lamarin Mu’azzam da na kowa, ita kanta ba a bakin komai ta ke ba in dai a kan Mu’azzam ne. She has to be careful don tsira da mutuncinta a idon mijinta-mai-kaunarta.
Da kyakkyawan sauti ta ce, “Ina ganin mu yi masa tuwo. Ka fahimce ni Mon Amour (my love), ba abin da ya saba ci ya kamata mu kai masa ba, ba za mu burge shi ba. African cuisine shi ya kamata. Idan Mu’azzam ya kasa cin tuwo na ka mare ni sau uku�.
Bai san sanda ya yi murmushi ba, amma kwarai ta bata masa rai da farko, zancen Mu’azzam fa yake mata, amma ta maida shi kamar wani marainin wayonta. Kodayake ya mata uzuri, ba ta sanshi ba, ba ta taba ganinsa ba, ba ta san komai a kanshi ba.
Wanka ya shiga kafin ta gama, ita kuma ta dukufa sarrafa kyakkyawan farin tuwon shinkafa da miyar danyar kubewa da ta markadata da blander. Ta yi masa kyakkyawan tuki, ta kwashe shi kananan malmala a farar leda ta jera a food warmer madaidaiciya. Kafin ta saka kaza a miyar sai da ta soya ta, sannan ta zuba su a miyar suka dahu tare. Kafin ta gama zobon da ta jika da ruwan zafi ya jiku, ta tace ta yi masa hadin danyar abarba da danyar ginger (citta), ta sa sukari da pineapple flavour. Ta juye a cooler irin ta zuwa picnick din nan. Ta jera komai a kwandon abinci har farantai da cokullan da za su yi amfani da su ta dauka. Sannan ta fada wanka.
Dukkansu sun yi tsaf cikin Hausa Attire, sai kamshi suke yi. Suna tafe a hanya Aboulkhair ya kunna musu kira’ar Abdurrahman Sudaith cikin suratul Ma’idah, wadda ta kara sanya nutsuwa da kwanciyar hankali a zukatansu. Aalimah cikin ranta cewa ta ke yi, yau dai za ta ga Mu’azzam din nan, ta ga shin me ya taka a rayuwarsa? Wane ne shi? Wane irin mutum ne shi? Zaman me yake yi shi kadai a gida babu iyali? Ba mamaki ma matan banza yake kai wa gidan, wanda ko gaida iyayensa ba ya yi, ba ta zaton masa wata rayuwa mai albarka. Sosai ta ke jin rashin kaunarsa a zuciyarta. Ta tuno kannensa da yadda suka tsane shi, da kuma yadda kullum zancensa ya ratso cikin hirarrakinsu suke kiransa ANNOYING son of Mum. Kalmar da ke da tarin ma’anoni masu yawa daidai da fahimtarsu. A saninta kalmar annoying na nufin irritating, infuriating, tiresome kuma troublesome. Da ta tattara ma’anonin wadannan kalmomi, hadida tattara su wuri guda in a nutshell suna nufin Yayansu Mu’azzam mai yawan fusata ne, mai tayar musu da hankali (ta hanyar yi musu fada), mai tilasta su su yi abu ko da ba sa so, mai yawan damuwa a karan-kansa, kuma mai tarin matsalolin rayuwa.
Idan ta jimlace wannan fassara a ma’auni na hankali da tunani da zurfin iliminta, za ta iya fahimtar lamarin ba komai ba ne; is simply a subject matter that others around him are not understanding what he is going through. Ita ce makalar da ke tattare da rayuwar Yayansu Mu’azzam, har ta kai ta kawo cewa, he lack positive emotions like happiness and laughter… wanda kannensa suka fassara shi yadda suka ga dama, ba tare da bin ba’asin dalilan da suka mayar da rayuwar tasa hakan ba, ko abin da ya janyo masa wannan rayuwar da yake ciki. everything has CAUSE! Wato komai yana da tushe.
Haka kawai ta ji jikinta ya yi sanyi, zuciyarta ta dugunzumarta da son sanin WANE NE MU’AZZAM??? Za ta bi kwakkwafi ta ji mene ne cikin rayuwarshi haka da ya maida shi hakan ta hanyar mijinta, mafi kusanci da shi ko da hakan na nufin canzawarta daga mai harhada magunguna zuwa ethnographer ne. Shebecame extremely intrigued.
Ta yi nisa cikin wasikar jakinta ta ji yatsun Aboulkhair saman fuskarta yana shafa kuncinta a hankali, ashe ya jima da kashe motar a kofar gidan Mu’azzam.
“Mrs. Thinker tunanin me ki ke yi? Ga mu gidan Mr. Mu’azzam Raazi, taho mu je�.
Sai kuma ya dakata alamar ya yi mantuwa, “In mun shiga kada ki zauna a kusa da ni, kunyarsa nake ji sosai, har fiye da Daddy. Ko hannunki ba zan kama ba�.
Dariya ta kama Aalimah matuka, da ma akwai wanda Aboulkhair ke jin kunya a duniya? Ta ga dai a gaban Mummy ya ce da Gumsu ta dawo dakinsa su kwana, ita ya bari da ji masa kunyar. Girgiza kai ta yi, ta murguda baki, ta ce, “In ka ce masa ma ba sona ka ke ba sadaka ta aka ba ka, duk daidai ne�.
Hannu biyu ya dora a ka yana leken idanunta, amma ta ki yarda ta kalle shi, ya ce,
“Ya fi ki sanin yadda nake son naki, da wahalar da na sha kafin in same ki. Ba don shi ba da ba’a kawo yau ba, da tuni na watsar da karatu na rungumi Aalimah a cikin gida. Da ma karatun don shi nake yinsa, kuma with his support and encouragement, yau na tsira da ku bakidaya (ita da karatun)�.
Murmushi ta yi tana kici-kicin fiddo kwandon abinci daga bayan motar. Ya karbe ta yana fadin, “Idan ina kusa, ko Babyn mu ba za ki dauka ba balle wasu kaya�.
Wata harara ta sake masa, “Wai baby, har yaushe akai daren da garin zai waye?� Ta fada a karkashin zuciyarta, tana dubansa ta kasan ido cike da so da kauna.
Aalimah ta daga ido a hankali tana kallon kyakkyawan gidan da aka kira mallakin Mu’azzam Raazee ta hanyar rubutawa a jikin kofar shiga gidan, wanda ke cikin kebantacciyar unguwar HillsboroughEstate, mai hawan sama da kasa. Irin gidajen da suka kira ‘Fairfield Terrace’ wadanda sai dai mallaka ba dai haya ba (rent). Wani mutum yana goge motoci da ya juyo, sai ta gane shi, shi ne direban da ya debo su daga airport ya kuma kai su Mummy gida. Da fara’a ya gaishe su, ya karbi kwandon hannun Aboulkhair ya bi bayansu.
A falon da suka fara tararwa Aboulkhair ya ce ta zauna ya hau sama ya kira shi. Da gudu-gudunsa yake hade steps biyu-uku yana kiran, “Mu’az�. Har ta daina ganinsa. Ta shiga wurga ido tana kallon wani irin English parlour da ko a talabijin ba ta taba ganin mai tsari da kayatuwarsa ba. Ta fahimci gidan ba mai girma ba ne da yawa, amma a yalwace yake. Komai fari tas a cikin falon, hatta curtains da kujerun leather duka farare ne kal-kal! Tana nan tana baza ido ta jiyo takun Aboulkhair yana saukowa, amma ba ta ji taku na bayan nasa ba, duk da cewa su biyu suke saukowa. His own steps ba ya making sound sabida babu takalmi a kafarsa. Kuma ma dai hatta tafiyarsu ta bambanta, taku yake kamar basarake.
Kallo daya ta yi masa ta ji ba za ta iya ci gaba ba, kada idanunta su samu rauni, ko nakasu.
Domin kwarai kwarjininsa da cikar zatinsa ya dusashe ‘yan idanunta. Ga wata irin kamala da charismatic personality. Da ganinsa ka ga ruwa biyu (Nigeria da Niger). Cikin iyayensa bai dauko mutum daya ba, mixed appearances dinsu ya debo sabanin Aboulkhair fari tas! Kalar abzinawa masu tarin sumar kai, Ishaq Raazee bakidaya.
Shi Mu’azzam kansa babu tarin suma, wani irin saisaye ne mai aji. Kananan kaya ne a jikinsa (farfetch) army green colour daga T/shirt har wandonta. Wani irin agogo daure a damtsen hannunsa mara walkiya, sai daukar hankali samfurin ‘Blooming Dale’s’ ruwan azurfa. Ya fi Aboulkhair tsayi, ya fi shi kauri. Alamu duk sun gama nuna mata he is living in an affluent life of the western world wanda a duniyarta ba ta san da irin rayuwarshi ba, ko mutane masu irin personality dinsa.
Duka wannan observations Aalimah ta yi su ne a kallon farko da ta yi masa, daga haka ba ta kara ba. Fargaba ma ta shiga ta yadda za ta bai wa wannan handsome GENTLE din tuwo, Aboulkhair ya fi ta gaskiya. Ji ta yi duk ta muzanta, ta soma Allah-Allah su bar gidan don ko a fuskarsa ba ta hango wani maraba da zuwanta gidansa ba.
Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta. Tana jin maganganun da suke yi shi da Aboulkhair sai Aboulkhair ya fadi biyar bai ba shi amsar biyu ba, kamar mai ciwon baki. A karshe ta ji zaman mutum a gefe ya ja kujera karama ya zauna yana fuskantarta. Kamar daga sama ta ji yana mata sannu da zuwa cikin harshen Hausa, sannan ya tambaye ta ya ya bakunta, kuma ya ta samu kanta a Las Vegas?
Zamowa ta yi daga kujera tana amsawa, sannan ta gaishe shi cikin nutsuwa.
Ya ce, “Koma kujera ki zauna, ni ba surukinki ba ne, dan uwanki ne. Ya ya Kawu Mansour, Mama Asi da Aboubacar?�
Mamaki kamar ya zauta Aalimah, sai kuma ta tuna su ma mutanen gidan nasu ai sun sanshi, har mamaki suke da ta ce ita ba ta sanshi ba. Kafin ta samu zarafin amsawa ya mike ya bi wata kofa. Sai ga shi da lemon Sangria Mocktail cikin kofin gilashi biyu, ya mika mata daya ya zauna da daya a hannunsa yana sha a hankali. Aboulkhair ya yi narai-narai da fuska, wai shi ba a ba shi ba.
Murmushi ya yi, ya ce, “Na dade da yayeka, ka bar ni in yi wa bakuwata barka da zuwa�.
Ita dai har zuwa lokacin duk da ya saki fuska yana kuma kulata ta kasa sakin jikinta. Ta rike kofin mai cike da kananan fruits kamar fruit-salad cikin ruwan grape juice, sanyinsa na ta ratsa tsokar hannunta. Sosai ta ke so ta sha ko don ta ji ya dandanonsa yake, amma ba za ta iya sha a gabansa ba.
Ya tambaye ta abin da ta karanta, ta gaya masa. Sai ya juya ya dubi Aboulkhair yana masa hararar wasa,
“Da ma kun zo garina ne don ku cika min gida da magani ko?�
Dariya Aboulkhair ya yi, itama tayi dan murushin abinda yace din, ya ce, “Da na rubuta zan bata ta hado in kawo. In har ita ma za ka nema mata ko cikin pharmacies din asibitinmu ne�.
Ya ce, “Wannan abu mai sauki? Ka ba wa Dr. Kennieth takardunta. Aalimah could you work at Las Vegas?�
Murmushi ta yi, ta ce, “In ya amince(tana nufin Aboulkhair)�.
Ya ce, “Karewar amincewa, ba ni na ce a nema miki ba? Youonly have to eradicate all kind of smiles from your lips, daga sanda kika fita har ki dawo aikin�.
Murmushi Mu’azzam ya yi kamar bai ji ba, ya soma duba agogo (kada su shiga lokacinsa). Aboulkhair ya janyo basket din nan gabansa, “Girkin dare ne amarya ta yi maka na neman albarka, ta ce in ka kasa ci in mare ta sau uku�.
Sunkuyawa ya yi ya bude yana murmushi, ya ce, “To zuba min in gani, ko Allah zai sa a yi marin amarya a gabana�.
Murmushi ta yi ta nade mayafi ta hau serving din, amma maimakon ta fara zuba masa, sai ta fara zuba wa mijinta, tukunna ta zuba masa. Mu’azzam ya lura da abin da ta yi, ya kuma yaba da hankalinta a ransa, “Miji first! Before anybodyelse�.
“Tastes good�. In ji Mu’azzam.
Daga haka bai kara magana ba sai empty plate ya ajiye wa Aboulkhair a kan cinyarsa,
“Ina ya kamata a mara kenan?�
Dariyar jin dadi Aboulkhair ke yi. Ya saci kallon Aalimah ita ma murmushin ta ke yi. Ya ce, “Ban taba ganinka kana cin tuwo ba ne shi ya sa na yi mata musu. Ko Mummy ce ta yi sai in ga ta maka wani girkin daban�.
Mu’azzam ya mike yana fadin, “Na gode da ziyara da girki mai dadi amarya Aalimah. Indeed bana son tuwo, amma na ji dadin naki, saboda kin yi shi da nutsuwa ga dukkan alamu. Kamar yadda na fahimci ke ma kanki mai nutsuwa ce. I wish you the best. Have a good stay in Vegas�.
Ya ciro biro ya yi rubutu a ‘yar takarda ya ajiye mata tare da wani dan kati, ya juya yana ce da Aboulkhair, “Na sallame ku, zan sha magani in kwanta gobe sammako zan yi zuwa seminar din nan da na gaya maka�.
Daga haka ya bi matattakala ya haye upstairs da tafiyarsa mai nutsuwa, wadda babu garaje a cikinta.
6/29/21, 9:00 AM - Buhainat: BEHIND
Aboulkhair ya damki hannayenta ya rike, ya ce, “Wuw! Thirty minutes cif ban kama Aalimah ta ba, gaskiya na yi kokari. Lets go tun kokarina bai tashi a banza ba, ya yi mantuwa ya dawo�.
Zame hannayenta ta yi, ta ce, “Da na sani ma kiss na yi maka a gabansa�. Ta yi gaba da sauri. Ta ma manta da abin da Mu’azzam din ya ajiye mata, ya dauko ya biyo ta da shi yana fadin, “Ka ji ta kamar gaske, alhalin ke kanki zama ki ka yi kamar wadda ta yi wa sarki karya a gaban nasa�.
Sai da ya tada motar ya dora mata katin da takardar a cinyarta. Credint card ne na bankin da Mummy ke aiki JP MORGAN CHASE da pin numbers din ya rubuta a jikin takardar.
“Ba ki ya yi, yarinya kin zama Madame, ki yi ta zara ana karowa duk wata. Ga shi ko shopping mall daya ba ki sani ba. In na koma hutu zan zagaya da ke ki ga gari, amma yanzu lalalala, sai na gama honeymoon dina�. Ya fada yana mai winking dinta. Murmushi ta yi, ta ce, “Ka ajiye a wajenka, ni ba abin da zan saya, beside komai nake so zan iya gaya maka�.
Haka suka yi ta musu, ta dage ba za ta karba a hannunta ba, ya dage nata ne shi ba zai mata ajiyar kudi ba, in Mu’azzam ya gani a hannunsa ba zai ji dadi ba. In ba abin da za ta yi da su din, ta kwashe ta tura wa Kawu Mansour ko mama Asi. Ta yarda da wannan shawarar.
Har suka zo gida Aalimah is very curious and questioning Aboulkhair a kan rayuwar Mu’azzam saboda al’amuransa bakidaya sun kara rikitata. Sun kara daure mata kai, mutum kamarsa mai cikar mutunci da kamala, ga rayuwar duniya Allah ya ba shi daidai misali, amma babu iyali, babu ranar zancensu? Kallon da ta ke masa daga nesa-nesa da ta zo kusa da shi ta ga ba haka ba ne. ba ta ga annoyance din a tare da shi ba banda ganewa da ta yi shi din is a very serious person, mai matukar tsantseni da lokacinsa. Mai girmama bako, mai tarin al’amuran yi fal a gabansa. Tambayoyin da ta ke yi wa Aboulkhair har ya rasa wanne zai fara amsa mata.
Tambayarta ta karshe ita ce, “Wane magani yake cewa za mu cika masa gida da shi? Maganin me yake cewa zai je ya sha ya kwanta?�
Aboulkhair ya sanya hannayensa biyu ya toshe kunnuwansa bayan ya kashe motar a ma’adaninta, ya ce, “Baby, ina da nawa matsalolin ki taimaka min in warware su. Sannan in waiwayi naki matsalolin which is MU’AZZAM. Na daya, hundred kiss at mouth, fifty at my nose, seventy at my tongue, eigthty at my eyes and two hundred at my neck. In kin gama wannan ki zo na yi miki alkawarin warware miki rayuwar Mu’azzam bakidaya, tun daga kuruciya har girma. Amma ko daya ki ka tsallake ina kirge da abuna, kin tsallake chapter daya cikin labarin Mu’azzam�.
Aalimah ta dora hannayenta biyu a ka tana fadin, “Na shiga uku! Mon Amour ka yi min sassauci, ba zan iya ba, and I really-really want to hear his story, amma haka zan ta binka ina sumbata kamar zan cinye ka? A tarihin gidanmu babu maye�.
Ya hadiye dariyar da ta ba shi, ya yi gaba yana fadin, “Za ki ga maita! Sai ki zaba ko maita ko labarin Mu’azzam�.
Ta ciji yatsa ta bi shi da gudu, suka shige gidan nasu. Ta riko hannunsa zai shige dakinsa, “Mon Amour ka saurare ni. Zan yi maka tausa dai kadai, Allah ba zan iya ba ina jin kunyarka�. Ta fada kamar za ta yi kuka.
Kwacewa ya yi ya shige yana fadin, “Ni fa na gama magana, ai it is an option, not a choice, ban ce dole ba, ki rike tausarki, in ita ce ina da injin da zai yi min. I just want to confirm I’m married to Aalimah Mansour, (kawai ina so in tabbatarwa kaina ina auren Aalimah Mansour) saboda har gobe ji nake kamar a mafarki… kamar za ki kubuce min Aalimah… kamar har gobe ban gama mallakarki ba. Kamar akwai wasu sauran gurabe cikin zuciyarki da ban kai ga isa ba�.
Intonation din da yake maganar da shi, da yanayin da ta gani cikin kwayar idanunsa su suka taru suka sukurkutata, suka rikitata, suka sa ta jin wani irin tsoro na ratsa ta. Sanda ta kankame shi ba ta sani ba… sanda ta soma rufe shi da sumbar a guraben da ya bukata da ma in da bai bukata ba, ba ta yi shawara da zuciyarta ba. Ba ta tuna akwai wata aba wai ita kunya cikin idanunta ba. Tun yana fadin, “Nice�. Ya koma, “Sweet�. Ya koma, “Splendid�.
Al’amarin da bai tuke a ko’ina ba sai a gadon barcinsu. Wata irin soyayya mai zafi da tsanani wadda a yau ba ta Aboulkhair ba ce shi kadai, 80% ta Aalimah ce da hobbasarta. Aboulkhair ya yaba, ya yi tukuici yadda ya kamata. Saida suka dawo hayyacinsu ya soma kyalkyala mata dariya. Ya ce ba wuya za a sayar da kanta a Las vegas. Shi duk abin da ya fada don ta yi masa abin da yake so ne, kuma ga shi ta yi.
“Ban da rashin wayo irin naki, wane gurbin ne ban kai ga isa ba? Yana ina? Nuna min shi�.
Hannayenta biyu ta kai ta rufe fuskarta, ya rungume ta tsantsan, ya ce, “Aalimah, Allah ya yi miki albarka, ya albarkaci rayuwarmu da ‘ya’ya masu irin tarbiyyarki, ba wata kubucewa da na yi tunanin za ki yi min banda ina so in koyar da ke yadda za ki tafiyar da ni. Kunyarki is too much… Ni kuma… ni kuma…�. Ya soma zagaye dan bakinta da yatsansa ibham, “…Ina so kullum in ji sulbinshi da sanyinshi da taushinshi kan fatar jikina. In ki ka yi min wannan kin gama min komai, kin kauda hankalina daga kowacce diya mace. Kin zama ni na zama ke, mun zama sirrin juna. Bude kunnuwanki in gaya miki ko wane ne MU’AZZAM???
LABARIN MU’AZZAM.
Wato tunda muka taso daga shekaru biyar a duniya zuwa sama, mahaifiyarmu ta dora mu a kan turbar duk abin da muke so sai mun same shi, kuma za ta iya samar da shi gare mu ta kowacce hanya in har hakan zai sa mu farin ciki. Tun muna kanana Mummy ta lalata mu da kashe kudi, a kullum tana gaya mana don mu ta ke aiki, burinta mu samu duk abin da muke so a rayuwa mu ji dadi a kasar da muke zaune, mu zama daya da ‘ya’yan turawa, mu manta da ‘yan kauyen dangin Daddy don ba kaunarmu suke yi ba. A cewar ta da ba su bar Nijar ba, da tuni sun raba ta da Daddy, saboda rashin son da suke mata. In za mu tafi makaranta haka ta ke damtso kudi ta ba mu, ta ce mu kashe duk da ga lafiyayyen abinci da abin sha ta cika mana lunch box da shi. Mu kuwa mu yi ta bushasha da abokanmu.
Duk kokarinta na hana mu yin abokai tana cewa, mu zama abokan junanmu kadai, abokai suna cutar da yaro ne kawai su canza masa tarbiyya. Wannan tsoratarwa ta Mummy ba ta yi wani tasiri sosai a kanmu ba, saboda muna neman wadanda za su taya mu cinye tulin kudin da ta ke ba mu ne, ba mu kuma san ya za mu yi da su ba. Abinki da makarantu na nasara masu tsananin kula da sanya ido, ba a dade ba school authority ta fahimci irin kashe kudin da muke yi a sayi banza sayi wofi, da irin abubuwan almubazzarancin da muke zuwa da su, ta yi wa Daddy magana. Ya kuma bincike mu kan inda muke samun kudi, inda ba tare da bata lokaci ba muka gaya masa Mummy ce ta ke ba mu. Don haka ya yi mata magana, ya kuma gaya mata tsawatarwar hukumar makaranta. Sabida haka Mummy sai ta koma sanya mana a jaka ba tare da sanin Daddy ba, ta kuma ce mu daina kashewa a makaranta sai mun dawo gida kafin ta dawo daga aiki.
Zancen nan da nake miki, lokacin mahaifinmu na aiki da consulate of Niger ne, ainahin aikin da ya kawo mahaifinmu kasar Amurka. Muna zaune a Washington D.C. Daddy ba wani babba ba ne a consulate din (diplomat officer) ne kawai, amma albashinsa dai mai tsoka ne, don a haka ya yi sponsoring karatun Mummy, har ta gama ba ta jima ba kuma ta samu aiki da daya daga cikin manyan bankunan kasar, wato JP Morgan Chase, matsayin akawu (Accountant) domin ta fito da digiri mai daraja ta farko, kuma a wannan zamanin samun aiki ga bakin haure bai yi wuyar da yake da ita a yanzu ba. Namu karatun kuwa ni da Mu’az ba shi yake daukar nauyinsa ba, ofishinsu ne. Don haka rayuwa muke cikin rufin asiri, ba mu nemi komai mun rasa ba. Da Mummy ta soma aiki sai muka koma cikin wadata fiye da baya, saboda duk albashin nata a kanmu yake karewa ni da Mu’az, suttura, kekuna, ciye-ciye da duk wani abu da yara maza masu shekaru irin namu za su bukata. Mummy ta sakar mana dukkan bakin aljihunta. Sai dai kuma aiki ya sa mun nesanta da juna, ita dai za ta ba mu kudi, ba ta damu da duk abin da muke ciki ba, ba ta san wace irin rayuwa muke yi ni da Mu’az ba idan ba ta nan tunda ta daukar mana house maid mai dafa mana abinci da kula da tsaftar jikinmu.
Kusa da gidanmu wani flat house ne, mallakin wani baturen Portugal da matarsa da dansa Clarson. Wannan yaron Clarson ya girmi Mu’azzam da shekaru biyar, amma haka ya shige jikin Mu’az suka zama abokai, ba komai ya sanya wa Clarson like wa Mu’az ba sai ganin gatan da yake ciki, da irin kudin da yake kashewa kullum, kekunan da yake hawa ma masu matukar tsada ne, ban da sitturunsa. Yayin da shi kuma Babansa giya yake sayarwa a wani Bar a nan cikin Washington. Lokacin da Mummy ta samu labarin alakar Mu’az da Clarson daga bakin mai aikinmu ta yi kokarin raba su, amma ta kasa saboda Clarson ya fi Mu’azzam wayo da budadden ido, don haka ya shiga jikinsa ba da wasa ba. Clarson shi ya koya wa Mu’az yadda zai dinga shan alcohol wadda babansa ke sayarwa, ya gaya masa ta fi komai dadi, kuma sai kana shanta ne ka ke zama babban yaro, wanda ya wuce kowa ya taka ka ko a raina ka.
A lokacin ni karami ne, ba su da mu da ni ba, ni ma kuma ban damu da abin da suke yi ba, shekaru biyar ne tsakanina da Mu’az, wadanda ya girme ni da su. Sannan Allah bai yi ni da daukar magana ba, ko iyayenmu in ba su tambaye ni abu ba, haka kawai ba za ka ji ina fade ba. I’m very quite tun ina karami, mara son kwaramniya da rashin hayaniya. A gidan su Clarson kuma a dakinsa suke consumption dinsu, wadda Clarson ke sayo musu wajen Babanshi da kudin Mu’az, da sunan aiko shi aka yi, kuma da yake yana taya uban kan sana’ar tashi wani lokacin ma shi yake zamar masa a bar din in zai je wani waje.
Clarson ko makaranta ba ya zuwa, neman kudi kawai ya kawo su Washington. Daddy bai samu gida a cikin Niger consulateba, amma consulatedin ke biyan hayar gidan da muke ciki. Kananan ma’aikatansu irin su Daddy kan zauna a cikin gari. Tun suna da shekaru kasa da sha biyar suke shan giya, sha na fitar hankali har Mu’azzam ya zama addicted.Daddy ba mazauni ba ne, haka Mummy, we spend 70% of our lives with a maid wata tsohuwar banasariya wadda abin da aka sanya ta kawai shi ta sa a gaba, wato kula da cikinmu da tsaftar jikinmu. Ta gaya wa Mummy yawan zuwan Mu’az gidan su Clearson tunda ta ja masa kunne ba ta dauki wani kwakkwaran mataki a kai ba. Ita ba ma rashin tarbiyyar Clearson ne damuwarta ba, kawai talaucin iyayensa ne, kuma dai ba ta son mu da abokai tun ba mu kawo lokacin ba. don haka Mu’az ya dade yana shan giya kafin Daddy ya ankara.
Watarana ne ya dawo gida ba lokacin dawowarsa ba. Mu muna hutun rabin zango a makaranta, shi da Mummy suna office. Ni kadai ya samu a gidan, Angela ta je cefane. Holiday assignment nake yi a falonmu. Ya tambaye ni ina Mu’az? Ba tare da na dago ba daga abin da nake yi, na ce da shi yana dakin Clearson.
Cikin mamaki ya ce, “Clearson yaron Mr. Ben?�
Na ce, “Eh, ai abokinsa ne�.
Firgicin Daddy ya kasa boyuwa, ya ce in tashi in raka shi har dakin Clearson din.
Ni ne a gaba, Daddy na biye da ni. Gidan a bude yake, kuma kamar kullum Mrs. Ben, wato mahaifiyar Clearson ba ta nan, ta tafi neman kudinta. Har dakin na raka Daddy inda ya gani, ganin idonsa Mu’az na kwankwadar beer. Ga kwalabe birjik mai nuna shan giyar ma na hauka suke yi. Mu’az ba ya ko iya bude idanunsa balle ya san waye a kansa. Haka Daddy ya sanya hannuwa ya dauko shi, ya saba shi a kafada yana hawaye muka dawo gida, ko kallo kwakkwara bai iya yi wa Clearson ba.
A wannan rana da Mu’az ya farfado ya ci duka a wurin Daddy, kamar ba zai barshi da rai ba. ya kuma yi threatening dinshi da maida shi Nijar, Nijar din ma Tessoua in bai daina ba. Amma Mu’azzam ya kasa dainawa, suka samu maboya shi da Clearson inda suke zuwa su sha, shan giya wanda ya wuce ka’ida da tunanin mai tunani. Giya kala-kala zafafa wadda ko manya ba sa ta’ammali da ita. Mummy kuma na ba shi kudin saye, mai tsada ta ‘ya’yan gata. Bayan lokaci mai tsawo Mu’azzam ya fara wata irin rashin lafiya kamar ba zai yi rai ba, wanda a binciken likitoci suka gano alcahol ta soma lahanta hantarsa da kwakwalwarsa.
Ita kanta Mummy hankalinta ya tashi, ta fara nadamar yadda ta ke ba shi kudin sayen giyar, ta san Mu’az yana shan giya, amma hakan bai taba damunta ba domin kuwa a can ba wani abu ba ne shan giyar, sai dai tana da masaniyar cewa it is wrong as well as prohibited a addininmu, kuma Mu’azzam ya yi kankanta da ya sha giya. Har a lokacin he is under eighteen. Al’adun nasara sun yi tasiri mai yawa a tare da Mummynmu a lokacin. Daga ita har Daddy babu wanda ya taba tunanin sanya mu a islamic school, duk da cewa ga su nan birjik a ko’ina na kasar nan. They only show us yadda za mu yi sallah, in Daddy yana gida yana sa mu a gaba mu yi tare, maghriba da isha. Da asubah ma yana tashinmu mu yi tare, amma kin ga azhar da la’asar ba kullum muke tunawa mu yi ba, musamman bayan haduwar Mu’az da Clearson. A wannan lokacin Daddy ya soma neman aiki wuri-wuri don dai ya raba Mu’azzam da Washington ya samar masa sabuwar rayuwa, bayan shafe shekaru goma a Niger Consulate of America, ya samu residence permit. Wannan ne dalilin barinmu Washington zuwa nan Boston (Massachusetts).
Daddy ya samu aikin gwamnati (permanent) a jihar Massachusetts, muka tattaro muka dawo, wannan ne ya raba Mu’az da Clearson. Sosai Daddy yake jan Mu’az a jiki bayan samun saukinsa, yana nuna masa illar giya da haramcinta a addininmu. Aka yi nasara Mu’azzam ya bar shan giya, amma sai ya fara wasu bakin halaye.
Abu kadan sai ya fusata shi, in ya yi fushin kuma he will destroy everything behind him, no one in the house can control his temper, not even me da yake matukar so. Komawa yake tamkar bai san kowa a cikinmu ba, burinsa ya lahanta komai da hannunsa zai iya kai wa. In yana cikin wannan halin Mummy ba ta iya komai, sai kuka. Daddy kan kama shi ya matse ya rungyme shi ta karfi yana gaya masa kalamai na kwantar da hankali, yana tofa masa addu’a. Da abin ya fi karfin Daddy, sai ya kai shi asibiti, inda da gaggawa suka yi referring dinshi zuwa Psychiatric.
A can ne bincike da gwaje-gwaje suka nuna yana da aggressive tendencies, wanda shan giya ya haifar cikin neuron dinsa. Ya soma karbar treatment yadda ya kamata. Sosai ya nutsu, ya koma yadda yake tun kafin ya san mene ne giya.
A Massachusetts Mu’az ya maida hankali ya gama karatun sakandirensa da takardu masu kyau, ya kuma zabi jami’ar Nevada ta garin Las Vegas ya fara karantar Petroleum Geology. Ya kama karatunshi sosai don a lokacin yana da shekaru ashirin da biyu, ya yi hankalin sanin abin da zai amfane shi, da abin da ba zai amfane shi ba. Yana shekararshi ta karshe a jami’a ya hadu da wata kaddarar bayan Clearson wato JUWAIRA.
Ni kuma a lokacin ne na fara jami’a a Louisiana, ba don komai ba na ki bin Mu’az Vegas ba, sai don ba abin da na tsana irin ganin Mu’az cikin black opisodes dinsa na aggressive temper. Abu ne da ke tayar da hankalina matuka, ya sa ni takurewa a gefe ina kuka.
Yana gama degree Daddy ya shiga nema masa aure ba da saninsa ba, daga dangin Mummy don ta ce ba ta yarda ya nemo a nasa dangin da ba kaunarta suke ba.
A ganin daddy, aure zai sassauta masa wannan ciwon fushin, bayan magani. Ashe shi Mu’az yana da wadda yake so, wato Juwaira. Iyayenta haifaffun kasar Ethiopia ne, zama ne ya kawo su America. Mu’azzam ya so Juwaira kamar ransa. Kafin Daddy ya furta masa niyyarsa na yi masa aure da cousin dinsa Halima, shi ya bayyana masa maganar Juwaira. Abin da Daddy ke so kawai shi ne kwanciyar hankalin Mu’az, don haka ya bar maganar Halima ya durfafi nema masa auren Juwaira, amma kememe iyayenta suka hana shi ita saboda akidarsu ta bambancin kabila, wato racism. Duk wani kokari Daddy ya yi don ya samar wa Mu’az auren yarinyar, amma bai yi nasara ba, iyayenta sun ki amincewa. A cewarsu ‘yarsu ba za ta auri dan Nigeria ko Niger ba, sai Ethiopian dan uwanta, kada ‘yarsu ta bace a wata kasa. Daga karshe ma suka dauke ‘yarsu daga America suka yi gaggawar yi mata aure a Ethiopia. Suka yanke mata karatu saboda Mu’az, don ita ma yarinyar tana sonshi sosai.
Lokacin da Mu’azzam ya samu labarin auren Juwaira da dauke ta da iyayenta suka yi zuwa kasarta ta haihuwa, he became frustrated, very tempered. Sai wannan dabi’ar tasa ta fushi da aggressiveness ta dawo sabuwa. Komai ya daina sa shi farin ciki. Not even me, neither our parent. A yayin da yake cikin fushin nan ba wanda ya isa ya zo kusa da shi. When he is frustreted nobody can come close to him. Ba ya duka, ba ya zagi, amma zai farfasa duk wani abu da zai iya fasuwa da yake gefensa, ya ji wa kansa ciwo, ya janyo wa Daddy asara mai yawa na gilassan gidan.
Mummy ta riga ta raine mu da cewa, duk abin da muke so za mu samu, ba ta taba zaunar da mu ta nuna mana hakuri da kaddara ba. Wannan ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar Mu’azzam. Hatta karatun addini sai da girmanmu muka koye shi, bayan dawowarmu Massachusetts ne ganin abin da ya faru da Mu’az ya sa Daddy ya sanya mu a islamiyya, wadda muke zuwa bayan mun tashi daga boko, maimakon mu zauna a gida kamar yadda muke yi a Washington tun muna kanana. Sai Allah ya so mu da rahamarSa, kwakwalenmu masu zafi ne, ba mu sha wahalar fahimtar karatun addini ko kadan ba, a wata babbar islamic school mai lasisi a kasar ta Amurka. Wadda Larabawan kasar Morocco ne suka bude ta.
Auren Juwaira ya tabarbarar da lafiyar kwakwalwar Mu’az a karo na biyu, abin da ya tada hankalin Daddy ya dawo da tsohon zancensa na aura wa Mu’az cousin dinsa Halima, a ganinsa auren shi zai daidaita Mu’azzam.
Daddy bai san cewa, son aure daban, soyayya daban ba. Mu’az ba aure ya damu ya yi ba, Juwaira yake so.
Auren Juwaira shi ya tado matsalar Mu’az ta zama sabuwa sharr! Watansa guda a psychiatric yana karbar magani kafin ya manta da Juwaira, ya koma normal life dinsa. Ya kuma nemi (MBA) a nan Nevada (Las vegas) a jami’ar da ya yi ya soma karatun (MBA inOil and Gas Management) tsayin shekara daya, ya gama cikin tarin nasara, domin hakika shi din gifted ne, irin jajirtattun mutanen da ba su da yawa a cikin al’ummah.
Ashe karfin kwayoyi ne kawai ya binne Juwaira daga zuciyar Mu’az, da ya samu labarin haihuwarta wajen wani makocinsu, sai abin ya dawo sabo. Sabida duk cikin wannan lokacin da ya samu nutsuwa jira yake Juwaira ta kaso aurenta ta fito daga gidan mijinta su yi aure. Haihuwarta da ya ji kuwa ya tabbatar masa Juwaira ta daidaita da zabin iyayenta, ba ta da sauran abin da za ta ba shi.
Aggressive tendency din ya motsa. Sai da ya kara kwanciya a asibiti, aka kara kokari ya dawo daidai, likitocinsa kuma suka bada shawarar a yi masa aure da gaggawa zai rage masa frustration din Juwaira da ke damunsa. Ba tare da bata lokaci ba aka yi auren Mu’az da Halima, aka taho da ita gidansa a Las Vegas.
Ranar da aka kai masa Halima a matsayin matarsa, a ranar ya samu labarin rasuwar Juwaira da iyayenta, a dalilin hadarin jirgin sama.
Bayan Mummy da Daddy da suka kai ta sun musu nasiha sun juyo ne aka yi masa wayar aka fada masa. Gabadaya sai kansa ya juye, ga Halima zaune a gefensa, ya kasa yarda da abin da aka gaya masa. ya juya yana kallon Halima da rinannun idanunsa kamar ita ce sanadin mutuwar Juwairan. Duk wani anger, duk wani temper, duk wani frustration dinsa na lokaci mai tsawo ya sauke su ne a kan yarinya Halima ‘yar shekaru goma sha bakwai. Bai taba zina ba, bai san neman mata ba, bai san ya ake yi ba, don haka aggressiveness dinsa na ranar maimakon fashe-fashe ya kare ne a kan Juwaira a matsayin auratayya ba tare da wani feeling ko kankani game da yarinyar a zuciyarsa ba.
Sai bayan ya fara dawowa hayyacinsa ne ya lura yarinyar ba ta motsi, ga ta kuma cikin jini face-face. Mummy ya kira, ya ce su zo su dauke wannan yarinyar da suka kawo masa, kawai don ya yi having sex da ita sau daya ta mutu.
Mummy da Daddy suna hanya ba su kai ga isa Massachusetts ba daga kawo masa Halima da suka yi wayarsa ta riske su. Hankali tashe suka juyo duka dawo. Suka shirya Halima suka kai ta asibiti, likitoci kin karbarta suka yi, suka ce rape case ne wannan,rape din ma wanda akayi da karshen rashin imani, sai police sun shigo ciki, duk da rantsuwar da suke musu na cewar matarsa ce, da marriage certificate, wanda Daddy ya yo musu daga Nigeria, kin yarda suka yi. Wane miji ne zai yiwa matarsa haka? Sai da police suka shiga sannan suka karbe ta, suka shiga kokarin nemo numfashinta.
Kin san Bature da rape case ba sauki, balle baturen Amurka. Shi ma Mu’az din nasa likitocin sun rike shi don sun ce za su kara bincike a kansa da Daddy ya kira consultant dinsa ya gaya masa abin da ya faru. Report din asibitin Mu’az shi ne kadai ya cece shi daga wannan lamari, da tuni ya kare behind bars, saboda ba’a shari’a da maipsychologicaldisorder kowanne iri, balle Mu’az da ya dade a cikinta.
6/29/21, 9:01 AM - Buhainat: KWATARKWASHI
Pg 100
Alhamdulillah, Halima ba ta mutu ba, amma tana samun kanta ta kafawa su Daddy kuka da tashin hankalinsu maida ita gaban iyayenta. In taga Mu’azzam kamar ta ga mala’ikan daukan ranta. Aka yi-aka yi kuma Mu’azam ya sake ta, ya ce shi yanzu ya fara aure. Ba wanda ya isa ya sa shi sakin Haleemah. Yana zamansa lafiya aka yi masa aure ba da yawunsa ba, sai da ya samu hanyar ajiye temper and frustration mafi sauki, sannan a zo a ce za’a raba aure? Da ya san haka auren yake da dadi ai da tuni ya dade da yinsa. A karshe da result din Mu’az na karshe ya fito, dole Daddy da Mummy suka dauke Halima daga Las Vegas suna kuka.
Result ya nuna bayan aggressive tendencies Mu’az na da lalurar hyper sexuality disorder wanda aka fi sani da compulsive sexual behaviour. Wadanda duka su biyun (aggressive tendency and hypersexuality disorder) alamomi ne na bipolar da kuma hypomania.
Amintaccen likitansa shi ne Dr. Nebrass, wani gawurtaccen neuro-psychiatrist ne da ake ji da shi a Amurka. Shi ke kula da komai na Mu’azzam. Ya gaya wa Daddy cewa, su kwantar da hankulansu ganin yadda suka fita hayyacinsu da jin wannan sabon sakamako na Mu’azzam, wanda duka alcohol ita ce sila, wato giya. Ga wasu victims din kuma drug addiction ne.
Dr. Nebrass ya gaya wa Daddy cewa, kamar yadda aggressive tendencies can be controlled by drugs and other clinical therapies shi ma compulsive sexual behaviour (hypersexuality disorder) can be controlled and monitored, kuma mutum ya zauna lafiya tamkar sauran mutane masu lafiya muddin an kiyaye shan magani. It’s a neurological disorder da za a iya magance ta ta hanyar amfani da kwayoyin ‘Anti-Androgens’, and mood stabilizers medicines, su wadannan kwayoyi na Anti-Androgens, suna kashe tasirin Androgens, wato sex hormones a jikin dan Adam mai fama da wannan lalura kuma suna taimaka wa wajen rage sexual urges, wato sha’awar jima’i.
Mutane masu fama da wannan lalura ta hypersexuality disorder (compulsive sexual disorder) suna amfani da sex as a quick fix to relieve anxiety, loneliness, pains, aggressiveness, frustration and other forms of stress without regard to potential consequences. It’s characterized by abnormal sexual drive and difficulty in forming emotional connections, e.g marriage and family life to the extent that the behaviour interferes with work, health, relationships, family and other normal activities. They use sex as an escape behaviour. They have intense sexual impulse. And the episode have to last over size months before it can be diagnosed. Drinking alcohol triggers the problem and increase aggression. (fasara; mutane masu fama da compulsive sexual disorder suna amfani da sex matsayin hanyar farko ta samun sauki daga tsoro, kadaici, zafin zuciya, radadin zuci, bacin rai da sauran stresses ba tare da la’akari da abin da hakan zai haifar ba. Ta yadda har hakan zai shafi ayyukan neman abincinsu, lafiyarsu, mu’amalolinsu, iyalinsu da sauran abubuwa na yau da kullum. Halayensu shi ne abnormal sexual drive wato yawan saduwa wanda ba a saba da shi ba, ko wanda ya wuce kima, shan wahala wajen gina soyayya a zukatansu (kamar soyayya ta aure) da gina iyali. Abin da suka fi maida hankali a kai shi ne, having sex to relieve their stresses and pains. Sai dai duka wannan ana iya magance shi da kwayoyin Anti-androgens da kuma mood stabilizers medicines, mara lafiya ya zauna lafiya cikin kyakkyawar rayuwa kamar kowa.
To kin ji Aalimah, wannan ita ce rayuwar Yayana Mu’azzam. Yau shekara goma kenan yana rayuwa cikin shan kwayoyi domin danne sexual urges tare da kuskurewa ba. Ko da aka tilasta masa ya saki Halima ya sake tan, amma ya gaya wa su Daddy kada wanda ya kara dosarshi da zancen aure kuma kada wanda ya kara yi masa aure ba tareda saninsa ba. Yana jin dadin rayuwarsa a haka, and he’s making it profitable. Kwayoyin anti-androgen suke hana Mu’az sha’awar aure kwata-kwata. He cannot even develop emotion balle ya ji yana son wata mace a ransa. Bayan gama MBA dinsa ya samu aiki da kamfanin man fetur na farko a Amurka, wato CHEVRONCORPORATION sun barshi a reshensu na Las Vegas inda yake zaune ya kasa barinta. Akwai sanda aka yi masa sauyin wajen aiki zuwa jihar OHIO amma Muazzam bai yi kaura ya koma can ba. Kullum zuwa yake ya dawo a jirgin kasa, ko ya je ya yi sati biyu ya dawo. A cewarsa Las Vegas is where all the memoirs of his adulthood began..... He cannot go far from it.
Ta canza shi daga spoilt, drunkard Mu’azzam, zuwa matashin da ya san ciwon kansa, ko kusa Mu’azzam ba ya son shiga mutane, har family dinsa kuwa, ya fi son rayuwar da yake yi ta kadaici da maida hankali ga ibadah wadda a shekarun teenage dinsa bai samu alfarmar yi ba sai shan giya. Sai kuma dedication ga aikinsa, saboda bai da wani abin yi mai muhimmanci bayan shi. Kamfanin chevron na ji da Mu’azzam fiye da zatonki, saboda yana daga cikin masu habbaka su da kawo musu innovations.
Tunda na shiga shekarun da na fara hankali, na kuma kai ga fahimtar matsalolin Yayana Mu’azzam na yi kudurin zama neuro-psychiatrist saboda in kula da shi a sauran rayuwarsa… Ina so in canji Nebrass in zamo ni ne mai kulawa da shi ba wani ba. Mu’az bai fiya zuwa Boston ba (Massachusetts) mu muke zuwa inda yake. Mummy ta fi kowa zuwa akai-akai, saboda a yanzu tana jin kanta culprit na duk irin rayuwar da Mu’azzam ke yi a yanzu, tana zuwa ta yi kwanaki tare da shi, a kan idonsa aka haife su Basma daya bayan daya, amma babu wata shakuwa a tsakaninsu, ba ya jansu a jiki, ba ya shiga sha’aninsu, tun suna damuwa har sun daina, sun fidda shi a jerin ‘yan gidan. Khaleesat kan ce ba iyayensu daya ba, he’s adopted. Wato dan tsintuwa ne. Sai dai duk da haka har gobe ba su san matsalarshi ba an barsu a yadda suka dauke shi din saboda a shekarunsu da matakin ilminsu ba za su taba fahimtar matsalarsa ba.
Ki taya ni addu’a Aalimah, Allah ya cika min burina in zama ni ne consultant din Mu’azzam Raazee, in ci gaba da zama tare da shi har karshen rayuwa ta…�
Sai a lokacin Aboulkhair ya lura matarsa Aalimah kuka ta ke yi, tunda ya yi nisa a ba ta labarin Yayansu Mu’azzam. Kukan kuma ba na komai ba ne, na tausayin Mu’azzam ne.
Murmushi ya yi ya ciccibe ta ya yi dakin barcinsu yana fadin, “My easily crying wife, da na san labarin hawaye zai fiddo daga idon matata da ba’a fara shi ba�.
Rungume shi ta yi sosai tana ci gaba da kukan, ta ce, “Insha Allah kai za ka koma kula da Mu’azzam, ina rokon Allah Ya cika wannan burin naka�.
******
Sabida yadda labarin Mu’azzam da tausayin shi ke tsunkulinta a zuci, kwananta uku ba ta walwala.
Jin labarin nasa maimakon ya kwantar da kishirwarta a kan saninsa, sai ya tafi ya bankado wasu sababbin inquisitivities din cikin zuciyarta a kan rayuwarsa. Sai dai tana ganin ya kamata ta kyale mijinta haka a kan dan uwan nasa kada ta wuce makadi da rawa. Ya gaya mata abin da zai iya kuma a matsayinsa na likita akwai abin da ba zai iya fada ba a kan patient dinsa, wani abin sirri ne tsakanin likita da patient dinsa kadai.
Ranar da Aboulkhair zai koma aiki ya ce da ita ta sake yin tuwo in ya dawo ya kai wa Mu’az, tunda ya nuna ya yaba, kuma yana so. Da karsashi da karfin gwiwa ta yi sallelen tuwon semo da miyar kuka wannan karon, yana dawowa ko hutawa bai yi ba ya dauka ya kai masa. Da ya dawo yake ba ta labari Mu’azzam ya ci tuwonta sosai fiye da na ranar da suka je, ya ce ya yi mata godiya, amma ya daina wahalar da ita ya barta ta dinga hutawa. Saboda shi ya dauki girki wajen mace wani abu mai matukar wahalarwa a gare ta ya fi dacewa da maza (a cewarsa).
Dariya ta yi, ta ce, “Ashe da zai yi aure da matarsa ta huta�.
Ya ce, “Sosai ma kuwa, in dai ta fannin girki ne, ko Mummy ba ki ga yadda suke kai ruwa rana ba in ta zo, she want to cook for him, a wurinta abincin gida ya fi na restaurant gamsarwa, a wurinsa hakan bautar da mace ne, musamman ita da shekarunta suka soma turawa�.
Watanni uku cif! Da auren Aboulkhair da Aalimah, Mu’azzam ya yi kokari ya samar mata aikin da ya yi alkawari a asibitin da mijinta yake.Sabida tana zaune a gida bata komai. Wani pharmacy suka tura ta a babban reshensu wanda shi ba asibitin kwakwalwa ne kawai ba, babban asibiti ne General hospital da ya kunshidepartments na kowanne bangare. Sun tura ta wani pharmacy dinsu a Ophthalmology department (bangaren harhada magunguna a tsangayar ido). Kowanne bangare na asibitin akwai pharmacy a cikinsa, don haka duk inda ka ke so a nan za ka sayi magani cikin katafaren asibitin.
Don haka kullum Aboulkhair sai ya fara sauke ta, ya raka ta har cikin ofishinta, ya cire mata abaya ya dora mata farar rigarsu damini hijab dinta da ba sa hana ta sakawa sabida kare martabar addininta, ya rungume ta ya sumbace ta, sannan yake tafiya.
Idan ya riga ta tashi zai zo ya jira ta har ta tashi, sannan su tafi gida. Idan akwai abin da za su saya su biya kasuwa, sannan su karasa gida. Idan kuma ita ce ta riga shi tashi komai dadewar da zai yi haka za ta zauna ta jira shi. Son juna suke kamar su hadiye junansu, ba sa taba gundura da juna. Soyayyarsu mai ban sha’awa da tsafta, wadda duk inda suka zauna sai ta fallasa kanta.
Tun zuwanta gidan Mu’azzam na farko, ba ta kara yarda ta bi Aboulkhair ba, shi kadai yake zuwa. Ta yarda kin mutane da Mu’azzam ke yi, yana da nasaba da mental state dinsa. Da ace za’a bata dama, da ta zauna dasu Basma ta fahintar dasu wanene Yayan su Mu’azzam? A yanzun sun mallaki hankulan kansu sunyi ilmi mai zurfi, sosai zasu yi masa uzri, su bude zukatansu su bashi gurbi. Gurbi na dan uwa mai tsananin kirki kamar Aboulkhair. Maganin wata guda Aboulkhair ke kai masa. Har ta haddace magungunan Mu’azzam don ita ke hadowa ta ba shi. Dose da mgduka ta rike. Rannan yake gaya mata babban likitan Mu’az ya ce zai kara karfin mood stabilizers dinshi, don a samu ya riki wasu al’amuran na social life bayan aiki da ya kwallafa kafatanin rayuwarsa a kansa. Ba ya tunanin kowa, ba ya tunanin komai, babu kowa babu komai a zuciyarsa sai proffession dinsa.
Mummy Zulaiha hankalinta ya dada kwanciya ganin cewa, Mu’azzam ya samu ‘yan uwa a garin da yake, duk da ba gidansu daya ba, ta san ko ya ya ne za su taimaka masa ta wani fannin. Ba zasu barshi cikin ragaita da zaman kadaicin nan nasa ba koda baya so.Ta san cewa, kulawar lafiyar tasa bakidaya ma yanzu a wuyansu ta ke ba.
Aalimah Mansour, na tsaye tana kare wa dan kyakkyawan ofishinta kallo, tana kuma kallon alert na damin kudin da ya shigo mata daga bankinta WellFargo, wai duk wannan albashinta ne na farko. Iyayenta ta shiga yi wa addu’a ba ji ba gani, har Daddy Ishaq ba ta cire cikin addu’arta ba. Wadanda suka tsaya tsayin daka tayi ilmin da ya bata wnnan matsayin. Fitowa ta yi ta rufo ofishin zuwa Atm mafi kusa ta yi wa Daddy transfer na gabadayan kudin, ko dala guda ba ta rage ba, ta hanyar western money transfer. Kudin na shiga Dr. Mansour ya kira Aalimah.
“Kudin me ki ke ta turo mana ne kamar wata ma’aikaciya? Kin yi ya kai sau hudu ina shiru, na yau yafi na baya, ina ki ke samu? Aalimah kada ki kasance cikin masu dora wa mazansu hidimar da ta fi karfinsu don ki wadata iyayenki. Mu din we’re contented with our life ba mu nemi komai mun rasa ba, Aboulkhair me ya tara, yaushe ya fara aikin da ki ke kwakularsa wadannan makudan kudaden?�
Dariya Aalimah ta yi, sannan ta soma yi masa bayani, cewa kudin farko, na biyu da na uku duk Mu’azzam ke saka mata cikin ATM don ta yi lalurorin gabanta ba tare da ta roke shi ba. Ita kuma ba ta da bukata shi ya sa ta tura musu. Na yau din kuwa halak dinta ne, guminta ne, albashinta ne na aikin da Mu’azzam ya samo mata daDesert Parkway Health Center.
Dr. Mansour kasa magana ya yi, akwai matashi mai zuciyar riko da zumunci a duniya irin MU’AZZAM ???
“Yaa Allah ka dubi wannan bawa naKa da tarin alherinsa da jin kansa ga ‘yan uwa da sauran al’umma, Ka ba shi lafiyar da ka ke jarrabtarsa a kanta, ya yi rayuwa mai dadi kamar kowanne dan Adam�. Addu’ar da Dr. Mansour ya shiga yi wa dansa Mu’azzam kenan, wani Da mafi soyuwa a zuciyarsa cikin dukkan ahalin Raazee, manyan su da yaransu.
*****
Shekaru guda biyu kwarara kenan da wannan aure mai dumbin albarka, wanda ya zamo wani tubali na hadin kan iyalin Malam Ibrahim Raazee bakidaya. Ya kawo alheri mai yawa ga kowannensu. Duk weekend Aalimah da Basma na rike da juna a kan waya, sabida a weekend din kadai ta ke samun lokacin gaisawa da ‘yan uwa da iyayenta, saboda yanayin aikinta da hidimar Aboulkhair da ba ta karewa. Shagwababbe, cingam, super glue din Aalimah, dan gatan Engnr. Mu’azzam Raazee. A karshen shekarar Aboulkhair ya koma John Hopkins University ya zana jarrabawar part 2 dinsa. Ba da jimawa ba sakamako ya fito, ya cinye komai da wata irin madaukakiyar nasara, ya dawo asibitinsu inda aka canza masa ofis a matsayinsa na cikakken consultant (Neuro-Psychiatrist) a halin yanzu.
A wannan lokacin ne Dr. Nebrass likitan Mu’azzam na shekaru masu yawa da suka gabata ya danka wa Dr. Aboulkhair Raazee kulawar dan uwansa Mu’azzam bakidaya, ta hanyar damka masa file dinsa sabida shi kansa jinjinawa kwarewa da fasahar Aboulkhair yake yi, kamar wanda ya shekara goma yana practicing. Bai sani ba, hakan na da alaka ne da zuciyar ‘yan uwantaka da shakuwa wadda aka gina karatun kacokam a kanta, sannan shi din shekarunsa na komawa gida ya huta (retire) sun cika.
Zuwa wannan lokacin Daddy Ishaq ya gama komai na shirin komawarsa gida Niger da iyalinsa mata bakidaya. Abu daya yake jira su ajiye ayyukansu su koma (takardar daukarsa aiki da ministere des affaires etrangeres), wato ministry of foreign affairs, hukumar hulda da kasashen waje ta kasar Niger mai location a babban birni Niamey, wadda wani tsohon abokinsa ma’aikaci a wurin da suka yi aiki tare tun a Niger Consulate America yake ta kokarin nema masa.
Sun hadu ita da su Mummy a Massachusetts sun je wa Aboulkhair jami’ar John Hopkins har can garin Baltimore (Maryland) ranar da ya karbi shaidarsa ta zama consultant, tare da shi suka taho Boston. Kwanansu biyu da iyayen nasu da kannensu su Khaleesat wadda ta gama karatunta ita ma a wannan shekarar, suka koma gidansu.
Kafin su shiga gida ya ce, lallai wannan karon sai sun je ta gaida Mu’azzam. Zuwanta daya a kulliyar zamanta cikin garin da yake, sai dai in suna waya da Aboulkhair yakan ba ta su gaisa a gajarce. Ita girmansa da respect dinta gare shi ke hana ta sakewa da shi, a wani bangaren kuma tausayinsa bakidaya. Yayin da shi kuma a nasa bangaren da ma ba ya sakewa da kowa sai Aboulkhair, sai kuma Daddy da kaninsa Mansour Raazee, da kuma kakansa mai ran karfe. Ko Mummy ba ruwanta da rayuwarsa. In ka ji suna magana mai tsawo, to nata matsalolin ne da ta ke neman ya taimaka mata ta fita daga cikinsu. Da shawarwarin Mu’azzam ne ta tabbatar a yanzu ta zauna lafiya cikin sukunin zuciya da kyakkyawar mu’amala da kishiya da dangin mijinta, mutuncinta ya dawo cikin idanunsu.
A halin yanzu ma ta neme shi kan babban kalubalenta na yanzu (barin aiki da Daddy ke so ta yi su koma gida). Tana cikin damuwa da hakan matuka. Abin da Mu’azzam ya ce da ita shi ne, “Mummy me kuma ki ke nema a rayuwa? Kin aurar da duka manyan ‘ya’yanki bayan kin ba su wadataccen ilmi, nan da shekara daya za ki aurar da wadda ta saura. Kudin da ki ka tara shekaru masu yawa ki ka ba ni, ki ka ce in sayi gida in bar rent, gaya miki ne ban yi ba, hannayen jari na siya miki da su a manyan bankunan Nigeria da Niger. A yanzu haka gidan nan da nake ciki mallakina ne, na dade ina biya da kadan da kadan na kuma hada da wani kaso kadan daga wanda ki ka ba ni. Don haka don Allah Mummy ki yi wa mijinki biyayya kamar yadda ki ka saba, ke ma ki zauna waje daya ki huta kamar kowacce matar aure ki fara rainon jikoki da tarbiyyarsu. Aboulkhair ya gaya min Basma ta kusa haihuwa, shi ma tashi matar ta samu yanzu, ga Khaleesat za ta shiga daga ciki ita ma. Mummy you are blessed ki kara gode wa Allah, ki koma neman lahira. Na yi miki alkawarin 40% na albashina duk wata�.
Kuka Mummy Zulaiha ta saka, abin da Mu’azzam ba ya so daga gare ta.
“Mu’azzam ban san da wane harshe zan daina cewa ni na jawo rushewar farin ciki da cikar rayuwarka ba. Ba zan iya daina cewa ka yafe min ba! Ka ambaci kowa zai haihu ban da kai, Mu’azzam naka na fi son gani. Mu’azzam ka taimaka min in sake yi maka aure ko me zai faru. Ni ban yarda da kafiran nan ba, namu addinin ya ce kowacce cuta tana da magani, Malam Raazee da kawunka Edrissa sun ce za su nemo magani…�
Ta ci gaba da kuka sadidan fiye da wanda ta ke yi a baya.
Mu’azzam ya dafe kansa da hannun damansa, jijiyoyin kansa na sarawa. Da kyar ya ce, “Mummy ki daina maganar nan don Allah. Na riga na karbi kaddarata da hannu bibbiyu. Mummy I don’t have a feeling to give to a woman. Mummy aure is not about having sex and children only, there’s a matter of LOVE and AFFECTION. And Mu’azzam don’t have any, not even a remnant. Ki sa a ranki ‘ya’yan Aboulkhair da Basma ‘ya’yana ne da na haifa tunda in an tsaga jikinsu za a ga jinina. Mummy please..... ki daina kukan nan, kina tayar min da hankali. In Aboulkhair ya san abin da ki ke gaya min zai hana ni yin waya da ke…�.
Alamun zaman mutum ya ji a kusa da shi, ya daga idanunsa da suka rine da sauri ya dube shi, Aboulkhair ne.
Gabadaya yanayinsa ya canza, bacin rai da tashin hankali sun bayyana karara a kyakkyawar fuskarsa. Idanunsa sun kada sun yi jazir. Mummy ba ta kyauta masa ba. Yana tufka tana warwara, maimakon ta shanye damuwarta ita kadai, ko shi ta kira shi ta yi masa. Me Mu’azzam zai maganta mata ban da ta kara masa damuwa, yana fama da jinyar tashi zuciyar da kwakwalwar? Mu’azzam din ya kamata ta gaya wa halin da ta ke ciki a kansa?
Mikewa ya yi zai fita, Mu’azzam ya rike shi yana daga zaune. Bai iya ya juyo sun hada ido ba saboda idanunsa da suka cicciko da hawaye. Murmushi Mu’azzam din ya yi duk da idanunsa sun kada, ya ce, “Ina ruwanka da hirata da uwata? Wato labe ka koma? Kuma meye laifi don ta yi sharing damuwar zuciyarta da ni?�
Ba tare da ya juyo ba ya ce, “I’m your doctor. Not a brother. I’m responsible for all the progress and the downfall of your health. Da ni ya kamata ta tattauna abin da ta ke tattaunawa da kai. Mummy ba ta kyauta min ba! Damuwa da tunani suna hana mood stabilizers aiki yadda ya kamata. Kuma na san abin da zan yi�.
Ya kwace hannunsa zai fita. Mu’azzam ya daga murya ya ce, “Aboulkhair uwata ce fa! Za ka hana ni magana da ita ne? Ka shiga hankalinka kai da likitancin naka. Rayuwa da ciwo duka a hannun Allah suke. Idan Allah ya ce ma mutuwa zan yi dukkaninku ba abin da za ku iya. Ni gara ma in mutu in huta da wannan rayuwar…!�
Da gudu Aboulkhair ya dawo ya rungume shi. Hawaye ya soma yana fadin, “Insha Allahu kai za ka binne ni, ba dai ni in ga kabarinka ba Mu’az, ba zan iya jura ba. Zan yi abin da ya fi hauka, ba zan iya rayuwa ba, na roke ka kada ka kara yi min wannan fatan�.
Ya dago shi ya zaunar kusa da shi, yana bubbuga bayansa.
“Na ji ba zan kara ba. Amma kada ka kara fadin in ba ni ba za ka iya rayuwa ba. kowanne rai sai ya dandani mutuwa Aboulkhair. Abin fatan shi ne mu cika da kyau da imani. Ka yi wa Mummy uzuri kada ka ce mata komai a kaina.
Ta hanyar expressing griefs and sorrows dinta (bakin cikinta) a kaina ne kadai za ta samu sassaucin tata zuciyar. Ni ne mai ciwo Aboulkhair, amma UWA ta fi ni ji a jikinta. Yanzu tashi mu je kasa in ba ka Sangria Mocktail (Non-Alcoholic fruit drink) ka sha, ka kai wa matarka ita ma. Dazu na yi order dinsa�.
Murmushi Aboulkhair ya yi, kaunar Yayan nasa na kara keta zuciyarsa. Ya san so yake ya gusar masa da bacin ransa. Sai a lokacin ya tuna tare da Aalimah yake ya barta a falon kasa.
“Tare ma muke da ita, mu je ka bata da kanka�.
Suka sauko tare.
Tun daga nesa ta hango su don haka ta kara nutsuwa ta ajiye littafin da ta dauka na Mu’azzam, wanda ta fahimci dubawa yake yi ya ajiye ya tashi, ‘The Danger Of Hypersexual Disorder (By Dr. Martin Kafka, 4thEdition)’.
Da sauri ta ajiye ba tare da kowannensu ya lura ba. Aboulkhair ya zauna a kusa da ita, Mu’azzam ya wuce firjinsa ya zuba mocktail din a manyan kofunan glass guda biyu, ya sanya straw a kowanne ya iso gare su. Aalimah ta sa hannu tana ture Aboulkhair daga kusa da ita, shi kuma ya ki turuwa har Mu’azzam ya iso. Karshe ita ta tashi ta matsa gefe, Aboulkhair ya bi ta da harara.
“Koma wajenki ki zauna�. In ji Mu’azzam da muryar manyantaka irin tashi in yana magana da ita, wadda ta dade da lura ba da irinta yake yi wa Aboulkhair magana ba.
Aalimah ta sunkuyar da kai tana murmushi, a kunyace ta ce, “Shi ya ce in mun zo gidan nan kada in zauna kusa da shi�.
Aboulkhair ya hangame baki, ya ce,
“Yaushe aka yi haka???�
Mu’azzam ya mika mata kofin, hannu biyu tasa ta karba ta yi godiya ya samu kujera mai fuskantarsu ya zauna. Ya dubi Aalimah ya ce,
“Kin ga kuma ni din, sanda ya fara sonki sai da na yi da gaske ya tsaya ya yi karatu. Sai da na ce zan aura masa mata hudu in ya dage ya zama Psychiatric dina. Yanzu haka yana min tunin ukun da suka yi saura ne a sama kafin mu sauko�.
Aboulkhair ya sake kwalalo idanu ya sake hangame baki, ya ce, “Yaushe aka yi haka???�
“To mu duka ka mana tambaya iri daya, wadda ke nufin dukkanmu kana nufin mun yi maka karya�.
Mutsu-mutsu ya hau yi da baki yana rokon Mu’azzam da ido ya warware masa gadar zaren da ya kulla masa ba tare da ya ce da ita ya yi karya ba.
Aalimah ta fahimci halin da Mu’azzam ya jefa mijinta, har gumi yake yi, duk da sanyin garin Las Vegas, ta ce, “Yaya Mu’azzam ai addini ya bashi dama�.
Mu’azzam ya zuba mata ido na ‘yan dakiku, ba tun yau ba ya fahimci yarinyar tana da hankali, ga nutsuwa da girmama na gaba. Ya ce,
“Haka ne Aalimah! To amma me ya sa ya ce kada ki zauna a kusa da shi a gidana?�
Da sauri Aboulkhair ya ce, “Ni fa ban san an yi ba Aalimah, ban sanki da karya ba!�.
Dariya ta yi har fararen hakoranta suka bayyana, ta ce, “Yaya Mu’azzam ka san ko zan yi karya kai ba zan yi maka ba. Wai kunyarka yake ji�.
Murmushi Mu’azzam ya yi, murmushin nan nasa ingentleness,ya juya yana kallon Aboulkhair da kyawawan idanunsa cike da kauna, bai ce komai ba. Duba agogo ya hau yi, Aalimah ta ce a ranta, “Mun shiga lokacinsa�.
Tun kafin ya ce, “Ku je na sallame ku�. Dinsa tayi buzut ta mike ta ce,
“Mun tafi Yaya Mu’azzam, sai mun sake shigowa�.
Yana mai kara yaba hankalinta ya ce, “Tun ban sallame ku ba? To na gode, kuma ki je ATM.I’ve nothing to give you�.
Murmushi ta yi ta ce, “Muna godiya ni da wadanda nake aikawa kudin. Allah Ya kara budi�.
Juyawa ya yi ya haye upstairs dinsa.
6/30/21, 11:09 AM - Buhainat: 💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔
€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€€
@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@
Suna tafe a hanyarsu ta zuwa gida, Aboulkhair ya ce, “Me ya sa ki ka gaya masa ba kya amfani da kudin da yake ba ki? Ai ba zai ji dadi ba�.
Ta gyara zamanta da lullubin kanta, ta ce, “Saboda ya san ba ni da matsala ni, kada in zamo mai hadama. Ga aiki ya sama min ana biyana albashi mai tsoka, kuma yana bina da kudi kusan kamarsu duk wata, ai na zama mara godiyar Allah. Zai yi tunanin me nake yi da su, ga mijina bai rage ni da komai ba�.
Girgiza kai kawai Aboulkhair ya yi, har yau Aalimah ba ta san Mu’azzam ba. Bai kuma san irin bayanin da zai mata ta fahimce shi ba. Ba ruwanshi da abin da kowa ke ciki ko me wani ke gudanarwa a rayuwarsa. Shi kansa bai damu da rayuwar da yake ciki ba. Ba komai cikin ransa sai kwarewa da aikinsa na hakowa da tace man fetur (Exploration and refining petroleum). Tana wahalar da kanta wajen son ya fahimci me ta ke ciki, ba fahimta zai yi ba. Wani saint (waliyyi) ne shi a cikin turawa, kowa ya je ya yi abin da ke gabansa.
A karshen sabuwar shekarar da ake ciki sun yi shawarar za su dauki hutu lokaci daya saboda su samu zuwa Nigeria daidai lokacin haihuwar Basma. Kuma watan haihuwarta ne watan bikin Khaleesat. Duk da rashin wadatacciyar lafiyar ita Aalimahr ita ma tana fama da laulayin ciki wata hudu, boye rashin karfin jikin nata ta ke ga Aboulkhair tana kwarara kanta a gabansa, don kada ya hana ta zuwa. She missed Basma so much yadda ba za ta iya bayyanawa ba duk da suna waya a kowanne karshen sati, ga dokin ganin abin da za ta haifa mata tunda kuwa dan Yaya Aboubacar ita za a haifa mawa halak-malak. Fatanta ma a nan gaba in za su amince su bata ta hada da wanda za ta haifa ta rike a nan Las Vegas.
Mu’azzam ya samu karin ‘yan uwa masu kula da walwalarsa, ta san in ya hana kowa damunsa ba zai hana ‘ya’yansa ba. Tun daga lokacin da ta san wanene shi, ta damu da al’amarinsa sosai.
KANO-NIGERIA
Sun sauka a birnin Kano ranar alhamis. Ba matar ba, ba mijin ba, kowannensu ya yi ‘yar kyakkyawar kiba kib-kib ga kumatu luwai-luwai a fuskar Aalimah wanda a da ba ta da shi. Yaya Aboubacar ne ya zuba su Sabrina a mota suka je filin jirgin saman Malam Aminu Kano suka dauko su.
Basma na ta kiran waya tana ita a wuto mata da Aalimah ba ta yarda ta fara zuwa sultan road a bata mata lokacin ganinta ba. Aalimah na ba ta hakuri tana gaya mata ba za ta iya kara minti goma ba ta ga Mama ba alhalin tana cikin Kano, ta mata alkawarin har kwana za ta yi a gidanta in ta huta, saboda an hana basma fita saboda ta shiga EDD ga cikin mai wani irin girma.
Sun yi waya da su Mummy su sai bikin Khaleesat saura sati daya za su samu tahowa, yau kuma saura sati biyu.
Mama ta fito kofar shiga falo tana kallon Aalimah na fitowa daga mota da dan matashin cikinta tsab da ita cikin wata irin shiga ta doguwar riga ruwan hanta kirar Abu-Dhabi, takalminta ma kalarsa kenan marasa tsayin dunduniya dan kasar Italy. Ta yi wani irin haske mai nuna yanayin rayuwar da ta ke ciki wanke hannu ka taba. Aboulkhair da Aboubacar suna cikin motar ba su fito ba, suna maganar da ba ta san ta mece ce ba (zancen tafiyarsu Nijar suke daga Kano don fara shirin auren kannen su Hamoud da Khaleesat sati mai zuwa idan su Daddy sun iso). Su Suhaima sun rirriko hannayenta kamar sa cinye ta don murna. Shi kansa Aboulkhair din da ta hango ta cikin glass ya yi kyau da kibar da da gani ka san na zaunuwar wadata da kwanciyar hankali ne, fiye da lokacin da yake neman auren Aalimah. Godiya ta shiga yi wa ubangiji a fili tare da binsu da addu’a iri-iri a zuciyarta.
Daidai lokacin da ta ji Aalimah da tattausan jikinta da kamshin jikinta sun rungume ta. Dariya ta yi ita ma ta yi mata kyakkyawar runguma. A yadda Aalimah ta zama matar Neuro-psychiatrist da yawan tu’ammali da patients din Aboulkhair ko duba su da yake tana zaune, da yawan tattaunawa da suke kan cututtukan, ita kanta tana da experience mai dumbin yawa a kan mental health illnesses. Ta fahimci akwai ci gaba sosai da stable treatment a tare da Mamanta fiye da baya.
Shi kansa Daddy da ya dawo nan-nan yake ta yi da Aalimah da maigidanta. Ya rasa ina yaka saka-ina-yaka-aje da su. Kowa ya yi kewar kowa. Shekaru uku cif kenan ba su ga juna ba. Baban da Aboulkhair suna labari, Aalimah da Mamanta da kannenta na yin nasu a daki. Hirar Baban su Aalimah da surukinsa Aboulkhair yawanci kuma kaso tamatin cikin dari ta Mu’azzam ce. Yau Dr. Mansour Raazee ya kara sanin abubuwa masu yawa dangane da Mu’azzam har da wadanda Daddyn su Aboulkhair ya cire a nasa labarin da ya basu a Nijar. Kamar cewa Clearson ya koya wa Mu’azzam kallon fina-finan batsa tun kafin shekarun balaga wadanda su ma suna cikin causes na hypersexuality disorder a shekarun girma. Daddy gefe ya koma yana share hawaye da hankalinsa, ya ce da Aboulkhair wa ya sani ma ko har kwayoyi ya banka masa? Wa ya sani ko ya koya masa ma wata lalatar bayan wannan?
Aboulkhair ya yi murmushi, ya ce, “Daddy ka daina kuka, abin da ya wuce ya wuce. Kuma ni ina tare da su a lokacin na san komai. Na san abin da suke yi da wanda ba su yi ba, duk da karancin shekaruna. Ka ga Clearson bai taba neman Mu’azzam ta wata hanya ba saboda ‘yan wani addini ne wai shi Rastafari, wanda ya haramta musu neman jinsi, sannan ban taba ganin wata yarinya mace ta shiga gidan su Clerson ba, shi kadai ne kwal a wurin iyayensa ya tsoka daya a miya, sannan a shekarun Clearson a lokacin ya san rape shi ne mistake na karshe a kasar Turai, musamman ga su bakin haure. Ya fito ne daga wata kasa Portugal shi da iyayensa. Kwayoyi kuma ba zan iya cewa ba su sha ba, tunda wanda ya sha giya sanda zai sha kwaya ma ba zai sani ba�.
Daddy sai kuka kamar wani karamin yaro, ya ce da Aboulkhair, yanzu ba don magungunan da yake sha ba, ci gaba zai yi da alcoholic consumption?
Aboulkhair ya girgiza kai, “Daga shekaru goma sha tara Mu’azzam ya san cewa, Clearson ya illata masa rayuwa. Daga wadannan shekarun shi da kansa ya daina sha’awar giya. Daga lokacin da ya tabbatar wannan aggressiveness din nasa da ke sa shi ya illata lafiyarsa ya ji wa kansa ciwo, ya yi wa Daddy asarar komai na gidansa giyar da ya sha ce sanadi, ko a boye bai kara kallonta ba. Daddy ya dauke Mu’azzam daga America tsayin shekaru uku ba tare da yardar Mummy ba, bayan mun bar garin da Clearson yake babu wanda ya san inda ya kai shi sai ni, har gobe. Kuma na tabbata kuma bai gaya muku ba. Daddy you are Mu’az’s father also, ina gaya maka Wadannan sirrukan na Mu’azzam ne saboda haka kawai jikina ke gaya mini watarana za ka taimaka masa sabida dumbin kaunarka gare shi. Ina raye ko ba na raye, and Daddy will not tell anybody wasu muhimman abubuwa irin wadannan da suka shafi Mu’azzam saboda daga shi har Mu’azzam din yanzu ba sa son tunawa.
Ya kai shi birnin Medinah shekaru uku a wani gari wai shi YAMBOU hannun wani shehin malami dan asalin Hijaz (Madinah) ya sanya shi a wata makarantar mmalamin a wani kauye Yambou. A can ya yi sauka, ya yi hadda ya manta da rayuwar da ke cikin America bakidaya da zaman da ya yi da Clearson, yana kuma zuwa duk bayan wasu watanni yana kai masa magungunansa. Bai dawo da shi ba sai da ya ga zai zarce shekarun shiga jami’a. Bayan ya dawo kememe ya ki zama tare da kowa, ya zabi zama nesa da gida, wato birnin Nevada (Las Vegas) inda muke gabadayanmu yanzu�.
Dr. Mansour ya saki baki da kunnuwa yana jin Aboulkhair, ba Mu’azzam kadai ya ji tausayi ba wannan karon, har da dan uwansa (Ishaq), su suna nan suna ta jin haushinsa ba ya kula ‘yan uwa sabida ya samu duniya, shi yana can yana fadi-tashi don gyara rayuwar dansa da aka lalata masa. ko zaryar zuwa Madinah daga America wani hanzari ne mai zaman kansa. Ko a ina ya samo Balaraben da ya kai wa Mu’azzam din? Oho!
Aboulkhair ya ce, “Through internet�.
Sheikh Bahari Limamin babban masallacin Yambou ne. A wata lecture da ya saki a yanar gizo ne ya ce, yana da maganin raba matasa da shan giya da drug addiction komai tsananinsa in dai za a iya yin tattaki a same shi har inda yake. A nan ne Daddy ya samu email dinsa suka tattauna ya taimaka musu da yadda za su samu visa kai tsaye zuwa Yambou ba ta umrah ba. Saboda in ta umrah ce ba za ka iya shiga Yambou ba, ta karatu aka yi wa Mu’azzam. Makarantar kuma mallakinsa ce mai zaune da lasisi daga gwamnatin Saudiyyah. Mu’azzam ya shiga ransa daga ganinsa na farko da shi kuma da bakinsa ya gaya masa yana so ya bari, ba ya son ganinta ba dadinta yake ji ba�.
Daddyn Aalimah sai karin hawaye.
Aboulkhair ya ce, “Wallahi Daddy bayan dawowar Mu’azzam daga Madinah ko sallarsa abin kallo ce, saboda hakkinta da yake ba ta, a wajensa na koyi gyara sallah ta, a wajensa na koyi komai na ibada na gane su kansu Malaman da ke koyar da mu a America duk rabi baragada ce, ilmin musulunci bai wani ratsa su ba�.
Daddy ya girgiza kai ya fyace hanci, ya ce, “To wai ni shi kenan haka zai dauwama? Aure da haihuwa sai dai ya gani wurin kannensa?�
Aboulkhair ya ce, “Daddy mu yi sirri mana ni da kai?�
Murmushi Dr. Mansour ya yi, ya ce, “Mu yi Aboulkhair, ko Ishaq bai isa ya ji ba idan ba kai ka yarda ya ji ba�.
Aboulkhair ya matso jikinsa sosai kamar zai shige jikinsa, ya ce, “Daddy sabida Mu’az na karanci Neuro-Psychiatry, saboda in san wannan lalurar ciki da bai dinta, saboda a yadda na fahimta su kansu likitocin Mu’azzam ba su da magana kwaya daya game da warkewarsa, ko rashin warkewarsa. Bakunansu sun rabu. Na zabi John Hopkins saboda duk duniya ita ce lamba daya a ilmin Psychiatry, Daddy har gobe bincike nake ban fasa ba, ko bayan zamowata consultant. Aalimah shaida ce kan cewa sai in kwana uku a asibiti ba ta gan ni ba, amma ko kusa ba ta damuwa. A gida ma na kan kulle kaina a study room dinmu yini guda in ce ko abinci kada ta ba ni sai na nema da kaina. Ta kan ce ba ta taba ganin mai son dan uwansa irina ba, tana fatan wannan zumuncin ya kai mu aljanna ni da shi bakidaya, saboda ta lura nawa kadan ne a kan nasa. Kowa ya je masa gida damunsa yake ban da ni. Kowa kamar a kansa yake in dai zai masa awanni cikin gida, amma ni in ya yi kwana daya bai gan ni ba sai ya neme ni. Akwai sanda na kashe waya tsayin kwana biyu ina bincike, ta ce fada yake mata kamar zai doke ta kan ta turo masa ni, ba ruwanshi da wani bincike na.
Daddy duk ina gaya maka wannan ne saboda ka gane irin son da nake yi wa Mu’azzam, Daddy dama ni ne wannan lalurar ta ke a kaina… In dai zan ga ‘ya’yan Mu’azzam da fararen hakoransa a waje yana dariya kamar kowa. Ranar da na dauki hutun tahowa na gama wallafa littafina na farko;A Psychometric Investigation Of The Hypersexuality Disorder- Aboulkhair I.R’, kuma har na yi submitting dinsa a sashenmu na Neuropsychiatry a John Hopkins, tsofaffin malamai za su sake duba shi kafin a sake shi a duniya da sauran jami’o’in America. Kuma Proffessors na tsangayarmu bakidaya da tsofaffin likitoci na asibitocinmu daban-daban, da wadanda suka shude kafinsu a fannin sun tabbatar da cewa, wannan shi ne dependent kuma tsaftacciyar magana ta karshe a kan aggressive tendency and Hypersexuality Disorder�.
Dr. Mansour Raazee ya kama hannunsa ya rike tamau cike da fargabar abin da zai fito daga bakinsa… wanda shi ke determining future din rayuwar Mu’azzam, sai dai kafin shi ko Aboulkhair su ce komi Aboubacar da Aalimah sun yi sallama sun fado dakin a hargitse, wai basma Aboubacar ya kai asibiti yanzun nan za ta haihu, kuma haihuwar ta zo da tangarda. Likitoci sun tabbatar musu ba za ta iya haihuwa da kanta ba, ‘yan biyu ne, kuma haihuwar fari, ga shi ba ta exercise duk karfinta ya kare. Ana bukatar ya saka hannu kafin a yi mata aiki, shi ne ya zo su tafi gabadaya.
Fada Daddyn ya hau shi da shi, kan me ya sa ya taho ya baro ta ba tare da ya saka hannun ba? cikinsu wa ya fi dacewa da sanya hannun? Ya kasa ganewa Aboubacar a rude yake ba abin da zai iya kulla wa kansa a wannan lokacin.
Dukkansu suka dunguma zuwa asibitin standard inda a can ne Basma ke awo, Aboulkhair ya taimaka masa ya sanya hannun aka shigar da Basma dakin tiyata.
Aalimah ban da kuka ba abin da ta ke yi. Damuwarta shi ne, ko tozali da juna ba su yi ba. Ba yadda Basma ba ta yi ba kan ta zo ta ganta ko na minti goma ne ta koma, ta ce ita sai gobe. Da ta san haka ce za ta faru da ta je din, ta san Mama ba za ta hana ta ba.
******
Suna nan zaune jigum-jigum kowanne da carbi a hannu, ABoubacar sai safah da marwa yake a cikin asibitin. Mama ta koma gidansu don ta dauko kayan haihuwar da gigicewa ba ta bar Aboubacar ya dauko ba.
Aboulkhair ne kadai mai karfin hali, don waya yake yi da Mummy yana gaya mata ta yi wa Basma addu’a tana dakin haihuwa, kuma an ce ‘yan biyu ne. Sai dai bai gaya mata CS ake mata a halin yanzu ba, kada hankalinta ya zarta. Ya san Mummy sarai a kan son ‘ya’yanta.
Suna cikin wannan hali nurses biyu suka nufo su dauke da jarirai biyu cikin fararen shawul. Haba! In ba ka yi ba ni wuri, kowanne da gudu ya riske su tun kafin ya karaso tsakanin Aboubacar da Aalimah da Mama, Aboulkhair na yi musu dariya, don ya san shi kam ba za su ba shi ba. amma Aboubacar sai ya bi su yana tambayarsu lafiyar uwar jariran, murnar tasa rabi-da-rabi ce. Murmushi daya daga cikinsu ta yi masa, ta ce,
“Nan da minti goma sha biyar za ka iya ganinta a dakin aminity�.
Sai da aka gyara Basma aka kai ta daki, sannan aka ba su izinin ganinta. Aalimah ce a gaba, suka yi tozali da juna bayan rabuwar shekaru uku, ga ba damar rungumar juna, Basman na kwance ciki a farke. Sai murmushi ta ke wa Aalimah, ta miko mata hannu ta kama ta matse hannun sosai, sai kuma suka saki dariya dukkansu.
“Welcome to 9ja�. In ji Basma.
Da ‘yar siririyar wahalliyar murya, Aalimahr kuma ta ce,
“I congratulate us for becoming mummies�.
Aboubacar ya karaso da Hussainar ya dora mata a gabanta, Aalimah ta karbo Hassanar daga hannun Aboulkhair ta jera mata a gaban ‘yar uwarta. Basma ba ko kunya aka bude ido ana kallon ‘ya’ya, bakin nan kamar zai tsage don murmushi, ko kunyar Mama da ke gefe.
Aboulkhair ya ce, “Kin ji haushi wollah, mutum ba kawaici ko kadan?�
Mama ta ce, “Kyale ta ta gode wa Allah baiwar da Ya yi mata, kyautar ‘ya’ya mata biyu lokaci daya ma’abota jin kan UWA!�
Aboulkhair ya ce, “Au abin haka ne Mama? Mata na iyayensu mata ne? Ma cherie ba zan yarda ba, in kin zo taki kihaifo biyuamma mace da namiji kowa ya dauki nasa, ko ki haifi namiji daya, daga baya ki haifo takin. Amma wannan ai wayo ne�.
Kowa sai dariya har Aalimahr, duk da ta ji kunya. Haka Aboulkhair yake, very friendly to all. Shi ya sa yake da shiga ran kowa. Ba yadda za a yi ka yi zaman minti goma da shi ba ka nemi kun yi alaka ba. Bai da miskilanci, bai da jin kai. Ba za ka taba zaton da consultant ka ke zaune ba, sai dai saurayi dan makaranta.
Sai da suka kwana uku aka sallami Basma, suna ta ja wa Mama kunne ban da wankan ganye, sai na tawul. Murna a wurin Basma ba a magana, da ma ita wannan wankan ganyen da runhu da Mama ta ce in ta haihu sai ta yi mata ba karamin tayar mata da hankali yake ba.
Nan sultan road suka taho, Aboubacar da Aalimah suka je Hotoron suka dauko mata duk abin da za ta bukata.
Aalimah ta dade tana sai wa basma kayan haihuwa, duk abin da Aboulkhair ya sayo ya kawo ya ce ta ajiye saboda babynsu, sai ta saya wa Basma irinsa. Don haka ba kananan kaya ta tara ta taho mata da su ba. har da laces da tsadaddun materials don fitar biki. Ga wadanda Mama ta saya, ga na Aboubacar maigida kan gida. Ba a maganar wanda Mummy da Gumsu za su kawo nan da kwana hudu in sun iso. Don haka Basma da ‘ya’yanta sun ga gata, kuma suna kan gani, don jin cewa ‘yan biyu ne Mummy da Gumsu aka bazama kasuwa aka yi discarding waccan sayayyar aka ce an bar wa Aalimah, komi bibbiyu suke saye, kuma iri daya, ga shi an san abin da aka haifa.
Kwanan Basma bakwai cif! Da haihuwa wanda ya yi daidai da saura kwana biyar daurin auren Khaleesat saboda su Niger sai an fara daura aure ake shiga shagalin biki. Su Mummy suka iso Nigeria ita da Daddy da amarya Khaleesat da sauran ahalin gidan su Gumsu da kananan ‘ya’yansu Yesmin da Nurat. Kodayake yanzu ba mai kiran Yesmin yarinya, tunda kuwa shekarunta goma sha biyar.
Gida ya kacame da hidima ko ta ina, Mama da Gumsu nata jajircewa wajen kula da maijego da ‘ya’yanta. Sun so su yi taron suna a ranar ba zai yiwu ba, kasancewar duka ‘yan uwansu na nesa daga na Mama har na mahaifansu maza sai ‘yan uwan mummy Zulaiha ne suka zo, da yake su ‘yan Kano ne, su ma ba dukkansu ba saboda ba a gaya musu da wuri ba. Don haka su-ya-su suka yi get-together dinsu. Aka ce in ta yi arba’in ta je Nijar da maid. Amarya Khaleesat ta sha ado, maijego da Aalimah sun yi anko na wani masifaffen leshi baki mai fararen duwatsu da Mummy ta taho musu da shi a dinke. Daga wani kwararren gidan hoto na kano Aboubacar ya dauko mai daukan hoto ya zo ya yi ta daukarsu. Shi da Aboulkhair ma sun shigo an yi hotunan da su, kowanne kuma ya yi da matarsa a falon Daddy kamar wasu sababbin aure a yanayin da suka firfito cikin hotunan.
Basma ga bikin zuwa, amma babu zanen daurawa, wai bikin Khaleesat amma an ce ba ita za a yi saboda kawai ta haihu, kuma yanka ta aka yi. Ta turka kuka da magiya, amma babu wanda ya bi bayanta har Mummy mai gudun bacin ransu. Fada ma ta hau ta da shi tana fadin, ba ta da hankali, wadannan jariran sabuwar haihuwa za ta zuba a mota zuwa wata kasa biki, saboda ba ta da imani? Idan ba ta tausayin kanta, kuma ba ta san muhimmancin lafiyarta ba? Mama saboda ita ta ce ta hakura da bikin. Amma duk ba ta gode ba.
Aalimah ce kadai ta ke rarrashinta, a karshe ta ce, tunda Basma ba za ta ba ita ma ta hakura, da ma aiki zai wa Mama yawa, tunda ita ke kula da su ita kadai, masu aiki aikin gida kawai suke yi, amma har girkin abinci a wuyan Mama yake.
Khaleesat kuma sai ta sa kuka ita ma ba ta yarda ba, aurenta guda babu manyan yayyenta mata ba a yi mata adalci ba.
Karshe Daddy Ishaq ne ya raba wannan rigimar. Ya bai wa Khaleesat hakuri soslai, ya ce ta gode wa Allah da kyautar da ya yi mata ta ‘ya’ya har biyu, ta bar Aalimah ta zauna da ‘yar uwarta. Babu abin da za a fasa, a can Niger ma wasu tarin yayyen na jiranta za su yi mata komai.
Gumsu ta ce, “Ba ga su Balkeesa ba? Kuma ita Aalimah sai ta raka ki har Japan insha-Allah (Khaleesat a kasar Japan za ta zauna inda aka tura Hamoud ya karo wani course duk dai a kan sojancin ruwa kafin ya kammala ya dawo ya yi wa kasarsa Niger Republic aiki na din-din-din)�.
Aka samu Khaleesat ta hakura, sai suka koma tsara yadda tafiyarsu Niger za ta kasance.
Daddy ya ce amarya da su Mummy za su wuce jibi, kwana biyu da suna kenan. Su kuma sai ana i-gobe daurin aure za su yi asubanci. Mu’azzam ma sai ana i-gobe daurin aure zai shiga Niger. Ya yi musu booking Niamey Flight bakidayansu, har kannen Aalimah mata amma dole sai sun je Abuja babu jirgin Niamey daga Kano.
Su Mummy suka tashi zuwa Niamey suka bar masu jego, Aalimah da dukkan zuciyarta da lafiyarta ta ke hidimtawa Basma da jariranta. A gefe ga takurar Aboulkhair wanda kawaicinsa ya fara karewa, zaman ya fara gundurarsa shi da matarsa sai daga nesa. A gidan Aboubacar suke zaune shi da Aboubacar din. Cin abinci kadai ke shigo da su gidan. Har bankin GT Aboulkhair ke bin Aboubacar yana ganin yadda suke gudanar da ayyukansu, inda Aboubacar yake a branch dinsu na Hotoro. System din aikin Nigeria yana ba shi mamaki, ka wuni kana aiki amma albashin bai fi ka kashe shi a sati daya ba. Wai ma banki kenan, bankin ma mai daraja irin Guaranteed Trust.
Aboubacar ya ce, “A wurinka kenan. Mu kam ai mun san yadda muke tattala kayanmu ya kai mu karshen watan. Basma ma a nan ta ke aikin, saboda jami’ar da ta fito da na kawo wa manajanmu takardunta da gudu suka dauke ta ba tare da la’akari da abin da ta karanta ba�.
Irin hirarrakinsu kenan na matasa masu jini a jika, ‘yan uwan da suka san muhimmancin junansu.
Ana i-gobe za su tafi Niger bayan sun zo sun ci abincin dare wanda Aalimah ta dafa ta yi serving dinsu a dining ta koma gefe tana cin nata. Tunda suka zo suka raba plate saboda idon iyaye da sanin ya-kamata. Amma a nasu gidan bayan plate guda ma da one spoon suke amfani. Aboubacar ya riga gamawa ya tashi ya nufi wurin iyalinsa, wadanda suke a dakin Aalimah na gidan. Kamar jira Aboulkhair yake ya tashi, ya ajiye cokalinsa ya mike. Ya juya kofar dakin Mama da alama ta kulle ta ciki duk da dai ya san ba ta yi barci ba. Hannun Aalimah kawai ya kama ya mikar da ita. Za ta yi magana ya dora yatsa a baki, “Zo mu je, sako zan ba ki, yanzu za ki dawo�.
Aalimah ba ta gane Aboulkhair so yake su bar gidan ba, sai da ta ji ta a motar Aboubacar, ya tada motar da gudu, suka harba kan titi.
Kasa magana ta yi har suka iso gidan Basma. Ya shigar da motar cikin gate maigadin ya rufe ya wuce ciki ba tare da ya bari sun hada ido ba. To amma ai ita ta san kan kayanta, a kwayar idanunsa ta ke gano komai nasa. Kuma a yadda ta san halittar mijinta ta san ya yi kokarin da bai taba yi ba tun bayan aurensu. Sai ko komawar saJohn Hopkins yin part two exams dinsa da suka jima ba sa tare. Ranar da suka hadun kuwa, har gobe ba za ta manta yadda ranar ta gudana gare su ba, with a fondest thought!
Girgiza kai ta yi cike da tausayin mijinta, ta fito ta bi bayansa. Tun a falon Basma al’amuransa suka soma ganar da ita kewar tata da ya yi ba ‘yar kadan ba ce. Ba ta hana shi komai ba, karewa ma samun kanta ta yi da ba shi hadin kai da zuciya da gangar jikinta bakidaya fiye da na kowacce rana cikin rayuwar aurensu. Da wani irin feeling a zuciyarta da ruhinta da ba za ta iya kwatantawa ba.
Gare shi jin ranar yau yake kamar ranar da ya bare ta a ledarta, komai nata ya kara canzawa fiye da baya, sakamakon matashin cikin jikinta. Aalimah, na cikin sahun matan da ba sa taba gundurar mazajensu sabida baiwar ni’imar da Allah ya yi musu, wanda ita kanta ba ta sani ba, shi kuma ba shi da bakin furta mata hakan sai dai ta gani practically daga yanayin da yake kasancewa a kullum suke tare, wanda ke kara mata kaunarsa.
Dukkaninsu ba su san sanda wani irin barci ya sure su ba, wanda ba shakka na gajiya ne, saboda dukkaninsu sun taimaki juna ne ta hanyoyi da dama da ba su taba samun kansu a ciki ba.
Karar wayarsa ce ta tashe shi, ya janye Aalimah daga kafadunsa ya ga Aboubacar ke kiransa.
“Ban tambaye ka inda ku ka tafi ba, kawai ku yi zamanku da asubah mu biyo mu dauke ka, ita kuma ta dawo da kanta, ai ta san gari�.
Dariya Aboulkhair ya yi, wadda ta tada Aalimah daga nata daddadan barcin, suka soma shirin barin gidan.
6/30/21, 11:09 AM - Buhainat: *I'm writing this chapter with heartfelt TEARS* ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜
Sanda suka iso karfe goma sha biyu na dare Aboubacar na kofar gida. Kasa fitowa daga motar suka yi dukkansu duk da sanin da suke da shi na cewa Aboubacar zai iya hango su ta glass. Hannunsa ya dora a kan cikinta yana sauraron harbawar jaririn yana lumshe idanu ya ce, “Kin san wani abu?�
Girgiza kai ta yi, haka kawai ta ji ranta ba dadi, kamar su koma gidan Basman su kwana tare. In ya tafi Niger ita da ganinsa sai nan da kwana goma in an gama bikin Khaleesat, sannan ne zai zo su koma. Ba lokaci daya za su tashi da ‘yan Massachusetts ba, su sai nan da sati biyu. Ko dai ta kyale Basma ne ta bi mijinta ga kyawawan ‘yammatan nan na zuri’arsu da ba ta san iyaka wadanda za su kalle mata shi ba? Wani bala’e’en kishi ya turnuke ta irin wanda ba ta taba sanin tana da shi ba. Sabida a inda suke rayuwa ba ruwansu da irin wadannan abubuwan kowa da life-partner dinshi ba mai shiga gonar wani. Ta girgiza kai, ba tare da ya fahimci tunanin da ta ke ba, ya ce, “In namiji ki ka haifa ‘MU’AZZAM zan sa masa, in mace ce, ‘AALIMAH’ (mai ilmi) yadda zan ji dadin gaya mata how sweet and loving her mum is, how helping and generous she is, how much I truly love her and the long time I spend waiting to marry her. Duka zan gaya mata Aalimah, idan kuma namiji ne zan gaya masa yadda na rayu cikin soyayyar dan uwana mai lalura, yadda nake sonsa da burin samun lafiyarsa. Yadda ya kyautata wa rayuwata, ya tsaya min against all odds. Ya mayar da ni abin da nake a yau; Aboulkhair mai rayuwa da tsayayyun kafafu mamallakin Aalimah. Har ga shi za ta samar da Da a gare mu ni da Mu’azzam…�
A lokacin ya ankara Aalimah kuka ta ke yi.
“Mon Amour na fasa zama, tare za mu tafi�.
Dan tsayawa ya yi yana nazarinta gabadaya ta birkice kamar ba ita ba. Nazarin maganganun da ya furta yake yi, ko akwai na tashin hankali a ciki? Iyakar tunaninsa bai gani ba. Kuka ta ke yi shabe-shabe da hawaye da majina. Janyo ta ya yi jikinsa, ya ce, “Aalimah�. Sunanta na hakika.
“Nda’am�. Ta amsa cikin rishin kuka, don rabon da ta ji ya kira ta tun zamanin samartaka (‘yammatancinsu).
“me na fada wanda ya bata miki rai?�
“Babu komai�. Ta amsa da sauri.
“To me ya sa za ki canza shawara cewa sai kin je Niger? You are kidding. Kada ki dauka ban san halin da ki ke ciki ba, ko daga kumburarrun kafafunki. Kina wasa ne ma da ki ke tunanin zan barki ki shiga kujiba-kujibar bikin nan na Niger, ki je kina girkin roti da rawa a wajen cocktail, ki jawo min asarar da ban taba shirya mata ba! Don haka ki saki ranki kawai mu yi rabuwar arziki ko a yi ta tsiya-tsiya�.
Ba ta san sanda murmushi ya kubuce mata ba, ga hawaye face-face a fuskarta. Ba ta yi aune ba ta ji Aboulkhair ya rungume ta, sai saukar harshensa a fuskarta yana dauke hawayen salla-salla daga kan fuskarta. Idanun kuwa har wani side su yake yi.
Aboubacar da ke gefe yana waya da Basma yana jiran Aboulkhair ya sallami Aalimah su tafi, gefen idanunsa ya dan hasko masa abin da ke faruwa. Da sauri ya yi cikin gida yana bai wa Basma labari, ta kai yatsunta ta rufe fuskarta wai tana ji masa kunyar abin da ya gano. Sai jinsa ta yi a nata kumatun yana fadin, “Bari in nuna miki yadda suke yi�.
Aboukhair da Aalimah ba su rabu ba sai karfe daya daidai na dare. Tana tafiya zuwa cikin gida tana waiwayonsa da murmushi, yana tsaye jikin motar Aboubacar shi ma murmushin ya ke mata. In ba ta yi kuskure ba ba ta taba ganin irin wannan kasaitaccen murmushin daga gare shi ba.
*****
Daddyn Aalimah, Daddyn Aboulkhair, Aboubacar da Aboulkhair afilin jirgin saman Malam Aminu Kano, fuskokinsu cike da takaici da bacin rai. Wai babu jirgi mai zuwa Niamey a yau sakamakon lalacewar jirgin da suka yi booking din a safiyar yau, yana can Niamey ma bai taso ba ana gyara shi.
Aboubacar ya duba agogon hannunsa, ya ce, “Daddy, da wannan zaman cinye lokacin da muke gara mu je mu bi mota. Tafiyar awanni goma sha biyu cif nan gaba za ta kai mu Niamey. Yanzu karfe takwas na safe, in muka yi sauri muka dauki hanya zuwa tara na safe za mu isa Niamey nan da karfe tara na dare. Za kuma mu samu daurin aure a kan lokaci�.
Duk sun yi na’am da wannan shawarar, Daddyn Aboulkhair ya ce, “Aboulkhair is a very good driver, na tabbata kafin lokacin ma mun isa�.
A gurguje suka dawo gida suka yi wa Mama bayanin canjin da aka samu. Ba su bata lokaci ba suka dauki sabuwar motar Dr. Mansour kirar Jeep 2015 model, Aboulkhair ya tada ita suka shisshigar da kayansu, sannan Aboubacar ya shiga gaba, iyayen suna baya su biyu. Ko su Aalimah ba su san da wannan sauyin da aka samu ba, ba sa gidan dukkaninsu tun sassafe, ta raka Basma asibiti, Hassana (Zulaiha) na fama da mura, Hussainar sunan mama aka sa mata (Aseeya).
Sai da suka shiga gidan mai suka yi full tank, sannan suka dauki hanyar jamhuriyyar Niger.
******
Mummunan hadarin motar ya afku ne kafin a kai boarder din da ta raba iyakar kasar Najeriya da jamhuriyyar Nijar, bayan sun tsallake garin Jibiya sun shiga boarder din kasar Nijar.
Wasu gungun fulani ne makiyaya suka koro shanu a kan titin za su tsallaka. Ga direban Jeep din ya kwararo motar da gudu irin na neman biyan bukata. Burinsa su shiga Niger kawai kafin azahar a kalla ya san suna cikin kasar ainahinta, inyaso su yi sallah su ci abinci su durfafi Niamey ba tare da sun bata lokaci ba.
Shanun sun taho fal da gudunsu, shi ma ya shararo motar, sai ya ga bari ya dauke kan motar da azama tunda daya titin babu mota ko daya, ba tare da lura da cewa wata karamar mota ta taho ita ma a guje ta bayansa ba, kawai ta ga motar a kan nata titin ba tare da ta tsammata ko ta ankara ba. Kafin direban karamar motar ya yi tunanin abin yi, ya yi mugun taho-mu-gama da bakar Jeep din wanda hakan ya sanya duka motocin biyu fara katantanwa a tsakiyar babban titin kafin a karshe su duka biyun su hantsila wani katon rami a gefen titin. Ba ka jin komai sai hailala da salatin mutanen da ke cikin motocin cikin mika wuya ga hukuncin mahaliccinsu.
******
Da asubahin ranar Hassana da Hussaina suka ci gaba da ruda gidan da kuka, wanda suka kwana suna yi suna hutawa. Tun daren jiya sun ki karbar nono. Daga Basma har Aalimah babu wacce ta runtsa, suna fama da yaran nan saboda mama na can dakinta kwance babu lafiya, ta ce kuma takamaimai ba ta san inda ke mata ciwo ba, amma ko hannunta ta kasa motsawa balle ta zo ta taimaka musu. Daga kwance ta ce su dinga yin addu’a suna tofa musu.
Basma gefe ta koma ta zuba tagumi, nonuwa sun mata suntum suna ta sukarta suna kuma diga, duk sun jika gaban rigarta. Aalimah na so ta yi sallar asubah don har masallacin kusa da su sun idar, yaran duka biyu suna hannunta tana jijjaga su, ta san in ta ajiye su Basma ko taba su ba za ta yi ba. ta zama dumm! Kamar wadda ta samu ciwon kurumta na lokaci mai tsawo.
Aalimah ta ajiye daya ta goya daya. Rabonta da goyo tun haihuwar Aunty Gumsu. Tunda aka sallamo Basma Mama ke goya su, ta zura hijabi ta tada sallah zuciyarta na harbawa da kukan da yarinyar ke zubawa a bayanta. Ga wadda ta ajiye ita ma ba ta fasa ba. Kawai ita ma sai ta soma kukan tausayin Basma, ta san tsananin damuwa ne ya sa ta daina tabuka komai a kansu. Allah-Allah ta ke ta idar su tafi asibiti, tukin motar da Aboulkhair ya nace ya koya mata duk da ba ta so yau zai yi mata amfani. Da safe ma ita ta kai su asibiti aka duba yarinyar aka ce mura ce kawai, suka sayo magani suka dawo.
Nan Mama ke gaya musu tafiyar su Daddy a mota sakamakon rashin jirgi. Duka addu’ar sauka lafiya suka yi musu, suka ci gaba da hidimar yaran.
Tun bayan maghriba kuma suka bude makogaro suke zunduma kuka. Wanda shi ne har yanzu suke fama. Tana idarwa ta fito goye da Husainar ta je dakin su Sabrina ta rufe su da duka suna barci. A tsorace duk suka tashi suna tambayarta me ya faru? Kuka ta hau yi a gabansu tana fadin, sai barcinsu na tsiya ya jawo musu masifa, uwarsu na kwance babu inda ta ke iya motsawa tun dare suna nan suna barcin asara, duk kukan da ‘yan biyu ke yi ba su san ana yi ba ko me? Rantsuwa suka hau yi mata suna dirgowa daga gado suna fadin, wallahi ba su sani ba, kuma su ba su ji kuka ba. Ta ce su je su kula da Mama ita da Basma za su je asibiti a duba yaran.
Wata na ture wata haka suka fita a gigice, ta bi su da harara da idanunta da suka yi jawur. Lokaci-lokaci gabanta na tsinkewa ya fadi, har sai ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta ta ambaci sunan Allah. Dan cikinta sai wani irin juyi yake kamar ya wuce watanninsa. Ta dawo tana rarrashin Basma, ta canza riga su tafi asibiti, amma ta yi gumm! Kamar ba da ita ta ke ba, gani kawai ta ke rasa yaran za ta yi, don haka ba ta ga amfanin su je wani asibiti ba. ga Aboubacar tun kafin azahar rabonsa da kiranta, ita kuma in ta kira shi wayar ba ta shiga. Dalilin damuwarta kenan.
Aalimah ta yi rarrashin duniyar nan, Basma ta ki tashi, kawai sai ta fashe da kuka mai karfi.
Ta ce, “Basma, ya ki ke so in yi da raina? Kina so na zauce? Ga Mama can ba ta san wanda ke kanta ba, ni ma zuciyata tsinkewa ta ke yi, karfin hali kawai nake yi, su kuma da gani akwai abin da ke damunsu. Jarirai su kwana ba su sha nono ba ki ce haka za mu ci gaba da zama da su muna kallonsu?�
Basma ko gezau! Sai ta rabu da ita ta sanya hijab din sallarta ta dauki mukullin motar Aboubacar da ya bar musu don irin hakan, kamar ya san za su bukace ta. Ta nade Hassanar a shawul mai kauri, ta dauki katinansu na asibiti ta tafi, Suhaima ta biyo ta da gudu ta karbi ta hannunta tana fadin, “Muje na raka ki in ji Mama�.
Da suka je asibitin a sashen sababbin haihuwa aka karbi jariran (Day old), likitoci suka hau bincikarsu. Suka samu wuri ita da Suhaima suka zauna. Sai a lokacin nutsuwa ta soma dawo mata jin ta daina jiyo kukansu. Tunanin Aboulkhair ya fado mata. Ta kira shi bayan sun dawo daga asibiti da safe ya ce mata suna Katsina, “in mun shiga Niger I will call you. Take care of yourself and my baby for me MON AMOUR!�.
Kiran da har yanzu ko kyallinsa ba ta gani ba. Tsabar jiran kiran wuni ta yi rike da wayar a hannunta, in sallah za ta yi a cikinta ta ke soke ta. Da ta gaji da jiran ta yi ta gwadawa ita ya ki shiga. Ta yi tunanin sun shiga sahara sun rasa network, amma har twins suka fara jiniyarsu babu kiran Aboulkhair ko na Aboubacar. Mama ta ce, Daddy ma bai kira ba. A lokacin ya isa a ce ma sun shiga Niamey. To balle yanzu da za a iya cewa sun kwana sun hantse, tunda har ga shi alfijir ya keto.
Ba ta kawo wani mummunan tunani a ranta ba, duk da ta san Aboulkhair yana da layin Niger. Ta sa a ranta bai samu sukunin kiran nata ba ne saboda gajiya duba da cewa, shi ya tuka motar tun daga Nigeria har Niger, har kuma babban birni Niamey. Sai dai wannan tsinkewar na zuciyarta shi yake damunta, saboda ba a son faduwar gaba ga mai ciki. A matsayinta na medical personnel ta san hatsarin hakan, don haka ta koma hailala da salatin Annabi cikin zuciyarta.
Daidai lokacin likitan da ya karbi yaran ya fito. Tambayarta ya yi, ina uwarsu? Ta ce tana gida.
Da mamaki ya dube ta, sai kuma ya basar ya
ce ta je ta zo da ita za a debi nonon a ba su ta hancinsu, masassara ce ta cika musu makogaro.
Ta ce da Suhaima ta zauna ta je ta zo da Basma, ba za ta jima ba. Har Mama za ta dauko.
Tun daga nesa ta hangi bakar motar ‘yansanda fake a kofar gidansu. Tsinkewar da gabanta ke yi ya fadi da ta samu ya lafa sabida karfin hailala ne ya sake faruwa da ita. ‘Yansanda biyu na tsaye tare da maigadinsu Bilyaminu.
A hankali ta ke rage gudun motar ta wuce su ta nufi gate tana danna wa Bilyaminu horn da nufin ya zo ya bude mata ta shige.
Bilyaminu ya karaso da sauri, maimakon ya bude mata sai ya tsaya yi mata bayanin wai ‘yansandan gidan suka zo. Wani babba a gidan suke son gani. Ba halinta ba ne raina babba ko na kasa da ita, amma ba ta san sanda ta sakar wa Bilyaminu harara ba, “Amma dai ka san daga Daddy har Yaya Aboubacar ba sa nan ko? Don me ba za ka gaya musu ba da za ka tare ni kana gaya min? Ka san uzurin da ke gabana? Tunda ka ga na fita da asubah na dawo yanzu ba sai ka bude min kofa ba ka san ya zaka yi da su ba, tunda ba sata na yi ba?�
Daya daga cikin ‘yan sandan ya karaso ganin ta ki kula su, kuma ta rufe dattijon da fada, “Excuse me Madam!� Ya fada da kyakkyawar siga.
Dole ta yi shiru ta bi shi da ido.
“Muna neman gidan Dr. Mansour Raazee, lecturer a jami’ar Bayero, tsangayar Mass Communication, da gidan Aboubacar Raazee, accounter GTBank Hotoro Branch�. Ya fada cikin harshen turanci.
A sanyaye ta ce, “Nan ne!�.
“Ko za ki turo mana namiji ya bi mu ofishinmu? Akwai bayani a kansu�.
Girgiza kai ta yi, abin gwanin ban tausayi ta ce, “Ni ce babba a gidan, babu namiji bayan su, uwata kuma ba ta da lafiya�.
Tsayawa ya yi yana tunani, bai kamata ya tafi da ita ba ya gaya mata al’amarin da ke tafe da shi, ga ciki yana gani tare da ita, kuma ga dukkan alamu dukkaninsu ‘yan uwanta ne. A hotunan da aka turo musu babu wanda bai yi kama da ita ba.
“Madam, daure ki turo min namiji ko makocinku ne, zan fi son magana da shi a kanki�.
“Ka yi hakuri Officer, ni ma bakuwa ce a unguwar ban san kowa ba. Ka yi hakuri ka bar ni in wuce in ba za ka hanzarta fadar uzurinka ba. Na baro jarirai a asibiti�.
Kawai sai ta soma hawaye a gabansu, zuciyarta ce ta tsinke, jikinta ya gama ba ta wani tafiyayyen labari ne suke tafe da shi, wanda zai kawo karshen duk wani farin cikin rayuwarta. Wanda suke shakkar tattauna shi da ita, ganinta mace, kuma mai ciki.
“Ok, since you insist (tunda kin dage), za ki iya biyo mu ofishinmu?�
Ta zuki numfashi da kyar, amma ta kasa furzo shi waje. Yau ita ce a ofishin ‘yan sanda a kan laifin da ba ta sani ba! Kodayake sun ce abin da suke tafe da shi din ya shafi babanta da yayanta ne. To ko laifi suka yi? Ko kama su aka yi a hanyar Niger din? To su kuma sauran da ba’a ambata ba ina suke?
Ba ta da amsa ko daya, don haka ta share hawayen da suka cika mata fuska ta ce su ba ta minti goma ta fada a gida, ta dauko ‘yar uwarta ta kai ta asibiti, sai ta same su a inda suka ce.
Tana shiga gida ta tarar da wani tashin hankalin. Basma ce a sume, su Sabrina na ta sheka mata ruwa. Duk tsananin da Mama ke ciki ta sa sun tayar da ita sun jinginar a jikin filo. Sabrina ke gaya mata tunda aka yo mata waya daga Niger aka ce su Daddy ba su isa ba tun jiya kuma an kasa samun kowannensu a waya ta ke suma tana farfadowa. Ta dubi Mama a firgice sai Mama ta lumshe ido, ta ce, “Ku hada karfi ku sa ta a mota, ki kai ta asibiti�.
Jikinta na rawa ta ce, “Mama har ke zan kai, wallahi ba zan barki a gida ba. Kuma yanzu zan yi wa Mummy waya har Niger din in gaya mata ga halin da ku ke ciki dukkanku, ni kadai ba zan iya ba, kwakwalwata kamar ta zauce. Yanzu haka ‘yan sanda ne a bakin gate sun zo tafiya da ni. Ba su je Niger ba, ina suka je? Na shiga uku ni Aalimah, ko dai ‘yan fashi ne suka tare su?�
Dukkansu babu wanda ya kawo wani abu a zuciyarsa bayan wannan, Mama ta ce ba za ta iya fita zuwa mota ba. Aalimah na kuka ta ce, “Ko a goye ne sai na kai ki asibiti�.
Ita da kannenta biyu suka ciccibi Mama, rabi kuma da kafarta suke janta a kasa zuwa mota. Suna fitowa harabar gidan Tabawa da Sabira suna shigowa (masu aikin Mama), wadanda ba aikin kwana suke yi ba.
Wata ajiyar zuciya Aalimah ta yi, da hanzari suka taimaka mata ta sa Mama a mota, ta gaya musu saura Basma, Tabawa ita kadai ta ciccibo Basma sabida kakkarfa ce. Gabadayansu suka duru a motar har su Sabrina, su biyu a gaba, ta ja su zuwa asibitin da ta kai su Hassana da Hussaina.
Dukkansu an karbe su ba bata lokaci, da yake asibitin na kudi ne, international. Ta gaya wa Mama za ta je ofishin ‘yan sandan ta dawo, Mama na daga kwance ta ce ba ta yarda ba. Ta kara gwada layin Aboulkhair, in har yanzu ba ta same shi ba, ta kira Uncle Oussama ta gaya masa, ko kofar asibitin ba ta yarda ta taka ba.
Hakan kuwa ta yi, duk da cewa ta so Mama ta barta ta je, don idan reality bai kassara ta ba, fargaba da zullumi dake zuciyarta za su haifar mata da hauhawar jini, wanda shi ma ba’a sonsa ga mai ciki.
Jiya-i-yau. Ba ta samu Aboubacar ko Aboulkhair ko Daddy ba. Don haka tana kuka ta kira Oncle Oussama wadanda ke can zugum-zugum sun kasa daura aure bayan sun tara jama’a makil daga birni da kauye, tunda babu labarin iyayen yaran bayan kowa ya tabbatar da tahowarsu tun jiya.
Kukan da ta ke yi bai hana shi gane me ta ke cewa ba. Duk halin da suke ciki tun jiya ta warware masa. ta gaya amsa yanzu haka duk an ba su gado daga su har jariran kuma Mama ta hana ta zuwa police station din.
“Za mu zo a yau, kada ki sake kije police station dinnan�. Abin da ya ce mata kawai kenan yana mai jin wani irin tsoro da tashin hankali na shigarsa.
Ango Hamoud da ya yi zugum a gefe, da Mu’azzam da ya iso tun jiya ya ja gefe ya ce su je su nema musu ticket yanzu-yanzu mai zuwa Abuja, shi da Edrissa da Mu’azzam da angon da Malam kansa. Bayan wannan bai kara musu bayanin komai ba. Ya karbi sadaki daga hannun kaninsa babban dan Inna Bintou ya daura auren Khaleesat da Hamoud ba cikin dadin rai ba, sai don ba yadda za su yi da jama’ar da suka tara. Tun ba a gama watsewa ba ya ja Malam gefe ya gaya masa duk bayanin da Aalimah ta yi masa a waya, ya kara da cewa, yana tsammanin suna hannun ‘yan sandan da suka je neman wani nasun, ko dai sun yi wani laifin ne an kama su, ko ‘yan fashi ko hadari. Abin da yake zato kenan.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un�. Shi ne abin da Malam Ibraheem Raazee ke ambato, babu kakkautawa. Zufa na keto masa ta ko’ina a jikinsa a lokacin da ya daga kai ya hangi Mu’azzam na fitowa daga mota.
Su waye suka mutu su waye zasu rayu? Kun yarda rayuwa bata da tabbas? Kun yarda ba abinda yake dorewa banda ikon Allah? Idan kun yarda da hakan to yanzu muka fara labarin Aalimah.!SumayyahAbdulkadir na tafe da cigaban labarin nan ba da jimawa ba!!!
7/2/21, 8:24 AM - Buhainat: ADAMU DANKOLI
A bakin gate ta tadda Mu’azzam din don already Oncle Oussama yayi masa waya ya gaya masa ga Aalimah nan zata zo ta dauke shi zuwa airport, Mu’azzam cikin kokarin controlling damuwarsa da boye bacin ransa na wannan kumbiya-kumbiya da Iyayen nasu ke ta yi masa ya tambayi Oncle Oussama su Daddy din fa? Sun same su? Amma sai Oncle Oussama yace ai suna tare, da su zasu wuce Niamey gabadaya, sun dan samu hatsari ne ashe, amma da sauki sosai.
Ya kara da cewa sun dauko su daga asibiti Ambulance ta taho dasu filin jirgin shi kadai suke jira, har an sa su a jirgi karkashin kulawar likitoci. Hamoud da Oncle Eidrissa zasu biyo su daga baya sabida kada a bar su Aalimah babu babba tare da su.
Ba don ya gamsu da wannan bayanin ba sai don bai isa ya musawa Kawun nasu ba, ko ba komai ya san bazai gaya masa karya ba, kuma koma me suke boyewar daga karshe dole zai sani ai. Tunda yace suna raye kuma sun gansu suna tare dasu to alhamdulillah.
Sanda Aalimah ta iso get din gidan yana waya ne da Oncle Oussama, saida ta jira ya gama. Ta bude masa kofar gaban motar da nufin ya shiga amma sai yace ta fito ta koma gaban shi ya tuka motar, ya fadi hakan ne ba tareda ya kalli direction din da take ba, yace in ya so ta dinga nuna masa hanya. Bazai iya ganin mace da ciki tana tuki ba. Dazu ba karamin tashi hankalin sa yayi ba jin cewa ita zata tuka su Malam. Haka suka dauki hanyar airport babu mai magana a cikin su, babu mai kallon dan uwansa, sai zukatansu dake cike da zullumi iri daya; (tunanin halin da Aboulkhair da iyayensu ke ciki), sai nuna masa hanya data ke yi lokaci-lokaci har suka shiga cikin filin jirgin.
Ta nuna masa inda ya kamata yayi parking ya kashe motar Suka fito a lokaci daya.
Passengers har sun fara shiga jirgin wanda zai tashi dasu zuwa Birnin Tarayyah, don haka suna hango su su Malam dake zaune a reception suka mike suka tadda su. Malam ya kama hannun ta, ya kuma dafa kanta ya sanya mata albarka, tare da yi mata fatan sauka lafiya. Tana tsaye a inda suka barta suka wuce zuwa cikin jirgi. Mu’azzam shine karshen shiga jirgin bai san me yasa baya ko waiwaye ba.
Tana tsaye inda suka barta ta yi folding hannuwanta a saman kirjinta, tana kallon su suna shiga a hankali babu mai walwala a cikin su. A rashin sanin ta tare da farin cikin rayuwarta zasu tashi, wanda yau ya ke kwance a karkashin fukafukan jirgi. Instead of first class seats da ya saba hawa a duk lokacin da zai hau jirgi. Kullum yana gaya mata shi baya son economy class ko da zai tatike account din sa. Yau gashi a karkashin fukafukan jirgi. Da gaske rayuwa mai iya canzawa ce a kowanne lokaci ba tare da dan adam ya shirya ba. Shi yasa ake so a kowanne lokaci dan adam ya zamo cikin shirin haduwa da Ubangijin sa. Wannan shi zai sanya ya zamo koyaushe cikin aikata kyakkyawan aiki. Ta dade a tsaye don har sai da jirgin ya soma barin kasa sannan ta juya ta koma gida, tana mai jin duniyar bakidaya na yi mata wani irin kunci ta kowanne bangare wanda bata san dalilin sa ba.
A Abuja ne dai sai da aka bata musu lokaci wajen bincike da cike-ciken takardu kafin aka amince musu suka wuce da gawar zuwa Niamey.
Tun a cikin jirgin farko Mu’azzam ya soma shan jinin jikin sa, sabida bai ga majinyatan cikin jirgi tare da su kamar yadda Oncle Oussama yace ba. Daga Malam har Oncle din sun kasa hada ido da shi. Lokacin da sukayi transit a Abuja ya kara tabbatarwa ba tare suke da Aboulkhair da su Daddy ba.
A cikin jirgin da zai kai su Niamey hakurin sa da dauriyar sa ya gaza. Kallon su kawai yake yi cikin tsanaki. Malam ne a kusa da shi, yayin da Oncle Oussama yana daga kujerar bayan su. Dukkannin su tazbaha kawai suke ja, babu mai kallon shi, wani irin kallo yake yi musu idanuwansa na wani irin bubbudewa suna kankancewa duka a lokaci guda.
Duk yadda ya so su bude baki da kansu su bashi bayanin wani abu akasin abinda suka fada da farko amma sun ki cewa komai. Sai ya cigaba da zuba musu idon kamar yadda suke so. Amma bangare mafi rinjaye na zuciyarsa na tabbatar masa da cewa labarin da ke bakunan su ba mai dadin ji bane. Watakila dai su Aboulkhair sun bata. Ko kusa ransa mai yawan soyayya ga iyaye da tilon dan uwan nasa duk nisan zangon tunani da kintace da iyakar tsinkayen sa bai kawo masa mutuwar ko daya a cikinsu ba.
Yawan faduwar gaban da yake ta samu akai-akai na kara tabbatar masa da zargin sa na cewa su Daddy sun bata akan hanyarsu ta zuwa jamhuriyyar Nijar. Mu’azzam bai san cewa da gawar dan uwansa Aboulkhair suke tafe ba, sai da suka sanya kafa cikin family house din su na Raazii a unguwar plateaux. Shi dai Malam burinsa su isa Niamey da Mu’azzam lafiya. Ko ba komai uwarsa tana can, in ciwonsa ya tashi a bakon wuri inda babu kowa nasa ba su da yadda za su yi da shi, kuma Alhamdulillahi sun zo lafiya.
Gidan ya kacame da hidimar biki kamar jiya, saboda yau ne cocktail, dangi sun taru kamar su fasa gidan. Na birni dana kauye, Inna Kasisi na ta rabon abinci, Mummy Zulaiha ta tsame kanta tana daki da tazbaha a hannunta. Haka kawai ta ji duk bikin ya ishe ta tunda har yau babu labarin danta da mijinta.
Gumsu na yi wa amarya Khaleesat kwalliya suka ji maza na shigowa, Oncle Mainasara na fadin, “A kawo tabarmi. Ku matsa ku bada hanya. Sun dawo da gawar Aboulkhair, an ce shi kadai ne ya cika a cikin su�.
Mummy tana daga cikin daki ne amma tsaf kunnuwanta suna waje, komai da ake yi akan kunnen ta ne. Silalewa ta yi a zaunen data ke a sume yayin da Gumsu ta fito da gudu zaninta na kuncewa. Khaleesat ma haka.
A tsakar dakin Malam aka shimfide gawar Aboulkhair. Duka ‘ya’yan gidan maza sun shigo da makwabta da sauran al’ummar Annabi da suka samu labari a waje.
Malam ya ce a kira mahaifiyarsa ta zo su yi sallama, kafin a yi masa sallah. Sabida munin gawar ko wanka ba za a iya yi mata ba, sai ruwa aka yayyafa mata. Inna Kasisi ruwa take ta shafa wa Mummy, amma ko da ta farfado aka kai ta gaban gawar ta bude kyallen ta ga yadda Allah ya mayar da Aboulkhairinta da sauri ta rufe don fuskar duka ta zube. Baka iya shaida komai nasa. Sake silalewa ta yi ta suma a wurin. Gumsu ce da su Inna Bintou masu karfin gwiwar yi masa addu’a tare da sauran ‘yan uwa maza da mata. Amma Kasisi ma ta kasa duk irin taurin ranta kuwa. Kuka kawai take yi tana kiran sunan Aboulkhair. Khaleesat ma suma take ta yi kamar Mummy tana farfadowa. Yasmin na kururuwa ana hanata.
‘Ya’yan Malam gaba daya suna tsaye a kan gawar cikin dimuwa, kowanne rike da Alkur’ani mai tsarki suna karanta masa. Sabida yawansu nan da nan suka hattama sauka. Malam ya yi wa gawar Aboulkhair duk wani gata da addinin musulunci ya tanadar wa mamaci, suka hadu shi da ‘ya’yansa maza da jikoki da abokan arziki suka sallace shi, suka mika shi zuwa gidansa na gaskiya.
Mummy a karshe sai asibiti aka nufa da ita, don idan ta farfado ta tuno wai Aboulkhair ne babu, sai ta sake sumewa. Har aka yi addu’ar uku Mummy ba ta daina suma tana farfadowa ba. Likita ya tabbatar ta samu hawan jini farat daya. Khaleesat da Yesmin suna cikin wani yanayi wanda sai wanda ya taba rasa shakiki ne zai iya bayyana shi. Shakikin ma irin Monsieur Aboulkhair dinsu.
****
Ina Mu’azzam???
Mu’azzam ya bai wa kowa matukar mamaki, don kuwa abin da aka zata ba shi aka tarar daga gare shi ba. Shi ya sanya dan uwansa a kabarinsa, babu ko digon hawaye a fuskarsa, da hannunsa ya debi kasa sau uku da hannu bibbiyu ya rufe shi. Abin da Oncle Oussama ya lura da shi kawai shi ne; daga ranar bai kara sanya komai a bakinsa ba! Har maganinsa kuwa. Bai zubda hawaye ba, bai sake cewa kala ba. Wannan ya daga hankalin Malam wanda ke kwana daki daya da shi don kula da duk wani motsinsa yana kuma yi masa addu’o’i. Ba ya bari ya matsa ko nan da can. Ko bandaki ya shiga sai ya bishi ya tsaya a kofa.
Ranar da aka yi sadakar uku, ya ce da malam zai koma America zai nemi asibitin da ya dace ya kai su Daddy, ya kuma nema wa Dr. Mansour da Aboubacar medical visa suma a ci gaba da kula da su a can.
Babu wanda ya hana shi, don sun san cewa, hakan shi ne daidai, musamman da yake ya daina shan maganinsa, suna tsoron abin da hakan zai haifar, gara ya koma inda za a kula da shi shima.
******
Bayan tafiyar Mu’azzam ci gaba aka yi da karbar gaisuwa a gidan na Malam Raazee. Mummy na shan drip a asibiti har ta soma karbar reality.
Khaleesat ta kasance cikin tashin hankalin da ya fi na kowa a gidan, don a cewarta sanadin aurenta ne Monsieur Aboulkhair ya rasa kyakkyawar rayuwarsa. Tana mai kaico da wannan aure! Gumsu na kwabarta a koyaushe da cewa; mutum ba ya tsallake ajalinsa! Fadin halin da wannan family suke ciki ya yi kadan biro ya rubuta shi.
Mu’azzam ya kira malam Raazee ya sanar da shi ya yi processing visa din Daddyn Aalimah da Aboubacar, za su taso sati mai zuwa dukkansu, kuma ya hada da Hamoud don ya taya shi kula da su a can.
Malam ya ce,
“In ce ko kana shan naka maganin takwara?�
Mu’azzam ya yi shiru.
Malam ya kwantar da murya, ya ce, “Takwara tafiyar wani tashin wani ce, rashin Aboulkhair ba yana nufin karewar taka rayuwar ba ne, tunda har yanzu kana numfashi. Na gane abin da ka ke yi, kana so ne kai ma ka illata kanka; ta hanyar kin shan magani. Takwara, mutuwar dan uwa na sani da ciwo, ciwo ba dan kadan ba, dan uwan ma irin Aboulkhairi mai tarin alkhairi, wanda samun kamarsa sai an tona.
To amma a matsayinmu na musulmi, dole ne mu yarda da kaddara komai dacinta. Mu kuma yarda cewa kulli nafsin za’ikatul maut. Ka yi hakuri Mu’azzam ka ji? Don Allah ka kula da lafiyarka…..�.
Sai a wannan lokacin ne Mu’azzam ya fara wani irin kuka… Ya yi kuka ya yi kuka kamar ransa zai fita, Kakan nasa bai hana shi ba, hasali ma shi ma taya shi ya shiga yi suka yi ta yi a waya. A karshe Malam Raazee ya ce,
“Ba zan bari ka dauki kowa cikin majinyatan nan ba sai ka sha magani, ka kai kanka ga likitocinka sun kula da kai, in ba haka ba su zauna a nan kusa da ni, duk zan iya jinyar su. Gobe da ma zan kwaso su duka daga Kanon bakidayansu�.
Bai bari Mu’azzam ya ba shi amsa ba ya kashe wayar sa.
******
KANO, NIGERIA
Aalimah ba ta san wainar da ake toyawa ba sai a daren ranar dasu Mu’azzam suka wuce Niamey. Oncle Eidrissa ne ya kira ta a waya, ya ce suna tare da su Daddy an gansu. Cike da farin ciki ta ce,
“Ouncle Oussama ya gaya mini, har na gayawa su mama, sune a Aminu Kano da muka je dazu ko? Yaya jikin nasu? Oncle ina fata basu ji ciwo sosai ba?�
Ya ce, “Eh, muna can, amma sun ji rauni sosai wallahi�.
Ya kara da cewa. Ta kawo musu dardumar sallah da ruwan sha.
Ta ce, “Oncle abinci fa?�
Sai dai kuma ta karaya, da amsar da ya bata, da yadda take jin yana magana babu karsashi ko kankani a amon muryar sa, karfinta kuma ya kare dama da dawainiyar jinyar data ke sha a kwanaki ukun nan, she’s very exhausted, idanuwan ta har zafi suke yi na rashin barci, amma don karfin hali ba ta fasa kula da majinyatan ta ba. Ko dama can ita mai karfin zuciya ce akan komai. Duk da zuciyarta cike take taf, da kewa da tunanin mijinta. Taraddadin halin da yake ciki ya hana ta mallakar kanta. Tana jin salama ne in ta tuna an gansu kuma suna cikin gari daya itada Aboulkhair sannan suna samun kulawa daga likitoci yadda ya kamata kamar yadda su malam suka gaya mata, ta dan yi hakuri za’a barta ta gansu ba da jimawa ba.
Hawaye ya zubo wa Eidrissa, tausayin yarinyar yake ji sosai har cikin ransa. Takabar dake gabanta yake hango mata, da yadda zata haifi da ya rayu bai san Ubansa ba, ya ce,
“Bar maganar abincin nan Aalimah, wa zai iya cin shi? Ba ni Aseeyah idan tana kusa, kuma zata iya karba waya�.
A lokacin mama ta soma warwarewa sosai, ta mika mata wayar, mama ta karba tayi masa sallama, ya ce,
“Aseeyah!�
Ta ce, “Na’am Kawunsu�.
Ya ce, “Mu musulmi ne ko?�
Ta ce, “Kwarai da gaske�.
Ya ce, “Wadanda suka yarda Allah ke rayawa kuma shi ke kashewa?�
A kwance ta ke a gado, amma jin inda zancen sa ya nufa sai ta mike zaune, Aalimah ta sanya mata pillow a bayanta ta ta jingina, sake manna wayar tayi a kunnenta. Ga Aalimah ta kafe ta da idanu kamar mai son a fadi komai akan kunnen ta, don haka ta mike daga gadon ta nufi bakin taga don kaucewa wadannan kaifafan idanu na Aalimah.
“Tafi kai tsaye Kawunsu�.
Ya rufe ido ya gaya mata komai. Ya ce, “Na rasa yadda zan yi in gaya wa Aalimah ta rasa mijinta, na ganta da ciki, wanda da alama bai gama girma ba�.
Mama ta shiga salati, hawaye na zuba mata tarara! Ta ma manta Aalimahr na dakin. Jikinta ya hau tsuma da karkarwa.
Aalimah da Basmah da ke dakin duk suka yo kanta. Basma ta dauki wayar da ta yasar a kasa ta bi kira na karshe, Oncle Eidrissa ta gani, don haka ta bi bayan kiran.
“Oncle Basma ce�.
“Ku yi hakuri Basma kun ji, da kaddarar da Ubangiji ya dora mana. Kulli nafsin za’ikatul maut, Aboulkhairi bai yi gaggawa ba, mu ma duk lokaci muke jira!�.
Basma ta shaki wani azababben numfashi, tana mai kokarin fizgo sauti daga makogaronta.
“Oncle Daddy? Hubby? Suna ina?�
Ya share hawaye, muryar yarinyar kadai za ka ji ka fahimci ta gama mika wuya da jin ko ma me za ta ji. Tana da dauriya sosai kamar ko fiye da Aalimah.
Ya ce, “Basma ki dayanta Allah, ki yarda da kaddara sai ki samu cikar imani. Dan uwanki Aboulkhair Allah ya yi masa rasuwa. Har sun wuce da gawar Niamey don a suturta ta. Ga iyayenku da mijinki a nan tare da mu a gadon asibiti, sun jikkata. Mummunar jikkata. Mu gode wa Allah a cikin kowanne hali�.
Basma sai juyawa ta yi ta ga Aalimah a kasa, tana shure-shure, ta manta tsabar rudewa a handsfree ta sanya wayar. Allah ya taimaka a cikin asibiti suke, nan da nan ta danna kararrawar kiran likitoci, likitoci biyu da nurses biyu suka shigo suka dauke ta suka aza bisa gado suka soma kokarin ceto numfashinta da ceton abin da ke cikinta. Sakamakon jini da ya tsinke mata duka a lokaci guda.
7/2/21, 8:24 AM - Buhainat: KWATARKWASHI
A daidai wannan lokacin rashin lafiyar Mu’azzam ya fado masa a rai. Da sauri ya juya kafin ya karaso inda suke ya dubi babban dan sa Oussama da ke gefensa na dama a tsaye.
“Oussama yaya za mu yi da Mu’azzam? Ba’a gaya masa tashin hankali, idan ciwonsa ya tashi anan ya ya za mu yi da shi? Gashi babu Aboulkhairi tare da shi, babu shaidar komai na rashin lafiyarsa ko asibitinsa tare da mu�.
Duk dauriyar Uncle Oussama da taurin ransa yau kallo daya zaka yi masa ka ga ya baka tausayi, murya a raunane ya ce.
“Yanzu ya za’a yi Malam? Dole ya je shima, za mu dauki Hamoud ne mu barshi? Tun jiya cikin damuwa yake, yana gaya min ya kasa samun nutsuwa saboda rashin samun wayar kanin nasa, da rashin isowarsu tun lokacin da ya kamata a ce sun iso din�.
Suka yi zugum-zugum a tsaye, idanuwansu sun kada.
Daidai lokacin da Hamoud da Mu’az din suka isko su. Har kasa suka tsugunna cikin ladabi suna gaya musu an samu jirgi mai zuwa Abuja, wanda zai tashi nan da awanni biyu. Kuma duk Mu’azzam ya saya musu tikitin bakidayansu, ya ce shi ma zai je, bai yarda ya zauna a Niger bai san halin da suke ciki ba.
Babu yadda suka iya, suka yi shahadar kuda dukkansu suka taho Abuja, inda daganan suka hawo jirgi mai zuwa Kano. Mata ba su san wainar da ake toyawa ba. ‘Yammata na can suna shirya wa angwaye roti, manya na girke-girke, an boye amarya Khaleesat a daki. Gumsu da Zulaiha kadai ke cikin damuwar da ba ta hana su shiga mutane ba, saboda yadda kowa ya zo gidan su yake nema, don yi musu Allah ya sanya alkhairi.
*****
Da jirgi ya sauke su a Kanon-Dabo taxi biyu suka yi shata zuwa gidan Dr. Mansour, duk da Mu’azzam ya ce su bari ya yi waya gidan kakanninsa na wajen uwa a zo a dauke su, amma cikinsu ba wanda yake jin zai iya minti goma cikin filin jirgin bai san halin da wadannan rabin jikin nasa ke ciki ba. Shi ma Mu’azzam dalilin da ya sa ya fi su kwanciyar hankali shi ne, bai san komai game da wayar da Aalimah ta bugo ba. Hamoud ma bai sani ba, manyan kadai suka yi maganar a tsakaninsu. Edrissa cewa ya yi da Mu’azzam sun biyo baya ne don su bincika abin da ya hana su tasowa tunda an kasa samun wayoyin kowa a cikinsu, har na Aseeya.
Tun kafin su karasa gidan Uncle Oussama ya fiddo waya ya kira Aalimah. Ta ce ga ta nan zuwa za ta dauke su zuwa asibitin da suke.
A kofar gidan suka sassauka, sai dai sun kasa shiga duk da Bilyaminu ya ce su shigo din. Har Aalimah ta iso wajen a motar Aboubacar duk ta yi wani wujiga-wujiga ta fita hayyacinta kwana daya rak! Dabara ta zo wa Uncle Oussama yadda za su hana Mu’azzam zuwa police station, sai sun fara zuwa sun tabbatar da abinda ya faru, ya ce shi da Hamoud su shiga gidan su jira su, tunda motar ba za ta kwashesu su duka ba. Mu’azzam ya soma shiga rudu, ko daga ganin yanayin Aalimah, bai taba ganinta cikin wannan yanayin ba, yarinya ce ‘yar kwalisa ta kin karawa mai tarin nutsuwa a iya sanin da yayi mata.
Damuwarsa ta soma bayyana karara akan fuskar sa, sannan ya za’a ce ita mace mai ciki ta tuka mota su tafi wani wuri su samari masu jini a jika a ce su koma gida su zauna? Amma bai furta tunaninsa ba, don a fuskokinsu basu bashi damar yayi musu tambaya ba, don haka ya zuba musu ido ya ga iya gudun ruwan su, sai Aalimahr ya daga idonsa dake a rine ya jefa wa tambaya.
“Ina Aboulkhair? Ina Daddy da Baba Mansour?�
Aalimah ta juyar da kai cikin wani yanayi mara fassaruwa, ba tareda ta dube shi ba kanta na kallon kasa tace.
“Ni ma ban sani ba!�
Sai hawaye suka zubo batare da ta ankare ba. Wadanda suka kara dugunzuma zuciyar Mu’azzam.
“To yanzu ina za ki kai su?�
Wannan karon kamar cikin fusata ya tambaye ta. Don ya kasa gane dalilin wannan kumbiya-kumbiya da ake masa.
Da sauri Uncle Ossama ya ce, “Mu’azzam, in na isa in fada ka bi, to ku je ciki ku jira mu kai da Hamoud, za ta raka mu mu yi bincike a kansu ne a ofishin ‘yan sanda�.
“I will drive you�.
Mu’azzam ya fada cikin soma jin wani abu mai kama da mugun tsoro da matsananciyar fargaba na shigar sa. Wace irin magana ce wannan, ba a san inda suke ba? Bata suka yi ko sace su aka yi? Sai ka ce wasu kananan yara?
“Ita ta san garin, kai kuwa baka san ko’ina ba, shi ya sa za ta tuka mu�. In ji Malam, yana mai dafa kafadunsa wannan karon cikin sautin lallashi, ganin cewa jan ido da nuna karfin iko bazai yi tasiri ba gare shi a wannan lokacin.
Bai ce komai ba ganin cewa sun fishi hujja, ya dan ja da baya ya bi su da ido suna shiga motar daya bayan daya. Da Hamoud ya sanya hannunsa cikin nasa ya sarke, ya ja shi a hankali zuwa ciki, sai bai yi masa musu ba.
Kai tsaye ofishin ‘yan sanda na Bompai Aalimah ta nufa kamar yadda ‘yan sandan suka gaya mata. Da tambaya da komai har suka samu ofishin da ya kamata su nema.
Da ta dan soma bayani, tun kafin ta gama aka yi musu jagora zuwa ofishin kwamishina. Kamar dama jiran su ake yi. Malam yace da Aalimah ta koma mota ta zauna ta jira su. Kuma bata yi musun bin umarninsa ba.
Mikewa kwamishinan ya yi ya ba su hannu dukkansu cikin mutuntawa. Ganinsu manyan mutane farare tas-tas dasu kamar larabawa, ga tsohon ya sha rawanin da ya sanar da shi malamin buzu ne. Sannan suka samu kujerun dake fuskantarsa suka zazzuna. Daga inda suke suna iya karanto sunan kwamishinan dake like jikin wani dan karfe ruwan gold akan teburinsa; Commissioner of Police Isma’ila Dauda Kataki.
Sai da kwamishina ya ga sun nutsu, sun bashi dukkan hankalin su. Sannan ya soma da yi musu tunasarwa a matsayinsu na musulmi da ya rataya a wuyan dukkanin mu da mu karbi kaddara mai kyau ko mara kyau, mai dadi ko mara dadi, domin samun cikar imanin mu. Dukkansu sun gama mika wuya ga karbar koma me zasu ji a wannan lokacin, wanda ba irin hasashen da basu yi ba kafin kwamishina ya gama zagaye-zagayen sa, zukatansu kamar su fito daga kirazansu a lokacin da Kwamishinan yake gaya musu mummunan hatsarin motar da ya afku kafin a shiga boarder din dake tsakanin Najeriya da Nijar, tsakanin motocin guda biyu babbar (Jeep) da karamar mota (toyota Camry), wanda a take ya yi sanadiyyar rayuka uku. Sauran suka jikkata, mummunar jikkata, kuma su ba su san wadanne ne na wannan motar ba, wadanne ne na waccan motar ba. Gabadaya sun cakude ta yadda sai wadanda suka san su ne kadai zasu gane su. An dai kai gawarwakin guda uku matuary kafin zuwan ‘yan uwansu don su tantance su. Wadanda suka ji ciwo kuma suna karkashin kyakkyawar kulawa.
Sun samu wadannan I.D cards dinne guda biyu na shaidar gida da wajen aiki a aljihun motar Jeep da ta ragargaje na wani Aboubacar da wani mai suna Mansour. Shiyasa aka taho dasu Kano.
A take Malam Raazee da ‘ya’yansa suka soma ambatar, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un�. Yi suke suna maimaitawa, wani ba ya jin na wani.
Kwamishina ya ci gaba da kwantar musu da hankali da tausasan kalamai. Ya fada musu su zo a je su tantance gawarwakin su kuma ga wadanda suka tsira a emergency unit na asibitin Malam Aminu Kano.
Ba su bata lokaci ba suka fito, a cikin mota suka tadda Aalimah ta kifa kai akan sitiyarin mota abin tausayi. Idanunta sun yi ja sun kankance. Fargabar halin da za’a ce mata su Daddy na ciki ya gama karar da dukkan kuzarin ta. Kafin ta dago har sun shigo motar jikin su yanata rawa. Suna masu kauda kai daga gareta. Ba wanda ya iya ya hada ido da ita. Motar ‘yan sandan da za ta yi musu jagora na gabansu, suka ce da Aalimah ta bi bayansu ba tare da sun yi mata bayanin komai ba.
A mutuary na asibitin Malam, ba su bi ta kan wadanda aka ce sun tsira ba, sai wadanda aka ce sun mutu!!!
Allah sarki! Kada ku so ku ga fuskar tsoho Ibrahim Sarhamu Raazee da manyan ‘ya’yansa a wannan lokacin. Shekarun su sun kara bayyana akan jajayen fuskokinsu. Azabtuwa suke a zuci da ruhi. Sun kasa shaida gawar kowa cikin ukun da aka nuna musu sabida yadda halittarsu ta jikkata. Wasu daga ciki hannu da kafa suka fita.
Eidrissa ne ya nuna daya daga ciki, ya ce ko mutuwa ya yi ya dawo wannan Aboulkhairi ne ba zai kasa shaida shi ba. sauran ba su da zabi ban da su amince a fitar musu da shi.
Da taimakon ambulance da kwamishinan ‘yan sanda aka tafi da gawar filin jirgi don yin cuku-cukun tafiya da ita Niamey. Malam ya ce a nuna musu rayayyun, inda likitocin suka kai su ga masu hatsarin.
Hailala suka saki da suka yi tozali da Dr. Mansour a gadon farko babu kafa guda, Daddy Ishaq na kwance cikin tsananin ciwo da karaya har biyar a kafa da hannu, bai san wanda ke kansa ba, sai Aboubacar wanda ke cikin wani irin hali na rai kwakwai-mutu-kwakwai.
Iyakar tashin hankali wadannan mutane sun shige shi irin wanda basu taba shiga a rayuwarsu ba. Duk abin nan da ake Aalimah ba ta sani ba, ta koma gida kamar yadda Oncle Oussama ya umarce ta yace in sun gama abinda suke za su kira ta ta zo ta dauke su. Ta kwantar da hankalinta an same su kuma babu wanda ya mutu amma sun ji rauni sosai kuma suna karbar kulawar gaggawa yadda ya kamata.
Da wannan dan kwarin gwiwar ta tuka motar a hankali kamar mai tafiya akan kwai ta koma gida, tana shiga ta wuce kitchen ta baiwa su Tabawa umarnin su dafa abinci za ta kai wa su mama asibiti, ga Hamoud da Mu’azzam can a falon Daddy su kai musu. Bata bi ta kan su Mu’azzam din ba, wadanda ke can falon Dr. Mansur sun yi zugum-zugum ko hira sun kasa yi a junansu tsakanin sa da kanin nasa Hamoud, Mu’azzam ya cure hannayensa wuri guda ya mikar dasu ya dora habarsa a kansu, banda sallah ba abinda ke tayar da su, ko ruwa basu iya sha ba tun shigowar su falon.
A lokacin ta samu ta rama sallolin da ke kanta, tayi wanka sama-sama, ta canza kayan jikinta. Suna gamawa Sabira tazo har daki ta sanar da ita, ta ba su umarnin su kai wa Mu’azzam da Hamoud falon Daddy, su kula dasu ko suna bukatar wani abu, ita kuma ta dauki na asibiti ta wuce gate ba tare da ta leka su Mu’azzam din ba, ta sanya a bayan mota ta tafi.
Malam Raazee da ‘ya’yansa sun yanke shawarar za su koma Niamey tare da Mu’azzam, don ya halarci jana’izar dan uwansa. Eidrissa da Hamoud su zauna tare da majinyatan kafin a gama jana’iza sai a san yadda za’a yi. In can za su koma da jinya to, in kuma Mu’azzam zai fita da su ne toh, duk da bai san halin da Mu’azzam din zai fada ba in ya fahimci ya rasa dan uwansa rabin-ransa, barin jikin sa, sanyin idaniyarsa, Aboulkhairi. Da haka suka bar asibitin suka bi motar ‘yan sanda tareda ambulance din zuwa filin jirgi. An yi sa’a akwai jirgi wanda zai tashi zuwa Abuja nan da awa daya don haka bazasu samu jinkiri sosai ba.
Kafin su isa airport, Aalimah Oncle Oussama ya kira a waya, yace ta dauko Mu’azzam daga gida ta kawo musu shi filin jirgi, zasu koma Niamey tare da shi, amma Kawu Eidrissa da Hamoud suna nan tare da majinyatan. Don haka ta fadawa Basma da Mama abinda Kawun nasu ya ce, ta tuko motar ta dawo gida don tafiya da Mu’azzam din kamar yadda Baffan nasu yayi mata umarni .
7/4/21, 10:50 AM - Buhainat: HARUNA TANKO
Da ATM card din Aalimah Mama ta biya duka hospital bill dinsu. Basma da ake jinya ita ta koma jinyar Aalimah. Ga danyen jego, ga jarirai sabuwar haihuwa har guda biyu. Abin duka babu dadi garesu ko ta ina. Abincin da masu aikin Mama ke kawowa babu mai iya cinshi. Duk kokari da kwarewar likitocin asibitin international sun kasa tsayar da cikin jikin Aalimah, dole aka yi mata tiyata aka cire shi babu rai, an gama masa halitta tsaf, don samun tata rayuwar. Abin gwanin ban tausayi.
In har kana da zuciyar imani dole ka kokawa iyalan RAAZEE a wannan hali na jarrabawar Ubangiji da suka tsinci kansu. Wanda basu taba tsintar kansu a kwatankwacin sa ba, Basma da jariranta da Mama sun warware, sune suke kula da jinyar Aalimah, yayin da Hamoud da Oncle Eidrissa ke kula da iyayensu da Aboubacar dake gadon asibiti. Duka daga ATM din Aalimah ake biyan duka asibitocin nan. Kafin sakon Mu’azzam ya cimmasu, na dauke marassa lafiyan daga Kano zuwa Amurka, tare da Hamoud.
******
Ranar da likitoci suka sallami Aalimah daga gadon asibiti, ranar ne Hamoud ya daga da su Daddy zuwa asibitin da Mu’azzam ya shirya musu jinya a garin Las Vegas, saukarsu a asibitin Southern Hills Hospital ke da wuya motar asibitin Southern Hills ta kwashe su karkashin kulawar likitoci zuwa asibitin. Dakuna na musamman Mu’azzam ya kama musu bakidayansu, kowanne dakinsa daban.
Tunda suka je ba su ga Mu’azzam ba, basu ji muryarsa koda a waya ba, asibitin ke ta dawainiya da su da bukatocin su tun daga airport, direban da ya dauko su ma na asibitin ne ba direban Mu’azzam ba. Ya kai majinyata asibiti, ya kai Hamoud gidan Mu’azzam ba tare da ya yi masa bayanin komai ba.
A gidan ne Hamoud ya tadda yaron Mu’azzam da direbansa Harrison inda yaron ya ce, zai dinga kawo masa abinci sau uku a kowacce rana bisa umarnin ubangidansa, direban kuma ya ce zai dinga kai shi asibiti wajen majinyatan duk sanda yake so, maigidansu an rike shi a asibiti tun jiya, shima ba shi da lafiya.
Duk kokarin Hamoud na su kai shi asibitin da Mu’azzam din yake sun ki. A cewar su ba’a yi musu wannan umarnin ba. Babu fuska ma daga gare su na a cika su da tambaya, they are very cautious akan aikinsu kowanne abin da ya kawo shi yake yi a gidan ya gama ya tafi.
Hamoud na takawa tsakiyar falon gidan ya ga gaba daya gilassan taga sun ragargazo kasa, duk wani abu na gilashi a fashe yake a gidan. Including talbijin dake manne jikin bango ta kwankwatse. Bai gama fita daga wanan mamakin ba sai da ya kutsa kai dakin barcin Mu’azzam.
Komai yayi raga-raga. Hatta kwan fitila bai tsira ba, da bed-side lamp, duk sun yi kwatsa-kwatsa ga jinin da ya tabbatar na Mu’azzam ne ya disa a wurare daban-daban.
Tsoro, mamaki, fargaba da tu’ajjibi suka cika Hamoud, rokon Allah yake cikin zuciyarsa ya sa ba Mu’azzam ne da kansa ya aikata hakan ba. To in ba shi bane wanene? Da sauri ya fito daga dakin ya rufe, ya nemi wanda zai iya kwana cikin dakunan dake kasa ya sauka a ciki.
Da safe da yaron Mu’azzam ya kawo masa karin kumallo ya tambaye shi dalilin da ya sa bai share gilassan dakin Mu’azzam ba, yaron ya ce, ba’a yi masa izinin shiga ba, amma ya share na falon kasa yanzu, jiya duhun dare bai barshi yayi aikin ba, amma shi zai iya shiga ya share na bed-room din tunda shi dan uwansa ne.
Hamoud ya karbi abin shara da mopper ya nade hannun riga ya shiga aiki, ya share dakin tas, ya goge ko’ina, ya feshe dakin da freshners, sannan ya yi wanka yaci abincin da aka kawo masa yayi shirin tafiya asibiti.
Ya samu su Daddy cikin kyakkyawar kama fiye da wadda suka zo a cikinta, an yi musu wanka, an sauya musu kaya, ga abinci mai rai da motsi suna ta ci, ya bi su daya bayan daya yana runguma yana hawayen farin-ciki. Sannan ya gaya wa Daddyn Mu’azzam abin da ya gani tun shigarsa gidan Mu’azzam.
Nan Daddyn ya ce da shi, kada ya damu, ya san likitoci suna kula da Mu’azzam yadda ya kamata yanzu haka, kuma sai ya dauki tsawon watanni zai fito daga hannunsu.
Cikin bayyanannen mamaki Hamoud ya tambayi Daddy Ishaq wanda ba ciwo ne kadai yake nukurkusar shi ba, ya maida shi ba umh ba uhum umh, ya fiddo tsufansa zahiri wanda jin dadi ke boyewa a baya, sai ido da dogon karan hancin su na iyalin Raazee kadai ya rage a fuskar ma’abociyar zati da kamala, illa rashin ‘Aboulkhair’ da Malam ya gaya masa. Koyaushe za ka same shi rike da carbi, rokon Allah kawai yake ya yi wa Aboulkhair rahama da gafara. Ya hada fuskokinsu da alkhairi. Yasa can ta fiye masa nan. Halin sa nagari ya bishi. Rayuwar duniyar bakidaya ta fice mai a ka.
“Daddy, Mu’azzam yana da disorder ne?�
Ya tsinkayo muryar Hamoud can saman kansa yana tambayar sa. Cikin murya mai ban tausayi da bayyanar da kauna.
Daga masa kai kawai ya yi, hawaye na bin fuskarsa na tausayin Mu’azzam. Ya san tabbas Mu’azzam ya yi dauriya, ya yi dauriya, ya yi dauriya har an zo gejin da kwakwalwarsa ta kasa jurewa, ciwonsa ya tashi, da taimakon rashin magani da baya sha. Shine ya yiwa gidan sa wannan aika-aikar. Wadda rabon da ciwon ya sake tashi yayi irin haka anyi shekaru tara.
Hamoud gefe ya koma ya sharbi kukansa mai isarsa, tausayin Mu’az da kewar Aboulkhair ya lullube masa zuciya, yana sharar hawaye da hankicin sa yake fadin.
“Ubangiji ka saukaka muna! Idan laifi muka yi gare Ka Ya ubangiji Ka gafarta mana!�.
Ya durkushe a wurin yana ta kuka. Daddy Ishaq ma na yi wiwi. Tunda aka fada masa rasuwar Aboulkhair bai yi kuka ba sai fa yanzu. Da Hamoud ya gaya masa halin da Mu’az ke ciki. Ga gabban jikinsa na zogi ta ko’ina, kashi yana hadewa da dan uwansa.
A fili yake fadin,
“Ya Arrahmanurrahim ka saukaka muna! Mun tuba Yaa Ubangiji mun tuba! Hamoud da gaske ne na rasa ABOULKHAIRI???�
Hamoud babu baki sai kuka, da istigfari a fili da yake ta yi.
Likita ne ya bude kofa ya shigo jin koke-kokensu, ganin halin da suke ciki ya ce da Hamoud zai hana shi zuwa asibitin kwata-kwata idan raunata majinyatan zai dinga yi, maimakon ya karfafe su sai ya zo ya raunana su?. Da hannu biyu Hamoud yake rokonsa kada ya hana shi shigowa wajen Kawunninsa. Yana ta kuka a fili kamar ba namijin soja ba, sojan ma na sama. Likitan ya ce, to ya daina kuka a gabansu. Rantsuwa ya shiga yi masa kan ba zai sake ba, amma kar ya hana shi ganinsu. Tausayi ya sa likitan ficewa daga dakin. Ya sayo musu kofa a hankali.
******
Sauki na samuwa gare su a hankali a cikin gangar jiki, amma ban da a zuciyoyin su. Sun gaya wa Hamoud za’a sanya wa Daddyn Aalimah kafar plastic leg da zarar ya samu lafiya. Mu’azzam ya sakar musu katunan bankinsa na bankuna guda biyu; WellFargo da JPMorgan Chase ya ce komai a cira a yi musu, komai ake bukata a cira kawai. Wannan nauyin ya dora shi ne a wuyan tsohon likitansa kuma wanda za’a iya kira amintaccen sa a Las Vegas bakidaya duk da a haife ya haife shi wato Dr. Nebrass Sheldon, wanda ya yi retire shekarun baya, daga baya kuma ya bude private clinic nasa na kansa. Shi ne amintaccen Mu’azzam sabida dadewar da yayi karkashin kulawarsa tun farkon lalurarsa, shi ya daurawa alhakin kula masa da iyayensa da ya kawo asibiti kafin gushewar nasa hayyacin. Yana karkashin kulawar manyan likitocin kwakwalwa yanzu haka abokan aikin Aboulkhair, karkashin jagorancin Dr. Nebrass din wanda yayi gaggawar nema bayan dawowarsa kamar yadda Malam Raazee yayi masa umarni.
A baya Nebrass ya damkawa Aboulkhair file din Mu’az, kulawar sa da komai da ya danganci lafiyarsa ya koma hannunsa, amma bayan dawowarsa daga tafiyar da yayi zuwa gida Niger da rasuwar Aboulkhair zaune cikin kwakwalwarsa, dole ya nemo Nebrass da ya fahimci yana cikin risk na tashin ciwon sa a kowanne lokaci daga yanzu, da kuma rokon da Malam Raazee ya yi masa na ya kai kansa ga likitocin sa, in ba haka ba bazai bar su Daddy a hannunsa ba.
Ko kafin Nebrass ya iso gidansa don ya duba shi, kasancewar baya gari yayi ‘yar tafiya zuwa Orlando Mu’azzam ya riga yayiwa gidansa mummunar illah, ya ji wa hannayensa ciwo, yayi asarar dukiya mai yawa, ya shiga black episode na aggressive tendency sabida ya dade baya shan magani kuma ya kasa karbar reality na rashin Aboulkhairi na har abada a tare dashi....
Nebrass da Daddy sun san juna tsayin shekaru goma sha a baya, tun Mu’azzam na Boston yake dubashi kafin ya shiga jami’a a nan Nevada (Las Vegas). Wato tun dawowarsu Massachusetts sakamakon lalurar Mu’azzam, aka hada shi da Nebrass a matsayin mashahurin neuropsychiatrist din da babu kamar sa a U.S. Tsayin lokacin da Mu’azzam ya dauka yana karbar treatment a hannunsa ne ya haifar da aminci da girmama juna a tsakaninsu, Nebrass ya zama kamar Babansa sabida ya manyanta. A wani bangaren abokin sa. Sannan Mu’azzam na yi masa alheri sosai.
Daddy na kan gadon asibiti, ga dori a ko’ina a kafafu da hannayensa, amma sosai yake magana, yana kuma gane komai da kowa da ke kansa sabanin su Aboubacar. Nebrass ya sameshi a wannan ranar da daddare, ya gaya wa Daddy kudin account din Mu’azzam sun yi kasa sosai, jinyarsu da tasa (wadda ta fi tasu cin kudi) ya lamushe komai, jinya a turai ba wasa bace har ta rayuka uku ban da shi uban gayyar mai karbar (special psychiatric care), ya kara da cewa ya yi reporting din rashin lafiyar Mu’azzam a kamfanin su a matsayin sa na likitansa don haka sun bashi isashshen hutu har zuwa ya samu ingantacciyar lafiyar da yake ganin zai iya komawa bakin aikinsa.
Kamfanin man petir na Chevron na ji da Engnr. Mu’azzam Ishaq Razee sabida hazaqarsa da zurfin ilminsa, don haka yana daga cikin ‘yan gaba-gaban goshin da ake ji dasu a Chevron Corporation. Ya gayawa Daddy salary account din Mu’azzam baya hannun sa, Mu’azzam bai bashi ba, kuma a halin da yake ciki bazai iya tambayar sa ba, don haka kudi tafiya suke ba sa shigowa.
Daddy ya ce ya zo masa da waya ya kira Mummy Zulaiha.
Mummy, wadda ke can Niamey cikin sabuwar rayuwa ta dayanta Allah da jin tsoronsa hadi da jingine farin ciki baki daya a muhallinsa, ta amsa wayar mijin nata a can kuryar dakin Inna Bintou. Gaba daya Mummy Zulaiha ta zama kashi da rai don rama, idanunta kyawawannan sun zama abin tsoro sabida yadda suka zurma cikin kwarmin idanunta. Fatar bakinta ta bushe rayas, alamun babu isasshen ruwa da jini a jikinta. Sakamakon rashin cin wadataccen abinci na lokaci mai tsawo. Tsufan ta da gayu ke boyewa a yanzu ya fito sarari bakidaya kowa na ganinsa.
Daddy Ishaq yace.
“Ku yi shiri ke da Gumsu ku dawo, ku taho da Khaleesat da Yesmin tunda mijinta yana nan tare da mu. Ki nemo (credit cards) dina a suitcase dina ku zo da su Las Vegas�.
Muryar Mummy Zulaiha gaba daya ta dushe sabida yawan kuka, wanda ya zama babban abin yinta tun ranar da aka ce da ita babu Aboulkhair, tun ranar da ta bude kyallen da aka rufe shi ko fatar fuskar sa ba ta yi saura ba, ta zagwanye kamar konewa ta wuta a sakamakon munin hadarin mota, al’amarin da ya jefa ta a wani hali na kaka-ni-kayi, har yau kuma ba ta fita daga cikinsa ba, da tashin hankalin da faruwar hakan ya jefa ta a ciki.
“Daddy Aalimah fa?�
Mummy ta tambaye shi, wasu sababbin hawaye na tsinke mata. Jin cewa zasu koma rayuwa a Boston, babu Aboulkhairi babu mai dakinsa Aalimah.
Shi ma hawayen yake yi, ya ce, “Zulaiha babu magana a kanta yanzu sai ta haihu. Ki barta kusa da mahaifiyarta zata fi sakewa. Kuna tare ne?�
Mummy ta rushe da kuka wurjanjan.
“Daddy cikin ma babu shi, ya tafi tare da Babansa. Na rasa laifin da mu kai wa Ubangiji Daddy, ya yi mana wannan talalar a lokaci daya…�.
“A’uzubillah! Kul Zulaihatu! Maza ki yi istigfari ga wannan sabon. Shi Ya ba mu, ba tareda mun san zai bamun ba, kuma Ya ga damar karbe abinsa a lokacin da ya ga dama sabida ya fi mu bukatarsa. Maza ki yi tuba ga sabonki Zulaiha, ki gode maSa da kyautar rayayyun ‘ya’ya har guda hudu da ya bar maki. Ki roka musu rayuwa mai tsayi da albarka tareda ke.
Hakika rashinsa ba karamin rashi ba ne gare mu baki daya, amma tunda Mu’azzam ya jure ke ma za ki iya jurewa. Ki yi hakuri Zulaiha kin ji, ki yi hakuri, ki yi hakuri ki fauwalawa Ubangiji�.
Mummy na ci gaba da kuka da hawaye da majina, ta ce,
“Na yi hakuri Daddy, na yi hakuri. Ya ya jikinku?�
“Muna kara samun sauki kullum cikin rahamar Allah, har an sayo kafar da za a sanya wa Mansour. Ki gaya wa Aalimah ya ce yana gaishe ta, amma ba yanzu zan hada su su yi waya ba, ina so duka su kara samun sauki a zukatansu tukunna�.
Mummy ta ce,
“Daddy ko kudin tikiti babu a hannuna, namu duk sun yi expire, dole in shiga cikin tsohuwar ajiya ta. Allah sarki Mu’azzam, yau shares (hannun jari) din da ya saya min da kudina zasu yi mana rana�.
Ya ce, “Amfanin neman naki kenan ai, ki rufa min asiri a sanda na gaza, ni ma yanzu aljihuna zan shiga mun cinye na Mu’azzam tas! Rayuwa kenan�.
7/4/21, 10:50 AM - Buhainat: KWATARKWASHI
Duk abin da Ishaq Raazee da dansa Mu’azzam suka mallaka cikin asusunsu na bankunan kasar America ya kusa karewa a wannan doguwar kwanciya jinyar ba da sanin kowa ba daga shi sai matarsa. Bayan su Mummy sun koma Hamoud ya hadu da amaryarsa Khaleesat don shi da direban Mu’azzam suka je debo su daga filin jirgi, sai dai kowanensu zuciya ba dadi. A motar babu wanda ya yiwa dan uwansa magana.
Kai baka ce masoyannan bane masu neman cinye juna sabida soyayya gabanin faruwar wannan al’amari. Saidai ko yaya Khaleesat ta motsa sai ta hango idanun Hamoud akanta ta mudubin motar tana mai mamakin rama da jemewar da yayi cikin ranta. Ta ji zuciyar ta ta tabu. Amma kallon su take shi da aurensa dake kanta matsayin silar rugurgujewar farin cikin iyayenta da ‘yan uwanta.
Dukkansu a tankareren gidan Mu’azzam suka sauka bayan Mummy ta je Boston ta debo katinansu na banki kamar yadda Daddy yayi mata umarni.
Mummy na tausayin wadanda ke kwance a asibiti, amma hakika tana tausaya wa Hamoud da Khaleesat. Wadanda suka dauki alhakin faruwar komai suka dora a kan ‘AURENSU’. Dalili kenan da ya sa suka bi suka tsani auren bakidaya. Har basa son ganin juna. Ga su dai a gida daya, amma Mummy sai ta takura wa Khaleesat ta ke gaida mijinta Hamoud da safe. A cewarta ita bata son ganinsa. Wajen aikinsa nata bukatarsa amma ya kasa tafiya ya bar Kawunninsa a gadon asibiti. A satin da su Mummy suka zo aka ci gaba da ba su treatment domin kafin su zo an yi suspending medical treatment dinsu saboda karewar kudin da ke cikin duka account din Mu’azzam dake hannun Dr. Nebrass.
A kokarin Mummy na rage musu kashe kudi, ta dakatar da sayo wa Hamoud abinci a restaurant da yaron Mu’azzam ke yi sau uku a rana, maimakon hakan sai ta yo cefane mai dimbin yawa ta ke dafa musu bakidayansu, su dama majinyatan asibitinsu ne ke ba su. Wanda ya dace da lafiyar kowannensu.
Mummy na zaune ita da Hamoud a falo aka kira shi a waya. Tana gani ya share kiran, akayi-akayi ya ki dagawa, shi kuma bai kashe ba.
Ta cira kai daga abinda take yi tace, “Mahmoud ba kiranka ake ba ne?�
Ya ce, “To ya zan yi Mummy? Su na gaya min ne hutun da aka deba min na aure ya kare in koma bakin aiki, ni kuma Mummy ba zan iya ba, har yanzu cikinsu babu wanda ya fara taka kafafunsa a kan kasa�.
Idanunsa suka kada suka yi jajir, ya ce,
“Mummy duk aurenmu ne ya jawo ko?�. Ya fara kuka.
Mummy ta tashi ta koma kusa da shi, ta manta da surukuta tasa hannu ta dafa bayansa tana rarrashinsa, sai ga Khaleesat ta fito daga kitchen da faranti shake da abinci a hannunta. Tana ganinsa yana kuka wani abu kamar kibiya ya soki zuciyarta, ta saki farantin a kasa, ita ma ta yi kan Mummy tana kuka.
“Mummy da na san abin da zai faru ke nan, da ban ce ina son auren ba!�.
Hamoud ya dago daga jikin Mummy jin abinda ta fada, yai mata wani irin kallo da saida Mummy ta rasa inda zata sa kanta don kunya, yace.
“Yanzu ne kika san hakan???�
Tace “ko dama can ni ban shirya aure ba, takura min ka yi� yace “nikuma fa da aka takurawa in taimaka in aure ki da wuri ake son yi miki aure ana tsoron kada ki rasa miji?� Sosai Khaleesat ta kulu da jin gorin da yayi mata tace “Ni ce zan rasa mijin? Ai wallahi ka dai fada ne kawai amma nice nayi maka alfarma�.
Mummy Zulaiha ta rasa yadda za ta yi da su Khaleesat, suna manne jikinta sai gori suke jefawa juna, amma kallo daya zaka yi musu ka fahimci fatar bakin su ce kadai ke magana amma cikin kwayar idanunsu kauna ce da soyayya zallah. Cece-kucen su da kukan Khalisat shi ya jawo Gumsu da ke kitchen.
Ta fito ta tsaya daga bakin kofar shigowa falon da ludayin miya a hannunta, hannunta daya ta sa ta kama kugunta, daya hannun ta nuna su da ludayin miyar hannunta, ta ce.
“Mummy, me nake gani haka? Wannan wace irin tabara ce? Kukan soyayya ne wannan ko mene ne???�
Mummy ta ce, “Taya ni gani dai Gumsun Babansu. Sun bi sun daga min hankali. To wallahi ba zai yiwu ba, ba za ku kara min hawan jini da tashin hankali kan wanda nake fama da shi ba.
Ka yi muku booking ku tafi, in ji da majinyatan da ke gadon asibiti�.
Khaleesat da Hamoud suka hau hararar juna, tareda janyewa daga jikin Mummy a lokaci guda, kowanne kamar ya rufe dan uwansa da duka haka yake ji. Gumsu ta yi dariya tace,
“Karshen munafurci yau ina ganinsa a gidan nan. Don Allah ku soke juna da mashi sannan zan yarda kun daina son juna�.
Babu wanda ya kula ta a cikin su.
Hamoud ya tashi ya bar wajen, ita ma Khaleesat haka, amma yana shiga daki ya zauna a bakin gadonsa sai ya samu kansa da sakin murmushi, wani irin lallausar murmushi wanda rabon sa da yin irinsa har ya manta. Zai iya cewa tun faruwar al’amarinnan ga ahalinsa rabon da murmushi ya ziyarci fatar bakin sa. Kalaman Khaleesat da yanayin innocent fuskarta a sanda take fadar su yake tunawa daya bayan daya suna ta sanya shi murmushi. At last she’s mine. Ya fada a hankali, ya mallake ta ta zama tasa da dadi ba dadi. Sai kawai ya hau duba travel routine na kasar Japan kamar wanda ake yiwa umarni. Koda yake umarnin ne Mummy ta yi masa amma mai kama da taimako a gare shi. Ita kuma Khaleesat tana shiga daki kayanta ta soma hadawa. Tana yi tana waiwayen kofa kada Mummy ko Gumsu su shigo su ga abinda ta ke yi.
Alhamdulillah a washegari Daddy 1 da Daddy 2 suka soma taka kafafunsu akan kasa. Da taimakon likitoci da malaman jinya, Aboubacar yana iya zama da kansa, ya samu lahani ne mai matukar hatsari, karfe ne da gilashi suka shige cikin cikinsa, kusan aikin da aka yi masa ya fi na su Daddy cin kudi, su sun taka kasa, shi kuma ya zauna da taimakon (pillow).
Suka yi hira da Hamoud sosai a wannan ranar inda ya gaya masa jibi zai koma bakin aikinsa, amma kafin nan yana matuqar son a barshi ya ga Mu’azzam. Aboubacar ya ce “idan Nebrass ya zo ka roke shi na ga alama yana da kirki. A hannunsu Mu’azzam yake a private clinic dinsa�.
Da shawarar Aboubacar Hamoud ya yi aiki. Washegari da Dr. Nebrass ya zo har kasa ya durkusa yana rokonshi ya bar shi ya ga Mu’azzam, shi yana yi Aboubacar na yi har da hawayen su, ya rasa yadda zai yi da su, shi da ma Daddy Ishaq bai sa aka ba. Ba su san Mu’azzam ba ne, yanzu haka ya dade da samun sauki, ba ya son ganin kowa ne. He prefers to be alone a irin wannan yanayin. Nebrass ya ce su yi masa alfarma ya fara neman izinin Mu’az din tukunna, kada su mayar masa da aiki baya.
Aboubacar ya ce,
“Ka gaya masa karfe da gilashi sun huda min hanta, ya bar ni in ganshi kafin in cika�.
Hamoud kuma ya ce,
“Ka gaya masa gobe zan koma Japan, kuma sai na yi shekaru uku ban zo gida ba, zan tafi tare da kanwarsa, muna neman albarkarsa�.
Dr. Mansour ya ce, “Kada ka gaya masa na rasa kafa, amma ka ce masa I want to shed my tears before him, sannan ne zan daina jin rashin Aboulkhair da na yi. Sai na ganshi zuciyata za ta rage ciwo!�
Dr. Nebrass ya ce, sakonnin sun masa yawa, ba zai iya rikewa ba, kowa ya rubuta nasa a takarda. Duk haka suka rubuta jiki na rawa suka ba shi. Ya dubi Daddy 1 (Ishaq) yana murmushi ya ce,
“Kai ba ka da sako?�
Murmushi ya yi mai fadi (broad smile) ya ce a gajarce,
“Babu!�.
Wanan kauna ta zahiri da badini da dan uwansa da ‘ya’yan ‘yan uwansa suka gwada wa Mu’azzam a kan idonsa, ta wadatar da shi da zuciyarsa, ya fahimci Mu’azzam din mutum ne abin so, mai matukar kima da daraja a gare su!!!.
****
Lokacin da Dr. Nebrass ya kai wa Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee sakon ‘yan uwansa da Baffansa, yana zaune gefen gadonsa na asibiti yana shan hot coffee. Coffee ne mai zafi da kauri wanda yayi daidai da yanayin da ake ciki na tsananin sanyi a birnin LasVegas a yammacin ranar wata Asabar. Yana sanye da thick coat ruwan toka a sama da karamar riga short-sleeved daga ciki da dogon bakin wando (Armani code). Suma ta taru a kansa sosai tasu ta buzayen usli duk da kasancewarsa ba ma’abocin tara ta ba. Amman zaman asibiti yasa yanzu ta taru sosai ta mummurde ta zama wani irin curl.
Takardun ya bi daya bayan daya cikin nutsuwa yana karantawa, Dr. Nebrass na tsaye a kansa yana son ganin reaction dinsa. A matsayinsa na likitansa komai na Mu’azzam din sai ya rubuta musamman ci gaba irin wannan ga lafiyarsa. Ana so Mu’az din ya dinga socializing da mutane na jikin sa musamman masoyansa irin haka, zasu taimaka kwarai wajen restoring farin-cikin da ya rasa.
Gani ya yi Mu’azzam ya yi dan murmushi abin da tun zuwansa gadon asibitin bai yi ba. Ya daga kai yana kallon likitan, murya a sanyaye cakude da damuwa ya ce,
“Haka Aboubacar ya ji ciwo???�
Nebrass ya ce,
“Duk ya fi su jin mummunan rauni�.
Har zai gaya masa Dr. Mansour babu kafa, ya tuna ya ce kada ya gaya masa. Cikin lallashi da siyasa ya ce,
“In zuciyarka ba ta amince wa ganinsu ba zan ba su hakuri. Amma hakika sun damu sosai da son ganinka, musamman mai rauni a cikin, har hawaye yake min. Shikuma dayan dana ji sun kira, Hamoud, daga yanayin sa zai iya bada komai da ya mallaka don ya samu ganin ka ko sau daya ne kafin ya wuce�.
Mu’azzam ya runtse idonsa, da sauri kuma ya bude su akan likitan ya ce,
“Let them in, please…�.
Dr. Nebrass ya bude kofar, Hamoud ya turo Aboubacar a hankali kan kujerar marasa lafiya na musamman, wadda ke hade da na’urori a jikinta, Mummy ta turo Mansour Raazee kan kujerar guragu, Mu’azzam sai ya saki kofin coffee da ke hannunsa ya zube a kasa, kofin ya fashe, ya sanya fuska a tsakanin cinyoyinsa ya sanya kuka mai tsuma rai.
“Wace irin kaddara ce ta fado wa rayuwarmu haka?�
Gumsu ce ta karshen shigowa, ta turo Daddy Ishaq a tashi kujerar, bai rasa kafa ko hannu ba, amma raunikan jikinsa da suka sha plasta Allah ya yi yawa da su. Har gaban Mu’azzam Mummy ta kai Daddy Mansour.
Matsawa yayi kusa da Mu’azzam din sosai ya runguma shi a jikinsa, ya kai hannu bayansa yana shafawa a hankali, yana mai magana cikin taushin lafazi, yana tunasar da shi ya godewa Allah cikin kowanne hali. Ni’imominsa gare mu sun fi jarrabawarSa yawa.
“Mu’azzam ka ce Alhamdulillah! Ka yi wa dan uwanka addu’ar samun rahma da gafarar Ubangiji�.
Wato duk inda Gumsu ta ke, sai an san tana wuri, yanzu ma cewa ta yi cikin kulawa,
“Doctor me Mu’azzam ke son ci in dafa masa gobe?�
A hankali Mu’azzam ya cira kai yana son ganin wace ce wannan ana ta rai da lafiya tana ta abinci?
Ganin kallon haushin da yake mata ta ce, “Kalle ni da kyau, ni ce Gumsun Daddynku. Mu’azzam komai ya yi zafi maganinsa Allah, ka daina kuka ka kama hailala. Na fi ka jin rashin dan uwanka, ni abokiyarsa ce, abokiyar shawararsa. Amma na san soyayyata da shi shi ne in ta yi masa addu’a ba zubda masa hawaye ba, ka ji Mu’azzam?�
Cikin ransa yake tambaya, ita kuma wannan wace ce a cikin dangi??
Dr. Nebrass surutun Gumsu ya fara hawa masa kai. To balle kuma Mu’azzam ya sani, don haka ya ce su koma su bar Mu’azzam ya huta, tunda sun ganshi.
Da ma motar asibitin da suke ce ta kawo su da taimakon Nebrass, aka maida kowa inda yake.
Mu’azzam ya jingina da taga yana kallonsu, ana sanya majinyatan a mota with care, iyayensa masu tarin koshin lafiya da kuzari. Wato rayuwa gaba dayanta ba ta da tabbas! Kuma dan adam har ya mutu ba’a gama mai halitta ba; yau Baba Mansur ne ya zama gurgu. Wasu zafafan hawaye suka kwararo masa. Fata yake ya bude ido ya ga cewa duka wannan mafarki yake yi, fata yake ya juya bayansa ya ga shigowar Aboulkhair rike da magungunan da zai sha wunin yau maimakon Nebrass. Fata yake ya juya ya ga shigowarsa da jarida ya zo masa da labari. Fata yake ya juya ya ji ya ce ya sauko kasa su ci abinci Aalimarsa ta dafa musu! Fata yake ya juya ya ji shi yana hawowa upstairs din gidan sa da takun nan nashi gudu-gudu, sauri-sauri irin na zaratan matasa masu cike da koshin lafiya da kuzari.
Hakika dan adan bai hada sani da Ubangiji ba; Da ya san rayuwarsa a Las Vegas gajeriya ce da ya bar shi sun zauna tare a gidansa kamar yadda Aboulkhair din ke matukar so. Da ya san rayuwarsa gajeriya ce a Las Vegas da ko kusa bai bari sun zauna a muhalli daban-daban ba. Da ya jure wa kowacce irin hayaniya ta Aboulkhair ya zauna tare da shi har karshen rayuwarsa.....!
Inama ana maida hannun agogo baya!!!
Ina ma… Ina ma… Da na sani… Duka abubuwa ne wadanda dan Adam ba shi da maganinsu! Wadanda ba sa wanke zuciya a lokacin da suka riga suka yi wa zuciyar kawanya… Azabtar da zuciya suke don sun san cewa sun riga sun yi mata illa ta ko’ina. Kalmomi ne da ya tabbatar ba za su daina yi wa kunnuwansa azaba da amsa-kuwwa ba, daga yau har zuwa karshen rayuwarsa.
7/4/21, 10:50 AM - Buhainat: ADAMA DAUDA
“Daure ki sha, ko kurba uku ne kin ji?�
Juyar da kai ta yi cikin son fashewa da kuka. Mama ta sake komawa barin da ta juyar da kan cike da damuwa da kofin mug na tangaran a hannunta mai cike da kunun kanwa.
“Kin san jikinki jikin jego ne Aalimah, ki dinga shan kunun nan ko da ba za ki ci komai ba bayan shi. A ce magana daya kullum sai an yi ta nanata ta kamar cin kwan makauniya?�
Fuska ta sanya cikin tafukanta biyu ta fara wani irin kuka. Wanda ke tasowa tun daga karkashin zuciyar ta. Sautin sa na mai bayyana halin kunci da ragaita da zuciyarta ke ciki.
“Ni Mama ki rabu da ni, don Allah ki kyaleni�. Ta furta cikin wata murya mai ban tausayi.
Daidai lokacin da likitar da ke kula da ita ta bude kofa ta shigo da Nurse biye da ita. Cikin sakin fuska ta isa gaban gadon da Aalimahn ta ke, inda sabo sun saba da wannan kukan na Aalimah tun kwantar da ita a asibitin. Gata bata jin lallashi. Tausayi dattijuwar take bata sabida yadda ta damu da ‘yar tata. Ta karbi kofin daga hannun Mama, ta cire hannun Aalimah daga fuskarta, wanda tuni ya jike sharab da hawaye.
“Mrs. Aboulkhair ba sai na sake maimaitawa ba, jikinki yana bukatar sinadarin abinci mai gina jiki, kada ki manta ‘Da’ aka cire a jikinki ba karamin ciki ba. Ki rage wa Maman ki da ‘yar uwarki damuwa ki dinga cin abinci kin ji?
Allah ba ya dora wa rai abin da Ya san ba za ta iya dauka ba�.
Ta kai kofin kunun bakinta. Aalimah ba ta da zabi ban da kurbar kunun. Tamkar koyaushe dandanon abinci ya fi dacin madaci daci a bakinta. Amma saboda wannan taron dangin da suka yi mata, Dr. Rayhanah na yi, Mama na yi, dole ta shanye kofin kunun nan tsaf. Nurse da Doctor na kara lallashi, Mama ma na yi da tattausan lafazi, yayin da Basma ke zaune daidai kafafun Aalimah tana shayar da jaririyarta, Hussainar na goye bayan Mama.
Halin da suke ciki kenan tun bayan rasuwar Aboulkhair da tafiyar Daddy 1 da Daddy 2 da Aboubacar kasar Amurka. Ba su da kowa da suke gani su ji dadi sai junansu. Wata irin kewa ke rarake zukatansu da ciwo mai tsanani. As a husband, ya kasance miji abin kwatance, kasaitacce a zuciyar matarsa wanda babu wanda zai iya tona zuciyarta ya ga halin da ta ke ciki, sai ita kanta. As a brother, shi dan uwa ne like a diamond a wajen kannensa, babu mai iya tona zuciyar Basma don hango zurfi da fadin wannan rashin da ta yi sai ita kanta. Amma sosai ta fi Aalimah juriya, domin ba a fada da ita a kan cin abinci ko don jariranta su samu nasu abincin da Allah ya halitta a jikinta. Sosai ta ke cin abinci, sai in abin ya ciyo ta ne ta ke dangwarawa Mama su ta kulle kanta a toilet ta yi ta kuka.
Yau likita ta ba su sallama, ba don zukata sun warke daga zogin da suke ba a’ah, sai don dukkaninsu suna da lafiya ta gangar jiki. Suka tattara suka koma gida, mama na ci gaba da gasa wa Aalimah da Basma jikinsu da tawul. Sun samu wayar Mummy da Aunty Gumsu inda suka yi musu sallama suka ce za su koma su ma don jinyar su Daddy, saboda Hamoud zai koma bakin aikinsa. Lokacin da suka bai wa Khaleesat wayar don ta yi sallama da su, domin tare da mijinta za ta wuce daga can ba su tsinana komai ba su duka ukun a handsfree sai kuka.
Mama ce ta kwace wayar. Tun daga ranar ba su kara ji daga su Mummy ba, suka ci gaba da jego karkashin kulawar Mama.
Ranar da Basma ta yada wanka aka yi arba’in din Aboulkhair a Yamai, sakon Malam Raazee ya isko su cewa, dukkansu su yi shiri su koma Niamey, zuwa har su Aboubacar su dawo gida. Mama ta soma yi musu shirin tafiya, an yi sa’a su Sabrina suna cikin hutun makaranta.
Basma ce ta saya musu tikiti, daga na Abuja har na Niamey. A washegarin ranar suka daga bakidayansu bayan Mama ta sallami masu aikinta Tabawa da Sabira da cewa inta dawo za ta neme su su dawo bakin aiki. Bilyaminu ya yi musu fatan alkhairi bayan Aalimah ta biya shi kudin aikinsa na gadi, har na wata uku masu zuwa a gaba.
A dakin inna Bintou suka sauka, Mama na dakin Inna Kasisi. Tunda suka zo Basma ba ta san kukan jariranta ba, kullum suna goye a bayan Bintou da Kasisi, idan Malam ya dawo zai ce a kai masa su su taya shi hira. Inna Bintou ba ta barinsu su zauna zugum-zugum din da suke zama, yanzu za ta dauke musu hankali da hira ko da ba za ta samu su tofa albarkacin bakinsu ba sukan yi murmushi. Ta ce Basma ce mai sa wa a yi kuka, don haka ta koma dakin ‘yammata ta bar mata Aalimah mai maida komai ga mahaliccinta.
Abin da ba ta sani ba har gara Basma na yin kuka ta ji dadi a zuciyarta, ita al’amarin da ta ke ji a tata zuciyar yanzu bayan dawowarsu Yamai ya fi karfin ta zubda hawaye. Baza ta gaji da cewa mutuwar Aboulkhair ta shammace ta ba; muguwar shammata. A daidai lokacin da take ganin babu diya macen data kaita sa’ar samun farin cikin dake cikin rayuwar aure. Rokon Allah ta ke yi ya dau ranta ta bi Aboulkhair a ko’ina yake, kuma cikin kowanne hali, a ganinta hakan shi ne kawai kwanciyar hankalinta da samun farin cikinta.
Ba ta son tuno komai na rayuwar da suka shimfida tare. Idan ta kai hannu ta shafa cikinta ta ji shi ma babu, zuciyarta neman fitowa ta ke daga allon kirjinta. Hakika an jarabci rayuwarta da mafi tsananin jarrabawa, tana rokon Allah cikin sujjadar kowacce sallar farillarta, ya kawo sanadin da za ta cinye wannan jarrabawa idan mai cinyuwa ce. Domin ta shafa a ko’ina ba ta ga ranar da za ta haye ta ba. Idan dawowar farin ciki cikin rayuwarta shi ne tsallake wannan siradin, tana da tabbacin har abada ba za ta tsallake shi ba. Ba mutane irin Aboulkhair ke shigowa cikin rayuwar dan Adam su fita da sauki ba. Ba mutane irinsa ke ajiye memories irin wadanda da za’a iya daina tunawa cikin rayuwar auratayya ba.
****
A LAS VEGAS
Watanni hudu kenan da faruwar wannan al’amari ga iyalan Raazee. Cikin wadannan watanni al’amura da yawa sun faru, majinyatan suna ta samun sauki cikin yardar Ubangiji. Dorin Daddy 1 da Daddy 2 na kafafu da hannaye duka ya yi kyau, an kuma kunce. Daddy 1 na tafiya da taimakon croches karafa guda biyu, yayin da Daddy 2 ana jiran raunin kafarsa ya karasa warkewa a makala masa plastic leg, wadda Mu’azzam ya saya masa. Aboubacar ya warware bakidaya sai dan sauran abin da ba’a rasa ba, don haka aka soma yi masa shirin tahowa gida don komawa cikin iyalinsa.
Duk tsawon zaman jinyar nan da Aboubacar ya yi ba su yi waya ba shi da Basma, asibitin ba sa barin majinyatansu rike waya don samun cikakkiyar nutsuwarsu. Haka Hamoud da ya wuce Japan shi da Khaleesat bai hada su sun gaisa ba ko sau daya. Mummy da Gumsu da ke yawan zuwa ganinsu, sai dai su fada masa lafiyar Basma data jikokinsu twins Don haka a yau da likitoci suka tabbatar masa da samun lafiyarsa suka kuma ba shi sallama, cike ya ke da dokin ganin iyalinsa.
Ba yadda Mummy Zulaiha ba ta yi da Aboubacar ba a kan ya kara sati daya ko ya kara murmurewa ya kara samun karfin jikinsa, amma Aboubacar ya ki. Yace Basma ta karasa jinyarsa. A daddafe ya kara kwana uku a gidan Mu’azzam bayan sallamarsa daga asibiti. Mummy ta saya masa tikiti mai zuwa Niamey kai tsaye daga Las Vegas babu transit.
Mummy Zulaiha a wannan dan lokacin ta yarda kishiya ‘yar uwa ce (idan ka yi katari da mai kyakykyawar zuciya kuma ta kirki). Gumsu ta zama kamar kanwarta ta jini, tare suke gudanar da dukkan al’amuransu na yau da kullum a gidan Mu’azzam, kama daga girki yau wannan ta yi, gobe wannan ta karba, jinyar mijinsu da dan uwansa da taimakekeniya a tsakaninsu. Gumsu-Moiram, ba ta da matsala ko kadan, ke dai barta da wauta, ban dariya da barkwancinta wadanda ke sayo mata soyayyar jama’a, inda duk ta zauna sai an san da ita a wurin saboda ban dariyarta. Mummy ta samu kanta da jin kunyar kanta in ta tuno haukan data rika yiwa mijinta da ‘ya’yanta akan auren Gumsu. Ita kam in haka kishiya take, to tana alfahari da tata, da zuciya daya take son ‘ya’yan ta. Sai ka rantse da Allah kwanciyar mijinsu jinya ba ta dame ta ba, harkan gabanta kawai ta ke, shi ma kansa Daddyn gaya masa ta ke a gaban kowa.
“Gara ma ka mike daga jinyar nan haka Daddy, Allah ya gani na yi hakuri. Gumsu ba ta da wani mijin bayan kai, ya ya ka ke so ta yi da ranta?�
Ko a gaban likitoci Gumsu kan fadi wannan magana idan ta bushi iska, sai dai Daddyn da Mummy su ji mata kunyar ita babu ruwanta.
Bayan tahowar Aboubacar, ya zama daga Daddy 1 sai Daddy 2 a gadon asibiti. Ba dakinsu daya ba, kowa da dakinsa daban, amma suna yawan haduwa, in an fito da su shan iska a garden din asibitin ko an fito da su motsa jiki a gym. A nan ne su kan yi hirarrakinsu da suka shafe su ko ‘ya’yansu, da kuma iyayensu da ke gida Niger.
A yau ma kamar kullum, an fito da su ‘garden’ domin shan iska. Daddy 1 ( Ishaq) ya dubi kaninsa Daddy 2 (Mansur) ya ce,
“Ina lissafe da watanni, Aalimah ta dade da gama takaba, me ka shiryawa rayuwar ta a bangarenka?�
Daddy 2 yayi saurin girgiza kai, a sanyaye ya ce,
“Me kuwa na shirya mata ban da abin da Ubangijinta ya shirya mata?
Muna namu Allah na nashi, kuma nashin shi ne gaskiya, dukkanmu lalube muke yi a cikin duhu.
A da ne nake wannan wautar (future planning) ga ‘ya’yana, amma yanzu kullum cikin istigfari nake a bisa hakan. Duk abinda Allah ya shiryawa rayuwarsu dai-dai ne�.
Daddy 2 ya yi murmushi, shi shaida ne a kan cewa Mansour ya fi shi shiga tashin hankali da rashin Aboulkhair, ya dade yana sambatu har a cikin baccinsa. Ko lokacin da ake masa gyaran karaya akwai Aboulkhairi cikin sambatunsa irin na radadin ciwo. Wani tunani ne mai nauyi ke yawo a zuciyarsa daga jiya zuwa yau, wanda ya ke tsoron furtawa gare shi, ko ko ya ce, ba shi da ikon furta shi ga kowa ko ta ina aka je aka dawo. Don haka ya ja bakinsa ya yi shiru, yana sauraron bugun da zuciyarsa ke yi, wanda ke tafe da sake da jaddada masa muhimmancin maganar da ba ya son yi din da kowa banda zuciyarsa a kowanne bugu guda daya na zuciyarsa, tunanin ya hana shi sakat, shi kuma yana bi yana danne shi da fin karfin zuciya da karfafa imani.
A yau ne aka sallame su bakidaya daga asibitin Southern Hills, direban Mu’azzam ne ya kwaso su dukkansu zuwa gidan Mu’azzam, Mummy ta ce ya lissafa mata albashinsu daga ranar da Mu’azzam ya shiga asibiti zuwa yau ta biya su. Budan bakin Harrison sai cewa ya yi, albashin shekara Mu’azzam yake kullawa a lokaci guda ya basu, kuma ko ba don haka ba shi mai hidimtawa iyayensa ne ko babu ko sisi sabida kyautayinsa, jin kansa da kyautatawarsa gare shi. Harrison ya kare zancensa da cewa;
“I wish him a quick recovery�.
Ya fita ya bar falon. Fuskarsa dauke da alhinin rashin sanin halin da Ubangidan nasa ke ciki. Wanda yake jin kamar ya dauka ya mayar a kansa.
Falon ya saura Daddy 1, Daddy 2 da matansa guda biyu, Yesmin da Nurat sun fita da Harrison zai kai su saloon, Daddy 2 ya ce,
“To alhamdulillahi, ni ma lokacin komawata gida ya yi, wannan gari naku sai ku, sanyin cikinsa mai takurawa da matsantawa ne. Yaya Ishaq, Zulaiha, Gumsu-Moiram na gode da dawainiyar ku, Allah ya rubuta a mizanin Hassanaat na zumunci, ya sa ya zame mana silar shiga aljanna baki daya, Ya jikan Aboulkhair, halinsa na gari ya bi shi. I have missed a darling son but I’m sure Ubangiji Rahmanur-rahimu ya fi ni son shi….�.
Bai rufe baki ba ya lura sun soma yin sana’ar tasu (sharbe) Zulaiha da Gumsu, babu yadda za’a yi a ambato Aboulkhair a waje ko a yi masa addu’a suna wajen ba su zubda hawaye ba. Don haka ya yi maza ya sauya zancen sa da tambayar Daddy 1 yaushe Mu’azzam zai fito daga asibiti?
Zai so ya ganshi kafin ya koma. Akwai zantuka masu muhimmanci da yake son yi da shi. A take Daddy 1 ya karbi wayar Mummy. Dr. Nebrass ya kira, suka yi magana ya maida wayarsa aljihu.
Ya dubi kanin nasa ya ce, sai sabon wata za su kyale Mu’azzam ya shiga harkokinsa, they are very cautious a kan aikinsu ba kamar kasashenmu na Africa ba, sai sun tabbatar ba shi da damuwar da za ta dami kwakwalwarsa, kuma zai iya aikinsa normally, sannan zai iya daukan al’amuran rayuwa a zahirin yadda suke ba tare da sun shafi matsalarsa ba, amma shi zai iya ganinsa idan Mu’azzam din ya amince.
Ko da Nebrass ya gaya wa Mu’azzam Kawunsa na son yin sallama da shi zai koma Nigeria, bai ki ba. Hasalima sosai yake son ganinsa shima, ko yana kin jama’a ban da kawu Mansour da Aboulkhair shi kansa bai san dalili ba. Watakila don sun fi kowa iya tafiyar da shi ne da odd behaviours dinsa (baudaddun halayensa). Tare suka shiga dakin Mu’azzam da yammacin ranar, inda suka same shi yana sallah, Dr. Nebrass ya fita, Daddy 1 ya zauna zaman jiransa ya idar yana jan tazbahar hannunsa.
Bayan ya yi sallama ya dade yana addu’a, ko ba’a tambaya ba Daddy 1 ya san me Mu’azzam yake roka. A yanzu ya sani ba shi da wata bukata mafi muhimmanci wadda ta wuce ta samun rahmar Aboulkhair a wajen Allah. A sanda yake raye, ba su da bukata mai muhimmanci sai junansu. Aalimah ta taba gaya masa sabida Mu’azzam Aboulkhair ya dage ya tsaya tsayin daka ya karanci neuropsychiatry.
Al’amarin da ya dade yana burge shi hadi da kayatar da shi a zuci. Ya dade bai ga ‘yan uwan da ke son juna fisabilillah irin Mu’azzam da Aboulkhairi ba ko a labaran hikaya. Ta kuma gaya masa irin takaddamar da suka sha da Mu’azzam kan su zauna gida daya amma ya ki amincewa. Ba ya karantar zuciya, amma ya san Mu’azzam na nan yana regretting. In ya ce regretting yana nufin nadama mai sa zuciya ciwo da hanata jin dadin rayuwa ko ta yaya. Allah kenan.
7/4/21, 9:48 PM - Buhainat: HABUBAKAR ADO
#######################################################
Cikin satin suka biyo jirgi da komai nasu suka baro kasar Amurka. Bari na din-din-din. Ishak Raazee na mai jin wata irin kewa wadda sabo ke haddasawa na mamayar zuciyarsa. Mummy na mai jin kamar ita daya ta rage a fadin duniya sabida kewar mijinta da ‘ya’yanta. Saidai ko kadan bata yi nadamar hukuncin da ta zartas ba. Yesmin na kuka kamar ranta zai fita a kan rabuwar iyayenta, suka taho shi da Moiram da diyarta Nurat, ya baro mata Yesmin ne don rage mata bacin rai.
Haka Mummy ta yi kokarin shanye damuwarta wannan karon ba tare da ta raba ta tare da Mu’azzam ba, ganin cewa bai jima da barin gadon asibiti ba. Kuma in ba za ta manta ba Aboulkhair ya hane ta dora wa Mu’azzam damuwa, ko dai ta shanye kayar ta ita kadai, ko ta raba ta tare da shi (Aboulkhair) din, amma sharing dinta da Mu’azzam babbar illa ce ga kyakkyawan treatment din da yake samu.
Ko da ta koma office a washegari da niyyar bada hakuri a maida ita bakin aikinta wani ta tarar a mazauninta (JP MORGAN CHASE) ba su daukar wasa da aiki, ko da kuwa da excuse. Balle ita nata babu excuse din ma. Rana daya aka nemeta a kasar aka rasa. Tsabar rudanin rayuwar data samu kanta ya mantar da ita cewa ita din ma’aikaciya ce, ma’aikaciyar ma ta babban bankin Amurka irin JP Morgan. Haka ta dawo kafafu a sage, ta soma neman wani aikin ta yanar gizo, amma har watanni uku suka shafe bata dace ba. Sakamakon matsin lambar da musulmin kasar ke fuskanta a lokacin daga sabuwar gwamnatin Amurka karkashin mulkin sabon shugaban kasa Donald Trump. Da yawa sai komawa suke kasashen su na asali. Ba don Yesmin da ke zuwa makaranta ba Las Vegas za ta tattara ta koma bakidaya, in Mu’azzam ba zai rike ta ba ita da autarta, ya san yadda zai yi da su. Shine kadai dolenta a yanzu.
******
FLASHBACK
An sallami Mu’azzam ranar wata lahadi, sati guda kacal ya kara a gida, sannan ya koma aikinsa. Ya hada wayoyinsa, ya kira duk wanda ya dace ya gaisar. Ciki har da Mummy, ta gaya masa tana Boston amma ba ta gaya masa cewa Daddy ya sake ta a kansa ba. Sosai ta koyi hadiye damuwa, in ta tuna da Aboulkhair.
Ta san da yana raye ransa zai yi matukar baci, za ta kiyaye abin da ba ya so a bayan ransa. Ta kasance mai bata masa rai da hakan a sanda yake raye. Zata kasance mai kiyayewa a sanda babu shi. Ta ce masa Daddy yana Niamey, kuma ta turo masa kudi cikin account dinsa kafin ya samu albashi ya soma shigo masa ta san zai bukace su sosai.
Sosai ya yi godiya, yana mai jinjina soyayyar uwa ga abin da ta haifa, ta Mummy is special. Ita dai ‘ya’yan ta kawai. Su samu jin dadi shine burin ta. Kada su nemi wani abu su rasa a rayuwar su. Bazata taba canzawa daga hakan ba.
Ya kira Daddy suka yi hira sosai, inda ya gaya masa ya koma Yamai, ya samu aiki a can da hukumar hulda da kasashen wajen su, yanzu kuma ya samu wani makeken fili kusa da gida ya saya ya fara gini. Gini yake so ya yi one in town wanda dukkansu zasu sake a cikin sa.
Ya cigaba da gaya masa amon muryarsa dauke da kauna irin ta uba ga dansa, irin tsarin duplex din da yake so a yi masa. Yace sai yafi gidansu na Boston kyau nesa ba kusa ba, zai masa part din sa guda wanda zasu ke sauka in sun zo shi da iyalinsa. Sosai ya baiwa Mu’azzam dariya. Ya canza position din rikon wayar daga dama zuwa hagu ya cigaba da sauraron almarar Daddy. Koko ya ce mafarkin Daddy. Ba tare da Daddyn ya kula da karbar da yake yiwa zancen nasa ba ya cigaba da labarta masa cewa har dakin yaran su za’ayi a cikin bangaren nasu, a zuba duk wani nau’I na kayan wasan yara. Mu’azzam tausayin mahaifin nasa yayi matukar kama shi, su iyaye wato har kullum fatan su nagari ne ga ‘ya’yan su ba ruwansu da reality din da rayuwar ‘ya’yan ke fuskanta.
Ji yayi idanunsa na son kawo ruwa, don haka ya matsu su yi sallama da Daddy. Ko kusa bai yi masa zancen mahaifiyarsa ba har suka yi sallama, hausawa suka ce wai ido da kunya. Ba zai iya kallon tsabar idanun sa ya gaya masa ya saki uwarsa ba sabida ta zabi zama a kusa da shi ta bashi kulawa. Sai Mu’azzam ya dauka za ta bi su ne daga baya in ta gama kintsawa, tunda ita ma’aikaciya ce. Bincike-bincike da zakule-zakulen halin da wani ke ciki da ma tun fil azal ba halinsa ba ne shi.
Cikin dan lokaci Daddy Ishaq ya gama ginin kyakkyawan duplex dinsa a nan unguwarsu plateaux suka koma shi da Gumsu. Wannan ya kawo tabbataccen kwanciyar hankali a zukatan iyaye da ‘yan uwansa. Ranar litinin ya soma shiga sabon ofishinsa a Ministère des affaires ètrangères na kasar Niger.
Duk da ko kusa ba za’a hada sauki da sukunin rayuwar yanzu da wadda ya yi a baya ba, yafi jin dadin rayuwar yanzu, akan ta baya. Cike yake da godiyar Allah da ikhlasi a zuciyarsa, da albarkar iyaye baibaye da shi. Kullum sallolin su biyar cikin jam’i suke yin su shi da ‘yan uwansa da mahaifin su a masallacin dake like da (main house) dinsu. Babu wanda ya san ya saki Mummy, sai Malam da Inna.
Mummy ta dukufa neman aiki a yanar gizo don saving dinta ya fara yin kasa sosai. Kason data ke karba duk wata na shares dinta duk a cikin su da lalurorin yau da kullum yake tafiya. Rayuwar mai tsada ce sosai. Ta dukufa neman aiki ba ji ba gani amma kamar wadda uwa ta cewa jeki kya gani ko aptitude babu wanda ya kira ta duk da experience dinta. Ita ke dauke da nauyin karatun Yesmin, cinsu da shansu da maintenance din gidan, ga wanda ta ke turawa Mu’azzam duk da ba shi ya tambaya ba kuma ya hana ta amma ta ki ji, kullum gani take kamar albashinsa baya isar sa sabida tsadar magungunansa da rayuwar da yake yi mai tsada. Tana cikin wannan halin aka zo aka ce ta tashi daga cikin gidan masu shi za su shiga, aka nuna mata shaidar mallakar takardu da komai.
Ba da saninta ba Daddy ya dade da sayar da gidan ya karbe kudinsa ya tafi da su kasar haihuwarsa don ya gina gida acan, da kuma niyyar sa ta fara kasuwanci da su irin wanda ya taso ya ga Malam da manyan yayyunsa na yi, wato na shigo da kayan abinci daga kasar Faransa zuwa jihohin kasar Niger.
Bala’i goma da ashirin ga Mummy, Ishaq ya shammace ta, bata taba tsammanin zai sayar da gidan nan ba, daga karshe kan ba yadda zata yi ta tattara ta taho Las Vegas ita da Yesmin gidan Mu’azzam.
Mu’azzam sai dawowa office yayi ya gansu da iyayen kayansu tirim! Sun gyare dakin da Mummy ke sauka in tazo sun baje suna barcin gajiya. Ya tura Harrison yayo musu takeaway din abinci. Kwanansu uku kacal hayaniyar Yesmin ta fara hana Mu’azzam sakat, duk da kokarinsa na bin shawarar kawunsa Mansour na ya bude zuciyar sa ya kaunaci ‘yan uwansa, ya ba su kauna da kulawar da Aboulkhair ke ba su, yayi acting na mutum biyu a gare su, ya ga cewa abun kamar da wuya ba zai iya ba! Ya yi duk iya kokarin sa amma ya kasa. Mummy ta riga ta gama shagwaba Yesmin ta yadda bai isa ya tsawata mata ba yanzu zai ga bacin ran Mummy, kullum Yesmin sanyata take a gaba tana kuka wiwi kamar ‘yar goye kan wai su koma Boston bazata iya barin makarantun ta na can ba ko a maida ita cikin ‘yan uwanta. Ita bazata iya karatu a ko’ina ba sai a Boston. Mummyn kuma tayi ta aikin lallashi amma Yesmin ba ta fasa komai cikin shagwabar ta. Wannan ba karamin kular da Mu’az yake ba, yayi mata tsawa kuma cibi ya zama kari daga Mummy.
Zaman Mummy da Yesmin a gidan, su ba zuwan bakunta ba kamar yadda suka saba, a’ah, wannan karon zama suke nufin yi na har illa masha Allahu. Ba abunda yake so a rayuwarsa irin (kadaici) yadda zai samu damar ayyukan sa na office a nutse da zurfafa bincike akan aikin nasa. Amma shikenan yanzu bashi da hutu da nutsuwa a gidansa?
Kullum cikin ciwon kai yake kwana, muddin yana cikin gidan. Ga shi Mummy ta ce Daddy ya sayar da gidansu ne. Wato babu ranar da zasu bar shi ya sarara. Shi ba abun ya ce su tafi ba, ina za su je? Su dafa wannan su dafa wancan, duk gidansa ya dume da kamshin abinci kamar wani restaurant abin da shi kuma ba ya so tunda ba iyali ya aje ba. Mummy enjoys cooking in her life. Dabara ta fado masa, ba don ya gaji da mahaifiyarsa da kanwarsa ba sai don ya samu nutsuwa yadda ya saba. Ya kira Daddy ya hau rokonsa don Allah ya zo ya tafi da Mummy, ya gaya masa zamansu ya takura masa, basa barinsa yayi bacci da aiki a nutse. They are giving him headache. Yesmin is very noisy. Kuma Mummy bata son laifinta. Daddy ya yi ta dariya har da kyakyatawa har ya godewa Allah, a karshe ya ce da Mu’azzam.
“Shin mutum ya taba gajiya da uwarsa da kanwar sa?�
Mu’azzam kamar zai yi kuka, ya ce, “Daddy ka fahimce ni, ni ba gajiya na yi da su ba, I love quietness, tunda suka zo na rasa samun sa, sannan suna mayar min da gida kamar gidan mata, alhalin ni ba aure ba. I want my house to be calm, cool, like before. Don Allah Daddy ka zo ka tafi da su�.
Damuwarsa ta bayyana karara cikin magiyarsa. Ga mamakinsa ko a jikin Daddyn sai cewa ya yi,
“Ku je ku yi ta cakudawa a haka, sonka ta ke, tunda har ta zabe ka a kaina. In ka ji ciwon kan ka sha paracetamol, in ka kasa zama da ita waye zai iya?
Gara ma ka sauya hali, ka fadada zuciyarka ka kaunaci kowa naka ka kuma koyi zama cikin mutanen da suka zame maka dole, don sauya maka akalar rayuwa zan yi bakidaya nan ba da jimawa ba, insha Allahu�.
******
Malam Raazee na cin tuwon dare Daddy Ishaq ya yi sallama, amsawa ya yi yana wanke hannunsa cikin bowl na silver. Daddy ya dauke kwanukan bayan ya gama wankewa ya yi gefe da su, ya zauna a muhallinsu.
Sake gaisawa suka yi irin gaisuwar su ta buzaye. Malam ya dube shi cike da kulawa yana tsane hannunsa da tawul. Ya ce,
“Ya ya Mu’azzam? Ya jikin nasa? Mun kwana biyu, ba mu yi waya ba�.
“Mu’azzam yana lafiya, ko dazu ya kira ni…�.
Nan ya ba shi labarin yadda suka yi dazu, suka yi ta dariya. Malam ya ce, “Ina ruwan Zulaiha, kaza uwar son ‘ya’ya, shi kuma dan gashi yana gudunta kamar kyanwa da bera�.
Daddy ya ce, “Abin da ta kasa ganewa kenan, shi Mu’azzam duk wata mu’amala in dai da shi za a yi ta, to a yi ta daga nesa-nesa, ko ya ya za ka zauna mai a gida, to fa zai ce ka takura masa. Zulaiha ta kasa ganewa, kodayake tausayinshi ta ke ji, shi kuma ba ya tausayin kanshi�.
Haka suka yi ta hirar Mu’azzam da Zulaiha suna cin dariya, Daddy Ishaq na fadin “Da kafarta za ka ganta ta dawo tunda masu gidan Boston suka bukaci abinsu, idan ita ba ta bar masa gidan ba na rantse shi zai bar mata�.
Aalimah ta yi sallama a dakin a hannunta karamar kwarya ce mai cike da nonon Rakumi mai dumi sabon tatsa, kai tsaye Malam ta nufa. Da murmushi a fuskarta ta russuna har kasa ta ce,
“Malam ga shi Inna Bintou ta ce a kawo�.
Hannu biyu ya sa ya karba ya ce, “Madalla da Bintou da jikanyar ta, an gaishe ku, madallah�.
Ta juya za ta fita, sai kuma ta dawo ta tsuguna.
“Malam Aunty Gumsu-Moiram ta yi min waya dazu tace in je in mata kwana biyu, na ce mata sai na tambaye ka tukunna�.
Ya ce, “Ba yanzu ba Moiram ta yi hakkuri, bana so ki je ko’ina sai kin warware dukkanki, har yanzu ban ganki kamar yadda nasan ki ba, a bai wa Gumsu hakkuri inji ni�.
Fuska a sake ta ce, “toh Malam�.
Ta juya ga Daddy ta gaishe shi cikin nutsuwa da sanyin muryarta.
Ya ce, “Anya Aalimah? Haka dan Adam zai rayu da damuwa bayan ba abin da za ta sa, ba abin da za ta hana? Dubi kasusuwan wuyanki, dubi idanunki yadda suka zuzzurma ciki. Don Allah don Annabi Aalimah ni Baban ABOULKHAIR ina mai cewa a karo na sau ba adadi, ki yi hakuri. Ki yi hakuri! Ki yi hakuri…�.
Ko kafin ya kai karshe ya fahimci hawaye sun gangaro daga idanunta. Muryarta ba ta fita sosai. A sanda take cewa.
“Na yi hakuri Daddy, na dade da yin hakuri. Zuciyata ce ta ki daukar reality, ce min ta ke ba shi ne ya mutu ba, zai dawo. Don Allah Daddy da gaske ne??�
Malam Raazee da Daddy Ishaq suka juyar da kai don share nasu hawayen.
Daddy ya ce, “Aalimah, wanda ya mutu ba ya dawowa. Ki yarda da ayar Ubangiji subhanahu wata’ala, kullu nafsin za’ikatul maut. Aboulkhair ba zai taba dawowa ba har abada. Ki bai wa rayuwarki da ke gaba kofa ko ya ya ne ta samu farin ciki kin ji Aalimah?�
Daga kai kawai ta yi, don ba ta da abin da za ta yi bayan daga kan, ko ta yarda ko ba ta yarda ba, ya ce,
“Tashi je ki cikin ‘yan uwanki, Allah ya yi miki albarka�.
Jiki babu lakka ta mike ta wuce cikin gida.
Bayan wucewarta da minti biyar daga Malam har dansa Ishaq babu wanda ya kara yin magana. Daga bisani Malam din yayi gyaran murya ya ce,
“Ni sai inyi ta wani tunani, a duk sanda Aalimah ta zo gabana�.
Daddy ya ce,
“Tunanin mene ne Malam?�
Malam ya girgiza kai, har da daga hannaye sama ya ce, “Uhum-um-umh-uhm, a bar kazar ‘yan boko cikin gashinta, yanzu in aka yi kokarin fige ta sai kun dawo da George Bush da Mungo Park gidan nan sabida kawo nassi na bijirewa da nuna kin amincewa�.
Murmushi Daddy ya yi, shi ma zuciyarsa ta yi nauyi. Babu mamaki idan ba irin tunaninsa Malam Raazee ke yi ba. Bai ja zancen da nisa ba ya yi wa Malam din sallama ya mike ya kwashi takalmansa ya fice don tafiya gidansa, wanda ba shi da nisa da gidan iyayensa trackable distance ne.
7/5/21, 8:20 AM - Buhainat: ADAMU DANKOLI
Mu’azzam ya mike daga kan abin sallarshi ya samu kujerar zaman mutum guda kusa da Kawun nasa wanda ke zaune cikin kujera ya zauna. Ya yi zurfi a tunanin da yake yi, har bai san sanda Mu’azzam ya zauna kusa da shi ba. Ajiyar zuciya ya saki lokacin da ya ji muryar nan ta Mu’azzam mai taushi da gardi a kunnuwan mai saurare na tambayarsa ko shi kadai ne?
Ya ce, “Eh, Harrison ya kawo ni�.
“Ina Daddy da Mummy da wannan matar Daddyn mai surutu?�
Daddy 1 yayi murmushi.
“Suna can gidanka, ga abinci ma na musamman mai surutun ta bani in kawo maka, amma su ma suna parking za su koma Boston, ashe ka damu da su ba ka nemansu?� Ya fada yana dan harararsa.
Murmushi ya yi, ya ce,
“Su ma ba sa nemana Oncle, especially Daddy�.
Da sauri ya katse shi, “Don sun san halinka ne, a zo dubaka ka ce an dame ka. Anya Mu’azzam ba za ka sauya hali ba? Ko kowa zai dame ka ai ban da iyaye! Zulaiha tausayi ta ke ba ni wallahi, ta damu da kai sosai, tana so ku dinga hira kuna tattauna al’amura amma ka ki ka ba ta dama, ina amfanin kadaici? Wane jin dadi ka ke samu a cikinsa?
Mai share musu wannan hawayen yau babu shi a doron kasa! Ina sake gaya maka Mu’azzam dole ka canza, ba aggressive tendency ba ko kai ka fi kowa zafin zuciya a duniya dole ka bude zuciyarka yanzu ka kaunaci mutanen dake zagaye da kai, ka rungume kannenka da iyayenka, ka ba su kulawa da farin cikin da mutum biyu za su ba su, in ba haka ba ka shirya gamonka da Allah ka ji na gaya maka.
In ma da lalura to da hali! Halin ka ne Mu’azzam rashin son mutane. Kai yanzu matsayin uba ka ke ga kannenka bakidaya, ba su Basma kadai ba har da su Aalimah. Don ba su da wanda ya fi ka.
Wanda ke sa su farin cikin yana mantar da su kai da wanzuwarka Allah ya yi ikonSa a kanshi, sabida kai din da baka son su kai yake so ka rayu tare dasu. Kuma dole mu karbi hukuncinsa da kyakkyawar zuciya. Ni na tafi, ka yi tunani a kan maganganu na da kyau. Allah ya kara maka lafiya�.
Ya mike ya fita, bayan ya sunkuya ya sumbaci Mu’azzam din a goshinsa. Bin bayansa ya yi da kallo yana dan dingisawa akan kafar robarsa kamar mai son tashi ya bishi, yana mai tauna kowacce kalma da ke fitowa daga bakinsa, yana mai yarda da ita cikin aminci da gaskatawa. He must be a changed man, amma ta yaya? Shi kansa bai sani ba.
Kawu Mansur na nufin ya dauki dukkan halayen Aboulkhair ya yafa yanzu, wanda ba abu ne mai sauki a gare shi ba. Aboulkhair is what he is kawai, charming, jovial, cheerful and passionate. Yana bukatar wanda zai taimaka masa hakan ta kasance da shi shima. Gashi kuma bazai iya rayuwa da kowa cikin gidan sa bayan Aboulkhair ba. Kenan wannan canjin da Kawu Mansur ke masa fata ba abu ne mai sauki a gare shi ba.
Shi kam abin tausayi ne, shi kadai aka yiwa mutuwa haqiqa. With Aboulkhair aside things are always easy for him. Ba tare da shi ba bai san yaya rayuwa zata koma masa ba. Yanzu in ya bar asibiti bai san ta yaya zai fuskanci sabuwar rayuwar ba. Rayuwar da babu Aboulkhair a cikin ta. Yana rokon Allah ya bashi juriya da karfin gwiwar karbar rayuwa a duk yadda ta zo masa.
******
Daddy Mansour ya koma Niamey ya tadda iyalinsa da sabuwar kafarsa ta roba cike da ikhlasi, kada ku so ku tona farin cikin da iyalin Raazee suka kasance a ciki. Kwana daya, biyu, uku ya huta ya ce zai koma Nigeria don komawa bakin aikinsa, kafar ta zauna masa sosai wadda ba za ka taba zaton ba ta gaske ba ce, ban da dan dingisawa da yake yi in yana tafiya.
Aboubacar da Basma tuni sun wuce. Malam Raazee da Inna Kasisi suka ce su yi ta tafiya tunda sun ga cewa zama a kasashen da ba su da kowa shi ya fi musu, amma su bar musu Aalimah.
Ita ma Aalimah ko da Mama ta tuntube ta da zancen ta fi son zaman Yamai din a kan komawa Nigerian. A cewarta za ta kasance cikin kadaici in ta koma wanda shi ne babban abin da ke jefa ta cikin kewa da tunanin mijinta Aboulkhairi.
Daddy 1, Mama Asi da ‘yammatansu uku; Sultana, Suhaima da Sabrina suka taho gida cike da alhinin halin da suka baro Aalimah a ciki.
Aalimah idan ta yi wanka da safe shi ke nan ko vaseline ba ya ganin fatar jikinta, balle kuma kwalli abin adon mata a idanunta. Hakika mutuwar Aboulkhair ta zo mata unexpectedly, a lokacin da ta ke at the zenith na jin dadin rayuwar auratayya. Ya lullube ta da dukkan so da kauna, ya maida ita sarauniya a cikin mata ‘yan uwanta. Don haka har zuwa yanzu da ake neman watanni shidda da rasuwarsa ta kasa karbar reality na rashin sa da sauki. Kullum mutuwarsa da kewarsa fresh suke dawo mata.
Har yanzu ji ta ke a jikinta kamar Aboulkhair ba mutuwa ya yi ba, ya je Boston ne bada jimawa ba zai dawo ya tadda ita, ya dauke ta su koma Las Vegas, su cigaba da rayuwar nan tasu mai ban sha’awa. Amma da ta ga watanni na shurawa da gasken-gaske babu ko waiwaye har an kwashi watanni kwarara guda tara, dole ta fara karbar reality na fara sabawa da rashin sa.
A kullum Inna Kasisi da Inna Bintou cikin tattashinta suke da nuna kulawa da kyautatawa. Abinci sai wanda ta zaba za’a dafa a gidan. ‘Yan uwanta kannenta su Balkissa dasu Rumana kullum kafafunsu na dakin Inna Bintou inda Aalimah ta ke, su kwaso labarai suyi ta bata na abubuwan da ke faruwa a gari, tamkar su goya ta don lallashi da son debe mata kewa. Dole ta fara sakin ranta, amma ba don ta yarda cewa za ta kara wata rayuwar farin ciki a gaba ba. Sai don ‘yan uwa, iyaye da kakanninta su yarda ba aikin banza suke yi ba, tana karbar rarrashinsu, kaunarsu da soyayyarsu.
******
A yadda Daddy ya so a karshen wannan watan za su yo hijira daga Boston din Massachusetts su koma kasarshi ta haihuwa Niger Republic shi da matanshi da sauran ‘ya’yan shi biyu, amma a yau komai ya canza, sakamakon Mummy Zulaiha data juyawa al’amarin baya. Mummy kuka ta ke yi tana karawa tun daren jiya kan cewa ba za ta iya barin kasar ta bar Mu’azzam shi kadai alhalin ta san ba shi da kowa a cikinta ba. Ta yarda Daddy da Gumsu su tafi, amma ita da Yesmin a barsu. Ya kada ya raya Mummy ta ce sai dai ya sake ta, wannan karon ta zabi Mu’azzam a kan aurenta.
Jikin Ishaq Raazee ya yi mugun sanyi, shi ma ya dade yana wannan tunanin, yadda za su tafi su bar Mu’azzam shi kadai babu kowa nasa. Ga lalura mai iya motsawa a kowanne lokaci. To abu ne in aka hada da iyayensa yanzu baya jin shakkar yin sa komai tsaurin sa don fatan gamawa da su lafiya.
Duk da ba gida daya suke zaune da shi ba, ba kuma gari daya ba, kowanne lokaci suke so suna zuwa ganinsa, uwarsa na kula da shi ta hanyar ziyartarsa akai-akai. A hakan da yake yana taka muhimmiyar rawa wajen gyara rayuwar mahaifiyarsa, yana da tabbacin shi ne ya canza ta ta koma mutuniyar kwarai. Yana amfanar da su da ‘yan uwansu na birni da na kauye, idan ya raba shi da aikinsa ya raba shi ne da madogarar rayuwarsa dungurungum. Balle aiki da ‘Chevron’, wanda sai mutum mai sa’a a cikin masu sa’a.
Ga shi ya riga ya gaya wa kowa zai dawo gida a wannan shekarar, har babban aiki ya samu a Yamai. Wanda ya tabbata zai rike shi shida iyalinsa a zamansa cikin kasarsa ta haihuwa har zuwa karshen rayuwarsa. Ta ya ya zai dawo ya ce da iyayensa wadanda burin su kenan ya dawo gida yace ya fasa saboda farin cikin matarsa?
Dan uwansa Mansour ya kira, don su yi shawara kan wannan al’amari.
To al’amari kowa ya san in dai akan Mu’azzam ne to fa Mansour Raazee baya wasa da shi, kuma bazai bi bayan kowa ba sai in da Mu’azzam zai amfana.
Budan bakinsa sai cewa yayi.
“Ai kowa ya san abinda ya faru, kuma kowa ya san Mu’azzam yana da lalurar da bai kamata a yi nisa da shi irin haka ba. Uwa wasa ce? Ko an san wahalar data ke sha akan dan ta da lafiyarsa? Ko kana tunanin hankalin ta zai taba kwanciya tana can yana nan? Wannan karon ina bayan Zulaihatu!�.
Wannan ita ce amsar kawu Mansour.
To shi an sa shi a kwana. Bayan wa zai bi? Mummy tana nan akan bakanta haka Malam da Inna Kasisi.
Da ya kira mahaifinsu cikin ladabi da tsanaki ya yi masa bayanin fasa dawowarsa yadda zai fahimceshi, da dalilin da ya janyo hakan. Da ikirarin Mummy Zulaiha na saidai ya sake ta. Shiru ya yi masa, shirun da ke nufin yana da ja a kan hukuncin da suka yanke shi da dan uwansa da mai dakinsa.
Malam Raazee ya yi gyaran murya ya ce, “A kan Mu’azzam ne ko?�
Ya ce, “Eh Malam�.
Malam ya ce, “A kan sa ne ka fasa dawowa cikin asalinka da tushenka?�
Daddy Ishaq ya yi shiru, Malam ya ce, “To ku ci gaba da shirinku na dawowa tunda dai ka samu aiki, wanda zai rike ka a nan din, duk wadda ta ce ba za ta dawo ba a cikinsu na yi maka umarni da ka sake ta din!
Mu’azzam yana hannun Allah! Shi din jarumi ne kuma sadauki a cikin mazaje. Na tabbatar maka cikin kowane hali zai iya kula da kansa. Ya riga ya tsaya da dugadugansa baya bukatar tallafin ku sai addu’arku. Rashin cikar lafiyar sa bai rage shi da komai a rayuwa ba. Cewa nake ko da ku ke kasa daya ba garinku daya ba? To ta ina ku ke sanin halin da yake ciki din?
Gashi ni kuma bani da buri a yanzu fiye da ya kasance duk sanda nake son ganin ka in budi ido in ganka a gefe na cikin ‘yan uwanka, ko in yi tattaki akan kafafuna zuwa gidanka. Shekara da shekaru kana yimin wannan alkawarin a-sha-ruwan-tsuntsayen. In kunyi hakuri kwana nawa ya rage min in baku fili kowa yayi rayuwar da ya zabawa kansa? Sai dai in dama can ba ku da niyyar dawowa�.
Jikin Daddy Ishaq har rawa yake. Ko’ina a jikinsa tsuma yake yana baiwa malam hakuri. Ya kira Mummy da karfin sauti ya ce,
“Zulaiha!�. Sai da gidan bakidaya ya amsa.
Ta ce, “Na’am!� Tana mai saukowa daga saman bene a nutse cikin takun gayuntan nan. Saida ya bari ta gama saukowa tsaf suna masu fuskantar juna, ya dube ta cikin tsakiyar idanun ta yace.
“Ki hada kayanki mu koma Niamey tare�.
Gyara zama Mummy ta yi cikin karamar kujerar falon, ko kadan muzuran da yake yi mata bai girgiza ta ba, ta ce,
“Na gaya maka ba sau daya ba ba sau biyu ba, ba zan koma in bar Da na ba�.
“To sai ki zabi daya, aurenki ko komawa Niamey�.
Kai tsaye (without a second thought) Mummy ta ce,
“Na zabi sakin, Allah ya sa shi ne mafi alkhairi a gare ni�.
Daddy ya rubuta saki daya cikin zafin rai ya ajiyewa Mummy akan cinyarta ya fice ya bar gidan.
Mummy ta tadda Gumsu a dakinta tana ta hada kaya. Ta ce,
“To Gumsun Babansu, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi, idan na taba bata miki a tsayin zaman mu ina mai rokon ki ki yafe mini. An ce zo mu zauna zo mu saba, hakika ni naji dadin zama da ke. Ni na karbi red card tunda na zabi zama kusa da Mu’azzam�.
Gumsu ta saki crystal din da ke hannunta zata saka shi cikin kwali, ji ka ke tush! Ya tarwatse a kasa. Salati ta shiga yi tana maimaita kalmar innalillahi… Mummy ba ta bi ta kanta ba ta juya ta fita daga dakin. Sai a lokacin hawaye suka zubo mata.
Karshen tashin hankali Gumsu-Moiram ta shige shi, ta yi kokarin rarrashin Daddy tana kuka kada a ce don ya aure ta ya rabu da uwar ‘ya’yansa, ya taimake ta kada duniya ta zage ta. Da wane ido zata sake kallon su Basma? Da kyar Daddy ya samu ya lallashe ta inda ya tabbatar mata rabuwarshi da Mummy Zulaiha ba ta da alaka da nata auren. Ya gaya mata zabin da Malam Raazee ya bayar ita kuma ta zabi sakin. Ko ita Gumsun ta zabi zaman Malam Raazee ya yi izinin a sake ta.
Jikin Gumsu ya yi mugun yin sanyi, ta rasa wanene mai gaskiya tsakanin Mummy da Daddy? Shi yana so ya yiwa mahaifinsa biyayya don ya gama da shi lafiya ita kuma Uwa ce mai jin qan abinda ta haifa mara cikakkar lafiya!
7/5/21, 8:20 AM - Buhainat: HABUBAKAR ADO
#######################################################
Cikin satin suka biyo jirgi da komai nasu suka baro kasar Amurka. Bari na din-din-din. Ishak Raazee na mai jin wata irin kewa wadda sabo ke haddasawa na mamayar zuciyarsa. Mummy na mai jin kamar ita daya ta rage a fadin duniya sabida kewar mijinta da ‘ya’yanta. Saidai ko kadan bata yi nadamar hukuncin da ta zartas ba. Yesmin na kuka kamar ranta zai fita a kan rabuwar iyayenta, suka taho shi da Moiram da diyarta Nurat, ya baro mata Yesmin ne don rage mata bacin rai.
Haka Mummy ta yi kokarin shanye damuwarta wannan karon ba tare da ta raba ta tare da Mu’azzam ba, ganin cewa bai jima da barin gadon asibiti ba. Kuma in ba za ta manta ba Aboulkhair ya hane ta dora wa Mu’azzam damuwa, ko dai ta shanye kayar ta ita kadai, ko ta raba ta tare da shi (Aboulkhair) din, amma sharing dinta da Mu’azzam babbar illa ce ga kyakkyawan treatment din da yake samu.
Ko da ta koma office a washegari da niyyar bada hakuri a maida ita bakin aikinta wani ta tarar a mazauninta (JP MORGAN CHASE) ba su daukar wasa da aiki, ko da kuwa da excuse. Balle ita nata babu excuse din ma. Rana daya aka nemeta a kasar aka rasa. Tsabar rudanin rayuwar data samu kanta ya mantar da ita cewa ita din ma’aikaciya ce, ma’aikaciyar ma ta babban bankin Amurka irin JP Morgan. Haka ta dawo kafafu a sage, ta soma neman wani aikin ta yanar gizo, amma har watanni uku suka shafe bata dace ba. Sakamakon matsin lambar da musulmin kasar ke fuskanta a lokacin daga sabuwar gwamnatin Amurka karkashin mulkin sabon shugaban kasa Donald Trump. Da yawa sai komawa suke kasashen su na asali. Ba don Yesmin da ke zuwa makaranta ba Las Vegas za ta tattara ta koma bakidaya, in Mu’azzam ba zai rike ta ba ita da autarta, ya san yadda zai yi da su. Shine kadai dolenta a yanzu.
******
FLASHBACK
An sallami Mu’azzam ranar wata lahadi, sati guda kacal ya kara a gida, sannan ya koma aikinsa. Ya hada wayoyinsa, ya kira duk wanda ya dace ya gaisar. Ciki har da Mummy, ta gaya masa tana Boston amma ba ta gaya masa cewa Daddy ya sake ta a kansa ba. Sosai ta koyi hadiye damuwa, in ta tuna da Aboulkhair.
Ta san da yana raye ransa zai yi matukar baci, za ta kiyaye abin da ba ya so a bayan ransa. Ta kasance mai bata masa rai da hakan a sanda yake raye. Zata kasance mai kiyayewa a sanda babu shi. Ta ce masa Daddy yana Niamey, kuma ta turo masa kudi cikin account dinsa kafin ya samu albashi ya soma shigo masa ta san zai bukace su sosai.
Sosai ya yi godiya, yana mai jinjina soyayyar uwa ga abin da ta haifa, ta Mummy is special. Ita dai ‘ya’yan ta kawai. Su samu jin dadi shine burin ta. Kada su nemi wani abu su rasa a rayuwar su. Bazata taba canzawa daga hakan ba.
Ya kira Daddy suka yi hira sosai, inda ya gaya masa ya koma Yamai, ya samu aiki a can da hukumar hulda da kasashen wajen su, yanzu kuma ya samu wani makeken fili kusa da gida ya saya ya fara gini. Gini yake so ya yi one in town wanda dukkansu zasu sake a cikin sa.
Ya cigaba da gaya masa amon muryarsa dauke da kauna irin ta uba ga dansa, irin tsarin duplex din da yake so a yi masa. Yace sai yafi gidansu na Boston kyau nesa ba kusa ba, zai masa part din sa guda wanda zasu ke sauka in sun zo shi da iyalinsa. Sosai ya baiwa Mu’azzam dariya. Ya canza position din rikon wayar daga dama zuwa hagu ya cigaba da sauraron almarar Daddy. Koko ya ce mafarkin Daddy. Ba tare da Daddyn ya kula da karbar da yake yiwa zancen nasa ba ya cigaba da labarta masa cewa har dakin yaran su za’ayi a cikin bangaren nasu, a zuba duk wani nau’I na kayan wasan yara. Mu’azzam tausayin mahaifin nasa yayi matukar kama shi, su iyaye wato har kullum fatan su nagari ne ga ‘ya’yan su ba ruwansu da reality din da rayuwar ‘ya’yan ke fuskanta.
Ji yayi idanunsa na son kawo ruwa, don haka ya matsu su yi sallama da Daddy. Ko kusa bai yi masa zancen mahaifiyarsa ba har suka yi sallama, hausawa suka ce wai ido da kunya. Ba zai iya kallon tsabar idanun sa ya gaya masa ya saki uwarsa ba sabida ta zabi zama a kusa da shi ta bashi kulawa. Sai Mu’azzam ya dauka za ta bi su ne daga baya in ta gama kintsawa, tunda ita ma’aikaciya ce. Bincike-bincike da zakule-zakulen halin da wani ke ciki da ma tun fil azal ba halinsa ba ne shi.
Cikin dan lokaci Daddy Ishaq ya gama ginin kyakkyawan duplex dinsa a nan unguwarsu plateaux suka koma shi da Gumsu. Wannan ya kawo tabbataccen kwanciyar hankali a zukatan iyaye da ‘yan uwansa. Ranar litinin ya soma shiga sabon ofishinsa a Ministère des affaires ètrangères na kasar Niger.
Duk da ko kusa ba za’a hada sauki da sukunin rayuwar yanzu da wadda ya yi a baya ba, yafi jin dadin rayuwar yanzu, akan ta baya. Cike yake da godiyar Allah da ikhlasi a zuciyarsa, da albarkar iyaye baibaye da shi. Kullum sallolin su biyar cikin jam’i suke yin su shi da ‘yan uwansa da mahaifin su a masallacin dake like da (main house) dinsu. Babu wanda ya san ya saki Mummy, sai Malam da Inna.
Mummy ta dukufa neman aiki a yanar gizo don saving dinta ya fara yin kasa sosai. Kason data ke karba duk wata na shares dinta duk a cikin su da lalurorin yau da kullum yake tafiya. Rayuwar mai tsada ce sosai. Ta dukufa neman aiki ba ji ba gani amma kamar wadda uwa ta cewa jeki kya gani ko aptitude babu wanda ya kira ta duk da experience dinta. Ita ke dauke da nauyin karatun Yesmin, cinsu da shansu da maintenance din gidan, ga wanda ta ke turawa Mu’azzam duk da ba shi ya tambaya ba kuma ya hana ta amma ta ki ji, kullum gani take kamar albashinsa baya isar sa sabida tsadar magungunansa da rayuwar da yake yi mai tsada. Tana cikin wannan halin aka zo aka ce ta tashi daga cikin gidan masu shi za su shiga, aka nuna mata shaidar mallakar takardu da komai.
Ba da saninta ba Daddy ya dade da sayar da gidan ya karbe kudinsa ya tafi da su kasar haihuwarsa don ya gina gida acan, da kuma niyyar sa ta fara kasuwanci da su irin wanda ya taso ya ga Malam da manyan yayyunsa na yi, wato na shigo da kayan abinci daga kasar Faransa zuwa jihohin kasar Niger.
Bala’i goma da ashirin ga Mummy, Ishaq ya shammace ta, bata taba tsammanin zai sayar da gidan nan ba, daga karshe kan ba yadda zata yi ta tattara ta taho Las Vegas ita da Yesmin gidan Mu’azzam.
Mu’azzam sai dawowa office yayi ya gansu da iyayen kayansu tirim! Sun gyare dakin da Mummy ke sauka in tazo sun baje suna barcin gajiya. Ya tura Harrison yayo musu takeaway din abinci. Kwanansu uku kacal hayaniyar Yesmin ta fara hana Mu’azzam sakat, duk da kokarinsa na bin shawarar kawunsa Mansour na ya bude zuciyar sa ya kaunaci ‘yan uwansa, ya ba su kauna da kulawar da Aboulkhair ke ba su, yayi acting na mutum biyu a gare su, ya ga cewa abun kamar da wuya ba zai iya ba! Ya yi duk iya kokarin sa amma ya kasa. Mummy ta riga ta gama shagwaba Yesmin ta yadda bai isa ya tsawata mata ba yanzu zai ga bacin ran Mummy, kullum Yesmin sanyata take a gaba tana kuka wiwi kamar ‘yar goye kan wai su koma Boston bazata iya barin makarantun ta na can ba ko a maida ita cikin ‘yan uwanta. Ita bazata iya karatu a ko’ina ba sai a Boston. Mummyn kuma tayi ta aikin lallashi amma Yesmin ba ta fasa komai cikin shagwabar ta. Wannan ba karamin kular da Mu’az yake ba, yayi mata tsawa kuma cibi ya zama kari daga Mummy.
Zaman Mummy da Yesmin a gidan, su ba zuwan bakunta ba kamar yadda suka saba, a’ah, wannan karon zama suke nufin yi na har illa masha Allahu. Ba abunda yake so a rayuwarsa irin (kadaici) yadda zai samu damar ayyukan sa na office a nutse da zurfafa bincike akan aikin nasa. Amma shikenan yanzu bashi da hutu da nutsuwa a gidansa?
Kullum cikin ciwon kai yake kwana, muddin yana cikin gidan. Ga shi Mummy ta ce Daddy ya sayar da gidansu ne. Wato babu ranar da zasu bar shi ya sarara. Shi ba abun ya ce su tafi ba, ina za su je? Su dafa wannan su dafa wancan, duk gidansa ya dume da kamshin abinci kamar wani restaurant abin da shi kuma ba ya so tunda ba iyali ya aje ba. Mummy enjoys cooking in her life. Dabara ta fado masa, ba don ya gaji da mahaifiyarsa da kanwarsa ba sai don ya samu nutsuwa yadda ya saba. Ya kira Daddy ya hau rokonsa don Allah ya zo ya tafi da Mummy, ya gaya masa zamansu ya takura masa, basa barinsa yayi bacci da aiki a nutse. They are giving him headache. Yesmin is very noisy. Kuma Mummy bata son laifinta. Daddy ya yi ta dariya har da kyakyatawa har ya godewa Allah, a karshe ya ce da Mu’azzam.
“Shin mutum ya taba gajiya da uwarsa da kanwar sa?�
Mu’azzam kamar zai yi kuka, ya ce, “Daddy ka fahimce ni, ni ba gajiya na yi da su ba, I love quietness, tunda suka zo na rasa samun sa, sannan suna mayar min da gida kamar gidan mata, alhalin ni ba aure ba. I want my house to be calm, cool, like before. Don Allah Daddy ka zo ka tafi da su�.
Damuwarsa ta bayyana karara cikin magiyarsa. Ga mamakinsa ko a jikin Daddyn sai cewa ya yi,
“Ku je ku yi ta cakudawa a haka, sonka ta ke, tunda har ta zabe ka a kaina. In ka ji ciwon kan ka sha paracetamol, in ka kasa zama da ita waye zai iya?
Gara ma ka sauya hali, ka fadada zuciyarka ka kaunaci kowa naka ka kuma koyi zama cikin mutanen da suka zame maka dole, don sauya maka akalar rayuwa zan yi bakidaya nan ba da jimawa ba, insha Allahu�.
******
Malam Raazee na cin tuwon dare Daddy Ishaq ya yi sallama, amsawa ya yi yana wanke hannunsa cikin bowl na silver. Daddy ya dauke kwanukan bayan ya gama wankewa ya yi gefe da su, ya zauna a muhallinsu.
Sake gaisawa suka yi irin gaisuwar su ta buzaye. Malam ya dube shi cike da kulawa yana tsane hannunsa da tawul. Ya ce,
“Ya ya Mu’azzam? Ya jikin nasa? Mun kwana biyu, ba mu yi waya ba�.
“Mu’azzam yana lafiya, ko dazu ya kira ni…�.
Nan ya ba shi labarin yadda suka yi dazu, suka yi ta dariya. Malam ya ce, “Ina ruwan Zulaiha, kaza uwar son ‘ya’ya, shi kuma dan gashi yana gudunta kamar kyanwa da bera�.
Daddy ya ce, “Abin da ta kasa ganewa kenan, shi Mu’azzam duk wata mu’amala in dai da shi za a yi ta, to a yi ta daga nesa-nesa, ko ya ya za ka zauna mai a gida, to fa zai ce ka takura masa. Zulaiha ta kasa ganewa, kodayake tausayinshi ta ke ji, shi kuma ba ya tausayin kanshi�.
Haka suka yi ta hirar Mu’azzam da Zulaiha suna cin dariya, Daddy Ishaq na fadin “Da kafarta za ka ganta ta dawo tunda masu gidan Boston suka bukaci abinsu, idan ita ba ta bar masa gidan ba na rantse shi zai bar mata�.
Aalimah ta yi sallama a dakin a hannunta karamar kwarya ce mai cike da nonon Rakumi mai dumi sabon tatsa, kai tsaye Malam ta nufa. Da murmushi a fuskarta ta russuna har kasa ta ce,
“Malam ga shi Inna Bintou ta ce a kawo�.
Hannu biyu ya sa ya karba ya ce, “Madalla da Bintou da jikanyar ta, an gaishe ku, madallah�.
Ta juya za ta fita, sai kuma ta dawo ta tsuguna.
“Malam Aunty Gumsu-Moiram ta yi min waya dazu tace in je in mata kwana biyu, na ce mata sai na tambaye ka tukunna�.
Ya ce, “Ba yanzu ba Moiram ta yi hakkuri, bana so ki je ko’ina sai kin warware dukkanki, har yanzu ban ganki kamar yadda nasan ki ba, a bai wa Gumsu hakkuri inji ni�.
Fuska a sake ta ce, “toh Malam�.
Ta juya ga Daddy ta gaishe shi cikin nutsuwa da sanyin muryarta.
Ya ce, “Anya Aalimah? Haka dan Adam zai rayu da damuwa bayan ba abin da za ta sa, ba abin da za ta hana? Dubi kasusuwan wuyanki, dubi idanunki yadda suka zuzzurma ciki. Don Allah don Annabi Aalimah ni Baban ABOULKHAIR ina mai cewa a karo na sau ba adadi, ki yi hakuri. Ki yi hakuri! Ki yi hakuri…�.
Ko kafin ya kai karshe ya fahimci hawaye sun gangaro daga idanunta. Muryarta ba ta fita sosai. A sanda take cewa.
“Na yi hakuri Daddy, na dade da yin hakuri. Zuciyata ce ta ki daukar reality, ce min ta ke ba shi ne ya mutu ba, zai dawo. Don Allah Daddy da gaske ne??�
Malam Raazee da Daddy Ishaq suka juyar da kai don share nasu hawayen.
Daddy ya ce, “Aalimah, wanda ya mutu ba ya dawowa. Ki yarda da ayar Ubangiji subhanahu wata’ala, kullu nafsin za’ikatul maut. Aboulkhair ba zai taba dawowa ba har abada. Ki bai wa rayuwarki da ke gaba kofa ko ya ya ne ta samu farin ciki kin ji Aalimah?�
Daga kai kawai ta yi, don ba ta da abin da za ta yi bayan daga kan, ko ta yarda ko ba ta yarda ba, ya ce,
“Tashi je ki cikin ‘yan uwanki, Allah ya yi miki albarka�.
Jiki babu lakka ta mike ta wuce cikin gida.
Bayan wucewarta da minti biyar daga Malam har dansa Ishaq babu wanda ya kara yin magana. Daga bisani Malam din yayi gyaran murya ya ce,
“Ni sai inyi ta wani tunani, a duk sanda Aalimah ta zo gabana�.
Daddy ya ce,
“Tunanin mene ne Malam?�
Malam ya girgiza kai, har da daga hannaye sama ya ce, “Uhum-um-umh-uhm, a bar kazar ‘yan boko cikin gashinta, yanzu in aka yi kokarin fige ta sai kun dawo da George Bush da Mungo Park gidan nan sabida kawo nassi na bijirewa da nuna kin amincewa�.
Murmushi Daddy ya yi, shi ma zuciyarsa ta yi nauyi. Babu mamaki idan ba irin tunaninsa Malam Raazee ke yi ba. Bai ja zancen da nisa ba ya yi wa Malam din sallama ya mike ya kwashi takalmansa ya fice don tafiya gidansa, wanda ba shi da nisa da gidan iyayensa trackable distance ne.
7/5/21, 11:40 AM - Buhainat: HAULATU66
Aalimah ta yi sallama a shigifar kakansu. Daga shi sai Daddy 2 ta tarar a dakin, babu kowa. Ta samu gefen Malam ta zauna. Malam ya dube ta cikin kulawa, ya ce,
“Uwata me ya faru ne?�
Ta saci kallon Daddy 2 wanda kallon fuskarsa kawai ta yi ta ji ya ba ta tausayi, da alama cikin damuwa mai tsanani yake. Ta ce, “Malam wai Daddy ne ya ce zai min aure�.
Yayi murmushi.
“Ke kuma ba kya so ko?�
Ta ce, “Malam ba zan iya mantawa da Aboulkhair ba, balle in hada rayuwa da wani a bayansa, kullum ji nake a jikina zai dawo. Idan ya dawo ya same ni da aure, na ci amanarsa�.
Murmushi Malam ya yi kafin ya ce, “Ko da a ce MU’AZZAM ki ka aura ba za ki manta da shi ba?�
Idanunta suka kara girma, at the same time suka kankance suka firfito waje, cikin sanyin murya tace.
“Malam, wanne Mu’azzam din?�
“Mu’azzam Raazee Yayan Aboulkhair�.
Wannan karon Daddynta ne ya ba ta amsa, with every affirmation a cikin muryarsa.
Sai Aalimah ta gurfana a gaban mahaifinta a kan gwiwoyinta. Rokonsa ta ke idan wasa yake yi tana mai rokonsa da girman Allah da darajar zatinsa da ya bari, Mu’azzam tamkar uba yake a gare su daga ita har Aboulkhair. Gara ya aura mata mazan duniya bakidaya ta amince, a kan ya aikata wannan babban zunubin a gare ta.
Kamata ya yi ya tasar da ita daga durkuson da ta yi a gabansa kamar mai neman gafara. Idanunsa sun kada sun yi jajir da tausayin ta. Sai dai ko sama da kasa za ta hade ba ya jin akwai abin da zai sa shi fasa hada wannan aure, muddin yana raye ita ma Aalimah tana numfashi.
Ya ce, “Ki nutsu Aalimah ki fuskance ni, Mu’azzam shi na so tun farko ki aura Allah bai cika min wannan burin ba. Idan har da gaske kina kaunar Aboulkhair ba abin da za ki yi ki nuna masa wannan kaunar a lokacin da kasa ta rufe masa ido, banda tallafar rayuwar Mu’azzam. Kin sani Aboulkhair ba shi da wani buri da ya wuce Mu’azzam da lafiyarsa. Aalimah ba kya tausayin Yaya Ishaq? Mutumin da ya dauke ki babu bambanci da ‘ya’yan cikinsa ya karrama rayuwarki? Kina sane da cewa ba shi da buri a yanzu da ya wuce lafiyar Mu’azzam da cikar rayuwarsa. Ba za ki kasance mai rama alheri da sadaukarwa ba?�
Aalimah cikin gunjin kuka ta ce, “Daddy, bana gudun Mu’azzam don rashin lafiyarsa. Ko kadan. Ina gudun aurensa ne kasancewar sa wanda ya fi kowa kusanci da Aboulkhair, ina matukar ganin girmansa, aurensa shi ne babban cin amanar da zan yi wa Aboulkhair a lokacin da babu shi…�.
Wannan karon malam ne ya tare ta, “Uwata, shi ne babban farin cikin da za ki sanya shi. Shi ne babban gatan da za ki yi masa. Shi ne kauna ta hakika da za ki nuna masa. Hakkin ki ne mu ba ki dama wannan karon ki zabi mijin aure, shi ya sa har muka zaunar da ke a nan muna neman yardar ki da amincewar ki, ba don haka ba da ba za ma ki san an yi ba sai bayan an yi.
Ni na san uwata mai biyayya ce ga umarnin mu, mai farin ciki da farin cikin iyayenta. Kin zauna da Mu’azzam ko da ba gida daya ba a kalla za ki iya bada shaida a kan WANE NE SHI? Kuma kin ga yadda dan uwansa ke kula da shi, akalla muna da kyakkyawan zaton za ki iya taimakawa rayuwarsa a matsayinku na shakikan juna, ku taru ku rufa wa juna asiri�.
Aalimah ta rasa abin cewa, ta rasa hujjar kare kanta wajen Daddy da Malam, ban da ta zuba musu ido, sun riga sunyi nisa akan kudirinsu, kome zata ce bazasu gane ba, bazasu saurareta ba, tana mai jin abin da suke fadi kamar almara a cikin kanta. Tana mai kallon fuskokinsu na wulgawa kamar a majigi, tana ganin wasu abubuwa masu kama da taurari cikin idanunta suna ratsa fuskokinsu cikin idonta. Daga haka ba ta kara gane me suke cewa ba, kuma ba ta kara samun kalmar furta musu ba.
******
Ta farfado ne daga shidewarta ta ganta a cinyar Gumsu- Moiram, tana mata firfita da maficin kaba, Gumsu ta sa hannu ta debi ruwa tana shafa mata a kan farar fuskarta wadda ta cure ta yi jajir. Mikewa ta yi daga kwanciyar ta tashi zaune. Idanunta ta ke rarrabawa a dakin kafin ta fahimci a dakin Inna Kasisi suke. Ga Innar a gefe ta hada tagumi, bayan su babu kowa a dakin sai ita cikon ta uku.
Inna ta ce, “Gumsu, ki tafi da ita gabanki ta kwana biyu in ji Malam. Ki ci gaba da nuna mata gaskiya na tabbata za ta fahimci iyayenta, kuma za ta fahimci abin da suke so ta fahimta�.
Zumbur Aalimah ta mike zaune, “Ba abin da zan fahimta in dai aure da Mu’azzam ne Inna, ba zai taba bani irin rayuwar da dan Uwansa ya ba ni ba, bayan ciwo da ke aiki a jikinsa har da hali. Halinsa ba irin na mutane ba ne. Na ce na yarda a aura min mazan duniya dukkansu, amma ban da Mu’azzam Inna…�.
“Me ya sa ba ki gaya wa ubanki ba? Ni me ye nawa ne a ciki?�
Inna kasisi ta katse ta cikin gatsali, kasan ranta cike da jin zafin kalaman Aalimah, duk wanda zai aibata Mu’azzam ko ba ta gaya masa ba, za ta ji zafinsa a kasan zuciyarta. Shi ne ya dauke su mutane masu daraja a lokacin da Zulaiha da Ishaq suka watsar da su. Shi ne ya fara kai ta dakin Allah kafin kowa ya kai ta. Shi ne ya dauki danginta da muhimmanci yake agaza musu fiye da kowa cikin ‘ya’ya da jikokinta. Shi ne ya dauke su mutane fiye da ubansa! Kaunar da ta ke masa ba ‘yar kadan ba ce, ba za ta juri ana aibata shi a kan idanunta ba.
“Gumsu na ba ki minti uku ki tattara Aalimah da kayanta ku tafi gidan ki. Zan iya hambare ta idan ta kai ni bango�.
Gumsu ta kama hannun Aalimah suka mike, da ma tuni ta dibar mata kaya kala biyu ta zuba a babbar leda. Za su iya tafiya a kasa daga nan babban gida zuwa gidanta, amma a motar Daddy Gumsu ta jefa ledar kayan Aalimah, ta bude mata kofa ta shiga ta rufe, sannan ta zagaya mazaunin direba ita ma ta shiga ta ja su zuwa gidan, ga tsohon ciki a jikinta kusan watanni bakwai.
A gidan ma aiki daya Gumsu ta ke ta yi, wato lallashi, ban baki da jan hankali. Tana nuna mata illar ja da iyaye da yin fito na fito ga umarninsu. Ta ce,
“Aalimah, idan na fahimce ki Mu’azzam ne ba kya so, ba auren ne ba kya so ba?�
Da sauri ta daga mata kai.
Gumsu ta yi murmushi, ta ce,
“In aka janye maganar Mu’azzam aka kawo wani za ki yarda ki yi aure ke nan?�
Da sauri Aalimah ta gyada kai, ta kara da cewa, “Ko waye Aunty Moiram ku kawo, ban da Mu’azzam�.
Gumsu ta kama baki, ta ce, “Ko kunyar idona ba kya ji Aalimah? To kuwa sai dai bakin ciki ya kashe ki mu ci gumba! Mu kuma ba damuwa muka yi ki yi aure ba, ki auri Mu’azzam ki zauna da shi cikin rufa wa juna asiri shi ne abin da ya dame mu�.
Kwana biyu kullum suna tirzawa, duk ta inda Gumsu ta billo sai Aalimah ta goce. Rashin kunya sosai take zubawa Gumsu son ranta. Gumsu bata taba sanin Aalimah nada baki ba sai a wannan lokacin. Itama bata raga mata, haushi take cusa mata ko ta ina, mai nuna soyayyar ta ga wannan hadin auren data fahimci lallashin bata lokacin ta take yi. Aalimah ta shirya ja da kowa don kubutar da kanta daga auren Mu’azzam. Daga baya ta je ta samu Inna Kasisi tace zata dawo da Aalimah gida, zuciyarta ta kasa jurewa, don kwarai Gumsu ke son Mu’azzam itama duk da ba wani sabo ne mai yawa a tsakanin su ba. Zuciyarta na matukar sonsa.
Ta kasa jure kiyayyar da Aalimah ke nunawa auren sa kiri-kiri bata shakkar kowa. Gata a cikin gidan ubansa. Amma duk abinda yazo bakinta shi take fada. Abubuwa da yawa akan kunnen Daddy take yin su. Ita kuma Inna Kasisi ta kwashe komai ta gayawa Dr. Mansour. Sai ya ga bari kawai ya kawo karshen komai, kowa ya huta, dama sun bata lokaci ne ko zata lallasu ta karbi auren da dadin rai. Amma tunda abin nata ba mai karewa bane bari ya karar da shi.
Ranar ta kama juma’a, bayan saukowa daga masallaci suka ga Daddy ya fito cikin shirin babbar shiga ta shadda Wagambari, babbar riga da hula sai kamshi yake yi.
Ya ce, “Gumsu, kira min Aalimah�.
A ladabce ta zo ta tsugunna a gabansa, ya kalleta cike da tausayin yadda ta rame ta fita hayyacin ta cikin sati guda kacal da yin maganar auren ta da Mu’azzam. Ya sassauta murya yace.
“Malam ne ya ce in tambaye ki, kin amince ki auri dan uwanki Mu’azzam?�
Aalimah ta samu kanta cikin rudu. A rasa wanda za a turo ya tambaye ta sai UBAN MU’AZZAM? Wannan ma ai wayo ne da son cutar da mutum, tunda ko giya ta ke sha ba za ta iya duban tsabar idon Daddy Ishaq ta ce ba ta son Mu’azzam ba.
Ta shiga tunano tarin alhairorin Daddy Ishaq gareta a Boston…. Da lokacin da take auren dan sa Aboulkhair….hawaye suka wanke mata fuska.
Ya ce, “Ke nake sauraro Aalimah, mutane suna jira na�.
Ta samu kanta da cewa, “Na amince’’ (without a second thought). Tare da zubowar tawagar hawaye a kan kundukukinta.
Albarka Daddy ya shiga sanya mata, sannan ya kama hannayenta ya mikar da ita daga tsugunnon da ta yi, ya ce,
“Insha Allahu ba za ki yi nadamar auren dan uwanki ba, kuma rashin lafiyarsa ba zai zamo kalubale ga rayuwar aurenku ba�.
Ya hada hannayenta da na Gumsu wuri guda, sannan ya fice.
Kuka Aalimah ta fashe da shi, ta zare hannunta daga na Gumsu ta shige bedroom din ta, tana mai tambayar kanta,
“wanne irin hukunci kunya tasa ta yanke wa rayuwar ta haka?�
Ba jimawa aka soma shigo musu da huhun goro da alewa, Balkissa ta shigo tana guda, kamar wata marokiya, tana gaya musu an daura auren Yaya Mu’azzam da Aalimah.
******
“Kana ina Mu’azzam?�
“Daddy I’m at San Francisco, na zo Seminar ta kwanaki uku da Valero Corporation sai jibi zan koma Vegas�.
“O.K, in ka koma masaukinka, ka samu nutsuwa, ka kira ni don Allah�.
Da haka suka yi sallama.
Mu’azzam na komawa hotel din da ya yi masauki wanka kawai ya yi da sallahr isha, sannan ya kira mahaifinsa.
“Wato kana ji ko Mu’azzam? Gyara nake so ka yi wa gidanka, gyara na sosai, in nace sosai ina nufin sosai, ya koma sabo kal!�
Murmushi Mu’azzam ya yi, a very gentle smile irin nasa. Wanda ba kasafai yake yin sa ba sai abu ya bashi dariya sosai. Banda abun Daddy shi kullum gidansa kamar sabo yake, ko’ina kal-kal yake yana sheki da daukar ido sabida kwarewar Jacob a gyaran gida, tare da fesar da kamshi mai sanyi, wanda ke fitowa daga furannin gidan da room fresheners masu kyau da Harrison ke fesawa akai-akai, ko su Mummy da ke wuni dafe-dafen da ba ya so ba su da bata wuri, suna tsaftace inda suka bata sosai. Ya ce,
“Daddy ai kullum gidan cikin gyara yake�.
Daddy ya ce, “Duk da haka, a fidda dakin nan dake rufe na kusa da naka, a yi masa gyara na musamman. A yi furnishing dinsa da furnitures masu kyau. Wannan dakin dake rufe na kusa da bedroom dinka�.
Cikin shanye mamaki Mu’azzam yace.
“Ok Daddy, za’ayi yadda kake so, yanzu dai bana gari amma ba abin da zai gagara insha Allah. Amma Daddy tukunna me za’a yi da dakin?�
Maimakon ya amsa masa tambayar da yayi masa sai cewa yayi.
“Zan turo maka kudin da suka saura min ka kara, kai dai ka yi yadda na ce, in an gama ka sanar da ni. Allah ya yi muku albarka�.
Bai bashi damar cewa komai ba ya kashe wayarsa. Daddy kullum mantawa yake da cewa shi din ma’aikacin Chevron ne. Chevron din da itace lamba daya kan petroleum a Amurka.
Mu’azzam ya jima rike da wayar sa, yana tambayar kansa ko sai yaushe su Daddy zasu daina wahalar bashi kudi daga shi har Mummy, su yarda shi din yanzu Engnr. Ne na man petir wanda ya tsaya da dugadugansa baya bukatar tallafin su a komai? Tsakanin Daddy da Mummy bai san wa ya fi son sa da tausayin sa ba.
Ajiyar zuciya yayi. Ya rasa wanda yafi wani tausayinsa da son samar da kykkyawar rayuwa a gare shi tsakaninsu. Domin daga baya Daddy ya gaya masa komai da ya faru tsakaninsa da Mummy da har ya kai ga saki, lokacin da ya fahimci su Mummy basu da niyyar barin gidansa. Wannan sacrifice da mahaifiyarsa tayi a kansa yasa shima ya cizge duk wata damuwa da zamansu ke jaza masa, yayi dammarar cigaba da zama tare da mahaifiyarsa cikin so da kauna tare da bata dukkan kulawa har karshen rayuwarsa.
Ta wani fannin tausayin mahaifinsa ya kamashi, tunda ya haife shi yake wahala da shi har gobe bai huta ba! A yanzun kuma da ya kamata ya hutan, ya ki yarda ya huta. Kullum kallon karamin yaro mai bukatar kulawar iyaye yake masa. A wani bangaren, ya fada tunanin abin da Daddy zai yi da daki a gidansa. Kuma ma kusa da dakinsa, saidai ko kusa tunaninsa bai kawo masa aure ba, don shine abu na karshe da ba zai zo cikin tunanin sa ba, daga karshe ya soma kiraye-kirayen waya yana bada order kan cika umarnin Daddy.
Kafin ya dawo an gama komai. Gidansa ya zama sabo kal daga sama har kasa. An zuba wasu gogaggun furnitures farare sol ‘yan kasar Italy an lullube shi da curtains ruwan madara. Dakin sai wani kamshin sabunta yake yi mai dadi. Haka gidan bakidaya an pente shi da wani irin fenti fari kal mai santsi da sheki. Alamu ne na cewa (white) is the favourite colour na mamallakin gidan. Har kitchen ba’a bari ba shima ya sha gyara ta ko’ina da sababbin kitchen cabinets sai daukar ido yake.
Yana shigowa gida daga tafiyar da yayi Mummy da jin motsinsa da sallamar sa ta fito daga daki da sauri har tana tuntube, zaninta na kuncewa. A dugunzume ta tare shi da tambaya ko bari ya huta bata yi ba daga gajiyar zaman jirgin kasan da ya kwaso tun daga SanFrancisco har Las Vegas.
“Mu’az, aure ka yi ne babu labari?�
Ya lalubi kujera guda cikin tausasan leathers din da ke falon, ya zauna cikin nutsuwa, a lokaci guda yana mai loosing neck tie din wuyanshi shi yadda zai ji dadin zaman. A gajiye yake matuka.
Dariya Mummy ta bashi sosai, ya yi murmushi, ya ce.
“Sai dai in ke ki ka sake yi min babu labari�.
Ta daure fuska ta ce, “Ka bar zancen wasa, tsakani da Allah aure za ka yi?�
Sai a lokacin ya ji gabansa ya fadi dammm! A wancan lokacin Mummy ce ta yi masa; ba ya fatan a wannan karon ya kasance Daddy ne ya yi masa ba da saninsa ba. A dinga janyo wa rayuwarsa bankada da terere yana zamansa lafiya cikin kwanciyar hankali babu gaira babu dalili.
Amma sai ya samu kansa da kasa kiran Daddy ya nemi ba’asi, sabida tsoron abin da kunnuwansa za su jiye masa.
7/5/21, 10:03 PM - Buhainat: KAUSAR LANTO
Da ya koma daki sai ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ya shiga safah da marwa. Addu’a yake cikin ransa Allah yasa kada zargin Mummy ya zam tabbatacce. Bashi da sauran buri wanda ya danganci aure a halin yanzu. Ya riga ya mika wuya ga kaddarar data same shi. Baya mafarkin wata rayuwar daban bayan wannan wadda yake ciki. A yadda ya ji muryar Daddy sanda suke waya ya fahimci yana cikin madaukakin farin ciki. Ya san in suna da wani buri a yanzu to bai wuce auren nasa ba, wani abu da shi kuma ya riga ya cire daga dictionary din rayuwarsa. Idan zargin Mummy ya tabbata haqiqa Daddy ya shiga rayuwarsa ta inda bai taba tsammani ba.
Mummy na zaune a falon Mu’azzam, Yesmin na yi mata matsar kafa, komi na duniya yayi mata zafi. Ta shiga tambayar kanta har tsawon yaushe za ta yi ta zama gidan Mu’azzam? Ga shi ba ya bukatar taimakonta a kan komai. Ya samu lafiya sosai. Komai shi yake yi wa kansa, lafiyarsa kuwa Dr. Nebrass ke kula da ita. Hana rantsuwa za ta ce yana amfanuwa da girkinta.
A wannan dan tsukin kewar mijinta na yawan damunta. Ga Yesmin na zaune babu karatu, ta ki yarda tayi karatu a Las Vegas. Ba karamin sabo tayi da Boston ba tun haihuwarta har girmanta. Ga Gumsu can ta samu miji a bagas ita kadai sunata barzar soyayya sai zubo masa ‘ya’ya take, mijin da tafi kowa cin wahalarsa tun bai mallaki komai ba, suna can rayuwa tayi musu daidai sun manta da ita. Ita tana nan tana gadin Dan ta wanda baya bukatar komai daga gareta. Gabadaya ta sauya, hatta Mu’azzam da bai faya shiga shirgin kowa ba ya lura Mummy ba ta cikin walwala a ‘yan kwanakinnan. Ba halinsa ba ne tambaye-tambaye ba, don haka bai tambaye ta ba. Ya san in wanda ya shafeshi ne da kanta zata zaunar da shi ta gaya masa.
A daren ranar suna gama cin abincin dare ya yi musu sallama ya haye sama inda bedroom dinsa yake, ya sha magani ya yi sallolin nafila raka’a hudu da yake yi duk dare kafin ya kwanta. Sannan ya yi light off ya kwanta. Amma tunanin me Daddy ke nufi da shi ya hana shi barci. A hakan da yake a kwance ya lalubo waya ya kira Daddy don ya san su a can yammaci ne, zai same shi a lokacin da ya dace.
Daddy na dagawa ya ce,
“Ya ya aka yi Mu’azzam? Ba ka yi barci ba?�
Ajiyar zuciya ya yi, cikin damuwa ya ce, “Na kasa barcin Daddy, tunani iri-iri nake yi kan dalilin da ya sa ka sa ni furnishing din gida�.
Ya ce, “Mu’azzam!�.
Ya ce, “Na’am Daddy�.
“Ka san dai ba zan yi abin da zai cutar da kai ba, sai wanda zai amfane ka da mu bakidaya ko?�
Ya ce, “Kwarai da gaske Daddy�.
Kai tsaye ya ce, “To aure na karba maka. Ka yi hakuri da ban yi shawara da kai ba. Nima abin ya zo mini unexpected ne, duk da na dade da wannan niyyar cikin zuciyata tun bayan rasuwar Aboulkhair�.
Wuta ta dauke wa Mu’azzam na lokaci mai tsawo. Numfashinsa ya nemi daukewa. Ya rasa a duniyar da yake. Shidewar wucin-gadi ce ta same shi a lokaci guda.
“Daddy, ka san abin da ka ke cewa kuwa?�
Ya tambayi mahaifin nasa in subdued (cikin karayar murya). Bayan ya tabbatar cikin zahiri ne abinda yake ji din daga bakin mahaifinsa ba mafarkin ido biyu ba. Kuma ta bakin sa yake son ya ji.
“Ni kuwa na san abin da nake cewa�.
Ya bashi amsa.
“Daddy, likitoci sun ce maka na samu waraka ne?�
Girgiza kai yayi kamar Mu’azzam din yana ganinsa. “Ko kadan Mu’azzam, kawai na mika komai hannun Ubangiji ne�.
Mu’azzam ya yi shiru cikin harhada kalmomin da zai jefa wa mahaifinsa, amma kunyar abin da zai ce din ta hana shi magana. So yake ya ce da shi cikin biyun wanne ya zaba masa? Za su zauna da matar ne ya zuba mata ido har abada a matsayin ta na matar auren sa, yana ci gaba da taking kwayoyin anti-androgens, ko kuwa zai daina shansu ne ya rayu da ita cikin compulsive-sexual behaviour? Da aggressiveness mai iya tashi a kowanne lokaci?
Kamar Daddy ya san abin da yake sakawa da warwarewa a zuciyarsa, sai ya sanyaya murya ya soma magana cikin yanayin rashin nuna karaya,
“Ni dai Ishaq Sarhamu, ban tanadar wa rayuwar ku komai ba, ban zabi daya ba cikin abin da ka ke tunani. Babu kuma likitan da yace min ka warke. Da Allah na dogara. Shi na damka wa rayuwarka Mu’azzam, Ya yi yadda Ya ga dama da ita, na amince (wa man yatawakkal alal-lahi fa huwa hazbuhu). Amma ba zan juri ganinka cikin wannan rayuwar da ka ke yi ba mara future, mara ma’ana, mara focus, mara aspiration. A matsayina na Uba dole in yi wani motsi a kai ko da kuwa motsin nawa ba zai zamo solution ba, ko da motsin nawa ba shi ne daidai ba. A kalla dai na samu sanyi a zuciyata na cewa na sauke nauyin da ke kaina, wanda Ubangiji ya rataya min
Likitoci basu ce bazaka iya aure ba, kaine ka zabi hakan Mu’az sabida bacin ran abinda Halima tayi maka da bakin cikin rasa ita waccan ‘yar Ethiopia. Amma zasu iya taimaka maka kayi normal rayuwar aure kamar kowa based on treatment. Please accept my decision and submit everything to Allah�.
Mu’azzam bai san lokacin da ya ce, “Daddy, ita kuma matar fa? Ba ka tunanin me zai faru da tata rayuwar? Me hakan ke nufi ga tata rayuwar? Ba ni da soyayyar da zan ba ta! Ba ni da kaunar da zan raba da ita. I have no feelings a kan diya mace. Daddy wannan zai zama zalunci ne a gareta....…�.
“Mu’azzam!!!�
Mahaifin ya kira sunansa da karfi.
‘‘Da kai da Aalimah duka ‘ya’yana ne, ba zan zalunci kowannenku ba, ina da kyakkyawan hope na cewa ban cutar da kowa a cikinku ba. Gata na yi wa dukkanninku.
Ba wanda zata samu da zai yi replacing Aboulkhair a gareta in ba kai ba. Ba wadda zaka samu ta rungume ka tsakani da Allah sama da ita. Ya rage naku ku karbi wannan gatan ko ku hambare shi ku bada mana kasa a ido. Suna nan tafe karshen satin nan, a kara gyara ko’ina na gidan kamar yadda na yi umarni�.
Daga haka ya kashe wayar sa. Ba tare da ya bashi damar cewa komai ba.
Ya dade rike da wayar a hannunsa, ya dade yana tauna kalaman mahaifinsa a bisa ma’auni na hankali da tunani. Da ya ji tunanin na son janyo masa ciwon kai, kuma babu wata hanyar kubuta a cikinsa dole ya hakura ya kwanta bayan ya kashe wayar sa. Amma duk yadda ya so ya runtsa hakan bai samu ba. Wani suna da Daddy ya ambata yake son tuno a inda ya san sunan.
“Aalimah!!!�
Ya fadi sunan a kan harshensa duk dai a kokarinsa na tuno mamallakiyar sa. Wa ya sani da wannan sunan a duniya bakidaya ban da matar rabin ransa ABOULKHAIR???
Mu’azzam ji ya yi duniyar na yin katantanwa da shi kafin ta dire shi a kan tsakiyar gadonsa. Tambayar kansa ya shiga yi; tsakanin shi da su Daddy wane ne mai cutar kwakwalwa? Wa ya fi dacewa da karbar rehabilitation? In har Aalimar da ya sa ni suke nufin sun karba masa auranta, tabbas lokacin da zai yi gammo ya bar gari ya zo kafin su zo su tadda shi. Abu na karshe da ba zai iya ba ko duk duniya za ta taru a kansa!!!
******
Gumsu ce tsaye a kan Aalimah tana fama da ita a kan ta yi wanka, yayin da ita kuma ta ce ko da a ce za ta fi kowa wari a duniya ta daina wanka.
Gumsu ta yi dariya wadda ke kara qular da Aalimmah, ta ce, “To ni da ki ke yi wa tambotsai mene ne nawa a ciki? Inji dai ba ni na kar zomon ba balle a bani ratayar sa? In ba tsoro ba ki yi a gaban Inna Kasisi mana? Sai a bayan idonsu ki ishe ni da rashin mutunci kala-kala, kada Allah ya sa ki yi wankan, Basma na hanya, ta zo ta ga abin da ki ke yi, wai don ba ki son dan uwanta�.
Wata irin harara Aalimah ta zuba wa Gumsu.
“Idan ita Basman uwata ce ta sanya ni karbar sadakin nan�.
Gumsu ta ce, “I can relate. Ni wallahi kin fara sa min ciwon kai, wajen Inna zan maida ki. Don in zan shekara ina fada musu rashin kunyar da ki ke min ba yarda za su yi ba�.
Ta jefa mata bath kit dinta ta bar wajen.
Waya ce ta iso wa Gumsu cewa Basma ta iso, tana dakin Inna Bintou, tana tambayar inda Aalimah ta ke. Basma ba ta san da sabon gidan da mahaifinta ya gina a nan Yamai ba, kamar yadda ba ta san da sakin da ya shiga tsakaninsa da mahaifiyarta ba. Ta dade da sanin Mummy na son zaman U.S kamar me. Ta gaya mata ita ta zabi zaman can, shi da Gumsunsa sun zabi dawowa don haka kowa ya kama hanyarsa.
Ba irin rarrashin da Basma ba ta yi wa Mummy ba kan ta bi sawun mijinta, ta ce sai ranar da Mu’azzam ya warke, bayan tana da masaniyar babu maganin da zai yi maganin lalurar Mu’azzam a dare daya, sai dai a bi alternative a gode wa Allah.
A ganin Basma, Mummy ta yi amfani da lalurar Mu’azzam ne kawai don ta ci gaba da zama a U.S, in ban da haka mutumin da ba gari daya suke ba, me za ta kulla wa rayuwarsa?
Hatta sayar da lodge dinsu na Boston da Daddy yayi Basma ba ta sani ba. Don haka bata san cewa Mummy a gidan Mu’azzam take zaune ba.
Isowar su Niamey kenan ita da tagwayen ‘ya’yanta, Daddy ne ya kira ta musamman don ta taya Gumsu lallashin Aalimah kasancewar ta wadda tafi kowa shaquwa da Aalimah din, su kuma raka ta dakin ta su biyu. Basma jin ta ta ke kamar a gajimare don farin ciki da kulla wannan aure da iyayensu suka yi. Koda Mu’azzam ba ya shiga rayuwarsu Allah ya sani tana matukar son dan uwanta. Kuma ta dade tana fargabar ranar da Aalimah zata yi aure a wani gidan daban ta bar hannun su, don haka ko ta’ina ita wannan hadin ya yi mata daidai.
Akwai wata magana da suka taba yi da Aboulkhair ta sirri gabanin rasuwarsa, wadda ta goge duk wani bacin rai da kullaci da ta ke da shi akan yayan nata Mu’azzam;
Ya gaya mata Mu’az ba shi da lafiya.
Ya gaya mata aggressive patient ne.
Alakar su ta nesa-nesa na da alaka da mental state dinsa.
Bayan haka bai gaya mata kowanne irin disorder yake fama da shi ba.
Basma a dakin Inna Kasisi, bayan sun gaisa ta karbi twins tana fadin,
“Masha Allah da ‘yan lukutaye, kun zo don ku amshe min miji, to kwalelenku duk jar fatarku�.
Dariya Basma ta yi tana fadin, “Kai Inna akwai kishi, ta ga ‘yammata masu lafiyayyar fata duk ta gigice�.
Inna ta ce, “Ke kuwa ai dole. Muna zaune da mijina lafiya, yana nan-nan da ni ya ga wadannan larabawan naki ai sunana ma mantawa zai yi�.
Basma ta sake kwashewa da dariya da ma gwanar dariya ce tun yarintar ta. Abin dariya bai da wuya a wajenta. Kullum fararen hakoranta a waje suke. Very jovial kamar Yayanta Aboulkhair Ta ce,
“Inna ina amaryar tamu ne? Na leka dakin Inna Bintou ba ta nan�.
Inna Kasisi wadda ke jin haushin Aalimah har iya wuya ta kyabe baki, ta ce,
“Tana gidan Gumsu, kafaffiyar yarinya mai zuciyar banza. Ni da Aalimah ai mun dade da raba jiha. Wanda duk ba ya son Mu’azzam ni ce ba ya so wallahi�.
Murmushi Basma ta yi ta ciro nono tana bai wa ‘yarta, ta ce, “Inna ku bi ta a sannu, ba son shi ne ba ta yi ba. Monsieur Aboulkhair ta ke tunawa da kusancin da ke tsakaninsu, it’s not easy to endure (jure hakan abu ne mai wuya)�.
Inna ta mike don zancen ba ya mata dadi ko ta ina, a ganinta Aalimah kiyayya ta ke yi wa Mu’azzam kawai don ba shi da lafiya.
Ta ce, “In dai lalura ce babu wanda ya wuce ta, uwarta ma yau shekaru goma sha biyar tana fama, haka ubanta ke hakuri da ita da kalar tata lalurar, ita ma ta je ta yi hakuri da lalurar dan uwanta, waraka a hannun Allah take, cewa nake kun ce bada magani ta karanta? Ba sai ta yi ta ba shi maganin ba su zauna lafiya?�.
Zancen ya so ya bai wa Basma dariya, da ta karanta bada magani ai ba likitar kwakwalwa ba ce. Likitancin ma sai neuro-psychiatry. Rokon Inna ta ke yi ta sa a raka ta gidan Gumsun (gidan mahaifinta), tana cijewa tana fadin,
“Kada ki wani je ki lallashe ta, bar ta da halinta na tsiya. Aure don Mu’azzam bai sa kansa ba ne, da tuni ya auri hudunta a rana daya�.
Basma ta tabbatar Inna Kasisi ba za ta sa a raka ta inda Aalimah ta ke ba, ta dau zafi da ita sosai, sai ta koma wurin Bintou, ita ce ta sa autanta Bello ya raka ta.
Daga bakin kofa Basma ta tsaya, tana kallon diramar da ake tsakanin Aalimah da Antinta Gumsu a kan cin abinci, Gumsun na fadin;
“Ki ci kada mu kai ki da komada, haka kawai ki sossoke min Da, rama ba ta kyau da amarya’.
Ta ce, “Anti Gumsu ina girmamaki, ina ganin girman ki, amma in ki ka kai ni bango zan yaye hijabin girman nan da nake ba ki. Na ce ba zan ci ba, ki yi min dura in ya zama dole�.
7/6/21, 4:51 PM - Buhainat: BASMA
Basma ta kama haba, tunda suke tare ba ta san Aalimah da tsiwa da rashin kunya ga na gaba da ita ba. Lallai da gaske ta ke kin Mu’azzam din. Tunda har ya sauyata rana daya. Gumsu ta ce,
“Gara da ki ka gani da idanunki, in wani na bai wa labarin rashin kunyar da Aalimah ta ke min ba zai taba yarda ba, ni kuma kamar dole sai na shiga sha’aninta. Babanku ke ba ni hakuri wallahi da tuni ta tsufa a Las Vegas, don ta soma kawo ni bango�.
Basma ta sako kafa tana shigowa falon ta ce, “I can relate. Amma ni lallashi ne nawa tunda ba zan so Yayana ya same ta duk kasusuwa ba, kada ta soke min shi. Na fi son ya ganta bul-bul, ko’ina ya taba ya ji tubus. Don haka don Allah don Annabi ‘Aal’ ki karbi abinci ki ci…�.
Kawai sai Aalimah ta sunkuya a kan stool ta fashe da kuka, maganganun Basma kamar sabon Ubangiji ta ji su a kwanyarta. Shigowar Daddy kenan har zai wuce dakinsa ya jiyo kukanta, har zai kyale ya rabu da su don ya san maganar daya ce dai, sai kuma ya dawo sabida tausayin da Aalimah ke ba shi. Dakin ya shigo yana fadin, “Gumsu! Gumsu! Sabida Allah ba za ki lallashe ta ba sai dai ki dinga tunzura ta ko?�
Sai kuma ya ga Basma, ya ce, “Ke kuma saukar yaushe? Me ku ka yi mata haka?�
Cikin kuka ta ce,
“Daddy, Basma ta zage ni�.
Basma ta hau gaishe shi da kokarin kare kanta, ya ki amsawa, ya hau ta da fada.
“Ku da za ku lallaba ta sai ku dinga kunnata, bayan kun san a kan tsini ta ke?�
“Ka yi hakuri Daddy, ba za mu sake ba�. Basma ta fada cikin ladabi.
Ya wuce cikin fushi. Basma da Gumsu suka kama abin da ke gabansu don yanzu tsoron sharrin Aalimah suke ji. Ka ce ‘allura’ ta ce ka ce ‘garma’, don ta ga Daddy yana biye mata.
Kwana biyu bayan nan Daddy ya umarci Gumsu da ta kai ta cikin gida ta yi sallama da kowa, wurin Malam ya zama daki na karshe da za su je. Tun Aalimah na kallon al’amarin a matsayin almara har ta yarda gaskiya ne. A lokacin da Malam Ibrahim Raazee ya dora mata sadakinta a tafin hannunta ya kuma bude kofofin nasiha, ban hakuri, ban baki da neman afuwa daga gare ta, kan cewa sun yi exercising power dinsu ta iyaye a kanta kan ba yadda za su yi ne su ma, su samu nutsuwa da kwanciyar hankali in ba hakan ba.
Wannan ne gata na karshe da suke jin za su yi wa rayuwarsu ita da Mu’azzam. Babu mijin da suke ganin zai rike ta da daraja da kima bayan Aboulkhair sai shi Mu’azzam, su ma kuma babu matar da za ta rike musu Mu’azzam da lalurorinsa tsakani da Allah sai ita. Wannan ne hujjarsu ta hada su aure, ta fi kowa sanin yanayin rayuwarsa bayan Aboulkhair tunda sun zauna tare, ta kuma zauna da Aboulkhair ta ga yadda yake kula da shi. Don haka suke da kyakkyawan fata a kanta. Ta yi hakuri kada ta bada musu kasa a ido. Ta manta da kusancin dake tsakanin shi da Aboulkhair ta gina sabuwar rayuwa mai inganci. Aboulkhair ya riga ya yi tafiyar da bazai taba dawowa ba, kuma shima hakan ne gata na karshe da zata yi masa wato tallafar rayuwar Mu’azzam a sanda babu shi.
Aalimah ta ji hawaye masu dumi sun zubo mata, a lokacin da kakansu ya gama yi mata wannan nasihar. Shima yana share nasa hawayen a karshe. Sosai yake tausaya musu dukkansu ita da Mu’azzam din yadda zasu fara fuskantar sabuwar rayuwar da babu Aboulkhair a cikin ta. Ta samu hannayenta da rike kudin sadaqin kam-kam ba tare da sun yi shawara da ita ba. Wanda ke nufin; sun karbi auren Mu’azzam da hannu bibbiyu, ba tare da sun ba ta damar yanke hukunci tsakaninta da zuciyarta ba.
Ana tsaka da zub da kankara (snow) suka sauka a Las Vegas. Don haka ba karamin shiri suka yi wa ‘ya’yan Basma ba, suka kuma sanya su a bayansu ita da Gumsu suka goye da zani. Aalimah ko taya su hidimar yaran ta ki yi sai cin fushi ta ke. Daga lokacin tashinsu da lokacin saukarsu Daddy ya gaya wa Mu’azzam. Wanda har zuwa lokacin yake cikin halin rudu da kidimewa, ya yi kokarin ya fahimtar da Daddy ba zai iya wannan auren ba Daddy ya ki sauraronshi, ya ce,
“Auran nan Mu’azzam an riga an daura shi, ka yi hakuri kawai kamar yadda ta yi hakuri. Ka karbi kaddara kamar yadda ta karba. Ita ma ba ta so, amma ta nuna muna da ikon sanya ta ta yi, ta yi ko da babu son ranta. Haka nake so kai ma ka karba.
Ya kare zancensa da cewa “Mu’azzam ba ka san ta ya ya aka kulla auren nan ba, ba da son ran wasu a cikin gida ba. Burin su ka dawwama a haka babu aure saidai ka ga ‘ya’yan su na yi. A hakan da kake ka tsolewa wasu da dama ido suna kullin ka ba tare da sanin ka ba.
Ina so ka sani duk duniya bayan ni da mahaifiyarka sai Mansour a masu kaunarka. Ka fidda ni kunyar dan uwana mai kaunata da zuri’ata mai kuma kaunarka tsakani da Allah, ka rike Aalimah amana tsakaninka da Mahaliccin ka, in ka yi min haka ka gama min komai Mu’azzam, albarka ta gare ka ba za ta taba yankewa ba!�.
Wadannan maganganu na Daddy sun firgita shi, sun sanyayar masa da jiki ba dan kadan ba.
Don haka Mu’azzam ya tattara damuwarsa ya hadiye. Babban jin dadinsa da ya kasance su Mummy suna cikin gidan. Ta samu abokan hira da taya ta zaman gidan. Don shi kam ba za a fara abin da ba za’a wanye lafiya tare da shi ba. Yana matukar jin dadin rayuwarsa a yadda yake yin ta, baya maraba da kowanne canji.
Ko Mummy bai gayawa su Basma na tafe ba, kamar yadda bai yi mata bayanin komai ba cikin abubuwan da suke tattaunawa da mahaifinsa. A ganinsa abin da aka dauka da muhimmanci shi ake tsayawa yi wa mutane bayaninsa, yadda suka ajiye ‘yarsu idan zaman ya ishe ta ya tabbata za ta yi musu waya su zo su dauke ta. Tunda shi an yi masa kandagarki da rabuwa da ita har abada.
Harrison ya tura ya dauko su a filin jirgi. Bai san da wanne ido zai kalli Aalimahn Aboulkhair wai a matsayin matar sa ba. Kasancewar Harrison ya san Aalimah bai sha wahalar gane su ba, ya shigar da kayansu booth yana ta yi wa Aalimah fara’a, shi a dole ya nuna ya santa, amma yadda ya ga fuskarta kamar hadarin da ya hadu ya nausa yayi gabas, dole ya hadiye sanayyarsa cikin cikinsa.
Mummy da Yesmin na barci a dakinsu da ke kasa suka ji tashin sautin su Basma. Da farko sun dauka cikin mafarki ne, amma da suka ji ‘ya’yan Basma na canyara kuka sun rasa inda za su sa kansu da wannan weather mai tsananin sanyi wadda ba su taba riskar kansu cikinta ba, dole suka yarda ba mafarki ba ne. Fitowa suka yi da azama sai kuma suka kwasa da gudu suka rungume juna.
Sun dade ba sa tare, sun dade ba su ga juna ba. Soyayyar Mummy da ‘ya’yanta ta motsa. Kwana suka yi a zaune. Duk da Mummy na sanyo Aalimah cikin hirarsu sai ta ga Aalimah din ta ki sakin jiki. Sai sunkuyar da kai ta ke ta kasa kallon fuskar Mummy. Sosai ta ke cikin rudu da damuwa, ita kuma haka za ta kare rayuwarta cikin auren ‘ya’yan mutum daya?
Gumsu ce ta fadi wa Mummy ko me kenan bayan sun sallaci asubahi. Mummy sai ta fashe da kuka wanda dukkaninsu ba su san ko na mene ne ba. Har sai lokacin da ta mike ta shige daki. Kukan damuwa ta ke dana farin ciki duka a lokaci daya, damuwarta shi ne ta san Mu’azzam ba shi da lafiya wannan ba karya ba ne. Ta san yadda aka wanye a aurensa na farko, tsoro ta ke ji kada a maimaita a kan Aalimah. Farin cikinta shine yau Allah ya cika mata burinta Mu’azzam yayi aure, ya zama cikakken mutum mai cikakkiyar rayuwa kamar kowanne dan adam. Babban farin cikinta kuma shine dawowar Aalimah cikin iyalinta. Don ta tabbata in ta kubuce musu sun yi asarar da ba zasu mayar ba.
Ta dade cikin tararradin sake yin aurenta tun bayan gama iddarta. Tana ganin kimar yarinyar domin a tsawon zamanta da Aboulkhair ba ta taba ganin wani hali na ashsha a tare da ita ba. Har gobe kuma tana jin kunyarta na mugun halin data nuna mata a baya, lokacin da Allah ya hada su zama tare a Boston.
Hakika tana son Mu’azzam ya yi aure amma ta wani fannin ba ta so Ishaq ya hada da Aalimah ba. Tunda ba su san me auren zai haifar ba. Ta so su ci gaba da zumuncinsu a haka, Aalimah ta samu miji mai lafiya kamarta ta aura, don tserar da zumunci da ganin mutuncin juna.
Ga shi sun ce an riga an yi auren, ba ta da wata kima gare su a yanzu balle har su yi shawara da ita kafin ayi. Za ta ci gaba da zama tare da Mu’azzam da Aalimah don ganin ba su kusanci juna ba, balle shakuwa ta shiga tsakaninsu. Har akai ga abinda zai bata komai. A ganin ta hakan kawai zata yi ta tserar da auren nasu.
Washegari tun karfe bakwai dai-dai Mu’azzam ya fito dining karyawa kamar yadda ya saba. Mummy kawai ya samu a dining din tana zaman jiransa, su suna can suna ta ramuwar barci wanda ba su samu sun yi ba a daren jiya. Ya yi shiri tsab cikin kayan sanyi bakake da jeans baki samfurin NEXT. Ya daure kafafunsa cikin bakin cambass. Cikin nutsuwa yake hada shayinsa wanda ya cikawa gahwah (coffe), amma kallo daya za ka yi masa ka fahimci cikin damuwa yake. Idan ya ce ba ya cikin damuwa kan auren nan da Daddy ya yi masa hakika ya yi karya. Ko ba komai wani nauyi ne aka dora masa wanda bai saba da shi ba.
Mummy ta yi gyaran murya ya dan daga manyan idanunsa farare kal! Ya dube ta, har wani sheki suke fitarwa na musamman da ba kowa yake lura da hakan ba sai wanda ya hada idanu da shi. Mu’azzam yana da kyau mai kayatar da idanu, mai sanyaya zuciya. Idan ka kalle shi za ka so ka maimaita ko don kyawun kwayan idanunsa. Sai dai kasaitar sa da jan ajinsa za su hana ka abokantake shi da sauri, idan ka samu ku ka gaisa ma ka gode. Bambancin sa da Aboulkhair kenan.
Wanda ya kasance mai faram-faram da son jama’a da yin haba-haba da su, balle makusantan sa. Matar sa tayi rantsuwa ta maya kan cewa babu mutum mai kirkinsa da saukin kansa a duniya.
Mummy har sau biyu tana gyara murya, amma ta rasa abin cewa, shi kuma hada shayinsa yake yi bayan gaisuwa bai ce mata komai ba. Ko yaya su Basma suka kwana bai tambaya ba, ta yi ta maza ganin cewa zai gama shan shayin ya tashi ne ya barta a wurin ba tare da sun tattauna akan zuwan bakin nasu ba, ta dube shi tace,
“Kana sane da zuwan su Basma?�
A gajarce ya amsa “Eh’.
Duk suka yi shiru, yayin da shikuma yake sipping shayin a hankali.
Mummy ta sake cewa,
“Ashe aure Daddyn ku ya yi maka ni ba ni da labari?�
Shiru Mu’azzam ya yi, kamar ba da shi ta ke magana ba. Ta ci gaba da cewa, “Shi kenan kuma don an sake ni ba ni da martabar da za a nemi shawarata kan al’amuranku? A kalla a ba ni hakkina na haihuwa ko?�
Mu’azzam ya soma zama bored da maganganun Mummy, don bai ga wanda ya shafe shi a ciki ba. Tsakaninta da tsohon mijinta, shi me ye nasa a ciki saboda Allah? Karewa ma shi kansa ba a yi shawara da shi ba. Mikewa ya yi tare da aje kofin hannunsa ya yi baya da kujerarsa ya hau duba agogon swatch da ke daure a damtsen hannunsa.
“Mummy zan wuce office kuna bukatar wani abu?�
Ta san in ta ce ta ji haushi ta wahalar da kanta a banza. Kewar Aboulkhairi ta zo ta lullube ta. Kawai sai ta soma hawaye, ta rufe fuska da tafukanta. Ta kifa kai akan teburin cin abincin ta na wani irin kuka mai ban tausayi.
Da yanzu yana nan yana lallashinta, da yanzu yana taya ta neman mafita ga damuwarta, da yanzu yana nan cikin damuwa da damuwarta… Da yanzu ya bata dukkan lokacinsa ya saurareta…. Sun tattauna lamarin yadda ya dace sun nemo mafita. Mu’azzam ya koma kujerar sa ya zauna ganin Mummy na wannan kuka. Wanda bai San musabbabinsa ba. Hankalinsa ya kai kololuwar tashi. Don shi har ga Allah bai ga cewa yayi wani abu wanda ba daidai ba. Ya kai hannunsa cikin sumar kansa yana cakudawa a hankali, ya ce,
“Mummy ki daina ganin laifina, ni ma ban san da zancen auren ba sai bayan da suka daura shi, Mummy I don’t want to talk too much…a kai, ba ni da masaniya a kan ala’amarin nan, me ki ke so in ce miki?�
Mummy ta cire hannu daga fuskarta, yana ganin yadda hawaye ya wanke mata fuska. Hankalinsa ya kara dugunzuma ya tashi.
“Ba abin da nake so ka ce min, illa ka damu da damuwata Mu’azzam. Sau da yawa ina hadiye abubuwa sabida lafiyar ka, amma na lura bayan rashin lafiya cikin dabi’unka har da ‘hali’. Halinka ne Mu’azzam rashin damuwa da al’amarin kowa…!�.
Zai yi magana ta katse shi, “Ni na san na yi rashin da ba zan mayar ba! Aboulkhairi, ban san muhimmancin ka ba sai da na rasa ka! Yadda ka damu da ni ni ban damu da kai haka ba! Ka taba cewa don Allah in so ka yadda nake son Mu’azzam. Yau ga ni ina kuka a dalilin rashin ka, Mu’azzam din da na kwallafawa rai ga shi a gabana, amma ban da bakin ciki ba abin da yake cusa mini.
Na hakura da aurena na shekaru sama da talatin saboda shi, amma ba ni da alfarmar tattauna matsala ta da shi…�. Sai kuka ya kara kwace mata.
Ba abu kankani ke sa Mu’azzam kuka ba, amma dole yau Mummy ta sanya shi kuka. Ya ji yana mai kaico da yanayin halayensa lokaci na farko a rayuwar sa.
Abin da ba ta sani ba, rashin Aboulkhair ya kara taimakawa wajen cire masa walwala da yawan magana. Tun da ya fito daga asibiti walwala ta kara karanci agareshi. Da yana nan ko ba ya son yin magana in dai ya zo inda yake dole ya yi ta, ko ba ya son yin dariya sai ya yi. Zai so Mummy ta ci gaba da yi masa uzurin da ta ke yi masa kada ta gaza…. Zai so Mummy ta daina kwatanta shi da Aboulkhair ta kowacce fuska, domin Ubangiji da ya halicce mu sai Ya halicce mu da halaye mabanbanta, da kamanni daban-daban da personality iri-iri. Shi haka Ubangiji ya halicce shi.
7/6/21, 4:51 PM - Buhainat: 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
A wannan lokacin ba shi da abin yi ban da ya koma ya zauna, ya bata lokaci wajen lallashi da bata hakuri kawai, ba tare da ya yi mata bayanin cewa; shi ma in zai samu mai lallashinsa so yake yi. Ya fi ta damuwa a wannan lokacin, kuma ya fi-ta kewar Aboulkhair.
Koda ya je office yau a makare ya je, saida ya bada hakuri sosai. Yana shiga bayan yayi loosing tie din shi ya zauna a kujerarsa wayarsa ya fiddo ya sake tura wa Mummy text na ban hakuri sannan ya fuskanci ayyukan dake gabansa.
Bayan fitarsa Mummy ta dade zaune a wurin, har zuwa lokacin da text din Mu’az ya shigo mata, murmushi ya subuce a fatar bakinta sabida irin tausasan kalaman da yayi amfani da su duk da cewa ba masu tsayi bane, sai kuma tausayin sa ya lullube ta. Ta sani kwarai shima baya jin dadin yadda rayuwar shi ke tafiya, da gaske yana bukatar mace a gefen shi ba tare da ya san cewa rashin macen ne ya maida rayuwarshi incomplete ba. Ta samu kanta da yi musu addua Allah ya hada kansu shi da Aalimah tare da godewa Mansour cikin zuciyarta, don tana da kyakkyawan zaton wannan kokarin nashi ne ba na wani ba.
Ta share hawayenta ta koma daki. Basma ce kawai ido biyu tana shayar da ‘ya’yanta. Nan ta karbi mai sunanta daga hannunta ta zauna suka soma hira, hirar da ta tada Gumsu da Aalimah daga baccin gajiyar da suke yi. Aalimah ta mike ta nufi toilet don yin wanka. Mummy ta bi ta da kallo tana tausaya mata cikin ranta. Gaba daya ta rame, tayi zuru-zuru ta fita hayyacinta. Babu wata alama ta amarci a tare da ita. Kafarta ko lalle babu.
Kwanaki uku da Aalimah ta yi cikin gidan ba ta hadu da Mu’azzam ba ko sau daya. Yana riga kowa ficewa, kuma sanda zai dawo sun gudu daki sabida sanyi. Ba sa iya zaman falon duk da room-heater da ke aiki. Yana shigowa kuma da sassarfa yake hayewa upstairs din shi kada ma su samu damar ganin sa. Mummy da Gumsu ke musu girki, Aalimah ba ta umh ba ta umh-umh sai in sun sako ta cikin hirarrakinsu ta yi murmushi.
Idan a da tana kallon al’amarin matsayin almara ko mafarki, yanzu ta tabbatar reality ne. Cikin gidan Yayan su Mu’az ta ke, kuma wai a matsayin matarsa ta sunnah. Yayan nan nasu ita da Aboulkhair data ke matukar girmamawa da hidimar dafowa abinci da hadowa magunguna. Irin rayuwar da ta yi da Aboulkhair ake nufin ta maimaita da Mu’azzam! To ta ina? Ta ya ya? Da wacce fuska? Ta wace hanya? How could that be possible? Ko da a ce Mu’azzam zai ba da fuska (wanda ta tabbatar hakan impossible ne) ita wacce irin butulu ce ga Aboulkhair da za ta aikata hakan gare shi? Me yayi mata a rayuwa banda alkhairi da zata saka masa da auren Yayansa mafi soyuwa a gare shi?
Anya iyayensu na aiki da hankali da tunani a lokacin da suka yanke wannan shawarar suka kuma zartar da wannan hukuncin?
Irin tunaninnikan da Aalimah ke yawan yi kenan a duk lokacin da ta kadaice kanta cikin daki ko a toilet, don in tana tsakiyarsu ba sa bari ta yi tunanin komai, yanzun nan Basma za ta janye mata hankali da hira, duk dai don kada ta barta ta yi tunanin wanda ita ta san ya zame mata dole ta yi shi.
Satin su Gumsu biyu a LasVegas Daddy ya fahimci basu da niyyar komawa gida, sun je sun shantake abinsu Mu’azzam na jika su da jin dadi, kudi wannan atm guda ya basu suna sayen duk abinda ransu ke so, ita Gumsu sayayyar haihuwa take ta yi, Basma ‘ya’yanta da mijinta take yiwa sayayya da kannen mijinta ‘yan mata su Suhaima. A ranar da suka cika sati biyu Daddy ya kira ta yana ta fada kan su dawo haka, sati daya ya ce su yi amma sun je sun canza booking sun yi zamansu. Gumsu ta ce.
“Mummy ce ta ce mu kara sati don Aalimah ta sake sosai�.
Cikin mamaki Daddy ya ce, “What? Da ma har yanzu tana gidan Mu’azzam? Na dauka tuntuni ta koma Kano? Ashe Zulaiha ba za ta taba yin hankali ba?�
Ita dai Gumsu ta yi shiru, ta kuma shiga dana sanin ambatar Mummy da ta yi, ba ta san cewa bai sani ba, da ba za’a ji a bakinta ba. Ko da ta ke da surutu na barkwanci ta ke yi amma ban da na tsegumi da munafurci. Daddy ko sallama bai yi mata ba ya kashe wayarsa.
Sun yi booking za su tashi a washegarin lahadi, don haka suka zauna a falo suka ki yin barci suka kuma ki shiga daki suna jiran Mu’azzam ya dawo, don su yi sallama da shi. Mu’azzam, wanda gidansa ya zame masa kurkuku a yanzu, ba shi ya shigo ba sai karfe goma na dare.
Hannayensa biyu cikin aljihun bakar kwat din jikinsa, kafarsa daure cikin fararen cambass samfurin (NIKE), da dan gudu-gudunsa ya shigo zai haye upstairs din sa kamar yadda ya saba. Bai yi tsammanin ganin ko mutum daya a falon ba kamar yadda suka saba, amma sai ya gansu dukkanin su suna zaune zaman jiran shigowar sa ban da Aalimah kadai. Ga dukkan alamu kuma zaman ba na komai bane dakonsa suke. Dole ya dawo ya zauna a kujerar da ke fuskantar Mummy yana tambaya ko lafiya ba su kwanta ba? Basma ta ce,
“jiran ka muke yi mu yi sallama, gobe za mu koma gida insha Allahu�.
Kada kai ya yi irin na ‘to ni me ye nawa a ciki?’ Kafin ya dawo ya samu kujera kusa da Basma ya zauna, ya sanya hannu cikin aljihun kwat dinsa ya fiddo kudi ko kirgawa bai yi ba ya bai wa Basman, ta sa hannu ta karba tayi godiya, ya dauko wasu ya bai wa Gumsu. Gumsu ta harare shi shida kudin nasa, ta ce,
“Ni ba kudi nake so ba, kawai Malam ka kular min da ‘ya ta. Na ba ka amanar ta, ka tausaya mata, ba ta da kowa a garin nan sai kai. Ba zaman Mummy ta ke yi ba, zamanka ta ke yi, don haka ba zan tafi ba sai an ba ta dakin ta da Daddy ya ce a ba ta, ba dakin Mummy ya ce min ta zauna ba�.
Mummy ta harare ta ta gefen ido, Gumsu kan ba ta haushi wani lokacin, ta fiye wuce gona da iri, tana nufin ta fi-ta sanin abin da ya kamata ne? Ta ce,
“In kin tafi zan raka ta dakin nata ai�.
Gumsu tayi tsalle ta dire ta ce atafau sai ta kai Aalimah dakin da ya zam mallakinta za ta bar gidan. Mu’azzam mikewa ya yi zai wuce ba tare da ya ce komai ba. Kansa ya dau zafi sosai, ba ya son hayaniya, komai kankantar ta. Ita kuma Gumsu ya gama fahimtarta ‘yar hayaniya ce ba tun yau ba. Ba shi da zabi ban da ya lallabata ta bar masa gidansa. Ya ce ta biyo shi ya nuna mata dakin da aka yi furnishig din da sunan ‘yar tata. Da karfin gwiwarta ta bi bayansa.
Kwarai ta yaba da bedroom din, sosai furnitures din suka burge ta. Ga dakin kusa da dakin barcinsa. Duk wani motsi da daya yayi dayan zai ji shi. Hakan ya yi mata sosai. Ta je ta takura Aalima ta yi wanka a gabanta cikin ruwan turare na musamman, ta fiddo mata kayan da za ta sanya sababbi kar! A ledarsu, ta feshe su da turare, ta gyara mata dogon gashin kanta. Sannan ta rufe ta cikin lullubi ta kai ta har dakinta gefen gadonta.
Ta gama karance Mummy Zulaiha tsaf! So ta ke ta hana kusanci tsakanin Aalimah da Mu’azzam, amma ba ta san dalilinta ba, shiyasa ta dage sai ta kawo Aalimah dakin ta da kanta, cikin zuciyarta ta ce, “Allah ya fi ki�.
Ta zauna a gefen Aalimah ta soma yi mata huduba, ta ce, duk runtsi ta zauna a dakinta, ba ta yarda ta koma dakin Mummy ba, ta shiga rayuwar Mu’azzam ko ba ya so. Ta cire kunya ta kutsa kanta cikin rayuwarsa kota yaya, don in ta biyewa Mu’azzam zata shekara cikin gidan sa basu gaisa da juna ba, wanda wannan ba shine kudurin iyayen su a kan su ba; so suke ta canza Mu’azzam ya dinga walwala da farin-ciki kamar kowa. Duk abin da ta ke so ta dafa da kanta kada ta dogara da girkin Mummy, gidanta ne ba gidan Mummy ba, ta kasa zaman nata auren kada ta sake ta hana ta nata zaman auren.
A hankali Aalimah ta ce, “Aunty Gumsu ni wace ce da zan yi fito-na-fito da ita a gidan danta? Dan ma da ba son shi nake yi ba dole aka yi mun?� Sai kuka.
Gumsu ta ce, “Zauna nan wawuya ki yi ta dakon rashin so, tunda kin ga shi zai fishshe ki. Ki dubi Mu’azzam daga sama har kasa za ki tabbatar ba karamar kyauta ce Allah ya zabo ki cikin dubban mata ya yi miki ba. Ruwan ne ki karbi wannan kyautar da hannu bibbiyu, ruwanki ne ki yi wasarere da ita ki yi wa kanki asara�.
Ta mike za ta fita, sai kuma ta juyo, ta dan rungumeta a jikinta ganin tanata hawaye ba kakkautawa.
“Take it easy my daughter. Insha Allahu sai kinyi alfahari da wannan aure. Mu’azzam is a genius you will soon come to love your husband fiye da son da ki kai wa kaninsa. Na zuba miki duka magungunan da na tanadar miki a lokar gadon ki, Enjoy yourself my daughter�. Ta yi murmushi sannan ta sumbaci goshin ta ta fita.
Ita ba karamar yarinya ba ce, ba kuma yau ta fara aure ba, sarai ta fahimci magungunan da Gumsu ke nufi. Wani siririn murmushi tayi mai kama dana tausayin kai. A ranta ta ce,
“Kin dai ajiye min sinadaran da zasu taimaka min wajen tafiya ta lahira duk ranar da ya waiwaye ni. Don ba ki san lalurarsa ba ne�.
*****
Gida ya zama daga ita sai Mummy da Yesmin. Tunda maigidan ba zama yake a cikinsa ba sai lokacin barci. Haka kawai shi da gidansa an haramta masa zaman cikinsa. Wannan abu na ci masa tuwo a kwarya. A da, ba abin da yake so irin ya bude ido ya ganshi a falonsa ko a balcony din gidansa, hakan na sanya shi nishadi matuka. The unbelievably beautiful building of his house wanda mutanen Las Vegas suka kira fierfield terrace and the scent of his tidy green grasses na sanya shi nishadi. Amma yanzu ya zama daga gida sai office sai kan titi.
Wani lokacin zuciyarshi kan shawarce shi to ya dinga zuwa BAR mana don rage lokaci kadai ko ba don ya sha ba? Wata zuciyar sai ta ce, kai yanzu in aka ce ka doshi inda giya ta ke da sadaka sai ka je? Bayan ita ce silar mutuwarka a tsaye ba don ka mutu ba? Ka dai nemo wurin zuwa, amma ban da matattarar shan giya. Kowa ya debo da zafi bakin sa.
Aalimah na kokarin amfani da hudubobin Gumsu a zamanta da Mummy cikin gidan. Ta amince Gumsu mai kaunarta ce da zuciya daya. Sosai take girmama Mummy kamar uwar data haife ta. Bata saukowa kasa sam sai za ta nemi abin da za ta ci. In Mummy ta dafa nasu tana aje mata a food warmer in tanaso ta dauka. In bai yi mata ba ta dafa abinda take so. Tsakaninta da Mummy gaisuwar safe da yamma, tana shiga ta gaishe ta. Ta kuma zauna suna hira da Yesmin. Ita ma ta lura da abin da Gumsu ta gane Mummy ba ta son zamanta upstairs, ta fi son ta dawo nan dakinta su zauna tare don dai ba yadda zata yi ta gaya mata hakan ne. Dalilinta na hakan ne ba ta sani ba. Yesmin kan haura saman wajenta su yi hira. Tana nuna mata damuwarta kan karatunta da aka katse mata a Boston. A bakin Yesmin ta ji cewa Daddy ya sayar da gidansu na Boston dalilin dawowar su nan kenan.
Aalimah ta dade tana mamaki, a baya in wani ya ce mata Daddy zai taba barin rayuwar Turai ba za ta taba yarda ba, sabida yadda Turan ta ratsa jikinsu shi da ‘ya’yansa. Ta san Mummy dole ta zauna don ba za ta iya karbar rayuwa a Nijar da sauki ba. Don ma Yesmin ta sakaya ba ta ce an saki Mummy ba.
Tunda ta koma benen ba su taba haduwa da Mu’azzam ba. Ba wanda ya san da zaman dan uwansa, tana da toilet dinta cikin dakinta. Daga karfe shidda na yamma in ta yi wa Mummy gaisuwar yammaci ta dauki abinda zata ci a kitchen ta haye sama ba ta kara fitowa sai wayewar gari. Mummy kullum cikin observing dinta ta ke don ganin ko akwai wani sauyi a tare da ita? In ta zo mata gaisuwar safe ta dinga saka mata ido kenan, amma ga kwanciyar hankalinta ras ta ke ganin Aalimar kuma tana da tabbacin Mu’az bai dawowa sai Aalimah tayi barci, kuma sammako yake ya tafi office.
Sai kuma ta shiga damuwar ina yake zuwa haka after office hours? Kada dai shan giyar ya komama wa? Tunda bashi da lafiyar da zai nemi mata? Abincin safe kawai yake ci a gidan, wunin ranakun ba ta san ina yake samu ba, sai dai tana da tabbacin a WALDORF ASTORIA yake ci don baya cin wani abinci sai nasu kamar yadda ya saba a baya. Ba abinci ne damuwarta ba, inda yake zuwa sai dare ya nausa, shi ne damuwarta.
Mummy ba ta kara shiga cikin damuwa ba, sai da likitan Mu’az ya zo har gida ya same ta, cikin sirri yake gaya mata cewa, cikin satin nan jinin Mu’azzam ya hau, ko ta san me ye matsalolin sa na yanzu? Don hauhawar jini matsala ne babba ga mai matsaloli irin na Mu’azzam.
Mummy ta gaya masa iya abin da ta sani, cewa aure mahaifinsa ya yi masa ba da saninsa ba, kuma matar Aboulkhairi mai rasuwa. Har ma tana gidan ta tare. Nebrass ya yi rubuce-rubucensa, sannan ya tambaye ta ba’a yi masa wani abun da ba ya so? Ma’ana ba’a takura shi yin abinda zuciyar sa bata so? Mummy ta yi shiru, ko zamansu tare da shi itada Yesmin sarkin rikici ai ba ya so. Biyayya kawai yake mata ya takura kansa matsayinta na uwarsa ya danne ransa yake zaune da ita amma a kasan ransa baya so. Ya fi son kadaici. To amma in ta bar gidansa ina za ta?
A yanzu kam ba ta da karfin kama gida a U.S tunda ba ta aiki, sannan ba ta son yin nisa da shi, tana matukar tsoron abin da zai faru duk ranar da Mu’azzam ya kusanci Aalimah. Ita zaman gadi ta ke yi, idan Aalimah ta ki Mu’azzam wace mace ce za ta yarda ta zauna da shi a karo na uku? Kwarai tana tsoron zuwan wannan ranar. Amma Gumsu da kilbibinta ta raba musu daki ita da Aalimah.
Hawaye ta share, ta ce da likita Nebrass,
“Ni kaina ai damuwa ce ga Mu’azzam, amma likita ba ni da inda zan je�.
Cikin mamaki Nebrass ya ce, “Ina mijinta? Yana nufin Baban su Mu’azzam?�
A sanyaye ta ce, “Mun rabu�.
Kamar ya ce da ita, “Kuma aka ce dole sai kin zauna a kasar da ba taki ba?� Sai kuma ya yi shiru, ya soma ja mata kunne a fakaice.
“Mu’azzam dai yana son nutsuwa, yana bukatar sarari daga hayaniya inda hali. Ita kanta matarsa ta yi nesa-nesa da shi, in ba shi ya neme ta ba, Madame, lafiyar dan ki ita ce first, ya kamata ki duba wannan�.
Ya yi musu sallama ya tafi.
7/7/21, 8:09 AM - Buhainat: Damuwar Mummy ta nunku. Ta ga cewa komawa Nigeria ko Nijar ya zame mata dole kada wani abu ya faru da Mu’azzam da kyakkyawan treatment din da yake samu Ubansa ya ce ita ce sila.
Kuma a ranar Daddy Ishaq ya kira Aalimah a waya, ya ce ta kai wa Zulaiha wayar yana son magana da ita. A sautinsa ta ji fushi mai tsanani don Nebrass ya kira shi ya gaya masa komai.
Daddy ya soma fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ya ce, in ta kashe Mu’azzam sai ya yi shari’a da ita. Mummy na kuka ta shiga ba shi hakuri, kuma ta gaya masa ba ta da kudin tikiti, sai karshen shekara take karbar kamashonta na banki, sannan tsoro ta ke ji kada wani abu ya faru da Aalimah, Mu’azzam zai rasa mata ta uku… ita kuma burinta shi ne ya zauna da aure ko da babu abin da zai shiga tsakaninsa da matar.
Murmushi Daddy ya yi, ya kuma fahimce ta. Ya ce,
“In dai tikiti ne zai saya musu ita da Yesmin, wannan maganar da ta ke yi kuma ba huruminta ba ne, tunda ko likitansa bai ce don me aka yi auren ba. Ta bar wa Allah komai kamar yadda kowa ya bar masa.
Da wannan nasihar da Daddy ya yi mata Mummy Zulaiha ta soma hada kayanta don barin Las Vegas. Yesmin ta fi kowa farin ciki, ko ba komai ta san Daddynta ba zai barta babu karatu babu aure ba. Kuma zata kasance cikin ‘yan uwanta, ita kuma dama damuwarta kenan.
Har karfe goma sha daya na dare suna zaman dakon jiran dawowar Mu’azzam don yin sallama da shi, wanda yau yayi nisan kiwo fiye da koyaushe, bayan Daddy ya aiko musu da ticket mai zuwa Nigeria ba Nijar ba. Wannan ya dan taba ran Mummy, amma da ta tuna babu aure a tsakaninsu sai ba ta ga laifinsa ba. Kamar tuni yake mata da hakan.
Mu’azzam bai tashi shigowa gidan ba sai karfe goma sha biyu na dare. Zai haye benen shi kamar yadda ya saba ya gansu a zazzaune kamar masu neman gafara.
“Lafiya Mummy ba ku kwanta ba?�
Mummy ta harareshi kafin tace. “Abinda yakamata da magidanci kenan ya dawo gidansa lokaci irin wannan Mu’azzam? Ina kake zuwa sabida Allah? To ba wani abu ya hanamu kwanciyar ba, jiranka muke mu yi sallama�.
Mummy ta fada idanuwanta sun yi rau-rau suna son zubar da hawaye. Jikinsa a sanyaye ya ciro kafarsa daga steps din daya soma takawa ya dawo ya samu waje a gefenta ya zauna.
Maimakon ya bata amsar waccan tambayar sai ya jefa mata tambaya shima.
“Mummy an yi muku wani abu ne wanda ya bata muku rai?�
Girgiza kai ta yi, “Ko daya Mu’azzam, kana kula da ci da sha na, suttura da lafiyata daidai karfinka. Ko da samun ka ya ragu ba ka gaza da ni ba ta kowanne fanni. Na sani ba ka son a zauna kusa da kai, amma ko a fuska ba ka taba nuna min hakan ba duk da na sani. Zan koma cikin iyaye da dangi, ina rokonka in na bata maka a tsayin zamanmu ka yafe mini�.
Ta kai gefen mayafinta tana share idon ta, “Ka rike Aalimah da mutunci da amana, don Allah Mu’azzam ko don alfarmar mahaifinta…�.
Sauraron Mummy yake yi attentively har ta yi shiru. Kafin ya ce,
“Ni Mummy zamanki bai takura ni ba, ni da ba zaman gidan nake ba? Ku ci gaba da zamanku har Allah ya huci zuciyar Daddy ya maida ke dakinki�.
Girgiza kai ta yi, “Gara in tafi Mu’az, ya dau zafi da yawa, tafiyar tawa ce kadai za ta sa ya sauko har yayi tunanin maida ni dakin nawa. Na dinga zuwa muku ziyara insha Allah lokaci zuwa lokaci. Kayi min alfarmar bazaka sake yin dare irin wannan a waje ba. Saduwar alkhairi don tashin asuba za mu yi. Je ka turo min Aalimah�.
Ya yi dan jimm! Kamar bai ji abin da ta ce ba. Tana da tabbacin ya ji din, duk da haka ta sake maimaitawa,
“Je ka turo min Aalimah mu yi sallama�.
Kamar ya ce, “Ba ga Yesmin nan ba?�
Ya tuna cewa, sallama yake yi da mahaifiyar tasa, gara ya yi mata duk abin da ta ke so su rabu lafiya, don haka ya mike ya nufi kafar benen cikin takunsa kamar na saraki. Zuciyarsa na tsukewa da wannan umarni na mahaifiyarsa, wanda babu yadda zai yi da shi ta ko’ina, domin kamar da gayya ta yi shi, don ta sa su ga juna shi da Aalimahr da yake gudarwa kwana da kwanaki.
Kayan barci ne a jikinta masu sulbi ruwan shanshanbale. Kanta cikin hular sanyi fara sol wadda ba ta rufe ko rabin gashin kanta ba. Ta hadashi ta nannade kamar gammo a tsakiyar kanta, ta rufe rabin jikinta da bargo mai tsananin laushi da santsi. Barci ta ke sadidan a lokacin da Mu’azzam ya murda kofar, bakinsa dauke da sallama kamar ta rowa. Ba ta amsa ba, don haka ya idasa shigowa dakin yana mai cije lebensa na kasa. Kamshin wani sassanyan turaren wuta dana mata ya bugi hancin sa. Saida ya tsaya ya shaqa sosai yayi ajiyar zuciya. Da alama mai nauyin barci ce, ya lura in zai kwana yana sallama ba za ta ji shi ba. Karasawa ya yi har gaban ta ya dan janye bargon kadan daga jikinta.
Maimakon ya tashe ta, sai ya tsaya kawai yana kallonta. Bai taba yi mata wani kyakkyawan kallo ba sai yau. Mace har mace, wadda ko cikin abzinawa sai an tona, mai tarin nutsuwa, kamala, kunya, kawaici da ilmi. Yana iya tuno kyakkyawar rayuwar da ta yi da mijinta abin kaunarsa Aboulkhair. Don me iyayensu suka yi wannan bahagon hadin?
Aalimah na matukar ganin girmansa, shi ma haka, yana bata respect har guda biyu; na kasancewarta matar kaninsa da yake matukar so, da kuma wanda halayenta ababen yabo suka sayo mata a idanunsa. Bai shirya wannan zubar da kimar ba (rayuwar aure da ita) daga nan har zuwa inda Allah ya nufa da rayuwar kowannensu.
Aalimah ta yi wani dan juyi cike da jin dadin barcinta jin sanyi na shigarta tun daga tafin kafa, sakamakon dan janye bargon da Mu’azzam yayi daga jikin ta. Jikinta ne ya ba ta akwai mutum tsaye a kanta. Da sauri ta bude ido, wadanda suka kada suka yi jajir sabida nauyin barci, sai suka rikide suka bada wani irin yanayi mai motsa zuciya, bata yi aune ba sai samun idanun ta tayi kane-kane cikin na Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee, wanda ke tsaye saitin kanta ya zuba mata ido. Da mugun sauri ta yayibi zanin gadon ta rufe jikinta gaba daya. Juyawa ya yi yana mai sakin tsaki ya bar dakin yana mai ce da ita da murya ciki-ciki,
“Ki zo Mummy na kiranki a kasa�.
Dakinsa ya karasa cikin takunsa na nutsuwa da kasaita, lokar jikin gadonsa ya bude. Lokacin shan maganin sa har ya wuce yana can yana yawo a titi duk don kar ya hadu da Aalimah, gashi ya tashi a banza tunda Mummy sai da ta san yadda tayi ta hada su. Magunguna ne ga su nan birjik! Wadanda aka rubuta mood stabilizers su ya cira ya dauko gorar ruwa cikin karamin firjin da ke gefen gadonsa, ya watsa su cikin bakinsa, ya bi su da ruwa. A hankali ya kwanta bisa gadonsa yana maida numfashi a sannu. Saukowar da bai kara yi ba kenan sai asubahin wayewar gari. Shi da kansa ya tuka Mummy zuwa airport bai hada ta da Harrison ba.
Har da Aalimah aka tafi kai Mummy airport, don haka a hanyarsu ta dawowa daga shi sai Aalimah cikin motar an rasa mai yin ko motsin kirki a tsakaninsu. Aalimah ko numfashi za ta fitar sai ta tabbatar ta sake shi a hankali, yadda ba zai zama takura ga Mu’azzam ba. Ta san halinsa sarai, ba yau ta sanshi ba.
Suna isowa gida ta bude motar a hankali ta fita, haka nan a hankali ta rufe ta silently. Ta juya cikin takun nutsuwa ta shige cikin gida, ko kofa za ta bude a hankali ta ke yi, don sanin cewa Mu’azzam ya biyo bayanta.
******
Tafiyar su Mummy sai ya mayarwa da Aalimah gidan kamar maqabarta. Har zuwa washegarin ranar bata kara sanya Mu’azzam a idanunta ba. Ko motsinsa bata ji ba duk da cewa dakunansu na daura dana juna. A washegari Mu’azzam sammako yayi ya fice office ko karyawa bai yi ba, tana iya jiyo fitar motarsa daga gidan. Tana daga kwance a gadonta tayi ajiyar zuciya. A lokacin zuciyarta tayi zurfi cikin tunani mai dimbin yawa. Shikenan rayuwarta da Aboulkhair ta zama tarihi? Mu’azzam ne zai maye duk wani gurbi da Aboulkhair ke kai a baya? Ta yaya hakan zai kasance?
Bata taba yiwa Mu’azzam wani kallo bayan na Yayan su ba, ko ta ce Yayan mijinta. Rayuwar shi da tata ba iri daya bace; ratar dake a tsakani mai tsananin fadi da girma ce. Ga matsalar da yake ciki wadda bata san ranar warkewar ta ba. Saidai tana da tabbacin aggressiveness dinsa bazai shafe ta da komai ba. Zata iya yin nisa da shi a duk lokacin da taga alamun yana kokarin shiga cikin sa. Tunda Aboulkhair ya gaya mata yadda yake. Wanda ana daukan shekaru ma hakan bai faru ba. To amma babbar lalurar fa?
Aalimah ta nisa, ta aje gwauron numfashi.
Ko lokacin da take tare da Aboulkhair ita ba mai son yawan auratayya bace, wancan ma kenan da ya kasance soyayya ce mai tsanani a tsakani balle wannan da ya zamo hadin iyaye, ba da son ran ko dayansu ba.
Tana matukar ganin girman Mu’azzam da ganin kimar sa cikin idanunta, bata fatan zuwan ranar da zama irin na auratayya zai kasance tsakanin su. Koma dai yaya ne, tasa a ranta zaman iyayensu zata yi a gidan nan ba zaman Mu’azzam ba, wanda take da tabbacin shima ba son auren yake yi ba koda ace bai bude baki ya furta ba. Alamu duk sun gama bayyana kansu.
Data gaji da tunanin wanda ta amince bazai kawo mata mafita ba cikin tarin kalubalen dake gabanta, sai ta tattara komai ta mikawa Ubangiji. Ta tashi ta dauro alwala ta shiga gabatar da nafilfili.
Lokacin gari yayi haske, ta yunkura ta mike daga kwanciyar bayan ta ture bargon rufarta. Kai tsaye toilet ta fada tayi wanka tayi brushing bakinta ta dauro towell ta fito. Ta bude closet dinta ta soma ruwan idon kayan sanyawa. Ba Mu’azzam take da niyyar yiwa kwalliya ba kawai ta samu kanta yau cikin sukunin zuciya irin wanda bata taba samu ba tun rasuwar Aboulkhair. Lallai ne da ake ce aure rahma ne, kuma gidan miji ‘yanci ne ga diya mace koda wane iri ne kuwa.
Ruwan idonta ya tsaya akan wata doguwar riga ‘dark blue’ wadda nauyin duwatsun jikinta yafi yadin rigar nauyi, ta cirota ta zura a jikinta sannan ta zauna kan stool gaban dressing mirrow tana gyara dogon sassalkan gashin kanta wanda saida dabara take iya tazarsa.
Wayarta dake kan bed-side tayi kara da kiran sallah wanda shine ringing tone dinta. Mikewa tayi ta isa ga wayar ta dauka. Ganin sunan mai kiran sai ta zauna a gefen gadonta cike da farinciki tana amsawa.
Mama ce.
Bayan sun gaisa cike da shauki irin na Da da mahaifi ta tambayi lafiyar kowa na gida, Mama ta tabbatar mata kowa lafiya, ashe Daddy na kusa, don Mama mikawa Daddy wayar tayi tace shi ke son magana da ita. Aalimah ta gaisheshi shi kuma ya dinga zuba mata albarka akan biyayyar data yi masa, ko daga sautin muryarta ya fahimci ta kwantar da hankalinta yanzu ta kuma rungumi kaddararta da hannu bibbiyu.
Dr. Mansur yace “Aalimah kinsan dai ni na haifeki ko?� Ta gyada kai cikin tabbatarwa kamar yana ganin ta. Yace “to ki yarda bazan taba yin abinda zai cutar da ke ba. Kada rashin lafiyar Mu’azzam yasa kiyi tunanin don bazai samu matar aure bane yasa muka aurar dake gareshi, ko kadan, Ko ‘yar wa Mu’azzam yake so a fadin kasar Nijar zai aura mun dai ga bashi da niyya ne. Bari in gaya miki wani abu wanda ko uban Mu’azzam da ya haifeshi bai sani ba.
Rana ta karshe dana gana da Aboulkhair a dakina, munyi maganganu masu yawa akan Mu’azzam, kin san dai fannin rashin lafiyar Mu’azzam ya karanta har matakin consultant, kuma yake kan cigaba da zurfafa ilmi akai a jami’ar Johns Hopkins, ya gaya min bincike na karshe da suke kan yi of recent research ya nuna Mu’azzam zai iya warkewa gabadaya, zai koma normal sexual life bayan shekaru kamar goma in dai an kula da bashi treatment. Ya gaya min yana so ya gayawa Mu’azzam amma ya fasa don kada yace sai ya warke zai yi aure, amma ko likitansa Nebrass yasan Mu’azzam zai iya warkewa daga yanzu zuwa kowanne lokaci in aka kidaya yawan shekarun da ya kwashe cikin lalurar karkashin kyakkyawar kulawa kuma zai iya rayuwar aure yanzu haka (under treatment).
Shine dai yake tsaurarawa kansa damuwa da ganin cewa rayuwar sa ta gama amfani. Amma babu cutar da Allah ya saukar a duniya ba tare da ya saukar da ita tare da maganin ta ba. Ki yi tawakkali ki tattara komai ki barwa Allah. Kiyi addu’a kan Allah ya hada kanku da kuma zukatanku wuri guda, ki zubawa sarautarsa ido.
Ni Mansur Sarhamu Raazee na tabbatar miki sai kinyi alfahari da wannan auren watarana kuma sai kin zo kin gode mini. Soyayyata gareki ce tasa nayi miki wannan zabin. Zabin da duk cikin family din RAAZEE babu mai kamar naki. Ki kwantar da hankalinki a gidanki kinji Aalimah? Ki kuma yi hakuri da halin Mu’azzam mutum ne mai wuyar sha’ani. A matsayin ki na mace, zaki iya canza shi zuwa duk irin yadda kikeso ya koma. Mu’azzam is a nice person kuma idan kinyi hakuri zaki ci riba watarana�.
Aalimah hawaye take yi tana sharewa da bayan hannunta. Ta san Daddy na sonta amma zata iya bayar da shaidar son da yake yiwa Mu’azzam ya nunka nata sau goma. Zuciyarta na mai amanna da kowacce kalma dake fita daga bakinsa.
Cikin rishin kuka Aalimah take fadin.
“Don Allah Daddy ka yafe mun gardamar dana yi maka a baya. Na rasa nutsuwa ta ne a lokacin. Ba kiyayya nake yiwa Mu’azzam ba, sannan ba rashin lafiyar sa ke damuna ba, ina dai duba kusancinsa da Aboulkhair ne. Amma daga yau na yi maka alkawarin cire komai daga raina insha Allahu, na yarda haka Allah ya rubuto mana bakidayan mu. Na san aure a tsakaninmu halastacce ne. Na yarda da duk abinda ka fada, ko Mu’azzam ba zai warke ba zan zauna dashi insha Allahu har karshen rayuwata. Ka taya ni addu’a Allah yasa nima ya so ni irin yadda Aboulkhair ke so na......!�.
Sai kukan ya kwace mata bakidaya.
7/9/21, 7:20 PM - Buhainat: Aalimah
Dan guntun scene din da ya faru a dakin Mu’azzam ta ke ta tunawa da ta koma nata dakin, wani ta yi murmushi, wani ta yi ajiyar zuciya. Ta kai gwauro ta kai mari a tsakiyar dakinta, tana mai naushin hannunta cikin tafin hannunta. Aalimah, ta samu kanta da son yin kyakkyawan bincike na ilmi bayan wanda Aboulkhair ya gaya mata a kan lalurar maigidanta Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee. Ta hakan ne zata san irin matakin da zata dauka akan zaman su da yadda zata bullowa rayuwar auren su, tunda kuwa abu ne wanda ba su da damar gujewa dukkanninsu. Auren su is inevitable. Don haka maganar wahalar da zukatansu ba shine mafita ba, mafitar itace ta nemi hanyoyin da zasu dorar da zaman nasu. Ciki kuwa har sai ta fahimci lalurorin sa bakidaya a ilmance, a likitance, a rubuce, a mu’amalance sannan in theory and practice.
Ta fara da shiga manhajar google inda ta binciki cikakken bayani a kan what the problem is all about? Sannan ta ke shiga library din Mu’azzam idan ya fita office, tana masa bincike, yana da manyan littattafai da suka shafi compulsive sexual disorder. Cikin manyan littattafan da ta debo daga library dinsa zuwa dakinta akwai ‘A Psychometric Investigation of the Hypersexual Disorder Screening Inventory’ (By J. Engel. 2019). ‘The Danger of Hypersexual Disorder’ (Dr. Martin Kafka), sai kuma ‘Compulsive Sexual Behaviour’ (A Review of the Literature) NCBI (By KL Derbyshire, 2015).
In takaice miki Aalimah sai da ta zama kamar wata ‘yar karamar Farfesa (Professor) a kan lalurar Mu’azzam sabida karatu da bincike, inda ta fahinci komai ta gane kan komai, ba tare da Mu’azzam din ya san tana yi ba.
Abu na gaba da ta ke son yi shi ne, ganawa da Dr. Nebrass Sheldon, ta kuma rasa hanyar yin hakan, tunda ba ta ganshi yana zuwa gidan su ba, ba ta kuma san a ina suke haduwa ba shi da Mu’azzam din. A lokacin da ta fahimci behaviour din, sai ta ga ba maraba da yadda Aboulkhair ya labarta mata. Ta dai samu faffadan bayani ne da cikakken ilmi akan lalurar.
Aalimah ta manta da wani abu wai shi ‘AURE’ dake tsakaninta da Mu’azzam, sai motive na ‘yan uwantaka. Sosai ta ke jin son ta tallafi rayuwar shi a haka, a hakan da yake da wannan lalurar, yadda Halima ta kasa. Ta ke ji a ranta cikin kowanne hali, za ta iya jimirin zama da Mu’azzam sabida biyayyar iyaye da kauna ta jini.
Ba abin da Uncle Ishaq bai yi mata a rayuwa ba! Ta tuno dauki ba dadin da ya dinga yi da matarsa a kanta. Ranar da ya gane Mummy ta hanata zuwa makaranta har na tsawon sati biyu ta maida ita boyi-boyin gidanta. In bata manta ba a ranar har hawaye yayi a kanta. Ya rungumeta a jikinsa kamar shi ya haife ta ya bata hakuri kamar zai ciro zuciyar sa ya bata don tayi hakuri ta cigaba da zama da su. Ya yi mata komai a rayuwa daga zamanta a gidansa har zuwa yau data auri Mu’azzam. Da yardar Allah jininsa bazai tozarta a hannunta ba.
Ta ji tana son shiga cikin rayuwar Mu’azzam ta kowanne bangare, ta fahimce shi yadda Aboulkhair ya fahimce shi, ta taimaka wa lafiyarsa yadda Aboulkhair ke taimakawa, ta kawo murmushi akan fatar bakinsa, ta kawo sauyin rayuwa mai tattare da nishadi. Duk da ba ta da shaidar ilimin da ya danganci wannan lalurar a yanzu, tana da fahimta a kai daidai gwargwado. Tana so ta shiga rayuwarsa ta ko ina yadda Aboulkhair ya shiga. Ta taimaka ta ko’ina, yadda Aboulkhair ke taimakawa. Har ake ganin murmushi a fatar bakinsa idan har suna tare, tana yiwa kanta kwadayin samun irin wannan matsayin a wurin Mu’azzam idan har zata samu dama! Tana rokon Allah Ubangiji ya dafa mata, ya agaza mata a bisa wannan niyya tata ta alkhairi akan mijinta.
******
Misalin karfe biyar na yamma Mu’azzam ya dawo office. Bai tsaya a ko’ina ba, kai tsaye cikin yanayin tafiyarsa mai kama data jinin sarauta ya soma taka matattakala ya haye upstairs don isa ga dakin barcinsa.
Bai dade da shiga ba ya ji Aalimah tana kwankwasawa. Wani abu da ba ta cika yi ba a tsayin watannin da suka kwashe tare, wato shigo masa daki in ba da kwakkwaran dalili ba, sai dai ta girka masa delicious ya ci ya more, in ba ta da lafiya ya kan kai ta asibiti, wanda sau biyu ne ma kawai tayi ciwon mara, ta fada masa abubuwan da ta ke bukata na cefane ya sa Harrison ya kawo mata. Ya lura bata komai yanzu sai karatu a library wanda bai san na menene ba. Ta dauki hankalinta da lokacinta kacokam ta mallakawa library, ko dakinta ya shiga zai ganta da glass tana karatu a ipad dinta, abinda ke gudana a tsakaninsu kenan a tsayin watannin su masu dan dama tare.
A tunaninsa tun wancan zuwan nata dakinsa da ya gaya mata maganar da ba ta taba zato ba, sanda tace ya maida ta makaranta ko aikin ta na pharmacy ba ta kara gigin zuwa dakin shi ba, don ta fahimci kamar ya gama karbar auren nasu, tana kuma tsoron abinda zai biyo bayan hakan, don haka tun daga lokacin ta janye jiki ta koma rufe jikinta a cikin hijabi yayin zirga-zirgar ta a gabansa, a falo ne ko a madafi. Duk wannan kwalliyar da ake cancadawa an daina. A wurin sa hakan ba karamin taimako ya zamo a gare shi ba, sabida ganin da yake yawan yi mata da dan kusancin da ya soma ginuwa a tsakaninsu ya soma birkita shi, ya gaya wa Nebrass yana so ya kara dose din magungunansa, kamar fa sun daina aiki a jikinsa kwanakin nan, don ya gaya masa yana kasa barci a yawancin lokuta da tunanin matar sa kuma ba ya son ya rabe ta. He is afraid of his new mood and the consequences.
Sun zauna sun yi magana heart-to-heart shi da likitocinsa, sun tabbatar masa zai iya rayuwar aure fa ya daina zancen a kara dose, amma ba lallai matar ta samu yadda ta ke so daga gare shi ba muddin yana cigaba da shan anti-androgens kamar yadda ya saba, bi ma’ana, ba lallai ya gamsar da ita a shimfida ba sabida karfin magungunan da suke bashi. Wadanda aikinsu shine kashe tasirin sex hormones a cikin jikinsa. Idan kuma aka dauke shansu shi ma matsala ne babba ga lafiyarsa, career dinsa da zaman lafiyarsa, don al’amarin zai zamo out of control. He will need nothing but sex. Mu’azzam ya gaya musu ya zabi ya zauna da ‘yar uwarsa a haka, cikin zabin da suka bayar duka babu mai sauki, babu wanda za’a ce gara shi. Tun dai ita ba ta nuna kosawa da zaman nasu a haka ba. Kuma da ma ba soyayya ce tsakaninsu ba.
Yana da tabbacin ta san lalurarsa, duk da ba su taba yin zance makamancin wannan da ita ba. Amma ai ta zauna da ABOULKHAIR.
Shi ya lura ma yanzu hankalinta ba ya kansa. Yana ga karance -karancen ta da rubuce-rubucen ta kamar mai rubutun thesis. A ganinsa zata fi kyau da zama malamar makaranta ba mai harhada magunguna ba.
To sai kuma yau da ya ji ta tana kwankwasa kofar sa. Bayan shigarsa dakin da mintuna biyu, ko zama bai kai ga yi ba, don haka daga inda yake tsaye ya bude kofar. Aalimah rike da zazzafan coffee cikin kofi mai zurfi ta dora akan karamin faranti na tangaran ta mika masa. Karba ya yi ya koma cikin lallausar kujerar dakin kwaya daya tal ya zauna. Itama ta zauna a gefensa dab da shi. A zuciyarsa gode mata yake yi sau ba adadi. Ta yi matukar sanin abin da yake bukata ta fannin ci da sha. Ta kuma san abin da ya kamata ta bai wa mutum ya ci ko ya sha a yanayi da lokacin da ya dace.
Ko da ya zauna coffee din ya hau sipping duk da zafinsa ba tare da ya cire takalman kafafunsa ba.
A yadda Aalimah ta sa a ranta daga yau ne za ta canza akalar rayuwar ta da Mu’azzam tunda ta gama research dinta. Ta gaji da wannan rayuwar da suke yi mara focus. Hijabi ne a jikinta dogo daga sama har kasa. Hannu tasa ta cire shi gabadaya ta ajiye a hannun kujerar da suke zaune. Saukowa ta yi ta gurfana a gabansa, ta debi kafafunsa ta hau cire masa takalman, ta gama ta hau zare masa safa (socks) ta debe su ta kai shoe rack, wato ma’adanar takalmansa. Ta jefa safar cikin kwandon kayan wanki.
Har ransa ya ji dadin wannan taimako data yi masa amma ko akan fuskarsa bazaka gane ba. Ba ta tsaya a nan ba, toilet dinsa ta wuce kai tsaye ta hada masa ruwan wanka mai dumi daidai da yanayin da garin ke ciki. Ta zuba turaren wankansa na desire dunhill ta aje masa towell a kusa, sannan ta fito.
A inda ta barshi ta same shi ko motsi bai yi ba yana mamakin ta da karfin halinta. Tunda yake a rayuwarshi ba wanda ya taba shigar mishi toilet including Aboulkhair. Tana fitowa tsugunnawa ta yi a gabansa hannunta akan kafafunsa cikin sanyin murya da kaskantar da kai ta ce,
“Yaya Mu’azzam na hada maka ruwan wanka�.
Cikin idanunta ya dube ta yana dan zaro ido na mamakin wannan canji da yake ta gani yau a tare da ita, bai ga komai ba cikin idanun ta sai tsantsar kulawa gare shi. Ko da ya mike don rage kayan jikin sa sai ta fita. Duk karfin halin ta da kankanbar ta ta kasa tsayawa. Murmushi yayi shi kadai sannan ya sunce ya shiga. Kafin ya fito daga wankan ya yi sallah, ta hada lafiyayyen lunch ta kawo masa.
Ta sanshi da son lemon Sangria Mocktail, ta san shi ne abin da ya tare ta da shi a zuwanta na farko gidansa tare da Aboulkhair. Bazata taba maanar ba. Ranar da ta fara ganin c a rayuwarta. Don haka tun safe ta duba procedure din yadda ake yi a yanar gizo, ta zage ta hada masa shi da kyau da ban sha’awa.
Sanda ya fito tawul ne mai fadi daure a jikinsa iya kugunsa, da wani a hannun sa yana goge jiki da shi, sosai ta sadda kai kasa kamar tace kasar ta tsage ta shige, ba ta iya ta dago ba ko yin wani kwakkwaran motsi har ya hangota ta mudubi ya ga halin takurar data ke ciki, da sauri ya lalubo kayan da zai sa ya saka. T. Shirt ce ruwan goro (Tommy Hilfiger) da shudin wandon chinose. Yana satar kallonta ta karshen idanunsa ita ma tana satar kallonshi. Bata da niyyar barin dakin, tayi zamanta a gefen gadonsa sai kace dakin ta. Yau yarinyar nan tana son shigar masa hanci da yawa, har kaya yasa a gabanta amma bata fita ba. Wanda bai ga dalili ba.
“I want to be alone, please�. Ya fada yana mai zama a gefen gadonsa.
Ko ta ji haushin kalamansa to ta shanye ba ta nuna ba, ta ce, “Abincinka zai yi sanyi�.
Bai yi musu ba wannan karon, don sosai yake jin yunwa, ya sauka kan karamin rug-carpet, dake gaban gadonsa, ya janyo tray din da ta aje ya soma cin abincin. Da ya kammala ya cika tambulan da lemon Sangria Mocktail yana dubanta da mamaki. Exactly wanda yake hadawa da kansa, ta kashe shi da murmushi, kafin ta ce “nayi kokari ko Yaya Mu’azzam?�
Shi kuma ya amsa da sauri, “Yes, and I appreciate, you really tried!�.
Murmushi ta yi, tana kallonsa yana shan lemon, komai da yake yi gently yana matukar burgeta.
7/9/21, 7:20 PM - Buhainat: Aboulkhair ya ce......... “He cannot develop emotion…�. Ita kuma so ta ke ta koya masa jin emotion ko ta halin kaka. Ya ji ta a ransa ko da bazai mata so irin na soyayya ba. Ba don tana jin soyayyarsa mai yawa a ranta ba, sai don tana so ta canza musu tsarin rayuwa, tayi enhancing yanayin rayuwar sa gabadaya. Ta kawo sauyi a cikin rayuwar sa ko yaya ne.
Yana gama cin abincin ta kwashe komai ta kai kitchen ta dawo, samunsa ta yi ya bude system dinsa ya kwanta rigingine tsakiyar gadonsa da system din a kan ruwan cikinsa. Cikin kokawa da abin da zuciyarta ke umartarta ta saci kallonsa. Ba abin da zai bukata a yanzu sai mutstsikar kafa da jan yatsu don warware gajiya. Wani bangare na zuciyarta na hana ta, wani na angiza ta. Idan ta biyewa Mu’azzam zasu shekara goma cikin mugun zaman da suke yi. Ita kuma ta gaji, don ita ke cutuwa, tana so ta kawo karshen komai. Idan bazai yi zaman aure da ita irin na sauran mutane ba, gara ya maida ita gaban iyayenta.
Daga lokacin da ta taso zuwa sanda ta zauna daga saitin kafafun sa Mu’azzam bai ankara ba. Sai kamshin jikinta da ya riga ya haddace mai birkita masa lissafi daya bakunci kofofin hancinsa na turaren NUDE by Rihanna.
Tafin kafarsa ya gani cikin hannayenta akan cinyoyinta tana tausarsu tana mutstsikarsu a hankali daya bayan daya cikin nutsuwa kamar wadda ta yi mastering a Physiotheraphy bayan ta zauna a gefen kafafun nasa.
Yana so ya hana ta, yana so ya dakatar da ita, amma pleasure din da yake samu daga hakan unabandonable ne. Kuma bai taba tsintar kansa a kwatankwacinsa ba. Aikin da yake yi mai muhimmanci ne amma sai ya kasa gane me yake yi. Aalimah ta ci gaba da yin abin da ta ke yin ba tare da tunanin komai a ranta ba, sai kawai ta ji muryar Mu’azzam ta soma canzawa har bata fahimtar abinda yake fadi sosai, a lokacin da yake rokonta da ta bari. “....Stop it Aalimah..... please stop it......!�. Ya taso ya zauna ya jefar da system din gefe, kama hannuwanta biyu yayi ya rirrike jikinsa yana wani irin kyarma. In ita ta shirya wa hakan a tsakaninsu shi bai shirya ba, har gobe a matar ABOULKHAIR yake kallonta.
Ta ce, “Yaya Mu’azzam, nifa tausa kawai nake maka don na ga ka gaji ba da wata manufa ba, sai ka barni ni kadai a daki alhalin bani da abin yi. Akalla mu dinga hira ni da kai, mu abokanci juna ko ya ya ne, mu dinga jin damuwar junanmu, mu debe wa juna kewar iyaye da ‘yan uwa tunda ba mu da kowa a nan sai junanmu.
In kai kana da aiki a system din da za ta taya ka hira, ni ba ni da shi. I just want us to be friends, abin da ka ke tunanin ina bukata ba shi ba ne Yaya Mu’azzam, na dade da cire wannan section din daga gangar jikina tun ranar da na rasa Aboulkhair, ban kara tunawa ni mace ba ce, balle in yi tunanin neman wani abu daga gareka�.
Wai kuma sai ya ji kamar kalamanta sun masa tsauri da yawa. Kamar ta dan zuba masa ruwan zafi….. Ta zo gabansa tana fadin tun ranar data rasa mijin ta kaza-kaza.......tsaki ya ja mai sauti. Da kyar ya fizgo sauti daga makogaronsa. Ya ce.
“Did I ask you how you are feeling when lost your husband?� Ta wani murguda baki ta juyo masa keya, yana hango lallusar gashin baki sidik data kalmashe a cikin bind. “Toh, Na ga ka yi min wata fassara ne daga yi maka tausa�. Murmushi yayi cikin takaici. “Friendship ki ke so?� Ya sake tambayar ta. Bayan ya kauda idonsa da sauri.
Ta ce, “Eh�.
Ya ce, “To na amince miki ki shiga makwabta ki cigita ki nemi sa’anninki watakila za ki dace da samun abokin�.
Rausayar da kai ta yi abin tausayi.
“Yaya Mu’azzam ka manta a inda muke ne? Ai ba ruwan kowa da kowa, ta yaya zan shiga gidan mutanen da basu sanni ba ban sansu ba, ba addini da yaren mu daya ba?�.
A dan harzuke ya ce, “Na ji, zan miki komai ki ke so, but don’t touch me like this again, please�.
Ta ce, “ba wani abu ne mai yawa nake so ba, hira nake so mu dinga yi tare, zuwa yawon cikin gari ni da kai da daddare, beaches, shopping malls da kasuwanni duk mu dinga zuwa tare a duk lokacin da zanyi cefane ko sayayya, ka kuma daina bani sako ta hannun Harrison ba na so, ka bani da kanka ba muharramina bane, duk wani sako tsakanina da shi daga yau ka yanke shi, zan kuma din ga shigowa dakin nan duk sanda na ga dama..…Na daina tsayawa a bakin kofa ina neman izni kamar wata almajira…..�.
Da sauri ya katseta,
“….Ban yarda da wannan ba. Ki shigo min daki duk sanda kika ga dama in kuma ba a shirye nake ba fa. You are just creating a problem, ….you and your problems…�.
Dariya ya bata sosai, da ganin fuskarsa ka san ta hada masa zafi. Ta hadiye dariyar ta ta ce “ba su kenan ba ai issues din nawa, sai kuma hada maka ruwan wanka kullum da aje maka towel, sai kuma zabo maka kayan da zaka dinga sanyawa, I also want be choosing neck ties for you. Tied it by your neck…. That’s all I want from you�.
Ajiyar zuciya ya yi, ya kura mata ido kamar ya maketa, me yarinyar nan ta ke so ta zama ne? Ya tambayi kansa.
“Close to your life�.
Abin da ta ke nufi kadai kenan, zuciyarshi ta bashi amsa, shi kuma wannan wani gurbi ne da ba zai iya bai wa kowa ba. Intimacy din zai yi yawa. Aalimar da ya sani da kunya da kawaici a lokacin Aboulkhair, wadda ko ido bata iya hadawa da shi, yau rana daya ta zo masa da wasu bakin halaye tamkar mai multi personality disorder! Ba ya tantama zama da matar Daddy ne ya maida ita haka. Tunda bata da kawar data fi ta.
“Ki yiwa Allah ki kyaleni Aalimah, kin ga inada ayyuka da yawa, in dai system ce zan saya maki gobe ki dinga yin karatu da ita insha Allahu�.
Turo baki tayi kamar kankanuwar yarinya “Yaya Mu’azzam ni ban ce ka saya min computer ba, inada ipad. I mean nothing, I only need a friend in you. Tunda an rabo ni da kowa nawa an kawo ni nan, inda ba ni da kowa sai kai�.
Ta soma jan hanci alamun kuka zata soma daga kowanne lokaci daga yanzu.
Mu’azzam ya shafo sumar kansa cikin damuwa, da sauri ya ce, “to shikenan na yarda, amma kar ki sake taba ni, don Allah�.
Aalimah ta sake cuno baki, ta mike tana kunkuni har da bubbuga kafa a kasa.
“Ai Allah bai ce kada in taba ka ba!�.
Abin ya ba shi dariya a karo na farko, amma ya gintse.
“To kuwa kada ki sake shigo min daki in ba ni na neme ki ba. Abincin a bar min a dining in na bukata zan zo da kaina in ci�.
Juyowa tayi cikin far’a mai yawa tace masa.
“Nan fa daya! Mun riga mun wuce wurin nan, ka riga ka amsa. I will be in my husband’s bedroom whenever I wish. Magana biyu ba taka bace Yaya Mu’azzam�.
Girgiza kai yayi ya bita da ido a sanda ta kama hanyar ficewa.
Har ta kai bakin kofa ta juyo ta marairaice. “To don Allah in zo ka kai ni shopping? Wallahi ko man shafawa ba ni da shi, ni ko kayan lefe babu wanda ya yi min just because an fi son ka a kaina�.
Bai san sanda ya ce “Je ki ki shirya� ba.
Har da dan tsallenta ta fice kamar wata kankanuwar yarinya.
Mu’azzam ya dafe kansa dake sarawa saboda rigimar Aalimah, ya dade bai yi magana mai tsayi irin wannan ba, ta sa shi magana mai yawa. Ita a dole sai ta koyar da shi sakin jiki da ita. Bayan da farko ta nuna masa ba ta da hayaniya, ashe shigo-shigo ba zurfi ta yi masa? Murmushi ya yi tare da lumshe idanunsa. Ashe hayaniyar ga wanda ya iya ta nishadi take sanyawa? Kwarai ya samu kansa cikin nishadi wanda rabonsa da irinsa har ya manta. Ya koma ya jingina da jikin gadonsa, yana mai hasashen inda karshen wannan tafiya za ta kai su???.
Suna tafe cikin motar Mu’azzam (Acura) fara sol, Mu’azzam ne ke tukin motar. Tunda suka taho kira’ar Sheikh Abdurrahman Sudaith ke tashi a motar cikin (Suratul Ali’Imran). A fili Mu’azzam ke bin karatun wanda ya sanya wa Aalima nutsuwa sosai. Ta nutsu, ta kwantar da kanta a masangalin kujerar da ta ke zaune tana sauraronsa. Ba ta yi mamakin iya karatun Mu’azzam ba, kasancewar Aboulkhair ya gaya mata komai na rayuwarsa har a Madinah.
Shagon da yake nasa shopping din ya kai ta, ya ce ta je ta yi siyayyarta zai jira ta a mota, idan ta gama ta yi masa flashing ya je ya biya su tafi. Ta fahimci abin da yake nufi (ba zai jera da ita ba) to ita kuturwa ce ko ko me yake nufi? Duk da haka ta gode, domin sauyuka ne da ba ta tsammata a nan kusa ba daga gare shi.
Ta shige cikin shagon kai tsaye wajen kayan kwalliya ta dosa. A sannu za ta canza komai da yardar Allah. Ashe dai duk laifinta ne wannan mugun zaman da suka shekara cikin sa. Mu’azzam yana da saukin kai matuka idan kayi hakuri da shi kuma a sannu zaka fahimce shi. Yadda ka bayyana kanka da haka yake biyar da kai. Tana rokon Allah ya ba ta kwarin gwiwar mayar da Mu’azzam ma’abocin walwala da farin ciki kamar sauran mutane koda ba entirely ba.
Mu’azzam bai san me Aalimah ta sayo ba, sai da suka dawo gida, ta ware nata siyayyar a dakinta ta dauki wata katuwar leda ta bi shi da ita. Yana kokarin canza kayan jikinsa zuwa pajamas ta yi sallama tare da tura kofar ta shiga gaba-gadi tana mai kawar da kai daga gare shi ba tare da ta bari yayi mata iznin shiga ba. Tsaki ya yi mai sauti ya juya mata baya, ya ci gaba da zarga igiyar pajamas dinshi. Yarinyar nan tana son shiga rayuwarsa da yawa, abinda ba zai dauka ba. A dan fusace ya juyo yana kallonta, ta ce shopping ya kai ta, an dawo kuma ba za ta barshi ya huta ba? He want to be alone ko ya samu ya sha maganinsa ya kwanta.
“Oh please Aalimah mene ne kuma?�
Ya tambaya, rabi a fusace, rabi cikin boye fushi.
Zama ta yi gefen gadonsa ta soma fiddo kayan da ke cikin ledar, shampoo ne na maza (Arganavita), shavers da after shaves kala-kala turaren wanka (bath robbs), handkerchiefs, vest, boxers da duk wasu tarkace na maza irin wadanda ta ga yana amfani da su. Ta marairaice tare da karyar da kai, ta ce,
“Da ma sayo maka na yi�.
“Na ce ina bukata?�
Ta yi kasa da murya,
“Don na san kana bukatar ne�.
Ta tattara su ta yi toilet din shi da su. Bin bayanta ya yi da kallo, ko’ina a jikinta rausaya yake kamar mai yi da gangan. Bai dauke idonsa ba sai da ta kule cikin toilet din. Ya yi ajiyar zuciya ya bar kallonta. Bai san me ta ke so da shi ba kuma, duk abinda take so yayi mata, amma bazata barshi ya huta ba, ta fara takura masa. Ba ya son damu, gara zaman su Mummy sau dubu da wannan Aalimar ta yau, ba sa gigin shigar masa daki. Amma Aalimah… Aalimah… ta fara shigar masa hanci, in ta yi wasa zai bar mata gidan gaba daya.
Cikin kwanaki bakwai da suka biyo baya Aalimah tayi nasara mai yawa akan Mu’azzam, ko baya son magana sai ta bashi dramar da zai yi dariya. Ta like masa ta nace masa kamar kaska. In zai tafi ofis sai ta bata masa lokaci. Har stool din mudubin dakinta ta dauka ta mayar nasa dakin saboda ta taka ta kamo tsahon Mu’azzam ta daura masa necktie, yana baya so ta bari amma sai tayi, bata damuwa da gwasalensa ko kadan, ba dama ya zabi kayan sanyawa sai tace ita basuyi mata ba, dole da wanda ta dauko zai yi amfani, undies dinsa ita ke wankewa kal duk bayan kwana uku wadanda duk farare ne.
In tana son sa shi dariya to tace a baki zata bashi abinci. Rannan data dage sai ta bashi ta ciko fork da dankalin turawa ta nufo bakinsa, abin yayi amusing dinsa sosai yace “Aalimah mai yasa bakya ji ne wai? Ni kuma gotai-gotai dani zan tsaya ki bani abinci a baki? Ki jira ki haifi dan ki tukunna sai ki yi ta bashi�. Sai ta rangwadar da kai tana masa wani irin kallo da ita kanta bata san tayi ba tace.
“Allah zai bani ne!�.
Mu’azzam sai ya samu kansa da amsa fatan Aalimah a cikin ransa na Allah ya bata Da. Sai dai method din samun dan har gobe bai san ta ina zai zo ba. Amma kwarai shima yake fata da addu’ar ganin dan kansa a duniya. Bai san irin soyayyar da wannan dan zai gani daga gare shi ba.
Abin da ta sa a gaba yanzu shi ne, neman Dr. Nebrass, kwarai ta ke son ganawa da shi. Amma ta rasa hanyar kai wa gare shi. Itama ta san wasa ta ke ta taba wayar Mu’azzam, yadda yake kaffa-kaffa da abarsa kamar munafukin miji mai mata hudu. Dabara ta zo mata, tunda dai ba ya shiga bayan gida da waya.
A wani marece ta yi sallama ta shiga dakin, asabar ce ba ya zuwa aiki, kuma gab ake da shiga lokacin sallar azahar.
Ko kallonta bai yi ba, yana bisa keken motsa jiki da ke can gefe a dakin. Waje ta samu ta zauna, in ta ce ba ta jin ciwon shakulatin bangaron da Mu’azzam ke yi da ita a wasu lokutan ta yi karya, sabida ba haka mijinta mai sonta ya sabar mata ba. Sai dai ta sa a ranta zamanta da Mu’azzam zaman jihadi ta ke yi. Zaman son maida shi mutum kamar kowa, mai cikakkiyar rayuwa kamar kowanne dan Adam. Albarkacin mahaifinsa da nata, wadanda ba su rage ta da komai ba a rayuwa. Kuma alhamdulillah ta san cikin kashi arba’in cikin dari (40%) tayi nasarar sauyawa Mu’azzam halayensa da dama.
Tunda an ce babu magani na farat daya a kan lalurorinsa, a ganinta dabarunta za su yi aiki wajen ba shi ingantacciyar rayuwa. Sannan fisabilillahi ta fara shiga halin ha’u’la’i mai tsanani da gangar jikinta, wanda har ya soma shafar lafiyar barcinta da sukuninta, bukata irin ta kowanne dan Adam mai lafiya a cikin gangar jikinsa, musamman wanda ya san cewa yana da aure. Kuma ga mijin yana tare da shi ko yaushe.
Dadin dadawa yawan shigewa Mu’azzam da ta ke yi duk da ya nuna ba ya so a yanzu yana tasiri sosai a zuciya da gangagar jikinta. Ita kuma a wannan dan tsukin ta zama infatuated akansa. In fact, bata taba jin son kusantar wani da namiji a duniya irin yadda take ji akan Mu’azzam ba. Amma shi ko a jikinsa.
Barin keken motsa jikin ya yi ba tare da ya ce da ita ci kanki ba don ya san wata matsalar ta zo masa da ita, wadda yau hutawa yake son yi, bashi da lokacin sauraronta, “you…. and your problems� (kamar yadda yake kiranta), ya shige toilet don dauro alwala. Aalimah ta yi wuf! Ta dauki wayarsa, ta lalubo lambar Nebrass ta shigar cikin tata, ta ajiye masa.
Fitowa ya yi daure da alwala, a lokacin da ita ta ke shirin barin dakin. Ciki-ciki ya ce da ita, “Ki zo mu yi jam’i�.
Ba tare da ta juyo ba ta ce da shi,
“bani da tsarki�.
Ta fice ta ja masa kofar.
7/9/21, 7:20 PM - Buhainat: RAAZEE'S
Bayan ya idar, ya zauna bisa darduma yana tunani. A tun sanin da ya yi wa Aalimah bayan aurenta da Aboulkhair yarinya ce mai kunya da kawaici, ko kwayar idanun shi ba ta iya kallo, wani irin respect ta ke ba shi irin wanda ta ga Aboulkhair na ba shi. Haka farkon zuwanta gidansa wannan halin bai canza ba ko kadan. Me ya sa ta sauya halin ta rana daya? Ta ke so shi ma sai ya sauya ko ta wanne hali? Haushinta da yake ji yau na wadannan sababbin halayen ne da ta aro ta yafa rana daya, ta cika masa gida da su. Wanda ke nufin tana da mission a kansa da ta ke son cikawa, amma ba halinta bane. Aalimah ba son shi ta ke yi ba in ya yi la’akari da tsayin lokacin nan ba ta taba neman shi da ya ba ta hakkinta na aure ba. Wata zuciyar ta yi saurin kare ta da cewa “ita za ta nema ko kai?
A al’adarta ta iyaye da kakanni, miji ke kai kansa ga matarsa ba matar ke kai kanta ga mijin ba. Ko babu soyayya mata basa jurewa wannan. Kuma ta san kana da lalura, tsoron hakan ma na iya cire mata sha’awar komai�.
Yana wannan tunanin ya ji motsinta tana shigowa. Daga kai ya yi ya dube ta a hankali, doguwar riga ce a jikinta (milk colour) samfurin Oman, yadin kamar na roba, don haka ya fiddo surar jikinta shapely, ta daure kanta da dankwalin rigar, gashin kanta ya kwanto ta baya. Ya samu kansa da kasa dauke ido a kanta. Wani magnet na jan idanunsa zuwa gareta. Ya kasa dauke ido a kanta.
Ba tare da ta ankara da irin kallon da yake mata ba a yau take ce da shi.
“Nan zan kawo maka lunch, ko in bar shi a dining?�
Zuba mata idanu ya yi kamar wani maganadisu na fizgar zuciyarsa zuwa gare ta. Kamar wanda aka yi wa wahayi; ji ya yi duk wani nauyinta da shakkarta da yake ji, a yau ya kau daga idanunsa. Hannunsa ya mika ya kamo nata a hankali, tare da ambaton sunanta da sassanyan sauti daga can karshen makogaronsa. Sai jinta ta yi gaba daya a jikin Mu’azzam ba tare da ta shiryawa hakan ba, ya soma wani irin sunsuna ta tun daga wuyanta har cikin jikinta. Turaren da ya dade yana ji daga nesa nesa yana dimautar dashi yau ya samu completely a jikinsa.
Aalimar da ya dade yana kallo daga nesa nesa yana kintata laushin fatar jikinta da sulbin bakinta, yau ya samu kwance a jikinsa.
And the skin is softer than he imagined.
Samun kansa yayi da rungumeta sosai tare da manna ta a kowacce kusurwa ta jikinsa.
Ajiyar zuciya yake saukewa a jejjere kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa. Is that the feeling of being with a woman???
Idan kuwa shine it’s the most pleasurable, and most intoxicating feeling in the history of man ever.
A hankali ya shiga kurdawa ta wuyanta har ya samu ya kai bakinsa zuwa ga nata.
It is a kind of gentle kiss wanda ya hautsinasu cikin dan lokaci bakidayansu.
Jikinta rawa ya soma yi tare da tasowar dadadden al’amarin da ta jima tana kokawa da shi da karfin hali da karfin addu’a. Kamshin jikin Mu’az da wanda ke fita daga bakinsa na mouthwash din da yayi amfani da shi shi ne babban abin da ya ribace ta. A lokacin da ya soma kissing din tsakiyar bakinta sai komai ya kwace mata. Ta manta cewa, wannan Mu’azzam ne ba Aboulkhair ba. Yanayin yadda yake sumbatar tata ba ta taba jin irinsa a duniya ba. Ya zamanto cewa ta gama mika wuya ga duniyar Mu’azzam…
Yayin da tafiya ta yi tafiya sai Mu’azzam ya rasa kuzarinsa bakidaya. Duk kokarinsa ya kasa komai bayan kissing din, cikin sanyin jiki ya koma gefen gadon ya zauna yana mai dafe kansa... Ita kuma Aalimah barin dakin ta yi tana mai jin har abada ba za ta sake iya hada ido da Mu’azzam ba.
Kwana uku suna buyar wa juna, sai dai ya samu abincinsa a ‘dining’, ta daina shiga dakinsa, duk wannan karambanin ta daina, ta zama calm, cool kamar farkon zuwanta, ta san ba karamin tsallake rijiya da baya ta yi ba, kunyarta ya ke ji, yana ganin ya zama raggon namiji, wanda bai iya biyawa matarsa bukata, tana ganin ta zama mara aji da tayi saurin bada kanta ga Mu’az haka. Gashi babu biyan bukata, ta san ba komai bane tasirin magungunansa ne. Ita dama bata da tsarki so bata cikin irin damuwar da Mu’azzam ke ciki. Ta kasa zaune ta kasa tsaye a daren yau da sabon al’amarin dake sakadar zuciyarta a hankali a hankali a kwanakin nan, yana rarake ruhinta kusufa-kusufa tun ranar da wannan dan physical relationship din ya shiga tsakaninsu, ba komai bane sai yawan tunanin MU’AZZAM da son ganin shi. Da kasancewa cikin wani irin shauki a duk lokacin da ta ji muryarsa yana magana a waya koda Harrison ko motsin sa zai shiga daki. Ba abinda take son ji sai muryarsa, ba abinda take son gani sai fuskar sa, ba abinda take so sai kasancewa tare da shi muddin rayuwar ta.
*****
Tayi kwalliya cikin atamfa Ghana wax koriya shar, daidai lokacin da ta fuskanci yana fitowa cin abinci sai ta fito ‘dining’ ta zauna, ta gaji da buyan tana so ta ganshi ko daga nesa ne in ba haka ba bata jin zata kai daren yau a raye, ta zuba abincin amma ta kasa ci sai juyi take da cokali a cikin tangaran. Dai-dai nan Mu’azzam ya fito daga dakinsa yana waya. Kallo daya tayi mashi ta ambaci “Ya Allah� cikin zuciyarta, sannan kuma tayi gaggawar kawar da kanta kada kwarjini da haibarsa su yi mata lahani a idanunta.
Ya shirya cikin ‘American suit’ bakake wuluk kamar kullum, neck-tie din wuyansa na yau red ne, amma sai ta ga kamar yau yafi kowacce rana yin kyau. Kamar yau ya fara sanya suit a jikinsa. Kamar yau ta fara ganinsa. Yayi fes! Yayi fresh! Kuruciyarsa ta fito sarari. Har ya zo kusa da ita ya ja kujera ya zauna bata sauke ido a kan shi ba.
Yayin da shi kuma ya ja ‘food warmer’ gabansa ya bude, ya dauki plate zai zuba sai ta mike ta karbe shi ta zuba masa daidai yadda ta san yana bukata, ta koma ta zauna tayi shiru tana satar kallon shi daga karshen idanunta tana cigaba da juya cokali a cikin abinci. Zuciyarta tayi haske, ko ba komai a ce Mu’azzam mijinta ne kadai ta gama morewa. Tunanin matsalar da ke kwance cikin auren nasu ta sanya jikinta yin matukar sanyi.
Mu’azzam yana cin abincin nashi amma hankalinshi na kanta. Ta koma ‘cool Aalimah’ din ta. Dama an ce ‘kayan aro baya rufe katara’. Murmushi yayi ya girgiza kai ya cigaba da cin abincinsa.
Da ace tuntuni ya san common hug da kiss zai ladabtar masa da ita ai da bai zauna tana bashi wahalar data bashi a baya ba. Da tuni an dade da wuce wurin. Ta dube shi da alamar tambayar ko me ya sanya shi yin murmushi? Ture plate din gaban shi ya yi, ya sunkuya a gabanta dai-dai fuskarta kasa-kasa ya ce da ita,
“Da za ki zauna a haka yadda ki ke, ai da na ji dadi�.
Murmushi ta yi, don sarai ta gane abin da yake nufi. Ya sarke hannayensa biyu, ya kuma dora habarshi a kansu ya yi magana cikin sanyin murya.
“Aalimah, why do you want to change me (Aalimah, me ya sa ki ke son ki canza ni?)�.
Da sauri ta cira kai ta dube shi, amma ta kasa magana, ashe ya ramfo ta tuntuni ita kadai ta ke shirmen ta?
Ya ce, “Answer me Aalimah, why? Me ya sa ba za ki barni a yadda ki ka same ni ba?�
Hawaye suka ciko idanunta, ba jimawa suka garzayo kan kuncinta, hanky dinsa ya ciro daga aljihunsa ya mika mata. Da sauri ta karba ta share, sannan ta furta masa abin da ke cinta a zuci.
“Because I want another Aboulkhair in you�.
Da sauri ya girgiza mata kai cikin gamsuwa da amsar da ta ba shi.
“Aalimah!�.
Ya kira sunanta cikin sanyin murya,
“Kama da wane ba ta wane! The fact that we belong to the same parents ba zai taba zama cewa za mu zama daya ni da shi a komai ba. Ki yi hakuri ki karbe ni a yadda nake, ni ma na fi son ki a yadda ki ke. Mai kunya mai kawaici mara hayaniya. Na kuma yi miki alkawarin zanyi miki duk abinda kike so gwargwadon ikona, amma ki daina aro personality din da ba naki ba kawai don kina so in canja daga yadda nake, zan kyautata miki iyakar iyawata insha Allahu but please accept me the way I was.
Na san ya fi ni kirki, ya fi ni dadin mu’amala, ya fi ni nuna miki soyayya. Aalima ki sani, ni ba ni da lafiya. Ina mai kokawa ne da kaddarar da ta same ni. Amma tabbas rayuwarmu tare na yarda cutuwa ce a gare ki. Aalimah na yanke shawarar in sauwake miki auren nan ko babu amincewar iyayenmu don ki samu farin ciki irin na kowanne ma’aurata. Iyayenmu su yi hakuri, na yarda ina cutar da ke a cikin gangar jikin ki da zuciyar ki.
Ni ma ba son raina ba ne zamowata a haka, I’m fighting with my destiny. Na san yadda zan bai wa su Daddy hakuri, in kuma nuna musu ba ki da laifi…�.
Girgiza kai ta ke yi da sauri, hawaye na bin kuncinta. Hankalin ta yayi mugun tashi.
“Na zabi zama da kai Yaya Mu’azzam a cikin kowanne hali a yadda na same ka. Babu saki tsakaninmu har abada. Ina son ganin iyayena da malam cikin farin ciki kamar yadda nake son rayuwa ta�.
“Ki sanya su farin ciki ki nakasa kuruciyarki Aalimah? I can’t give you sex�.
Da dukkan affirmation na zuciyarta ta daga masa kai, mai nufin, eh ta amince, zata zauna da shi haka. Mu’azzam bai san lokacin da ya bude mata dukkan hannuwansa ita kuma ta tafi a hankali ta shige, suka rungume juna suna hawaye da runguma mai tsananin karfi (tight-hug). Rungumar data bude shafin sabuwar rayuwa a gare su.
******
A haka suka ci gaba da rayuwar, sai dai su yi dan romancing a tsakaninsu. Wanda ke matukar wahalar da Aalimah a karshe. Ta rasa inda za ta sanya kanta a matsayinta na mace mai cikakkiyar lafiya. Rannan ta ce, bari ta kwaso magungunan Aunty Gumsu, watakila za su taimaka wa Mu’azzam ya ba ta farin cikin da gangar jikinta ke bukata.
Amma a karshe, matukar azaba suka sanya ta, wanda sai da Mu’azzam ya tausaya mata, ya kuma soma tunanin dole ne ya yi wani abu don inganta rayuwar aurensa.
A washegari ta ce da Mu’azzam za ta fita shopping ya ce ta bari ya dawo office sai ya kai ta, ta ce, a’ah ya sa Harrison ya kai ta da wuri ta ke bukatar shopping din. A yadda yake tattalinta ba ya son duk abin da zai bata mata rai, dole ya amince da tsarinta.
Ba ta ce da Harrison ya kai ta ko ina ba, sai asibitin Mu’azzam, tana son ganin Dr. Nebrass.
Da karramawa tsohon baturen ya karbe ta, a lokacin da ta gaya masa ita ce maidakin Engnr. Mu’azzam Raazee.
Ya ba ta wajen zama, ya kuma ba ta abin sha, amma ba ta sha ba, ya kuma ba ta dukkan hankalinsa don ya fahimci muhimmiyar magana ce ta kawota.
“Doctor I want my husband to live without the help of Anti-Androgens�.
Ta kifa kai a kan teburinsa ta saka masa kuka mai cin rai, wanda dole duk wanda ya ji ya fahimci tana cikin tsananin damuwa, ya tausaya mata a kan hakan, don ya san da ma hakan za ta faru.
Ba ta fito ta yi masa bayani baro-baro ba, saboda kunya ta diyan musulmi, amma ya gane dalilinta na zabar Mu’azzam ya zauna da lalurarsa yadda Allah ya bar masa ita, ba tare da sun daddaure shi da magungunan kashe tasirin androgens (sex hormones) a cikin jikinsa ba.
“It’s o.k Mrs. Raazee, its ok stop crying. Tunda kin zabi hakan shikenan. Daman maslahar taki ce, amma tunda kina ganin zaki iya jurewa it’s quite okay�.
Shi ne amsar da likita Nebrass ya ba ta. Ba haka taso al’amarin ya kasance ba babu yadda zata yi ne. Ta yi hakuri har na tsawon shekara guda da rabi, amma wutar son Mu’azzam da ke ruruwa a zuciyarta sannu a hankali, da kuma yawan physical relationship dake faruwa tsakanin su yanzu, da kwana da suke yi bisa gado guda kalmashe cikin juna, ya sanya ta kasa cigaba zuba masa ido kamar watannin baya.
*******
Dr. Nebrass, ya gaya wa Mu’azzam zai rage karfin anti androgens a jikinsa tunda yanzu yana da aure. Ba tare da ya gaya masa matarsa ta zo ta same shi ba. Mu’azzam ya yarda nan da nan, don shi kanshi al’amarin ya fara damunsa. Ba soyayyar Aalimah ce ta yi masa katutu ba, a’a, tausayinta ne. In don ta shi ne, yana jin dadin rayuwarsa a haka. Amma ya sani Aalimah tana cutuwa matukar cutuwa ba dan kadan ba, kawaicinta da alkunyar ta ke sa tana danne komai bata nuna masa gazawarta, tunda ya ba ta option na zama da shi ko a’ah, kuma ta zabi cigaba da zaman anyhow.
Aalimah ba za ta taba mancewa da wannan ranar ba. Rana mai dumbin tarihi a gareta. Ana tafka ruwan sama har da kankara kamar da bakin kwarya. Ranar da ta zama sirrin Mu’azzam, ya zama sirrinta shima, cikin wani yanayi mai ban mamaki a gare su bakidaya.
Tun abubuwa na tafiya gentle-gentle, har komai ya kwace wa Mu’azzam. Ya zama out of his control. Tsayin daren bakidaya za ta iya cewa, ko na minti talatin Mu’azzam bai barta ta huta ba. Har ita da kanta ta gane ba ta da wayo, abin da ta je ta sa likita ya yi masa.
Washegari ko da ya je office ma bai wuce awanni uku ba sai ga shi ya dawo a wani yanayi da dole ta amsa kiransa. Ya sake komawa office ba a yi closing ba ya dawo. Tsayin kwanaki bakwai a haka suke, tana kwarara kanta, tana karfafa gangar jikinta da zuciyarta. Ga dai biyan bukata ta samu, amma kuma shi Mu’azzam din tana tausaya masa. Ta kuma gane hakan zai iya zama barazana ga aikinsa, tunda ba ya maida hankali gare shi. Ba inda yake zuwa, ya daina kulla komai, in dai yana cikin gidan to aikin kenan, ko isasshen abinci ba ya iya ci, har ramewa ya yi, ita ma ta jigata ta rame. Don haka dole ta sake satar jiki ta sake garzayawa wajen likita Nebrass ta gaya masa kukanta, don an bai wa Mu’azzam query daga Chevron kan yana wasa da aiki yanzu, za’a iya sallamarsa ko rage masa matsayi daga yanzu zuwa kowanne lokaci idan bai gyara ba.
Dr. Nebrass ya zauna da taimakon wasu manyan likitoci ‘yan uwansa kan lamarin Mu’azzam. Domin sosai yake tausayawa Aalimah, ta damu da mijinta sosai, ya kuma gama fahimtar tana matukar son sa. A daya bangaren yana tausaya wa Mu’azzam din. Shekaru daidai kenan har goma sha biyar, yana rayuwa kan shan magani. Ya yi aure matar ta kasa jurewa. Ya warware maganinsa ya zama barazana ga aikinsa. Don sam Mu’azzam ya daina yin cikakkun awanni uku a office sai a jikin Aalimah. Daya daga cikinsu wanda ya zo daga asibitin Johns Hopkin, shi ne ya yi suggesting wani magani wanda yake ganin zai yi daidai da Mu’azzam, ya zauna lafiya da matarsa da kuma aikinsa.
Amma yana da matukar tsada. Amma da gudu Mu’azzam ya amince da wannan tsadadden maganin. Sai ya kasance Mu’azzam na yin sati ma bai bukaci sex ba, amma bayan cikar satin a duk ranar da abin ya juyo, Aalimah na ji a jikinta, amma ba ya wuce na kwana biyu, rabin albashinsa kuma na tafiya wajen sayen magunguna. Wannan ita ce rayuwar auren Aalimah da Mu’azzam a birnin Las Vegas.
Daidai wannan lokacin Aalimah ta fahimci yaron ciki a tare da ita.
A ranar data fahimci hakan, daki ta shige ta fuskanci alqibla ta yi sujudush-shukr ga Ubangijinta.
7/11/21, 9:41 PM - Buhainat: Don haka iyayen suka mika al’amarin kotun muslunci, inda kotu ta dankawa Aalimah mas’alar auren ta a tafin hannunta. Cewa in ta fi son zama da Aboulkhair za’a yi amfani da shari’ah, kotu ta yi wa Mu’azzam khul’i ta ci gaba da rayuwar aure da Aboulkhair, idan kuma ta zabi ci gaba da zama da mijinta uban ‘ya’yanta, to ta koma dakinta. Wannan karon babu wanda zai yi mata shisshigi. Sun ba ta dukkan damar ta da addini ya ba ta.
Aalimah bata yi wata-wata ba ta ce ta zabi Mu’azzam ya cigaba da auren ta sabida ‘ya’yan dake tsakaninsu da wasu dalilai da dama. Sannan ta nisa, kafin ta dago idanunta cike da hawaye ta nemi kotu alfarmar tana son Mu’azzam ya sake ta (ba khul’i ba), bata da ra’ayin sake zama da ko dayan su alhalin duk suna raye, in har da gaske addini ita ya bawa zabi a hannunta, to ta zabi Mu’azzam, a gefen hakan tana neman alfarmar ya sake ta, ba kuma don ta komawa Aboulkhair ba, sai don rabuwa dasu bakidaya yafi mata kwanciyar hankali. Ba zata iya kallon daya ba, alhalin tana auren daya. Tana kuka take rokon Alkali mai shari’ah ya roka mata Mu’azzam wannan alfarmar in har da gaske an damka mata ragamar auren nata a hannunta babu takurawar kowa cikin iyayen su. To wannan shine zabin ta.
Gabadaya iyayen sai suka sadda kansu kasa. Alkali kuma yace wannan tsakaninta da mijin ta Mu’azzam ne amma kamar yadda tace ya roka mata alfarma sai ya maimaitawa Mu’azzam alfarmar da Aalimah ta roka daga gare shi.
Koda aka waiwayi Mu’azzam kan wannan alfarma da Aalimah ta nema, daburcewa yayi, wata irin kidima ya shiga irin wadda bai taba shiga a rayuwar sa ba, daga bisani ya karfafi kansa da ya ga irin kukan da Aalimah take yi a gaban kowa, ya ce shi da hannunsa bazai iya rubuta saki a gareta ba, amma ta je ya warware igiyar aurensu guda daya (a fatar bakinsa). Tunda abinda ta zaba kenan. Kuma ta ce shine kwanciyar hankalin ta. Yana mata fatan alkhairi a gabadayan tsayin rayuwarta ta gaba. Daga haka ya mike ya bar kotun.
Mummy sai ta fashe da kuka, ta kifa kanta cikin cinyoyinta tana ta yi, wannan wace irin kaddara ce ta fadowa rayuwar ‘ya’yanta haka! Aboulkhair kuma ya sunkuyar da kansa, hawaye na tsirgowa daga cikin idanunsa, cike da nadamar dawowar sa cikinsu.
Da ya san abinda zai tarar kenan, da abinda dawowar sa zata haifar a rayuwar Mu’azzam, da ko kusa bai yi gigin dawowa ba.
Da ya karasa rayuwarsa can inda yake, a matsayin matacce a garesu.
Bai so ya zamo barrier ga farin cikin rayuwar Mu’azzam ba!.
Bai so dawowarsa ta rusa kyakkyawar rayuwar Mu’azzam da iyalin sa ba!!
Ya yarda rabuwarsa da Aalimah a yanzu, daidai yake da maida hannun agogo baya!!!
Haka suka koma gida kowa jiki a mace. Kowa ka gani gidan Malam Raazee a wannan rana sai ka fahimci akwai babban al’amarin da ya taba zuciyarsa.
Walwalarsu ta ragu, kuzarinsu ya ragu, kowa jikinsa a sanyaye.
Amma Oncle Mainasara ya ji dadin wannan lamari. Ya tabbata wannan karon Dan sa Anas zai samu abinda ya dade yana so. Tsuntsu ne ya fado daga sama gasashshe.
A daren ranar Mu’azzam yayi booking zai tashi U.S a safiyar washegari tare da ‘ya’yansa.
Ko a fuska bai canzawa Aboulkhair ba, Aboulkhair din ne ya kasance cikin damuwar da har ta kai shi ga kuka akan cinyar Mu’azzam. Ba kukan Aalimah bata zabi zama da shi yake yi ba, kukan zamowar sa silar rugurgujewar farin cikin rayuwar Mu’azzam ne.
A ganinsa Mu’azzam bai cancanci haka daga gareshi ba. Me yasa ya kasa sadaukar masa da Aalimah tun a tashin farko?
Gashi yanzu an bata goma daya bata gyaru ba.
Ji yayi soyayyar Aaliman tana yin wani irin fiffike tana ficewa!!!
Domin Mu’azzam ya cancanci ya bashi rayuwarsa dungurungum in ana badawa.
Bai gayawa Aboulkhair yayi booking ba ganin halin damuwar da yake ciki ya kuma kasa tsaida hawayen idanunsa tun dawowar su daga kotu kada ya kara masa damuwa.
Baya so ya kara raunana shi.
Amma dole da asubahin ranar bayan sun dawo masallaci ya gaya masa zai tashi Las Vegas da karfe goma na safe, yana bashi shawara idan ya kara hutawa ya gaggauta zuwa ya taho da matarsa Sa’eedah.
Hankalin Aboulkhair ya kara tashi, shi ya manta da Sa’eedah. Fargabar halin da Mu’azzam zai fada in ya koma gida shi kadai da kananan yara ya addabi zuciyar sa. Ko bai fada ba Mu’azzam ya ga hakan a kwayar idonsa.
Murmushi yayi ya dafa kafadunsa da hannayensa biyu yace “Aboulkhair relax, Mu’azzam din daka sani a baya bafa shine yanzu ba. Akwai improvement mai tarin yawa a lafiyarsa ta yanzu. I promised you i will be safe, kuma ga su Basma zasu debe min kewa I will not be alone�.
Ya tsugunna a gabansa ya dora tafin hannunsa bisa tafin kafar kanin nasa.
“Ina neman gafarar ka, for all the inconveniences!!!�.
Aboulkhair couldn’t keep it, banda ya rungume Mu’azzam da karfi ya saki kuka. A lokacin shima ya soma neman gafararsa, ya gaya masa yayi nadamar dawowa, da ya san abinda dawowarsa zata janyo kenan da ko kusa bai yi ta ba.
Da sauri Mu’azzam ya toshe masa baki yace “Ka isa ka kankare abinda Allah ya rubuta ne Aboulkhair? Bana son wannan maganar kar ka sake yin irin ta. Dawowar ka ta fiye min mata dari a doron duniya. Zan iya sake Aalimah amma kai bazan iya taba sake ka ba. Allah ya riga ya rubuta karshen zaman mu kenan. Wani wayo ko dabara ko dana sani bai isa ya kankare wannan kaddarar ba.
Ina mai kara gaya maka Zan iya sake Aalimah, amma kai bazan taba sake ka ba. Kai na yiwa laifi Aboulkhair dana biyewa zuciyata ta fada cikin soyayyar macen dana san ka tafi ka bari ne ba don ka daina so ba! Ka yarda dani a baya nayi duk kokarin da zan yi kada sabo ya shiga tsakanin mu, all my efforts was futile sabida nagartattun halayenta. But i trust myself now. I can manage a life without Aalimah. After all ta bani mafi darajar abinda zai debe min kewarta; ‘ya’ya har guda biyu a lokaci daya�.
Yayi Murmushi mai taushi “so ka daina damuwa, ka bar ni in tafi sabida ofis da makarantar yara, insha Allah ba abinda zai faru damu sai alkhairi. Aalimah will soon come and regret her judgement ni kuma zan bata mamaki, na gama zama da ita kenan insha.....�.
“.... Please Mu’az.....daina fadin haka, har zuwa abubuwan su lafa a zuciyar ta. Tension ne kawai ke damun ta ba wani abu ba. I’m sure da sannu zata huce, kuma komai zai koma daidai. Tunda da kanta tace ta zabi cigaba da zama da kai sabida ‘ya’yan dake tsakaninku, haka kuma sabida su ne zata huce bada jimawa ba. Alhmdulillah da ka yi amfani da hankali da tunanin ka wajen yin sakin da muslunci ke so.
Ni yanzu kallon Basma da Khaleesat nake yiwa Aalimah! Wallahi komai da ya dangance ce ta ya shafe daga kaina da zuciyata. Ni na jawo komai kuma ni zan gyara da yardar UBANGIJI, don Allah kada kayi fushi da ita�.
Mu’azzam ya hau girgiza kai. Ya dafa kafadar Aboulkhair, kana iya karantar kwantaccen bacin rai cikin kyawawan idanun sa. Abinda Aalimah tayi a court ya bata masa rai sosai, akalla in shi ta ki shi, to ta tuna kananan ‘ya’yan ta da za ta mayar marayun dole at a tender age. Cikin kaushin murya yace da Aboulkhair.
“For now, ka bar zancen Aalimah a tsakanin mu. Mu fuskanci muhimman abubuwan dake gaban mu, yadda zaka koma aikin ka, garin da zaka zabi zama da hijirar iyalinka. Aboulkhair dole ka baro Jeddah you don’t have a life there. You are a medical consultant not a shepherd (baka da rayuwa a can, kai likita ne mai matsayin consultatant ba makiyayi ba). Yanzu kokarin da zan yi dana koma shine na nemo takardunka dana ke ta boye dasu, na nema maka aiki a garin da ka zabi zama�.
Kawai sai Aboulkhair ya fashe da kuka, ya sake rungume Mu’azzam yana mai jin Aalimah da komai nata na kara yin wani irin NESA cikin dubban kilometres daga zuciyarsa… ji yake ko ita kadai ta saura ‘ya mace a duniya daga yau ya haramtawa kansa ita, ya barwa Mu’azzam iyalinsa. Haka Allah ya rubuta musu cewa zai fara aurenta, amma uwar ‘ya’yan Mu’azzam ce. Wannan itace rubutacciyar kaddararsu. Zai yi duk kokarin da zai iya na ganin cewa ta koma gaban ‘ya’yanta.
Da gari ya yi haske bayan sun yi wanka sun shirya tare suka tafi gidan Daddy don yin sallama dashi da Mummy, bai fada musu tun jiya ba cewa yau zai koma kada su dakatar da shi, ba ya jin akwai abinda zai yarda ya hana shi tafiyar nan tareda ‘ya’yan sa a yau ba sai gobe ba, don ita ce kadai kwanciyar hankalinsa, kamar yadda Aalimah tace rabuwa dashi shine kwanciyar hankalin ta. Zai nesanta kansa da ita, nesantawa da babu ranar waiwaye don ta samu kwanciyar hankalin da ta ke hangowa.
Ya saya kwayan idanunsa cikin bakin PRADA mai duhu ainun. Shadda ce fara kal (getzner) a jikin sa dinkin tazarce. Kasancewar ba kasafai yake irin wannan dressing din ba sai ya fito kala daban a yau. Hakika kalar mamansa ‘yar asalin kasar Nigeria yau ta nuna sosai a jikin sa. Ko turare bai iya ya fesa ba sabida yadda yake sauri ya bar kasar Niger, amma kamshin sa ya riga ya kama komai nasa.
Sanda suka shigo Daddy da matan sa guda biyu da Yesmin tare da yaran Gumsu hudu Nurat da kannenta su Ikhram suna karin kumallo. Daddy ya bisu da kallo suna shigowa, wani farin cikin sake ganin su a tare ya tsirga masa. Yayi godiya ga mahaliccinsa mai yawan hikima da kyautayi ga bayin Sa. Murmushi yayi yana ja musu kujera akan dining din. Har kasa suka tsugunna suka gaida iyayensu sannan suka zauna a kujerar da Daddy yayi musu tayi aka cigaba da karin kumallon tare da su. Gumsu ta daina surutu, ta yarda yanzu babu muhallin yinsa. Sosai ta kame bakinta.
Suna gamawa Mu’azzam yake gaya musu sallama yazo musu zai wuce yanzu sabida ofis, kuma tare da su Basma zai tafi. Mummy ta zaro ido tace “ka bar min su mana Mu’azzam yaya zaka yi da kananan yara har biyu?� Babu kunya Mu’azzam yace ai babu matsala zai iya kula dasu. Tare zasu dinga fita ya saukesu makaranta ya wuce ofis, sanda yake tasowa suke tashi suma, kuma zai daukar musu dattijuwa mai raino musulma.
Mummy zata sake magana Daddy ya tare ta yace “Allah ya tsare, ya kiyaye ku, yayi muku albarka�. Ya mikawa Aboulkhair mukullin motarsa yace ya kai su filin jirgi. Ya kara da duban Aboulkhair sosai wani abu ya fado masa, da sauri yace “drive with care. Fasten your belt. Da bismillah da ayatul kursiyyu kafa bakwai kafin tukin mota�. Aboulkhair ya amsa, tare da cewa “insha Allahu�.
Gumsu dakinta ta shige hawaye na zubo mata na tausayin Mu’azzam. Haushin Aalimah ya cika ta, har cewa tayi a ranta ba ita ba Aalimah insha Allahu. Tunda bata da tausayi ko kankani, kanta kawai ta sani da maslahar kanta. In bata tausayawa Mu’azzam ba, ai ta ji tausayin kananan yaranta.
Gidan Malam Razee suka koma, shine yaso batawa Mu’azzam lokaci don cewa yayi sam bai yarda ya tafi ba, ya zauna har Aalimah ta huce a maida aurensu su koma tare. Abinda Mu’azzam bai taba yi masa ba yau yayi masa wato gardama. Nan ya gane da gaske yake tafiyar yake so kuma ya yi fushi da Aalimah fushi mai tsanani. Aboulkhair shi ya ciwo kan Kakan nasu da kyar ya hakura ya yarjewa Mu’azzam tafiyar. Don ya gaya masa (a matsayin sa na likita) Mu’azzam is okay. He can handle himself.
Aalimah bata jima da tashi daga barci ba suna karyawa da yaranta a falon Inna Bintou ta tsinkayi sallamar Mu’azzam a tsakar kanta. Sallamar data ratsa har cikin kashi da bargon ta. Wuta ta dauke mata na lokaci mai tsawo domin sosai muryar ta ratsa cikin kunnuwa da jijiyoyinta. Su Basma suka dangwarar mata da kofin shayin ta har ya bare a jikinta, basu bi ta kanta ba suka kwasa da gudu sai wurin mahaifinsu. Rage tsaho yayi ya bude musu hannuwa suka shige ciki yana sumbatarsu daya bayan daya, ba tare da bata lokaci ba yace.
“Oya! Kowa ya dauko jakar kayansa tafiya zamuyi�.
Nan da nan suka hau tsalle suka runtuma daki da gudu sai ga kowanne rike da takalminsa a hannu, janye da trolley din kayansa. Basma tace “Mummy ki tashi ki dauko kayan ki� Mu’azzam yace “No Bassy, Mummy will stay at home, tana da abun yi�. Ya hau saka musu takalmansu. Tana zaune kamar an dasa ta tana kallon ikon Allah. Zuciyar ta na wani irin raurawa. Ya iso har gabanta ya ajiye mata passport dinta bisa cinyar ta. Ya kama hannun ‘ya’yansa yaja jakunkunan suka fice. Inna Bintou nata yi musu addu’a yana amsawa suka fice daga dakin.
Aalimah ta rasa abun da zata yi a wannan lokacin, kawai sai ta dora hannayenta biyu aka ta rushe da wani irin kakkarfan kuka, ta yaya zai zo har gabanta ya kwashe mata ‘ya’ya? Zuwa wata uwa duniyar da babu mai kula dasu???
Inna Bintou yi tayi kamar bata san da ita a dakin ba ta dau mayafi ta yafa ta fice don yiwa ‘yan biyu rakiya bakin mota.
Aalimah ta san ba mai kula ta ko kukan jini zata yi, haka ta tattara ta shige uwar daka, duniyar bakidaya tayi mata zafi. Ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji sanyi. ‘ya’yanta sanyin idaniyarta, ‘yan biyun ta abin farin cikin ta, wadanda bata iya barci batare da ta jisu cikin jikinta ba.
Haka ta ci kukan ta ta koshi, wanda ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani, ko sannu bata samu daga jama’ar gidan ba. Nasu mai sauki ne akan na Inna Kasisi, wadda ko gaisuwarta bata amsawa yanzu.
7/12/21, 4:49 PM - Buhainat: Inna Bintou ta zubowa jikanyar ta Hafsu shinkafa da miya ta shi go dakin da shi, Hafsu kai tsaye ta nufi Aalimah da abincin nan tana fadin ta sakko su ci. Warin miyar wadda taji tafarnuwa ya bigi hancin Aalimah. Wani bala’i ya ziyarceta kafin ta yunkura ta zauna ta kwararo wani uban amai wanda ya wanke Hafsu da shinkafar ta, ta cigaba da sheko shi kamar zata amayar da kayan cikin ta.
Da gudu Hafsu ta fita ta kira Inna Bintou. Wai Aunty Aalimah tana amai. Bintou da Kasisi dake madafi suka yi kasake! Suna kallon yarinyar tana digar amai kafin su juya su kalli juna. “Amai dai?� suka hada baki wurin tambayar ta. Daga bisani Bintou ta yunkura tabi bayan yarinyar zuwa dakin nata.
Ita ta taimaka mata ta wanke jikin ta, ta kuma gyara wajen ta kunna fanka da turaren wuta. Tun daga ranar Aalimah ta kwanta jinya, komai taci sai ya dawo, ta kuma ki yarda a kaita asibiti, kuka ma ta sakawa Inna Bintou ita Kano zata koma. Inna taje ta fadawa Malam halin da Aalimah ke ciki da Kano da take son komawa. Ta kuma ce tana zargin Aalimah karamin ciki gareta.
Malam yace zai turo Aboulkhair ya dubata, zai kuma sa shi ya saya mata tikitin tafiya Kanon.
Bayan fitar Bintou Malam Raazèe ya fada a tunani, wato hikimomin Ubangiji yawa gare su. Zuri’a tsakanin Aalimah da Mu’azzam ashe bata kare ba. Duk yadda Ubangiji ya shirya al’amarinsa dole bawa ya karba yayi imani. Idan Allah ya rubuta akwai sauran zama a tsakaninsu Aalimah bata da tsimi bata da dabara. Ga auren da kakar sa ke nema masa. Wanda shi sam hankalinsa bai kwanta da shi ba, don yana tsoron abinda ka je yazo, tunda Mu’azzam ba wai warkewa yayi daga lalurorinsa ba, su kadai suka san yadda suke zaune da junansu.
Aboulkhair Malam ya kira a waya yace yazo ya duba masa Aalimah bata da lafiya, ya sayo abinda yasan mara lafiya zai iya ci ya kawo mata kumallo take yi kullum. Abinci baya zama a cikin ta.
Shi da Yesmin suka zo gidan, Yesmin niki-niki da ledojin sayayyar da suka yo mata a supermarket. Dakin Inna Kasisi suka fara shiga suka gaisa, yace.
“Inna Aalimah muka zo dibawa�.
A take far’ar fuskarta ta canza tace.
“Kun bani ajiyarta ne?�
Ko kadan Aboulkhair bai ji dadin abinda ya fahimta daga Kakar su akan Aalimah ba, ya san kuma abinda ya janyo hakan, zama yayi ya soma yiwa Inna nasiha yana gaya mata Aalimah bata isa ta tsarawa kanta rayuwa ba face abinda Ubangijin ta ya tsara mata, idan Allah yace iyakar zamanta da Mu’azzam kenan fushinta da ita bazai canza komai ba, da ita da Mu’azzam duka jikokinta ne, nunawa daya soyayya akan daya ko bin bayan daya ba nata bane. Yana rokonta ta zamo mai adalci a tsakanin su.
Inna Kasisi bata ce komai ba amma jikinta yayi sanyi ainun. Mamakin juriyar Aboulkhair ya kamata, kamar ba shine wannan da ada ake tunanin bazai iya rayuwa ba sai da Aalimah. Ta san kuma ba komai ya sa shi sadaukar da sayayyar ba sai kaunarsa ga Mu’azzam. Tana mai addu’ar Allah yasa wannan zumuncin nasu ya zame musu silar shiga aljannah.
Ta dubi Yesmin tace “to wadannan uban kayyayakin da kuka kwaso kuma na menene?� Yesmin tace “kayan dubiya ne� tace “to a sammin nawa� Yesmin tayi dariya tace “sai in zaki taso muje dubiyar tare� Inna tace “albarkacin kaza ai kadangare na shan ruwan kasko, muje mu ganta, koda dai ciwon nata ai ba mai warkewa bane sai ranar da ya bushi iska�.
Aboulkhair ya fiddo ‘fresh milk’ mai sanyi daga cikin kayan ya dauki tambulan ya cika shi taf ya mikawa Inna yana murmushin jin abinda ta fada. Duk da bai gane hausar sosai ba. Ta karba tana sha tace “amman wannan madara da gardi take, gara ma ku bar min don bazata zauna a cikin ta ba�. Saida Inna ta gama shan madara tana santi, Aboulkhair na kara cika mata kofi, duk don ya lallashe ta taje ta duba Aalimah.
Saida ta sha ta koshi, tana yi tana binkito masa tsofaffin laifuffukan Aalimah a gareta tun fara maganar auren ta da Mu’azzam da irin kiyayyar data nunawa auren, tace ta san dole aka yi mata zama da Mu’azzam, amma tunda ga zuri’a a tsakani shi kuma data kwallafawa rai yayi aurensa tun kan ya dawo don me bazata hakura ba? Ai ga aya nan Allah ya nuna mata haihuwa da Mu’azzam yanzu ta fara.
Da sauri Aboulkhair ya daga kai ya dubi Inna yana son gane me take nufi, amma bata kara cewa komai ba tace su wuce su je tana dakin Bintou.
Aalimah na kwance bisa doguwar kujerar falon Inna Bintou, duk ta dashe tayi fari fat. Ta rame ta fita hayyacinta, idonta na fuskantar kofa sanda Aboulkhair ya sawo kai, Yesmin biye da shi da katuwar leda, sai Inna Kasisi karshen shigowa. Mamakin ganin Inna ya kasa boyuwa a idanunta. Kallo daya Inna Kasisi tayi mata ta tabbatar da zargin da suke mata. Aboulkhair tsintsiyar hannunta ya kama na wasu ‘yan mintuna ya kuma gwale idonta sannan ya taba temperature na wuyanta. Yace “tun yaushe ne kika fara vomiting din?� Ta rufe idanunta a hankali tace “last week� yace “banda aman sai me kuma?� Ta dan cuno baki tana kunkuni ita an dame ta. Haushi ya kama Inna tace “zaki bude baki kiyi magana ko ya tafi ya barki da ciwon ki?� Ta zumburo baki kafin tace “ciwon kai da zazzabin dare�. Aboulkhair ya dan kura mata ido kafin yace “when last kika ga period dinki?�.
Zaro ido tayi tana masa kallon tsoro da razana. Ita ta san rabonta da period tun a Las Vegas, bata taba damuwa ba sabida dama ta kanyi tsallaken wata, amma yanzu daya yi mata wannan tambayar sai taji damuwar duniya ta rufto mata. Shiru tayi ta kasa cewa komai. Sai zuciyarta dake ta kai kawo a allon kirjinta tana son fitowa ta bakinta sabida tsabar kidima. Ta zazzaro ido kawai tana kallonsa.
Murmushi yayi mata ya zauna sosai a gaban ta. Kayan da suka kawo mata ya janyo gabansa, ya fiddo kwalin boost (locozade) karami ya bude ya saka straw a ciki ya mika mata tunda Inna tace madara zata sanyata amai. Saida ta harare shi sannan ta yunkura ta tashi zaune. Har yanzu murmushin bai bar fatar bakin shi ba yace “karbi ki sha wannan Maman Aboulkhair. It will boost your energy ki daina wannan kwanciyar kamar ruwa�.
Ta mika hannu ta karba jikinta har rawa yake yi sabida yunwa, duk abinda ake dafawa a gidan babu wanda zuciyar ta ke sha’awa. Wadannan masu ruwa-ruwan su take so. Nan da nan ta shanye ta bashi kwalin, zai bude wani ta nuna fresh milk din tace shi take so. Ya bude ya zuba mata. Ta kafa kai kamar Allah ya aikota ta shanye gorar madarar nan bakidayanta. Tayi wata irin ajiyar zuciya mai nauyi. Kafin ta sunkuya ta fashe da wani kakkarfan kuka.
Tace ita tun kafin su zo Niger rabon ta da period dinta. Amma ta saba tana tsallaken wata shi yasa bata damu ba. Idan ciki ne ita ina zata tsoma rayuwar ta?
Aboulkhair yayi mata wani irin kallo, yace “shi uban Dan yace baya so? Koko bashi da yadda zai yi da shi in an haife shi?� Tace “ni bazan haifi Da bana gidan ubansa ba� yace “to da kyau, kisa a ranki kin haife Dan nan lafiya kin gama, ko kwarzane kika yi mishi muma mun san hanyar kotu. Taimaka min da fitsarin ki Yesmin ta kawo min yanzu�. Wata uwar harara ta zabga masa ga idanun kaca-kaca da hawaye tace “bani badawa din� mikewa yayi daga zaman da yayi a gabanta yana wani makalallen murmushi. Allah-Allah yake ya bar wajen ya kira Mu’az don yi masa wannan kyakkyawan albishir, yace.
“Rike abunki. Shi ciki ai dan duma ne da sannu zai bayyana kansa. Bansan me zai zama tukuicina na wannan albishir din ba. Oh me!�.
Inna Kasisi ta dade da barin dakin tun sanda Aalimah ta soma kukan nan nata mai ban haushi. Yesmin dai na jinsu bata tofa ba amma zuciyarta ta cika fal da farin ciki. Tana addu’ar Allah yasa albarkacin wannan cikin Aalimah ta hakura ta komawa Mu’azzam.
Yace “zan dawo na kawo miki magungunan da zasu taimaka aman ya tsaya dana karin lafiya, saura ki ki sha, wallahi zaki ga abinda baki so�.
A wannan rana Aalimah yadda taga rana haka taga dare. Ta rasa inda zata tsoma ranta. Wannan ciki shi ake kira unwanted pregnancy. Tun tafiyar Mu’azzam da ‘ya’yansa bata ware lokaci tayi tunaninsu ba sai yau, kullum makomar rayuwarta kawai take tunani.
Ta tuno ranar da aka yiwa Mu’azzam albishir din tana da ciki, riritawar da ya dinga yi mata lokacin rainon cikin ta, bautar da ya dinga yi mata don ta haife masa ‘ya’yansa lafiya, yadda ya hanata girki daga samun cikin ta zuwa haihuwarta. Duka rabin rainon ‘ya’yansa shi yayi abinsa. Duk abunda ya mallaka nata ne da ‘ya’yanta. Kulawar Mu’azzam a gareta unexpressable ce. A cikin maza samun mijin da ke muhimmanta matarsa da daga girman darajarta kamar sa, abu ne mai matukar wuya.
Yau gata zata yi rainon ciki a dakin kakarta, ba wanda ya damu da ta ci ko bata ci ba sabida son zuciyar ta. Yo son zuciya mana! Laifin me Mu’azzam yayi mata data yanke wa rayuwar su wannan tsatstsauran hukuncin? Wanda ta tabbata cutuwa ne ga dukkannin su. Ba don Allah ya jefo su Aboulkhair ba, da haka zata kwana da yunwa. Ba abinda ya damu su Inna Kasisi, dan gara-gara Inna Bintou tana sassauta mata.
Aboulkhair din da ta ke fadin bazata iya kalla alhalin tana auren Mu’azzam ba, shi gashi yana rayuwa da wata macen a kan idanunta. Har da albarkar zuri’a a tsakani.
Me Mu’azzam yayi mata a rayuwarsu banda alkhairi? Abinda ya faru dasu Ubangiji ne ya rubuta shi bata isa ta kankare faruwarsa ba. Yanzu gashi sakamakon rashin tawakkalinta ta janyowa kanta kiyayya a zukatan mafi yawan ‘uwan ta. Ta janyowa kan ta rainon ciki a dakin kakarta, ta yi missing duk wannan gatan na Mu’azzam! Ta tabbata Mu’az yayi mummunan fushi da ita, tunda har ya kai tsayin wannan lokacin bai taba nemanta ba, bai taba hada ta da ‘ya’yanta sun gaisa ba, anya bata yi kuskure ba? The deadly mistake din da ba zata iya gyarawa ba?
Gashi da Ubangiji ya tashi nuna mata bata isa ta kashe auren da kwanansa bai kare ba, ya kaddareta da boyayyen ciki, wanda ke tabbatar da har yanzu tana cikin zummar mijin ta har sai ta haihu. Ko yaya yake rayuwa da yaran shi kadai? Koda yake ko tana nan abubuwa da yawa shi yake musu, a wannan fannin bata jin sa, sai ko ta bangaren lafiyarsa.
Anan din ma tana da tabbacin he is doing well, in dai da Dr. Nebrass a raye, to kowacce irin matsala zata zo masa da sauki. Yawan ibadarsa kuma zai zamo kariya a gare shi.
Abu daya take da yaqini dashi akan Mu’azzam, duk fushinnan da yake yi da ita, bazai shafi abinda ke cikin ta ba. Zai so shi tamkar sauran ‘yan uwansa.
Zata yi masa rainon abunsa, ko albarkacin sa ya dubi nadamar ta ya yafe mata kuncin data jefa shi a ciki, koda bazai yi mata alfarmar komawa dakinta gaban ‘ya’yanta ba.
A washegari kowa dake gidan ya ji batun cikin Aalimah. Anas murna ta koma ciki, domin kuwa a baya yana kirge da watannin cikar iddarta. Yanzu kuwa ya fara fidda rai duk da ance faduwar gaba asarar namiji.
A daren ranar da suka baro Aalimah, Aboulkhair ya kulle kansa a daki ya kira Mu’azzam. Yana cike da wani irin doki da farin ciki.
A can Las Vegas, adaidai lokacin Mu’azzam na yiwa yaransa shirin kwanciya barci zasu kwanta, sabida gobe litinin don haka da wuri suke kwanciya.
Ya amsa wayar Aboulkhair da hannu guda, daya hannun yana shafa kan Basma, wadda ke dan rikici irin na mai jin barci.
“Mu’az.... kunnenka nawa? Menene goron albishir dina? Aalimah dai ciki gare ta, kuma a yadda na kintata yayi watanni uku�.
Gaba-gadi ya fadi sakonsa, ba tare da jan rai ba .
Wani irin shiru Mu’azzam yayi, tamkar ruwa ya cinye shi.
“Mu’az.... Mu’az kana kan layi?�
Aboulkhair ya tambaya jin shirun nasa yayi yawa.
“I’m on the call� ya fada a matukar gajarce.
“Ba zaka yi hakuri ba ku daidaita haka ko sabida shi? I didn’t expect it to be that longer, ban zaci fushin naku zai kai har zuwa wannan lokacin ba�
Murmushi yayi, yace “Aalimah ba zata taba sona ba Aboulkhair, I’m sure she is not happy with it. A da ne ban damu data so ni ko ta ki ni ba, abinda nafi baiwa muhimmanci shine kasancewar mu tare.
A yanzu kuwa na san how it feels to be loved by the one you love. Ciki kuma nayi farin ciki da shi Allah ya raba su lafiya in karbi Da na. Ka barta tayi rayuwarta yadda ta zabe ta. Yanzu haka aure zan yi ni�.
Aboulkhair ya kaskantar da murya yace “na roke ka kada kayi wannan kuskuren, ka bata lokaci. Auren huce haushi kake so kayi, kuma bazai haifar mana da alheri ba�.
Murmushi Mu’azzam yayi, har ransa ya san Aboulkhair gaskiya ya fada, auren da ya amsawa Inna zai yi na huce takaicin Aalimah ne, amma ba zai iya rayuwa da wata diya mace bayan Aalimah ba, amma wani bangare na zuciyarsa yana insisting da ya yi auren don ya huce haushin tozarcin da Aalimah tayi masa. Ta rasa inda zata ce ya sake ta sai a gaban Alkali. In ta bukata cikin sirri ita da shi ai shi me iya sadaukar da komai ne don farin cikinta da kwanciyar hankalin ta.
Har suka yi sallama bai ce da Aboulkhair ya fasa ko bai fasa ba.
Cikin kwana bakwai Aalimah ta samu karfin jikinta, sabida kulawar data ke samu daga Aboulkhair da Yesmin. Ya hadata da magunguna masu kyau wadanda suka taimaka wajen rage mata yawan aman data ke fama da shi, ga kayan dadi iri-iri kullum yana baiwa Yesmin ta kawo mata leda-leda, tuni ta barwa su Inna abincinsu sai kayan kara jini dana kara kuzari da yake aikowa. Mummy Zulaiha kuma kullum sai tayi mata waya ta tambayeta abinda take son ci, tun tana jin nauyi har ta daina. Don haka kwanon abincin ta na musamman ya koma gidan Daddy wanda Mummy da kanta ke shiga kitchen ta girka mata, kullum Yesmin da Nurat ke kawo mata.
Saida ta warware sosai ta maida jikin ta Malam yayi mata iznin tafiya Kanon kamar yadda ta bukata.
A daren ranar ta hada kayanta tsab tana cike da doki. Washegari Aboulkhair ya saya mata tikiti ta tafi Nigeria. A Abuja tayi transit kafin ta taso ta sanya layin ta na Nigeria ta kira Yaya Aboubacar ta gaya masa lokacin da zata sauka. Kafin aje Kano ta jigata sosai. Amma tarbar data samu a gidan su tasa ta mance da duk gajiyar data kwaso.
Ta samu gidan nasu da albarkar baki na musamman, Dr. Suraj Kashim wan Mama da matarsa Ilham da biyu daga cikin yaransu Mustapha da Maryam sun zo ganin gida daga kasar Canada. Maryam zata yi sa’ar Sultana itace ta biyu a ‘ya’yan aunty Ilham. Mustapha zaiyi sa’an autarsu Suhaima. Don haka tuni ta ware a cikin ‘yan uwanta data dade bata gani ba anata harkar arziki, tana ta taka-tsan-tsan kada wani cikin su ya fahimci cikin nan da bata so a sani. Sai fama take da zumbulelen hijab tun zuwanta har aunty Ilham na tsokanar ta ko Mu’azzam ne yasa ta yawo da hijabi, anan Mama take gayawa Ilham ai babu auren, ta gaya mata duk abinda ya faru.
7/13/21, 5:59 PM - Buhainat: Aunty Ilham ta taimaka mata ta sanya lallausar leshin data kawo mata, ta zaunar ta gefen gadon ta tana yi mata sassanyan make-up. Sai gyaran muryar Uncle suka ji a bakin kofa yana fadin “Ilham ina ‘yar taki ne? Ta zo suje ko tausa ta yiwa mijinta ya rage gajiyar zirga-zirgar nan da ya sha�. Ilham tayi dariya Aalimah ta sadda kai kamar tace kasar ta tsage ta shige. Yace “maza fito ki same shi a mota driver zai kai ku masaukin shi. Daga yau har kwana uku na sallame ku, in zaku wuce U.S kuzo muyi sallama�.
Aalimah kamar tayi kuka bayan wucewar Daddy, bata ankara ba kuwa ta ji hawaye sun sauko mata data ji cewa da gaske zata bar Ilham da iyalin ta bada jimawa ba. Aunty na cewa ta yi hakuri ta bi umarnin babanta, ta bar Mu’azzam ya fanshe watannin da ya yi ba tare da ita ba cikin kwanaki ukun nan. Ta armasa masa su su shiga cikin kundin tarihin rayuwar su. Sakamakon haka Allah zai iya bata Aljannah. Ga bin iyaye ga bin miji�. Dariya tayi don ta san aunty Ilham wayo take mata.
Ita ta tsitstsintar mata duk abinda tasan zata yi amfani dashi ta jefa mata a jaka. Ta dauko mata jakar suka fito tare. Mu’azzam da Uncle na bakin motar Uncle suna magana direban yana daga cikin motar. Fitowarsu yasa suka yi sallama, aunty ta bude mata kofa shi kuma Dr. Suraj ya bude masa, suka shiga suka rufe musu tare da daga musu hannu.
Har suka iso hotel din da Mu’azzam ya sauka basu yi magana a junansu ba, shi Mu’azzam waya yake da Aboulkhair yana gaya masa gashi a Canada ya zo biko, Aboulkhair yace “Canada kuma?� Murmushi yayi yace “can ta yi kaura, tunda zaman gidan Malam Raazee ya gagara, kasan mace in ta wuce zaman gida tace kuma sai ta zauna to akwai matsala, don bazata taba jin dadin sa ba, musamman a cikin dattijai� Aalimah ta harare shi ta gefen ido. Aboulkhair yace “gidan Dr. Suraj ta koma kenan?� yace “eh, in dama ta ki ba sai a koma hagu ba?� Murmushi Aboulkhair yayi yace “kuma Inna Kasisin tana can tana cigiyar ta, ta dade da saukowa, auren data ke nema maka ma da bakinta tace ta fasa, ba za’a samu macen da zata zauna da Mu’azzam tsakani da Allah cikin kowanne hali irin Aalimah ba.
Tana fadi da bakin ta “Aalimah ce ta zauna dashi a halin rashin lafiya, don lafiya ta samu bazata amince wata ta more ta ba Aalimahr ba�. Duk zancennan da suke yi akan kunnen Aalimah sabida a hands free Mu’azzam ya sanya wayar.
Ta tsurawa Mu’azzam ido jin abinda Aboulkhair ke fada. Mu’azzam ya samu lafiya as in how? Dama lalurarsa mai warkewa ce? A take kuma kwakwalwarta ta tafi tunano mata wani zance makamancin wannan da suka taba yi da Daddynta farkon aurenta da Mu’azzam. Cewa Mu’azzam zai iya warkewa bayan samun accurate treatment na akalla shekaru goma. Kuma ya dade da cika wannan ka’idar. Yadda yake romancing dinta dazu passionately kuma cikin nutsuwa ba yadda ya saba ba. Idanunta suka cigaba da budewa akan Mu’azzam yana ta hira da Dan uwansa yana ta murmushi kamar ya manta da ita cikin motar. Irin murmushin da ba kasafai yake yi ba sai yana cikin matsanancin farin ciki. Sassalkan sajensa ya kwanta lufff akan fuskarsa ya kara masa ilhama da cikar zati. Fararen hakoransa a waje, kamar wanda aka yi wa bushara da Aljannah.
Lumshe Idanunta tayi, a lokacin data ji sanyin hannun Mu’azzam a cikin nata. Ta kuma ji motar ta daina motsi wato sun iso masaukin nasu. Direban ya daukar mata jakarta da Ilham tasa mata daga bayan mota, ya rakasu da ita har kofar dakinsu ta cikin lifter. Sannan ya sake biyo lifter ya dawo kasa ya dauki motar don kaiwa ubangidansa.
Tun daga shigarsu dakin da Mu’azzam ya sanya mukullin shi ya bude, abubuwa basu kara daidaituwa ga Aalimah ba, duniyar ta bata kara zama cikin seti ba, haka shima Mu’azzam. Duk yadda ta zaci kewar data ke jin ta yi ta Mu’azzam mai dumbin yawa ce, ashe na fatar baki kawai ta sani. Ba da sanin ta ba kowacce gaba ta jikinta tayi kewar tasa ba zuciyarta kadai ba. Da farko akwai dari-darin abin da ‘yar fargaba a tare da ita. Kafin wani dan lokaci kuma ta tsinci kanta da mika wuya bakidayan ta. Sakamakon ganewa data yi cewa Mu’azzam din da ba shine yanzu ba. Gabadaya Mu’azzam din data sani a baya ya canza mata, things are going very soft and gentle from him. Ta yarda bayan lafiya da nutsuwa harda kwas (course) a soyayya ya samu wanda a baya bashi da kamarsa.
A can baya ta haqqaqe abinda ya sani shine ya biya bukatar sa anyhow; disregarding her own emotions. Kuma akai-akai kamar cin abinci. A hakan kuma take son abinta, take kula da dukkannin bukatun sa, domin tana gamsuwa ta kowannne bangare. Amma yanzu it goes along with her own pleasure and contentment. Tare da kula da rashin jigatar da ita a matsayin ta na mai tsohon ciki. Hawaye ta soma yi na farin ciki da godiya ga Allah. Ta yarda Mu’az ya samu lafiya. Komai ya koma dai-dai yadda ya kamata ya koma. It tastes good.... It tastes romantic. Wata rayuwa ce da bata taba mafarkin samu a Mu’azzam ba.
Daga nan kuma sai barci, barcin da suka dade basu yi mai nutsuwar sa ba a kafatanin rayuwarsu. Ba su suka farka ba sai karfe biyar na asubahi, tare suka yi jam’in sallar asubah. Sun dade suna addu’a batare da kowanne ya san abinda dan uwansa yake roka akan dan uwansa ba. Aalimah rokon Allah take ya dorar da lafiyar Mu’azzam, bata taba samun nutsuwa a rayuwar aure irin ta yau ba. Tana rokon Allah ya dorar da wannan rayuwar ya dawwamar dasu cikin alherinsa.
Ga Mu’azzam, rokon Allah yake ya sauki Aalimah lafiya, ya raya musu ‘ya’yansu rayuwa ta addinin muslunci. Abubuwan da bai taba ji akan Aalimah ba, su suke kara overwhelming dinsa yanzu. Ashe wannan sune feelings.....sune emotions. ..... sune affection… sune so da kauna wadanda a baya bai san su ba? Idan kuwa har sune dan uwansa Aboulkhair yayi kokari, kokarin da a yau ya jinjina masa, yayi masa sadaukarwar da shi ba zai iya ba! Don abu na karshe da bazai iya ba a yanzu shine rabuwa da Aalimah!!!
Suna kwance kalmashe cikin jikin juna, lullube cikin lallausar duvet, sanyin Ontario na yau kamar har yafi na kullum ratsa kashi da bargo. Mu’azzam yace “umh Aalimah, gaya min yaya bayan rabo? Na same ki cikin yanayi na kwanciyar hankali da jin dadin rayuwar da ta same ki, sabanin ni da darare suka yi ta wucewa da yawansu idona biyu har ketowar alfijir. Bana komai sai zubawa ‘ya’yanki ido suna nasu baccin ina kallon fuskar ki cikin fuskokin su. Me yasa ki kayi tunanin cewa rabuwar mu ita ce mafi alkhairi?�
Aalimah ta kwantar da kai bisa kirjin Mu’azzam tana mai jin komai na rayuwa yanzu yayi mata daidai, daidai da yadda take kwana tana addu’ar Allah ya mayar mata da shi, daga lokacin data yanke musu hukuncin da ta ke ganin shine abinda ya dace dasu bakidaya, tace.
“Ya Mu’az nima bansan dalilin da yasa na yanke hukuncin dana yanke ba, abinda na sani a lokacin shine I’m desperate, hopeless. Amma daga ranar da hakan ta faru ni kuma ban kara rayuwar farin ciki da jin dadi ba, ji nake kamar na yanke bangaren daya kunshi dukkan farin cikin na yar. It was regrettable, though, ko kai ne a matsayi na a lokacin abinda zaka yi kenan. Dawowar Monsieur Aboulkhair abin farin ciki ce a garemu amma hakika ta ruda ni sosai. Wani al’amari sai Ubangiji.
Zawarcin bashi da dadi ko kadan, bana son tunawa, kowa bai min ta dadi ba sai Daddy da Mummy, su kadai suka karbi uzrina, kai dan gata ne Ya Mu’az ban ga wanda ake so a zuri’ar mu kamar ka ba�.
Dariya Mu’azzam ya saki yayi cuddling dinta sosai, dan kankanin bakin ta yayi kissing kafin yace.
“Kina jin dadin yimin wannan gorin Aalimah; ba wanda ake so a gidan RAZEE kama na, na yarda basu yi miki ta dadi ba amma kisa a ranki duk a cikin son da suke miki ne. Fatan su da burinsu shine mu kasance tare, mu raini ‘ya’yan mu tare.
Me nake da shi a duniya da zan sakawa Aboulkhair wannan sacrifice din da yayi min? Wallahi babu. I love him to an extent. Ji nake idan zan yi ta haihuwar ‘ya’ya maza ina saka musu Aboulkhair yayi kadan ya nuna godiyata a gare shi�.
Haka suka karar da wunin yau bakidaya a gadon barcinsu, sallah kadai ke tada su. Abinci daga hotel din ake shigo musu dashi, Ilham ta ce zata aiko Mu’azzam ya ce ta bar shi. Baya son ko kuda ya gitta a tsakanin su. A shekaru bakwai da suka yi tare a baya, basu taba samun shaquwar da suka samu a kwanaki ukun nan da sukayi a Ontario ba. Soyayyar ta ninku, ta karu, ta rubanya. Basa ganin kowa a gabansu sai junansu.
Mu’azzam ya kira Madame Ruqayya mai rainon su Basma yace ta bashi Aboulkhair da Basma. Basma na karba ya mikawa Aalimah, sallama kawai Aalimah tayi Basma ta shaida ta, soyayyar uwa da Da sai Allah. Maimakon Basma tayi murna da jin mamarta kuka ta saki, tana fadin Mummy kin guje mu, kin barmu mu kadai a wajen Madame da Daddy, kin ki dawowa saboda kin daina sonmu.....�.
“Basma uwa tana daina son dan ta? Wannan impossible ne. Baki San uzrina ba Bassy, I’ve a green great giant surprise gift for you. Tare da sabon Baby zan dawo, mace ko namiji wanne kika fi so?� Nan da nan Basma ta share hawaye ta saki dariya tana fadin “Allah Mummy? In dai da gaske kike to na daina fushi, dama duk ‘yan ajin mu suna da baby a gidan su banda ni, yaushe zaki dawo?�
Aboulkhair ya kwace wayar daga hannun Basma, “Daddy your boy is missing you, yaushe zaka dawo?� Aalimah ta lumshe idon ta, soyayyar uwa da Da na ratsa ta. “Yaron na Daddy ne kadai ko? Ya manta da Mamansa?� Aboulkhair ya zabura, ya sake kankame wayar a hannunsa. “Mummy ke ce?� Nice Monsieur Aboulkhair, ina fatan ba ka yiwa Madame Ruqayyah rikici?� Shima sai yasa kuka yana fadin “mummy me muka yi miki kika tafi kika bar mu mu kadai? Ko a waya bakya kiran mu? Daddy kullum baya bacci sabida kin ki dawowa, don Allah Mummy ki dawo bana son zama da Madame Ruqayya ke da Daddy nake so....�.
Ta kasa tsayar da hawayen da suka shimfido mata, ta kai yatsunta ta share su, tace “Aboulkhair it’s a promise nan da kwana biyu zaka ganni a Vegas tare da Daddy. Amma sai ka daina cewa baka son zama da Madame Ruqayyah, kaga bazata ji dadi ba tana iya kokarinta a kan ku�. Ya juya ya dubi matar ya yi mata murmushi ya ce “Madame sorry. My Mummy is coming back soon�.
Yau dai wayar ta uwar da ‘ya’yanta ce ko uban basu nema ba har suka kare hirar, wadda ake yin ta ana sharar hawaye da koke-koke. Mu’azzam yana daga gefe Aalimah ta yi matashi da gadon bayan sa duk yana jin su yana murmushi.
Ya karbi wayar daga hannunta ya kira Malam Razee, ita kuma ta shiga toilet don yin alwala. Tana jin su suna hira yana gaya masa ai yazo yayi biko gashi a hotel tare da Aalimah. Daga bayin Aalimah ta saki salati tana fadin “haba haba Ya Mu’az? Haba don Allah� Malam Razee yace “hotel kuma? A wane gari kuma?� Yace “wani kayataccen hotel ne a birnin Ontario, ita Ontario din cikin kasar Canada take, nan Aalimah tayi hijira gidan Baffanta na wajen uwa, a cewar ta tunda bakwa son ta�.
Murmushi Malam Raazee yayi yana hamdala a fili da boye saida ya baiwa Mu’azzam tausayi. Ya tabbata har hawaye yake yi duk da baya ganinsa. Malam yace “ko yau mutuwa ta zo, burika sun gama cikka. Kowa dake cikin ‘ya’ya da jikoki na ya samu rayuwar da hankalina ya kwanta da ita. Ka rike ‘yar uwar ka amana Mu’azzam ku rufa asirin juna. Allah yayi muku albarka, ya albarkaci zuri’ar ku�.
7/13/21, 6:00 PM - Buhainat: Kafin kace meye wannan zance ya tadda su Inna Kasisi, Inna Bintou, gidan su kawu Oussama da gidan Daddy1. Aalimah da Mu'azzam sun koma har sun tafi yawon amarci. Zancen ya baiwa Gumsu dariya tace da wanda ya zo ya gaya musu “wane amarci da zungureren cikin?� Amma zuciyar ta kal kamar takarda.
Gumsu ta dau waya ta hau doka kira Nigeria, Basmah ta kira tace “kin ji wai yar tawayen can ta gaji da zaman gida ta koma gidan ta har an tafi honeymoon wata kasa, nace wane yawon amarci da zungureren ciki?� Basmah tace “kayyasa! Dadi na da gidan Malam Raazee karawa miya gishiri, wani lokacin har da onga, ba wani yawon amarci da suka tafi dama tana can shine ya bita� Gumsu tace “wai ba tana gidansu ba?� Basmah tace “tunda son kai ya rufe maku ido yaushe zaku damu da inda take? To masu sonta sun dauketa zuwa Canada ko wata daya bata rufa anan Kano ba�. Gumsu ta ji duk kunya ta kama ta, tunda Aalimah ta bar Niamey bata kara neman ta ba balle ta tambayi lafiyar cikin jikin ta tace “don Allah ki bani lambar ta�. Basmah tace “wallahi banni badawa, in da kunya ai baza ki nemeta ba yanzu data dawo gidan Dan ki. Watanni sama da hudu baki kirata ba ko don jin lafiyar abinda ke cikinta sai yanzu data yarda ta koma gidan dan ki? Wannan son kai a fili da me yayi kama!�.
Gumsu tace “ki yarda dani Basmah ba son kai bane ba, tausayin Mu’azzam da yaran nake ji. Yanzu data yarda ta koma baki ji dadin dana ji ba, ba shikenan komai ya wuce ba?� Basmah tace “to shi da kike jin tausayi baya tausayin kansa, da yana tausayin kansa da ya dade da neman sulhu�. Sai da Gumsu ta kafa naci sannan Basmah ta hakura ta bata lamabar Aalimah ta Ontario.
Sanda Gumsu ta kirata Mu’azzam take wa cumbing kanshi ya fito daga wanka. Don haka bata daga ba sai da ta gama, ta kuma taimaka masa ya gama shiryawa, Mus’ab ne zai zo ya daukesu zuwa gidan Uncle suyi sallama ta hada kayanta don gobe jirgin asubah zasu bi zuwa U.S. Gumsu bata fasa kira akai-akai ba har Mu’azzam ya gaji yace ta daga wayar nan. Tana dagawa taji Gumsu. Ajiyar zuciya tayi tace “ko dai wrong number ne?� Gumsu da borin kunyar ta tayi ta bata hakuri tana gaya mata abinda take hange na barinta gaban ‘ya’yanta tunda in ta ki Mu’azzam ta ki Aboulkhair karshenta dole wani daban zata aura ta bar yaran cikin maraici ita abinda bata so kenan tayi hakuri ta fahimceta ta daina kullatar kowa akan haka, soyayyar da suke yi mata ne ya janyo hakan�. Mu'azzam ya gaji da jiran Aalimah su fita yace da hannu wacece ne? A hankali ta motsa labbanta tace masa “Gumsu-Moiram� murmushi yayi ya karbi wayar yace “inason fita da iyali na, ko za’a bar wayar sai mun dawo?�
Gumsu ta shaqa tace “ina can ina maka kamfen, har gaba na kulla sabida kai, kana nan kana min kora da hali ko?�
Yace “to ai ni ban sa ki ba, dadi na dake sa-kai a uku babu gaira babu dalili�. Aalimah bata san sanda ta saki dariya ba, in Mu’azzam ya san yadda Gumsu ta damu da al’amarinsa da bai yi mata haka ba. Ta karbi wayar tace mata ta hakura, sannan ta barsu suka fita.
Sunyi kwalliya ta alfarma cikin shigar mutanen Nijar dukkansu. Mus’ab na tuki suna baya. Ya dan juyo ya dubi Aalimah yace “we’re gonna miss you so much Adda, kwana ukun nan da baki gidan baki ji yadda gidan ya koma boring ba kowa baya walwala musamman Maryam�. Murmushi tayi tace “nima zanyi kewar ku, yadda halshe bazai iya bayyanawa ba, duka gidan I enjoyed your company so much�. Mu’azzam yana jin su bai ce musu komai ba.
Daidai lokacin da suka iso gidan, duk mutanen gidan suka tarar a falo. Kowa yayi jigum kamar wadanda aka yiwa mutuwa. Aalimah na shigowa Maryam ta nufe ta ta rungume tana kuka tana rokonta kada ta tafi. Daddy yace “yau naji ikon Allah in da za’a ce kada mace ta je gidan miji, kema kwana nawa zakiyi a gidan da zaki hanata zuwa nata? Kuma wai don rashin kunya a gaban mijin ta?� Su Taufeeqah suka hau dariyar Maryam, Mu’azzam yace “Maryam duk sanda kike son ganin Adda zan miki visa kije Las Vegas. I promised�. Ai nan da nan Maryam ta saki Aalimah ta hau tsalle.
Anan suka ci abincin dare suka nitsa hira har saida yaran suka yi barci, Anty da kanta ta hadawa Aalimah kayanta tsab, Mus’ab ya sanya a mota. Anan suka karar da rabin daren, sai da zasu tafi Anty ta fiddo sayayyar data yi mata na kayan jarirai unisex cikin katuwar jakka, dana su Basmah suma kowa ya samu jaka guda. Daddy kuwa kudi ya zuba mata cikin account din da ya dade da bude mata tun zuwanta kamar sauran ‘ya’yansa, duk wata yana saka musu kudi don bukatocinsu, yace in tana so ta kwashe ta mayar U.S account din ta ta rufe account din in kuma zata bar shi to, Aalimah sai hawaye, ta rasa bakin godiya, tace bayan dawainiyar da suka sha da ita wata da watanni, kuma har da karin wannan dawainiyar. Uncle Suraj Kashim yace “akul! Ta sake kira masa dawainiya, dole ne yayiwa Asseya da ‘ya’yan ta dawainiyar don bata da kowa sai shi�. Da haka suka yi sallama Aalimah na ta kuka. Don ji take kamar wannan shine lokaci na farko da zata je gidan miji.
Basu samu sunyi barci ba don suna shigowa lokacin sallar asubah na yi. Sallah suka yi daga nan suka kimtsa. Chauffeur na hotel din shi ya kaisu filin jirgi tare da kayan su.
******
A cikin jirgi Aalimah ta kwantar da kai a kafadun Mu’azzam, rayuwarta bakidaya ta dinga gilma mata tamkar a majigi. Ta faro ne daga zuwanta Boston, inda daga nan tarihin rayuwar ta ya fara, rayuwarta gidansu Mu’azazam, haduwar ta da Aboulkhair, aurensu har zuwa rabuwar su. Aurenta da Mu’azazam da irin kalubalen data fuskanta a cikin auren, haihuwarsu zuwa rabuwarsu da kuma kalubalen data fuskanta a cikin rabuwar. Har kuma zuwa yau da Ubangiji ya sake binding dinsu together. Hakan kadai ya ishi bawa ya yarda Ubangiji Subhana mai yawan hikima ne, komai yayi kada bawa yasanya ayar tambaya. Duk abinda ya tsara ya san dalilin yinsa. Data yi hakuri da kaddarar auren Mu’azzam yau gashi ta ci ribar hakurin ta. Ubangiji ya san cewa Mu’azzam shine mafi alkhairi gareta akan Aboulkhair shiyasa ya canza rayuwar su ta fuskar da ya ga dama. Hakurin data yi a zama da Mu’azzam bai tashi a banza ba. Hakika kowa ya bi iyayensa ya kuma fawwala al’amarinsa ga Allah zai iya masa.
The fact that ana son juna kamar a hadiye juna baya hana rabuwa a wa’adin da Allah ya tsara, ko ba’a mutu ba rayuwa tafe take da kaddarori kala-kala masu sabbaba rabuwar. Kuma karfin soyayya baya hana karewar aure a wa’adin da Ubangiji ya nufa. Wannan shine ya faru tsakanin ta da Aboulkhair wanda har abada bazata manta ba a karkashin zuciyar ta. Abu guda take da tabbacinsa; daga ranar da ta soma son Mu’azzam a matsayinsa na mijinta, daga ranar da ta zama sirrin Mu’azzam ya zama sirrinta, gabadaya rayuwar data yi da Aboulkhair ta zama shudadden al’amarin da bata sake tunawa da wani feeling ba. Aboulkhair ya rikide ya juye ya koma kamar Yaya Aboubacar a idanunta.
******
Kada kaso kallon soyayyar data afku tsakanin Aalimah da Mu’azzam da yaransu a filin sauka da tashin jirage na garin Nevada (Las Vegas) a wannan rana, wadanda Harrison ya debo ya taho dasu don su tarbi iyayen nasu. It was so emotional da har ya fiddo hawaye daga idanun Aalimah. Kwannaki suka cigaba da juyewa zuwa satittika har Aalimah ta shiga watan haihuwar ta.
A wadannan satittikan numfashi ne kawai Mu’azzam baya yiwa Aalimah sabida tattali da soyayya. Idan ofis ya tafi hankalinsa yana kansu, Allah-Allah yake ya dawo gida ya tadda su, idan yana gida lokutansa nata ne. Har Allah ya nufi Aalimah da haihuwa lafiya ta haifi da namiji tamkar Mu’azzam yayi kakhi ya tofar.
Wannan karon rigima ta barke tsakanin matar da mijin kan sunan da za’a sanyawa yaron, Mu’azzam yace wancan lokacin ya bata dama ta sa Basmah wannan karon ta bar masa Malam Raazee zai sa, ita kuma ta dage Daddy 1 (Ishaq) za’a sanya, bazata taba manta gudummuwar sa da soyayyar sa cikin rayuwarta ba, cikin halin dadi ko sauyin rayuwar da suka samu kansu. Rigima kafin ranar suna tsakaninsu ta ki karewa har kunnen Daddy 2. Ba da wata-wata ba ya bi bayan Mu’azzam yace ta bari asa tsohonsu, shekara mai zuwa war haka tasa himma ta sake haifowa sai asa mata Ishaq din. Tsohon mu mai ran karfe ki bari mu samu magajinsa. Aalimah tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka tace “Daddy, abinda yasa nace asa Daddy 1 sabida Khaleesat ta saka Malam recently ko wata biyu ba’a yi ba� Daddy yace “Malam Raazee ai baya isar mu, ya kamata a ce dukkan ku ya kasance cikin ‘ya’yan ku da Malam Raazee, na Khaleesat daban naki daban�. Aalimah ta sakar masu don sun fita gaskiya.
Ranar suna Mu’azzam ya yiwa jaririnsa khutbah da suna Ibrahim (Sarham). Lokacin da ya kira Malam Raazee ya gaya masa baya jin dadi, jikin girma ya motsa masa, a kwance yake amma don farin ciki cewa yayi wannan karon sai ya taka kafafunsa gidan Mu’azzam har kasar Amurka.
Shi da Oncle Oussama da Eidrissa Mu’azzam ya yi wa visa zuwa U.S. Duk da tsufa da karancin koshin lafiya yace sai yaje gidan Mu’azzam koda sau daya ne a rayuwar sa. Mu’azzam din kuma ya kudurce a ransa zai yi amfani da damar a duba masa lafiyar Malam din sosai. Mummy, Gumsu, Daddy 1 da Daddy 2, Mama Aseeya, Hamoud da matarsa Khaleesat, Aboubacar da matarsa Basmah duk haka suka dunguma zuwa birnin Las Vegas. In da suka tarar da Dr. Aboulkhair da iyalin sa (Sa’eedah da danta Abu Turab) suma sun zo daga Boston don halartar sunan Sarham.
Aalimah ta kasa tsaye ta kasa zaune da shirin tarbar iyaye da ‘yan uwansu, wadanda za su zo takanas don taya su murnar alherin da ya same su na karin girman da Mu’azzam ya samu a CHEVRON da kuma haihuwar magajin Malam wato Sarham. Ita da Aunty Sa’eedah ke ta wannan shirye-shiryen tun gabanin zuwan bakin nasu da kwanaki uku. Kafin bakin su iso hatta cokalin da za su ci abinci sun tanada. Sun yi time-table na girke-girken da zasu ke musu a kullum a tsayin kwana bakwai da za su yi tare da su. Sun tsara za su rike matan a nan gidan Mu’azzam tunda yana da girma, Malam Raazee ma a gidan zai zauna, sun gyare masa daki a downstairs kada ya sha wahalar hawa bene, maza kuma tuni Mu’azzam ya kama musu hotel din da za su sauka.
A ranar da za su iso, bakidaya iyalin Mu’azzam dana Aboulkhair suka dunguma filin jirgin saman (John F. Kennedy) suka tarbo su zuwa gida.
Mummy Zulaiha don farin ciki tana arba da Mu’azzam da Aboulkhair tsaye a tare, sun juya baya suna magana da junansu, ta tuno lokutan data kwashe cikin kukan zuci dana fili, na tunanin Aboulkhair ya bar su kenan har abada, da lalurar Mu’azzam da bata taba barin ta kwanciyar hankali ba tsayin shekaru masu yawa, hakan kadai ya ishi bawa ya kara imani, ya tsoraci Allah, mutuwa ba karya bace, tana iya zuwa a kowanne lokaci babu notice, bazamu taba guje mata ba, sai in lokaci bai yi ba, haka rashin lafiya duk arzikin ka da gatan ka sai idan Ubangiji ya ga damar yaye maka a lokacin da ya so. Ji kawai suka yi Mummy ta rungume su ta baya su duka biyun ta saki kuka mai sauti tana hamdala a fili. Dukkan su sai suka sanyata a tsakiyar su suka rungumeta suna lallashin ta.
Ko da suka iso gida hira ce ta yaushe gamo ta tsinke a tsakanin wannan family don daga Aboulkhair har Mu’azzam da iyalinsu sun kwashi lokaci ba su je gida ba. Gumsu nata aikin nata na bada dariya, ba ruwanta da surukai ko Kakanni, komai ya zo bakin ta fade take.
Aalimah da Sa’eedah suka hade da su Basma da Khaleesat, Yesmin da karamarsu Nurat suka yi ta dawainiya da iyayensu da Kakansu. Kowaccen su ta aje iyali abin gwanin ban sha’awa. Yau Basma da Aalimah da Khaleesat har rayuwar Boston sai da aka tabo aka dara cikin nishadi.
Masha Allahu laquwwata illa billah.
Karshen littafin AALIMAH kenan.
Kuskuren da ke ciki ku taya ni rokon Allah ya yafe mini. Alherin da ke ciki, Allah ya raba mana ladarsa ni da ku bakidaya.
Taku har abada; Sumayyah Abdulkadir.
TAKORI
Karin Bayani
Na samu fatawar malamai mabanbanta akan makomar auren Aalimah da Mu’azzam, bayan bayyanar Aboulkhair, fahimta fuska, wasu malaman sun ce miji na farko shi ke da mata amma wannan fatawar ta tsaya ne akan shekaru hudu da bacewar mijin bai bayyana ba, kuma babu iddar mutuwa, Abulkhair sai bayan shekaru bakwai ya bayyana, sannan da iddar mutuwa, don haka nayi amfani da mafi rinjayen fatawar malamai wadda tace miji na biyu keda mata, ko a bata zabi ita matar, ta zabi wanda take son cigaba da zama da shi a tsakanin su biyun in bayan shekaru hudu ne kuma bata yi khul’iy ba. Allah shine mafi sani. Wallahu a’alam Allah shine mafi sani. Idan nayi kuskure ina rokon Allah ya yafe mini.
No comments