Abul Khair Complete Hausa Novel
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:* ✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga mahaifiya ta Abar Alfahari na, uwata maganin kuka na, I Love You so Much Momma ❤️, Allah ya taimake ki da taimakon sa._ 😭
_Bismillahir rahmanir Rahim, in the Name of Allah the most Beneficient, the most marcerfull praise be to God Lord of the words.._
_My Follow Fans, I'm starting my New Book, I ask Allah subhanahu wata'ala to guide me through and make me it sussufull till End. Amin ya Allah._ 🤲🏽
*________________________________*
*PAGE* 1
*________* *ALH. HAYAT SUNUSI* da Matar sa *BARRISTER DEEBIZAH* _(Khadeejah Yunusa Ubale)_ kamar yanda kuka sani a Littafin *LABARIN DEEBIZAH,* mazaunan Kano ne, kuma har yanzu ɗin suna cikin Kano da zama, yanzu haka suna da yara biyar da suka haifa.
*ABUL-KHAIRI* Shi ne ɗan su na farko, me sunan mahaifin Brr. Deebizah wato *YUNUSA,* lokacin da aka haife shi time ɗin Brr. Deebizah tana shirin shiga B.U.K ne, hakan yasa tun daga kansa suka jingirta da haihuwar har sai da ta kammala karatun ta, sannan ta sake ɗaukan wani cikin, lokacin ABUL KHAIRI na da shekaru 7 a duniya sannan aka haifi ƙanwar sa, yarinyan ta ci sunan Kakar Alh. Hayat ne (wato Gwaggo) Zainab, sai dai basu ɓoye mata sunan ba; da Zee suke kiran ta, a cewar Gwaggo gwara a kira Takwaran ta da sunan ta ya fi, Allah da ikon sa kuma an haifi Zee da watanni biyar Gwaggon ta rasu, sosai mutuwar ya girgiza ahalin su duk da kasancewar ta tsohuwa, sai dai Gwaggo mace ce me tsananin kirki da daɗin zama, musamman ma Alh. Hayat ya fi jin mutuwar ta fiye da kowa, sabida duk a cikin jikokin ta tafi ƙaunar sa, kuma sun fi shaƙuwa matuƙa.
Bayan Zee Brr. Deebizah da yanzu suke kiran ta Mamy, ta sake haihuwar ɗa na miji, sai dai be zo da rai ba tun sanda aka haife sa, daga shi kuma sai da Zee tayi shekaru uku da watanni kafin ta sake haihuwar Fatimah, suna kiran ta da Batool kasancewar sunan ƙanwar Mamy ne, kuma sunan kishiyar Mahaifiyar Alh. Hayat ne, Falmata.
Daga Batool kuma sai Sunusi me sunan Mahaifin Alh. Hayat, suna kiran sa Amir, sai kuma Auta Maryam, wacce taci sunan Maman Brr. Deebizah, suna ce mata Baby, sai dai kasancewar Brr. Deebizah (Mamy) tana ce mata Auta na, shiyasa gaba ɗaya gidan hakan suke kiran ta, ya fi kama bakin su a kan Baby ɗin.
Yanzu haka Zee tayi aure watanni Goma kenan, sai dai bata haihu ba, but tana da ciki yanzu haka.
Waɗannan su ne iyalan gidan Alh Hayat (Abba), ku bi Ni a sannu don jin Labarin rayuwan *ABUL-KHAIRI* da iyalan gidan su.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Lumsassun idanuwan sa da suke cike taf da barci ya ware su a kan ta
Tana kwance gefen sa, hannun ta ɗaya saman ƙirjin sa da babu riga, barci itama take shararawa wanda yayi wa cuty face ɗin ta kyau matuƙa.
Idanu kawai ya zuba mata cike da takaicin ganin ta kusa dashi, sake ware idanuwan sa da suka sauya kala zuwa ja yayi, ya mayar dasu kan hannun ta dake ƙirjin sa, dogon tsaki yaja kafin ya saka hannayen sa biyu ya riƙo hannun nata ya sauke kan jikin sa ya yarfar dashi
Wanda hakan sai da yasa taji zafi sosai cikin barcin ta, babu shiri ta farka tana zare idanu ba tare da ta motsa ba
Shi kuwa tuni ya ma sauka a kan gadon, yana gyara rigan zuwa jikin sa, tare da ɓame bottles ɗin gaban rigan da suke a buɗe gaba ɗaya
Kallon sa kawai take yi tana karantan yanayin sa, sai da ta gama ƙare masa kallo har ya gama abinda yake yi, ya zari makulle zai fice ba tare da ya sake kallon ko inda take ba, ai kamar ƙiftawar ido ta dira daga kan gadon ta sha gaban sa da sauri, har da saka hannu tana kare sa alamun bazai wuce ba
Sauke idanun sa yayi a kan ta cikin ɓacin rai da ya nuna a face ɗin sa, sai dai be iya ce mata komi ba illa kallon ta da yake yi yana sake haɗe rai
Ita kuma yatsina kyakykyawar fuskar ta tayi, kafin ta kafa masa manyan idanuwan ta tace, "Wai ina zaka je ne ka bar Ni bayan kasan me ya kawo Ni wajen ka? Bie babu inda zaka je wlh sai mun tsayar da maganar mu, tunda ka ƙi ɗaukar waya ta to na biyo ka". Sai kuma taja numfashi tana ci gaba da faɗin, "Wlh idan har baka yarda da buƙata ta ba Bie, na rantse da Allah zan nemi mafita kamar yanda na faɗa maka, kasan kuma Ni ɗin ina da waɗanda suke jira na in Kai musu kain..."
"ZIYA.." Yafaɗa da ƙarfi cikin tsananin ɓacin rai da ya ninka wanda yake ciki, lokaci ɗaya farar fuskar sa ta sauya kala tayi jazur, haka ma jijiyoyin kansa sosai suka fito raɗau
Ƴar siririyan dariya ta saki tana kallon yanda gaba ɗaya ya sauya lokaci ɗaya, hakan kuma sosai ya faranta mata don ta fi son yayi zuciya yabi ra'ayin ta, cikin yatsina tace, "kar ka yimin tsawa Bie, kasan bazan ɗauka ba, kuma kabar tunanin bazan iya rabuwa da kai bane, wlh a kan haka sai mu raba hanya.."
Damtsen hannun ta da ya damƙe ƙam, shi ya hana ta ƙarisa maganar ta, domin sosai zafin ya shige ta
Matso da fuskar sa kusa da nata yayi yana huci, idanun sa sun sake yin jazur fiye dana da, cikin amon muryan sa me haɗe da fushi yace, "Wlh kinji na rantse miki idan har kika ba ma wani daman riƙe hannun ki; ba shiga jikin ki ba ma, wlh wlh sai kinyi dana-sanin sani na a rayuwan ki! bazan hana ki rabuwa dani ba, sannan bazan hana ki aika ta duk abinda kike so ba, fine ki aika ta kinji ko?" Ya ƙarike maganar da girgiza ta yana ware mata jajayen idanun sa, sai kuma ya janye ta daga gaban sa ya nufi ƙofa dasauri ya fice
Duk da ba wani jan ta yayi ba sai da ta faɗi ƙasa sabida rashin ƙwarin jiki, ƙofan tabi da kallo cike da tsoro a ranta, babu shakka ta san Kishin da yake mata zai iya aikata komi, idan tace komi tana nufin komi zai iya yi a kan ta, sai dai kuma ba ta tunanin zata nuna tsoro ko gajiyawa da buƙatan ta, domin baza ta zauna dashi ba ya biya mata buƙatan ta ba, sannan kuma ya hana ta zuwa inda za'a biya mata, tabbas zata ci gaba da tunzura sa don ganin ta cin ma burin ta
Itama miƙe wa tayi ta zura Takalman ta, sannan ta ɗau gyalen ta; ta rataya a kafaɗa ta fice da sauri.
▪️▪️▪️
Motan sa ya gangarar da ita gefen titi, babu abinda zuciyar sa ke yi sai suya, iska kawai yake faman fesar wa daga bakin sa yana riƙe da sitiyarin motan, ya rasa meke masa daɗi a lokacin, sabida kalaman ta daga jiya zuwa yau sai kai komo suke masa a rai
Hannu ya saka ya soma hargitsa gashin kansa cike da tsagwaron KISHI dake cin sa, sai kuma ya kwantar da kansa jikin kujeran yana lumshe kyawawan idanun sa, ya jima a haka be ɗago ba illa numfashi da yake sauke wa yana faman ci je leɓe, daga ƙarshe kuma yayi wa motan keey ya fige ta da gudu yayi gida.
Gate man na buɗe masa Gate ɗin gidan ya kutsa motan ciki, a parcking space yaja birki yana kashe motan, sai dai be yi yunƙurin fitowa ba illa ma gyara zaman sa da yayi yana dafe kansa.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Eyeglasess ɗin fuskarta ta sake gyara masa zama a kan cikakkiyar kamilalliyar farar fuskar ta, murmushi yalwace a fuskar ta take kallon su tana magana, "Ba na son ku je ku zauna a can har in kira waya, idan kuwa kuka bari na aikata hakan, to Ni da ku ne, don kun san bazan sake barin ku zuwa ba".
Da sauri Batool ta dafa gwiwowin ta, har da ranƙwafo da kanta tana faɗin, "Wlh Mamy baza mu daɗe ba, idan muka je ma muna gaishe ta da jiki zamu dawo".
Jinjina kanta Mamy tayi kafin ta maida idanun ta kan Maimuna tace, "je ki kira min Aƙilun zan ba sa saƙo ne".
Da sauri Maimuna ta tashi ta fice daga ɗakin Mamyn, da gudu ta nufi hanyan parlour, ta buɗe ƙofan fita tana shirin saka kai waje taji tayi karo da mutum, kafin ta tabbatar da wanda suka ci karon, sai ji tayi an janye ta da ƙarfi an yi wurgi da ita gefe, ai babu shiri ta saki siririyan ƙara jin ta faɗa a saman hannun ta, da sauri ta ɗago kanta tana bin sa da kallo idanuwan ta cike fal da hawaye
Shi kuwa be ma bi ta kanta ba, ya taka ya shige fuskar sa a ɗaure tamau kamar be taɓa dariya ba
Bata dena kallon sa ba har ya shige ɗakin Mamy, sai taja majina tana matse idanunta hawayen ciki suka samu daman zubo wa, jiki babu ƙwari ta tashi ta fice don kiran Aƙilu drever'n su.
Tura ƙofan yayi da sallama ciki-ciki
Mamy da Batool suka amsa mishi duk kan su suna juya wa ga ƙofan, da sauri Batool ta miƙe ta nufi ƙofan tana mishi sannu da zuwa
Be amsa ta ba, ita kuma ta fice abun ta
Tako wa yayi ya zauna a kan kujeran dake cikin ɗakin, hakan yasa yake fuskantan Mamy dake zaune gefen gadon ta tana kallon sa
"Baba na lafiya kuwa?" Ta tambaye shi cike da kulawa sabida sauyawan da ta gani a tattare dashi
Sakin faukar sa yayi sosai yana ƙoƙarin dai-dai ta kansa, cikin ƙwaƙulo murmushi yace da ita, "Mamy lafiya ƙalau me kika gani?"
Hakan yasa ta saki murmushi wanda ya zame mata ɗabi'a, koda yaushe fuskar ta a sake yake cike da annurin fara'a, sake tsare sa da idanu tayi tace, "Baba na kana son ɓoye min halin da kake ciki ko? Jiya haka ka wuni da ɓacin rai, yanzu ma ga shi ka dawo a yanayin, but kana son ɓoye min, Why?"
Sosa Kansa yayi cike da basarwa yace, "Mamy babu komi fa, ki yarda dani, idan da akwai ke ce ta farko da zan sanar ma wa".
Mamy ta murmusa cike da ƙaunar ɗan nata, shi dai daban yake cikin ƴaƴan ta, koda yaushe a zurfin ciki yake, idan har abu ba yayi tsamari bane, ba ya iya fitowa fili ya sanar musu su da suke iyayen sa, ya dinga ƙunbiya-ƙunbiya dashi kenan a ransa, sai dai wuni yana cikin ƙunci da ɓacin rai, wanda hakan ya jawo ba kasafai zaka ga yana shiga cikin jama'a yana walwala ba..
"Mamy har yanzu Abba be dawo bane?" Maganar sa ta katse mata guntun tunanin ta
"Be dawo ba, lafiya dai ko? In ce dai ba wani abun ka samo zaka ba shi Ni ka hana Ni ba?". Tayi maganar cike da barkwanci
Hakan ya saka shi sakin yalwataccen murmushin da ya fito da jerin haƙoran sa
Sanyi taji a ranta ganin ya ɗan saki ransa fiye da ɗazu ɗin, hakan yasa taci gaba da jan sa da hiran tsokana don dai ta dawo mishi da walwalan sa
Shiyasa sau tari yafi ƙaunar kasancewar ta kusa dashi fiye da kowa a duniyar nan, tabbas uwa daban ce, a duk sanda yake cikin matsala, ita ke fara gane damuwar sa fiye da kowa dake gidan, that's why yake tsananin ƙaunar mahaifiyar shi fiye da komi da kowa dake cikin duniya.
▪️▪️▪️
Koda Maimuna ta dawo kiran Aƙilu drever, zaman ta tayi a Parlour ba tare da tayi yunƙurin komawa cikin ɗakin Mamyn ba.
Tana zaman itama Batool ta fito ta zauna gefen ta tana tambayan ta, "shin ta kira Aƙilun?"
Kafin ma taba ta amsa Aƙilu ya shigo yana baza idanuwa cikin parlour'n, hannun sa ɗaya riƙe da aswakin da ya cire daga bakin sa ya ƙariso cikin parlour'n, ya zube ƙasa yana faman washe baki tare da yiwa Batool kirarin da ya saba
Ita kuwa nan ta biye masa suna kwasan dariyan Aƙilun daga ita har Maimuna, kasancewar sun fi saba wa da Batool ɗin, kullum suna cikin surutu da junan su, ita kuma Maimuna koda yaushe dama nata ido ne idan suna yi, sai kuma ta dara idan abun ya bata dariya, idan kuma sun sako ta sai ta tsulmiya baki, dayake ita ɗin ba me yawan surutu bane, bata da hayaniya ko kaɗan.
Lokacin ne Mamy da ABUL KHAIRI suka fito daga ɗaki
Kai tsaye ABUL KHAIRI hanyan ɗakin sa ya wuce ko kallon inda suke be yi ba
Mamy ne ta ƙariso cikin parlour'n ta zauna tana amsa gaisuwar Aƙilun, sannan ta kalli Maimuna tace, "Maimuna tashi ki haɗa wa yayan ku abincin sa ki kai masa".
Amsa mata tayi da "Toh". tana miƙe wa tsaye, ta kalli Batool tana mata alama da ido ta biyo ta
Maƙe kafaɗa Batool tayi tana mata dariya ƙasa-ƙasa
Sai Maimunan ta marairaice fuska ta soma tafiya, har da haɗe hannayen ta biyu alamun roƙo
Amma ƙiri-ƙiri Batool ta ƙi motsa wa, sai ma gwalo da tabi ta dashi
Babu yanda ta iya haka ta nufi kichen jiki a sanyaye, tasan halin Yayan nasu yanzu abu kaɗan zaka yi masa kuskure yaci uban ka, bare ma shi da ya tsane ta fiye da kowa dake gidan, ko kaɗan bata san meyasa ba ya ƙaunar ganin ta ba, shiyasa ba ta son ma a aike ta wajen sa bare tayi kuskuren abun da zai haɗa su.
Ita Mamy tuni ta maida hankalin ta kan Aƙilu tana ba shi saƙo, sai kuma ta juyo tana kallon Batool ɗin tace, "ke baza ki je ki shirya bane kin zauna? Ai kuwa idan Abban ku ya dawo ya hana ku fita babu ruwana, ki zauna kasa kunne kina ji na kar ki tashi ki wuce".
Da sauri Batool ɗin ta tashi tayi hanyan ɗakin su tana faɗin "wlh Mamy Ni ban ma ji me kuke cewa ba".
Itama Mamy bata tanka ta ba tamayar da hankalin ta ga Aƙilu tana sallaman sa.
Lokacin ne Maimuna ta fito daga kichen riƙe da Faranti a hannun ta, kanta tsaye ta nufi ɗakin ABUL KHAIRI ta soma Nocking a bakin ƙofan, sai dai har ta gaji babu amsa, dole ta haƙura ta tura ƙofan ta shiga da sallama.
Yana zaune a bakin gadon sa idanun sa kafe a kan ƙofan, ashe duk yana jin Nocking ɗin but yaƙi amsa wa
Shiyasa tana shigowa idanun su suka haɗe cikin na juna, saurin sad da kanta ƙasa tayi gaban ta na matsanancin faɗuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar ta haɗa idanu dashi sabida kwarjinin da yake mata, shi kaɗai ne mutumin da idan suka haɗa idanu dashi take jin daban a cikin rayuwan ta, tana shiga wani yanayi da har yanzu ta kasa fassara shi
Jiki a sanyaye ta ƙariso cikin ɗakin, ta nufi gefen sa inda Centre table ke ajiye gaban gadon da yake zaune, akai ta ajiye farantin muryan ta na ɗan rawa ta soma gaishe shi, tare da son isar da saƙon abincin daga Mamy
Amma kuma ko ci kanki be ce mata ba
Don haka ta juya da ninyan fice wa ba tare da ta kalle sa ba, sai jin saukar dakakkiyar muryan sa tayi yana faɗin
"Kee Ina zaki je da wani dogon goshin ki a nan wajen? Wa kika bari ya zuba miki?"
Saurin juyowa tayi kanta a ƙasa ta duƙa ta soma zuba masa abincin a cikin Plate, sai da ta gama sannan ta zuba masa Coke cikin Cup; tunda ta san yana so sosai, kuma ko ta tafi zai iya dawo da ita, shiyasa tayi gwanintan zuba masa kar tayi laifi
Mi ƙe wa tayi da zumman tafiya, sai ji tayi an riƙe ta.
😲 _Hmmm wannan salon labarin na daban ne, shin wace ce ma wannan Maimunan? Me ya kawo ta gidan nan har take zaune da ahalin ABUL KHAIRI?_
_shin wace ce Ziya?_
_Ni dai taku JIKAR LAWALI Ni ce nake da amsoshin tambayoyin ku, ku kasance dani don jin ya za'a kaya?_
_kar ku manta comments ɗin ku kaɗai nake buƙata, idan har yayi muku to ina son nima ku faranta min ta hanyar comments, sannan kar ku manta ku yi following ɗina a Wattpad da kuma bakandamiya, sannan ku danna min Vote. Nagode_
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:* ✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
𝗣.𝗪.𝗔✍️
*JIKAR LAWALI CE* ✍️
*Wattpad: UmmuDahirah* 👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga mahaifiya ta Abar Alfahari na, uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma._ ❤️
*________________________________*
*PAGE 2*
*________* Da sauri ta juyo domin a tunanin ta shi ne, saɓanin tunanin ta ashe ƙasan rigan ta ne ya maƙale a jikin Centre table ɗin
Shi ko kallon inda take ma be yi ba, duk da kuwa yana ganin abinda ke faruwa
Jiki na rawa taja rigan ta da sauri, wanda hakan ya ja Centre table ɗin; Cup ɗin dake kai yayi tambal-tambal ya zubo saman cerfet ɗin gaba ɗaya, kasancewar dama a baki-bakin table ɗin ta ajiye. "Innalillahi.." tafaɗa a matuƙar firgice tana kai hannayen ta duka kan bakin ta ta rufe, tare da zaro idanuwan ta kan shi jikin ta na rawa
Zuba mata idanu kawai yayi fuskar sa a murtuke tamkar be taɓa sanin wani fara'a ba
Hakan ne ya sake tsorata ta; ta duƙe ƙasa da sauri, bakin ta na rawa ta soma ba shi haƙuri
Sai dai kamar tana yi da dutse, duk da kuwa be cire idanun sa a kanta ba
Cup ɗin ta ɗauke daga ƙasa ta'ajiye saman table ɗin, ta miƙe da sauri don zuwa ɗauko abun goge wa tun kafin ya natse a cikin cerfet ɗin
Mi ƙe wa yayi da sauri ya saka mata ƙafa, sai jin ta tayi a ƙasa timm a ruf da ciki, hakan yasa ta bugu sosai har ta bige haɓan ta, duk da Allah ya so ta cerfet ɗin ɗakin me taushi ne, amma sai da taji zafi sosai wanda yasa ta saki ƙara me haɗe da kuka
Shi kuwa tuni ya koma mazaunin sa tamkar ba shi ne yayi aika-aikan nan ba, sai ma ɗauke kai da yayi yana faɗin, "idan na ƙirga biyu baki bayyana a gaba na ba, wlh sai na fitar miki da haƙora".
Babu shiri ta yunƙura ta tashi, ta rarrafo gaban sa tana ci gaba da kukan ta har da ƙara Volume
"Rufe bakin". Ya daka mata tsawa da faɗan hakan
Da sauri ta saka hannu ta kama bakin ta tana runtse idanu jikin ta na mazari
Kallon ta kawai yake yi yana nazartan ta, sai ya ja dogon tsaki cike da takaicin abinda ya tuna yana cewa, "ta shi ki je Toilet ki ɗauko abin Moping ki gyara min wajen, shashashan yarinya".
Still jikin ta na rawa ta tashi tabi umarnin abinda yace mata
Shi kuwa kwanciya yayi yana lumshe idanuwan sa, shi kaɗai yasan halin da yake ciki a wannan lokacin, har yanzu ya kasa samun nutsuwa a zuciyar sa, yasan halin Ziya sarai, ya kuma san me zata iya aikata wa tunda ba hankali ne da ita ba, dole ya nemo mafita, fushi ba nasa bane yanzu, shawaran da zuciyar sa ta ba shi dashi zai yi amfani..
Har Maimuna ta gama gyara wajen be ma sani ba, sai buɗe idanu yayi ya hangi bayan ta ta buɗe ƙofa ta fice, tsaki ya ja cike da tsanar yarinyan, shi fa gaskiya ba ya tunanin zai iya rayuwa da wannan tatsitsiyan yarinyan, kallon ta kawai yake yi tamkar wata munafuka, sabida kullum a shiru-shiru take, irin su ne sumui-sumui kasau.. macijin ƙaiƙayi
Tashi yayi ya gyara zaman sa ya soma cin abincin sa.
▪️▪️▪️
Koda ta fita babu Mamy a parlour'n, don haka ta tsaya ta share hawayen ta da suke kwaranya saman fuskar ta, ɗakin su ta wuce kanta tsaye
Tana shiga Batool dake zaune gefen gadon ta, har ta rigada ta gama shiryawa ma, ta miƙe da sauri ta nufo ta tana tambayan ta "lafiya kika daɗe baki dawo ba?"
Duƙar da kanta ƙasa Maimuna tayi, hawayen da ta tsayar dasu don dole sai ga su sun soma kwaranya, dama ƙiris take jira ayi mata magana, sai ta soma gunjun kuka
Hankalin Batool a tashe ta riƙo ta tana sake tambayan ta "ko wani abun yayi mata?" Don itama ta rigada tasan halin Yayan su akwai mugunta
Ganin ta kasa yin mata magana, sai ta hau share mata hawayen tana bata haƙuri, "Sorry Sister kiyi haƙuri, kin san halin Yayan namu mugunta ne fal cikin sa, haka nan zamu riƙa haƙuri har Allah ya kawo ƙarshen zaman mu tare, ya haƙuri kinji ki dena kuka".
Shashsheƙan kuka take yi tana saka hannu itama tana share hawayen nata da suka ƙi tsaya wa, ba tare da tace uffan ba sai ajiyan zuciya da take faman sauke wa
Hannun ta Batool ta riƙo cike da tausayin ta tace, "kiyi haƙuri kinji? Yanzu mu je ki sauya kayan ki mu tafi".
Babu musu Maimunan ta nufi wajen gadon, inda Batool ɗin har ta fid do mata kayan da zata saka irin nata; da taji ta shiru bata dawo ba
Saka kayan tayi riga da skert na atamfa, fuskar ta kawai ta gyara ta saka Hijab ɗin ta kalan na Batool ɗin suka fito, sai da suka je ɗakin Mamy suka ce mata "sun tafi" kafin suka fito, drever ya ɗauke su suka bar gidan
Gidan su Juwairiyya ƙawar su, wacce suke school tare zasu je, mahaifiyar ta bata da lafiya shi ne suka yi mata alƙawarin zuwa duba ta.
Suna fita babu daɗe wa, su ma su Amir da Baby suka dawo daga school; school Bus ɗin su ta ajiye su a bakin Gate.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Sanda Ziyada ta fito daga gidan gonar ABUL KHAIRI, itama kai tsaye gidan su ta nufa, tana yin horn me gadi ya wangale mata Gate ɗin ta shige ciki, bayan ta fito daga cikin motan ta rufe ta nufi ciki
Momyn ta na parlour'n ƙasa tana kallo ta shigo ba tare da tayi sallama ba, sai ma kwaɗa wa mahaifiyar nata kira da take faman yi
"Kaiii wannan kira haka Daughter kamar zaki bani wani abun? Lafiya dai?"
Ƙarisowa tayi ta zauna kusa da ita tana shigewa jikin ta tamkar wata ƙaramar yarinya, sai dai tsaban sangarta ta da aka yi ne yasa ba ta shakkar shigewa jikin iyayen nata ko agaban waye kuwa
Shagwaɓa ta soma mata tana ƙorafin, "yunwa take ji"
Momy shafa kanta tayi tana faɗin, "ban da abun ki Daughter don kina jin yunwa sai ki zo kina min kiran mafarauta? Ai sai ki saka naji tsoro wlh, don zan yi tunanin wani abun aka yi miki".
Dariya Ziyada ta ƙyalƙyale dashi tana cewa, "kai Momy ke dai kin cika tsoro".
Murmushi kawai Momyn tayi, kana ta soma kwaɗa kiran me aikin su
Tana zuwa, taba ta umarnin ta kawo ma Ziyada abincin ta
Amsa mata tayi ta juya da sauri don cika umarnin ta.
Babu jimawa ta dawo da abincin ta kawo mata, sannan taje ta ɗauko mata drinks a fridge ta ajiye mata ta juya
Abincin Ziyada take ci suna hira da Momy, har sanda ta gama ta miƙe tana cewa, "Momy wai yaushe Dady zai dawo ne? Na matsu ya dawo wlh coz Ina da maganar da zamu yi".
"Mun yi waya dashi yanzu, zuwa 08:00pm. Yace zai shigo". Momy ta bata amsa da faɗin hakan
"Ok bari inje in ɗan yi wanka Momy zafi nake ji".
"To agwagwa Sarkin wanka".
Buga ƙafa ta soma yi tana mata shagwaɓa, wai don tace mata agwagwa
Sai da Momyn ta lallaɓa ta kafin ta wuce sama inda ɗakin ta yake
Tana shiga wankan ta soma yi, ta sauya kayan ta zuwa farar t.shirt dogo har gwiwar ta, sai ta saka leggings kalan ruwan ƙasa, ko ɗankwali bata saka a kanta ba tunda dama ba ta saba sawan bane, zama tayi kan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun ɗakin nata, ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana faman duba wayan ta, tsaki kawai ta dinga ja saboda ganin ABUL KHAIRI be kira ta ba, har ta danna masa kira saboda sosai take sha'awar jin muryan sa, duk da kuwa yanzu suka rabu but ya rigada ya sabar mata da koda yaushe suna manne a waya, sai kuma ta katse tana maida akalan kiran ga ƙawarta Rahina, tana jin ta amsa call ɗin ta gyara zaman ta tana jingina bayan ta a kujeran
"Hello Rahy kina gida ne?"
Daga can Rahina ta amsa mata tana me faɗin, "lafiya dai ta samu ne in zo?"
Sai da Ziyada ta saki numfashi kafin tace, "ina buƙatar ki wlh, akwai maganar da nake so muyi dake yanzu idan babu damuwa".
Rahina tace, "ok gani nan yanzu ɗin kuwa, dama ina kwance ne ina huta wa, amma yanzu zan zo".
"Ok sai kin zo". Ziyada tafaɗa tana cire wayan daga kunnen ta. Ajiye wa tayi tare da kwanciya tana rufe idanun ta.
Kamar mintuna 20 sai ga Rahina ta shigo ɗakin da sallaman ta
Tashi Ziyada tayi tana kallon ta tare da amsa mata
Rahina ta ƙariso ta zauna gefen ta tana faɗin, "ƙawata lafiya dai, kin ga yanda idanun ki suka yi ja, meke faruwa?"
Ɓata fuska Ziyada tayi tana shafa fuskarta, sai kuma ta cire hannun tana maida idanun ta kan Rahinan tace, "wlh Bie ne yake son bani matsala Rahy, na rasa ya zan yi". Taƙarishe maganar tana buga tagumi tamkar zata yi kuka
Hannu Rahina ta saka ta zame mata tagumin tana cewa, "dama maganar ba ta wuce na gizo da ƙoƙi, yanzu kuma me ya faru? Mene ne ya haɗa ku?"
Haɗe hannayen ta waje ɗaya tayi idanun ta a kan Rahinan tace, "kin san yanda Dady yake da burin in yi karatu me zurfi, ko kaɗan ba ya son maganar aure na da Bie da nake ta kawo masa, yace dole sai nan da two years sannan na haɗa degree ɗina, kuma kin san halin ABUL KHAIRI yana da taurin kai da kafe wa a abu ɗaya, shi yaƙi ya gane matsalan da nake ciki, yanzu a kan abinda be kai ya kawo ba ya dage bazai kusance ni ba dole sai mun yi aure, iyakan sa romancing ko kaɗan yaƙi ya bani haɗin kai, kuma zafin kishin sa ya hana Ni zuwa ga wani, wlh na kai limit ɗin da bazan iya jure wa ba, jiya munyi tsiya-tsiya dashi don nace zan nemi wanda zai biya min buƙata ta tunda shi bazai iya ba, shi ne yayi fushi sosai yaƙi nema na, Ni kuma na kasa jure wa sai na bi shi gidan gona amma kuma yau ma ya sake wulaƙanta Ni don na sake yin masa maganar". Taƙarishe maganar nata da jan numfashi fuskarta cike da damuwa
Rahina da ta zuba mata idanu tana sauraron ta, wani daɗi ne ya kamata, sai dai bata nuna a fuska ba sai ma nuna alhinin ta da tayi, ta saka hannu ta riƙo na Ziyadan tana faɗin, "to ke me kika yanke yanzu?"
"Shawarar ki nake nema Rahy, gaskiya Ni na gaji, bazan iya jira har muyi aure ba, kullum sai dai ya tada min da sha'awa amma babu biyan buƙata, ga shi kuma Saleem yana ta bibiya na naƙi ba shi dama, Ni yanzu na yanke shawara ne zan ba ma Saleem dama ba tare da sanin Bie ba, don wlh bazan iya bin ra'ayin sa ba, sai dai zuciyata tana cike da tsoron idan muka yi aure da Bie ya gane na ba da kaina a waje, ban san me zai faru ba ranan, don na san kashi na ya bushe, don wlh duk son da yake min zai iya rabuwa dani, Ni kuma tsoro na ya rabu dani, domin bazan iya rayuwa babu shi ba, Bie nawa ne Ni kaɗai, babu macen da ta isa ta shiga tsakanin mu ban kawar da ita ba". Sai tayi shiru tana maida idanun ta kan Rahina, sai kuma taci gaba da maganar, "Rahy ke kaɗai ce ƙawata da zan iya faɗa mata sirri na da Bie sabida tsantsan KISHI NA a kan ko wace mace, Yanzu shawaran ki nake nema, me kike ganin ya kamata in yi?"
Ajiyan zuciya Rahina ta sauke a hankali, ta ɗan muskuta zaman ta tana cewa, "tun farko dama nayi tunanin hakan zai iya faruwa ƙawata, wannan hanyan nake ta son nuna miki amma soyayyar ABUL KHAIRI ya rufe miki ido, sam kin kasa gane daɗin rayuwa, ke a ganin ki ABUL KHAIRI kaɗai zaki iya wa tanadin kanki, wa ya faɗa miki ana haka? Ai yanzu duniya ta waye wlh, idan kika ga mace tana zaune ba ta wannan harkan, to, tabbas bata waye bane, kinga kuma ke kina Big Girl ace kin zauna har yanzu baki san karatun nan ba, wlh maza da yawa suna kallon ki a wayayyiyan yarinya ce, but sai an zo aga ba haka ba, ina ce irin haka ne Saleem ya gani wajen ki yake son ƙulla alaƙa dake? amma kuma kin ƙi ba shi haɗin kai, kin yi watsi da zafafan Guys da suka zo wajen ki duk a kan ABUL KHAIRI, uhm ƙawata zan wayar dake abinda har yanzu kika kasa gane wa, shi fa wannan abun idan kika yi, wlh ba ABUL KHAIRI ba, ko da gogaggen ɗan duniya ne wanda ya san kan mata; ya fita ajikin wannan ya shiga jikin wancan, to sai kin so zai iya gane kin taɓa irin wannan harkan, yanzu duniya ta waye komi kika gani an rigada an tanadi mafitan sa, akwai wacce zan haɗa ki da ita ƙawata ce me siyar da maganin mata, wlh duk ƙwaƙwan mijin ki idan ya aure ki bazai taɓa gane namiji ya kusance ki ba, ke in faɗa miki ma; magungunan da zata baki kina amfani dashi kafin bikin ki tuni kin koma kin ɓame koda kuwa kin taɓa haihuwa ne, ko budurwa baza ta nuna miki budurci ba".
Tuni fara'a ya baibaye fuskar Ziyada saboda jin maganar ƙawarta, cikin zaƙuwa tace, "kina ganin ABUL KHAIRI bazai taɓa gane ba na tare da budurci na ba?".
Ɗan gajeren tsaki Rahy ta saki tace, "me aka yi akai ABUL KHAIRI ƙawata? Shi da be san ma kan komi ba sai idan ya aure ki".
Washe baki Ziyada tayi tana gyaɗa kanta, "Gaskiya ne Rahy, Bie be san wannan harkan ba, dani kaɗai yake iya haɗa jiki, tunda har yaƙi kusanta ta, to ina ga babu macen da Bie zai iya kusanta a faɗin duniyar nan idan har ba aure aka yi musu ba, na yarda da shawaran ki kuma zan bi".
Murmushi Rahina ta saki cike da murnan cin Nasara, kana ta sake gyara zaman ta taci gaba da ɗaura ta kan turban da take so, sai da tasan komi yayi tasiri a zuciyar Ziyada kafin ta tashi tayi mata sallama tace mata "zata tafi gida".
Rahy na fita Ziyada ta ɗauki wayan ta ta soma ƙoƙarin neman layin saurayin ta Saleem, shi kaɗai ta yarda zata iya harka dashi sabida shi zuciyarta tafi aminta dashi, domin dai a komi ABUL KHAIRI ba zai nuna wa Saleem ba, sai ma shi yafi shi, sai dai kuma zuciyarta ABUL KHAIRI take tsananin ƙauna ba wanin shi ba, shi kaɗai take iya kallo a masoyi kuma mijin da zata iya rayuwan aure dashi, tana mishi wani irin mahaukacin so da baki ma bazai iya faɗan sa ba, ta rigada ta sallama zuciyarta ga ABUL KHAIRI kamar yanda shima ya rigada ya mallaka mata nashi tuni.
Three missed calls tayi masa amma be ɗauka ba, don haka ta tura masa Text message a kan "su haɗu Gobe"
Kashe wayan tayi sabida kar ma ABUL KHAIRI ya same ta, a ranta tana fatan Allah yasa kafin goben ya sauya ra'ayin sa, ba sai ta je ga Saleem ba.
.
_Uhmmmm Mu je zuwa fans._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧*LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:* ✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A* ✍️
*JIKAR LAWALI CE* ✍️
*Wattpad UmmuDahirah* 👈
*SADAUKARWA*
𝙽𝚊 𝚜𝚊𝚍𝚊𝚞𝚔𝚊𝚛 𝚐𝚊 𝙼𝚊𝚑𝚊𝚒𝚏𝚒𝚢𝚊 𝚝𝚊 𝙰𝚋𝚊𝚛 𝙰𝚕𝚏𝚊𝚑𝚛𝚒 𝚗𝚊, 𝚞𝚠𝚊𝚝𝚊 𝚖𝚊𝚐𝚊𝚗𝚒𝚗 𝚔𝚞𝚔𝚊 𝚗𝚊, 𝙸 𝚕𝚘𝚟𝚎 𝚢𝚘𝚞 𝚜𝚘 𝚖𝚞𝚌𝚑 𝙼𝚘𝚖𝚖𝚊 ❤️
*NASIHA*
'''Sallah ta ƙwarai, ingantacciya, wadda aka yi ta cikin tawali'u da ƙasƙan da kai, tana haskaka zuciya, ta tsarkake ta, kana tana koya wa mai yin ta tsintar hanyar Ibada da abubuwan da suka rataya a kansa, waɗanda suka shafi Ubangijin sa, don kuwa ta sallah ɗin ce girma da ɗaukakar Ubangiji za su tabbata a zuciyar sa. Sallah tana sa mutum ya zama sahihi, mai gaskiya da riƙon amana, mai fahimtar abubuwa, mai kunya mai auna kome yake yi, mai yawan kyauta. Tana daɗa nuna masa cewa dai Allah Ɗaya ne, yana kuma jin tsoron sa, yana kuma girmama shi. Ta yin Sallah ne yake inganta rayuwar sa, ya tsarkake zuciyar sa, ya nisanci ƙarya da makirci, zamba, fushi da fariya, gaba, tauye wa mutane haƙƙi, rowa, ƙeta da rashin biyayya, da dai sauran miyagun halaye.
Sallah Ibada ce ta zuci da ta jiki. Mai yin ta zai haskaka da harshen Allah. Yin Sallah shi ne babbar alamar cikar imani, mafi darajar hanyoyin Ibada, kuma hanya mafi tabbata ta nuna godiya ga Allah saboda tarin baiwar da ya yi mana. Yin watsi da Sallah yana nesanta mutum da Allah, ya rasa rahamar sa da falalar sa da jin ƙan sa.
Martabar Sallah ta kai ma cewa mutum ba ya iya barin ta a cikin ko wane hali ya sami kansa. Dole ya kawo ta ko yana tafiya ko yana gida, ko cikin tsoro ko cikin aminci. Allah yasa mu dace.'''
*________________________________*
*PAGE 3&4*
*________* Sai da ya gama cin abincin sa kafin ya tashi ya nufi cikin Toilet, wanka yayi ya fito ɗaure da towel, be saka kaya ba sai da ya tsane jikin sa ya shafa Lotions sannan ya shirya cikin farin yadi, ɗinkin tazarce da yaji aiki da brown ɗin zare, turare ya fesa sama-sama ya zauna a gefen gadon sa. Wayan sa ya ɗauka ya soma neman Numban Ziya sabida zuciyar sa da ta hana sa sukuni, sai dai jin wayan a kashe yaja dogon tsaki yana wulwula ta a kan gadon, ya dafe kansa da hannu biyu tare da runtse idanun sa gam, zuciyar sa wani irin suya take masa tare da zafi, gaba ɗaya ta hana sa sukuni, shi ya rasa meyasa ya zama soko wawa a kan ƙaunar Ziyada ne, ko kaɗan ba ya iya jure fushi da ita, idan har suka samu saɓani shikenan ya rasa farin cikin sa da walwalan sa har sai ya samo mafita, idan kuma ba haka ba ya dinga zama kenan cikin ƙunci yana shan wahala da zuciyar sa. Soyayyar da yake ma Ziyada ya wuce kwatancen mutum, yana mata wani irin mahaukacin so tare da tsantsan kishin ta, wanda idan har ya rasa ta ba ya jin zai sake mintuna biyu a duniya, kallon fuskar Ziyada kaɗai ya ishe sa samun farin cikin duniya.
Numfashi ya fesar yana cire hannayen sa daga kan shi, ya miƙa hannu tsakiyan gadon da ya jefa wayan sa ya wawura ya soma typer mata Text, sassanyan kalamai me haɗe da ban haƙuri ya rubuta ya tura mata. Riƙe wayan yayi a hannu ya tsira mata idanu ba tare da ya ajiye ba, babu abinda zuciyar sa ke tsimaye sai son ganin kiran ta, ko kuma samun reply, but har mintoci suka shuɗe babu kiran Ziyada, dole ya ajiye wayan ya miƙe ya nufi gaban dressing mirror, ya ɗauki farin Wrest watch ɗin sa ya soma ɗaura wa a tsintsiyan hannun sa na dama, gaba ɗaya fuskar sa babu fara'a. Sai da ya gama saka wa sannan ya koma gefen gadon ya zauna, ya janyo cover Shoes ɗin sa dake ƙasan gadon ya soma zira wa, bayan ya gama ya miƙe tare da wayan sa da keey ɗin mota ya fice
Be shiga ɗakin Mamy ba tunda ya ga ba ta a Parlour, sai ya fice kansa tsaye
Sai dai yana fita haraban gidan ya haɗu da Abba da dawowar shi kenan, shi ya maido dashi ba da son ransa ba, a kan "zai raka sa wajen gaisuwa," haka suka koma ciki ABUL KHAIRI na zumɓura baki a ran sa, don dai bazai iya ce ma mahaifin sa wajen budurwa zai je ba, tunda har yanzu babu wanda ya san labarin Ziyada a gidan su, kuma shi ba kasafai yake son ƙarya ba.
Sai da Abba ya ci abinci kafin suka sake fita shi da ABUL KHAIRI.
Ba su daɗe da ficewan ba su Batool suka dawo
Lokacin Mamy na kichen tana ɗaura abincin dare
Don haka Hijab kaɗai suka cire suka shiga kichen ɗin taya ta, tunda gaba ɗaya tare suke haɗuwa su yi komi na gidan, Mamy ba ta son masu aiki shiyasa suke yi da kan su, duk da ita ɗin ba mazauniyan gida bane tana zuwa aikin ta, su kuma su Batool suna zuwa school, shiyasa idan da safe ne da wuri suke tashi su haɗa Breakfast su yi aiyukan su, wanki ne kaɗai suke da me musu, itama nan ƙasan layin su gidan ta yake, ita da kanta take zuwa ta kwasa taje tayi ta kuma goge, sannan ta dawo musu dashi
A cikin su kuma duk wanda ya riga dawowa zai ɗaura girkin rana, idan Mamy ta dawo Office da wuri sai ta ɗaura, idan kuma su Batool sun riga ta dawowa school sai su ɗaura, dayake ma Exams suke yi na S.S 2 Third time, that's why ba sa daɗe wa suke dawo wa.
Maimuna ita ta saki aikin kichen ɗin, ta koma Parlour don share wa, sai dai ma tuni Amir ya gama share wa yana ƙoƙarin yin Moping ne
Karɓa tayi tana masa dariya da cewa, "Ina kai ina aikin nan Amir? ina Auta na da ta barka kana aikin mata?"
Dariyan shima yayi yana faɗin, "wannan uwar son jikin, tana can ta hangame baki tana sharan barci a ɗakin Mamy, kuma ma ai baza ta iya komin ta ba, gwara Ni zan ɗan fi iyawa".
"Haka ne kuma".
Tana Moping ɗin yana taya ta da hira har ta gama, ta wuce ɗakin su don ta gyara can ɗin.
*MAIMUNA NASEER*
Maimuna ɗiya ce ga ƙanwar Mamy, _Ameera (Adama Yunusa Ubale),_ yanzu suna kiran ta da Ummu, Maimuna ita ce ƴa ta huɗu wajen Ummu. Yanzu haka shekarun ta 16years da haihuwa, ta dawo wajen Mamy ne tun sanda ta gama J.I.S 3 ɗin ta, yanzu haka school ɗin su ɗaya da Batool, kuma ajin su ɗaya tunda Sa'anni ne
Ta dawo wajen Mamy ne saboda wani dalili na iyayen su. Wanda za mu ji shi nan gaba.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Da dare suna zaune gaba ɗayan su a tsakar Parlour, abinci suke ci, dayake hakan suke yi sau tari ba sa zaman kan dainning, sai su shimfiɗa ledan cin abinci a tsakiyar parlour'n su ci a nan.
Sai da suka gama, Batool da Maimuna suka kwashe komi suka kai kichen sannan suka dawo.
Abba dake shan ruwa, yayi wa ABUL KHAIRI alamun ya dawo ya zauna, ganin ya tashi da ninyan shigewa ɗakin sa
Shi be ma kula ba, sai da Baby tayi masa magana
"Yaya, Abba yana maka alamu da hannu ka dawo".
Kallon ta yayi, sai kuma ya maida kallon nasa ga Abban
Time ɗin ya cire Cup ɗin daga bakin sa yana shirin ajiye wa yace, "Dawo nan mu yi magana".
Babu musu ya dawo ya zauna
"Yauwa wai me ke hana ka leƙa su Momy ne?" (yana nufin iyayen sa, wato kakannin su ABUL KHAIRI)
Mamy ta amshe maganar da cewa, "Nima dai abinda nake ta son mishi magana akai kenan, Mama ma har ta gaji itama tana min ƙorafi". (Kakar su ta wajen uwa)
Sosa Kai ABUL KHAIRI yayi yace, "Abba wlh time ne ba na samu, but insha Allahu zan ƙoƙarta in ga na je".
"Da dai ya fiye maka, kasan halin tsofaffin nan da naci, kuma babu ruwana idan suka sako ka gaba".
Murmushi Mamy tayi tace, "kai Abban su, har da kai?"
Shima murmushin yayi yana ɗaukan tufan da Batool ke yanka wa, yace, "to ai gaskiya na faɗa".
Murmushi Mamy kawai tayi, tana mayar da idanun ta kan ABUL KHAIRI tace, "babu wani uzuri da zaka ba mu Baba na, ka tabbatar ka samu time wannan weekend ɗin, sai ku tafi da ƙannin ka su ma su je su gaishe su".
Jin abinda Mamy tace ne, Batool da Maimuna suka kalli juna suna murmushi cike da murna
Shi dai ABUL KHAIRI amsa mata kawai yayi ya tashi ya wuce ɗaki, Allah-Allah yake yi ya keɓe don kiran sanyin idaniyan sa, sai dai duk saurin da yake yi wajen ya ga ya kira ta, amma har yanzu wayan ta a kashe ne, duk ya rasa sukuni, sai faman kira yake yi duk da kuwa ana faɗa masa a kashe layin yake, but be fasa ba, sai da ya gaji don kansa kafin yaja dogon tsaki cike da takaici ya ajiye wayan, tashi yayi ya shiga wanka
Be ɗau lokaci ba ya fito, ya shirya cikin brown ɗin jallabiya da gajeren wando fari, fitowa yayi Parlour don ya samu ruwa ya sha
Babu kowa sai Baby dake kwance tana gyan-gyaɗi
Ƙarisawa yayi gaban Fridge ɗin ya buɗe ya ɗauki goran ruwa Robber biyu, ajiye wa yayi saman Fridge ɗin sannan ya sake buɗe wa ya ɗauko Glasses Cup, zuba ruwan yayi ya sha sannan ya rufe sauran, sai da ya ɗauki ɗaya goran da raguwan ya tako wajen Baby, hannu ya saka ya ɗan ja mata hanci
Buɗe ido tayi tana kallon sa
Yace, "Autana barci kike yi rabin jikin ki a ƙasa? Tashi ki je ɗaki ki kwanta".
Tashi tayi ba tare da tayi magana ba ta wuce, don barci ne a idanun ta sosai
Shima ɗakin sa ya nufa ba tare da ya kashe t.vn dake aiki ba, don ya san mutanen gidan ba kwanciya suka yi ba zasu fito.
Washe gari ƙarfe 06:30am. Su Batool suka tashi daga barcin safen da suka koma, nan suka fito suka sami Mamy na haɗa Breakfast a kichen, gaishe ta suka yi su ma suka kama aiyukan da suke yi, sai da suka yi shara suka yi Moping ko ina kafin suka koma ɗaki don so ma shirin school
Itama time ɗin Mamy ta gama haɗa musu Breakfast ɗin, dayake Koko da ƙosai tayi musu, sai dankali da ƙwai da ta soya musu, ga wanda be son cin ƙosai sai yaci tunda ta san wasu ba sa so a cikin su, sai da ta jera komi a kan dainning kafin ta wuce ɗaki, time ɗin ma Abba shima ya gama shirin sa, sai ya fito Parlour don yin breakfast ɗin sa ya wuce, ita kuma ta shiga Toilet yin wanka.
Maimuna ita tayi wa Baby wanka ta shirya ta a kayan school ɗin ta, sannan itama ta shiga tayi lokacin har Batool tayi nata, sai da suka gama shiryawa suka fito yin breakfast
Lokacin Abba da ABUL KHAIRI tuni har sun wuce wajen aiki su.
Sai da school Bus ɗin su Batool ya zo sannan suka fice, Mamy kaɗai aka bari daga baya, itama tana gama shiryawa ta wuce nata wajen aikin.
▪️▪️▪️
Yau ma su Batool sun riga kowa dawowa, can suka baro Amir da Baby tunda dama Pepper ɗaya suke yi a rana
Koda suka dawo girkin rana suka ɗaura kamar yanda suka saba, suna cikin yi ne Zee tazo gidan, rungume ta suka yi suna murnan ganin ta, ita kuma sai tsokanar su take yi da ƴan biyun Mamy, dayake hakan take yawan ce musu, kasancewar suna kama da juna ainun, saboda duk kan su iyayen su mata suka biyo, kuma dama Mamy da Ummu suna tsananin kama basu da wani banbanci.
Tare suka gama girkin da Zee, sannan ta ɗaura faten tsaki nata don tasha, duk da cikin ta ya ɗan girma har yanzu bata dena kwaɗayi ba.
Wajen ƙarfe 01:00pm. Itama Mamy ta dawo, a tare suka shigo gidan da su Amir, su ma dawowan su kenan.
Zuwan Zee gidan, dama ta zo ne kawo wa Mamy kuɗin lefe da Uncle Abbas ya aiko ta dashi, (shine autan ɗakin su Mamy) yanzu haka ya kusa aure nan da wata ɗaya, shine zasu je haɗo masa kayan lefen, kasancewar Mamy ce babba dole ita ce zata ɗau ragaman komi.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Zuwa Ƙarfe 02:30pm. Shima ABUL KHAIRI ya dawo daga aikin sa, sanda ya shigo parlour'n Zee ce kaɗai zaune tana yanka ganye zata yi kwaɗon shi
Sallaman sa ta amsa tana kallon sa
Ƙarisa shigowa yayi shima idanun sa a kan ta
"Yaya sannu da zuwa".
A gaban ta ya tsaya yana amsa mata tare da ƙara wa da faɗin, "yau Uwar ƴan uku ce a gidan namu?"
Murmushi tayi tana ajiye wuƙan hannun ta tace, "kai Yaya don Allah ka dena min wannan fatan, ina Ni ina haihuwan Triple's?".
"Ok ba kya so kenan? Shin baki ji daɗi ba ma nayi miki fata na gari? A lokaci ɗaya kin haifo uku".
"A'a Ni yaya bana so wlh, kai baka san wahalan haihuwa bane tunda ba ku ke haifan ba, amma Ni dai gwara in haifi ɗai-ɗayan".
Hararan ta yayi yace, "dalla ji be ta sai kace ta san zafin haihuwar? Sai ki bari idan kin haihu kya yi maganar".
Dariya Zee tayi tace, "uhm Yaya me ya rage mana yanzu? ai lokaci kawai ake jira".
"Yarinyan nan baki da kunya, Ni kike faɗa wa haka ko?" Yayi maganar yana saka ƙafa ya biga nata, sannan ya kai hannu kanta zai ranƙwashe ta
Saurin kawar da kanta tayi tana turo baki tace, "kai yaya, kai yaya! Wai meye laifi na ne? Na girma fa yanzu na wuce duka".
Taɓe baki yayi yace, "don kinyi auren shi ne kika wuce duka? To Ni a waje na baki wuce ba, har yanzu kallon ki nake yi tamkar Auta na, kuma tsaf zan saka tsumagiya in zane miki jiki babu ruwana".
Ita dai Zee kumbura fuska tayi tana faɗin, "caf ɗi".
Ƙura mata ido yayi yana ci je leɓe, kafin yace, "me kika ce? Ban ji ba".
"Yaya Ni ban ce komi ba".
Kafaɗa ya ɗage yana nufan hanyan ɗakin Mamy yace, "ki ce Batool ta kawo min abinci ɗaki na".
"Tom". Ta'amsa mishi tana ci gaba da yankan latas ɗin ta
Sai kuma ta ɗaga murya tana kwaɗa wa Batool kira
Fitowa tayi da gudu tana amsa mata
"Ki je ki haɗo wa Ya ABUL abincin sa ya dawo".
Batool amsa mata tayi ta wuce kichen da sauri.
Lokacin shima ABUL KHAIRI ya fito daga ɗakin Mamy ya wuce ɗakin sa, yana shiga rage kayan jikin sa ya hau yi, ya rage daga shi sai Singlet da dogon wandon shaddar jikin sa, zama yayi gefen gado ya ɗau wayan sa ya soma kiran Ziyada, duk da be sa ran zai same ta ba, tunda tun jiya taƙi ta kunna wayan nata, da zaran ya kira Switch off. Sai dai yanzu ɗin ya yi Sa'a wayan a kunne take, but har ta katse ba'a ɗauka ba, sake kira yayi idanun sa ƙyam akan wayan.
Batool ce ta shigo da sallama
Ya ɗago kansa yana kallon ta, ciki-ciki ya amsa mata sallaman bayan ya maida idanun sa kan wayan sa
Ƙarisowa tayi ta ajiye abincin saman Centre table, sannan tayi masa sannu
Amma be amsa ta ba, don shi hankalin sa na ga wayan sa
Kamar yanda ta san halin sa, dole ne idan ka kawo masa abinci sai ka zuba masa, don haka bata tsaya tambayan sa ba ta hau buɗe coolarn don ta zuba masa.
Time ɗin ne Ziyada tayi peacking Call ɗin, don haka yayi saurin haye wa kan gadon sosai don yaji daɗin yin wayan, ya kalli Batool dake ƙoƙarin zuba abincin, ganin ba ta kallon sa sai yace, "tashi ki wuce".
Da sauri ta ɗago kai tana kallon sa
Shi kuma ya sake yin mata alama da hannu a kan ta fice, at the same time yana yiwa Ziyada sallama
Tashi Batool ɗin tayi ta fice abun ta.
Kwanciya yayi yana lumshe idanun sa jin zazzaƙan muryan Ziyada ta bugi kunnen sa, har wani ajiyan zuciya ya sauke sabida jin sanyin da ya ratsa shi, cikin ƙasa-ƙasa da murya ta yanda zai narkar mata da zuciya ya kira sunan ta
"ZIYA.. LOVE".
Daga can Ziyada itama gyara kwanciyar ta tayi kan makeken gadon ta, a ranta tana jin wani daɗi na ziyartan ta jin muryan mafi soyuwa a gare ta, sai dai kuma jan aji ya saka taƙi amsa mishi, tayi shiru abunta tana sake sauke numfashi, wanda ke dukan kunnen ABUL KHAIRI yana saukar masa da kasala tare da ƙara mishi wutan ƙaunar ta, ji yake yi kamar ya buɗe ido ya ganta a kusa dashi ya rungume ta ya nuna mata how much he missed her; and how much he love her, sai dai babu hali, don haka ya janyo pilow ya matse yana sake kiran sunan ta cikin wani irin murya da sai da ya saka ta amsa mishi babu shiri, don sosai wannan karon muryan nasa ya tsarga mata har cikin jini da ɓargo
"Wai ba na baki haƙuri ba, meyasaka kike fushi dani?"
Shiru tayi bata amsa shi ba, sai ma mutsu-mutsu da take faman yi
"ZIYAAA.. LOVE".
"Umm.." tafaɗa a hankali
"I say you are silent".
"Ba kai ne ba.." tayi maganar cikin shagwaɓan da ya sake zautar dashi
Domin abinda yafi ƙauna wajen ta yaji tana masa shagwaɓa
"Me nayi Ziya.. Love?". Ya tambaye ta a hankali
Shiru tayi masa
Sai ya sauke numfashi kafin yace, "Ziya.. Love kin san mene ne?"
Tace, "Um.. um".
"Meyasa kike son saka Ni abinda Allah ya hana ne? Ko kin manta cewa Allah ya hana mu aikata Zina? To meyasa kike son muyi?"
Shiru tayi don bata da abin cewa
Don haka yaci gaba da faɗin, "Ziya.. love Ni ina guje miki wulaƙanci ne, idan na rigada na san ki a waje babu ta yadda za'a yi na daraja ki in mun yi aure, duk da ina matuƙar ƙaunar ki Love, but duk idan aka ce na gama sanin ki sannan muka yi aure, dole zaki fuskanci wulaƙanci a wuri na, kuma bazan yi ɗokin ki ba tunda mun rigada mun gama sheƙe ayar mu a waje, Ni kuma wannan abun ne nake guje miki, wlh Ziya ina son ki, ina matuƙar ƙaunar ki, ƙaunar da nake miki ne yasa bazan taɓa cutar dake ba, bazan wulakanta ki ba, sannan nafi son idan na aure ki in riƙa ganin ki da ƙima da daraja kamar ko wace mace ta ƙwarai, Please Ziya ki danne duk wani abu da kike ji har mu kai ga Aure, tunda Dady yace sai nan da Two years mu bari zuwa lokacin, kamar yanzu ne zaki ga ya zo kinji? Kinga nima Ina cikin wani hali sosai a kan buƙatar ki, amma babu yanda zan iya, tunda muna rage zafi shikenan mu bar shi a haka".
Numfashi Ziyada taja kafin tace, "to naji Bie, bazan sake maka maganan ba na bari".
"Yauwa ko ke fa ƴanmata na uhm, har kin sa naji sanyi a raina, kar ki damu ai muna tare, kuma kamar yau ne zaki ga an kawo ki gida na sai yanda muka yi da juna ko?"
Murmushi me sauti ta saki tace, "uhm Bie kenan".
Dariya shi kuma yayi yace, "ko dai kunya na kike ji ne? Ki faɗa abinda ke ranki don nasan Ziya.. love ba ta rasa abun faɗa".
"Bie ina kewar ka ne fa kawai".
"Da gaske Love?"
"Umm".
Sake matse pilown hannun sa yayi yana faɗin, "nima haka Love, ina matuƙar kewar ki a kwana biyun nan da kika taso Ni gaba, ji nake yi tamkar mun shekara bamu ji ɗumin juna ba, kin san jiya wlh daƙyar na iya daure wa ban fisgoki jiki na ba a lokacin da na tashi na ganki kusa dani".
Dariya ta ƙyalƙyale dashi tana cewa, "kai Bie amma sai ka nuna kamar baka damu dani ba, har da ture ni". Taƙarishe maganar cikin sigan shagwaɓa
Datse leɓen sa na ƙasa yayi kafin yace, "sorry dear bazan sake ba, yanzu ina buƙatar jin ɗumin mata ta in fito mu haɗu?".
"A'a".
"Why Loveeee?" Yayi maganar da jan sa a hankali
Daga can numfashi kawai Ziyada take sauke wa, cikin tsantsan sha'awa tace, "Ni nayi fushi ba yanzu zan sauko ba, sai dai ka bari sai gobe".
Mamakin maganar ta yayi, musamman yanda yaji muryan ta yasan itama tana buƙatar sa, amma kuma sai yayi shiru be ce mata komi ba
Ita kuma ta sake cewa, "Byee Bie zuwa gobe zamu haɗu". Bata jira yayi magana ba ma, ta tsinke wayan
Kifar da wayan yayi yana rufe idanun sa tare da sake ƙanƙame jikin sa yana fid da numfashi a hankali.
▪️▪️▪️
Ziyada tana tsinke wayan ta soma neman layin Saleem, sai dai kafin ma ta kira sai gashi ya kira ta, da sauri tayi peacking jikin ta na rawa, nan suka soma hira me tada junan su hankali, daga ƙarshe ta buƙaci zuwa wajen sa
Dama yana gidan sa ne, don haka cikin zumuɗi ya amsa mata
Babu ɓata lokaci ta miƙe ta sauya kayan ta zuwa doguwar rigan abaya, baƙa me kwalliya sosai, yane kanta tayi da gyalen rigan; ta zari HangBag ɗin ta da keey ɗin mota ta fice
Ko ɗakin Momyn ta bata leƙa ta faɗa mata zata fita ba ta fice abin ta, motan ta taja ta miƙa gidan Saleem.
.
_Mu je zuwa, more Comments more typing._
_kar ku manta Vote and share please._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
𝐏𝐄𝐑𝐅𝐄𝐂𝐓 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎𝐂𝐈𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
𝗣.𝗪.𝗔✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad UmmuDahirah*👈
_Wannan shafin naki ne Sweetheart, SAFNA ALIYU JAWABI, Allah ya daɗa ɗauka ka ki amin._
*________________________________*
*PAGE* 5
*________* Batool da ta fito daga kichen, jin ana Nocking ta nufi wajen ƙofan ta buɗe, ganin Sagir Abokin ABUL KHAIRI sai ta washe baki ta soma gaishe shi cikin girmamawa
Murmushi yayi mata ya amsa yana shigo wa ciki
"Babu kowa ne a gidan sai ke?"
"A'a suna ciki, ya ABUL ma na ciki ai".
Sagir yace, "Ai na ga motan sa a waje, Mamy fa tana ciki?"
"Eh tana ciki". Ta ba shi amsa idanun ta a kansa
Shima dai kallon ta yake yi, ya sakar mata murmushi yace, "ya dai ƙanwata wannan kallo haka? Ko dai na sauya miki ne?"
Saurin sauke kanta ƙasa tayi tana rufe bakin ta tare da dariya ƙasa-ƙasa
"Uhm tom kira min Mamyn mana mu gaisa".
"To". Tayi maganar da sauri tana juya wa ta wuce
Da kallo ya bi ta har ta shige, sannan ya saki ajiyan zuciya yana ƙarisa wa cikin parlour'n ya zauna.
Tare da Mamy suka fito Parlour'n, ƙarisawa Mamyn tayi wajen Sagir suna gaisawa, ita kuma Batool ta shige ɗakin su
Maimuna dake zaune tana duba book ɗin ta na English; ta ɗago kai tana kallon ta, har ta zauna kusa da ita bata ɗauke idanun ta a kanta ba, sai ma tambayan ta da ta soma yi, "Sister lafiya wannan fara'a haka?"
Wani fara'an ne ya sake tabaibaye Batool, ta saki murmushi tace, "uhm sister babu komi fa".
"Ya za'a yi ki ce babu komi bayan na ganki kina murmushi da fara'a?".
"Babu komi wlh, kawai dai na tsinci kaina cikin farin ciki ne matuƙa tuna wani abu".
Kaɗa kai Maimuna tayi kafin ta mayar da hankalin ta kan Book ɗin ta, kasancewar ta ba me son magana ba shiyasa bata ja zancen ba.
▪️▪️▪️
Ɗakin ABUL KHAIRI ya shiga bayan sun gama gaisawa da Mamy
ABUL KHAIRI dake kwance tun gama wayan sa da Ziyada, ko motsi ya kasa yi sai faman ajiyan zuciya yake sauke wa idanuwan sa a lumshe, duk da kuwa ya ji sallaman Sagir be sa ya buɗe ido ba bare ya motsa
Kusa dashi Sagir ya ƙariso ya zauna gefen gadon; ta wajen ƙafafuwan sa, a tunanin shi barci yake yi don haka ya saka hannun sa ya janye pilown da ya matse a ƙirjin sa
Hakan yasa ABUL KHAIRI buɗe idanun sa ya sauke a kan sa
Murmushi Sagir yayi yace, "lallai ka samu lafiya wannan barci haka? Idanu har sun sauya kala, Kana jin daɗin ka fa aboki".
Shima ABUL KHAIRIN murmushin yayi yana ƙoƙarin tashi zaune yace, "uhm babu barcin da nake yi Aboki, ƙanwar ka ce dai ta caza min kai, ina tunanin gaskiya wata rana sai dai ku zo ku ga gawana idan baku aura min ita ba".
Sagir sheƙewa yayi da dariya yana tafa hannu yace, "iyeee abun har ya kai haka kenan? Lallai kam kana ruwa kusa da kada tsundum".
Hararan sa ABUL yayi yana saka hannu ya ƙwace pilown sa yace, "kai dai ka sani, Ni dai wlh na gaji ko ku bani ita ko in mutu".
Dariya Sagir kawai yake tuntsura wa, ganin yanda ABUL ɗin ya kwaɓe fuska tamkar zai yi kuka
"Allah kuwa da gaske nake yi Aboki, meye shawara? ina buƙatar aure da gaggawa, sannan kuma Ni bazan iya auren wata ba sai Ziya.. love, kai ka san matsala na, abun ya kai maƙura tunda har Mamy ta fahimta, kuma ka san idan ta ga babu sauƙi zata iya tada zancen wancan ƙwailan, musamman idan naje mata da maganar ma". Sai yaja numfashi yana sake sauya fuskar sa na tausayi, yaci gaba da faɗin, "amma kuma idan da maganar Ziya.. love na san bani da damuwa, zan iya shawo kan matsalan duk idan naje musu da maganar aure nake so, tunda ina da wacce zan nuna musu".
Sagir dake kallon sa yace, "haka ne Aboki, ko Ni ban goyi bayan ka je da maganar auren ka yanzu ba, sabida idan sun amince maka da maganar Ziyada, to ka ga shi Dady ya ce, "ba yanzu ba", hakan zai jawo maka matsala, don wlh maganar mutumiyar ka za'a tado dashi". Yaƙarishe maganar da dariyan shaƙiyanci
Pilown hannun sa ABUL KHAIRI ya wurga masa yana sakar masa wani kallo tamkar idanun sa za su faɗo ƙasa, yace, "ɗan iska uban wa yace maka mutumiya ta ce ita? Ka kiyaye Ni wlh, kasan hali na fa".
Shi dai Sagir be dena dariyan sa ba, har da ƙware wa sabida tsaban dariya
Hakan ya ƙular da ABUL yaja dogon tsaki yana cewa, "ka ga fa ban son iskanci idan zaka bani shawara ka bani, Allah zaka fitar min a ɗaki".
Rufe bakin sa Sagir yayi sabida wani dariyan da ya taho masa, daƙyar ya iya buɗe baki cikin dariyan yace, "to to Aboki Na dena, Allah ya ba ka haƙuri ko? Yanzu wani shawara kake so in ba ka?".
Shiru ABUL KHAIRI yayi be tanka sa ba, sai ma wani kallo da yake aika masa dashi
Matse bakin sa yayi yana haɗiye dariyan sa yace, "to shawaran da zan ba ka Aboki na, Ni a gani na ba wata matsala bane idan ka jira ta nan da two years ɗin, abinda zaka riƙa yi kawai ka nemi maganin sha'awa ka riƙa sha ko zaka ji sauƙi, sannan ku dena wannan banzan soyayyan shan mintin da kuke yi, hakan ke jawo maka matsala, kuma wlh duk wayon ka Aboki a kan baza ka kusance ta ba sai kun yi aure uhmmm wata rana abun da kake gudu; aikata zina shi ne zai biyo baya, to wai shin ma meye Bambancin abinda kuke yi da zinan? Kar ka manta ana zinan ido, ana yin na chart.."
Katse sa ABUL KHAIRI yayi da faɗin, "Ka ga Malam ba wa'azi na kira ka kayi min ba, yaushe ma ka zama malamin da zaka zo kana maganar?"
Sagir yace, "ai ba sai na zama Malami sannan zan maka wa'azi ba, kai ma ka san hakan babu kyau, kafi kowa sanin hakan, Ni dai shawara na ba ka kamar yanda ka nema, in ka so kayi amfani dashi; in kuma ka so ka zubar a ƙasa kabi ta kai ka tattaka, ya rage na ka. duk ranan da ka jawo mana abun kunya wlh babu ruwana, kar ma ka nuna ka san Sagiru".
Lumshe idanuwan sa ABUL yayi, tabbas ya san maganar abokin sa gaskiya ne, amma kuma a yanzu sun rigada sun yi nisa ga wannan halayyan, domin hakan ne kaɗai ke rage masa raɗaɗin wutar ƙauna da sha'awar da yake yiwa Ziyada, bazai iya juran yana ganin ta kullum be iya taɓa ta ba, itama haka, abun dai da yaga zai iya kawai shi ne bazai taɓa sanin ta ɗiya mace ba har sai da igiyoyin sa uku a kanta...
"Kai tunanin me kake yi haka ina magana kana ji na?"
Maganar Sagir ɗin ne ya sanya sa buɗe ido yana kallon sa
Sagir ya sake faɗin, "tashi mu yi sallah ana kira".
Toilet Sagir ya soma shiga ya ɗauro alwala, kafin shima ABUL ya shiga yayi nasa, a tare suka fito suka nufi masjid, ana idar da sallan magriba suka fito, a hanya suka haɗu da Abba suka yo gida gaba ɗayan su, sai dai shi Abba ciki ya shiga yabar su a waje, sai da suka ɗan tattauna kafin Sagir ya hau motan sa ya bar gidan, shima kuma ABUL ya shige ciki
A Parlour ya tarar da Abba suna zaune shi da Mamy da Amir, zama yayi gefen Amir yana sauraron hiran da su Abba da suke yi, har aka kira sallan isha'i kafin su sake fice wa su uku zuwa masallaci.
Da suka dawo time ɗin har an shirya dinner a kan leda a tsakar parlour'n, zama suka yi suka soma cin abincin.
Bayan sun kammala Mamy ta kalli ABUL dake latsa wayan sa yana tura wa Ziyada text, kasancewar ya ji wayan ta akashe, tace, "Babana gobe idan Allah ya kai mu su Maimuna suka dawo school, za su je gidan gona su ɗibo Fruits sabida na gida ya ƙare, kuma ka ga har yanzu ban samu keey ɗin fannin ba, sai ka bani naka muyi amfani dashi za su ɗibo min".
Ɗago kai yayi yana kallon ta yace, "a'a Mamy kibar su kawai, zuwa goben zan je da kaina sai in ɗibo".
"To babu matsala, ɗazu Zainab ta faɗa maka saƙon uncle ɗin ka kafin ta tafi?"
Girgiza kansa yayi yace, "a'a bata faɗa min ba".
Gajeren tsaki Mamy tayi tace, "kai! wani lokacin Zainab shirmammiya ce, ce min tayi akwai saƙon da Abbas ya aiko ta zata ba ka, to Ni dayake ina aiki ban bi ta kanta ba, ai sai ka kira a waya kaji meye saƙon".
Batool tace, "ai ta faɗa min kafin ta tafi, tace kaje gobe wajen aikin Uncle yana son ganin ka".
Wani kallo ya aika mata dashi yace, "dama kina ji kenan ake magana?"
Sauke kanta tayi ƙasa cikin tsoro
Abba dake jin su yana aiki a cikin computer'n sa yace, "tashi ka je kar ka zare wa ɗiyata ido, ba yanzu kuke maganar ba kuma ta baku amsa?"
ABUL dai be ce komi ba ya tashi ya wuce ɗakin sa
Ita kuma Mamy cewa tayi, "Abban su ai ta san halin yayan na su, da taji ana maganar meyasa bata faɗa ba?"
Batool tace, "wlh ban ji ku bane, muna can muna magana da Maimuna".
"To ya wuce dai abar maganar". cewar Abba, kafin ya mayar da idon sa kan Baby da tazo ta maƙale masa tana kallon abinda yake yi, sai da ya shafa kanta yace, "Autana baza ki kwanta bane kin san da school gobe? Kar kuma a tashe ki kina ƙi".
"Abba Ni ban jin barci".
"To yi zaman ki, saura inji an kawo min complain an tashe ki kin ƙi tashi".
Murmushin jin daɗi tayi tana sake shigewa jikin sa ta yanda zata kalli computer'n da kyau.
A haka dai suka zauna suna ta hira jefi-jefi gaba ɗayan su, don itama Mamy tuni ta saka Amir ya ɗauko mata Laptop ɗin ta a cikin ɗaki
Maimuna da Batool kuma kallo ya ɗauke musu hankali, sai Amir ne dake kwance kan kujeran yana buga Game.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Ƙarfe 08:30pm Ziyada ta dawo gida, ana buɗe mata Gate ta shiga Shima Sagir ya shigo da tashi motan gidan, time ɗin da ta fito daga motan shima ya fito yana bin ta da kallo, gaishe sa tayi,
Ya amsa yana faɗin, "Daga ina haka my sister da daren nan?"
Murmushi ta saki tana ɗan sosa kai tace, "Yaya daga wajen Bie mana nake".
Kafe ta da ido yayi yace, "faɗa min gaskiya, ABUL KHAIRIN da muke tare yanzu da magriban nan muka rabu, shi ne kuke tare?"
Turo baki tayi cike da borin kunya tace, "sorry yaya nayi maka ƙarya, ina tare da Rahy ne".
Ɗan tsira mata ido yayi na wani lokaci kafin yaja numfashi yace, "mu je to, but ki dena fitan dare kina jina ko Dear?".
"Insha Allahu yaya, wannan ma buƙatar hakan ne". Ta amsa mishi tana bin bayan sa
A tare suka shiga parlour'n, sai dai babu kowa
Kallon sa tayi tace, "Yaya bari in Kira maka Momyn maybe tana ciki ne".
"No bar ta ta fito, nima ba yanzu zan wuce ba".
"Ok bari in shiga to in watsa ruwa". Ziyada ta faɗa tana yin upstairs
Da kallo yabi ta har ta ƙule wa ganin sa, kafin ya sauke ajiyan zuciya yana lumshe idanun sa, shi kaɗai yasan me yake ji, tabbas idan yaci gaba da zama a haka watarana zuciyar sa zata iya bugawa, dole ya san mafita a kan halin da yake ciki, amma kuma taya? Wannan hanyan ce ya kasa samun sa bare ya magance abinda ke addabar sa shekara da shekaru.
▪️▪️▪️
Ziyada na shiga ɗakin ta tayi saurin dafe ƙirjin ta, domin duk a tsorace take jin ta, ji take yi tamkar za'a iya gane abinda ta aikata a yau ɗin, tafiyan ta ta dai-dai ta kafin ta ƙarisa bakin gadon ta ajiye jakan ta, a dai-dai time ɗin ne wayan ta tayi ƙarar shigan text, ciro wa tayi ta duba, sai ta ga ABUL ne ya turo mata kalaman soyayya kamar yanda ya saba akoda yaushe, karanta wa tayi sannan tayi masa reply a kan "zata kira sa ya bata time tana wani abu ne". Ajiye wayan tayi ta shiga Toilet, nan ta sake haɗa ruwan wanka me ɗumi ta yanda zai gasa mata jiki sosai ta rage raɗaɗin da take ji, shiga tayi cikin ruwan ta lumshe idanuwan ta tana jindaɗi na ratsa ta, nan ta afka tunanin da yaja ta time me yawa, sannan daga bisani tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da wando na Barci, ta fice a ɗakin
Koda ta isa parlour time ɗin tuni Sagir ya bar gidan, sai Momy da Dady ta gani zaune suna hira, da sauri ta ƙarisa wajen sa don baza ta iya yin gudun da ta saba ba, ta rungume sa tana faɗin, "Dady i miss You so Much".
Dariya yayi yana shafa kanta yace, "i miss You more than you Babyna, yaushe kika dawo ne? Momyn ki ta ce, "kin fita".
Zama tayi tana dariyan farin ciki tace, "tare muka shigo da Yaya Sagir ai, na je wajen Rahy ne".
"Ok Masha Allah Baby na, to ya school ɗin ki, ana dai karatun ko?"
"Eh Daddy sosai ma, ka tambayi Momy ma, ba na wasa ai".
Murmushi Momy tayi tace, "ai ba sai na faɗa masa ba, shima ya shaida hakan, Babyn mu me ƙoƙari ne ba ta wasa da karatun ta".
Dady yace, "yauwa good girl, dama fatana kiyi karatu sosai Baby, hakan zai faranta min rai sosai, shiyasa ma yanzu na sanjo miki mota don ki samu farin ciki kamar yanda kike faranta min".
"Wow! Da gaske Daddy?" Tayi maganar tana ware idanun ta tare da rufe bakin ta da hannayen ta
"Ƙwarai kuwa Baby, but zuwa nan da two days zai iso insha Allahu".
Rungume Dadyn tayi cikin tsantsan farin ciki, ta dinga mishi godiya, su kuma suna mata dariya. Daga ƙarshe dainning suka nufa suka zauna cin abinci, suna yi suna hira cike da nishaɗi.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
𝗣.𝗪.𝗔✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga mahaifiya ta Abar Alfahari na, Uwata maganin kuka na. I love You so Much Momma._ ❤️
*________________________________*
*PAGE 6 & 7*
*________* Washe gari ƙarfe 01:00pm. ABUL KHAIRI ya tashi daga aiki, sosai ya ƙosa ya isa gidan gonan sa yaje ya haɗu da Ziyadan shi, sabida ji yake yi tamkar ya shekara be ganta ba, tun faɗan da suka yi shekaran jiya rabon shi da ita, wanda hakan be taɓa faruwa ba, don a rana sai su ga juna sau uku ma, kuma kusan ko yaushe suna tare, idan basu a gidan gona, to zai bi ta school ɗin su, wajen aikin sa ne kaɗai ba ta zuwa sabida Companin mahaifin sa ne, kuma shima yana aikin a ciki, idan taje dole wata rana zai ji labarin yana kawo mata, ya san halin mutanen Abban shi, akwai ƴan sa ido sosai.
Ƙarfe 01:40pm. Ya ƙarisa gidan gonan, Gate man na buɗe masa ya kutsa hancin motan ciki, a inda Ziyada tayi parcking shima ya ajiye nasa
Dama ita tuni ta iso tunda yau ba school take dashi ba, tana zuwa ta ɗaura musu girki me rai da lafiya sai tashin ƙamshi yake yi, kasancewar ta me tsananin ƙaunar girki shiyasa take zaƙe wa tana koya, babu girkin da Ziyada bata iya ba, domin har makarantar koyan girki tana zuwa, duk idan ta yiwa ABUL KHAIRI girkin ta, sai yaji tamkar babu wanda yafi shi sa'ar samun mata, domin Ziyada ta haɗa abubuwa ta ko ina, komi da komi da yake nema wajen mace ya samu a wajen ta, idan dai biyayya ne tana masa sabida tsananin ƙaunar da take masa, sabida shi zata iya barin ko me yace, dai-dai gwargwado tana da tarbiyya duk da iyayen ta sun shagwaɓa ta, sannan uwa uba tana da tsantsan kyawu matuƙa, wanda ko wani namiji ya kalle ta sai ya rasa nutsuwar sa, ga shi ita ɗin ƴar gayu ce ta ko ina, tana da son kwalliya sosai akwai ta da tsafta, ga iya wanka, ga iya girki, kaii komi dai a wajen sa ta iya ne.
Tunda ya buɗe ƙofan parlour'n ƙamshin girkin ya doki hancin sa, sai kuma runguman da Ziyada tayi masa ya biyo baya, nan da nan shima jikin sa na rawa ya ƙanƙame ta sabida jin tattausan ni'imar jikin ta a jikin sa, yanda suke ƙwaƙume da juna zai tabbatar da cewa sun matuƙar kewar juna, be sake ta ba sai ma ɗaukan ta da yayi zuwa kan kujera ya zauna yana aza ta ajikin sa, nan ya soma gaya mata kalamai masu tsananin tsada da babu wanda ya isa ya ji su face ita, wanda suke ƙara dulmiyar da ita a kogin shauƙin ƙaunar sa, tana sake jin babu wanda ya kai ta Sa'a na samun abokin rayuwa, ji take yi tamkar ta jawo ko wani second, ko wani minti, ko wani awa; ko wani rana, sati, Wata, zuwa shekaran da ya rage musu, ta mallaki magudanan numfashin ta, wanda idan babu shi a cikin rayuwan ta, to, tabbas babu ita ne, domin tana ji a ranta muddin ta rasa ABUL KHAIRI ta dena numfashi, ƙaunar sa ya rigada ya mamaye jiki da ɓargon ta, ya zama jinin jikin ta.
Tun a kan kujeran soyayyan tasu ta sauya salo tamkar yanda suka saba, daƙyar suka iya tashi suka shiga wanka, a tare suka yi suka fito suka haye gado suka ci gaba da nuna wa junan su ƙauna tsantsa, wanda babu algus a cikin ta, kowa so yake yi ya nuna wa ɗan uwan sa yafi sa iyawa, kuma yafi sa buƙatan sa.
Sun shafe fiye da awa suna abu ɗaya ko gajiya ba sa yi, domin da gani kasan ba sa gajiya da junan su, sun yi romancing tamkar zasu haɗiye juna, daƙyar suka haƙura suka sake koma wa Toilet suka sillo wanka, sannan suka yaɗa zango a kan dainning; ko kayan kirki babu wanda ya saka a cikin su, abinci suke ciyar da juna cike da nishaɗi tare da soyayya me tsananin garɗi, domin ji suke yi tamkar babu wani mahaluki a duniyar su sai su kaɗai.
Bayan sun gama kujera suka koma suka kwanta a tare saman Three sitter Suna hiran su.
Sai ƙarfe 05:40pm. Sannan suka yi haraman tafiya, kayan su suka maida suka fito a tare riƙe da hannun juna suna ma junan su kallon soyayya, suna magana ƙus-ƙus babu me ji sai dariya suke yi, har mota ya kai Ziyada, ta zauna tana kallon sa tamkar baza su rabu ba, sun daɗe a wajen kafin taja motan tabar gidan
Shi kuma nufan cikin gidan gonan yayi, inda masu aiki suke nan ya ƙarisa, ya kira su ya saka su aiki wajen ɗebo masa Fruits ɗin da Mamy ta buƙata, komi da komi sai da ya saka aka ɗibo masa, har kaji da su kifi, zabi, talo-talo, kasancewar duk yana kiwon su a gidan, sai da ya saka aka yayyanka mishi kafin aka zuba a buhu suka kai mishi mota, daga nan shima ya shiga motan ya nufi gida.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
*ZIYADA ALH. MUH'D IYAAL*
Ziyada ɗiya ce ga Alh. Muh'd Iyaal, da matar sa Hajiya Turai, ita kaɗai Allah ya ba su, kuma sun ɗau son duniya sun ɗaura mata, duk abinda take so shi take yi babu harara ko tsangwama a rayuwan ta, sai dai mahaifin ta yana bala'in son tayi karatu me zurfi, wanda hakan ne yaja tsaiko ga auren su da ABUL KHAIRI, wanda sun shafe tsawon shekara biyu suna tare.
Ziyada bata da ƙawa aminiya sama da Rahina, tun suna yara suke tare har kawo girman su, ita ma dai yarinyan masu kuɗi ne, kuma gaba ɗaya school ɗin da suka yi tare suke yin sa tunda Allah ya haɗa jinin su, duk da cewa anguwan su ba ɗaya ba.
Tun farko Rahina da ta fara ganin ABUL KHAIRI ta kamu da tsananin ƙaunar sa, sai dai babu ta hanyar da ta samu damar sanar masa, kasancewar shi ɗin saurayin Ziyada ne, kuma shi kansa ABUL KHAIRI be taɓa bata ƙofan da zata iya sanar dashi ba, domin shi mutum ne me yawan ɗaure wa mata fuska, ko kaɗan ba ya shiga harkan mata sai da ya haɗu da Ziyada, ita kaɗai ce macen da ya taɓa so, kuma ita yake ganin zai ci gaba da so har ƙarshen numfashin sa.
Sagir ɗa ne ga ƙanwar Hajiya Turai mahaifiyar Ziyada, lokacin da yana ƙarami Hajiya Turai (Mom) ita ta riƙe sa kafin ta haifi Ziyada, kasancewar ba sa haihuwa, ita kuma ƙanwar ta a time ɗin tana da yara biyu, sai shi Sagir ɗin na uku, shiyasa ta bata shi har zuwa sanda zasu samu na su
Koda suka haifi Ziyada sai Sagir yaci gaba da zama a hannun su har tasowar Ziyada, sai ya zamana koda yaushe Ziyada na hannun Sagir, sabida ba ƙaramin ƙaunar ta yake yi ba, Allah ya haɗa jinin su matuƙa, sun shaƙu fiye da tunanin mutane, idan ka gansu sosai za su ba ka sha'awa saboda ƙaunar da suke yiwa juna, har time ɗin da Sagir ya tafi ƙasar Ghana inda yake karatun sa na degree a can
A lokacin ne kuma suka haɗu da ABUL KHAIRI tunda shima a can yake karatu, sai Abokantaka ya shiga tsakanin su, ga shi kuma duk abu ɗaya suke karanta Shiyasa koda yaushe suna tare, har sanda suka gama, kuma suka ɗaura Masters ɗin su, izuwa lokacin sun zama aminai sun shaƙu sosai, tamkar ƴan uwan juna.
*ABUL KHAIRI* yana yawan jin labarin Ziyada a bakin Sagir, tunda ba shi da abun yabo sai ita, domin har ABUL ya kan tone sa yace masa, "ko dai da ita za'a yi?" Sai Sagir yayi dariya kawai, don ba ya ba sa amsar komi, kuma shi ABUL be taɓa damuwa ya san ta ba, duk da kuwa yana yawan jin suna waya da Sagir, be taɓa amsa su gaisa ba ko da Sagir ɗin ya buƙaci haka, shi dai karatun sa kawai ya saka a gaba
Har zuwa sanda suka gama suka dawo gida gaba ɗaya, inda ABUL KHAIRI ya soma aiki a Companin Abban sa na sarrafa amfanin gona, kasancewar shima Abba ya gada ne wajen Mahaifin sa, sai dai yanzu haka ya bunƙasa Companin fiye dana da, har wasu abubuwan da ya shafi kayan saka wa suke yi, wanda ake haɗa su da adduga, sabida a Companin suke yin addugan, wancan kuma abun da ABUL KHAIRI ke so kenan, shiyasa ma ya buɗe gidan gona yake kiwo, don yana son shuka.
Yanzu haka Sagir ya koma wajen iyayen sa da daɗe wa, sai dai yana zuwa gidan su Ziyada tunda ya zama ɗan gida, yana da ɗakin sa idan yaga dama ya kwana a can, idan kuma yaga dama ya koma gidan iyayen sa.
Lokacin da suka gama school ne, ABUL KHAIRI ya kai masa ziyara a gidan su Ziyada, to, wannan shi ne farkon haɗuwar su, wanda ya jawo soyayya a tsakanin su, don tun a farkon haɗuwar su suka kamu da ƙaunar juna, kuma shi ABUL be yi sanya ba ya sanar mata, inda ya amsa Numban ta a nan take, kuma duk a gaban Sagir aka yi hakan, domin shi ne ma ya ba shi ƙwarin gwiwan bayyana mata
Sai dai abinda ABUL ya kasa fahimta, gaskiyar soyayyar da Sagir ke yiwa Ziyada tun tana ƙarama, duk yawan maganar da Sagir ke yi na Ziyada be sa yayi la'akari da hakan akwai ƙauna ba, idanun sa ya rufe lokaci ɗaya da soyayyar Ziyada, burin sa kawai ya ƙulla tashi soyayyan
Shi kuma Sagir ganin abokin nasa da ita Ziyadan gaba ɗaya sun afka ga junan su, sai shi kuma ya danne nasa soyayyar da yake da ninyar sanar da ita a lokacin, sai ya ci gaba da ba su gudummawa a tasu soyayyar ba tare da sun san me ke cikin ransa ba.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Washe gari Asabar Mamy da su Maimuna kasuwa suka wuce, za su taya Mamy sayayyar kayan Uncle Abbas, basu dawo ba sai yamma.
The following day gaba ɗaya yaran suka shirya don ziyarar Kakannin su, ABUL KHAIRI ne zai kai su
Koda suka gama shirya wa, motan suka wuce suka shiga suna jiran sa, don shi a time ɗin be rigada ya shirya ba
Amir ne ya zauna a gaba, sai su Batool a baya, hira suke tayi har sanda ABUL ya fito, yayi shirin sa na manyan kaya dakakkiyar shadda maroon Colour, sai tashin ƙamshi yake yi, yana shiga cikin motan suka nutsu waje ɗaya, be bi takan su ba yaja motan ya nufi bakin Gate, me gadi na buɗe masa Gate ɗin; ya cilla motan waje.
Tafiyan mintuna sha biyar suka isa gidan Alh. Sunusi mahaifin Abba
Fitowa suka yi suka yi cikin gidan gaba ɗaya, ABUL KHAIRI na biye dasu a baya.
*****
Hajiya Falmata na zaune a parlour'n suka shigo dukan su da sallama, amsa musu sallaman tayi cike da fara'an ganin su, ta soma musu lale marhaba
Zama suka yi suka soma gaishe ta cikin girmamawa
Ta amsa cike da fara'a tana tambayan su mutanen gida.
Nan shima Alh. Sunusi ya fito daga ɗakin sa, ganin su ya saka shi washe fuska cike da farin ciki ya soma tsokanar su yana ƙarisowa wajen, kusa da ABUL KHAIRI ya zauna yana dafa shi yana sake tsokanar sa cike da farin ciki.
Dariya duk kan su suke yi, don sun san halin Dady akwai son tsokana musamman idan ya tasa ABUL KHAIRI a gaba, sun fi ɗasa wa sosai, shi kansa ABUL yafi sakin jiki dashi
Nan suka soma hira cike da barkwanci suna kwasan dariya, har shi ABUL KHAIRIN da be cika sakin jiki a gaban ƙannin sa ba, su ma sun sake sosai, illa Maimuna ne kaɗai da ba ta iya surutu sai dai tayi dariya kawai.
A lokacin sai ga Umma Hassana itama ta zo da yaranta biyu, ƙanwa ce wajen Abba, kuma tserayan su da ABUL KHAIRI be fi shekara uku ba
Nan gidan ya sake hautsine wa, ana ta hira da dariya.
A gidan suka wuni har zuwa sallan azahar, sai da su Dady da ABUL tare da Amir suka je masallaci suka dawo, kafin suka yi haraman tafiya.
Daga nan gidan su Mamy suka wuce, a anguwan da suke har yanzu a nan Hajiya Mama mahaifiyar su Mamy take, sai dai yanzu gidan gaba ɗaya uncle Abbas ya gyara shi, ya rushe yayi Plet, Part ɗin sa daban; na Hajiya Mama daban, sai ƴan aiki da ya zuba mata masu yin mata komi da komi, duk da a yanzu akwai yarinyan Hajiya Fatima ƙanwar su Mamy (suna kiran ta Aunty Fatima, tana aure a Kaduna, ɗaya daga cikin ƴan uwan Mijin Ummu mahaifiyar Maimuna shi ke auren ta, sai dai ita yanzu tana Zaria sabida mijin ta a can yake aiki)
sunan yarinyan Humaira, kasancewar sunan marigayiya A'isha taci, itama ƙanwa ce wajen su Mamy da ta rasu da daɗe wa
Humaira Sa'ar Amir ne, yanzu haka ta dawo wajen Hajiya Mama da zama ne, wajen shekara ɗaya da dawowar ta, tunda ta dawo uncle Abbas shi ke ɗaukan nauyin ta na komi, har school shi ya saka ta.
Uncle Abbas be taɓa aure ba, karatu kawai yake yi har kawo yanzu da ya sami wata ƴar cikin anguwan nasu zai aure ta, kuma har a yanzu ɗin be dakata a karatun ba, don a halin yanzu degree na uku yake yi, saura four months ya gama, be cika zama ba yana tafiye-tafiye ne sabida yanayin aikin sa. Wannan auren ma da zai yi su Mamy suka matsa mishi, don shi a nashi ra'ayin be shirya aure yanzu ba, ba wani shekaru ne dashi ba, tunda yanzu ba zai fi 36years ba.
▪️▪️▪️
Hajiya Mama tayi murnan ganin jikokin nata, nan tayi ta haba-haba dasu, su kuma suna faman tsokanar ta tunda sun fi saba wa da ita sosai, kasancewar ta me sakar musu fuska, shiyasa suke wasan jika da kaka
Humaira itama tana cikin su ana ta hira, dayake sun saba da ABUL, nan ta shige masa suna ta hira tare, ya bata wayan sa suna ɗaukan pictures, idan suka yi kuma sai su koma kallo suna dariya, idan ita ce bata yi kyau ba a hoton, ko ta ɓata hoton; ya dinga dungure mata kai kenan yana faɗin, "ta ɓata masa waya da munin ta". Ita kuma dayake akwai sokonci irin na ƴan fari, sai tayi ta masa shagwaɓa tana zumɓura baki a kan, "baza ta yarda ba, sai dai a sauya wani" haka zai biye mata su yi ta ɗauka.
Su kuma su Batool suna gefen Hajiya Mama suna tiƙan dariyan labarin da take basu, wani abubuwan duk labaran iyayen su take faɗa musu, idan kuma suna da tambaya sai suyi mata
Baby ne kaɗai babu ruwan ta, tunda ta shigo ta kwanta abunta sai barci.
Da za su tafi Hajiya Mama sai da ta tilasta wa ABUL a kan, "lallai su wuce gidajen Uncles ɗin su; su gaishe su."
Shi ba kasafai yake son zuwa ba, don ya tsane su matuƙa sabida yanda su ma ba sa son su, amma babu yanda ya iya tunda Hajiya Mama ta tilasta mishi.
Gidan Uncle Shamsu suka soma zuwa, yana nan dai kamar yanda yake, tun sanda ya taɓa samun hatsari ƴan daba sukai mishi dukan tsiya, shikenan kuma ƙafafuwan sa da suka samu karaya suka ruɓe, aka yi ta magani ana ɗori ba'a dace ba, yanzu haka an yanke masa ƙafa ɗaya, kuma be taɓa yin aure ba tunda tun kafin yayi aure abun ya same shi.
Mahaifiyar shi da mahaifin shi Kawu Shehu sun daɗe da rasuwa, yanzu shi kaɗai yake rayuwa a gidan, sai kuma ƙanwar sa Aliya dake taimaka masa daga gidan auren ta, tana kawo masa abinci, wataran ta turo ƴaƴan ta su gyara masa gidan, su kula dashi, duk da dama ƙafa ɗaya ne ya rasa.
Suna zuwa suka gaishe sa, ABUL KHAIRI yace, "su tashi su tafi". Da za su tafi haka ya ajiye masa tsibirin kuɗi suka bar shi da godiya yana zubar da hawaye, babu abinda yake tunawa sai tozarcin da suka yiwa A'isha marigayiya, sanadiyar Fyaɗen da suka yi mata shi da abokan sa ta rasa ranta, sai gashi a cikin ƴan uwan ta suke taimakon sa, don Mamy idan ta samu dama koda yaushe tana zuwa duba sa, kuma ta ajiye masa kayan dubiya me yawan gaske, idan har bata samu damar zuwa ba, sai ta aiko drever ya kawo masa, har yanzu ita take saka wa ana duba masa ƙafan, sosai likitoci suke kula da shi a gidan. Ummu ce kaɗai (Ameera) ba ta mishi wannan taimakon, domin har yanzu taƙi manta abinda suka yi musu, musamman ma Uncle Sani da tafi tsanar sa, ko biyar ba ta basu nata, kuma ko ta zo garin ba ta neman su, ko Hajiya Mama zata nace sai ta je, to ba ta zuwa, sai dai ta haƙura ta ƙyale ta, domin har yanzu Ummu halin ta na nan, sai dai baka taɓo ta ba.
Daga nan gidan uncle Sani suka wuce, shima dai mahaifinsa Kawu Bala ya daɗe da rasuwa, sai mahaifiyar sa Umma tana nan a raye, sai dai ta tsufe sosai sabida talauci, ko fitowa ba ta iya yi sai da dalili
Sulaima matar Uncle Sani ƴaƴan ta biyu, namijin Salihi sunan sa, yanzu haka ya kai ABUL a girma, sai dai shi ABUL ɗin ya ba shi shekaru kusan uku, sai ƙanwar sa Azeeza me shekaru 20 sa'ar Zee ce ita
Yaran sun tashi babu tarbiyya ko kaɗan, sabida yanda uwar su da suke kiran ta Umma Sulaima ta ɓata su matuƙa, dayake itama ba ishashshen tarbiyya ne da ita ba tunda tsohuwar karuwa ce, bare kuma akai ga uban su, yanda kuka ga uncle Sani yana matashi, haka shima Salihi yake, ba ya jin magana ko kaɗan, shaye-shayen nan babu wanda be sha.
Tunda suka shiga gidan ABUL KHAIRI ke faman yamutsa fuska sakamakon tozali da yayi da ƙaton kwatan dake tsakiyar gidan, har yanzu dai gidan nan ne da Mamyn sa tayi rayuwan ƙunci da azaba a ciki, be sauya ba sai ma lalace wa da ya sake yi.
Su dai su Batool tuni sun isa ƙofar ɗakin Umma Sulaima suna kwaɗa sallama
Daga ciki ta amsa musu tana ba su umarnin shigowa
Shiga suka yi gaba ɗayan su
Da idanu take bin su har ta gyara zaman ta daga kwancen da ta tashi, yamutsa fuska kawai take yi tana amsa gaisuwar su cike da gadara da iyayi, kafin kuma tace, "ku kuma daga ina haka?"
"Daga gida muke Umma, mun zo muku ziyara ne". Cewar Batool tana washe baki, don ita babu ruwan ta da irin tsanar da suke musu
Taɓe baki Umma Sulaima tayi tace, "lallai kam, ai naga ziyara, ko dai an turo ku yin wani muna-furcin? Ita ina uwar taku take?"
Yanzun ma dai Batool ce ta ba ta amsa tana murmushi, "Mamy na gida ta ce a gaishe ku, tare da Yaya ABUL muke yana waje".
"To me zan mishi? In CE dai bazai shigo ba? To ya ruɓe a can mana, Ni dai ba fita zan yi ba".
Batool tace, "ai kin huta rabon naki ya wuce ki, ina Aunty Azeeza ne wai?"
Wani shegen harara Umma Sulaima ta buga mata tace, "kee! Uwar ki zan ci wlh, an ce miki Ni irin fatararren Kawun ku ne da zan je ina roƙo wajen ku? Da shi da uwar taku ba ku da abinda za ku bani sai ma Ni in baku".
Dariya Batool ta kwashe dashi jin abinda ta faɗa, Amir na taya ta, ita dai Maimuna nata ƙasa-ƙasa take yi tana ƙumshe baki
Ai kamar sun kunna Umma Sulaima ta fara sababi tana zagin su
Kuma suka ƙi tashi bare su dena dariyan da suke yi, sai kallon ta da suke yi
Ai kuwa tayi ta ƙunduma musu zagi tana kiran sunayen iyayen su tana aibata su.
*ABUL KHAIRI* dake tsaye bakin ƙofa yana jin duk abinda suke yi, ya banko labulen yana kallon su fuska babu fara'a, ya daka musu tsawa a kan, "su fito"
Tashi suka yi jikin su na mazari, don basu yi tunanin yana nan kusa ba tunda daga can tsakar gidan suka bar shi
suna fita itama ta biyo su tana ci gaba da sababi, sai ta koma kan ABUL tana zagin sa
Shi kuwa be ma bi ta kanta ba suka shige ɗakin Umma mahaifiyar Uncle Sani.
A lokacin ne Azeeza ta shigo gidan tamkar an jeho ta, ganin Umman ta na sababi sai ta soma wurwurga idanu cikin gidan tana faɗin, "Umma ina Yaya ABUL ɗin?"
Nan Umma Sulaima ta sake cika da takaicin ɗiyar ta, bata kai ga magana ba; taga Azeezan ta nufi ɗakin Kakarta da gudu tana washe baki
A time ɗin ABUL har ya sako ƙafa zai fito suka ci karo, ai da sauri yaja da baya yana sake ɗaure fuska ganin Azeeza ce
Ita kuwa bata damu ba illa washe baki da ta sake yi tana faɗin, "Yaya ashe ka zo? Ina gidan Gwaggo Maria ( ƙanwar Mahaifin ta) aka zo aka bani labarin zuwan ka, sannu da zuwa yaya, ina wuni?"
Duk maganar da take yi da kallo yake bin ta, kafin yace, "bani hanya na wuce".
Babu musu ta matsa mishi, sai ma time ɗin taga su Batool, sai ta sakar wa Batool murmushi tana cewa, "ƙanwata ashe har da ke aka zo? Shi ne ko ki neme Ni Ko?"
"A'a wlh Aunty, sai da na tambayi Umma Sulaima ina kike?"
Azeeza na kallon ABUL dake tafiya tace, "Yaya don Allah ku jira Ni nima zan bi ku".
Ko bi ta kanta be yi ba ya bar gidan, yayinda su Maimuna suka take masa baya
Riƙo hannun Batool tayi da itama zata bi bayan su kar ABUL yaji ta shiru, amma sai Azeeza ta riƙe mata hannu tana faɗin, "Plz Sister jira ni na ɗauko kayana mu tafi tare, kinga idan kika fita zai tafi ya bar Ni".
Waro ido Batool tayi tace, "a'a Aunty Azeeza bar Ni in tafi, sai dai ki je ki haɗo kayan zan faɗa masa ya jira ki, wlh idan ya ji Ni shiru tafiya zai yi".
Umma Sulaima dake tsaye tana sauraron su tace, "ai kuwa babu inda zaki bi su Azeeza, sakar ta ta tafi, wa billahil lazi kika bi su Ni dake ne, shashashan yarinya kawai, ki rasa ma wanda zaki manne ma wa sai irin tsiyan nan".
Turo baki Azeeza tayi tace, "wlh Umma babu uban da ya isa ya hana Ni bin su, ko Baba ne kuwa bare ke".
Ita dai Batool tunda ta samu ta zame hannun ta daga riƙon da Azeeza tayi mata, bata tsaya sauraron cacan uwa da ƴar ta ba tayi saurin fice wa, time ɗin ma har ABUL yaja motan yana da ninyan tafiya, ai da gudu ta ƙarisa wajen tana kiran sunan sa kamar zata yi kuka
Yana ganin ta yaƙi tsayawa, sai da yayi nisa kafin yaja birki
Time ɗin har Batool ta soma kuka tana bin motan da gudu, tana ganin ya tsaya ta sake sheƙawa a guje ta nufi motan, tana zuwa ta buɗe ta shige ya ja motan da gudu ganin Azeeza itama ta sheƙo wajen su, sai dai ya bar mata ƙurar motan
Ci je baki tayi cike da tsantsan takaici, Allah ya gani tana tsananin ƙaunar ABUL, kuma baza ta taɓa bari ya suɓuce mata ba, ko wane hanya sai tabi don mallakan sa.
Juyawa tayi ta nufi gidan da sauri, tana shiga ta wuce ɗakin su ta hau haɗa kayan ta cikin akwati
Umma da ta biyo bayan ta ta soma sababi, "gidan uban wa zata je?"
Bata saurare ta ba sai da ta haɗo kayan ta kafin ta juyo tana kumbura fuska tace, "Umma ki dena ma wannan haukan taki, zan je gidan su Yaya ABUL ne in Yi kwana biyu, sabida ina kewar sa matuƙa, idan har ban je kusa dashi ba na nuna masa ƙaunar da nake mishi, bazai taɓa gane wa ba, bazai taɓa gane zan iya ba da raina sabida shi ba, Umma ina tsananin ƙaunar Yaya ABUL KHAIRI, kuma wlh duk wanda yace zai shiga tsakani na dashi, na rantse da Allah sai naga bayan shi, ABUL KHAIRI nawa ne Ni kaɗai, kuma dole shi zan aura, tun wuri ma gwara ki bi abinda nake so". Tana gama faɗar haka tayi fuuuu ta wuce jaye da akwatin ta.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga mahaifiya ta Abar Alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma._ ❤️
*________________________________*
*PAGE 8*
*________* Su ABUL sun shigo gidan babu daɗe wa, itama Azeeza ta sauka daga keke napep ta shigo gidan, da sallaman ta ta isa parlour'n fuskarta cike da annashuwa
Mamy, Maimuna da Batool dake zaune a cikin parlour'n suka bi ta da kallo, sai kuma suka amsa mata sallaman a tare, yayinda Mamy ta ƙara da faɗin, "a'ah Azeeza ke ce a gidan na mu?"
Ƙarisowa Azeeza tayi ta zauna kusa da Batool tana amsa mata, sannan ta gaishe ta tana washe haƙora
Cikin fara'a Mamy ta amsa mata tana tambayar ta mutanen gidan
Tace, "suna lafiya". Tare da faɗin, "sun ce a gaishe ta".
Mamy murmushi tayi tace, "ina amsa wa, Azeeza kwana biyu shiru ko leƙo mu ba kya yi?".
Dariya Azeeza tayi tace, "ai Gwaggo gani na zo, sai kin gaji da gani na tunda da kayana na taho".
Itama Mamyn dariya tayi tana cewa, "ai kuwa kin kyauta wlh, Batool ku je da ita ta ajiye kayan nata a ɗakin ku, sai ki zo ki ci abinci".
Da sauri Azeeza ta tashi tana ɓashe baki, har tayi gaba kuma sai ta dawo tana sosa kai tana kallon Mamy tace, "Gwaggo wai ina Yaya ABUL ne?"
Mamy na murmushi tace, "yana ɗakin sa ai, halan baku haɗu bane da suka je gidan na ku?".
"Mun haɗu Gwaggo, bayan ma sai da nace ya jira Ni zan biyo su yaƙi, ya tafi abun sa".
"Allah Sarki be kyauta ba kuwa, amma zai fito zan yi mishi magana".
Ɓashe baki tayi tabi bayan Batool
Mamy ta raka ta da kallo a ranta tana me faɗa wa tunani.
Ita dai Maimuna kanzil bata ce ba, don ita ba shiri suke yi sosai da Azeeza ba, ko kaɗan jinin su be haɗu ba, ko Maimuna ta gaishe ta ba ta amsa mata, sai dai ta riƙa bin ta da harara, ta rasa mene ne ya jawo hakan
Koda su Azeezan suka dawo, Maimuna taje ta ɗibo mata abinci ta kawo mata, ta zauna gefen Mamy tana ci tana zuba mata surutu, dama ita gwana ce wajen iya surutu, sai dai hiran nata gaba ɗaya ya tafi kan ABUL KHAIRI ne
Ita dai Mamy ba ta cewa komi sai kallon ta da take yi tana murmusawa.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Sai da aka kira sallan la'asar sannan ABUL KHAIRI ya fito daga ɗakin sa
Lokacin har su Mamy sun tashi yin na su sallan, sai Azeeza dake zaune tana kallo tana ɓashe baki da ya zame mata jiki, ganin sa sai tayi saurin tashi tana faɗin, "Yaya.."
Wani kallo ya sakar mata da dole yasa tayi shiru, ta tsaya tana sosa kai, hanyar fita yayi ba tare da yace mata uffan ba, ko kaɗan a rayuwan sa ba ya ƙaunar yarinyan shi dai, jinin su be haɗu ba, tana da matuƙar rawan kai, ga ta ko kaɗan bata da class, duk da idan ka kalle ta tana da waye wa a ido, sannan tana da kyau matuƙa.
Azeeza tana kallon sa har ya fice, sai ta ja tsaki tana komawa ta zauna, a fili tace, "dani kake zancen, wlh sai ka so Ni ABUL KHAIRI, baka da wata mace da zaka aura sai Ni, mu zuba dani da kai yanzu aka so ma wasan".
Sai dai maganar nan duk a kunnen Mamy suka faɗa, tsayawa tayi daga bakin ƙofan ta tayi shiru tana kallon Azeeza da bata san ma tana wajen ba, sai kuma ta juya cike da sanyin jiki ta koma ɗaki, a bakin gado ta zauna tana buga tagumi ta hau tunani, maganganun Azeezan ne kaɗai ke mata yawo a kwanya, kallo ɗaya idan kayi mata zaka san hankalin ta ba ya jikin ta, ta jima a wannan yanayin kafin ta ɗauki wayan ta dake ajiye kan drowern gado ta hau latsawa, Numban ƙanwar ta Ummu ta soma lalubo wa.
▪️▪️▪️
ABUL KHAIRI tare suka shigo gidan da Abba, shima dawowar sa kenan fitan da yayi zuwa dubo kayan da aka sauke masa, shi ne suka wuce masallaci a tare ba tare da ya shigo ba
Babu kowa a parlour'n sai t.v dake faman aiki, shi dai ABUL ɗakin sa ya wuce yana faman latsa wayan sa
Time ɗin ne su Batool suka fito daga ɗaki suna ma Abba, "sannu da zuwa."
Cike da fara'a ya amsa musu yana ɗaga Baby ya ɗauke ta
Ita kuma sai washe baki take yi tana masa nata, "sannu da zuwan."
Nan ya biye mata suna ta surutu yana tambayan ta su Kaka da yanda suka baro su
Labarin komi ta hau ba shi suna dariya.
Azeeza ce ta fito daga ɗaki itama, gaishe da Abba ta hau yi
"A'a Azeeza ce a gidan na mu? Ku ce muna da babban baƙuwa?"
Murmushi tayi tana amsa mishi
Sai da ya gama tambayar ta mutanen gida, kafin ya wuce ɗakin Mamy riƙe da hannun Baby da ya sauke ta.
Abba sallama yayi suka shiga cikin ɗakin
Dai-dai time ɗin da Mamy ta gama wayan ta, sauke wayan daga kunnen ta tayi ta'ajiye gefen gado tana amsa sallaman na sa, sannan tayi masa sannu da zuwa
A kan sofa ya zauna yana amsa mata, sannan ya kalli Baby dake zuba masa surutu tana ba sa labarin Exams ɗin su, yana mata murmushi
Mamy tace, "Abban su idan ka biye ta yarinyan nan baza ta barka ka huta ba, ba ta gajiya ko kaɗan da labarin school ɗin su".
Still Abba na murmushi yace, "ban da abinki ADDAN MU kin taɓa ganin sabon shiga ya gundura? Ki bar ta tayi abun ta, nan gaba ai baza ta yi ba idan ta saba".
Dariya Mamy tayi sabida jin sunan da ya kira ta da shi, ta san tunda ya kira ta da wannan sunan, to, tsokana yake jin yi, ita kuma tana son su tattauna magana me muhimmanci shiyasa baza ta biye masa ba, sai ta kalli Baby tace, "Auta na je ki Parlour wajen ƴan uwanki, zamu yi magana da Abban ki".
"To Mamy". Baby tafaɗa tana miƙe wa tayi waje da gudu.
Itama Mamy tashi tayi ta dawo kan kujeran kusa da Abba, sannan ta kalle shi tace, "Abban su magana zamu yi a kan Babana".
"To, ina jin ki ADDAN Mu, Allah yasa dai lafiya?".
Murmushi kawai tayi tana girgiza kanta, sai ta ɗan ja numfashi tace, "Abban su maganar shi da Maimuna ne nake son a tado shi yanzu".
Ɗan gyara zaman sa yayi yana sake kallon ta yace, "kamar ya fa? Ban fahimce ki ba?"
"Ya kamata ayi auren su a huta, ina ga zai fi, nima hankali na zai fi kwanciya, duk da har yanzu be sake nuna alamun ciwo ba, amma kuma ka san halin Baba na, ta yiwu jure wa yake yi, amma wlh yana son aure". Taƙarishe maganar da marairaice wa tamkar zata yi kuka
Murmusawa Abba yayi yace, "ban da abun ki Adda dama wa yace miki ba ya son aure tunda har ya isa? ba kya ganin hakan zamu shiga haƙƙin Maimuna ne? Ki duba fa ki gani yarinya ce ita, duka-duka nawa take? yanzu ne za su shiga ajin ƙarshe na Scondary".
"Na sani Abban su, nima ba wai na ce yanzu za'a yi auren ba, amma ina so a tsayar da ranan auren zuwa nan da shekara ɗayan, idan ta gama karatu sai a ɗaura auren, inyaso taci gaba a gidan ta, kuma wannan ba Shawara ta bane shawaran Ameera ce (tana nufin mahaifiyar Maimuna) kuma nima naga hakan ya fi, ka ga za su fi saka wa a ransu dole za su auri junan su, Ni dai ba na ƙaunar maganar nan ta tashi a banza Abban su, sabida take-taken Baba na ya nuna hakan ƙarara ba ya son Maimuna matsayin mata".
Still dai Abba murmushi ya sake yi, kafin ya riƙo hannayen ta duka biyun yace, "ki kwantar da hankalin ki matata, insha Allahu burin ku ke da ƴar uwan ki na son haɗa zumunci sai ya cika, ABUL KHAIRI yana jin maganar mu bazai taɓa watsa mana ƙasa a idanu ba, sannan ma ai Maimuna jinin sa ne, bazai taɓa ƙin ta ba, ki dena ma maganar nan kin ji? zan neme sa zuwa nan da kamar sati ɗaya tunda a time ɗin Maimuna sun gama Exams ɗin su, inyaso sai a sanar musu har ita domin tasan da maganar itama".
Yalwataccen murmushi Mamy ta saki, cike da farin ciki tace, "to hakan ma yayi, Allah dai ya dafa mana baki ɗaya".
"Ameen Matata, yanzu tashi mu koma Parlour mun bar yara su kaɗai kar suyi zaton wani abun muke yi".
Dariya ta sheƙe dashi tana bugun kafaɗan sa na hagu, tace, "kai Abban su kaji ka da wata iriyan magana, to me kake nufin za su zarga? Ko yau suka saba ganin mun ƙule a ɗaki?".
Ɗage giran sa ɗaya yayi yana dariya yace, "to ke ce fa don Allah da wani korar Autana don zamu yi magana, kuma ai su sun san mu ba tsofaffi bane, da sauran mu dai".
Mamy ta harare sa tace, "kana da kamar Baba na kace baka tsufa ba? Ga shi har ka kai ɗiya cikin ɗaki".
"To mutane nawa ne suka kai ɗiyoyi cikin ɗakin, amma ganin kansu suke yi tamkar yara ƴan shekara ashirin?"
"Haka ne, amma dai ban da kai, don su ma basu san inda kansu ke musu ciwo bane, sun ci zamanin su, sannan suna son su ci zamanin ƴaƴan su, nan gaba ma zamanin jikokin su za su ce zasu ci, Allah dai ya kyauta, yasa mufi ƙarfin zukatan mu".
"Ameen ameen ADDAN MU Deebizah".
Murmushi kaɗai tayi masa, ta miƙe tana nufan ƙofa
Shima tashi yayi yabi bayan ta suna sauya wani hira.
🌐🌐🌐
Da dare da suka zo kwanciya, Azeeza kan gadon Maimuna ta kwanta, (asali gadon Zee ne kafin tayi aure) don a cewar ta a kan gadon take son kwanciya yafi girma, shiyasa suna gama cin abinci, da ta tabbatar yaya ABUL ya shige ɗakin sa, itama sai ta miƙe ta shige tayi kwanciyar ta.
Su Batool basu taso ba sai da suka gama kallon su, Maimuna ta soma shigo wa ɗakin, nan tayi turus tana kallon Azeeza dake saman gadon ta tana faman kashe murya tana waya, tsayawa tayi tana kallon ta, sai kuma taja ƙafafuwan ta cike da sanyin jiki ta nufi gefen gadon, har ta ɗaga ƙafa zata haye, Azeeza ta tsayar da ita da hannu
Sai da ta kashe wayan kafin ta tashi zaune tana buga mata harara tace, "a gidan uban wa zaki kwanta ke kuma?"
Murya a sanyaye Maimuna tace,"zan kwanta a nan ne Aunty".
Dogon tsaki Azeeza taja tana sake banka mata harara tace, "dalla ware a nan, babu ƙatuwar da zan kwana da ita, gwara ma ki nemi wajen kwanan ki, don nima nan yayi min kaɗan idan zan samu ƙari ina so".
Kasa motsi Maimuna tayi a wajen
Azeeza koma wa tayi ta kwanta tana ɗaukan wayan ta, ta soma latse-latsen ta.
Lokacin ne Batool ta turo ƙofan ta shigo, sannan ta mayar ta rufe ta juyo tana kallon Maimuna dake tsaye, ta kasa motsa wa a inda take ɗin
"Lafiyan ki ke kuma kika tsaya a tsaye?"
Ɗago ido tayi ta kalli Batool ɗin, sai dai ta kasa cewa uffan
"Nima dai wlh duk ta ishe Ni a nan, tana ta tsotse min ruwan kai, ki tashi min a kai da Allah". Cewar Azeeza cike da taƙama
"A'a a kan me zata matsa miki a kai, ba gadon zata hau ba?" Batool tafaɗa tana ƙarisowa wajen
"Sai dai ta hau gadon ki amma ba nan ba, Ni kaɗai zan kwana ba na son a takura min".
Turo baki Batool tayi, sai kuma ta mayar da idanun ta kan Maimuna da har ta soma shimfiɗa zani a ƙasa zata kwanta, wafce zanin tayi tana jan tsaki tace, "kee dalla wuce can! wlh kina da kayan takaici, a ƙasan ne zaki kwana?"
Murmushi Maimuna kaɗai tayi mata bata ce komi ba
Cike da takaicin ta tace, "ki hayo gado na mu kwanta don wlh baza ki kwana a ƙasa ba". Daga haka Batool ɗin haye wa gado tayi ta bar ta a nan
Sai itama daga baya ta hayo gadon, tunda ta san ko tayi ninyan kwana a ƙasa Batool baza ta barta ba
Ita kuwa Batool sosai take takaicin halin Maimuna, wani zubin ji take yi tamkar ta maƙure ta sabida haƙurin ta yayi yawa, ko kaɗan in an cuce ta baza ta taɓa rama wa ba, "in ba iskanci ba ita Azeezan ina taga irin gadon a gidan su da zata ce za'a takura mata?". Dogon tsaki taja tana juya wa Maimuna baya.
Duk da Maimunan taji ta, kuma ta san ɗayan biyu ko da ita take yi, ko kuma da Azeeza, amma bata yi magana ba bare ta motsa, illa sake lafe wa da tayi tana lumshe idanu.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT *🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
𝙽𝚊 𝚜𝚊𝚍𝚊𝚞𝚔𝚊𝚛 𝚐𝚊 𝙼𝚊𝚑𝚊𝚒𝚏𝚒𝚢𝚊 𝚝𝚊 𝙰𝚋𝚊𝚛 𝙰𝚕𝚏𝚊𝚑𝚛𝚒 𝚗𝚊, 𝚞𝚠𝚊𝚝𝚊 𝚖𝚊𝚐𝚊𝚗𝚒𝚗 𝚔𝚞𝚔𝚊 𝚗𝚊, 𝙸 𝚕𝚘𝚟𝚎 𝚢𝚘𝚞 𝚜𝚘 𝚖𝚞𝚌𝚑 𝙼𝚘𝚖𝚖𝚊 ❤️
*________________________________*
*PAGE 9*
*________* Washe gari gaba ɗaya gidan watse wa suka yi suka bar Azeeza, tunda ita dama ba ta zuwa makaranta, tunda ta gama Secondary School ɗin ta ta'ajiye karatu a gefe.
Yau ma kamar kullum su Batool suka soma dawowa, Azeeza na ganin hakan ta shiga tayi wanka ta fito tayi musu sallama a kan, "zata je ta dawo". Ba ko ina ta zarce ba sai gidan su ƙawarta dake ƙasan layin, dama ta rabu da zuwa shiyasa ta shirya zuwa mata wuni tunda ta zo anguwan.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
Ƙarfe 09:00am. Ziyada suke da Lectures yau, sai dai koda ta shirya gidan su Rahina ta wuce ta ɗauko ta a motan ta, suna zuwa bakin titi tayi peacking suka zauna zaman jiran Saleem kamar yanda yace mata.
Suna nan a zaune suna hiran su Saleem ya ƙariso a motar sa, sai suka fito daga motan. gaisawa suka yi da Rahina cikin barkwanci suna tsokanar juna, sannan ya kalli Ziyada dake ta faman yauƙi yace, "Baby taho muje ko?"
Murmushi tayi masa tana masa fari da ido, kafin ta kalli Rahina tace,"Besty mun tafi, insha Allahu zuwa kafin a tashi zan dawo, sai ki wuce school ɗin da motan".
"Babu damuwa ƙawa ta". Rahina tafaɗa tana murmushi, kafin ta sanya hannu ta amshi keey ɗin motan, shiga motan tayi ta zauna tana kallon su ta mirror
Suna tsaye ne suna magana basu rigada sun ƙarisa inda Saleem ɗin yayi peacking ba
Wani irin murmushi Rahina tayi tana ɗaukan wayan ta ta hau ƙesta musu hotuna ba tare da sun sani ba, sai da ta gama taja motan tayi gaba, tayi nisa sosai kafin ta tsaya, tana hango motan ta mirror can daga nesa. Sai da taga sun yi gaba kafin taja motan ta karya kwana tabi bayan su.
A wani hotel suka tsaya, itama sai taja ta tsaya, ta ɗauki wayan ta tayi musu hotuna kafin ta saki shu'umin murmushi tana faɗin, "yanzu aka soma wasan, tabbas Ziyada nayi alwashin ko ta halin ƙaƙa ne sai na raba ki da ABUL KHAIRI, domin ABUL KHAIRI nawa ne Ni kaɗai, da sannu zan cire soyayyar ki a ransa, in kuma dasa nawa a cikin ransa". Sai ta sake sakin murmushi taja motan ta nufi school ɗin su dake BUK.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
*03:30pm.*
Lokacin da Azeeza ta fito daga gidan su ƙawarta, sai ta sami keke napep kanta tsaye ya wuce da ita gidan gonan ABUL KHAIRI. Bayan me napep ɗin ya sauke ta tana biyan sa kuɗin sa; ta hangi motan Ziyada tana buga horn a bakin Gate ɗin, da idanu tabi motan da kallo har ta shige, sannan itama ta nufi bakin Gate ɗin. Tana isa ta ƙwanƙwansa ƙofan
Me gadi ya buɗe ya fito yana tambayan ta, "lafiya?"
"Baba don Allah ABUL KHAIRI na ciki?"
"Eh yana ciki, in ce dai lafiya ko?"
Gyara tsayuwar ta tayi tana faɗin, "eh Baba, dama so nake Yi in gansa, don Allah idan babu damuwa ka taimaka min".
"To shikenan, bari inje in sanar masa".
Azeeza tace, "a'a Baba ba sai ka je ba, ka bar Ni in shiga dan Allah".
Ɗan jimm.. yayi yana kallon ta, sai kuma yace, "gaskiya Hajiya baza ki samu ganin sa ba, sai dai ki bari inje in sanar masa kamar yanda yace na riƙa yi".
Jakan ta tabuɗe ta ciro dubu biyar ɗin da suka rage mata, ta miƙa masa tana cewa, "don Allah Baba kayi min wannan alfarman, ka yarda dani kaji babu abinda zai faru bare ya sami aikin ka, yanzu zan shiga in fito, tunda dama shi yace in zo".
Me gadi washe baki yayi ganin farare bugun Abuja a hannun ta, ya saka hannu ya amsa yana cewa, "to Hajiya babu damuwa ai, in ce dai shi ne yace ki zo ɗin ko?"
"Eh shi ne".
"Tom shiga, a fito lafiya". Yafaɗa yana matsa mata a hanya
Shiga tayi ta nufi hanyan Part ɗin sa, ɗan ƙaramin Plet ne da aka yi sa tamkar bukkan Fulani, sai dai da gini aka yi, saman rufin kuma ya kasance irin na Bukka ne.
Tana isa sai ta zagaya ta bayan ginin, babban windows ta gani guda biyu, waɗanda aka yi su da Glasses, dama a buɗe suke sai ta leƙa kanta ciki. abinda ta gani ne ya ɗaga mata hankali
ABUL KHAIRI da Ziyada ta gani zaune saman kujera, Ziyada na kan cinyan sa yana bata abinci dake cikin take-away, ita kuma sai zuba masa shagwaɓa take yi
Da sauri Azeeza ta runtse idanuwan ta tana jin zuciyarta na tafarfasa, sake ware idon tayi kan su ranta duk a ɓace, tsananin baƙin ciki ne da kishi ya mamaye ta. "Wace ce wannan yarinyan?" Tambayan da yazo mata a zuciya kenan. Sai dai bata da me bata amsa illa ƙura musu idanu da tayi tana kallon kayan takaici, zuciyarta na sake tafarfasa tamkar zata mutu, da sauri taja jiki ta matsa a wajen hawaye na kwaranya a face ɗin ta, ta daɗe a haka tana dafe da ƙirji kafin ta sake kallon windown, kamar ta leƙa sai dai tana tsoron abinda zata sake gani, dole ta nufi hanyan fita daga gidan
Tana hango me gadi ta saka gefen gyalen ta ta share hawayen fuskarta, ta dai-daita kanta sannan ta nufi bakin Gate ɗin, sallama suka yi da me gadin tafice da sauri.
Tafiya kawai take yi tana tunanin abinda ta gani, sosai ranta ke suya tamkar ta koma ta kashe su duka biyun haka take ji, a ranta ta ɗauki alwashin dole sai ta raba su, koda kuwa hakan na nufin sai ta kashe Ziyada ne, sai yanzu ta gane cewa sabida Ziyada ne ABUL KHAIRI ba ya kula ta, tunda ya samu wacce tafi ta komi da komi, tabbas ta ɗau alwashi sai ta raba su, kuma sai ta saka soyayyar ta a zuciyar ABUL KHAIRI, domin shi ɗin nata ne ita kaɗai, ba'a yi macen da zata riga ta mallakan sa ba. Tana tafiya tana share hawayen ta, a haka har ta kai bakin titi, ta tare me napep tayi gida.
Koda ta shiga gidan babu kowa a Parlour, kanta tsaye ta shige ɗakin su Batool
Suna zaune a kan gadon Maimuna suna duba Books a tare, suna muhawaran yanda jarabawar zai kasance musu gobe, sai ganin ta suka yi ta shigo ko sallama, da idanu suka bi ta dashi babu wanda ya tanka mata cikin su
Ita ma kuma bata bi ta kansu ba, ta nufi wajen jakanta ta hau haɗa kayan ta, har ta fice babu wanda ya kula ta
Batool ce ma me ƙoƙarin shiga harkan ta, tunda tasu tafi zuwa ɗaya, amma dayake tana jin haushin ta shiyasa bata kula ta ba, sai ma taɓe baki da tayi a fili take faɗin, "a gayas, dama bamu gayyar ki a nan, mtsww! Ƴar wahala".
Ita dai Maimuna bata ce komi ba, illa murmusawa da tayi tana mayar da kanta zuwa ga kallon littafin dake gaban su.
Azeeza na fita ta shige ɗakin Mamy
Mamy dake zaune da Laptop a gaba, sai ganin Azeeza tayi cikin ɗakin ta babu ko sallama, kallon ta tayi cike da mamaki ganin ta da kayan ta, tace, "ah ah Azeeza lafiya, ina zaki je da jakan?"
Azeeza tace, "tafiya zan yi Gwaggo".
"Tafiya kuma? Me ya faru ne, wani abun aka yi miki?"
"A'a kawai dai..." Shiru tayi don bata san me zata ce ba
Mamy tace, "ko dai kin fasa mana kwana biyun ne? Ko kuma wani yayi miki wani abu ne wanda baki ji daɗin shi ba? Ki faɗa min don Allah".
Murmushi Azeeza tayi tace, "wlh Gwaggo babu komi, na fasa zaman ne sabida na tuna akwai bikin da zan je wannan satin, kuma ina so in je gidan Gwaggo Halisa gobe (Ƙanwar Mahaifin ta)".
Murmushi Mamy tayi sabida jin abinda ta faɗa, sai tace, "ki ce dai zaki tafi Azeeza, amma me ya haɗa tafiyan ki da bikin da zaki je sati me zuwa? Kwana wajen biyar fa, sannan nan da Jigawa gidan Adda Halisa ai ko gobe zaki iya komawa gida kuma ki je a goben. Ki faɗa dai idan su Batool ne suka yi miki wani abun sai in ɗau mataki".
Azeeza cike da borin kunya jin ƙaryan ta be shiga ba, ta saka hannu tana sosa ƙeya tace, "babu komi wlh, zan tafi ne, amma zan dawo ai Gwaggo tunda ina nan".
"To shikenan. bari in baki na mota, idan kin je ki gaishe da iyayen naki, ki gaida min da umma itama, insha Allahu zan saka lokaci in zo duba ta".
Ita dai Azeeza da, "to". Kaɗai ta amsa mata tana tsaye a inda take
Jakar ta ta janyo dake kan gadon, ta ciro kuɗi masu yawa, ta ƙirga ta cire mata duba goma cif, sannan ta miƙa mata tace, "ga shi to sai ki siya kayan kwalliya, babu yawa, Allah ya kiyaye hanya".
"Amen amen Gwaggo". Azeeza ta faɗa hakan tana washe baki bayan ta saka hannu ta amsa
"Koda yake nasan Aƙilu na nan, ki duba idan yana nan sai ya kai ki gida kawai, Allah ya tsare hanya, ina nan dai ina jiran ki". Mamy tace hakan tana murmushi
"To Gwaggo". Ta'amsa tana fice wa
Ta daɗe Mamy tana tunani a ranta, kafin ta ja numfashi taci gaba da latsa Laptop ɗin ta.
▪️▪️▪️
Azeeza na fita ta samu Aƙilu a bakin famfo yana wanke mota, ƙarisawa wajen sa tayi, tana shan ƙamshi tace, "Kai Drever kazo ka kai Ni gida in ji Gwaggo Deebizah".
Ɗagowa yayi yana kallon ta, sai ya taɓe baki a ransa yace, "ji da Allah yanda take yi sai kace ita ɗin ƴar wasu shegu ne a garin, mtsww". Ya ja tsaki yana mayar da kansa yaci gaba da wanke tayan motan ba tare da ya tanka ta ba
"Kai dan uwar ka ba da kai nake yi ba? Dama ai matsalan ƴan ƙauye kenan a kawo ku birni, Ku zo kuna nuna kun fi ƴan birnin, matsiyacin banza matsiyacin hofi".
Still ɗago da kansa Aƙilu yayi, ya kalle ta da murmushi a face ɗin sa yace, "daɗin abun ma, su uwayen ki duk daga ƙauye su ke, in ji dai duk asalin ku kenan?"
Ta banka masa harara tace, "mun fi ƙarfin ƴan ƙauye wlh, sai dai iyayen ka ne ƴan asalin can, banza kawai ajawo. Kuma wlh idan baka shiga mota ka kai Ni ba na rantse da Allah sai na je nayi maka sharrin da baza ka taɓa cire kanka ba a gidan nan, ɗan iska ɗan tasha".
Ran Aƙilu sosai ya ɓaci, sai dai kasancewar shi me yawan dariya da barkwanci, dole ya danne ɓacin ransa, sai ma murmushi da ya sake yi yana kallon ta yace, "to ranki ya daɗe! Ki jira Ni mana saura taya ne kaɗai in wanke, idan na gama sai mu tafi ko?"
Ƙwafa tayi tana mishi kallon wulaƙanci, bata ce komi ba ta juya ta ɗaya side ɗin motan ta shige
Shi kuma Aƙilu be sake bi ta kanta ba ya ci gaba da wankin sa, har sanda ya gama amma ya ƙi shiga motan, sai faman ƙalƙale motan yake yi, ya wanke nan ya wanke can
Azeeza fa ta shaƙa da yawa sabida jiran nan da take yi, sai ta zuge Glasses Motan ta leƙo tana faɗin, "wai uwar me ka tsaya yi ne har yanzu baka gama ba?"
"Uwar ki na tsaya yi". Ya faɗa ƙasa-ƙasa yana hararan gefen ta
"Ka ce mene?"
"Cewa nayi gani nan zuwa na kammala". Ya faɗa da sauri yana nufan ƙofan motan ya buɗe ya shiga
Dogon tsaki taja tace, "ƙaryan iskanci kake yi wlh, matsiyaci wanda be gaji arziƙi ba".
Aran Aƙilu yace, "ban gaji arziƙi ba ko baki gaji arziƙi ba, shegiya birgi-birgi! Yau da Ni kike zancen sai na koya miki hankali". Jan motan yayi da gudu yayi bakin Gate, horn yayi me gadi ya buɗe masa ya fice
Yana fita shima motan ABUL ya ƙariso wajen, hakan yasa me gadin be mayar da Gate ɗin ba, ya bar masa ya shigo. Shi ABUL KHAIRI be kalli motan ba bare ya san waye a ciki
Ita kuma Azeeza kallon motan ABUL KHAIRI take tayi, a ranta tana ayyana abubuwa da dama, ta so tana gidan ne ya dawo tayi masa magana, sai kuma ta saki murmushi a fili tace, "na san duk tsula tsiyan nan da kake yi babu wanda ya sani a gidan ku, amma mu je zuwa da sannu zan fasa ƙwan, tabbas wannan hanyar kaɗai ya isa na raba ka da tsinannaniyar can dana ganku tare".
"Wai da Ni kike yi ne?" Cewar Aƙilu yana kallon ta ta mirror
Harara ta sakar masa tace, "a'a da uwar ka nake yi".
Dama yayi ne don ya tsokane ta, shiyasa yayi murmushi ya soma jan motan da wani irin Speed, sosai yake gudu kamar zai zubar da su a kan kwalta, ga shi titin a cike take maƙil, haka yake yin over taking, sai yayi kamar zai buga wata motan sai ya ja birki ya rage gudun a lokaci ɗaya
Hakan yasa Azeeza dake baya take ta bige wa da kujerun gaba, sosai ta jigata a ɗan lokaci ƙanƙani. Cikin fusata tace, "wai kai haka ake tuƙi a garin ku ne? Ba ka da hankali ne zaka ji min ciwo?".
Cikin murmushin ƙeta yace, "yi haƙuri, wlh kinga sauri nake yi Alhaji na jira na zai aike Ni, kuma ke kin ce sai na kai ki, yanzu idan ya dawo be gan ni ba akwai matsala, shiyasa nake wannan gudun in je in dawo".
Zagin shi ta hau yi, tana gaya masa maganganu
Shi kuma be fasa tsula gudu ba, yana tuƙin ganganci ta yanda zata sha wahala, har suka kai ƙofar gidan su Azeeza sai ƙunduma masa ashar take yi
Tana fita ya ja motan ya baɗe ta da ƙura ya bar wajen yana sheƙa dariyan mugunta
Ai kamar ya kunna Azeeza, nan ta tsaya tayi ta auna masa zagi tana cewa, "za su haɗu ne, sai ta shuka masa rashin mutunci duk sanda ta dawo gidan nan". Sai da ta gama tijaran ta a waje har yara sun soma taruwa kafin ta ɗau jakar ta ta shige gidan na su.
Umman ta na bakin ƙofa a zaune tana lissafin kuɗin awara, sai ganin Azeeza tayi ta shigo, da idanu tabi ta, kafin tace, "a'a ke kuma da waye ne kike ta wannan kumburin? Koro ki suka yi ne kika dawo yau?"
Sai da taja tsaki kafin tace, "ba koro Ni suka yi ba, Ni ce na dawo don ganin dama na". Taƙarishe maganar tana shigewa ɗaki
Taɓe baki Umma Sulaima tayi tace, "ina nan zaune ai zaki zo ki sanar dani duk abinda ke faruwa". Taci gaba da abinda take yi.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN*💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT *🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
..... *SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga mahaifiya ta Abar Alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love you so much Momma._ ❤️
*HIKIMAR FARILTA SALLAH*
'''An farilta sallah domin a cikin ta akwai godiya ga Mani'imcin sarki jalla Ta'ala, wanda yake shi ne macancancin godiya da yabo, kuma shi ne kaɗai muka keɓe shi da ruku'u da sujada. Ba wani mahaluki da ya dace da wannan. Idan wata masifa ta sami mutum yakan yi maza ya fake da Allah ta yin Sallah, kamar dai yadda Allah yayi umurni a cikin suratul Baƙara, aya ta 45 da cewa:
"Kuma ku nemi taimako da yin haƙuri, da Sallah".
Ganawar da bawa yake yi da Ubangijin sa a cikin Sallah ita ce bauta wadda take ƙarfafa zumunta tsakanin bawan da Ubangijin nasa. Ubangiji kuma yana yi wa bawan baiwar darajar samun kusanta da shi. Hikima ce kammalalliya da aka farilta sallah, don kuwa ta yin Sallah ne ake kankare wa bawa zunubai, muddin dai ya yi sallah yadda ake so.
An ruwaito cewa annabawan da suka wuce, ko wannen su yana da Sallah da yake ibada da ita. Sallolin suna da lokatai biyar; asuba, azahar, la'asar, lokacin faɗuwar rana da na isha'i. Ashe za mu lura cewa Allah ya tara wa Annabi da al'umma tasa sallolin dukan annabawan da suka gabata.
Allah ya sa mu dace.'''
*________________________________*
*PAGE 10*
*________* *AFTER TEN DAYS*
Gaba ɗayan su suna zaune a Parlour da misalin ƙarfe 09:00pm na dare, bayan sun gama cin abinci Abba ya tsayar da su a cewar, "Zai yi magana da su," in ka ɗauke Baby da take barci a saman kujera kowa ya zauna ya nutsu yana sauraron Abban
Sunan ABUL KHAIRI Abba ya kira
Sai ya ɗago kansa yana kallon sa tare da amsa mishi cikin girmamawa
"Na san baka mance maganar da muka taɓa maka shekaru biyu baya da suka wuce zuwan Maimuna gidan nan ba, da kuma maƙasudin zaman nata a gidan?"
A tare gaban Maimuna da na ABUL KHAIRI suka yi mummunan buga wa, wanda har sai da Maimuna ta saka hannun ta ta dafe ƙirjin ta tana sake sad da kanta ƙasa tare da runtse idanu
Shi kuwa ABUL ya kasa cewa Abban komi, illa kafe sa da idanu da yayi yana sauraron yanda gaba ɗaya jikin sa ya sauya da wani irin yanayi me wuyan fassara wa, tare da bugawan zuci da fargaban abinda ke shirin faruwa da shi ɗin da har Abba yake son tayar da maganar
"Kayi shiru Babana ana maka magana?" Cewar Mamy da ta tsare sa da idanu tana karantan yanayin nasa
"Ina ji ai Mamy". Yafaɗa a hankali yana mayar da kansa ƙasa
Abba yace, "to maganar ce yanzu zamu yi ta, don mun rigada mun tsayar da magana nan da shekara ɗaya me zuwa idan ta gama karatun ta". Sai ya mayar da idanun sa kan Maimuna, ya kira sunan ta
A hankali Maimuna ta amsa mishi cike da tsananin fargaban da bata san dalili ba
"Maimuna muna fatan zaki yi mana wani alfarma a matsayin mu na iyayen ki, wanda baza mu taɓa zaɓa miki abinda zai cuce ki ba, sai dai ma idan mun ga abun dake shirin cuta miki mu yi gaggawar tare wa. Mun yanke shawaran haɗa ku aure dake da yayan ki ABUL KHAIRI. Da fatan zaki yi mana biyayya kamar yanda muka nemi alfarma wajen ki?"
Lumshe idanuwan ta tayi hawaye na zubo wa a saman kuncin ta suna ɗiga a ƙasa, take jikin ta ya soma rawa wanda ya saka ta kasa ma buɗe baki bare tayi magana
Batool dake kusa da ita, cike da sanyin jiki ta saka hannun ta ta riƙo nata tana matse wa a cikin nata
"Maimuna.." Mamy ta kira sunan ta cikin sanyin murya
Sai dai har a time ɗin ta kasa amsa wa Mamy, kuma ta kasa ɗago kanta
Mamy tace, "idan har ba kya son wannan haɗin kiyi magana kin ji? don babu wanda zai miki auren dole ɗiya ta, Ni da Mahaifiyar ki ne muke son mu haɗa ku, kuma kinga zaɓin mu be zama dole ya zama zaɓin ku ba, idan har ba kya so, to, babu wanda zai miki tilas".
ABUL KHAIRI dake sauraron duk abinda ke faruwa, zuciyar sa na wani irin tuƙuƙi tamkar ya tashi ya maƙure Maimuna, ita kawai yake jin haushin ta a halin yanzu, jira kawai yake yi yaji amsar da zata ba su. Runtse idanuwan sa yayi jin muryan ta me tsananin sanyi ya bugi kunnen sa
"Na amince".
Gaba ɗaya da Abba da Mamy murmushi suka saki
Abba yace, "yauwa ƴar albarka, dama mun san baki da matsala baza ki taɓa watsa mana ƙasa a idanu ba, Allah ya miki albarka".
Batool ce kawai ta amsa, fuskar ta cike da murmushi tana kallon Maimuna da ke sake sunkuyar da kanta
"Kai kuma kaji ta amince, saura kai ka amincen ne ko kuwa har yanzu shirun ne maganar ka?" Cewar Abba yana tsare ABUL KHAIRI da idanu
Kansa a ƙasa cike da tsananin takaicin Maimuna gami da tsanar ta yace, "abinda kuka zaɓa min nima shi ne zaɓi na".
Sosai amsar nashi ya faranta ransu, cikin fara'a sukai ta saka musu albarka, kamin suka ba su damar tafiya
ABUL KHAIRI ya soma tashi ya shige ɗakin sa
Su ma su Maimuna miƙe wa suka yi suka bar parlour'n, suka shige ɗakin su.
Da shigar su Maimuna ta nufi kan gadon ta ta zauna, kanta a ƙasa ta hau zub da hawaye a hankali
Batool ƙarisowa kusa da ita tayi ta zauna gefen ta fuskar ta yalwace da murmushi, don sosai wannan haɗin yayi mata daɗi, ta saka hannu ta ɗago kan Maimuna tana shirin magana, sai ganin hawaye saman fuskar ta tayi, take a nan fara'an ta ya gushe, tayi saurin tambayan ta da, "lafiya, mesaya take kuka?"
Shiru Maimuna tayi mata tana ci gaba da kukan ta
Sosai jikin Batool yayi sanyi, ta saka hannu tana share mata hawayen
Amma kuma Maimuna ta kasa dena kukan, sai yi take yi har da shashsheƙa
"Maimuna meyasaka kika amsa musu bayan kin san ba kya son shi? Idan har kin san zaki Cutu me zai saka ki amsa musu?"
Lumshe idanuwan ta Maimuna tayi tana sauke ajiyan zuciya akai-akai, ba tare da hawayen sun tsagaita daga zubar da suke yi ba, sai ta gyara ta aza kanta saman pilow ba tare da ta tanka wa Batool ba
Ita kuma Batool sai ta tsaya kawai tana kallon ta, tsawon mintuna goma suna a haka amma Maimuna bata dena shashsheƙan kukan da take yi ba
"Sister bazan iya ganin ki cikin wannan halin ba, zan je in sanar wa da su Abba ba kya son wannan haɗin". Batool tafaɗa tana miƙe wa zata fice
Da sauri Maimuna ta tashi zaune ta riƙo mata hannu, cikin rawan murya tace, "a'a.. kar ki je don Allah".
Kallon ta tayi na ɗan wani lokaci, kafin ta koma ta zauna, cikin tausayawa tace, "meyasa baza ki bar Ni in je in sanar musu ba tunda ke kin kasa? Shikenan kuma sabida wannan sanyin halin naki sai ki zauna koda yaushe kina cutan kanki? Tabbas wannan haɗin yayi min daɗi matuƙa, amma kuma yanzu da na tuna irin zaman da kuke yi da yaya ABUL kullum cikin tsangwaman ki yake yi, sai naji sam hakan ba me yiwuwa bane, zaman ku a inuwa ɗaya babban illa ne a gare ki".
Murmushi Maimuna ta saki, tana son mayar da ƙwallan da ya cika mata idanu, sai dai kuma bata yi nasaran hakan ba, sai da suka zubo saman fuskar ta, ta saka hannun ta ta share still tana murmusawa tace, "ke ma kin faɗa da bakin ki haɗin nan ya saka ki farin ciki, to su ma su Mamy hakan yake a wurin su, to me zai saka Ni in ɓata muku wannan farin cikin a kan abinda be fi ƙarfi na ba? Kar ki manta Mamy tace ita da Ummu suke son su haɗa mu, kinga kuwa idan har na nuna ba na so na san Mamy baza ta taɓa bari ayi auren nan ba, wanda kuma hakan dole zai saka su ji babu daɗi a ransu, Ni kuma ba na fatan hakan, zan so in faranta musu rai kamar yanda suka nemi alfarma a waje na, Ni babu wanda nake so a raina tunda har yanzu ban taɓa yin saurayi ba, sannan kuma ba na ƙin Yaya ABUL KHAIRI a cikin raina, kawai dai na kasa jure wa ne, amma ban san dalilin da ya saka nake yin kuka ba.." ta ƙarike maganar nata tana me fashe wa da wani sabon kukan
Batool itama hawaye ta soma yi na tsananin tausayin Maimuna, ta san halin Maimuna tana da sanyin hali da tsananin haƙuri, zata iya jure ko ma mene ne sabida ta faranta wa makusantan ta, Allah yayi ta da haƙuri da jure ko wani hali ne da ya same ta, tamkar dai Mamy ce ta haife ta, halin su ya zo ɗaya matuƙa, domin kuwa Maimuna ita kaɗai ce ta fita Zakka a ɗakin su, gaba ɗaya sauran ƴan uwanta halin Ummu suka biyo, basu da haƙuri ko kaɗan, idan kayi musu za su rama ko kai uban waye, amma ita Maimuna idan ka cuce ta, sai dai ta bi ka da murmushi, halin ta daban ne, har tafi Mamy haƙuri da sanyin hali, ga ta shirun ta yayi yawa matuƙa, akasari tafi son yin murmushi a kan ta buɗe baki ta baka amsa.
Rungume ta Batool tayi suka ci gaba da kukan tare.
▪️▪️▪️
ABUL KHAIRI tunda ya shiga ɗakin sa ya haɗa kai da gwiwa, sosai ya shiga cikin wani hali da abinda ya faru yanzu ɗin, gaba ɗaya ya nemi natsuwar sa da farin cikin sa ya rasa. Ba zai taɓa iya yin ma iyayen sa musu ba, sabida be saba ba, be kuma tashi da hakan ba, tun farko a kan turban da suka raine shi kenan, ba su taɓa neman abu wajen sa ya ƙi musu ba, don haka wannan ma ba ya tunanin zai iya musa musu, sai dai kuma ya ɗau alwashi a ransa sai ya ƙuntata wa Maimuna tunda har ta amince da auren nan, yana ganin kamar amincewar ta shi ne yasa auren su zai yiwu, kuma hakan shi ne babban kuskuren da ta tafka a rayuwan ta, da bakin ta sai ya saka ta dawo ta faɗa musu ba ta son auren, bazai taɓa bari ayi auren nan ba, duk hanyar da zai bi sai yabi ya saka ta ta faɗa musu ba ta son auren nan..
Lumshe idanun sa yayi yana jin wani irin tuƙuƙin baƙin ciki a zuciyar sa, ya jima a haka kafin ya ɗago kansa ya soma neman inda ya ajiye wayan sa, can ya hange sa saman mirror, a hankali ya sauka ya ƙarisa wajen ya ɗauka, komawa yayi ya zauna a bakin gadon ya soma duba wayan, missed calls ɗin Ziyada ya gani har wajen goma, yayi dialling Numban, sai dai a kashe ne, sosai ransa ya sake ɓaci, ya ajiye wayan yana kwanciya cike da baƙin ciki da tsanar Maimuna a ransa, Allah-Allah yake yi gari ya waye ya aiwatar da ƙudirin sa a kan ta. Numfashi yaja yana sake gyara kwanciyar sa, daƙyar barci ya ɗauke shi a wannan daren cike da mafarkai kala-kala, har da mummunan mafarkin da yayi a kan Ziyada ta rabu dashi sabida auren sa da Maimuna, a firgice ya tashi jikin sa duk ya jiƙe da zufa, sosai hankalin sa ya tashi da mafarkin nan duk da kuwa ya san ba gaske ne ba, amma kuma a yanda ya ɗauka hakan zai iya faruwa a gaske ɗin, tunda ya fi kowa sanin baƙin kishin Ziyada. Be iya komawa barcin nan ba a daren, illa zagaye ɗakin da yayi ta yi ya hana kansa sukuni.
.
_Hmm akwai chakwakiya fa, yanzu ne aka soma wasan._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
𝙽𝚊 𝚜𝚊𝚍𝚊𝚞𝚔𝚊𝚛 𝚐𝚊 𝙼𝚊𝚑𝚊𝚒𝚏𝚒𝚢𝚊 𝚝𝚊 𝙰𝚋𝚊𝚛 𝙰𝚕𝚏𝚊𝚑𝚛𝚒 𝚗𝚊, 𝚞𝚠𝚊𝚝𝚊 𝚖𝚊𝚐𝚊𝚗𝚒𝚗 𝚔𝚞𝚔𝚊 𝚗𝚊, 𝙸 𝚕𝚘𝚟𝚎 𝚢𝚘𝚞 𝚜𝚘 𝚖𝚞𝚌𝚑 𝙼𝚘𝚖𝚖𝚊 ❤️
*________________________________*
*PAGE 11 & 12*
*________* Washe gari da wuri ya bar gidan zuwa wajen aiki. Koda ya je Office be zauna ba, yayi ta zagaye yana faman ƙulla wa da kwance wa a zuciyar sa, sai da ya tabbatar Abban sa ya zo Companin kafin ya lallaɓa ya baro. Gida ya wuce kai tsaye tunda ya san itama Mamy ta tafi wajen aikin ta.
Yana shiga Parlour ya tarar da Baby da Amir suna kallo
Da gudu Baby ta taso ta nufo sa tana murna. "Yaya sannu da zuwa". Tafaɗa da ƙarfi tana dariya
Jan hancin ta yayi shima yana murmushin yace, "Auta na an samu hutu sai zaman kallo ko?"
Still dariya tayi tace, "Yaya ai ba Ni na kunna ba Ya Amir ne".
A lokacin ne Amir yayi masa sannu da zuwa, yana ƙaryata abinda Baby ta faɗa
Yace, "to ya isa haka, ai ban hana ku kallon ba sai dai ku riƙa yi kuna karatu, musamman na islamiyya tunda yanzu kun samu hutu, lokacin da Yakamata ku riƙa yi kenan".
"To Yaya".
"Yauwa good Baby". Ya faɗa yana sake jan hancin ta, sannan ya miƙe daga ranƙofowar da yayi zuwa tsawon ta, yace, "kira min Maimuna ta same Ni a ɗaki".
Da sauri ta amsa mishi ta nufi ɗakin nasu
Shi kuma ya wuce cikin ɗakin sa.
Da shigar sa ya wuce kan gadon sa ya zauna, wayan sa ya zaro cikin aljihu yana latsa wa, sai kuma ya miƙe ya shige Toilet.
Lokacin ne Maimuna tayi Nocking tana jiran a bata iznin shiga, sai dai jin shiru sai ta sake yin Nocking ɗin, nan ma shirun da taji sai ta buɗe ƙofan ta shiga bayan da tayi sallama. Bata ga kowa ba, sai ta ja ƙafafuwan ta a sanyaye kamar yanda ta saba koda yaushe, ta nufi ciki ta duƙa a ƙasa tana jiran sa, kanta a ƙasa yake tana murɗa yatsun hannun ta, amma kuma a baɗini tsoro ne fal a zuciyarta, tana tunanin, "meyasaka Ya ABUL ya dawo gida kuma ya nemi ganin ta?" Tabbas tana ji a ranta ba alkhairi bane kiran nan da yayi mata..
Buɗe ƙofan Toilet ɗin da yayi, shi ne ya katse mata ɗan guntun tunanin nata, ta ɗago kai tana kallon sa, ganin fuskar sa a matuƙar ɗaure sai ya sake ɗaga mata hankali, da sauri ta mayar da kanta tana gaishe shi cikin girmamawa
Be ce mata komi ba sai da ya zauna a gefen gado, ya kuma ɗaukar wayan sa ya soma latse-latse, sai da ya gama can kuma ya kara a kunne yana sakin murmushi me sauti. "wai har yanzu barcin kike yi baki tashi ba?" Yayi maganar cikin wani salo na kashe murya
Daga can Ziyada ta ba shi amsa cikin shagwaɓa, tana faɗa masa, "kasala ne take ji, shi ne ya sa ta kasa ta shi."
Lumshe idanuwan sa yayi, kafin ya buɗe yace, "ko in zo in taimaka miki ne?".
Maimuna na a yanda take tana sauraron sa, sai dai ba ta jin muryan wacce yake waya da ita. maganar da yayi yanzu ɗin ya hautsina mata ciki, har ta ɗago tana kallon sa..
"Kin san idan har na zo ba iya nan zan tsaya ba, Ni zan miki wankan da kaina, sannan in shirya ki, kin san ba na son wahalar ki fa, amma fa bazan tsaya a iya nan ba, zan...."
Da sauri Maimuna ta sake duƙar da kanta tana ƙudundune jikin ta, sabida yanda maganar nasa suka bata matuƙar kunya, ai nan da nan ta rufe kunnuwan ta jin sauran maganar sun fi ƙarfin tunanin ta bare ƙwaƙwalwan ta, tuni jikin ta ya soma rawa, a ranta kawai raya wa take yi, "dama haka Ya ABUL yake ba ya da kunya?"
Shi kuwa ko a jikin sa wai don a kwai ta a wajen, yana kuma lura da ita, don idanuwan sa a kanta suke, sai dai yayi tamkar ba ita yake kallo ba, kuma yana hakan ne da gayya don taji ɗin. ya ɗau lokaci yana wayan kafin ya gama, ya ajiye wayan a gefen sa yana ɗago kai sosai ya kalle ta, cikin yatsina da dakakken muryan sa ya ce, "kee! Zo nan".
Jikin ta na rawa ta janyo jikin ta ta iso gaban sa, cikin rawan murya tace masa, "ga ta".
"Ɗago kanki ki kalle Ni".
Kasa ɗago kan nata tayi sabida kunya irin nata, ga kuma maganar da ya gama yi yanzu a waya, ya saka ta sake jin kunya matuƙa
"Wlh idan baki ɗago kai kin kalle Ni ba sai na miki..."
Kafin ma ya ƙarisa maganar har ta ɗago kan nata ta zuba masa idanuwan ta, sai dai yanda idanun suka shige cikin na sa sai ta kasa jure wa, ta sauke ƙwayar idanun nata ƙasa
Ƙare ma fuskar ta kallo yayi, sai kuma ya yatsina fuska yana sake ɗaure fuskar sa yace, "kina ji na? Ina son ki je ki samu su Abba ki sanar musu ba kya son auren nan tun wuri, idan ba haka ba, kika kuskura kika shigo gida na, wlh tallahi sai na ƙabari ya fi ki jin daɗi, sai na wulaƙanta rayuwar ki, sai na sa kin gudu da ƙafar ki, babu ke babu samun rahama duk sanda kika zama mata a waje na, domin baki kai matsayin da zan haɗa shimfiɗa da ke ba. Ki sani zaɓi na baki, ko ki je ki san yanda zaki yi ki faɗa musu ba kya son auren nan, ko kuma ki dauwama cikin uƙuba da baƙin ciki har ƙarshen rayuwan ki".
Tun sanda ya soma maganar na sa, Maimuna ta duƙar da kanta tana hawaye
Sai ya daka mata tsawa a kan, "ta tashi ta bar masa ɗaki".
Har ta miƙe sai taji muryan sa ya kuma cewa, "I hate you! I hate you more than anything's in this world! sabida kina son ki shiga cikin rayuwa ta, kina son ki shiga tsakani na da wacce nafi ƙauna".
Bata iya cewa komi ba ta nufi ƙofa ta bar masa daƙin.
Tana fita, Batool dake zaune a Parlour ita da su Amir, sai dai su suna kallo ne, yayinda ita kuma tana tsimayen fitowar Maimuna. ganin ta da tayi sai tayi zumbur ɗin mike wa ta nufo ta da sauri ganin hawaye a fuskar ta. Riƙo ta tayi ta hau tambayan ta, "me yayi mata?"
A lokacin ne ABUL KHAIRI ya fito daga ɗaki, harara ya wulla mata, sabida tambayan da tayi wa Maimuna a kunnen sa ya sauka
Da sauri ta sad da kanta ƙasa cike da tsoro
Be ce komi ba ya taka ya bar parlour'n ya fita waje.
Ita kuma Batool jan hannun Maimuna tayi suka nufi ɗakin su. Suna shiga ta zaunar da ita saman gadon ta, itama ta zauna ta hau tambayan ta, "wani abun yayi mata?".
Amma Maimuna tayi shiru illa kukan da take yi
"Don Allah ki faɗa min abinda yayi miki, be kamata ki zauna kina zurfin ciki a kan abinda kika san tabbas akwai matsala ba. shin mene ne yace miki? Ko wani abun yayi miki ne?" Batool ta sake jero mata waɗannan tambayoyin
Ɗago idanun ta da suka kaɗa suka yi ja tayi ta sauke a kan Batool ɗin, cikin sanyin murya da rauni irin nata tace, "cewa yayi in sanar da su Mamy ba na son auren, domin ya ce idan na aure shi babu Ni babu farin ciki har abada". Sai ta sake fashe wa da kuka tana ɗaura kanta saman cinyoyin ta
Hannun ta Batool ta saka ta ɗaura saman bayan ta, nan ta soma rarrashin ta cike da tsananin tausayin ta, ita kanta ta rasa tunanin da zata yi domin ta sama mata mafita. "Me zai hana ki bi abun da ya ce miki, ina ga shi ne kawai mafita kamar yanda ya faɗa miki, wlh bazan iya juran ganin ki kina shan wahala wajen ya ABUL ba, tunda ba ya ƙaunar ki ki sanar da su Mamy kema ba kya son auren.."
"Taya kike tunanin Ni zan iya zuwa in sanar musu ba na son auren?" Maimuna tafaɗa hakan bayan da ta ɗago kanta tana kallon ta, sai taci gaba da faɗin, "wlh bazan iya ba, meyasaka shi bazai je ya faɗa musu ba? tunda shi yana da wacce yake so".
Batool tace, "yana da wacce yake so, haka ya faɗa miki?"
"Eh mana haka ya faɗa min, kuma a gaba na yayi waya da ita, sannan ya ce min ba ya ƙauna ta, ita yake so". Ta sake faɗar haka tana me fashe wa da sabon kuka
"To Ni zan samu Mamy in sanar mata tunda ke baza ki iya ba, kiyi shiru don Allah ki bar kukan nan".
Daƙyar Batool ta rarrashe ta tayi shiru, sai dai ta kasa taɓuka komi a ranan, dole ita Batool ɗin ne taje ta ɗaura musu girkin rana, ta bar ta nan a kwance tana faman tunani, gaba ɗaya ta hana kanta sukuni illa maganganun ABUL KHAIRI da take faman tuna wa, da kuma yanda makomar ta zai koma
Ta sani a ranta bata taɓa tsanar sa ba, duk halin da yake nuna mata bata taɓa jin haushin sa ba, kuma zata iya yin biyayya ta aure sa ta zauna dashi da zuciya ɗaya ko wanne irin wahala zai ba ta. sai dai itama zata so a raba auren nan tunda ba ya son auren nan, "amma ta ya?" Ita baza ta iya zuwa ta faɗa ba.
▪️▪️▪️
Koda Mamy ta dawo, Batool da kanta ta sanar wa Mamy abinda ke faruwa, dawowar da ABUL KHAIRI yayi da abinda ya faɗa wa Maimuna
Mamy bata iya cewa komi ba sanda Batool ta gama zayyano mata, sai da ta jima tana tunani kafin ta kalli Batool ɗin, tayi mata umarnin, "ta je ta kira mata Maimuna."
Bayan ta kira ta ne, Mamy ta sake tambayan ta, nan Maimuna ta sake faɗa kamar yanda Batool ta faɗa ɗin
Ajiyan zuciya Mamy ta saki, kana ta ce, "babu damuwa, insha Allahu bazan bari ayi auren nan ba, da yardan Allah maganar nan ta mutu daga yau, kema kuma ki cire komi a ranki kinji?"
Gyaɗa kanta Maimuna tayi, cike da sanyin jiki ta miƙe ta fice kamar yanda Mamy ta bata umarnin tafiya, sai dai sosai taji tausayin Mamy ganin yanda fuskarta ya kasa ɓoye damuwar dake zuciyarta, amma babu yanda ta iya.
Da fitar ta, Mamy ɗaukar waya tayi ta kira wo Ummu ta sanar mata da komi
Amma sai Ummu ta hau masifa a kan, "ABUL KHAIRI be isa ya hana su ƙulla zumuncin da suka daɗe suna buri ba".
Sai da Mamy tayi ta ba ta baki kafin ta haƙura, Mamy tace, "Ni Ina ga, ba sai lallai sai da Baba na zamu iya haɗa zumunci ba, Allah ya sani na so mu ga wannan al'amarin ya ƙullu, sai dai tunda ya ƙi haka zamu bar sa kamar yanda yake so, ina ga idan Sulaiman da Batool za su iya amince wa sai mu mayar da akalan zumuntan namu ta nan, amma ba ina nufin su ma a matsa musu bane, mu bi abun a sannu mu sanar musu, idan sun amince shikenan sai ayi".
Sosai Ummu tayi farin ciki da maganar, ta ce, "shikenan Adda Allah ya tabbatar mana da alkhairi, insha Allahu duk yanda mu ka yi da Sulaiman ɗin zaki ji".
Daga nan sallama suka yi, ko wannen su ya ji sanyi a ransa, tunda sam sun manta da ko ba da ABUL KHAIRI ba za su iya yin haɗin zumuncin su, tunda ba shi ne kaɗai namiji ba.
Yaran Ummu su Takwas ne, amma biyu sun rasu. Aunty Naana _(Nana Aminatu)_ ita ce ta farko, sai Aunty Rufaida, ita ce sa'ar ABUL KHAIRI, kuma duk sun yi aure ko wacce da yaranta, sannan sai Sulaiman shi ne ɗa na uku wajen Ummu, shekara biyu da rabi ABUL ya ba shi, sannan sai twins da tayi Hassana da Hussaini, sai da suka girma kafin suka rasu gaba ɗayan su, daga su ne tayi Aliyu sannan ita Maimuna, sai kuma autan su Yunusa takwaran ABUL KHAIRI, amma su suna kiran sa da Shureim.
▪️▪️▪️
Koda Abba ya dawo haka Mamy ta zayyane masa abinda ke faruwa, sosai ran Abba ya ɓaci har yake mamakin har yaushe ABUL KHAIRI ya kai da za su yi mishi magana a kan abu, amma ya ce ba ya so bazai bi umarnin su ba?
Yanda Abba ya ɗau zafi, sai Mamy ta koma rarrashin sa, duk da be kai ta jin zafin abun ba a ranta, sai dai kasancewar ta me haƙuri da danne abu a rai shiyasa bata fito da ɓacin ranta a fili ba
Sai da taga ya sauko sosai sannan tayi masa maganar haɗin da suke so su yi na Sulaiman da Batool. Yayi na'am da maganar sai dai sun ajiye maganar ba yanzu za su sake tayar da maganar ba, za'a bari bayan sun gama school ɗin su, tunda shi dama Sulaiman yanzu yana N.Y.C.E ne, in yaso idan ya amince shima sai a turo sa nan ɗin, ya nemi soyayyar Batool ɗin ba tare da su sun faɗa mata za su haɗa su ba, da haka suka bar maganar.
Amma da dare sai da Abba yayi ma ABUL KHAIRI zaga-zaga, sannan ya ce, "ya ba shi dama ya kawo zaɓin nashi, maganar kuma Maimuna an soke".
Farin cikin da ABUL ya shiga har ya kasa ɓoyuwa, domin be damu da faɗan Abban ba, duk da kuwa ya ga rashin jin daɗin iyayen nashi ƙarara a fuskar su, amma be damu ba, sai ya faɗa musu yanda Daddyn Ziyada ya ce mishi a kan "bazai aurar da ita yanzu ba, sai nan da shekara biyu masu zuwa".
Abba cike da ɓacin rai ya ce, "to Ni kuma ban yarda ba, na baka nan da watanni uku ka kawo min matar da zaka aura, idan ba haka ba wlh tallahi sai ka auri Maimuna, kaji na rantse maka".
Sosai ABUL KHAIRI ya sake shiga damuwa da jin abinda Abba ya faɗa ɗin, ba shi kaɗai ba har ta Maimuna da har taji sanyi a ranta, sai ga shi magana ta sake dawowa sabuwa
Mamy ta ce, "Abban su da ka bar zancen ma, tunda ya.."
Katse ta Abba yayi yace, "dole ne ya bi abunda na ce masa, na gama magana". Ya miƙe ya bar wajen
Itama Mamy tashi tayi tabi bayan sa. Koda ta shiga ɗakin a bakin gado ta same shi har ya janyo computer ya fara latsa wa, zama tayi gefen sa tana cewa, "Abban su Ni a gani na da an bar maganar tunda ba ya so, don Allah kar ka ɗau zafi a kan maganar tunda mun rigada mun ajiye ta gefe".
Ɗago kai yayi yana kallon ta, ya san halin ta akwai sanyin hali, haƙurin matar shi yayi yawa duk da sosai yake hango damuwa a fuskar ta. Ɗan numfashi ya sauke kafin ya riƙo hannayen ta ya ce, "kar ki damu matata abar alfahari na! nima ba wai na zafafa maganar bane, ki ƙyale ni Ni dashi ne".
Zata sake magana ya katse ta da faɗin, "Please Dear ya wuce ba na son damuwar ki kinji?"
Gyaɗa masa kai tayi tana sauke ajiyan zuciya
Shi kuma yaci gaba da aikin sa yana sauya maganar da zancen bikin Uncle Abbas da ya rage kwanaki.
Nan kuwa ta saki jikin ta suna ta zanta wa.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISA ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
🇵 𝐄𝐑𝐅𝐄𝐂𝐓 🇼 𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 🇦 𝐒𝐒𝐎𝐂𝐈𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍🌞
( 𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔻𝔼ℝ𝕊💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
𝗣.𝗪.𝗔✍️
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝙽𝚊 𝚜𝚊𝚍𝚊𝚞𝚔𝚊𝚛 𝚐𝚊 𝙼𝚊𝚑𝚊𝚒𝚏𝚒𝚢𝚊 𝚝𝚊 𝙰𝚋𝚊𝚛 𝙰𝚕𝚏𝚊𝚑𝚛𝚒 𝚗𝚊, 𝚞𝚠𝚊𝚝𝚊 𝚖𝚊𝚐𝚊𝚗𝚒𝚗 𝚔𝚞𝚔𝚊 𝚗𝚊, 𝙸 𝚕𝚘𝚟𝚎 𝚢𝚘𝚞 𝚜𝚘 𝚖𝚞𝚌𝚑 𝙼𝚘𝚖𝚖𝚊 ❤️
*________________________________*
*PAGE 13 & 14*
*________* Tun daga ranan kuma, sai ABUL KHAIRI ya ta da wa Ziyada ɓalli a kan maganar auren su, sai ya zauna ya haɗa mata ƙarya da gaskiya don ta ɗauki maganar da muhimmanci, a kan, "Iyayen sa za su yi masa aure da ƴar uwan sa, kuma sun ce dole sai ya aure ta idan be kawo wacce yake so ba." har da ƙarin gishiri da maggi
Ai hankalin Ziyada yayi matuƙar tashi fiye da zaton ABUL KHAIRI, nan kuwa ta je ta samu Daddyn ta da zancen
Shi kuma yace, "be yarda ba, ba yanzu zai mata aure ba".
Haka Ziyada ta tada rikici, dole ba don ya so ba ya amince, sai dai ya ce, "ba yanzu za'a yi auren ba, za'a saka ranan auren ne nan da shekara biyu masu zuwa". Time ɗin ta gama school
Haka Ziyada ta sanar wa ABUL KHAIRI, shi kuma ya zo ya sanar wa Abba, amma Abba ko bi ta kansa be yi ba, daga ƙarshe ma be sake tayar da maganar ba
Shi kuma dama Daddyn Ziyada be wani ɗauki maganar shima da muhimmanci ba, ya amince mata ne kawai don ta kwantar da hankalin ta, dama tafiya zai yi, haka ya tsallake maganar ya bar garin ba tare da ya ce ABUL KHAIRI ya turo magabatan sa ba.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Su Mamy suna ta shirye-shiryen bikin Uncle Abbas tunda har ya matso, tun ana kwana huɗu Ummu ta taho tare da Shuriem da Aliyu da ya biyo ta, sai Aunty Rufaida itama tare suka taho da yaran ta duk ta kwaso. Aunty Naana sai ana gobe bikin zata zo, dama shi Sulaiman yana kudu yin service, ba ma zai halarta bikin ba.
Gidan Mamy suka sauka gaba ɗayan su, ai a ranan su Batool tamkar baki zai tsage sabida murna, musamman ma Maimuna da tayi missing ɗin su ainun, nan taje ta ɗare jikin Ummu tana murna har da ƙwallar ta
Aliyu yana tsokanar ta da faɗin, "ke dai an yi sokuwa wlh, meye kuma na kuka? Wlh da ke Auta ce an bani da sangarta".
Turo baki tayi gaba tana share hawayen fuskar ta
Dariya gaba ɗaya suke mata
Ita kuwa sai kwaɓe fuska take yi tana ƙara shige wa jikin Ummu
Ummu tace, "to Ni sake Ni da Allah ban son sakarci".
Ɗaga ta tayi tana komawa kusa da Aunty Rufaida, Nan itama ta maƙure mata tana zuba mata surutu
Batool ta matso kusa da ita a hankali tace, "ashe haka kike kina surutu? Tunda mu kin mayar damu dodannin ki ai ba kya mana".
Hararan ta Maimuna tayi tana kau da fuska
"Uhmmm yi da kyau yanzu zan je in sanar da Yaya ABUL in ce kin murguɗa mishi baki". Batool ta sake faɗa a hankali
Juyowa wajen ta tayi ta saka hannu ta ranƙwashe ta, sai kuma ta kalli Mamy da suke hira da Ummu tace, "Mamy kin ganta ko?"
"Ah ah lafiyan ki ƙalau kuwa Batool? Me kike mata?" Cewar Mamy dake kallon su
Ita dai dariya Batool take yi
yayinda Maimuna take kumbura fuska tana faɗin, "tono na take yi Mamy".
"To ki mayar da hankali kinji?". Mamy ta sake faɗar hakan tana mayar da hankalin ta kan Ummu dake magana.
A haka ranan suka wuni suna hira, daga ƙarshe ma barin gidan suka yi su Maimuna, suka bi Aliyu da ya fita a motar gidan yawon ganin gari, duk suka bi shi har yaran Aunty Rufaida su uku maza da ta taho da su.
Sanda ABUL KHAIRI ya dawo gidan, ai kuwa ya ga faɗa wajen Ummu, sai da ta zauna ta sille sa da bala'i ta inda take shiga ba tanan take fita ba, wai a cewar ta, "har su za su zaɓa mishi abinda suke ganin ya dace da shi, amma ya shafe wa idanuwan sa toka ya ƙi bin umarnin su".
Shi dai be ce komi ba sai haƙuri da yayi ta ba ta, tunda dama ya san halin ta da shegen faɗa, bata da haƙuri ko kaɗan. Daga ƙarshe barin mata gidan yayi ya fito haraban waje ya zauna, tunda ta ƙi dena wa domin ta shaƙa ba kaɗan ba. Mamy da Aunty Rufaida suna ba ta haƙuri amma ina, sai da tayi ta gaji don kanta kafin a koma hira kuma ita da Mamy, ita kuma Aunty Rufaida ta wuce kichen yin musu girki.
▪️▪️▪️
ABUL KHAIRI na zaune a farar kujeran da ya turke ta a farandan gidan, ya hangi motar da Aliyu ya fita da ita ta shigo, dayake jip ce motan; su wajen rai Tara a cikin ta. yana kallon su duk suka fito a cikin motan suna ta hayaniya. Sai da suka taho ne ma suka lura da shi, ai gaba ɗayan su suka nufe sa ban da Batool da Maimuna da suka yi cikin gida
Haka yaran sukai ta gaishe shi, yana amsa musu yana musu wasa tare da tambayar su school da mutanen gida. Aliyu shima gaishe sa yayi kafin ya aiki Amir ya ɗauko masa kujeran shima, yana kawo masa ya turke ta kusa da na ABUL ya zauna, sannan yaran kuma duk suka yi cikin gidan suka bar su nan suna hira.
Sai dare duk suka tarkata suka tafi gidan Hajiya Mama, ban da Ummu da ba yau zata je ba, sai jibi za su wuce da su Mamy
Batool dai ta bi su, amma ita Maimuna taƙi bin su, kasancewar ta me ƙulafucin uwa, don ta ga Ummu ne ta ƙi tafiya, ita kaɗai ce a yaran aka bari.
A gidan su Mamy suke ta shirye-shiryen bikin, duk sun yi toye-toyen su a nan ne, itama Zee nan ta taho aka yi aikin da ita, har Aunty Rufaida da ta tafi can sai da ta dawo aka yi da ita, tunda can gidan Hajiya Mama babu wani aiki. A ranan itama Aunty Fatima ta zo, da yaran ta ƙannin Humaira. a daren suka tarkata suka koma can suka ci gaba da hidiman bikin, sai aka bar ABUL KHAIRI da Abba kaɗai.
Washe gari Aunty Naana ta taho da nata iyalan, gida dai ya cika Masha Allah sai zuwa ake yi, har su Inna Aliya da su Inna Maria duk a ranan suka zo bikin, Inna Halisa ce kaɗai bata zo ba, itama ta bar wa gobe ne tunda yanzu duk ana mutunci da ita, duniya ta koya mata darasi.
Washe gari aka ɗaura auren Abbas Yunusa Ubale, tare da Amaryan sa Safiyya Usman, da yake itama ƴar cikin garin ne. Gaskiya an samu mutane ba kaɗan ba a bikin nan, Allah yayi ruwan mutane, ta inda ba ka zato mutane sun taho, gidan Hajiya Mama ya cika maƙil duk girman sa, ta ko wani ɓangare su Mamy, Ummu, Aunty Fatima da suka yi gayya duk an zo musu. An sha biki an ragargaje, dayake su ba su yi wani Event na bidi'a ba, gaba ɗaya har aka gama taron babu wani bidi'a a ciki, sai Walima da suka yi da yamma, zuwa dare kuma aka kawo mishi matar sa tunda a gidan Part ɗin ta yake.
Tun a ranan mutane suka soma watse wa, washe gari da yamma su ma su Maimuna suka wuto gida suka bar Mamy a can, itama Aunty Fatima a ranan ta wuce Zaria, haka ma yaran Ummu su Aunty Naana da Aunty Rufaida duk a ranan suka nufi Kaduna garin gwamna kasancewar duk a can suke aure, Ummu ce dai sai washe garin ranan Litinin suka wuce da yamma, itama Mamy da dare ABUL KHAIRI ya zo ya mayar da ita gida
Aka bar Uncle Abbas da matar sa Safiyya ana cin amarci, sai mu ce Allah ya sanya alkhairi ya ba da zaman lafiya.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 15 & 16*
*________* *TWO WEEKS AGO*
Zaune yake a cikin Office ɗin sa, ya tasa takardu sai faman rubutu yake yi, gaba ɗaya yau ba shi da lokacin kansa, duba da yanda aiki suka yi masa yawa birjik, kuma be samu ya zo ba sai yanzu ɗin, sabida kiran gaggawa da Uncle Abbas yayi masa, kuma yana son ya tashi a kan lokaci saboda yaje gidan gonan sa su haɗu da Ziyada su huta, shiyasa komi nasa cikin sauri yake yi
Wayan sa da tayi ƙaran shigowar saƙo, shi ne yasa ya ɗago kai yana kallon wayan, a tunanin sa ko Ziyada ce, saɓanin haka private number ya gani aka turo masa text, ɗaukan wayan yayi ya buɗe ya soma karanta wa:
_"Yunusa Hayat Sunusi, Na san zaka yi mamakin ko waye yake bibiyan rayuwan masoyiyar ka, amma ba abun mamaki bane, domin Ni ɗin me ƙaunar kace, saboda ina son kasan wani sirri a tare da ita, idan har kana son sanin wace ce Ziyada, to ka shiga WhatsApp yanzu na tura maka saƙo ka duba.."_
Abin da aka tura masa kenan, ya karanta har sau biyu ba tare da ya ajiye wayan ba, tsayawa kawai yayi yana son fahimtar inda saƙon ya nufa, sai kuma ya buɗe data ya shiga WhatsApp kamar yanda aka ce masa. Sai da ya bari komi ya gama daidaita na shigowar messages, kafin ya ga ɓoyayyiyar Numban da aka tura masa saƙo, shiga yayi don ganin mene ne. Wani irin zabura yayi tamkar zai yar da wayan, har sai da takusa faɗi yayi saurin taro wa, jikin sa na rawa yaci gaba da kallon hotunan da aka tura masa
Hotunan Ziyada ce ita da Saleem, wasu hotunan suna tsaye a tare suna magana, wasu kuma suna riƙe da hannun juna a wajen shaƙatawa, babu abinda yafi ɗaga masa hankali sama da hoton da yaga an ɗauke su suna shirin shiga hotel, har wanda suka kai bakin ƙofan ɗakin da za su shiga an ɗauke su suna dariya, tamkar dai masoya idan an gan su
Sosai a lokacin jikin ABUL KHAIRI yake rawa, nan da nan zufa ya soma keto masa, zuciyar sa na wani irin bugawar tashin hankali, a lokaci ɗaya jijiyoyin kansa dana wuyan sa suka fito raɗo-raɗo, motsin kirki ya kasa yi illa hango Ziyadan da yake yi tare da Saleem ɗin a kan gado ɗaya suna... Wani irin kishi ne ya rufe sa, take ya jefar da wayan, ya buga saman table ɗin sa da ƙarfi yana me faɗin, "no impossible! Ziya..." Sai kuma ya kasa ƙarisawa saboda rawan da bakin sa yake yi. zube wa yayi saman kujeran sa yana huci tamkar zaki, gaba ɗaya zuciyar sa zugi take masa kamar zata fito
Ƙaran wayan sa, yasa ya ɗago jajayen idanun sa ya zuba a kan wayan dake yashe a ƙasa, kallon ta kawai yake yi ba ya motsi, tamkar dai yana son a tabbatar masa da cewa ƙarya ce abun da ya gani, sai kuma ya saka hannu a hankali ya ɗauko wayan hannun sa na rawa kamar an jona sa a shock. Text ɗin dai Numban ne da aka turo masa saƙo, buɗe wa yayi ya soma karanta wa:
_"hhhh abun mamaki ko? Na san dama zaka ruɗe duba da yanda kake matuƙar son masoyiyar ka, but taci amanar ka, wannan ma kaɗan ne daga abubuwan da take aikata wa, amma da sannu zan ci gaba da bayyana maka wace ce ita, zaka san cewa kana tare ne da baƙar macijiya.. hhhhh amma fa ina ga laifin ka ne, tunda ka kasa yin mata abinda take so.. HHH don ta nema a wani waje ba laifi bane.."_
Lumshe ido ABUL yayi, sai ga hawaye sharrr sun soma zubo masa, kifa kansa yayi a saman table ɗin ya hau zirarar da hawaye tamkar mace, sosai zuciyar sa take suya kamar ya ciro ta ya jefar, gaba ɗaya fuskar sa tayi jawur sai haɗiyar zuciya yake yi. Ya jima a haka a wani mawuyacin hali kafin ya ɗago kansa da yayi sharkaf da zufa, fuskar sa kuma ta jiƙe da hawaye, numfashi kawai yake sauke wa tamkar ransa zai fita tsaban kishi, ji yake yi kamar ya kashe kansa saboda baƙin ciki, macen da yafi ƙauna a duniya ita ce take tare da wani, har ta iya ba shi kanta. kama kansa kawai yayi yana jin hajijiya na son kada shi daga zaunen, da sauri ya miƙe yana ɗaukar keey ɗin motan sa ya fita da mugun sauri, Allah ne kaɗai ya kai sa wajen motan sa, don be san ma inda yake jefa ƙafafuwan sa ba, motan ya shiga yaja ya figa ya bar Companin da mugun gudu kamar zai tashi sama.
Kai tsaye gidan gonan sa ya wuce, wani irin mugun horn yake saki har sai da Gate man ya buɗe masa Gate ɗin, figan motan yayi ya shige a tsiyace, ilai kuwa abinda yake zato ne, ya hangi motan Ziyada a ciki. Be yi ƙwaƙƙwaran parking ba ya fito ya nufi cikin gidan da mugun sauri ransa a matuƙar ɓace.
**** ***** ******* *********
Lokacin da ABUL ya shige da motan sa ciki, a lokacin ne Azeeza ta sauka daga keke napep, tana hangen sanda ABUL ɗin ya shiga gidan, hakan yasa tayi saurin biyan me napep ɗin kuɗin sa ta ƙarisa ciki, me gadi na shirin rufe ƙofa ta taho tana gaishe sa
Nan da nan ya washe baki yana amsa wa, tare da tambayan ta kwana biyu wai, "bata zo ba?"
Murmushi tayi tace, "Baba kenan, ai yanzun ma saƙo nazo amsa wajen Yaya ABUL, kuma naga kamar yanzu ya dawo ko?"
"Eh eh yanzun nan ya dawo, amma fa ina ga ba lafiya ba! sabida yanda na gansa kamar hankalin sa a tashe ne".
"Eyya! To bari in shiga wajen sa, ga wannan babu yawa". Ta miƙa masa 3k
Amsa yayi yana ta zuba mata godiya kamar ta ba shi garin
Ita kuwa bata bi ta kansa ba ta shige abun ta, dama tana son ne su haɗu sabida maganar da ta zo mishi dashi, ita a ganin ta idan har zai so ta, to ta amince zata ba shi jikin ta kamar yanda Ziyada take yi, tunda ai bata fi ta da komi ba a jiki ba, don haka itama a shirye take ta ba shi jikin ta in dai zai so ta, shiyasa ta biyo shi nan don su yi magana
Amma kuma tana shiga taga motan Ziyada, ta rigada ta shaida motan nata ne tunda ta ganta wancan zuwan, tunda motan guda biyu ne, daga na ABUL sai nata. tsaki taja tana nufan bayan windown kamar yanda tayi wancan karon, so take yi ta tabbatar da me suke yi kafin ta burma ciki, don ya san cewa ta san me yake yi, inyaso ma ta ɗauke su hoto ta tona masa asiri wajen iyayen sa idan har be yarda da abinda tazo mishi dashi ba, tayi alƙwarin duk hanyar da zata bi sai tabi don ta mallake sa, shiyasa ta saki wani miskilin murmushi taƙarisa windown da sauri tana saka hannu ta buɗe a hankali, babu Lock hakan sai yayi mata daɗi, ta saka hannu ta ɗage labulen da ya kare mata ciki.
A lokacin ne ABUL KHAIRI ya saka hannu ya kwashe Ziyada da mari, tsaban gigita sai da tayi ƙasa daɓas tayi zaman ƴan bori tana kwatsa ihu
Jiki na rawa Azeeza ta ciro wayan ta ta hau yin musu Video, zuciyar ta fari ƙal tsaban farin cikin abun da ta gani yana shirin faruwa
Yana huci ya matso kusa da ita ya saka hannu ya shaƙo mata wuya
Yanda Ziyada taga idanun sa sun juye sun zama jazur tamkar tattasai, har wani ƙyalli suke yi wanda ke nuni da hawaye ne a ciki, sosai ta firgita da yanayin sa, ga shi ya shaƙe mata wuya ba damar tayi magana illa ƙaƙari da ta hau yi kamar zata mutu
Tsaban fushi ma ya kasa yin magana, daƙyar ya iya tattaro numfashin sa dake ƙoƙarin ɗauke wa daga gangan jikin sa, tare da tattaro miyau ɗin bakin sa da ya kafe ya ce da ita, "Ni ABUL KHAIRI zaki ci amana? Ni?.. abun da na hana ki aikata wa shi kike aikata wa a bayan idanu na ko? Wlh Ziyada ban taɓa jin cewa son da kike min ƙarya bane da har zaki iya bayar da kanki ga wani bayan Ni, yanzu asirin ki ya tonu, I hate you ZIYADA! I hate you so much, i will never be able to marry you tunda har kika haɗa Ni da wani, a kan kishin ki zan iya kashe ki Wlh". Sai ya saki wuyan nata yana miƙe wa daga durƙushen da yayi a gaban ta, cikin hawaye yace, "fitan min a gida yanzun nan ko in kashe ki, na tsane ki! Kar ki sake zuwar min gida, ba na son sake ganin fuskar ki ZIYADA, I hate you..!" abun da yake ta maimaita wa kenan cikin raunin murya yana kuka kamar mace
Sosai idan ka kalli Ziyada zaka ga ta fita hayyacin ta lokaci ɗaya, domin tunda ta gane inda ya dosa ta tabbatar da asirin ta ne ya tonu a wajen sa, sai tayi suman wucin gadi, sai dai hawaye dake zubar mata kamar famfo ta kafe sa da manyan idanun ta da suka sauya kala lokaci ɗaya tsaban tashin hankali...
Sai da ya daka mata tsawa yana bata umarnin, "ta fice masa a gida." kafin nan ta dawo hankalin ta
Cikin kukan da kamar ana yankan naman jikin ta tsaban ruɗe wa ta hau ba shi haƙuri, tana faɗin, "ya tsaya yaji, ita baza ta taɓa cin amanar sa ba."
Wani irin haushi maganar nata ya ba shi, nan da nan ya saka hannu ya fincike ta yayi waje da ita, ya jefar da ita a bakin ƙofan yana me garƙame ƙofan sa, a nan bakin ƙofan ya zube yaci gaba da tsiyayar da hawayen sa, zuciyar sa na ƙuna tamkar zata fito
Itama tasowa tayi da rarrafe ta jingina da ƙofan tana kuka tana mishi magiyan, "ya buɗe kar ya rabu da ita, baza ta iya rayuwa babu shi ba, sharri ake mata ƙarya ne, bata karya masa alƙawari ba, dashi kaɗai zata iya rayuwan jin daɗi."
Lumshe ido yayi, wasu zafafan hawaye suna sake sulmiyo masa, sosai ransa ke raɗaɗi sabida babu abinda yake hango wa sai Ziyadan sa tare da Saleem a kan gado ɗaya suna cin amanar sa, "yanzu duk ƙaunar da ya gwada mata ashe zata iya ba da kanta ga wani bayan shi? Mene ne ya rage da ba ya mata? Komi yana mata na jin dadi da zai iya mantar da ita ko wani ɗa namiji, amma ko kaɗan bata ga haka ba, sai da tabi hanyar da zata bi ta bayar da kanta ga wani, wanda hakan shi ne babban kuskuren ta, bazai taɓa iya auren ta ba idan har wani namijin ya kusance ta, yana da matuƙar kishi, duk son da yake mata zai iya rabuwa da ita in dai a kan haka ne."
Jin ta dame shi da kuka sai ya tashi ya shige bedroom Yana sake rufo ƙofan.
◾▫️◾▫️◾
Komi da ya faru sai da Azeeza ta naɗa, wani irin farin ciki ne ya mamaye ta tamkar ta zuba ruwa a ƙasa tasha, ganin yanda komi ya wakana a wajen su, tabbas tana jin cewa aikin ta ya zo da sauƙi, domin tasan cewa tunda ABUL KHAIRI ya furta ya rabu da ita, to tabbas ba ta tunanin zai koma mata, tasan yanzu aikin ta zai soma
Da sauri ta janyo wayan ta waje tayi serving ɗin videon, ta juya tayi bakin Gate zuciyar ta fari ƙal.
◾▫️◾▫️◾
Ziyada ta ƙi tashi a wajen sai kuka take yi tana buga masa ƙofa tamkar zata karya, sosai ta fita hayyacin ta, sai kiran sunan sa take yi tana ba sa haƙuri.
ABUL KHAIRI dake kwance a kan gado ya danne kan sa da pilow, amma duk da haka yana jiyo bugun ƙofan da take yi. Miƙe wa yayi ya fice a matuƙar fushi, yana zuwa ya buɗe ƙofan, sai ta biyo ƙofan ta faɗo kan ƙafafun sa, janye ƙafafuwan sa yayi ya fito ya soma rufe ƙofan
Da sauri ta tashi ta rungume sa tana me sake fashe wa da wani irin kuka me ban tausayi, sosai take kuka wanda ya hana ta yin magana illa faɗin, "sorry! Sorry." kaɗai da take yi
Ɓanɓare ta yayi a jikin sa ya ture ta yana kallon ta da jajayen idanuwan sa, abun takaicin ma duk baƙin cikin da yake ji da abinda tayi masa, sake jin ƙaunar ta yake yi na shigan sa, tabbas idan ya tsaya a wajen ta komi zai iya faruwa
Janye idanun sa yayi daga kallon ta ya juya da sassarfa ya nufi motan sa
Biyo sa tayi tana kuka tana roƙon sa, har da sake shige wa jikin sa tayi
Amma ina tuni ya ɓanɓare ta yayi wurgi da ita yana kallon ta yace, "Wlh if you touch my body again I will surprise you ZIYADA". Motan sa ya shige ya ja ya nufi bakin Gate Yana buga uban horn
Da sauri me gadi ya buɗe masa jikin sa na rawa, shi kuma ya fice.
Ziyada zube wa tayi a nan ƙasa tahau birgima kamar wacce ta hau iska, kuka sosai take yi tana faɗin maganganun da ba'a jin ta
Da sauri me gadi ya ƙariso wajen ta yana faman bata haƙuri
Amma ko kulasa bata yi ba
Dole ya tashi ya koma bakin aikin sa ya zauna yana faman kallon ta, a ran sa yana mamakin abinda ya haɗa su yau suka yi baram-baram na tsiya, domin tunda yake be taɓa ganin sun yi faɗa makamanciyar wannan ba, duk da sau tari yana jin hayaniyan su wani lokacin. Jinjina kai yayi a ransa yana cewa, "cabb! yau waɗannan masoyan ko me ya haɗa su?".
Ziyada kuwa sai da ta gaji don kanta kafin ta miƙe ta faɗa motan ta ta figa tabar gidan tamkar mahaukaciya.
◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️
Kai tsaye ABUL KHAIRI gida ya wuce, yanda yake buga shegen horn sai da ya tsorata me gadi, da gudu ya buɗe masa ya shigar da motan a tsiyace, wani wawan birki yaja ya fito ya nufin cikin gidan.
Maimuna na zaune a Parlour ita da Sa'ima, (ƴar wajen Umma Salamatu, ƙanwar Abba ce, Sa'ima ita ce ɗiya ta biyu a wajen ta, me sunan Batool Fatima ita ce ta farko, amma suna kiran ta da Ummee, tayi aure har da ɗiyar ta ɗaya)
Sa'ima sa'annin su Maimuna ce itama.
Suna cikin hira suna dariya suka ji ya bugo ƙofan ya shigo, da sauri dukan su suka soma gaishe shi
Amma ina be ma san suna yi ba ya nufi ɗakin shi
Yanda suka gan sa sai da duk kan su suka tsorata, sabida yanda fuskar sa babu fara'a sai faman huci yake yi, idanun sa sun yi jazur
"Keee anya Angon naki lafiyan sa ƙalau? Me ke damun sa?" Cewar Sa'ima tana kallon Maimuna
Ita kuma hararan ta tayi tace, "ban son haka fa wlh, ki dena".
Dariya Sa'ima tayi tace, "wlh Maimuna dariya kike bani, gwara ma ki dena haka wlh kun dace, Ni ina miki fatan samun Ya ABUL, sabida ba ƙaramar Sa'a kika yi ba idan kika same sa, ai Ni tunda Batool ta faɗa min abinda ke faruwa nake Allah-Allah na zo inji ƙarisan labarin, wlh har kwana nayi roƙon Allah yasa ku mallaki junan k.."
Duka Maimuna ta kawo mata, dole tayi shiru tana miƙe wa da sauri tana mata dariya, sai ta kuma cewa, "Allah ba batun wasa ba Maimuna, baza ki je ki ji mene ne ya ɓata wa gwarzon naki rai ba?"
Tashi Maimuna tayi tabi ta tana cewa, "wlh Sa'ima sai na fasa miki baki idan na kama ki, kuma da Mamy zan haɗa ki".
Sa'ima tuni ta shige ɗakin su
Maimuna tabi bayan ta itama da gudu
Batool na kwance tana sharan barci, sai ji tayi an faɗo kanta, da sauri ta buɗe jajayen idanun ta ta sauke a kan Sa'ima dake son tsallakawa ta jikin ta ta guje wa Maimuna
Ita kuwa Maimuna tuni ta dakata ma tana cewa, "wlh ki dena ba na so Sa'ima".
Ita kuma sai mata dariya take yi har a lokacin tana jikin Batool bata gama sauka ba
Ɗaga mata duka Batool ɗin tayi tana faɗin, "wannan wani irin wulaƙanci ne ina barci zaki faɗo kaina?"
Riƙe cinyan ta inda ta bige ta tayi tana cewa, "Batool ke muguwa ce wlh, shi ne zaki yi min wannan banzan dukan don na hau jikin ki, wani nauyi ne dani?"
Harara Batool ta balla mata tana cewa, "a'a uwar baki da nauyi ne, kina ji da wannan shegen jikin naki kamar dutse kike ce min baki da nauyi?"
Maimuna kuwa me zata yi in ba dariya ba
Nan dambe ya kaure a tsakanin Batool ɗin da Sa'ima, sai dukan juna suke yi suna cacan baki, ga shi gaba ɗayan su babu me haƙuri cikin su
Maimuna na gefe tana tiƙan dariya, musamman yanda suke tsinan kansu sai abun yake bata dariya.
Dayake sun san babu Mamy a gidan ta tafi gidan su Abba ita da Baby da Amir, daga can zata wuce anguwan su zata duba Uncle Shamsu, an aiko jikin sa ya tashi, sannan daga can sai ta biya ta gidan su
Abba kuma be daɗe da fita a gidan ba ma.
Wani irin hautsine wa cikin Maimuna yayi da ta wulƙa ido ta hangi ABUL KHAIRI tsaye a bakin ƙofa yana riƙe da belt ɗin wandon sa, idanun nan nasa tamkar ma yanzu ne suke ƙara juyewa tsaban jan da suka yi
A dai-dai lokacin ne su ma su Batool suka hange sa, ai tuni sun dakata daga jefawa junan su pilown da suke yi, sun nufi ƙarshen gadon suna ƙanƙame jiki tare da zare idanuwa kamar sun yiwa sarki ƙarya an kama su.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 17 & 18*
*________* Yanda ran ABUL KHAIRI yake a matuƙar ɓace ga shi ya samu inda zai huce, shiyasa ya haɗa su har Maimuna yayi musu mugun duka, ga shi babu damar guduwa, tun suna neman ceto har suka gaji sai kuka da suke yi, babu wanda yafi jibga sai Maimuna, kamar an aiko mishi da jaka haka yake kiman ta, tunda duk yafi jin haushin ta
Maimuna baiwar Allah, abinda bata taɓa ji bane ya faru da ita, duba da yanda take ba me rashin ji ba, shiyasa zai yi wuya ka ga an bige ta ko da a school ne, ita rabon ma da ace an bige ta tun tana ƙarama ƙila, duk saurin hannun Ummun su ba ta dukan ta, shiyasa abun ya zo mata a wani irin baƙon yanayi, nan da nan ta sume sabida tsaban firgita
While ABUL KHAIRI be San ma ta sume ba, jibgan su kawai yake yi, sai da gaba ɗayan su ya farfasa musu jiki, su Batool duk an yi musu haɓo, Maimuna ma ba'a maganar ta
A dai-dai wannan lokacin ne Abba ya dawo gidan, kukan su kawai ya jiyo ya zo yana dukan ƙofan, sabida tuni ABUL ya rufe ƙofan
Sai da yaji muryan Abban su yana kiran sunan sa kafin ya dakata da dukan nasu, ya nufi ƙofa ya buɗe yana kallon Abban
Yayinda Abba tuni ya shigo ciki yana bin su Batool da kallo, cikin tashin hankali ya kai duban sa ga ABUL KHAIRI wanda ke tsaye kamar an shuka sa, cike da ɓacin rai yace, "Me suka yi maka kayi musu wannan dukan? Shin kana cikin hankalin ka kuwa?"
Ihun da Sa'aima ta saki ne yasa Abba ya nufe su da sauri, ganin Maimuna bata numfashi ne yasa ta saki wannan ƙaran
Sosai hankalin Abba ya tashi ganin Maimuna ba ta motsi, ga shi kanta duk ya jiƙe da jini, wanda takamaime ma ba'a san inda taji ciwon ba
A fusace Abba ya ɗago kai zai yiwa ABUL KHAIRI magana, amma sai yaga babu shi, da sauri ya nufi ƙofa ya fita yana me kwaɗa masa kira
ABUL KHAIRI da har ya shige ɗakin sa ya mayar da ƙofa ya rufe, dole ya fito yana amsa kiran Abba jin kamar zai tsaga gidan
Yana fitowa suka ci karo ya wanka masa mari a fuska, cikin fusata yace, "haukan naka ya kai har ka kashe musu ɗiya ko? To wlh muddin wani abu ya same ta sai na kai ƙaran ka wajen hukuma, shashasha mara tunani, wuce muje ka ɗauke ta mu tafi asibiti".
Da sauri ABUL KHAIRI yayi gaba dafe da kuncin sa, sosai ya tsorata da yanayin da mahaifin sa ya nuna masa, shi kansa be san abinda ya aikata ya kai haka ba saboda hankalin sa ba ya jikin sa, zugin abinda Ziyada tayi masa ne sai ya fanshe a kansu. Sosai ya sake tsorata ganin yanda Maimuna ko numfashi ba ta yi duk jikin ta jini, ga su Batool sun tasa ta gaba suna ta kuka kamar ransu zai fita, su ma duk ciwuka jikin su
Sai da Abba ya daka masa tsawa sabida tuni ya fita tunanin sa, sannan ne ya ɗauke ta suka yo waje gaba ɗaya har su Batool, don su ma dole su ga likita da wannan raunin da suka ji.
Sai da suka isa can da kamar mintuna goma, sannan Mamy ta kira wayan Abban su tana tambayan sa, "bata ga su Batool ba, sannan ta ga ɗakin su a birkice duk jini bata san me ke faruwa ba?"
A nan Abba yake sanar mata da komi, don dama ya ƙi kiran ta ne kar hankalin ta ya tashi
Sosai kuwa hankalin nata ya tashi, nan da nan ta juya kan mota ta nufo asibitin bayan ta sauke su Amir, tana zuwa ta hange su a reception, daga Abba sai su Sa'ima da aka gama musu dressing inda suka ji ciwon, hannayen su ne kawai ya farfashe, sai haɓon da suka yi a hanci duk kan su
Babu ABUL KHAIRI a wajen, don tuni Abba yayi masa koran kare
Mamy duk ta rikice ganin yanda ta gansu, cikin hawaye tace, "yanzu Abban su me suka yi da Baba na zai yi musu wannan hukuncin?"
Cikin kuka Batool tace, "babu abinda muka yi masa wlh, kawai ya shigo ɗakin mu ne ya ga muna sa'insa da Sa'ima a kan tashi na da tayi daga barci, shi ne ya hau jibgan mu har Maimuna da bata yi masa komi ba".
Itama Sa'ima na kukan ta amshe zancen da faɗin, "wlh Mamy ba muyi masa komi ba, da fushi ya dawo gidan shi ne ya ƙare a kan mu".
Sosai ran Abba ya sake ɓaci, yace, "wlh muddin wani abu ya sami Maimuna sai na ba shi mamaki, domin Nasan da gayya yayi mata wannan dukan, yau sai nayi mummunan ɓata masa rai wlh, bari mu koma gida". Yana gama faɗar maganan yayi waje don duba ABUL KHAIRIN idan be tafi ba, tun yanzu yaci mutuncin sa, sai dai ina tuni babu shi a haraban asibitin, har motan nasa ma.
Lokacin da Doctorn dake duba Maimuna ya fito, nan suka je gaba ɗaya suka same sa, yace, "su biyo sa office". Suna zuwa ya sanar musu da abinda ke faruwa
Ba wani abu bane illa mugun dukan da aka yi mata ya haddasa mata firgita, hakan yasa ta sume, sannan sai raunuka da taji a kanta da jikin ta da ya farfashe, an samu yanzu ta farfaɗo, sai dai sun yi mata alluran barci sun saka mata ruwa, sannan kuma baza a sallame ta ba sai zuwa gobe ko jibi saboda yanayin jikin nata akwai zazzaɓi me zafi da ya kama ta.
Duk da haka dai sun ɗan ji sanyi a ransu tunda lafiyan ta lau, tare suka je gaba ɗaya suka duba ta, inda Abba ya wuce da Sa'ima har gida ya kaita, ya sanar wa Umma Salamatu da komi (Ƙanwar sa ce idan baku manta ba)
Duk da hankalin ta ya tashi, amma bata wani damu da dukan su Sa'iman ba, a ganin ta su ne ba sa ji, sabida son da take yiwa ABUL KHAIRI shiyasa ko kaɗan bata ga laifin sa ba, illa tausayin Maimuna kawai da taji
Tare suka dawo da Abban asibiti ta duba ta, a lokacin ma har ta farka, sai dai gaba ɗaya jikin ta ciwo yake mata, duk yayi tsami, ga zazzaɓin da ya ƙi sauka.
Mamy bata sanar wa kowa ba, har Ummu duk ta ƙi faɗa musu, ko su Hajiya Mama bata sanar musu ba, ta bar abun daga su sai su, tunda an ce zazzaɓin na sauka za'a sallame su, kuma komi ya zo da sauƙi alhamadulillah. Tayi kiran wayan ABUL KHAIRI amma duk ya ƙi ɗauka
Yana can ya bar ta a ɗaki, shi kuma ya ƙi komawa gidan, gaba ɗaya ya rasa inda zai saka kansa, ko kaɗan bazai so ya koma gida a wannan halin ba, domin yasan muddin ya koma sai ya haɗu da fushin Mahaifin sa, ga Sagir ba ya nan bare ya ba shi shawara, ga baƙin cikin abinda Ziyada tayi masa yau, ya rasa inda zai saka kansa, duk damuwa tayi masa yawa, har kansa ya soma masa ciwo tuni, dole ya nufi gidan gonan sa, don yana jin a nan zai kwana ƙila, ko kuma zuwa dare ya koma gida, amma ya san zai sha faɗa, shiyasa ma ya yanke shawara be koma ba, a can ya kwana.
Zuwa dare zazzaɓin ya ɗan sauka kaɗan, Mamy ta kwana da ita dole. Washe gari kuma Batool ta kawo musu Breakfast, ita da Abba suka zo, bata jima ba ta koma tunda an bar su Amir.
◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️
Da safen ABUL KHAIRI ya shirya ya wuce Office daga can, tunda yana da komi nasa a gidan babu abinda zai buƙata sai wayan sa da jakan sa, amma kuma ya ƙi zuwa gida ne don gudun haɗuwan su da Abba da Mamy, don be san me zai ce musu ba
Yana zuwa Office ɗin sa kuwa, aka sanar masa, "Abba ya zo neman sa yanzu," yana jin haka ya fito ya bar Companin, gida ya wuce kai tsaye, ya ci Sa'a babu Mamy tana asibiti, sai yaran. wayan sa ya ɗauka ya bar gidan, ya gummaci ya tafi wani wajen har sai sun huce kafin ya dawo, don shi ya tsorata sosai.
Kai tsaye gidan Umma Hussaina ya wuce (itama ƙanwar Abba ce) amma gidan ta da nisa sosai, ya san ba lallai taji labari ba, shiyasa ma ya wuce can.
◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️
Yau ma Azeeza shirya wa tayi ta fito ta nufi gidan ABUL KHAIRI, don tasan a can zata gansa, tunda kullum sai ya zo idan ya tashi aiki, kuma tasan yanzu haka lokacin zuwan sa ne
Jiya da farin ciki ta kwana, Allah-Allah take yi dama yau tayi ta sake koma wa, don yau tayi ninyan nuna masa videon da tayi musu, zata ce masa, "idan har be aure ta ba, to, zata je ta nuna wa Iyayen sa komi, sannan ta faɗa musu duk yanda suke rayuwar soyayyar su". Ta san dole zai amince, dole ne zata ci galaba a kan sa.
Me nepep na sauke ta ta fito ta biya sa kuɗin sa, sai ta nufi bakin Gate ɗin, buga ƙofan tayi. Sai dai shiru babu me Gadin kusa, sai ta tura ƙaramin ƙofan ta ga ya buɗe, tayi shigewar ta
Abun baƙin cikin tana shiga ta hangi motan Ziyada, "kenan dai har yanzu baza ta rabu da shi ba? To tabbas yau zan yi mata iyaka dashi na har abada". A zuciye ta nufi cikin gidan zuciyar ta na tafarfasa.
◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️◾▫️
A dai-dai wannan lokacin ne ABUL KHAIRI ya nufo gida, ya san cewa dole yanzu zuciyoyin iyayen sa sun sauka, duk da ya ga basu kira sa ba, amma dai gwara yau yaje ya ba su haƙuri zai fi
Yana cikin tuƙin ne aka kira sa a waya, a tunanin sa ko Abba ne shiyasa yayi saurin ɗaukar wayan yana duba wa, sai dai ba shi bane, baƙuwar number CE. Shiru kawai yayi yana tunani, domin tuni zuciyar sa ta raya masa numbern da jiya ta hargitsa masa rayuwa ce, duk da wannan ɗin ba'a rufe ta ba. "yanzu to meyasa aka kira sa? Ko wani abun ne Ziyada tayi?" Nan da nan zuciyar sa ta harbu da ɓacin rai, sai faman ajiyan zuciya yake yi ya kasa ɗaukar wayan, domin tsoro ne tsantsa ya shiga zuciyar sa har wani mugun bugawa take yi, saurin tsayar da motan yayi a gefen titi yana dafe ƙirjin sa tare da runtse idanu, ya hau karanta, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" domin ba ƙaramin hautsinewar zuciya yake ji ba, tamkar wani abu mummuna zai same sa
Me kiran be fasa kira ba, har sai da aka yi masa two missed calls, ana ukun ne ya ɗaga yana karawa a kunne hannun sa na faman rawa
Maganar na miji ne ya duke kunnen sa, sai dai babu ko daɗin ji muryan nasa, don daƙyar ma yake iya gane me yake cewa, tamkar dai ya toshe bakin nasa, ko kuma ya cika bakin nasa da wani abu yake magana
Dariya ce ta fara biyo baya, sannan ne ya soma magana, "Yunusa Hayat Sunusi.. shin kana ina tashin hankali ke jiran ka a gidan gonan ka? Tabbas idan har baka ƙarisa da wuri ba, to, zaka yi nadamar rayuwan ka. Hhhhh".
Ƙittt aka kashe wayan
Sosai a wannan karon ya dafe setting ƙirjin sa, sabida wani mahaukacin buga wa da take yi, gaba ɗaya jikin sa rawa yake yi, ya rasa me ke masa daɗi, addu'an ma daƙyar yake iya karanta wa, sabida ba jikin sa kaɗai bane yake mazari har ta zuciyar sa ta gama hautsine wa, kuma ya rasa dalili, be ma fahimci me maganar nasa yake nufi ba, amma haka ya daure yaci gaba da tuƙin nasa ya nufi gidan gonan.
◾▫️◾▫️◾▫️
A rikice Azeeza ta fito daga cikin gidan, wani irin rawa jikin ta yake yi tamkar mazari, har tuntuɓe take yi wajen sauri, Allah yasa me gadin be dawo ba har yanzu, shiyasa ta lallaɓa ta fice da gudun gaske. Tana fita ta hangi Motan ABUL KHAIRI ya shanyo kwana, wani irin sara wa gaban ta yayi, tayi saurin ɓuya a jikin bango har ya wuce ta, ajiyan zuciya ta sauke taci gaba da sauri-sauri tana waigen bayan ta, tana fita bakin titi ta sami napep ta shige sai gida.
◾▫️◾▫️◾
Horn me ƙarfi ABUL KHAIRI yake danna wa jin ba'a buɗe masa ƙofa ba
Da gudu me gadin ya ƙariso, dama ashe yana can baya wajen masu aiki ya shantake suna hira. Da sauri ya buɗe masa ya shigo da motan
Tunda ya hangi motan Ziyada ya ɗaure fuska kamar hadari, zuciyar sa gaba ɗaya ta sake hassala, ya fito a wani yanayin da jikin sa ko kaɗan babu ƙwari, kiran me gadin yayi ya tambaye sa, "tun yaushe Ziyada ta zo gidan nan?"
"Ranka ya daɗe tunda ka fita da safe ta zo".
"Meyasaka ka buɗe mata ƙofa? Ban maka kashedi ba?"
"Ranka ya daɗe ka yi, ayi haƙuri, wlh balbale Ni tayi da tsiya dole na buɗe mata".
ABUL KHAIRI be sake cewa komi ba ya nufi cikin gidan, yana buɗe ƙofan idanun sa suka sauka a kanta tana kwance a tsakar ɗakin, be hangi komi ba sai da ya shigo sosai yaga kamar wuƙa ne a jikin ta, ga jini na kwaranya ta ƙasan jikin ta, da ƙasan ƙafafuwan ta.
Daskare wa ABUL yayi a wajen tamkar an zare masa rai, sai da yaji wani dumm kamar ba ya duniyar kafin ya dawo hayyacin sa, wani irin zaro idanu waje yayi ya nufe ta da sauri yana salati. Duƙawa yayi gaban ta, ya saka hannyen sa da kamar za su tsinke tsaban rawan da suke yi, wuƙan ya ɗauka yana me kiran sunan ta
"Ke.. ke ZIYADA.. ke.. tashi mana meye.. haka?" Yayi maganar kamar zuciyar sa zata faso ƙirjin sa tsaban tsoro. Girgiza ta ya hau yi, amma dai kamar ba ta motsi, kamar dai ranta ya daɗe da fice wa a jikin ta. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Abinda yake ta maimaita wa kenan yana zame wa dirshan ya zauna a ƙasa. "Me ke shirin faruwa ne?" Yayi maganar a cikin zuciyar sa yana kama kansa da hannayen sa biyu ya soma hautsina gashin kansa, sai kuma ya sake saka hannu yana girgiza ta yana faman kiran ta, sai ga hawaye shaaa sun soma zubo masa.
A dai-dai lokacin ne jiniyan ƴan sanda suka cika anguwan, kan kace me har sun ƙariso gidan sun shigo
Ruɗewar da ABUL KHAIRI yayi har ya kasa motsa wa a inda yake zaune, kawai kafe ƙofa yayi da manyan idanun sa da suka sauya kala lokaci ɗaya tsaban rikici.
_Ya za'a kaya? Shin wani irin tsaka me wuya ABUL KHAIRI yake ciki? Wa ya saka shi a wannan mawuyacin halin?_
_Anya ma Ziyada ta mutu? Ko tana raye?_
_Shin waye ma ya kira ƴan sandan nan?_
_Me Azeeza ta aikata?_
_amsar ku na waje na. Ta Comments ɗin ku kaɗai zan gane kuna son ci gaba. More Comments more typing_
*HAPPY JUMA'AT MUBARAKH FAN'S 🤩*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*TARIHIN FARILTA SALLAH*
'''An farilta sallolin nan biyar ne gabanin ƙaura, watau hijira, da shekara ɗaya da rabi. Sallah ce kaɗai ibadar da aka farilta ta a sama a daren Isra'e, kamar dai yadda aka ruwaito a hadisin nan na Anas. Da farko an umurce shi da Sallah guda hamsin ne; da sannu aka dinga rage su har suka zama biyar a bisa roƙon da shi Manzon ya yi wa Ubangijin sa. Da suka zama biyar, sai Allah ya ce masa su biyar ɗin nan, dai-dai suke da hamsin.
Malamai da yawa sun yi bayanin yadda sallar ma'aikin Allah, mai tsira da aminci, take gabanin Isra'en.
Wasu malaman sun ce, "Gabanin Isra'e, babu wata sallah wadda aka farilta sai sallar dare (Ƙiyamul lail) wadda aka umurci ma'aiki da yin ta ba da iyakataccen lokaci ko adadi ba, kamar yadda yake a suratul Muzzammil, ayoyi huɗu na farko:
"Ya wanda ya lulluɓe! Ka tsayu domin yin Sallah a cikin dare (duka) face kaɗan, rabin sa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi, ko ka ƙara kansa...
Ma'aikin Allah ya kasance yana yin sallar a kashi biyu cikin uku na dare ko a rabin sa ko kuma sulusin sa. Musulmi suka dinga yi tare da shi kamar shekara guda har suka gaji; daga nan sai Allah ya shafe ta don jin ƙan su.
An ruwaito cewa sallar da Musulmi suke yi gabanin tafiyar dare suna yin ta ne kafin faɗuwar rana da kafin ketowarta kamar yadda yake a sallah littafin Almanhalil Azb. Gabanin ƙaurar Annabi zuwa Madina raka'o'in sallah bibbiyu ne, bayan ƙaura ne suka zama hurhuɗu, illa magriba da ta kasance raka'a uku, ita kuma sallar subahi ta tsaya a kan biyu saboda dogon karatun da ake yi cikin ta. Buhari da Ahmad sun ruwaito daga Nana A'ishah cewa, "an farilta sallah raka'a bibbiyu, bayan ƙaura ne aka mai da ita raka'a hurhuɗu, amma an bar sallar tafiya a kan raka'a ne bibbiyu, sai sallar magriba ita ko da ma raka'a uku-uku ce."
Allah ya sa mu dace.'''
*________________________________*
*PAGE 19 & 20*
*________* Gaba ɗaya wajen sa suka yo suna me ƙale sa da bindiga, yayinda Shugaban cikin su yace, "You are under arrest".
ABUL KHAIRI be ma San suna yi ba, domin kuwa tuni tunanin sa ya tsaya cakk ya dena motsi
Ɗaya daga cikin ƴan sandan ne ya cafke hannayen sa ya zagayo dasu ta baya ya saka mishi hand cuff
Har ya gama ABUL KHAIRI be motsa ba, domin shi gani yake yi tamkar mafarki yake yi, kuma zai farka nan ba da jima wa ba, sai da ya ji sun daka matsa tsawa a kan, "ya tashi". Sannan ne ya dawo hayyacin sa, ya bi su da kallo da manyan idanun sa da suka ƙanƙance tsaban firgita suka yi jazur, wasu sabbin hawayen ne suka wanke masa fuska, nan da nan jikin sa ya soma rawa, muryan sa na fita daƙyar yace, "Wlh ban san komi ba a kai.., ba.. Ni ne.. na aika ta.."
"Yi mana shiru. Idan ka je can zaka amsa ne". Cewar Ogan cikin su, sannan ya ba su umarnin su tafi dashi
Da ƙarfi suka ja sa dole ya miƙe, suka tasa ƙeyan sa suka yi waje
Inda shugaban da wasu biyu cikin Yan sandan suka yi saura a wajen
Ogan ya kalle su yace, "ku duba min wancan jakan ko za'a sami address ɗin ta".
"Ok Sir". Suka amsa a tare suka nufi jakan Ziyada dake kan kujera
Shi kuma ogan sai ya ciro wayan sa ya nemi agajin gaggawa wajen masu jinya.
Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci motar asibiti ta iso gidan, inda aka ɗauko Ziyada aka saka ta cikin motan aka yi asibiti da ita
Gidan kuma ABUL KHAIRI nan aka zuba police ko ta Ina aka hau bincike, gaba ɗaya an tarkata daga me gadi da masu kula da gidan, duk an wuce da su station.
Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya je wa iyayen Ziyada, inda suka ji mummunan labarin ɗiyar su na nan rai a hannun Allah a asibiti, babu ɓata lokaci suka garzaya can. A lokacin har an tabbatar da mutuwar ta ma. Daga Dady har Mom Kuka suka saka, gaba ɗaya sun hargitsa asibitin da koke-koke, nan da nan labari ya soma bin dangin su, har wasu sun rigada sun iso, haka ma iyayen Sagir duk sun zo, har shi Sagir ɗin ma da ba ya garin ya ji mummunan labarin. musamman inda aka ce masa wai ABUL KHAIRI ne yayi kisan, take a nan ya kusa yanke jiki ya faɗi, sai da aka riƙe sa, nan da nan ya biyo hanya ya nufo Kano cikin tashin hankali.
Iyayen ABUL KHAIRI ma tuni labari ya je musu, domin tuni sun matsa shi ya faɗa musu address ɗin sa, kai tsaye gidan suka wuce, inda suka sami Abba dawowar sa kenan, suka faɗa masa mummunan labarin nan, salati kawai ya dinga rafka wa yana shirin faɗi, shima daƙyar ya samu ya tsayar da ƙafafun sa, nan da nan hankalin sa yayi mugun tashi, kai tsaye ya wuce Hospital tunda har yanzu ba'a sallami Maimuna ba, sai dai yau ake saka ran sallaman nata dama, Batool ma na can. Sai dai sanda yaje ya kasa sanar wa Mamy
Ita kuma ganin hankalin sa a matuƙar tashe, sai ta hau tambayar sa
Sai da yace, "su fita waje su yi maganar". Kafin ya sanar mata
Take a nan ta yanke jiki ta faɗi. Tashin hankalin da ba a saka mishi rana
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, a cikin awanni biyu labari ya zaga ko ina a dangin su, domin tuni kowa ya sani, dangi na kusa duk sun taho gidan Mamy, sai dai Mamy har yanzu tana asibiti bata farfaɗo ba, domin sosai take a mawuyacin hali
Su Batool kuka sosai suke yi, daga ita har su Maimuna da su Amir, duk suna asibitin
Sai da Abba ya je ya amsar mata sallama, sannan ya saka Aƙilu ya mayar da su gida, haka mutanen anguwa da dangi duk sun cika gidan, kowa ya zo jaje. Gaba ɗaya ahalin sun ruɗe da wannan babban al'amarin.
◾◽◾◽◾
Fannin Ƴan sanda suna ta binciken su, inda suka saka ABUL KHAIRI a gaba da tambayoyi tare da gana masa azaba, amsa ɗaya yake ba su, "ba shi ne ya kashe ta ba". Gaba ɗaya ya rasa tunanin sa, domin ba kaɗan ba mutuwar ta shige sa, wai mutuwar Ziyadan shi abar ƙaunar shi? kuma wai shi ake zargi? wannan abun da me yayi kama?
To abun ya haɗe masa biyu, ga dukan da yake sha, lokaci ɗaya suka nemi numfashin sa suka rasa, sun zuba masa ruwa ko zai farfaɗo, amma ina ya ƙi farfaɗo wa, gaba ɗaya jikin sa sai da suka yi masa ruɗu-ruɗu da duka, dole suka wuce dashi Hospital don bashi taimakon gaggawa
Zuwa lokacin dama tuni Abba da Abokanan sa, tare da Mijin Umma Salamatu, sun ta sintiri a bar su su ganshi amma abun ya faskara, suna tafiya aka kawo shi asibiti cikin mawuyacin hali, ai shima sai Abba ya yanke jiki ya faɗi tsaban tashin hankali. Wannan abu dame yayi kama? wai ɗan su ake zargin yayi kisan kai?
◾◾◾
Haka zalika iyayen Ziyada su ma suna can a tashin hankalin, itama Mom sume wa gau tayi har yanzu bata farfaɗo ba, Dady ne kawai yake da ƙarfin hali, amma fa kuka kashirɓan yake yi yana faɗin, "a bar sa ya je ya kashe ABUL KHAIRI, domin duk wanda ya kashe masa tilon ƴar sa, to, sai ya ga bayan sa". Daƙyar su Dadyn Sagir suka hana sa zuwa.
Duk wani bincike sai da likitoci suka yi, kafin suka ba da gawan ta domin ayi mata Sallah. tunda aka kai gawan ta gida mutane suka cika gidan, sai koke-koke ake yi, zuwa lokacin Mom ta farfaɗo har an mayar da ita gida, ta sha kuka sosai musamman sanda ake shirin kai Ziyada makoncin ta, ko addu'a ta kasa mata, sai ma ta ƙara sume wa, sai da aka zuba mata ruwa ta farfaɗo, ana yin sallan magriba aka sallaci gawan ta aka kai ta gidan ta na gaskiya. Sai mu ce Allah ya jiƙan ki ZIYADA, Allah yasa mu yi kyakykyawar ƙarshe Amin.
◾◽◾◽◾
Abba hawan jinin sa ne ya tashi, dole aka ba shi gado
Ita kuwa Mamy dogon suma tayi, sai bayan isha'i ta farfaɗo, sai dai tunda ta farka take kuka. Su Umma Hassana da Umma Husaina ne suke ta faman rarrashin ta, amma ina Mamy sosai take kuka. Ji take yi tamkar a mafarki, wai ɗan ta shi ne yayi kisan kai? Kisan kai? Abun sosai ya girgiza ta
Sai da su Hajiya Falmata da Alh. Sunusi suka taho, su ne suka yi mata nasiha sosai a kan, "yarda da ƙaddara". Daƙyar suka samu suka rarrashe ta. Har ta samu tayi sallan da suka wuce ta, ta duƙufa roƙon Allah a kan, "ya kawo ma ɗanta mafita, domin ta san bazai taɓa yin kisan kai ba, tabbas ɗan ta ya taka sahun ɓarawo ne".
A taƙaice dai duka asibitin suka kwana, inda su Batool da Maimuna suka koma gida tare da Umma Salamatu, tunda dama sun dawo asibitin duba su Mamy. Su kuma su Hajiya Falmata suka wuce da Amir da Baby Gidan su.
A ranan Mamy kwana tayi kai kukan ta wajen Allah, haka ma su Hajiya Falmata, da sauran masoyan su. Hajiya Mama ma ta kasa zuwa sabida tashin hankali, sai dai addu'a da ta duƙufa yi babu ji babu gani.
*WASHE GARI*
Kai tsaye Dadyn Sa'ima da Uncle Abbas da ya dawo tun daren jiya jin mummunan labarin, dayake ba ya gari, Hospital ɗin da aka kai ABUL KHAIRI suka wuce, sai dai nan ma an hana su ganin sa. Sun sha wahala matuƙa kafin suka samu ganin sa, dayake DPO ɗin da case ɗin ke hannun sa akwai tsauri, dole sai da suka bi ta hanyoyi kafin suka samu shiga ɗakin da aka kwantar dashi, don ma su manya ne da wahalan sai tafi haka.
A safiyar Ummu da Mijin ta Alh. Naseer duk suka iso, babu daɗe wa itama Aunty Fatima ta iso, duk can asibitin suka wuce kai tsaye, inda Zee da su Safiyya matar Uncle Abbas tare da su Umma Hassana duk suna ɗakin da aka kwantar da Mamy, tunda shi Abba an hana kowa shiga wajen sa, saboda ana son ya huta ne sosai, wataƙil jinin sa zai sauka
Zee Kuka sosai take ta yi, ga ciki da take fama dashi, daƙyar Umma Salamatu ta rarrashe ta, amma duk da haka ta ƙi yin shiru
Ummu na zuwa sabon kuka ya ɓarke, domin rungume Mamy tayi suka fashe da wani sabon kukan. Aunty Fatima na gefe tana taya su.
Lokacin ne su Dadyn Sa'ima suka shigo ɗakin, tare da Alh. Naseer (Mahaifin Maimuna, da suke kiran sa da Baba), tunda shi dama kai tsaye asibitin da aka kwantar da ABUL KHAIRI ya wuce, saboda sai da ya kira Uncle Abbas yayi masa bayanin suna can, sai yanzu suka shigo tare. Su ne suka rarrashi su Mamy tare da musu nasiha, suna faɗa musu, "ba kuka ya kamata su yi yanzu ba, addu'a da kai wa Allah kukan su ya kamata".
Hakan yasa su Ummu suka dakata da kukan, sai hawaye da suke ta faman share wa.
Fita suka yi suka sake koma wa wajen Doctorn da yake duba Abba, sun jima a can har suka nemi ganin sa, a lokacin ma ya farka sai ƙarin ruwa da ake masa, nan suka zauna a wajen sa suna ta mishi nasiha tare da nuna masa, "wannan ƙaddaran su ce, kuma da sannu idan har yana da gaskiya zai fito".
Hankalin Abba sosai ya ɗan kwanta, sai dai da suka sanar masa ABUL KHAIRI na a mawuyacin hali sai hankalin sa ya sake tashi, dole suka ci gaba da ba shi baki.
Haka gaba ɗaya ahalin biyu suka kasance a cikin mawuyacin hali, babu me jin daɗin rayuwar sa a tsakankanin kwana biyun nan da suka shuɗe, sai dai jikin Abba da ɗan sauƙi, haka ma itama Mamy, dole aka ba su sallama suka koma gida.
**********
Inda a gefe ɗaya ABUL KHAIRI yana can shima a mawuyacin halin a asibiti, kwanan sa biyu ya farfaɗo, sabida shima har da alluran barci aka yi masa, yanda gaba ɗaya suka kasa gane kansa, gaba ɗaya tamkar dai ya samu taɓuwa haka ya koma, dole suka yi masa allura har sanda ya sake farfaɗo wa a kwana na uku da kai shi, a nan ne ya dawo hayyacin sa, sai dai kuka sosai yake yi, duk yanda likitocin suka so ya kwantar da hankalin sa sabida halin da yake ciki amma ina, bazai yiwu ba. Dole suka ƙyale sa, idan sun ga ya cika matsawa kansa sai su sake mishi alluran Barci. A haka kwana biyar suka shuɗe yana amsar treating hannun likitoci, da aka ga jikin nasa da ɗan sauƙi sai ƴan sandan suka matsa a sallame shi domin a mayar da shi station su ci gaba da bincike, domin gaba ɗaya Dadyn Ziyada ya tasa su gaba da, "sai sun aika su kotu an amsar mishi haƙƙin ɗiyar sa". Dole aka sallami ABUL suka wuce Station aka ci gaba da bincike.
Su Abba sun sake zuwa, daƙyar suka samu suka gansa, gaba ɗaya ya Gama fita hayyacin sa, har baƙin dole ya yi, duk jikin sa shatin bulala ne, dole ka zubar masa da hawaye, idanun sa sun yi luhu-luhu, bakin sa ya bushe duk ya rame, domin ko abinci ba ya ci, tun yana amsa wa ƴan sandan, "ba shi ne yayi kisan ba" har ma ya dena, sai hawaye da kullum yaƙi ƙafe wa a idanun sa
Sanda ya ga mahaifin sa da Uncle Abbas kuwa, kuka ya fashe dashi me tsuma rai, domin tunda wannan iftila'in nan ya faɗa masa be yi tozali da wani jinin sa ba, shiyasa yayi matuƙar kewar su
Rungume sa Abba yayi yana share hawaye, yayinda shima Uncle Abbas Yana gefe yana share nasa. Sai da suka saki juna kafin shima Uncle Abbas ya rungume sa, sun daɗe a haka yana bubbuga bayan sa, kafin suka saki juna, ya kama sa ya zaunar dashi suka saka shi a tsakiya, babu wanda ya iya magana cikin su, domin ba ƙaramin tashin hankali suke ciki ba, musamman da suka yi tozali da ABUL ɗin
Sai Shi ABUL KHAIRIN ne ma ya soma magana, "Abba Mamy fa?"
Kallon sa Abba yayi, sai ya kawar da kansa yace, "tana nan lafiya.. itama zata zo ta duba ka".
Lumshe idanu kawai yayi yana tsiyayar da hawaye
"Ka kwantar da hankalin ka, mun san cewa ba kai ne kayi kisan nan ba duk da ba mu san me ya faru ba, amma ka daure kayi mana bayanin komai, domin kotu ake son tura mu". Cewar Uncle Abbas Yana me riƙe masa hannu
Buɗe idon sa ABUL yayi ya aza a kansa, sai ya gyaɗa masa kai yana me shashsheƙan kuka. Nan ya soma faɗa musu abinda ya faru a ranan.
"Amma mene ne alaƙar ka da yarinyan da har ta zo maka gida?" Uncle Abbas yayi masa wannan tambayar
Shiru ABUL KHAIRI yayi yana share hawayen fuskar sa da ya ƙi tsaya wa, "me zai ce musu? Shin zai faɗa musu alaƙar su komi da komi ne? Ko kuma kawai zai ce musu ita ce yarinyan da suke soyayya? Kuma a kanta ne ya bijire wa iyayen sa zaɓin da suka yi masa. Amma kuma ya san cewa dole ne asirin sa zai tonu, dole ne duniya ta san mene ne ainihin alaƙar shi da ita na ɓoye. Sabida ya san bincike dole ne ya binciko hakan. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. wannan musiba da me yayi kama? Allah na tuba! Allah ka yafe min.. na San saɓon ka ne ya ja min shiga wannan mummunan ƙaddaran. Ya Allah na tuba! Ka cece Ni!"
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*NASIHA*
_Muna iya lura cewa ga al'ada in an Kira talaka zuwa fadar sarki yakan gyara fuska, ya yi ado don ya sami kyakkyawar maraba daga Sarki. To, in haka ne, ina ga in ya tashi zuwa tsayuwa gaban Ubangijin sa? Bawan da aka neme shi ya zo gaban Ubangiji, Sarkin sarakuna, mamallakin mamallaka, lalle kam ya fi kamata ya gyara kansa saboda wannan muhimmin muƙami. Ya kamata ya gyara kansa ta tsarkake tufafin sa da jikin sa, ya fito cikin kama mafi kyawu, kamar dai yadda aka umurci musulmi duka a cikin suratul A'ARAF, aya ta 31:_
_"ya ɗiyan Adam! Ku riƙi ƙawar ku a wurin ko wane masallaci"_
_Allah yasa mu dace._
*________________________________*
*PAGE 21*
*________* "Kai lokacin ku ya cika ku fito haka nan, daga yau babu me sake ganin sa sai lauyan sa, don haka ku nemi lauya kafin a shiga court". Cewar wani tsagerar ɗan sanda dake kula da ABUL KHAIRIN
Kallon juna suka yi, sai suka miƙe kuma. ABUL KHAIRI na ji yana gani suka yi masa sallama suka tafi babu yanda zai iya, sai kawai ya kifa kai ya soma kuka, abinda yake yi kenan ko da yaushe, babu abinda ke damun sa sai kewan gida, tare da kewar Ziyadan shi, har yanzu ya kasa yarda cewa Ziyadan shi ta mutu, gani yake yi mafarki ne kuma zai farka, ko kaɗan halin da yake ciki ba ya damun sa, mutuwar Ziyada ya fi komi ɗaga masa hankali, shi ke saka shi fita hayyacin sa lokaci ɗaya. "Wai Ziyadan shi ce ta mutu?" Tambayan da kullum yake wa kansa kenan, kuma ya rasa me ba shi amsa, domin zuciyar sa ta ƙi yarda da hakan duk da azaban da yake fuskanta.
Su Abba suna koma wa gida, suka tarar da su Mamy na jiran su, daga Mamy sai su Maimuna, sannan sai Ummu da Safiyya matar Uncle Abbas, dayake su Umma Salamatu zuwa suke yi su koma kullum, yau kuma babu wacce ta zo a cikin su, ƙila sai anjima, ita kuma Ummu tun ranan tana gidan, Baba shi ya koma Kaduna. su Aunty Naana da Aunty Rufaida ma duk jiya suka zo da mazajen su, itama Aunty Fatima ta koma jiya, amma zata dawo.
Da sallama suka shigo, inda su Ummu suka amsa musu suna bin su da kallo. Zama suka yi su Maimuna suna musu, "sannu da zuwa" suka amsa su da, "yauwa"
Ummu tace, "Yaya kun samu ganin nashi kuwa?"
Sai da Abba yaja numfashi kafin yace, "eh mun ganshi amma daƙyar, kuma sun ce daga yau ba wanda zai sake ganin sa sai dai a samu lauya, domin court za'a je".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Cewar Ummu cike da tsananin damuwa
Itama dai Safiyya salatin tayi tana me zuba tagumi da hannu biyu
While Mamy hawaye ta soma yi tana me riƙe da kanta
Hakan da su Batool suka gani ne yasa su ma suke nasu hawayen, har ta Baby da take ƙaramar su kuka take yi, duk da bata gama fahimtar ma abinda ke faruwa da Yayan nata ba, sai dai ta san an kama shi.
Uncle Abbas yace, "haƙuri za ku yi Adda, Ni hakan ma yafi wlh, gwara a tura Court ɗin ayi-ayi ko zai samu ya fito".
"Amma taya kake tunanin zai fito bayan ba mu da ƙwaƙƙwaran sheda? Yarinyan nan a gidan sa ta mutu, ina jiye mana shiga kotun nan a yanke masa hukunci". Cewar Ummu kenan cike da tsananin damuwa
Abba yace, "ya zamu yi? Allah zai fitar dashi insha Allahu, dole zamu dage da addu'a domin nasan ɗan mu be aikata ba". Sai ya kalli Mamy da ke ta faman hawaye bata ce komi ba yace, "ki dena kuka don Allah, hakan na ƙara min tashin hankali, sai in rasa me ke min daɗi".
Ɗago kai tayi ta kalle sa da hawaye a fuskar ta tace, "Abban su dole nayi kuka, yanzu wai Baba na ne ake zargin yayi kisan kai? Wannan abun da me yayi kama? wlh ji nake yi kamar na haukace tsaban baƙin cikin wannan lokacin.."
"Subhanallah.. kar ki sake faɗar hakan kin ji ko? Ke musulma ce fa, sannan na san ki da yarda da ƙaddara, Khadijah kina da haƙuri sosai, don haka kar wannan ƙaddaran ya sanya ki ki kauce hanya". Abba ya faɗa yana kallon ta
Gaba ɗaya parlour'n shiru aka yi in ban da shashsheƙan kukan su Batool da suka kasa dena wa
Uncle Abbas yace, "yanzu to ya za ayi? Wani lauya zamu samu? Ni shi ne damuwa na".
Ajiyan zuciya Abba ya sauke, ba tare da yace komi ba illa tunanin mafita da yake yi a ransa
Mamy tace, "Ni zan tsaya masa, zan tsaya wa ɗana".
Gaba ɗaya kallon ta suka yi
Inda Abba yace, "taya zaki tsaya masa bayan ga halin da kike ciki? A'a baza ai haka ba, wani lauyan za mu samo".
"Meye amfani na idan har ban tsaya masa ba? Kar ka manta nima lauya ce. Don Allah Abban su ka bar Ni in tsaya masa don Allah". Ta ƙare maganar da rawan murya tana me ci gaba da hawayen ta
"Yaya ka bar ta kawai tunda zata iya, hakan ma ya fi wlh". Cewar Uncle Abbas
Ummu tace, "Adda don Allah ki bari a samu wani yayi aikin nan, baza ki iya ba".
"Nima haka nake gani". Abba yace hakan
"Zan iya, zan iya, Ni zan tsaya wa ɗana, babu wanda zai fi Ni ƙoƙarin ƙwato wa ɗana haƙƙi, domin babu wanda ya san me nake ji". Ta ƙare maganar da kuka tana me miƙewa ta shige ɗakin ta
Shiru suka yi duk kan su suna me bin ta da kallo, inda Ummu kuma ta tashi ta bi bayan ta
Shi kuma Uncle Abbas yace, "ka bar ta tayi don Allah Yaya, aikin ta ne fa, na san Adda ta tana da ƙware wa a aikin ta, memakon ma a samo wani gwara ita tayi hakan zai fi".
"To shikenan Allah ya shige mana gaba". Abinda Abban ya faɗa kenan
Sosai Uncle Abbas yaji daɗi, inda ya miƙe yana cewa Abban, "za su tafi, ko zuwa gobe ko jibi za su dawo, idan kuma da matsala za su yi waya".
Itama Safiyya miƙe wa tayi tana gyara mayafin ta, kafin ta kalli Uncle Abbas tana cewa, "bari in shiga in Yi musu sallama". Wuce wa tayi ta shiga ɗakin Mamy, nan ta tarar da su suna tattaunawa wa, domin har Ummu ta rarrashi Mamyn tayi shiru, sallama tayi masu a kan, "zata tafi," sai kuma tace, "Aunty ko dai in wuce da su Amir da Baby ne? in ya so su zauna a wajen mu, na ga su ma suna shiga damuwa da halin da ake ciki, gwara su je can ko sa samu sukuni".
Ummu tace, "nima haka na gani, ku wuce kawai tare ɗin".
"To shikenan, sai mun dawo goben, Allah ya bayyana gaskiya, Allah ya ba mu haƙuri da juriya".
"Amin Amin". Suka amsa daga Ummu har Mamyn
Sai da suka fito suka yi sallama da Uncle Abbas
Maimuna kuma taje ta haɗo wa Baby kayan ta ɗan kala biyar haka cikin jaka, shima Amir ya haɗo nasa. suna fito wa suka wuce
While Batool da Maimuna suka shiga kichen ɗaura girkin dare. Suka bar su Ummu suna tattaunawa a Parlour.
***** ****** ***** ***** ******
*TWO DAYS*
Yau Mamy ta shirya ta wuce police station don gana wa da ABUL KHAIRI, tana isa ta nemi iso wajen DPO, bayan ya bata iznin shiga, sai ta shiga suka gaisa, sannan ta faɗa masa, "ita ce mahaifiyar ABUL KHAIRI, ta zo ganin sa ne".
DPO yace, "Madam ai an rufe ganin sa har zuwa ranan da za'a gurfanar dashi Court, shawaran dai da muka ba ku ku nemi lauya, domin Monday na sama Mahaifin yarinyan yace za'a shiga court".
Kallon sa tayi fuska babu walwala tace, "DPO Ni dama ba na zo nan bane a matsayin wacce zata gan shi, a matsayin lauyan sa na zo". Sai ta ciro I.D Card ɗin ta ta nuna masa
Ɗan kallon ta ya yi yana gyaɗa kai, kamar yana shirin magana sai kuma yayi shiru yana duba I.D ɗin, bayan ya gama ya miƙa mata yana murmushi yace, "Good Madam, uwa zata kare ɗan ta a court? Abun gunun burge wa! Allah ya taimaka".
"Amin". Tace dashi still fuska babu fara'a
Daga nan kiran ASP ɗin da Case ɗin ke hannun sa DPO ɗin yayi, inda ya faɗa masa, "a bar ta ta shiga lauyan sa ne." don haka aka yi mata jagora har ɗakin da ABUL KHAIRI yake ciki.
Yana zaune kamar kullum ya haɗe kai da gwiwa ya maƙure a jikin bango, babu abinda yake yi sai tunanin da ya zame masa jiki.. buɗe cell ɗin da ake yi ya dawo dashi hayyacin sa, sai dai be ɗago kai ba bare yaga me shigo wa, illa sake ɗaura hannayen sa da yayi a kansa yana matse wa
Shigo wa Mamy tayi idanun ta a kansa, ko bata ga fuskar sa ba tabbas ta ga sauyi sosai a tare da shi, nan kawai taji hawaye na son cika mata idanu sabida yanda ta ga ya ƙare sosai, fatar jikin sa yayi baƙi alamun wahala. A hankali ta taka izuwa inda yake zaune, bakin ta na motsi amma bata iya cewa komi ba
Ƙamshin turaren ta da bazai taɓa manta shi ba, wanda ya san wajen mutum ɗaya yake iya jin sa, wato mahaifiyar sa, jin sa yasa ya ɗago kai a wani irin firgice don gasgata abinda hancin sa ya jiyo masa, ilai kuwa itan ce tsaye a gaban sa ta zuba masa idanu, shima haka zalika idanun ya zuba mata ya kasa ko motsi, yayinda idanuwan sa suka cika fal da hawaye har suka soma zubo wa saman kuncin sa
"Baba na". Tafaɗa a hankali hawayen itama na zubar mata a fuska, zuciyar ta cinkushe da tsananin tausayin sa na ganin yanda fuskar sa ya yi matuƙar sauya wa, gaba ɗaya fuskar tayi baƙi da rama, ga kumburan da tayi sabida dukan da yake sha, duk ciwuka ne a jikin sa. "Ba..ba na". Ta sake faɗa da rawan murya tana me ɗaura hannun ta ɗaya kan bakin ta
"Mamy". Shima ya faɗa da sauri yana me miƙe wa tsaye, rungume ta yayi yana me fashe wa da wani irin kukan da tunda ya zo cell ɗin be yi irin sa ba, kuka sosai yake yi yana ƙara ƙanƙame ta
While itama tana taya sa, ta kasa rarrashin sa har tsawon wani lokaci, kana kuma ta ɗago sa tana me bin fuskar sa da kallo. "Baba na haka ka zama?"
Lumshe idanu yayi wasu sabbin hawayen na zubo masa, kana ya buɗe a kanta, cikin rawan murya yace, "Mamy.. kin ga ƙaddaran da ta faɗa min ko?.. wlh.. ban aikata ba, wlh ban kashe ta..."
Hannu tasa ta rufe masa bakin sa, kana ta riƙe sa suka zauna a saman bencin dake cikin cell ɗin, shafa kansa tayi hawaye na ci gaba da zubo mata, sai kuma ta soma bin jikin sa tana shafa wa da hannayen ta
Shi kuwa yana kallon ta ba tare da ya ce komi ba, still shima ya kasa tsayar da hawayen fuskar sa
Numfashi taja kafin tace, "na san baka aikata ba Baba na, ko da kowa be yarda da kai ba, Ni bazan taɓa ƙaryata ka ba; domin na san abinda zaka iya da wanda baza ka iya ba, na san ƙaddaran ka ce haka, kuma Allah shi ne zai fitar da kai, insha Allahu duk me bin ka da sharri Baba na; wlh bazai taɓa yin nasara ba".
Kuka ya ɓarke dashi yana me ɗaura kansa saman kafaɗan ta
Bata ce mishi komi ba illa bubbuga bayan sa da take yi
"Mamy na fi kowa sanin haka, na san cewa zaku goyi baya na duk da baku sani ba Ni ne na aikata ko ba Ni ba, amma wlh bani bane, tabbas na san hakan ƙaddara ta ne, amma kuma ji nake yi a raina abinda nayi muku shi ne sila, da ace tun farko na bi zaɓin ku nayi muku biyayya na rabu da ita, da tuni hakan be faru ba, da ace ba na kawo ta gida na da hakan be faru ba..."
"Haka Allah ya so ka dena faɗar haka, na tabbata ko da baka da alaƙa da ita; idan Allah ya so hakan ya faru da kai sai ya faru".
Shiru kawai yayi be ce komi ba illa hawayen da yake yi
Ɗago kansa tayi tana kallon sa, kafin kuma tace, "ba na zo nan bane domin na duba ka, na zo ne a matsayin lauyan ka".
Shiru yayi yana kallon ta shima
Sai ta gyaɗa masa kai kana taci gaba da cewa, "eh na zo nan ne domin na kare ka, don haka ina son sanin komi, ina son na san mene ne ainihin alaƙar ka da yarinyan?".
Sauke kai yayi ƙasa, be san me zai ce ba, a yau yana nadamar mummunan rayuwan da yake yi, ya gummaci mutuwar sa da ace iyayen sa sun san ainihin alaƙar sa da Ziyada, taya zai iya bayyana musu cewa yana rayuwar banza da ita? Yana aikata abinda Allah ya hana? Wannan abun kunya ne a tare da shi, duk da dai be taɓa aikata zina ba, amma hakan babu bambanci a wajen sa, kuma kunyan da zai ji idan ya aikata zinan; shi ne yake ji a yanzu, ji yake yi kamar ya tsaga ƙasa ya burma yake ji...
Mamy katse masa tunanin sa tayi da dafa masa baya, zuciyar ta na buga wa saboda ganin yayi shiru, tunanin ta ya tafi, "kar dai ace da gaske shi ne ya kashe ta? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" take maimaita wa a zuciyar ta, kana tace dashi, "ka faɗa min gaskiya ABUL KHAIRI, ba na son ka ɓoye min komi, Ni mahaifiyar ka ce, ba zan taɓa gudun ka ba". Ta ƙare maganar da guntun murmushi ganin ya ɗago kai yana kallon ta.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 22*
*________* Cikin rawan murya ya soma ba ta labarin duk alaƙar su da Ziyada, tun farkon haɗuwar su har irin rayuwar da suke yi da ita, da kuma abinda ya faru a ranan da ya je gidan gonan sa ya tsinci gawan ta
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Shi kawai Mamy take ambata a bakin ta, idanun ta a kansa tamkar za su faɗo don kallon sa
Cikin kuka yace da ita, "wlh.. wlh Mamy iya gaskiya ta na faɗa miki, wlh ban taɓa sanin ta ɗiya mace ba, ina tsoron abinda Allah zai min idan na aikata zina, wlh ban bi son zuciya ta ba..."
Katse sa tayi da faɗin, "baka bi son zuciyar ka ba Yunusa ko kuwa ka bi son ranka? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. wlh ko da wasa wani ya zo ya sanar min da wannan halin naka; wlh sai dai Allah ya bi mini haƙƙi na a kan ƙazafin da yayi maka, domin bazan taɓa yarda dashi ba, amma sai ga shi da bakin ka kake sanar dani?.. Kake sanar dani wai kana aikata wannan mummunar aika-aikan ABUL KHAIRI? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ina wayon ka yaje ABUL KHAIRI? Ina tarbiyyar da muka ba ka? Ashe kana cin amanar mu haka?"
"Mamy don Allah don girman Allah kiyi haƙuri ki yafe min, wlh nayi nadama matuƙa nayi nadama, Mamy bazan sake ba wlh, ki yafe min kinji ki yafe min, ko haka Allah ya bar Ni wlh nayi nadama". Kuka sosai yake yi yana roƙon ta, gaba ɗaya ya susuce ya durƙushe ƙasa yana ta kuka magashiyan
Sosai ya bata tausayi, abinka da uwa da ɗanta, nan ta ɗago sa tana cewa, "ba komi ya wuce, Ni babu abinda zan iya tunda komi ya rigada ya faru, me zan yi to? Haƙurin shi ne ya fi, sai dai kuma ka roƙi yafiyar Allah domin ganin dai-dai a rayuwar ka Baba na, haƙiƙa kayi kuskure matuƙa, tunda har ka zaɓi wannan ɗabi'ar banzan a matsayin waye wa, su ma waɗanda suke yi Allah ya shirye su domin basu san inda kansu ke musu ciwo bane, sun manta cewa za su tashi gaban Allah kuma duk rayuwar su za a nuna shi tamkar t.v, abinda suke tunanin sun yi a ɓoye suna ganin suna da wayau babu wanda ya gani, to, haƙiƙa akwai ranan jin kunya, akwai ranan nadama, kuma dole na sanar da Abban ku komi dole zai sani".
Mamy sai da ta rarrashe sa sosai domin ya ƙi yin shiru, sai da ta tabbatar da ta kwantar masa da hankali kafin ta tafi. A waje suka ci karo da Sagir shima ya zo
Gaisawa suka yi kafin yace, "Mamy ya ABUL KHAIRIN yake? Na je gida su Batool suka ce min kina nan shi ne na taho, Allah yasa dai yana lafiya?"
Murmushi tayi masa tace, "yana nan lafiya Sagir".
Fuskar sa da damuwa yace, "wlh sun hana Ni ganin sa, na shiga damuwa matuƙa da halin da yake ciki, na san halin ABUL KHAIRI bazai taɓa aikata ko da kisan kiyashi bane bare mutum, mutum ɗin ma Ziyada wacce yake matuƙar ƙauna, Mamy don Allah ku yarda dashi wlh ba shi ne yayi kisan nan ba, duk da Ziyada ƴar uwata ce amma ina goyan bayan Aboki na, na san halin sa bazai taɓa aikata wa ba".
"Kar ka damu Sagir insha Allahu mun fahimce shi, Allah dai ya shige mana gaba kawai, yanzu ma zan wuce in soma aiki na ne a gidan nasa tunda babu lokaci".
"To Mamy bari in raka ki mu je tare".
Mamy ta amsa mishi da, "to" sannan ta wuce motan ta ta shiga
Shima ya shiga nasa yabi bayan ta.
Kai tsaye gidan gonan suka wuce, inda suka tarar da me gadin a bakin aikin sa
Gaishe su yayi, domin ya san su duk kan su, kuma ya san matsayin su wajen ABUL KHAIRI
Sagir shi yace masa, "su shiga ciki suna son magana dashi ne."
A waje suka bar motan su suka shiga, suka zauna a bencin me gadin; da shi me gadin da Sagir ɗin. Ita kuma Mamy ta zauna a kujeran Robber tana fuskantar me gadin
Kiran sunan sa tayi tace, "Baba Iro zan so ka sanar min komi a ranan da abun ya faru?"
Baba Iro gyara zaman sa yayi ya soma sanar mata da komi, lokacin da Ziyada ta zo gidan, da kuma sanda ABUL KHAIRI ya zo shima, sannan da maganar da suka yi kafin ya shiga cikin gidan, sai kuma abinda ya biyo baya na zuwan ƴan sanda gidan a matsayin an yi kisan kai
Numfashi Mamy taja bayan ta gama rubutun ta, kana ta kalle sa ta sake jeho masa wani tambayar, "Baba Iro a tunanin ka baya ga su; babu wanda ya shigo gidan?"
"Eh gaskiya babu".
"Kuma babu inda kaje?"
"Eh to, na fita gaskiya, domin na zaga bayi sosai a ranan sakamakon gudawa da nake yi, sannan na fita bakin titi saboda rashin kati da babu a waya na, ina son Kiran Matata domin inji lafiyar ɗana da be da lafiya, to a lokacin zan kira ta sai na fuskanci kamar babu kati, shi ne na fita domin na siyo".
Kallon sa kawai Mamy take yi har ya dire maganar sa, kana tace, "to, amma kana da masaniyar wani saɓani da ya shiga tsakanin su a ranan? Ko kuma kafin dai ranan haka? Wanda zai iya jawo wani zargi?"
Baba Iro yace, "eh to, Hajiya Ni dai bazan iya cewa a'a ba ko eh, domin dai na saba ganin saɓani makamanciyar haka, duk da hayaniyar su nake ji a cikin gida, amma kuma a ranan da mummunan abun nan zai faru, ana gobe sun yi wani saɓani da shi, wanda har nan waje suka fito suna faɗa, inda ita Ziyadan take kuka tana ba shi haƙuri amma shi kuma yana sanar mata, "idan ta sake taɓa masa jiki to zai bata mamaki." sannan ya hau motar sa ya bar gidan, ita kuma a lokacin zama tayi tasha kukan ta, har naje ina bata haƙuri amma taƙi kula Ni, inda daga baya kuma ta bar gidan, to, bata sake dawowa ba sai washe gari a ranan da abin zai faru, bayan shi Alhaji ya fita gidan, tunda shi a gidan ya kwana a lokacin".
Bayan Mamy ta gama rubutun ta sai ta sake kallon sa tace, "Bayan haka babu wani abun kuma?"
"Gaskiya babu, domin sun ɗan kwana biyu babu abinda ya shiga tsakanin su, tun wani faɗa dai da suka yi, to kwana ɗaya ne ina ga suka shirya".
Mamy ta sake cewa, "to babu wanda ya shigo gidan a ranan ko kafin ranan? Ko da yaushe su ne kaɗai masu shigo wa?"
Shiru ya ɗan yi yana faman tunani yana zare ido
Sai Sagir da ya nutsu duk yana sauraron su yace dashi, "ana magana, ka faɗa mana komi don Allah domin samun kuɓutar Aboki na, ko meye ma idan ka sani ka daure ka sanar mana".
Baba Iro yace, "eh to akwai wata wacce ta taɓa zuwa kwanakin baya.."
"Wace ce? Shin ka santa?" Cewar Mamy cikin ƙosawa tana me katse masa zancen sa
"A'a ban san taba gaskiya, sai dai ta ce min ita ƙanwar Alhaji ne, kuma na bar ta ta shiga, to, ban dai sake ganin ta ba sai ana gobe abin nan ya faru, ta zo ta ce min saƙo zata amsa a wurin sa".
"Shin baka san sunan ta?" Mamy ta sake tambayar sa
"A'a ban sani ba wlh, sau biyu na taɓa ganin ta, kuma wlh na ga suna yanayi da Alhaji shiyasa na yarda na barta".
"Taya zaka bar ta bayan baka santa ba? Sannan kuma baka damu da sanin me take yi a ciki ba?" Sagir ya faɗa hakan a ɓacin rai
Me gadin na shirin magana, sai Mamy ta katse sa da faɗin, "zaka iya fasalta min kamannin ta?"
"Eh zan iya Hajiya, tana da tsawo dai yarinyan, sannan fara ce, kuma bata da jiki sosai; ƴar matsakaiciya dai".
Shiru Mamy tayi tana tunani, sai kuma ta sake jeho masa tambaya, "a lokacin da take zuwa gidan Tana daɗe wa? Kuma tana tarar da shi ABUL KHAIRIN?"
"Eh duk a lokacin tana tarar dashi, domin har ita Ziyadan a lokacin tana gidan, amma dai ba ta daɗe wa sosai gaskiya, sai dai zuwan ta na biyu ta fi daɗe wa".
"Tom na gode Baba, kayi min magana da masu aikin ciki sai mu tattauna dasu su ma".
"To babu damuwa Hajiya, bari in Kira su". Me gadin ya faɗa yana tashi da sauri ya nufi cikin gidan.
Babu daɗe wa sai ga su sun dawo tare da masu aikin gidan su uku, domin su kaɗai ne masu aiki yanzu a gidan, da su huɗu ne amma ɗayan ya daɗe da yin tafiya, saboda rasuwan da aka yi musu shi ne ya tafi gida.
Duka Mamy sai da tayi musu tambayoyi, sannan suka yi sallama suka fito
A nan Sagir yayi mata sallama shima ya wuce gida
Itama kai tsaye gidan ta wuce. Tana shiga Parlour da su Batool taci karo
Ita Batool tana zaune saman Three sitter, ta kwantar da kanta a jikin kujeran tare da lumshe idanu
While Maimuna tana kwance kan One sitter, ta ɗaura kanta a hannun kujera tare da ƙudundune ƙafafuwan ta a saman kujeran, ta tsira wa waje ɗaya ido tana faman tunani, gaba ɗayan su sosai abinda ke faruwa da Yayan nasu ya shige su, barin ma Maimuna, domin ita akwai ta da tausayi, duk abinda zaka yi mata idan har wani abu ya faru da kai, tana nuna tausayawan ta matuƙa, bata da riƙo ko kaɗan, bata damu da ABUL KHAIRI na musguna mata a gidan ba, tausayin sa gaba ɗaya take ji, idan ta zauna tana tunanin, "yanzu haka yana can yana shan duka a wajen ƴan sanda." sai hakan ya riƙa saka ta kuka, ta san shi ba me son wahala bane a rayuwa, ta dinga tunanin, "ko me yake yi yanzu? Ya yake yanzu?"..
Har sau biyu Mamy tayi sallama amma basu amsa mata ba, gaba ɗaya hankalin su ba ya jikin su, sai da ta shigo ta sake yi kafin suka ɗago kai a tare suna amsa wa
Da kallo ta bi su dashi, kana kuma tace, "tunanin me kuke yi haka har ya ɗauke muku hankali?"
"Babu komi Mamy, sannu da zuwa". Cewar Batool kenan tana kallon Mamyn
Itama Maimuna sannu tayi mata
Ta amsa su tana zama a gefen Batool, sannan kuma tace, "Abban ku be dawo ba?"
"Ya dawo ya sake fita yanzu". Batool ta sake bata amsa
"Ok kawo min ruwa Maimuna".
Tashi tayi da sauri taje ta kawo mata
Amsa tayi tasha da yawa, sannan ta tashi ta wuce ɗaki.
Dayake tun jiya Ummu ta koma Kaduna, sai ranan da za'a shiga Court za su sake zuwa.
Babu jima wa Abba shima ya shigo gidan, inda su Batool suka yi masa sannu da dawowa, ya amsa su yana wuce wa ɗakin Mamy
Sallama yayi ya shiga
Mamy dake zaune kan gado ta tuɓe riga tana ɗaura zani a ƙirji, ta amsa mishi sallaman tana kallon sa, kana kuma tayi masa, "sannu"
Ya amsa ta yana zama shima a gefen gadon, sannan yace, "har kin dawo?"
"Eh wlh".
"Ya yake?"
Numfashi taja kana kuma tace dashi, "lafiya..." Sai tayi shiru
Kallon ta yayi yace, "ki dena saka damuwa a ranki kinji? Insha Allahu Allah zai taimake mu".
Amsa mishi tayi da, "Amin" kafin kuma tace, "mun tattauna da Baba na, sannan na je gidan gonan nasa mun tattauna da masu aikin gidan". Nan ta sanar mishi da duk abinda ABUL KHAIRIN ya sanar mata
Shiru Abba yayi be ce komi ba
Hakan yasa Mamy ta kalle sa tace, "baka ce komi ba?"
"To me kike so in ce? Duk abinda ya faru yanzu sai ya ɗau izna, yanzu zai gane abinda yake aikata wa dai-dai ne ko ba dai-dai ba, duk abinda mutum zai ɓoye wa Mutane Allah ƙyale sa kawai yake yi, domin duk ranan da ya so tona masa asiri lokaci ɗaya zai yi, ba a masa wayau ko dabara". Yana gama faɗar haka ya miƙe zai fice
Mamy ta kira sunan sa tace, "Abban su don Allah kar kayi fushi dashi, don Allah".
Murmushi yayi bayan da ya juyo yana kallon ta, sannan yace, "ba fushi zan yi dashi ba Addan mu, abinda ya faru ma dashi ya ishe shi ishara, zan fita Parlour ne ko ba wanka zaki yi ba?"
"Eh wanka zanyi".
"To ki gama akwai maganar da zamu tattauna ma".
"To". Tace dashi tana me miƙe wa tsaye ta wuce Toilet.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 23*
*________* *MONDAY*
*RANAR SHIGA COURT*
Ƙarfe 02:30pm. A lokacin court ɗin da za'a gabatar da Shari'ar na cikin garin Kano ta cika maƙil, gaba ɗaya ahalin su sun iso wajen, har su Ummu da Aunty Fatima tun safe suke Kano, haka ma Uncle Abbas yau ya iso Kanon, tare da matar sa Safiyya suka zo, su Umma Salamatu, Umma Hassana, Umma Hussaina duk sun zo, haka ma Alh. Sunusi da Hajiya Falmata su ma suna cikin court ɗin, ita dai Hajiya Mama ta gaza zuwa domin hankalin ta a tashe yake matuƙa, baza ta iya ganin shari'ar ba. Zee itama Abba ya hana ta zuwa sabida cikin dake jikin ta, su Maimuna ma suna ciki, kai duk wasu masoyan su sun hallara a court ɗin har Inna Aliya ta zo, ita da Inna Maria duk sun zo, in ka ɗauke Inna Halisa da su Umma Sulaima da Uncle Sani su ne kawai basu da ninyan zuwa.
Alƙali na isowa aka tashi aka yi masa gaisuwar ban girma, kana suka zauna bayan ya zauna
A lokacin ƴan sanda suka iso da ABUL KHAIRI dake cikin Hand cuff, aka shigar dashi ɗan zagayen da ake ajiye masu laifi, ko kuma waɗanda ake musu tambayoyi
Maga-takarda ya miƙe ya soma jawabi kamar haka: "A yau June ɗaya ga wata, shekara ta dubu biyu da ashirin da ɗaya. 1 June 2021. Zamu saurari ƙara wanda Alh. Muh'd Iyaal ya shigar, a kan kashe masa ɗiya da Yunusa Hayat Sunusi yayi a gidan sa na gona dake bakin titi G.R.A". Sai ya miƙa wa Alƙali File ɗin
Amsa yayi yana gyara zaman sa, tare da gyara zaman Eyeglasses ɗin sa ya soma duba wa. Ɗago kansa yayi bayan ya gama yana kallon jama'ar wurin sannan yace, "Ina lauyoyin? Su gabatar da kan su".
"Suna na Brr. Sharif Muhammad El-emam, Ni ne lauyan dake kare masu kawo ƙara".
"Ni kuma suna na Brr. Khadeejah Yunusa Ubale, Ni ce me kare wanda ake zargi".
Rubutu Alƙali yayi kafin ya ba su damar su soma
Brr. Sharif ne ya miƙe ya soma magana, "Ya me girma me Shari'a, Yunusa Hayat Sunusi wanda aka fi sani da ABUL KHAIRI, saurayi ne ga Marigayiya Ziyada Alh. Muh'd Iyaal, kuma shi ne wanda ya kashe ta da hannun sa.."
"Of jection my low, Brr. Sharif Yana son ɗaura wa ABUL KHAIRI laifi bayan kuma zargin sa ake yi, har yanzu ba'a gano gaskiya ba".
"Ka gyara kalaman ka Barrister". Alƙali yace dashi
"Na gode ya me Shari'a". Yayi maganar cikin girmamawa, kana ya gyara wuyan rigan sa yaci gaba da faɗin, "ya me Shari'a ABUL KHAIRI shi ne saurayin Ziyada, kuma a gidan gonan sa dake bakin titi G.R.A aka samu gawan ta, sannan ƴan sanda sun same sa a lokacin da suka isa gidan gonan nasa, sun tarar dashi riƙe da wuƙan da ya kashe ta a hannun sa, kana kuma likitoci sun yi bincike a kan sawayen hannayen sa; kuma bincike ya nuna tabbas shi ne ya kashe ta, domin shi yayi amfani da wuƙar, ya me Shari'a muna son kamar yanda kotun nan take da adalci; ta yiwa ABUL KHAIRI hukunci dai-dai da abinda ya aikata, na gode ya me Shari'a". Sai ya koma ya zauna bayan ya miƙa wasu takardu ga Maga-takarda
Itama Mamy miƙe wa tayi kana ta soma magana, "Ya me Shari'a abinda ake zargin ABUL KHAIRI da cewan shi ya kashe budurwan sa wannan ba gaskiya bane, samun gawan ta cikin gidan sa ba shi ne zai tabbar da cewan shi ne ya kashe ta ba, hasali ma ABUL KHAIRI ya isa gidan ne bayan da aka yi masa waya a kan yaje gidan gonan sa akwai abinda ke faruwa, kuma ya isa gidan inda ya tarar da gawan ta, ruɗe wa ya saka shi ɗaukar wuƙar ba tare da ya san me zai je ya dawo ba, kuma ya me Shari'a a lokacin ABUL KHAIRI ba sa tare da Ziyada, domin saɓani ya shiga tsakanin su, shi kansa be san meyasaka ta shigo gidan ba, ya me Shari'a ta ya idan ABUL KHAIRI ne yayi kisan za'a kira sa a sanar masa yayi gaggawar zuwa gidan akwai abinda ke faruwa? Sannan ta ya ƴan sanda suka san abinda ke faruwa bayan ko ma'aikatan gidan basu san da cewan yayi kisan ba amma kuma labari har ya je ga ƴan sanda? Ya me Shari'a kamata yayi kotu tayi duba da idon basira domin gano ainihin wanda yayi kisan amma ba ABUL KHAIRI ba, wasu ne kawai suke ƙoƙarin laƙaba masa kisan domin ganin bayan sa, na gode ya me Shari'a". Koma wa tayi ta zauna
Inda Alƙali yayi rubutu bayan ya duba file ɗin da aka sake miƙo masa, sai kuma ya ɗago kai yace, "Kotu na buƙatar ƴan sanda su yi bayanin ta yanda suka san an yi kisan kai a gidan sa har suka je can?"
ASP wanda binciken yake hannun sa ya fito ya tsaya a gaban court ɗin
Inda Alƙali ya buƙata yayi bayani
Yace, "ya me Shari'a muna zaune a Office aka yi kiran mu da wata baƙuwar number, aka sanar mana akwai wani wanda yayi kisa a bakin titi G.R.A mu yi gaggawar zuwa, wannan yasa na ɗauki abokan aiki na muka isa gidan domin tabbatar da abinda aka sanar mana, kuma mun je mun tarar da shi ABUL KHAIRI a gaban gawan Ziyada riƙe da wuƙa a hannun sa, wannan yasa muka kama shi muka wuce dashi Station".
Rubutu Alƙali yayi kana ya ɗago yace, "shin kun yi bincike a kan wanda ya kira ku?"
"Eh ya me Shari'a, daga baya mun yi bincike ba mu samu komi ba, kuma alama ya nuna mana layin ta dena amfani gaba ɗaya, har dai yanzu muna kan bincike da inda aka siya Simcard ɗin".
"Ok zaka iya zuwa ka zauna". Cewar Alƙali bayan ya rubuta jawabin nasa. "Lauyoyi za su iya ci gaba da kawo shaidun su".
"Ya me Shari'a ina neman izni a bani damar yiwa ABUL KHAIRI tambayoyi". Cewar Brr. Sharif da ya miƙe
"Kotu ta baka dama". Alƙali ya ba shi amsa
Isa yayi gaban kantan da ABUL KHAIRI ke ciki, wanda tun soma shari'ar kansa ke ƙasa be ɗago ba, shiyasa baza ka iya gane a halin da yake ciki ba
Brr. Sharif yace dashi, "ABUL KHAIRI zan so ka yiwa kotu bayanin alaƙar ka da ita Marigayiya, da kuma abinda ya jawo saɓani a tsakanin ku ana gobe zata mutu?"
Ɗago kai ABUL KHAIRI yayi idanun nan nasa sun kaɗa sun yi jazur, duk me imani idan ya gansa sai ya tausaya masa, tamkar dai ba shi ba, ya sauya ya gama fita hayyacin sa gaba ɗaya, kai da gani ka san yana a cikin tashin hankali tsantsa
Su Batool da su Umma Salamatu har sharan hawaye suke yi a yanzu ɗin, domin tunda abun ya faru ba su ganshi ba sai yanzu
Be iya magana ba sai da Brr. Sharif ya sake maimaita masa tambayar kana yace, "kotu tana sauraron ka kana ɓata mana lokaci ABUL KHAIRI."
Murya a dishe ya buɗe baki a hankali ya soma magana, wanda ba kowa yake ji ba
Dole Alƙali yace dashi, "ka ɗaga murya ba ma jin ka".
Hakan yasa ya sake ɗan ɗaga murya kaɗan, duk da haka muryan ba ta fita sabida ta rigada ta disashe, kukan da yake sha da kuma kwana a inda be saba ba; shi ya haifar masa da wannan yanayin
Tiryan-tiryan ya soma bayar da labarin soyayyar su, sai dai be faɗa alaƙar dake tsakanin su ba, har zuwa ranan da suka yi faɗa ya kore ta, kana kuma washe garin ranan ya zo ya tarar da gawan ta
Murmushi Brr. Sharif yayi yace, "kenan kana so ka ce mana ba kai ne kayi kisan ba? Amma to ya aka yi gawan ta yazo gidan ka? Infact ma ya aka yi wani ya zo har gidan ka ya kashe ta bayan kai ne me gidan, kuma kai ne ke da damar shiga ciki?"
Shiru ABUL KHAIRI yayi ba tare da ya amsa ba, illa runtse idanu da yayi yana tunano ranan da abun ya faru, masoyiyar sa a kwance babu rai, yayinda shi ne ake zargi da kisan nata
"Muna sauraron ka fa ABUL KHAIRI? Nan fa kotu ne ba wajen wasa ba, ka buɗe baki ka yiwa kotu bayanin yanda aka yi ka kashe Ziyada, idan kuma kana son ɓata wa kotu lokaci ne sai ka faɗa mana, bamu da time ɗin wasa a nan. Shin mene ne ainihin abinda ya haɗa ku wanda yaja faɗa a tsakanin ku a ranan? Wanda kowa ya san ku masoya ne meyasa kuma a ranan kuka yi baram-baram? Hakan na nufin kai ne ka kashe ta kenan?"
"Ya me Shari'a Barrister ya dena kausasa kalaman sa ga ABUL KHAIRI, hakan zai zamo barazana a gare sa har ya faɗa abinda ba shi ne ba". Mamy tafaɗa lokacin da ta tashi a fusace, domin sosai zuciyar ta ke ƙuna tana jin baƙin ciki da abinda ke gudana ga ɗan nata, ko kaɗan ta kasa control ɗin kanta, wanda hakan ba halin ta bane, amma bata san meyasa yau take matuƙar jin haushi ba, ƙiri-ƙiri tana gani ana son laƙaba wa ɗanta kisan kai, wanda hakan yasa ta kasa jurewa
"Ka kiyaye Barrister, sannan kaima ABUL KHAIRI ka amsa wa kotu tamboyin da yake maka, domin shirun ka na nufin raini ne ga kotu". Cewar Alƙali yana kallon ABUL KHAIRIN
Shiru dai ABUL KHAIRI yayi be ce komi ba
Hakan yasa Brr. Sharif yace masa, "muna sauraron ka, wani saɓani kuka samu?"
Daƙyar ya buɗe baki ya soma sanar musu da abinda ya faru sanda yake Office, text ɗin da aka yi masa da kuma hotunan da aka tura masa, wannan yasa ya isa gidan gonan sa har suka samu saɓani da Ziyada, kuma ya yanke alaƙar su tare
Alƙali yace, "ina buƙatar wayan sa yanzu domin bincika gaskiyar zancen sa".
ASP ya miƙe ya sanar da cewan, "ya me Shari'a wayan sa ta samu matsala sakamakon faɗin da tayi a ranan da muka je kama sa ya saki wayan, yanzu haka tana office".
"To ya kamata a kai gyara domin tabbatar da abinda yake faɗa a zama na gama". Cewar Alƙalin
Brr. Sharif yace, "ya me girma me Shari'a ABUL KHAIRI zai iya shirya wannan ƙaryan ne domin ganin babu idon Marigayiya, kuma babu ta yanda za'a yi a tambaye ta, shiyasa ya shirya wannan ƙaryan da son laƙaba mata sharrin fasiƙanci, wanda kuma shi ne mutumin da yake tare da ita a ko da yaushe, Ziyada bata da wani saurayi da take kula wa sai shi, kuma iyayen ta sun tabbatar da hakan, abun mamaki koda aka kai ta asibiti a sanda abun nan ya faru, likitoci sai da suka yi binciken gawan ta, inda suka gano tana ɗauke da ciki, ta mutu tare da cikin ABUL KHAIRI, shi ne kaɗai take mu'amala dashi kuma cikin nasa ne, yana son kawai ya zame kansa ne tare da ƙulla mata sharri".
Nan kotu ta hautsine da surutu, inda Alƙali kuma ke ta faman rubutu, sai da ya ɗago ya tsawatar musu kana yace da Brr. Sharif, "shin kana da shaidan hakan?"
"Eh ya me Shari'a, a bani damar gabatar da doctor ɗin da ya duba ta domin jin cikakken bayani daga bakin sa".
"Kotu ta baka dama".
"Na gode ya me Shari'a". Yafaɗa cikin girmamawa
Inda Maga-takarda ya miƙe yayi kiran doctor ɗin
"Kotu zata so jin cikakken sunan ka, da kuma bayani gamsashshe game da binciken da kuka yi a kan gawan Ziyada?". Brr. Sharif ya faɗa hakan sanda yake gaban Doctor
"Suna na Dr. Aliyu Mu'awiyah, Ni ne likitan da nayi bincike a kan gawan Marigayiya Ziyada Alh. Muh'd Iyaal, mun gano tana ɗauke da ciki a jikin ta har na tsawon watanni uku, ga kuma bayanan". Doctor ɗin yayi wannan furucin yana miƙa takardun hannun sa ga Barrister
Amsar takardun Brr. Sharif yayi, yaje ya miƙa aka ba wa Alƙali, shi kuma sai da ya gama duba wa kana yace, "idan Brr. Khadeejah tana da tambayar da zata yiwa Doctor zata iya gabatar wa".
Brr. Sharif koma wa yayi ya zauna
Ita kuma ta tashi ta nufi inda doctor yake, fuskar ta babu walwala ko kaɗan jin ƙazafin da ake son ƙara liƙa wa ɗanta, "kana da tabbacin cikin jikin ta na ABUL KHAIRI ne? Wani shaida kake dashi da zai tabbatar da hakan?"
Shiru Doctor Yayi don be da tace wa
Sai Brr. Sharif ya miƙe yace, "ya me Shari'a be kamata Barrister tayi wannan tambayoyin ba, domin kuwa an tabbatar da cewar ABUL KHAIRI kaɗai shi ne saurayin Ziyada, kuma iyayen ta sun tabbatar min da haka, babu wanda ya taɓa zuwa wajen ta illa shi, don haka wannan cikin nashi.."
Katse shi tayi cikin fusata da faɗin, "ya me Shari'a babu ta yanda za'a yi a tabbatar da cikin nan nashi ne don kawai shi kaɗai ne saurayin ta, kamar yanda ABUL KHAIRI ya faɗa an turo mishi hotunan ta da na wani, dole hakan zai tabbatar mana da cewan tana tarayya da wasu ba tare da sanin iyayen ta ba.."
Shima Brr. Sharif ɗin amshe maganar yayi da zafin rai yace, "ya me Shari'a Barrister Khadeejah tana ƙoƙarin dole sai ta laƙa wa Ziyada sharri ne, tunda har iyayen ta suka tabbatar da cewan ba ta mu'amala da kowa, dole cikin nan nashi ne, Ziyada ba ta fita ko ina sai da yardan iyayen ta, kuma daga makaranta sai makaranta, taya za'a ce tana mu'amala da wasu mazan ba tare da sanin iyayen ta ba?".
Kallon sa Mamy tayi cike da baƙin ciki, zata yi magana sai Alƙali ya buga musu gudumar sa
"Ya isa haka, Barrister Sharif zaka iya zama, ka bar ta tayi tambayoyin ta suna bisa kan tsari".
Zama yayi cike da takaici
Wanda hakan kuma ya sanyaya wa Mamy rai, sai ta mayar da hankalin ta kan Doctor tace, "Ina jinka Doctor, ya aka yi ka san cewa cikin jikin ta nashi ne?"
Doctor yace, "gaskiya Ni ban sani ba, amma dai bincike ya nuna mana tana da ciki a jikin ta".
"Good, to babu ta yanda za'a yi ku bincika cikin na wane ne? Ai ana yin gwajin NDA ko?"
"Eh akwai halin yin hakan, sai dai matsalan tun farko ba muyi hakan ba, kuma ga shi babu yanda za'a yi a dawo da gawan ta. Kuma dai an fi yin hakan bayan haihuwa ne".
Murmushi Mamy tayi, kana ta juya ga Alƙali tace dashi, "ya me Shari'a wannan ƙazafin cikin da ake son liƙa wa ABUL KHAIRI, basu da wani shaidan da zai tabbatar cikin sa ne, duk da an san cewa shi kaɗan ne saurayin ta, amma babu wanda ya san ko tana mu'amala da wasu mazan a ɓoye ko kuma ba ta yi? Don haka ya me Shari'a ayi duba da rashin hujja da basu dashi, a wanke ABUL KHAIRI daga zargin shi ne wanda yayi mata ciki, na gode ya me Shari'a". Ta koma wajen zaman ta ta zauna
Alƙali yayi rubutu kana ya ɗago yace, "kotu tana buƙatar Brr. Sharif ya kawo ƙwararan shaidu da suka ga lokacin da ABUL KHAIRI yake mu'amala da Ziyada, wanda hakan ne kawai zai tabbatar wa da kotu shi ne yayi mata ciki, idan babu, to, kotu tayi watsi da zancen". Sai kuma yaja fasali yaci gaba da cewa, "zamu ɗaga sauraron wannan Shari'an zuwa nan da sati biyu masu zuwa". Sai ya buga gudumar sa
Mutanen kotun suka tashi suna me giramama sa
Yana fita ƴan sanda suka tasa ƙeyan ABUL KHAIRI suka yi waje dashi
Mamy na tsaye tana kallon sa idanun ta sun cika taf da hawaye
Abba ne ya zo wajen da take, ya dafa kafaɗan ta
Hakan yasa ta juyo tana kallon sa, wanda hawayen ta suka sami damar zubo wa
Shima ƙarfin hali yake yi, ya sakar mata murmushi don ƙara mata ƙwarin gwiwa yace, "kin yi ƙoƙari Addan mu, Allah ne zai fito dashi insha Allahu, baza mu sare ba kinji? Ki dena zubar da hawayen ki yanzu lokacin juriya ce". Daga nan hannun ta yaja suka yi wajen su Ummu
Babu wanda ya samu halin magana har suka fito, haka haraban kotun ya cika da jama'a, har da ƴan jarida suna ɗiban labarai
Kai tsaye Abba wajen motan su ya nufa da Mamy, ko kaɗan be bari ƴan jarida sun yi mata tambayoyi ba. Suka shige motocin su suka yi gida, kai tsaye gidan su Abba suka wuce gaba ɗaya har su Alh. Sunusi.
Bayan sun isa, a nan ne Alh. Sunusi ya sake ƙarfafa wa Mamy gwiwa, ya kuma musu nasiha tare da fatan alheri, kana suka wuce shi da Hajiya Falmata
Su ma su Umma Salamatu basu daɗe ba suka tafi gida, sai kuma ranan da za'a sake zaman kotu
Haka ma su Ummu bayan sun huta sosai, sai suka wuce gidan mahaifiyar su Hajiya Mama, inda a nan za su kwana washe gari su koma garin su, su ma sai ranan da za'a sake zaman kotu na biyu za su sake zuwa.
Su Batool bayan sun gama koke-koken su, da alhinin ganin yayan nasu, sai suka shiga kichen don ɗaura musu abincin dare
Inda kuma Mamy da Abba suka ci gaba da tattaunawa a palon, Abba yana sake tausan ta tare da ƙara mata ƙwarin gwiwa
Ajiyan zuciya Mamy ta saki, tana share ƙwallan da suka sake cika mata idanu, ta kalle sa tace, "yanzu Ni Abban su zuciya ta rawa take yi sosai, ina ga kamar baza muyi wani nasara ba, babu wani shaida da nake dashi da zan tabbatar ba Baba na ne yayi kisan kan nan ba, ni kaina ban yi tunanin za mu iya tsallake yau ba".
"Haka ne, amma ai Allah shi ne ya san dai-dai, kuma shi muke roƙo, idan har ABUL KHAIRI ba shi ne yayi kisan kan nan ba, Wlh sai ya fita, tunda Allah ya baki ƙwarin gwiwar gudanar da Shari'an nan yau har kuma kika yi nasara, to insha Allahu shi zai taimaka miki, amma dole ki yi bincike ta fannin yarinyan, ya kamata ki gano ƙawayen ta da kuma waɗanda take mu'amala dasu don samun shaidu sosai, ta hakan ne ma zaki gano idan tana mu'amala da wasu maZan".
Jinjina kai Mamy tayi cike da gamsuwa, tace, "insha Allahu zuwa gobe zan fita in bincika, amma Abban su abinda ke raina yanzu shi ne, yanda zan gano yarinyan da take shiga gidan ABUL KHAIRI, wacce ta yiwa me gadin gidan ƙaryan cewa ita ƴar uwan Baba na ne".
Gyara zama sosai Abba yayi yana kallon ta, yace, "akwai wacce take zuwa gidan sa ne?"
"Eh haka me gadin yace min, ta taɓa zuwa gidan ta nemi ya barta ta shiga, ita ƙanwar Baba na ne, to ya bar ta ta shiga, kuma yace min a ranan da suka yi faɗan ta sake shiga gidan, shi ne shigar ta na ƙarshe".
"To idan ko haka ne, ya zama dole ki gano ko wace ce, shin wa kike zargi?" Abba yace hakan yana kallon ta
Numfashi taja kana tace, "Ni ina zargin Azeeza ce, domin tun sanda ta zo gidan nan kwanakin baya, naji tayi wasu maganganu wanda ya tabbatar min da cewan tana son ABUL KHAIRI, wannan ya ɗarsa min zargin tabbas ita ce zata bi shi har gidan gonan sa, kuma yanda me gadin ya fasalta min ita, dai-dai da Azeeza ce".
Shiru Abba yayi na ɗan soconni, kana yace, "to yanzu ya zamu yi idan ita ce?".
Mamy tace, "abinda ke raina kenan Abban su, Azeeza baza ta yarda ta zo kotu ba ko da kuwa mun gano cewar ita ce ta shiga gidan, idan ma da akwai abinda ta sani duk da ba na zargin ta da ita ce ta aikata, kuma ban san ma yanda za'a yi in gano ita ce ta shiga gidan ba ko ba ita ce ba, iyayen ta baza su taɓa yarda da abinda zan je musu ba, ka san halin su".
"Haka ne, tabbas akwai rikici, yanzu dai ki je kiyi sallah tunda ana kira, idan na dawo masallaci zan faɗa miki hanyar da zamu ɓullo wa al'amarin, idan ma ita ce dole za'a gane".
Daga haka Abba miƙe wa yayi ya wuce Toilet ɗin parlour'n don ɗauro alwala
Inda Mamy ta miƙe itama ta wuce kichen tana ce ma su Maimuna, "su bar girkin su je su yi sallah tukunna, kafin su dawo su ci gaba". Tana faɗa musu hakan ta wuce ɗakin ta
Su ma ɗaki suka wuce don bin umarnin ta.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 24*
*________* Ana jibi za'a koma COURT, ƴan sanda suka isa gidan su Azeeza suka ƙwamuso ta, iyayen ta basu san hawa ba basu san sauka ba aka zo aka tafi da ita, ita kuwa da tasan laifin ta tuni ta tsure sai kuka take yi tana roƙon iyayen ta da, "kar su bari a tafi da ita, wlh ba ita ce tayi kisan ba". Amma haka ƴan sanda suka tasa ƙeyan ta suka wuce da ita
Kai tsaye police station aka wuce da ita
Babu jima wa sai ga Mamy ita da me gadi sun je, lokacin da me gadin ya ganta sai ya tabbatar musu da cewa, "ita ce tazo gidan ABUL KHAIRI".
Numfashi Mamy taja kafin tace wa me gadin, "to zaka iya tafiya Malam Iro, amma zuwa jibi ka tabbatar da ka zo court domin bayar da sheda kaji?"
"Insha Allahu Hajiya zan halarta".
Bayan tafiyan sa sai Mamy ta nemi ganin Azeeza, har inda aka ajiye ta ta shiga, amma duk yadda taso Azeeza tayi mata bayanin ko ta san wani abu? Ta ƙi cewa komi illa kuka da take tayi, hankalin Mamy ya tashi matuƙa, "kar dai ace ita ce tayi kisan?" Babu yadda ta iya haka ta fice ta koma office ɗin Asp Shazali, inda ta tambaye shi, "ya labarin gyara wayan ABUL KHAIRI?"
Yayi mata bayanin, "sun gyara, kuma duk sun bincika akwai bayanan da ya faɗa a kotu, sannan kuma Abun mamaki Numban da aka kira su dashi ranan da aka sanar musu da kisan, shi ne dai aka kira shi dashi a ƙarshen call ɗin da yayi, kuma sun samo inda aka yi register da layin amma sun je basu samu me shagon ba, an tabbatar musu cewa wajen sati Uku kenan da barin sa wajen, be sake dawowa ba".
Jinjina kai Mamy tayi, kana kuma tace, "Asp idan babu damuwa nima ina son ka bani Numban, sabida ina son nayi bincike a kai, sannan ina son sanin wajen".
"Babu damuwa ai, bari in rubuta Miki". Nan ya rubuta mata address ɗin da Numban ya bata
"Amma don Allah ina neman alfarma, don Allah kar ku taɓa wannan yarinyan idan har taƙi muku bayani, kawai ajiye ta za ku yi har zuwa ranan shiga kotu, na san yanzu a tsorace take, duk wani abinda ta sani zata yi bayanin sa a kotu, kuma ba wai ina zargin ita ce tayi kisan ba, amma hakan zai iya yiwuwa, abinda yasa nace ku taimaka min wajen kamo ta, sabida na san ko na buƙaci ganin ta baza ta zo ba, amma yanzu iyayen ta za su ɗauka ku ne kuka kama ta".
"Ok Barrister, insha Allah baza muyi mata komi ba".
Sallama taya masa ta tafi.
Tana isa gida ta tarar da Uncle Sani yana ta jaraba wai, "a kan me za su saka ƴan sanda su kama mishi ɗiya? ai duk abinda ke faruwa ya sani, ɗan su yayi kisan kai amma ana son liƙa wa ɗiyar su, kuma wlh idan basu sako mishi ƴar shi ba sai sun ga abinda sai biyo baya". Jaraba dai kala-kala haka yake sauke musu a gida
Abba na jin sa be ce mishi komi ba, kuma be hana sa ba
Mamy na shigowa ya koma kanta, fata-fata yayi mata, tana ba shi haƙuri amma ko sauraron ta ya ƙi yi, sai da ya gaji don kansa kafin ya tafi ya bar su.
Sosai Mamy ta shiga damuwa, dama ga shi ba shiri suke yi ba har yanzu, tun sanda ta bar gidan Uncle Sanin, ya tabbatar da ya rasa ta har abada lokacin da ta auri Abba, shikenan jituwa yayi ƙaranci a tsakanin su, duk alkhairin da Mamy zata yi musu ba sa ganin hakan, gaba ɗaya ya ɗauki karan tsana ya ɗaura mata, haka ma matar sa Umma Sulaima, ita wannan kishi ne yayi mata yawa, har yanzu gani take yi Uncle Sani na son Mamy, shiyasa ta tsane ta sosai.
Umma ( Mahaifiyar Uncle Sani) ita dai duniya ta koya mata darasi, shiyasa tayi sanyi yanzu, duk sanda Mamy tazo gidan tana amsar ta hannu bibbiyu, a ɗakin ta ma take sauka. Mamy tana da haƙuri shiyasa har yanzu take bibiyan su duk da ta san ba sa ƙaunar ta, duk wani abinda ya faru baya ta manta dashi, ita so take yi su ƙulla zumunci sosai, tunda su ne dangin mahaifin ta, su kaɗai ke gare ta, baza ta so su raba hanya ba, ga shi yanzu abinda ya biyo baya na maganar ABUL KHAIRI, duk da shawaran da Abba ya bayar amma sai da saɓani ya sake shiga tsakanin su, wanda ba hakan ta so ba, tunda ga shi ƴan sanda suka kamo Azeezan amma Uncle Sani ya zo gidan su yana tijara, a ganin sa su ne suka kama ta.
Yanda Mamy ta tayar da hankalin ta ne, dole Abba ya koma bata haƙuri da tausar ta, domin faranta masa rai haka ta nuna masa babu komi ya wuce.
*RANAR SHIGA COURT*
Yau ma duk ƴan uwa da abokan arziƙi sun hallara a court ɗin, inda ta cika maƙil ko ta ina, ga ƴan jarida a gefe suna jiran su samu na yaɗawa. Su Uncle Sani wannan karon har da su sun biyo sahun ɗiyar su.
Bayan Alƙali ya zauna a kujeran sa, sai kowa ya koma ya zauna ciki girmamawa
Asp Shazali shi ya fara gabatar da wayan ABUL KHAIRI, inda yayi musu bayanin duk abinda ke ciki, sannan ya miƙa aka ba ma Alƙali
Alƙali bayan ya duba ya tabbatar da abinda ABUL KHAIRIN ya faɗa gaskiya ne
Asp Shazali ya ƙara da faɗin, "ya me Shari'a har yanzu muna kan binciken layin da aka kira mu dashi ne, kuma bamu samu wani abu akai ba, sannan mun gano cewa Numban da aka yi kiran ABUL KHAIRI aka tabbatar masa da kisan, shi ne wanda aka yi amfani dashi wajen kiran mu aka sanar mana". Sai ya duƙar da kansa cikin girmamawa kana ya koma ya zauna
Bayan Alƙali ya gama rubuta bayanan, sai ya ɗago kai ya ce da lauyoyin, "idan akwai me magana a cikin ku zai iya fara wa".
Mamy ta miƙe tace, "ya me Shari'a zan so kotu tayi duba da bayanan da Asp Shazali ya kawo, ta gane cewa ABUL KHAIRI ba shi ne yayi kisan kan nan ba, wani ne daban yayi sannan ya laƙaba masa, bincike ya nuna tabbas kiran sa aka yi aka sanar masa, kuma kotu ta tabbatar da hakan tunda ga shaidu nan, sannan ina son in gabatar da sheda ta ta gaba wanda zai nuna cewa text ɗin da aka yi masa tare da hotunan da aka turo masa gaskiya ne, hakan zai bamu damar gane tabbas Ziyada tana tarayya da wasu mazan bayan ABUL KHAIRI".
"Kotu ta baki dama". Alƙali ya faɗa yana me kallon ta
"Na gode ya me Shari'a, ina son a gabatar min da Rahina Sulaiman".
"Rahina Sulaiman idan tana nan ta fito". Cewar Maga-takarda
Rahina dake zaune cikin mutanen kotun, ta miƙe ta nufo gaban kotun
Mamy ƙarisa wa kusa da ita tayi tace, "zan so ki gabatar da sunan ki a gaban kotu domin kowa yaji, da kuma alaƙar ki da marigayiya Ziyada".
"Suna na Rahina Sulaiman, kuma Ni ƙawa ce kuma Aminiya ga Ziyada".
"To a zaman ki da ita zaki iya sanar damu halayyar ta, ina nufin mu'amalar ta da samari? Da kuma yawan samarin nata? Shin ABUL KHAIRI shi ne kaɗai saurayin ta ko kuma akwai wasu wanda kika sani?"
Shiru Rahy tayi tana kallon mutanen wajen, sai kuma tace, "eh saurayin ta ɗaya ne Ni dai dana sani wato ABUL KHAIRI, kuma tunda muka taso muna tare da ita har girman mu, ban taɓa ganin ta da wani saurayi ba, domin soyayyar da take ma ABUL KHAIRI shi ne silan da yasa ba ta iya kula kowa, tunda ta sha ce min ABUL KHAIRI yana da kishi a kanta, kuma muddin ya ganta tare da wani zai iya rabuwa da ita, wanda kuma hakan yasa ta dena kula kowa sai shi kaɗai".
Mamy tace, "kina nufin har ta mutu bata da wani saurayi sai shi?".
Cikin sanyin murya tace, "a'a kafin ta rasu tayi saurayi guda ɗaya wanda take kulawa ba tare da sanin ABUL KHAIRI ba, wanda shi ne ABUL KHAIRIN ya ganta tare dashi a hoto".
Murmushi Mamy tayi, domin abinda take son ji kenan, "to ki faɗa mana alaƙar dake tsakanin su? Kina da masaniyar hotunan da aka turo masa?"
Rahina cike da ƙwarin gwiwa ta gyaɗa kanta, domin ta ɗau alƙawarin bayyana gaskiya saboda ta kuɓutar da ABUL KHAIRI, baza ta so a kama shi da laifin kisan kai ba a yanke masa hukunci ba tare da ya aikata ba, tana son sa kuma tana ganin wannan damar ne kaɗai zai sa ta mallake sa tunda babu Ziyada a duniyar, idan har ya samu damar kuɓuta daga sharrin da aka yi masa, to, ta hakan ne zata same shi ya zama nata, shiyasa sanda Mamy tazo wajen ta domin jin ta bakin ta, ta yanke shawaran faɗan gaskiya ba tare da ta ɓoye ba. Ɗago kai tayi ta kalli inda ABUL KHAIRI ke tsaye, sai hawaye ya cika mata ido saboda tausayin sa da taji ya tsarga mata...
"Rahina muna sauraren ki, kiyi mana bayani da bakin ki yanda zamu fahimta". Mamy ta katse mata tunanin ta
Ajiyan zuciya ta sauke kana taci gaba da faɗin, "Saleem shi ne saurayin da Ziyada take mu'amala dashi a ɓoye ba tare da sanin kowa ba, illa Ni da nasan komi, kuma babu shakka cikin jikin ta nasa ne domin bata taɓa mu'amala da kowa ba sai shi, abinda yasa hakan kuwa saboda ABUL KHAIRI ya ƙi bata wannan damar, ya ƙi yarda su aikata zina har sai idan sun zama mallakin juna, wadda ita kuma ta kasa jure wa har hakan yake kawo saɓani a tsakanin su, wannan dalilin ne yasa tazo waje na neman shawaran yanda zata yi". Shiru tayi tana share hawayen fuskar ta, sai kuma taci gaba. "Ni ce na bata shawaran ta ƙulla alaƙa da Saleem ba tare da sanin ABUL KHAIRI ba, tunda shi yana da kishi kuma idan yaji zai iya rabuwa da ita duk son da yake mata, Ni kuma wannan damar nake so domin raba su". Sai ta ɓarke da kuka ta kasa ci gaba da maganar
Gaba ɗaya kotun tsit yayi kowa na sauraron abinda Rahinan ke faɗi
"Muna sauraron ki Kici gaba". Mamy tafaɗa tana kallon ta
Cikin shashsheƙan kuka tace, "Tun sanda na ɗaura ido na a kan ABUL KHAIRI nake matuƙar ƙaunar sa, sai dai ko kaɗan be taɓa min kallon yanda nake masa ba, nasha nuna mishi hanyoyi da dama domin ya gane soyayyar da nake masa, amma be taɓa nuna min wani alama da ya gane manufa ta ba, ban sani ba ko be gane bane ko ya gane nufi na nuna min ne kawai bazai yi ba ko a'a da gasken dai be gane bane? Amma haka naci gaba da tusa kaina wajen sa duk saboda ina ƙaunar sa, sai dai ganin ba na gaban sa Ziyada ce kaɗai yake iya mata kallon soyayya, sai zuciya ta ta soma bani shawara yanda zan yi in raba sa da Ziyada domin Ni na shiga zuciyar sa, wanda na rigada na gane muddin akwai Ziyada a tare dashi, to, Ni bani da sauran amfani a wajen sa, bazai taɓa kallo na a matsayin masoyiya ba, wannan dalilin ne yasa sanda Ziyada ta nemi shawara a waje na sai naga na samu damar raba su ta hanya me sauƙi, sai na bata shawara tayi mu'amala da Saleem a ɓoye ba tare da sanin sa ba, sannan kuma nabi duk hanyar da zan bi domin ganin na samu hujjojin da zan iya nuna wa ABUL KHAIRI domin ya yarda da taci amanar sa, shiyasa nake bibiyan su duk inda suka je ina ɗaukar su hotuna, kuma na tura masa tare da text a kan, "Ziyada tana cin amanar sa ba tare da sanin sa ba". Wanda Ni nasan cewa dole ne sai ya rabu da ita, domin na san halin sa sosai na kishin da yake dashi, to, a ranan da abun ya faru haƙana ya cin ma ruwa, domin a ranan ne Ziyada ta zo gidan mu cikin tashin hankali tana kuka sosai, take sanar dani duk faɗan da suka yi dashi, Sosai labarin da ta bani ya faranta min rai, amma yanda ta nuna min tayi nadama tana son koma wa ta bashi hakuri sai hankali na ya tashi, na san soyayyar da ke tsakanin su me girma ne, zai iya yiwuwa ABUL KHAIRI ya yafe mata muddin ta nuna nadamar ta, sai na zigata na hana ta koma wa, shawara ta tayi amfani a ranan, domin bata koma gidan sa ba, amma kuma ta kasa jurewa zuwa washe gari ashe ta koma ba tare da ta sanar min ba". Numfashi taja idanun ta jage-jage da hawaye. "Wannan shi ne iya abinda na sani, kuma ta sila ta suka samu saɓani".
Alƙali ɗauke idanun sa yayi a kanta, inda ya ci gaba da rubutun sa
Ita kuma Mamy ta koma ta zauna
Alƙali ɗago da kansa yayi yace, "Barrister Sharif kana da tambayoyin da zaka yi mata ne?"
"A'a ya me Shari'a".
"Ok Barrister Khadeejah kici gaba da gabatar da shedar ki idan kina dashi, ke kuma zaki iya koma wa ki zauna". Ya ƙare maganar da kallon Rahina
Tashi Mamy tayi tace, "ina son gabatar da sheda ta ta gaba Malam Iro".
Malam Iro ya fito gaban kotu
Inda Mamy ta ƙarisa tayi masa tambayoyi kamar yanda tayi masa sanda taje gidan gonan ABUL KHAIRI
Be rage daga bayanan da yayi mata ba a wancan lokacin, haka ma yanzu ya sake maimaita wa
Sannan Mamy tace, "tana son zata gabatar da Azeeza Sani Bala".
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 25*
*________* ƙarisawa inda take Mamy tayi, sannan ta kalle ta tace, "Azeeza zan so ki yiwa kotu bayanin abinda yake kai ki gidan gonan ABUL KHAIRI ba tare da sanin shi ba?"
Ɗan jim Azeeza tayi kanta a ƙasa, sai kuma ta buɗe baki a hankali tace, "ina zuwa ne domin sa".
"Kamar ya domin sa? Kiyi bayani ne sosai yanda kotu zata fahimce ki".
Cikin muryan kuka Azeeza tace, "wlh Allah ba Ni ce na kashe taba, hasali ma Ni gawarta nazo na tarar a gidan".
Gyara tsayuwar ta Mamy tayi jin abinda ta faɗa, sai tace, "Azeeza ki kwantar da hankalin ki ba wai an ce ke ce kika yi kisan ba, abinda kika sani kawai nake son ki sanar da kotu, sannan me yake kai ki gidan gonan shi?"
Shashsheƙa ta soma yi, daƙyar ta buɗe bakin ta tayi musu bayanin abinda yake kawo ta, da kuma zuwan da take yi tana ganin ABUL KHAIRI tare da Ziyada, wannan dalilin ne yasa itama ta yanke shawaran ta bashi kanta domin ta same shi kamar yanda Ziyada take yi, a ganin ta hakan zai jawo hankalin ABUL KHAIRI ya so ta itama. Shiru tayi a wannan gaɓar sanda kukan yaci ƙarfin ta
Tsit kotun yayi ana sauraron ta
Sai da taja soconni kafin taci gaba da faɗin, "sai kuma ranan da na dawo na uku sanda ban tarar da Me gadi ba, na shiga gidan kai tsaye nabi ta ƙofa, na je da ninyan in nuna masa videon dana ɗauke su a lokacin da suka yi faɗa, idan be yarda da buƙata ta ba Ni kuma zan kaiwa iyayen sa su ga abinda yake aikata wa, sai kuma ina shiga na ga gawan Ziyada a cikin parlour'n, na ruɗe sosai har ban tsaya ba na fito da gudu na fice a gidan, kuma a lokacin ne na hangi motan ABUL KHAIRI shi kuma ya taho gidan, iyakan abinda na sani kenan".
Kotun yamutse wa da hayaniya suka yi
Sai da alƙali ya dakatar dasu sannan aka natsu, yace da ita, "yanzu ina wayan taki?"
Hannu tasa ta share hawayen fuskar ta da yayi caɓe-caɓe tace, "yana gida".
"Ina buƙatar yanzu aje a taho da wayan nata". Sai kuma ya kalli Mamy yace, "zaki iya ci gaba".
Daga nan Sagir aka kira, wanda shi ne ya bada shedan halayyar ABUL KHAIRI da kuma soyayyar su da Ziyada, ya ƙara da cewa, "duk da na san Ziyada ƙanwa ta ce amma bazan iya ƙala wa aboki na wannan mugun sharri ba, aboki na yana matuƙar ƙaunar ta, ba zai taɓa iya kashe ta ba, tabbas ba shi ne ya kashe taba domin ko ba ita ba bazai iya kashe ƙuda ba bare masoyiyar shi".
"Da haka nake roƙon wannan kotu me adalci ta wanke ABUL KHAIRI daga zargin da ake yi masa a kan shi ne ya kashe Ziyada, wannan ba gaskiya bane, duba da ƙwararan shedu da aka gabatar wanda ko ta wani fanni an tabbatar da cewa ABUL KHAIRI ba shi da laifi, na gode ya me Shari'a". Cewar Mamy tana juya wa ta zauna
Barrister Sharif Alƙali yace, "idan yana da abinda zai ce ya tashi ya gabatar".
Sai cewa yayi "be dashi".
Alƙali bayan ya gama rubutu ya ɗago kai yace, "zamu ɗaga wannan Shari'an zuwa nan da sati ɗaya tunda har yanzu ba'a gano wanda yayi kisan ba, don haka lauyoyi suna da daman da za su je su sake kawo ƙwararan shedu, sannan kuma a tabbatar a ranan an kawo mana videon da Azeeza ta ɗauka domin ganin abinda suka faɗa da idon mu, a kuma ci gaba da tsare ABUL KHAIRI har zuwa ranan". Sai ya buga guduma ya miƙe tsaye
Daga nan kowa tashi yayi aka soma fice wa. Wannan zaman ya yiwa masoyan ABUL KHAIRI daɗi sosai, duk da ba sakin shi aka yi ba, amma hakan ya tabbatar musu da cewan ba shi ne yayi kisan ba.
Washe gari Mamy shirya wa tayi tabi address ɗin da aka bata na shagon me siyar da Simcard, tana zuwa ta ga shagon har yanzu a rufe yake, sai na maƙocin shi dake buɗe, ƙarisa wa tayi tayi masa sallama
Ya amsa yana kallon ta
Tace, "bawan Allah don Allah me shagon nan nake nema?" Ta nuna shagon kusa dashi
"To gaskiya Hajiya nima ban san inda yake ba, saboda nima jiyan nan na dawo daga tafiya, wata na biyu kenan ba na gari sai yau na buɗe shago".
"To da Allah baka san inda ya tafi ba? Ko kana da labarin wani abu game dashi, ko da inda zan same shi ne don Allah?" Mamy tafaɗa tana kallon sa
Shiru yayi na ɗan soconni, yayi kamar yana tunani sai kuma yace, "wlh Hajiya babu inda zan ce miki zaki same shi tunda shi dama ba ɗan nan anguwan bane, ƙauyen su yana can... Me ma yake da suna?" Ya ɗaga kai yana ɗan buga yatsar sa a kan gefen goshin sa. "na manta Hajiya".
Mamy tace, "don Allah ka tuna ka taimaka min abu ne me muhimmanci shiyasa nake neman sa".
Duk yanda ya so ya tuna ɗin amma ya manta, sai ya kalle ta yace, "wlh Hajiya na manta, garin nasu da wahala, domin sau ɗaya ya taɓa faɗa min".
"To amma in tambaye ka? A nan Kanon ne ko kuma a wani gari yake?"
Yace, "a nan Kano yake, sai dai daga ƙauyaku ya taho".
"To babu damuwa, bari in baka number na idan ka tuna sai ka kira Ni ka sanar min, don Allah kayi min wannan alfarman".
"To shikenan insha Allah zan yi ƙoƙari".
Wayan sa ya ciro ya kwashe Numban ta da ta karanto mishi
Sannan tayi masa godiya tare da yin masa alheri ta wuce.
Kai tsaye gida ta koma, Abba na Parlour shi da su Batool suna hira.
Sannu da zuwa suka yi mata
Inda ta zauna tana amsa musu tare da zame gyalen ta
Maimuna ta tashi ta ɗauko mata ruwa
Ta amsa ta sha tana amsa tambayar da Abba yayi mata, "a'a Abban su wlh ba'a dace ba, sai dai muna sa rai insha Allah". Nan ta sanar mishi da komi abinda ya faru
Abba yace, "to Allah yasa a dace, Allah ya bayyana gaskiya, baza mu gaji da roƙon Allah ba".
"Amen amen". Duk kan su suka amsa
Mamy tace, "ya kamata Aƙilu ya je ya dawo da su Amir gida tunda an koma school tun wancan satin, ya kamata ku koma school gaba ɗayan ku". Ta ƙare maganar da kallon su Batool
Batool ɗin ne tace, "a'a Mamy don Allah ki bari har a gama Shari'an nan, wlh ko mun je baza mu mayar da hankalin mu ba".
Kallon ta tayi Mamyn tace, "ƙaniyar ki Batool! Ku koma makarantan ki ce baza ku koma ba? Kin san ranan gama Shari'an ne?"
Zumɓuro baki kawai tayi bata ce komi ba
Abba yace, "ai muna sa ran insha Allah wannan zaman da za'a yi shi ne na ƙarshe, ko da ba'a gano wanda yayi kisan ba dole su sake shi tunda bashi da laifi".
"Haka ne Abban su. Amma Ni dai na faɗa muku ku san da sani gobe zaku je school".
Maimuna ce kawai ta amsa
Ban da Batool da take ta zumɓura baki gaba, sai kuma ta kalli Abba tace, "Abba ka saka baki mana Mamy ta bar mu zuwa Monday".
"Allah Batool zan zane ki ba na son rashin hankali, kin san dai yanzu ina ji da kaina ne kar ki saka in ci ƙaniyar ki".
"A'a baza ayi haka ba ke kuma kar ki huce min a kan yara, ban san ki da wannan ɗabi'an ba, Batool Maimuna gobe ku shirya ku je school kuna ji na?"
"Eh Abba". Suka amsa shi su duk ka biyun
"Yauwa ƴaƴan albarka, yanzu ke Maimuna je ki sanar wa Aƙilu ya je ya ɗauko su Baby".
"To Abba". Ta amsa shi tana tashi tsaye ta wuce
While Batool tuni tabi bayan ta itama ta ficeWar ta
Girgiza kai kawai Mamy tayi tana tashi ta wuce ɗaki
Yayinda Abba ya ɗauki remote yana sanja channels.
Washe gari da yamma sai ga kiran me shagon nan da Mamy ta bashi number, ya sanar mata da sunan ƙauyen da ya tuna
Sosai tayi masa godiya cike da murna, da Abba ya dawo ta sanar masa an dace.
The next day bayan su Batool sun dawo school ta shirya ta wuce ƙauyen
Koda ta isa da tambaya ta gane gidan sa, ta shiga da sallama
Matar dake tsakar gidan ta amsa mata tana mata lale marhabun
Fuskar Mamy da murmushi ta ƙariso ciki
Tabarma ta shimfiɗa mata tana cewa, "zauna Hajiya zauna".
Zama Mamy tayi sannan matar itama ta zauna, sai suka sake gaisuwa sosai
Mamy tace, "dama wajen Mijin ki Sadau nazo".
"To Allah yasa dai lafiya?" Matar ta tambaya tana kallon Mamy da mamaki
"Lafiya lau wlh, don Allah idan yana nan ki faɗa mishi yayi baƙuwa".
shiru matar tayi har yanzu idanun ta a kan Mamy, sai kuma ta kaɗa kai kamar ƙadangaruwa tace, "bari in Kira miki shi yana ɗaki ne yana barci".
"To na gode".
Koda matar ta dawo sai ta dawo da ruwan sha, ta ajiye mata a gaban ta tana faɗin, "ga shi nan zuwa, ga ruwa Ki sha".
Mamy godiya tayi mata, kafin ta ɗauki ruwan ta ɗan sha kaɗan gudin kar tace ƙyamar su take yi, duk da hankalin ta be kwanta da ruwan ba
Sosai kuwa matar taji daɗi, ganin yanda Mamy bata nuna ƙyamar su ba ta sha ruwan gidan su a matsayin ta na ƴar gayu
Lokacin ne Sadau ya fito yana hamma, ganin Mamy sai ya bi ta da kallo kafin yace, "ke ce baƙuwar tawa Hajiya?"
"Eh Ni ce".
"To sannu da zuwa amma ban waye ki ba?". Yayi maganar cikin fara'a
"Haka ne, amma idan babu damuwa zan so in yi maka bayanin kai na". Mamy tafaɗa tana kallon sa
Jinjina kansa yayi kafin ya kalli Matar tashi yace, "bamu wuri Kande". Sannan ya ƙarisa ya zauna a saman turmin dake kusa da inda Mamy ke zaune
Ita kuma tuni Kanden ta wuce madafa kasancewar dama girki take yi.
Gyara zaman ta Mamy tayi tace, "suna na Barrister Khadeejah Yunusa Ubale, idan babu damuwa don Allah ina so kayi min bayani a kan wani layi da aka zo aka siya wurin ka, kuma kai ne kayi registern Numban a ranan".
"Amma Hajiya Ni ya zan yi in san waɗanda suka siya layi a wuri na har nayi musu register? Ni wajen wata ɗaya kenan rabo na da zuwa birni buɗe shago".
"Eh haka ne naji labarin hakan wajen me shagon kusa da kai, amma ai na san da dalilin rashin zuwan ka, kuma ina maka maganar tun wancan watan ne aka siyi layin, ka ga kuwa a wurin ka aka siya".
Zazzare idanu yayi yana share zufa yace, "amma Hajiya mene ne alaƙa ta da ke da har zaki zo min gida nema na? Ni ban ga abun da nayi ba".
Murmushi Mamy tayi tace, "ba wani abu bane ya kawo Ni wajen ka ba Malam Sadau, idan har zaka bani haɗin kai zan yi maka tambayoyi ne kaɗai in tafi, in kuma ka fi son ƴan sanda su yi maka tambayoyin fine babu matsala, saboda yanzu haka neman ka suke yi shiyasa ka gudu".
Shiru yayi har yanzu zufa na keto masa, sosai cikin sa ya ɗuru ruwa
Mamy jakar ta ta buɗe ta ciro Numban da aka rubuta a cikin takarda, "na san kana da bayani a kai da kuma ranan da aka siya, don haka kayi min bincike".
"Ai Hajiya ba sai ma nayi bincike ba tunda na san wanda ya siya layin, kuma sanadin hakan na baro aiki na tsawon wata ɗaya da satikai yanzu". Sai da ya ɗan goge fuskar sa kafin yace, "Alal haƙiƙa wani ne yazo ya siya Simcard a wuri na har nayi masa register, bayan kwana biyu sai ya dawo ya bani kuɗi har dubu ɗari yace min in bar buɗe shago har na wani lokaci, sabida idan har naci gaba da buɗe wa tabbas da yiwuwar ƴan sanda za su zo su kama Ni, kuma ko da sun tambaye Ni bayani a kanshi bazan san shi ba, don haka yake bani shawara in Yi abinda yace min. To, Ni kuma gaskiya na tsorata a tunani na shi ɗin ɗan kidnapping ne za'a bi diddigin inda ya yi registration azo a kama Ni, wataƙil ma ace har dani tunda na san yanzu abubuwa sun ci gaba, abu kaɗan ne zai saka a san inda ya siya layin, sai na amshi kuɗin da yayi min tayi a ranan na kulle shago na na dawo ƙauyen mu, daɗin da naji ma ba'a cikin gari nake ba kuma babu wanda ya san inda nake sai me shagon kusa dani, shima sau ɗaya muka taɓa hira dashi har na faɗa masa inda nake, a tunani na bazai iya tunawa ba ma tunda abun ya daɗe, wlh iya abinda na sani kenan kar ki daɗa kar ki raga". Ya ƙare maganar kamar zai yi kuka duk ya gama haɗa gumi yana faman fifita da hannayen sa
"Idan muka je can da kai zaka iya gane shi?"
"Taya zan gane shi Hajiya bayan sau biyu na taɓa ganin shi? Kuma ban san ma inda zan ganshi ba a halin yanzu, mutum daga zuwa siyayya wuri na sai azo ana titsiye Ni?"
"Ba maganar titsiye ka bane bawan Allah, idan har ka taimaka kamar kayi jihadi ne domin ta sanadin ka za'a kama wanda yayi kisan, kuma na tabbata shi wanda ya siya Simcard ɗin a hannun ka shi ne wanda yayi kisan". Cewar Mamy cikin kwantar da murya
"Innalillahi... Kisa kuma? Hajiya don girman Allah ki fitar dani a wannan maganar wlh ban san inda yake ba, ki yiwa Allah ki yiwa Annabi".
Ganin ya ruɗe sosai sai Mamy ta sake kwantar da murya tana cewa, "don Allah Mlm Sadau ka kwantar da hankalin ka, ba wani abu bane nace zaka bi Ni can saboda ka ba da shaida ne, Ni ko baka je kotu ba na san zaka iya cin karo da mutumin, ka ga idan ka nuna min shi shikenan aikin ka ya ƙare, nayi maka alƙwari zan ruɓa maka abinda ya baka har sau biyu".
"To Hajiya amma ke taya kike ganin zan ganshi? Garin Kano fa ba ƙaramin gari bane?"
Shiru Mamy tayi tana tunani, sai kuma tace, "to shikenan na gode, amma don Allah idan da hali zan dawo zan iya neman ka".
"To.. to babu damuwa, nima na gode". Ya faɗa yana me yaƙe haƙora
Sallama suka sake yi har da matar shi, sannan ta fice tahau motan ta ta wuce gida, a ranta duk tunani ya cika ta, "waye to wannan mutumin da yayi kisan? Taya zata iya gane shi? Ya zata yi ta fitar da ABUL KHAIRI a wannan zargin da ake mishi? Ta tabbata duk wanda yayi kiran shi ya sanar masa da kisan, sannan kuma ya kira ƴan sanda tabbas shi ne wanda yayi kisan. Kuma da ikon Allah sai tayi iyakan bakin ƙoƙarin ta."
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 26*
*________* Mamy har ta kusa isa gida sai kuma ta juya kan motan ta ta koma ƙauyen nan, tana yin parcking shi kuma Sadau ya fito
Ganin ta sai ya tsaya nan bakin ƙofar gidan har ta fito ta same shi
"Malam Sadau nayi mantuwa ne, idan babu damuwa ina son kayi min kwatancen yanayin mutumin don Allah, hakan zai sake taimaka min ƙwarai".
"To shikenan bari in kwatanta miki shi, Mutumin dogo ne kuma yana da kauri, don zan iya ce miki kamar fasalin jiki na, kuma baƙi ne shi yana da yawan gashi a fuskar sa, amma ba ya barin gashi sosai a kanshi, sannan gashin giran sa sun haɗe waje ɗaya, iyakan abinda zan iya faɗa miki kenan gaskiya, amma dai gaskiya ɗan gayu ne sosai".
"To amma a mota yazo wurin ka?"
"Eh a mota yazo wuri na, sai dai motan da yazo dashi sanda ya siya Simcard a wuri na daban ne da wanda ya dawo yace dani na gudu nabar buɗe shago na ɗan wani lokaci".
"Yi min bayani don Allah wani irin mota ce? Ya kuma sunan su?"
"Hajiya wlh ban san sunan motocin ba, Ni dai na san motan farko baƙa ce, sai kuma ta biyun kalan ruwan goro ce me ɗan fatsi-fatsi".
Numfashi Mamy taja kafin tace, "Nagode sosai da bayanan ka Sadau Allah ya saka. Ga wannan ka ƙara na gode".
Washe baki yayi ya amshi kuɗin jikin sa na rawa shima yana bin ta da godiyar
A haka Mamy ta wuce tahau motan ta taja ta koma gida, tana shiga cikin parlour'n da sallama
Baby ta soma ganin ta ta ruga aguje ta rungume ta tana mata sannu da zuwa
"Yauwa Auta na".
Shima Amir yayi mata sannu da zuwan
Ta amsa tana shirin tambayar sa su Batool sai ga su sun fito daga kichen a tare
"Mamy sannu da zuwa". Cewar Maimuna tana amsar Jakar ta
Itama Batool tace, "Oyoyo Mamy sannu da dawowa".
Duk amsa musu tayi kafin ta tambaye su Abban su?
Baby tayi saurin cewa, "Mamy yanzun nan suka fita shi da Yaya Sagir".
"Ok to sake Ni inje ɗaki".
Sakin ta tayi sai dai tabi bayan ta tana faman tsalle tana cewa, "Mamy tsaraba na".
"Auta ba anguwa naje ba, aiki naje yi kin ji".
Shagwaɓa ta soma mata tana bin ta duk inda tayi a ɗakin
Bata kula ta ba har sai da ta zauna tana janyo computern ta, ganin zata takura mata sai tace, "je ki wajen Maimuna ta baki sweet a cikin na school ɗin ki, yi maza ki je".
Ai kuwa da gudu ta fice, ganin basu a Parlour sai ta nufi kichen
Suna ciki kuwa suna girkin dare, ita Maimuna ne take girkin, while Batool ta zauna a kujeran Robber tana latsa waya tana bata labarin abin dariyan da ta gani cikin group ɗin *MATA ADON GARI* na facebook, dariya suke yi duk su biyun
Baby ta faɗo da gudu cikin kichen ɗin, wajen Maimuna ta nufa tana sanar mata da saƙon Mamy
"Me bakin kwaɗayi ke ko? Sai na yanka bakin wlh". Cewar Batool tana hararan ta
Ita kuwa sai cinno mata baki tayi tana sosa goshin ta
While Maimuna na dariya bata ce komi ba
Batool ta sake cewa, "to uban wa kike cinno wa baki? Wuce dalla idan mun fito sai ta ɗauko miki".
Kuka take shirin yi domin har ta fara murza ido zata fara
Sai Maimuna ta riƙe mata hannu tana cewa, "A'a Autana kar kiyi kuka kinji ƙyale wannan Auntyn naki, Bari in gama wannan sai muje in baki ko?"
Gyaɗa kanta tayi tana cire hannun nata a idon, sai kuma ta soma tsalle-tsalle a dole sai ta gano abinda Maimunan take yi, dayake tsawon ta bazai kai ta hango abinda ke cikin tukunyan ba
Dariya Batool dake kallon wayan ta takwashe dashi
"Ke kuma dawa?" Maimuna ta tambaye ta tana juyo wa tana kallon ta
"Wlh labarin nan ne ya bani dariya, wai fa wata ce tayi tambayar wai, "shin maza suna shagwaɓa ne?" Shi ne wani ya bata amsa. "Sai kin ɗaura shi a kan Nono zaki ga zahiri".
Dariya Duka suka saki daga ita har Maimunan, inda Maimunan take cewa, "halan a Twitter ne?"
"Wlh kuwa. Bari ma kiji wani, wata ce tace, "dama azumi 300 ake yi". Sai wani ya bata amsar, "da yanzu duk zuri'ar ku kiristoci ne".
Nan ma dariya suka sake kwashe wa dashi
"Wlh sai kin ma gaji da jin irin wannan rainin hankalin, bari dai mu fita duk ki gani a zahiri, kwanaki ma naga an yi posting ɗin su ai a wani group ..Sirrin ƴa mace.. a facebook, wata ce tayi wai tana neman posting ɗin twitter tayi missing shi ne ake ta turo mata, baki ga yanda na sha dariya ba ranan kina barcin nan, na so in tashe ki amma sai na ƙyale ki, sai kuma wannan matsalan ta Kunno Kai na Ya ABUL shi ne ya mantar dani".
Murmusawa kawai Maimuna tayi tana kakkaɓe hannayen ta da ta gama ɓare Maggi ta zuba a girkin, sai kuma tace, "Ai group ɗin nan ina son shi ana ƙaruwa sosai wlh".
Batool zata yi magana sai ɓarin da Baby tayi ya katse ta, tace, "wannan yarinyan ba kya ji wlh, dama yaushe zaki zauna haka nan baki yi ɓari ba, dalla fice a nan".
Kuka ta fashe dashi zata fice a guje
Sai Maimuna ta riƙe ta tana cewa, "kiyi shiru ƙyale ta kinji? Mu je in baki sweet ɗin". Sai kuma ta kalli Batool da ita har ta mayar da idanun ta kan wayan ta domin ya ɗauke mata hankali. "Batool ɗan kwashe min albasan nan don Allah kafin in dawo."
Batool bata kula ta ba don ma ba ta ita take yi ba
Ita kuma Maimunan tuni ta fice riƙe da hannun Baby.
Suna shiga ɗakin su shi kuma Abba ya shigo da sallama
Amir dake kallo ya amsa mishi yana mishi sannu da zuwa
Amsa shi yayi ya wuce ɗakin Mamy, sallama yayi ya shiga
Mamy ta amsa shi tana ɗago kai daga latsa computern da take yi, sannan tayi mishi sannu da zuwa
Ya amsa yana zama kan kujera yace, "agogo Sarkin aiki".
Murmushi Mamy tayi tace, "Ayya Abban su yanzun nan na fara fa, ban daɗe da dawowa ba aka ce min kun fita".
"Eh wlh, Sagir ne yazo gaishe mu, shi ne kuma nace ya raka Ni wani waje. Amma an dace ko?".
Gyara zaman ta sosai tayi tana fuskantar sa sai tace mishi, "Eh naga mutumin kuma mun tattauna dashi, amma Abban su akwai wanda ya tambaye ka game dani a yau ɗin nan?"
"Kamar ya ban gane ba?" Yayi maganar shima yana kallon ta
"Ina nufin a game da aiki na, ko akwai wanda ya tambaye ka inda naje ko ci gaban da ake samu?"
Shiru Abba yayi na ɗan wani lokaci, sai kuma yayi dariya yace, "kai ku dai louyoyin nan sai a hankali, yanzu kuma wani abun zaki gano kenan?"
Itama dariyan tayi kafin tace, "ai Abban su ba na son wani ya san inda naje ne da abinda nake yi ne saboda tsaro".
"Haka ne kuma, nima na san da wannan ai, sai dai babu wanda ya tambaye ni, duk da dai mun yi waya da Abbas yau kuma mun tattauna a kan matsalan, ya tambaye Ni ci gaban da ake samu amma ba muyi maganar zancen ki na zuwa ƙauye dubo inda aka siya layin nan ba, sai kuma Sagir yanzu da yazo gaishe mu yake tambayar ki, shi ne nace mishi kin fita, amma ban sanar mishi ga inda kika je ba".
Ajiyan zuciya Mamy ta sauke, sannan ta mayar da idanun ta kan computern ta, sai dai ba aikin taci gaba da yi ba illa faɗa wa zuzzurfan tunani da tayi
Sai da Abba yayi magana har sau biyu bata ji ba, kafin ana ukun ta ɗago kai tana kallon sa
"Me kace ne Abban su?" Ta tambaye sa stiil tana kallon sa
"Wannan tunanin me kike yi haka? Anya ba kya takura wa kanki? Yanzu daga magana har kin faɗa tunani me zurfi haka?"
"Kayi haƙuri dan Allah wlh wani abu nake tuna wa".
Ɗan tsira mata ido yayi, sai kuma yace, "to faɗa min abinda ya faru da kika je ƙauyen".
Nan ta faɗa mishi komi
Sai shima kawai yayi shiru yana me faɗa wa tunani
Dama ta san hakan zai faru, abinda ke ranta dole shima zai kawo hakan, bata ce komi ba dai ta tashi ta shige Toilet, kamar mintuna biyar ta fito tana nufan computern ta ta rufe
"Amma wa kike zargi?" Abba yayi maganar yana kallon ta
Sai da ta zauna kafin tayi ajiyan zuciya tace, "Abban su har yanzu dai tunani na be bani wanda nake zargi ba, ni kaina abin yana ɗaure min kai wlh, na rasa ya zan yi, amma kai da wanda kake tunani ne?"
"Eh akwai wanda ya faɗo min a rai, duk kwatancen nan da mutumin nan yayi miki dai-dai ne dashi, amma taya zai kasance shi ne?"
"Wa kake zargi Abban su?" Tayi maganar cikin zaƙuwa da ji
Murmushi yayi yace, "ki bari don Allah hasashe ne". Sai ya tashi yana ci gaba da faɗin, "bari inje akwai inda zan je, zuwa dare zan dawo insha Allah".
"To amma baza ka faɗa min ba?"
"Idan na dawo zamu yi maganar kinji? Domin akwai shawaran da nake so in baki". Yayi maganar yana kallon ta tare da gyara wa hulan sa zama
"To shikenan sai ka dawo".
Fita yayi ya bar ta cikin tunani, ta jima a wurin ita kanta bata san iya lokacin da ta ɗauka ba tana faman tunani, sai da taji kiran sallan magriba kafin taja numfashi fuskar ta cike da damuwa ta tashi ta wuce Toilet don ɗauro alwala.
_Please kuyi haƙuri da wannan, kaina ke ciwo wlh daƙyar nayi muku._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 27*
*________* *COURT*
Yau ma kotun cike maƙil da mutane, inda aka soma gabatar da Shari'a cikin tsari. Wayan Azeeza aka soma kunna bidiyon da tayi musu aka saurara
Bayan an gama sai Brr. Sharif ya tashi yace, "ya me Shari'a kamar dai yanda muka saurari wannan videon ne, tabbas a ciki ABUL KHAIRI yayi iƙirarin sai ya kashe Ziyada, kuma ga shi ya cin ma burin sa, don haka ya me Shari'a ina so ayi duba da wannan kalaman nasa a yanke mishi hukunci nan take sabida shi ne ya kashe ta. Na gode ya me Shari'a". Sai ya koma ya zauna
"Brr. Khadeejah ko kina da wani shaidar da zaki iya gabatarwa?"
"Eh ya me Shari'a". Tafaɗa tana tashi tsaye
"Ok muna sauraron ki".
"Ya me Shari'a ina son a gabatar min da Malam Sadau Aliyu".
"Idan Malam Sadau na kusa ya fito".
Fitowa yayi ya tsaya
Mamy kuma tazo dai-dai wajen sa ta tsaya tana cewa, "Malam Sadau kotu zata so ta san abubuwan da ka sani game da lokacin da aka zo aka siya Simcard a wurin ka?"
Gyara tsayuwar sa yayi sosai kafin ya soma ba da bayani tiryan-tiryan kamar yanda ya sanar wa Mamy
Bayan ya gama sai Mamy tace, "ya me Shari'a ina so in gabatar da shedata ta gaba wanda Sadau zai tabbatar mana da shi ne wanda ya siya Simcard a wurin sa. Sagir Alh. Muh'd Iyal".
"Sagir Alh. Muh'd iyal ya fito".
Sagir dake cikin mutane tun kiran Sadau da aka yi ya soma zufa, gaba ɗaya fuskar sa ta jiƙe da zufa, be taɓa tunanin asirin sa zai tonu lokaci ƙanƙani haka ba, don haka ya ma kasa fito wa kanshi na duƙe. Sai da aka sake maimaita sunan shi kafin ya samu ya fito jikin sa a sanyaye
"Sadau wannan shi ne mutumin da yazo wurin ka ya siya Simcard?"
"Eh tabbas shi ne wanda yazo ya siya, kuma ya dawo yayi min barazanar barin wurin zuwa nan da ɗan wani lokaci".
Jinjina kai Mamy tayi zuciyar ta babu daɗi, ta kalli Sagir ɗin tace, "zaka iya mana bayanin abinda ka sani?"
Hannun sa dake rawa ya saka a fuskar sa yana sharce gumin sa, daƙyar ya iya buɗe baki yace, "ban san komi ba game da abinda kuke magana akai, hasali ma lokacin da abun nan ya faru ba na nan ina wurin aiki na".
Murmushin takaici Mamy ta saki tana jin idanuwan ta na son ciko wa da hawaye, sai ta juya ga Alƙali tace, "Ya me Shari'a Sagir shi ne wanda ya kashe ƴar uwan sa Ziyada, kuma shi ne wanda muka kama dumu-dumu da kiran layin ABUL KHAIRI da police ya sanar musu da kisan kan bayan ya aikata ya gudu, shi ne yayi ƙoƙarin laƙaba wa ABUL KHAIRI bisa hujjar sa mara tushe, ina roƙon kotu da ta tursasa shi ya faɗi gaskiya".
Alƙali sai da ya gama rubutu kafin ya ɗago yana kallon Sagir yace, "ka sanar mana da abinda ka sani kar ka wahalar da mu, domin muddin aka gano gaskiya kotu zata tuhume ka da ɓata mana lokaci da kayi, muna jin ka ka sanar mana da abinda ya faru tun kafin ƴan sanda su yi bincike akai, idan ba kai kayi kisan ba taya ka sanar musu cewa an yi kisan?"
Tsit kotun tayi suna sauraron abinda zai faɗa
Inda shi kuma jikin sa na rawa sosai duk ya fita hayyacin sa wanda zai sa ka gane be da gaskiya, kuma dubun sa ta cika da be yi zaton hakan ba, haƙiƙa yau yana nadamar abinda ya aikata, be san da wani ido zai kalli iyayen sa da mutanen da suka san shi ba...
"Muna sauraron ka". Cewar Alƙali
"Ziyada ƴar uwa ta ce kuma na taso da ƙaunar ta tun muna yara, sai dai abin baƙin cikin tun sanda na kawo Aboki na ABUL KHAIRI gidan mu ya ganta sai ya nuna yana son ta, itama hakan ne a wurin ta, inda suka ƙulla soyayya ina ji ina gani bayan tarin soyayyar da nake mata, wanda na tabbata Aboki na ya san da hakan amma be nuna min ba, kanshi kawai ya sani a wannan lokacin, Ni kuma hakan yasa na ɓoye tawa soyayyar da zummar in cire ta a zuciya, but hakan ya gagara, kullum zuciya ta tana gaya min hanyar da zan bi don ruguza tasu soyayyar domin samun Ziyada a matsayin mata ta, wanda har na je wa iyaye na da maganar amma suka nuna in aje zancen gefe tunda mahaifin ta ba yanzu zai mata aure ba, duk sanda aka tashi sai su nema min auren ta, duk wani alaƙar dake tsakanin ABUL KHAIRI da Ziyada na sani saboda yana sanar min be ɓoye min komi, wanda Ni kuma hakan ke matuƙar ƙona min rai nayi iya ƙoƙari na wajen na hana sa domin kishin da nake yi dashi, a kullum sai na riƙa faɗa masa rayuwar da suke ɗauka a matsayin wayewa su daina hakan haramun ne, wanda Ni kuma ina yin hakan ne domin ya dena shiga gona ta. kwatsam sai na gano cewa Ziyada tana tarayya da wani bayan ABUL KHAIRI, ta rigada ta sallama kanta gare shi, sai abin yayi min ciwo matuƙa har na tafi gida neman ta domin in nuna mata soyayya na kuma in CE mata Ni kaɗai ne wanda ya kamata ya keta ta ba wani ba, amma ban cid da ita ba, sai na wuce kai tsaye gidan gonan ABUL KHAIRI wanda na san a can zan same ta, a waje na bar mota na na shiga ba tare da sanin me gadi ba. Sanda na shiga tana zaune a Parlour, Bata Yi tunanin komi ba ta tarbe Ni da fara'a, amma hakan be sa abinda nake ji a kanta ya ragu ba, domin sosai naji zafin sallama kanta da take yi a wurin wani na mijin. Kai tsaye na nuna mata idan har hakan take so Ni zan iya mata sabida ina matuƙar ƙaunar ta, tayi mamakin zantuka na har ta ruɗe lokaci ɗaya da ta san na san abinda take aikata wa, amma cewa da nayi sai dai ta dawo waje na in maye mata gurbin wancan. Sai tace, "sam ita bata taɓa ɗauka na a matsayin wanda zata iya aura ba, ta ɗauke Ni a matsayin Yaya ne wanda muka fito ciki ɗaya, kuma ABUL KHAIRI kaɗai zata iya aura". Share hawayen sa yayi kafin yaci gaba da faɗin, "naji zafin maganganun ta ƙwarai domin ban zata zata ƙi Ni haka ba, inda zuciya ta ja Ni naso nayi amfani da ita ta ƙarfi da yaji, amma ita taƙi yarda tana kuka a kan, "in ƙyale ta baza ta taɓa tarayya dani ba domin Ni Yayan ta ne," Ni kuma ban saurare ta ba, haka muka yi ta tirka-tirka a kan dole sai na cin ma buri na, wanda tsautsayi ya ja Ni na ɗauki wuƙa domin in Yi mata barazana, amma kuma sai ta buga hannu na garin ƙwatan kanta na caka mata wuƙan ba tare da sani na ba". Kuka ya fashe dashi a sanda yazo nan a zancen sa. "Haƙiƙa nayi nadamar abinda na aikata a wannan lokacin duk da ba'a son Raina bane, Amma tsautsayi ya ja Ni na aikata abinda zai zo ya rusa min gaba ɗaya rayuwa ta, na rasa ya zan yi ne shiyasa na bar gawan a nan na fita jiki na na rawa, babu wanda ya gan Ni shiyasa na yanke shawaran kawai in Kira ƴan sanda in sanar musu bayan na kira ABUL KHAIRI ya je gidan, hakan zai sa kawai su kama shi a matsayin wanda yayi kisan, ina da tabbacin ABUL KHAIRI bazai taɓa ganin gawan Ziyada ya barta haka ba ba tare da ya taɓa ta ba, wannan ne zai sa kawai duk wani abinda za'a iya zargi na ya goge".
Gaba ɗaya kotun ta ruɗe da hayaniya, iyayen Ziyada kuwa kuka sosai suke yi da jin asalin labarin, wanda suka raina tun yana ƙarami shi ne ya zama makashin ƴar su ɗaya tilo da suke matuƙar so? Haƙiƙa yau suna dana-sanin abinda suka aikata a gare shi, da basu kawo shi gidan su ba da duk hakan be faru ba
ABUL KHAIRI kuwa dake tsaye da hand cuff a hannu, idanun sa a ƙasa sai tsiyayar da hawaye yake yi, sosai abinda Sagir ɗin ya faɗa ya matuƙar girgiza shi, hawayen kawai da yake zubar wa su suke rage masa raɗaɗin da yake ji a ransa.
Sai da Alƙali ya buga gudumar sa kafin suka yi shiru, inda ya ɗauki lokaci yana rubutu kafin ya ɗago yace, "a bisa hujjojin da aka gabatar da kuma amsa laifin shi da Sagir yayi, kotu ta wanke ABUL KHAIRI da zargin kisan kan da ake mishi. Shi kuma Sagir kotu ta yanke mishi hukuncin kisan kai ta hanyar rataya bayan an yi masa horo me tsanani". Sai ya buga gudumar sa yana miƙe wa
Haka kotun suka haɗa baki wajen faɗin, "koooootuuuuuu". Kowa na miƙe wa
Inda ka ga ahalin ABUL KHAIRI kowa murna yake yi tare da godiya ga Allah da yau ya nuna musu wannan ranan
While shi kuma yana tsaye a wurin da yake ya lumshe idanuwan sa hawayen ciki suna ci gaba da kwaranya, bazan iya faɗa muku irin baƙin ciki da ɗacin da yake ji a zuciyar sa ba, duk da a wani gefe yana me farin cikin wanke shi daga zargin da ake mishi, yau ya sami free a matsayin sa na wanda ake tuhuma da kashe rai.
gefe ɗaya kuma mutane sai Allah wadai da halin Sagir suke yi, gaba ɗaya kotun ta hargitse da hayaniya, ana fita ne ma tamkar ba a yi
Iyayen Ziyada sai kuka suke yi musamman Mom ɗin ta, haka shima iyayen Sagir ɗin, duk kunya ya cika su ga dangi ta ko ina.
Su Abba dai tuni sun tarkata sun fice tunda aka kwance ABUL KHAIRI, basu tsaya hira da ƴan jarida ba suka yi gida, gaba ɗaya gidan ya cika maƙil saboda masu taya su murna, ƴan uwa da abokan ariziƙi har da maƙota sai shigowa suke yi
Lokacin itama Zee mijin ta ya kawo ta, cikin ta ya tsufa sosai haihuwa ko yau ko gobe, tare da mutanen gidan mijin nata suka zo taya su murna
Dole su Ummu suka tashi suka ɗaura girki tunda ga su su da ba yanzu za su tafi ba ma, baza a zauna haka nan ba.
Lokacin su Maimuna su ma suka dawo school, suka cidda wannan daddaɗan labarin. Lokacin ma ABUL KHAIRIN yana ɗaki har yayi wanka an ba shi magani sabida zazzaɓin da ya rufe shi, dayake dana barci shi ne ya samu barcin ya ɗauke shi.
Da ake mayar da zancen ne su Maimuna suka ji wanda yayi kisan, ai sai Batool ta tashi tsam ta shige ɗakin su
Tana shiga ta faɗa kan gadon ta ta soma kuka sosai, domin ba kaɗan ba hankalin ta ya tashi da jin Sagir ɗin ta ne wanda yayi kisan, shikenan ita kuma baza ta taɓa cika burin ta ba? Wanda take matuƙar ƙauna tun tasowan ta shi ne ya aikata wannan mummunan aika-aikan, shikenan ta rasa shi har abada, taya zata iya rarrashin zuciyar ta Bayan ta gama sallama ta gare shi? Shiyasa ta kasa jure wa ta gudu ɗaki take wannan uban kukan tana toshe bakin ta da filo
Maimuna ce ta shigo ɗakin domin tuɓe uniform ɗin ta ta koma cikin ƴan uwa, don bata san ma Batool ɗin ta taso a wurin ba tunda bata lura ba, tana shigowa ta ganta a haka tana kuka, da sauri ta ƙarisa wajen ta ta zauna cike da tashin hankali take tambayar ta, "abinda ke damun ta take kuka?" Gaba ɗaya ta gama ɗaga hankalin ta ganin Batool ɗin a haka
Ita kuma Batool tashi tayi tana share hawayen ta amma wasu suna zubo wa, zuciyar ta na ƙuna daƙyar tace, "ban san ya zaki kalli zancen nawa ba Maimuna, ban san wani irin fassara zaki yi min ba. Wanda aka kama da kisan kai ya laƙaba wa Yayan mu shi ne yau nake kuka domin shi, ina kuka ne domin na rasa shi gaba ɗaya a rayuwa ta Maimuna". Ta ƙare maganar tana me sake fashe wa da kuka
Da sauri Maimunan ta saka hannu ta janyo ta jikin ta wanda har nata idanun sun soma tsiyayar da hawayen tausayin Batool ɗin, kasancewar ta me tausayi da damuwa da damuwar wani, bubbuga bayan ta ta hau yi kafin tace, "idan na fahimce ki Batool kina nufin kina son Yaya Sagir ne?"
Gyaɗa mata kai tayi tana ci gaba da kukan ta
"Kiyi haƙuri haka ƙaddaran ki take, Allah zai musanya miki da wanda ya fi shi, don Allah ki dena kuka kinji kar wani yazo ya ganki a haka?" Sai ta ɗago ta kuma tana share mata hawayen yayinda nata kuma suke zuba. Bata barta haka ba sai da ta tabbatar ta kwantar mata da hankali wajen bata baki kafin suka tashi suka cire kayan su, sannan ita Maimunan ta fice don kar aji su shiru, daga nan ta duba idan an gama abinci ta zubo musu.
Sai yamma kowa ya watse a gidan, har su Ummu duk sun koma gida a yau ɗin, inda saura mutanen gidan ne kaɗai
Sai a time ɗin ne ma su Maimuna suka ga ABUL KHAIRI da ya fito za su yi sallama da su Ummu, shi ne ya zauna a dainning yake cin abinci, inda su kuma gaba ɗaya mutanen gidan suke Parlour suna ɗan taɓa hira
Sai da ya gama ne Abba yace mishi, "yazo ya zauna akwai maganar da za su yi".
Zama yayi a ƙasa yana duƙar da kanshi
Kowa tsit yayi suka mayar da hankalin su kan Abban da ya soma magana.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 28*
*________* Da faɗa Abban ya soma mishi, bayan ya gama ya ɗaura mishi da nasiha kafin kuma ya ƙara da faɗin, "daga yanzu an tsayar da ranan auren su shi da Maimuna nan da wata biyu me zuwa, tunda ya ga alaman aure yake so abinda yake aikata wa kenan, to, za su yi masa can ya ƙarata, abunda ya faru dashi sai ya zamar mishi izna, tunda a ganin shi yana saɓon Allah ne a ɓoye, sai ga shi da ya tashi kama shi ya tona mishi asiri ta inda ba ya zato".
Mamy itama sai da ta ƙara da nata Nasihan
Kafin Abba ya sallame shi
Haka ya tashi jiki babu ƙwari ya shige ɗakin sa
Su ma su Batool ɗin ce musu yayi, "su wuce su je su kwanta tunda suna da makaranta".
Haka suka tashi suka wuce ɗaki, ran Maimuna duk babu daɗi, shikenan ita kuma nata ya ƙare, dole dai sai ta auri ABUL KHAIRI, mutumin da ya tsane ta, shin ya zaman nasu zai kaya, gaba ɗaya ta kasa sukuni har sai da ta zubar da hawaye
Batool da ta kula da yanayin ta tun shigowar su ɗakin, ita ta matsa kusa da ita tana ta rarrashin ta, ta san haka ƙaddaran su yake, ita ga shi an haɗa ta da wanda ba ta so, ita kuma ga shi tana fama da son wanda be ma san tana yi ba, babu halin auren shi tunda yayi mata nisa, sai duk tausayin kansu ya kamata, amma kuma ta san Maimuna ta fi ta buƙatar a tausaya mata, dole ta ɓoye nata damuwar tana rarrashin ta.
Daƙyar dai a ranan suka samu barci ya sure su
Inda ita Maimuna ma har mafarkin ABUL KHAIRIN tayi, haka ta farka a firgice duk jikin ta ya jiƙe, barcin da bata koma ba kenan ta ɗauro alwala tana neman zaɓin Allah, a nan ta ƙarisa daren nata har zuwa kiran sallan asuba, sai da ta tashi Batool kafin ta tayar da Sallan.
Bayan sun gama suka sake kwanta wa na ɗan mintoci, sannan suka tashi suka fara aikin gida
Suna cikin yi ne itama Mamy ta fito ta soma taya su
Sun gama komi inda suka yi wanka suka shirya cikin uniform ɗin su, sannan suka karya suka fito suka tafi.
Shima Abba shirya wa yayi ya tafi wajen aikin sa
Ita Mamy dayake ta ɗau hutu, sai zuwa gobe zata je, shiyasa ta shige ɗaki ta kwanta don ta sake huta wa, bata yi yinƙurin tashin ABUL KHAIRI ba tunda ta san yana buƙatar hutu shima.
Bata sani ba ma shi ya rigada ya tashi tunda ya kasa barcin ma, damuwa ce cinkushe a ranshi, komi ya jagule mishi, ji yake yi kamar yayi ta kurma ihu sabida tsaban damuwar dake addabar shi, daga ƙarshe dai tashi yayi ya shiga Toilet yayi wanka, sannan ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya ya fito Parlour, jin shiru gidan sai ya wuce kanshi tsaye saman dainning, haka ya haɗa tea kaɗai ya ɗan kurɓa sannan ya koma Parlour, kanshi ya ɗaura a jikin kujeran yana me lumshe idanun sa, shiru yayi kawai yana ƙara nutso a cikin tunanin da ya addabi ruhin sa. Motsin da yaji shi yasa ya ɗago kansa yana me sauke kyawawan idanun sa da suka sake girma suka sanja kala saboda tsaban damuwa da rashin barci, kallo ɗaya zaka yi masa ka san ba ya cikin mood ɗin sa
Mamy da ta ƙariso ta zauna gefen shi, ta kalle shi tace, "Baba na lafiya kuwa? Me ke damun ka?"
Sai da ya ɗan saki numfashi kaɗan fuskar shi babu walwala yace da ita, "babu Mamy, ina kwana?".
Murmushi tayi tana shafa kanshi tace, "lafiya lau. Ya ka tashi?"
"Alhmadulillah".
"Kana saka damuwa a ranka ko? Me ke damun ka?"
Shiru yayi
Sai tace, "don Allah ka cire komi a ranka kaji? Duk abinda ya faru a rayuwar ka ƙaddaran ka ce, kuma ka ɗau komi cikin sauƙi don Allah ba na son kana saka damuwa a ranka, komi zai wuce ka manta komi, sannan maganar ka da Maimuna na san har yanzu ba son ta kake yi ba, amma da sannu zaka fahimci wace ce ita, zaka san cewa ita kaɗai tafi dace wa da kai, ita kaɗai ce zaka ji daɗin zama da ita, har yanzu baka fahimce ta bane, ka zauna kayi tunanin magana ta sannan ka koya wa kanka zama da ita, da sannu kaima zaka ƙaunace ta, Maimuna me sauƙin kai ce, duk yanda ka juya ta ta hakan ne zaku zauna".
Ɗan ɗago idanun sa yayi da suke cike da hawaye yana kallon ta, be iya cewa komi ba illa gyaɗa mata kai da yayi, duk da bakin sa yana son furta wa
Murmushi tayi tace, "Allah ya maka albarka, ka je kayi Breakfast Kar ka zauna da yunwa".
"Nayi". Ya faɗa a hankali
"Anya Baba na?"
"Allah kuwa". Yayi maganar cikin shagwaɓa
Dariya tayi tana jan kumatun sa tace, "har yanzu baka girma ba, ga shi har kana shirin ajiye iyali ko".
Shima murmushin yayi kaɗan yana ɗaura kansa a kafaɗan ta yace, "Mamy ai Ni a wajen ki yaro ne Ni har yanzu, kuma bazan taɓa girma ba".
"To ai na kusa huta wa tunda ga Maimuna zata amshe min wannan nauyin, sai dai ka riƙa mata".
Shiru yayi kawai be amsa ta ba
Itama sai ta sauya hiran nata don dai kawai ya saki jiki sosai yayi fara'a, haka tayi ta jan shi da surutu
Shima ɗin sai ya biye mata. Koda ta tashi ma shiga kichen raka ta yayi yana taya ta da ɗauko wannan da wancan, hakan sai ya mantar dashi kaso arba'in daga cikin damuwar sa.
Sai da suka gama ya wuce ɗakin sa ya kwanta tunda a lokacin barci sosai yake ji, dayake be yi ishashshe jiya ba, sai ya kwanta zuwa kafin a kira sallan azahar.
◾◾◾◾◾◾◾◾◾
Gadan-gadan aka tayar da ginin gidan da ABUL KHAIRI zai zauna, a cikin anguwan su filin yake, sai dai akwai ɗan tafiya sosai da gidan su, tafiyan mintuna goma sha biyar ne a mota zai kai ka
Abba shi ya ɗau nauyin komi yake mishi, dayake da kuɗi shiyasa komi yake tafiya cikin sauri
Gefe ɗaya kuma biki na ta ƙarato wa. Har yanzu Maimuna ko kallon arziƙi ba ta samu daga wurin ABUL KHAIRIN, shi manta wa ma yake yi ita ce wacce za'a haɗa su aure, sai idan ya ganta tunanin sa yake zuwa gare ta, sai ya dinga bin ta da kallo yana aiyana ta yanda zai iya zama da ita, sam bata dace da shi ba a ganin shi, kwata-kwata ba irin kalan matar da yake so bace ita, ba wai don kyau ba, tunda tana da kyan ta, kuma suna kama ma dashi sosai tunda duk kan su su Mamy suka biyo, dayake itama ta biyo Ummu ne, kuma Ummu da Mamy sak kamannin su ɗaya, tamkar tagwaye haka suke, shi dai ya fi son mace wayayyiya me shekaru kamar wacce ta shiga jami'a, Ziyada ce kawai dai tayi dai-dai da ra'ayin shi, har yanzu ya kasa manta ta, idan yana tunanin ta har zubar da hawaye yake yi, Allah be ƙaddara zai mallake ta ba, soyayyar ta ta rigada ta bi jini da tsokan shi, manta ta kuwa zai mishi wahala tsantsa, domin ya daɗe da mallaka mata zuciyar shi, be jin zai sake son wata bayan ita, ya ɗau auren nan ne tamkar ƙaddara wanda bazai iya guje mata ba, amma ba wai don jin daɗin ruhin sa ba.
◾◾◾◾◾
Ana saura sati Uku bikin ne Zee ta haihu ɗiya mace, inda aka yi sunan yarinyan aka sanya mata A'isha sunan mahaifiyar mijin ta, suna kiran ta da Iman
Su Batool can suka tare gidan ta saboda taya ta aikace-aikace, duk da akwai umma Salamatu dake zaune da ita tana mata wankan jego
A can ne ma Zee ɗin take yiwa Maimunan gyaran jiki, ita take koya mata duk wani kissa da zata janyo hankalin ABUL KHAIRI, tunda sun san ba ta gaban sa, zaman su sai an shirya
Duk kunyan Maimuna haka ta zage tana koyan komi da ake koya mata, tunda ta ɗau alƙawarin faranta ran mijin ta har ta dawo da hankalin sa gare ta, duk da har yanzu ba wai son shi take yi ba itama, amma kuma zuciyar ta ko kaɗan ba ta ƙinsa, ABUL KHAIRI yana ɗaya daga cikin mazajen da suke matuƙar burge ta, wanda tana jin zata iya zama dashi a matsayin mijin ta idan har za su zauna lafiya, shiyasa take ƙoƙarin ta ga ta karkato hankalin sa itama, har tana jin a ranta tana matuƙar ƙaunar auren, amma gefe ɗaya kuma tana tausaya wa kanta, tana ga kamar baza ta iya ba, sai dai yanda kowa ke ƙarfafa mata gwiwa ne yasa take dagewa, a ganin ta ai itama mace ce, zata iya jawo hankalin sa wata rana ya so ta.
Sai da satin bikin ya shiga kafin suka koma gida, inda gidan har ya soma cika da jama'a Masha Allah. Ana ta shagulgulan biki.
Har ranan auren da aka ɗaura musu aure, aka shaida ɗaurin auren Yunusa Hayat Sunusi (ABUL KHAIRI) da Amaryan sa Maimuna Naseer.
Dare na yi aka miƙa ta gidan mijin ta
Su Batool su ne amara ƙirjin biki, su da sauran ƙawayen su na school suke zaune da ita har sanda su ABUL KHAIRIN suka zo shi da Sulaiman Yayan Maimunan da shima ya zo bikin, sai dai zai zauna a gidan su Batool ne saboda burin iyayen su, tunda har an gaya mishi ana son haɗa su da Batool, shi kuma dama ra'ayin shi yana son ta, shiyasa yayi na'am da maganar nasu ya dawo gidan da zama tunda ya gama service ɗin sa, a nan zai zauna har ya jawo hankalin ta ya sami soyayyar ta.
Shiyasa da suka tashi tafiya shi ya kwashe su gaba ɗaya, ya mayar da sauran gida sannan suka wuce gida shi da Batool ɗin, tunda ya zo dama yake shige mata ita duk bata san yana yin hakan bane domin ya sami soyayyar ta ba, tunda ta san cewa suna ɗasawa da shi sun saba sosai idan ya zo gidan su, amma ta ga salon na yanzu daban ne, yanda yake nuna mata kula wa da kuma yanda yake shige mata, sai dai bata kawo komi dai a ranta ba.
_To ya zaman ABUL KHAIRI da Maimuna zai kaya? Ga dai su a gida ɗaya inda aka kawo mishi matar sa . Sai mu ce Allah ya sanya alheri._
_Afwan na san babu yawa kuyi manage, da babu ne nace gwara kaɗan ɗin._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 29*
*________* Gidan two bedroom ne ko wanne da Toilet ɗin sa, sai babban Parlour da Toilet da wurin dainning table, sannan sai kichen dake da babban store ɗin sa da aka cika mata maƙil da kaya, shi kanshi kichen ɗin abun kallo ne bare akai ga zuwa kyakykyawar parlour'n nata da ya ci kujeru har set biyu, sun yi matuƙar kyau sosai, kuma komi an saka mata kalan ruwan madara ne da coffee shiyasa komi ya bada kala kamar ka sace ka gudu, har ta ɗakin ta kalan ruwan madara da coffee ne, sai abubuwan da baza a rasa ba da suka kasance baƙi
Iyayen ta da su Abba sun yi ƙoƙari wajen sun cika mata kaya ko ta ina, komi sai dai ace Masha Allah tubarakalla.
Tunda su Batool suka fice a ɗakin take zaune a tsakiyar gadon ta tana jiran next abinda zai faru, duk da a tsorace take a wannan lokacin, shiru-shiru tana zuba idon ganin ABUL KHAIRI ya shigo saboda ta san ƙila zata ganshi, amma tsit kake ji daga ya je raka Sulaiman waje, har gyangyaɗi ya soma ɗiban ta bata motsa a wurin ba domin ba ƙaramin tsoro take ji ba ganin ta ita kaɗai babu kowa, ko ba komai tana son ganin ABUL KHAIRI domin zuciyar ta ta samu sukuni
Daga ƙarshe da barcin yaci ƙarfin ta ta ji shiru be dawo ba, sai ta ƙudundune kanta a saman gadon, da haka tana tunani tana gyangyaɗi har barcin ya sure ta gaba ɗaya.
*******
Shi kuwa ABUL KHAIRI tunda ya raka su Sulaiman bakin ƙofa sai ya rufe gidan shi ya wuce ɗakin sa kanshi tsaye, gaba ɗaya fuskar sa babu walwala jin sa yake yi kamar an ɗaure shi, jikin sa har rawa yake yi tsaban yanda yake ji a zuciyar sa
Wannan ranan da ya ci burin zuwan ta shi da masoyiyar sa, ita ce yau ta zo masa a bahagon yanayi, sai dai wata ba ita ba, mutuwa ta ɗauke mishi wacce yake matuƙar so da ƙauna; kuma yake fatan su kasance a inuwa ɗaya cikin rayuwar Aure, be taɓa tunanin ƙaddara irin wannan zata zo masa ba, yau ace ya auri wata ba Ziyada ba, haƙiƙa yau yana cikin baƙin ciki tsantsa, be san ya ya zai iya rayuwa da wata bayan ita ba, be san ta yanda zai ba wa zuciyar sa haƙuri har ta manta ta ba, ita kaɗai yake so a duniya, kuma ita ce kaɗai wacce zai so har ya koma ga mahaliccin sa, ba ya jin ko ɓurɓushin ƙaunar Maimuna a ransa, shiyasa bazai iya rayuwa da ita a matsayin matar sa ba, gwara su zauna a haka har sanda iyayen su za su fahimci zaman nasu su raba auren.
Haka ya kwanta a wannan daren a cikin mawuyacin hali, babu abinda yake yi sai mafarkin Ziyadan shi, yana kuma burin ace ko a mafarki ne su riƙa kasance wa tare har abada.
🔵🔵🔵🔵🔵
Washe gari da safe Maimuna ta tashi a makare, wuyan ta duk ya sanƙare sabida a yanda tayi barcin, daƙyar ta iya motsa wa har ta sauka a kan gadon, Toilet ta shiga ta soma ɗauro alwala ganin safiya tayi sosai, sai ta fito ta nemi Hijab cikin akwatunan ta da aka jera mata su a ɗakin
Sallah tayi har ta idar, kafin ta zauna nan tana lazimi, a lokacin ne har ta samu damar bin ɗakin da kallo, kawai sakin baki tayi tana bin ko ina da kallo, a ranta kuma tana mamaki da kuma farin cikin ganin duk wannan daulan ɗakin ta ne, me ya fi wannan daɗi?
Lumshe idanuwan ta tayi tana sake buɗe wa a lokaci ɗaya, a hankali ta tashi ta ninke sallayan ta ajiye, sannan ta fice don taga gidan, duk da a ranta tunanin ABUL KHAIRI kawai take yi, "ko ya shigo mata a jiya sanda tayi barci?" Shi ne bata sani ba, bata san ya zaman nasu zai kaya ba. Da wannan tunanin nata ta gama zagaya ko ina, ɗakin nasa ne kawai bata yi gigin shiga ba don zuciyar ta tuni ta kawo mata tunanin nan ne nashi ɗakin, sai ta koma nata ta cire hijabin jikin ta ta ninke ta mayar sannan ta fito ta wuce kichen, yunwa take ji shiyasa gwara ta nemi abinci ya fiye mata alkhairi
Abu me sauƙi ta haɗa, daga ruwan tea da ta dafa ta sake shi a flaks, sannan ta soya ƙwai biyu ta ɗauko bread duk ta Kai saman dainning, ajiye wa tayi ta zauna ta ɗiba ruwan zafin ta haɗa tea a Cup, ta sha da bread ɗin tare da ƙwan da ta soya.
Bayan ta gama ta gyara wurin, shima ABUL KHAIRI duk ta ajiye masa abun da zai buƙata sannan ta wuce ɗakin ta, wanka ta shiga ta fito ta nemi kayan saka wa, riga da zani ne raffer na atamfa, sun yi mata kyau sosai kuma sun yi mata Cass a jikin ta, kasancewar ta ba me girman jiki ba komi nata ɗan dai-dai ne tubarakalla Masha Allah, tayi kyau matuƙa bare ita ba baya ba wajen iya ɗauri, matsalan ta kawai bata iya kwalliya ba, saboda bata saba ba ko kaɗan, idan ta shafa Powder da jan-baki ya wadatar da ita, amma kuma tunda tana da kyau sosai take yin kyau, yanzun ma ta fito a Amaryan ta sak sai walƙiya take yi
Zama tayi a kan gadon ta tana tunanin kuma me zata yi, sai duk taji ta wani iri sabida rashin sabo, gani take yi kawai komi kamar a mafarki wai yau ita ce tayi aure? Kuma auren ma ABUL KHAIRI shi ne mijin ta? Sai kawai ta hau yin dariya tana tallabo kumatun ta, a fili ta furta, "oh wa ya ga Maimunatu Amarya, wlh gani nake yi kamar ba gaske ne ba zan ji Batool ta tashe Ni. To wai Ni ya rayuwata zata kasance a gidan Yaya ABUL? Shin ta ya ya zaman mu zai kasance? Abun da kunya wlh". Sai ta sake darawa lokaci ɗaya tana jin ƙwalla na cika mata ido na tausayin kanta da kanta, sosai take jin tausayin kanta matsananciya ya kama ta, tana jin kuma kamar baza ta iya wannan sabon rayuwar ba. Kwanciya tayi tana me lumshe idanun ta sai ga hawayen ciki sun zubo, bata yi yinƙurin share wa ba illa janyo wayan ta dake kan gadon da tayi ta soma latsawa, Mamy ta soma kira don sosai tafi jin kewar ta
Ring biyu ta ɗauki wayan. Ita ta soma kiran sunan Maimunan bayan da tayi mata sallama
Cikin matuƙar ɗoki da rawan murya ta amsa ta tana cewa, "Mamy nayi kewar ki. Yaushe zaki zo?"
Dariya daga can Mamyn tayi tace, "Haba ɗiya ta kar ki saka Abban ku yayi mana dariya bayan na gama cika baki a kanki".
Dariya itama Maimunan tayi kana ta gaishe ta cike da kunyar ta
Mamy ta amsa cike da farin ciki tana tambayar ta, "ya ta kwana?" Kafin kuma ta tambaye ta, "Ina ABUL KHAIRIN?"
Ita kuma tayi mata ƙaryan, "ya shiga wanka".
Daga nan Abba ta ba wa wayan suka gaisa yana ta tsokanar ta
Ita kuma sai dariya take yi tana ɓoye fuskar ta
Da Mamy ta amshi wayan take faɗa mata, "ga su Batool nan za su taho yanzu".
Ai nan ta dinga murna tana faɗin, "Mamy me zan dafa musu?"
Dariya daga can su Mamy suka yi, don har su Aunty Naana suna jin ta
Mamy tace, "ke da kike Amarya ina ke ina girki? Kar ki soma ki girka musu komi don su ma ba daɗe wa za su yi ba, za su zo su sake gyara miki gidan ne".
Kamar zata yi kuka tace, "to Mamy".
Daga nan kuma suka yi sallama ta kashe wayan, miƙe wa tayi sabida zumuɗi ta koma Parlour zaman jiran su.
Babu jima wa kuwa sai ga su sun zo, duk ƴan uwa ne gaba ɗaya ƴan bikin suka zo don ganin ɗaki, dayake wasu a lokacin za su tafi shiyasa suka yo zuga, da su Aunty Naana aunty Rufaida yayyin Maimunan duk suna nan, tunda a nan aka yi bikin gaba ɗaya ba'a kai Maimuna can Kaduna ba, dangin Mahaifin ta ne kawai suka yi tasu bikin a can, kuma daga ƙarshe suka taho nan, har da su yanzu a ganin ɗakin amarya tunda yau za su koma, sai su Aunty Fatima ƙanwar Mamy, da kuma Zee me jego.
Sosai Maimuna tayi murnan ganin su har da ƙwallan ta
Su kuma su Aunty Rufaida sai tsokanar ta suke yi da faɗin, "ƴar ƙanwar mu ta zama babba".
Ita sai dai tayi dariya ta ɓoye fuskar ta a jikin Batool
Haka suka zazzagaya gidan ko ina suka gani, sannan suka gyara mata abun da ya kamata, har ɗakin ABUL KHAIRI sun so shiga amma sai dai suka ji shi a garƙame, da suka tambaye ta, "ina yake?"
Tace musu, "ya fita".
Duk sun yarda shiyasa suka ci gaba da harkokin su
Su Aunty Naana da suka gane tamkar wani abu be faru ba, ai nan suka saka ta a ɗaki sukai ta mata lectures ta yanda zata kama ABUL KHAIRI a hannun ta
Ita kuwa kunya duk ya rufe ta kamar ta nitse
Aunty Naana da tafi su zafi har make ta tayi tace, "sai ta ci uban ta idan ta sake rufe fuska, gwara ta tsaya ta saurari abinda suke faɗa mata don idan bata yi wasa ba sai ta titsiye ta ta maimaita abinda suka faɗa mata kaf".
Dole ta nutsu ta mayar da hankalin ta sabida ta san zata aika in dai Aunty Naana ce
Daga ƙarshe da za su tafi suka ce mata, "ta cire kayan nan ta saka ƙananan kaya. Kar kuma ta sake saka wasu kaya a gidan nan idan har ba ƙanana ba".
Da "to". Ta bi su dashi jiki na rawa ta sanya wanda Zee ta ciro mata, duk ta takura amma babu halin musu
Hijabi ta sanya ta rako su har waje da za su tafi kamar zata yi musu kuka, daɗin abun ma an bar mata Batool tunda ita ba yanzu zata tafi ba shiyasa taji ɗan dama-dama
Suna tafiya suka dawo parlour'n suka zauna
Batool ta ƙwage murya tana tonon Maimuna da faɗin, "Amarya Amaryan Yayan mu".
Da sauri Maimunan ta rufe mata baki tana zaro ido tace, "keee wlh yana ciki".
"Ɗan girman Allah fa?". Batool ɗin tafaɗa da sauri itama tana zazzare ido
Dariya sosai ta ba wa Maimuna, sai kawai ta hau mata dariyan tana nuna ta da yatsa
Dukan ta Batool tayi tana hararan ta tace, "ba na son sharri kinga har kin sa ciki na ya ɗuri ruwa, wlh sai in tashi in koma".
Daƙyar Maimunan ta tsayar da dariyan nata tana rufe bakin ta tace, "wlh da gaske nake miki yana ciki babu inda ya je".
Tsaki taja Batool ɗin tana gyara zaman ta, sai kuma ta kalli ƙofan ɗakin sa sannan ta mayar da idanun ta kan Maimuna, ƙasa-ƙasa tace, "amma shi ne kika yiwa su Aunty Naana ƙarya?"
"To me zan ce musu bayan kina gani suka buga ƙofan yaƙi buɗewa? Idan ban ce musu haka ba kinga baza su haƙura ba kin san halin Aunty Naana".
"To tashi mu je ɗakin ki don zan fi sake wa a can, nan ba wurin zaman mu bane".
Dariya Maimuna tayi tana miƙe wa tabi bayan ta, "kai Batool ban san ki da tsoro ba wlh".
Itama dariyan tayi tace, "hmm ai naga da alamu kin soma manta Yaya ABUL ne tunda kika shigo gidan shi, amma Ni ban manta waye shi ba, koda yake kina da hujjar ki me ƙarfi, ƙila yanzu tunda kin zama matar shi bazai miki komi ba, amma Ni idan ba so nake in Koma wa su Mamy da ƙafafu a karye ba ai gwara in kama kaina".
Tsaban dariya Maimuna har da faɗa wa kan gado
Batool ta maka mata duka a cinya tana cewa, "yanzu kin zama muguwa ko? Kema da alamu ya koya miki muguntar daga kwana da shi sau ɗaya".
Tana dariyan tace, "ke dai ki rufe bakin ki kar ya ji ki wlh don babu ruwa na".
Kama bakin ta kuwa Batool ɗin tayi tana matsowa kusa da Maimunan, tsaban gulma ya ci ta kamar dole sai tayi ta ɗan rage murya tace, "to bani labarin fisrt night ɗin naki? Me ya faru don Allah?"
Sai kawai Maimuna ta soma zazzare ido tana faɗin, "ke rufa min asiri don Allah, Ni fa yarinya ce har yanzu wlh, kuma kin san Yaya.."
Tsakin da Batool ɗin taja shi yasa tayi shiru, tana hararan ta tace, "dalla rufe min baki, su Mamy sun san ke yarinyan ce suka yi miki Aure? tunda haka ne nima zan yi auren nan in huta tunda baza ki bani labari ba".
Maimuna tace, "hmm Batool kin san dai babu abinda zai faru kema neman magana ne dake, idan akwai ai bazan ƙi faɗa miki ba, Ni wlh ban ganshi ba tun sanda suka fita da Yaya Sulaiman jiya".
"Allah Sarki Sister na tausaya miki, ko ya ya zaman ku zai kasance da shi? Amma kuma be kamata ki zauna haka ba wlh idan Ni ce babu na mijin da zai wulaƙanta Ni haka, ai dole wlh sai ya bani kula wa ko ya ƙi ko ya so, tashi maza yanzu ki je ki taso shi, ai ma be kamata ki bar shi yana yin abinda yaga dama ba, ya ƙuntata miki kuma ya je shi yayi farin ciki".
"Ni kuma ce miki nayi ya ƙuntata min? Don Allah ki ƙyale Ni kinji".
"Allah wlh sai kin je kin taso shi kinji ma na rantse, idan ba haka ba sai dai in kira Mamy in sanar mata komi, yanda ya bar ki jiya ke kaɗai kika kwana don uban ki ba ƙuntata miki yayi ba? Wataƙil ma ko barcin kirki baki yi ba shi ya je yana sharan nashi".
Maimuna ɓata fuska tayi tace, "Ni kike zagi ko? Kin san dai yanzu Ni matar yayan ki ne kuma dole ki ce min Aunty, yanzu babu wasa a tsakanin mu".
Hararan ta Batool ɗin tayi tace, "don ina faɗa miki gaskiya? Tashi dalla ko in Kira ta wlh".
Ƙin tashi Maimunan tayi tana sake ɓata fuska don dai Batool ɗin taji shakkar ta ta barta, amma da ta ga ta ɗauki waya ai da sauri ta tashi tana cewa, "to ga shi na tashi ko malama. Wlh ni har kin fara saka min ciwon kai".
Bata saurare ta ba sai ma jawo hannun ta da tayi tana fadin, "baza ki gane bane Maimuna, idan kika tsaya sanya kina jiran sanda Yaya ABUL zai karkato gare ki kina da jan aiki, ai ke ce zaki riƙa shige masa wlh, duk wani haƙƙi nasa ki je ki sauke masa, yanzu ba wani abu fa nace kiyi ba, zuwa zaki yi ki taso sa ki ce mishi ga Breakfast ɗin sa".
Ita dai Maimuna bata ce komi ba illa sauraron ta da take yi, har sanda ta ajiye ta a gaban mirror tana mata kwalliya
Sai da tayi mata light make-up kafin tace, "yauwa to ko ke fa, har fuskar taki ta sake yin kyau, yanzu cire hijabin nan". Kafin ma tayi magana har ta saka hannu tana cire mata
"Haba kiyi min a hankali mana". Maimunan tafaɗa tana hararan ta
Banza tayi mata tana janye hijabin ta wurgar saman gado, sai ta washe baki kawai tana bin Maimunan da kallo riƙe da ƙugu. "Kai my sister don Allah ki kalle ki fa".
Ɗago kai tayi tana kallon kanta a Madubin tana kallon yanda kayan suka lafe mata a jiki, cike da kunya tace, "wai kina nufin haka zan je?"
"Eh mana. Gaskiya kinyi kyau wlh. Tashi mu je in raka ki".
"Kai wlh bazan iya zuwa ba ai wannan iskanci ne sai yayi zaton na kawo kaina ne".
Taɓe baki Batool ɗin tayi tace, "sai me? Dama haka kuke ai matan hausawan nan, ke dashi kun zama ɗaya meye kuma na kunya? duk abinda zai ce sai dai yace, abinda ke cutar daku kenan, na rantse da Allah da Ni ce a ranan farko sai na fara shiga zuciyar miji na ko ya ƙi ko ya so sai nayi kane-kane a ciki".
"Allah ya sa dai kema bahaushiyan ce".
"A'a amma Ni kin san nayi gadon su Hajiya Mama ce, kuma kin san ita Banufiya ce don haka Ni babu ruwa na da Hausa wa da kuma gidadancin su".
Tsaki Maimuna taja tace, "hauka. Kanki ake ji dai domin ko kin ƙi ko kin so ke bahaushiya ce, kuma daɗin abun ma Hausawan sun fi Nufawan kamun kai".
"To tashi mu je dai." Ta ja ta suka fice, har bakin ƙofan ɗakin ABUL KHAIRI ta kaita, kana ta juya ta tsaya a bakin ƙofan ɗakin Maimunan tana leƙen ta, ƙasa-ƙasa take ce mata, "baza ki buɗe ba".
Tura baki Maimunan tayi kafin ta soma Nocking a hankali
Ganin haka sai Batool ɗin ta iso wajen ta ta hau buga ƙofan da ƙarfi
Da sauri ta riƙe mata hannu tana zare ido, cike da tsoro da murya ƙasa-ƙasa tace, "na shiga uku Batool don Allah ki bari".
"To kiyi Nocking da kyau idan ba haka ba zan ta buga ƙofan wlh, kuma idan ya fito ɓoye wa zan yi".
"To naji naji zan yi please".
Sai Batool ɗin ta juya da gudu har tana cin tuntuɓe jin kamar ana taɓa ƙofan za'a buɗe
Ita kuwa Maimuna sandare wa tayi a wurin idanun ta a waje tana kallon ƙofan.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( '''WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS''' 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 30*
*________* Yana buɗe ƙofan ya sauke idanun sa a kanta, wani irin abu ne ya tsarga mishi ganin ta a irin wannan shigan da be taɓa ganin ta ba, duk yanda ya so ya janye nashi idanun daga kallon ta amma ina ya kasa, daga sama har ƙasa yake bin ta da kallo ba tare da ya ko ƙyafta su ba
Ita kuwa yanda taga wannan kallon nashi tuni ya sanya ta rawan jiki, saboda gani take yi kamar zai duke ta yanda fuskar sa yake a ɗaure. Daƙyar ta iya haɗo kalmomin bakin ta wajen faɗin, "uhm.. hmmm dama..." Sai kuma ta rasa abun faɗa illa murɗa yatsun ta da take yi hawaye har sun soma cika mata ido, dole ta sauke idanun ta ƙasa saboda kallon da yake mata yanzu, cikin rawan murya sosai ta furta, "Break..fast.. naa..yi.." shiru tayi ganin ya juya ya shigewar sa tare da rufo ƙofa.. da sauri ta saki ajiyan zuciya hawayen dake maƙale a idanun ta suka zubo mata sanda ta lumshe su. Jin an dafa ta a firgice ta juya don ta manta akwai Batool a gidan, a tunanin ta ko shi ne
Dariya sosai yaso kama Batool, amma sai ta rufe bakin ta ta janyo mata hannu suka yi ɗakin ta. Suna shiga ta sake ta ta dinga mata dariya. "Wlh ke babban matsoraciya ce, ban taɓa tunanin haka kike ba sai yanzu.. wayyo Allah na". Sai ta sake kwashe wa da dariya har da riƙe ciki. "Kin ga yanda kika yi kuwa?"
Hannu Maimunan ta saka tana share hawayen fuskar ta kafin tace, "baza ki gane bane wlh na tsorata, nayi tunanin duka na zai yi da yake min wannan kallon shi ne yasa jiki na yake rawa duk na tsorata, kuma kinga da irin kayan da naje wajen sa wlh shi ya ƙara tsorata ni". Ta ƙare maganar tana zama bakin gadon ta har da dafe kai
"Ke banza ce ai, wannan kallon shi ake ce mishi alamun nasara, taya idan baki tafi da hankalin shi ba zai tsaya kallon ki? Wlh ni na tabbata shigan ki ne ya ɗauke mishi hankali. Kinga da haka wata rana shikenan zaki shiga zuciyar sa, kar ki damu ƴar uwa da sannu komi zai wuce".
"Kina nufin in ci gaba da yi wata rana ya make Ni kenan? Ke baki san yanda naji bane kamar in nitse tsaban kunya".
Batool tace, "ai kuwa zaki nitse wata rana, ke fa sokuwa ce ba mijin ki bane?"
"Kar ki sake ce min sokuwa". Cewar Maimunan tana banka mata harara
Taɓe baki ita kuma tayi tace, "to tunda kinyi baki yanzu ai sai ki rama. Ni kinga bari in je in ci wani abun don ban yi kari me kyau ba". Ta ƙare maganar da yin hanyar ƙofa ta fice.
Maimunan bata ce komi ba illa ɗaukar hijabin ta da tayi ta rataya tabi bayan ta. A kan dainning taga Batool ɗin tana haɗa tea. Zama tayi gefen ta tana cewa, "mu ga wayan ki in yi turi saboda in samu abun taya Ni hira".
Cikin ƙasa-ƙasa da murya Batool ɗin tace, "ba ga Yaya ABUL nan ba kin samu shi ne zai taya ki hiran ai".
Ɗaukan wayan tayi bata ba ta amsa ba ta shiga File manager ta soma duba waƙoƙi, tana yi tana saka wa idan yayi mata sai ta tura
A haka suke zaune babu wanda ya sake magana, illa Batool ɗin dake bin waƙan idan Maimuna ta saka, tana yi tana kurɓa tea ɗin ta
Wayan ce ta soma ringing, ganin Sulaiman ne sai Maimuna ta ɗauki wayan tana kara wa a kunne, cikin ɗoki da murna ta amsa mishi sallaman da yayi, "tace Yaya na ina kwana".
"Amarya kina lafiya? Ya Angon naki?"
Cike da kunya tace, "kai yaya bayan ma baka zo ka gan ni ba?"
Dariya yayi yace, "to ban da ke da abun ki jiya fa aka kawo ki ko?"
"To yaushe zaka zo Yaya?".
"Yanzu ma zan zo, dama kiran Batool nayi in ji ko zata tafi ne sai in zo in ɗauke ta".
"To Yaya amma dai tare da Yaya Aliyu zaku taho ko?"
"A'a Aliyu na gidan Hajiya Mama, amma ai shima zai zo ya duba ki na san bazai koma be zo ba".
"To Yaya".
"Yauwa ki ba wa Batool ɗin wayan idan tana kusa".
Sai da ta kalli Batool ɗin ta ɗan yi dariya kafin ta amsa mishi, sannan ta miƙa mata wayan
Ita kuma ta amsa wayan tana ajiye cup ɗin hannun ta. "Ina kwana Yaya, na tashi ai ban ganka ba".
"Ai baki damu dani ba tunda baki kira Ni ba, Ni kuwa kin ga na damu dake har na tambayi Mamy tace min kin taho nan ne".
"Ayya Yaya wlh ba haka bane, ka ga muna sauri ne shiyasa ban kira ka ba".
"To ai babu komi, yanzu yaushe zaki tafi in zo in ɗauke ki?"
"Sai yamma Yaya".
"Ah ah har yamma ƙanwata? Anya baza ki takura wa ma'auratan nan ba? kin san fa jiya aka yi auren nan be kamata ki zauna musu a gida ba, Ko kema kina son ayi miki haka ne?"
Dariya tayi cike da kunyan sa tace, "Ni kuma Yaya Sulaiman?"
"Eh mana kefa, gaskiya ba na son kema ayi miki haka, don haka yanzu zan zo in ɗauke ki".
Murmushi tayi kawai tace, "to".
"Baki ce Allah ya kawo Ni lafiya ba, haka ake yi babu addu'a?"
Batool dai duk jinta tayi wani iri, sai kace wasu masoya, amma a ranta sosai take jin farin ciki tsantsa, shiyasa tayi masa addu'ar kamar yanda ya buƙata, daga nan suka yi sallama tana ajiye wayan fuskar ta yalwace da murmushi
Maimuna da ta kafa mata ido tace, "wai Ni ban gane ba, meke shirin faruwa ne?"
"Aina kenan?" Batool ta tambaye ta a rashin fahimta
Ɗage mata gira tayi tace, "ke da Yaya Sulaiman mana, Anya ba soyayya kuke yi ba?"
Zaro ido tayi kafin tace, "soyayya kuma? Haba ke kuma idan soyayya ne ai zaki fi kowa sani, kema kin san wanda nake so".
"Yes I know. Amma tunda yanzu babu halin soyayya dashi Ni ina ma yaya na kamu, I'm serious wlh".
Jinjina kai Batool tayi kafin ta ɗauki Tea Cup ɗin tana cewa, "kanki ake ji dai, kin san dai Yaya Sulaiman baza a rasa shi da budurwa ba, so karma ki Yi wannan zancen ya ji ki".
"Ni yanzu da nayi tunanin nan har na ga kun fi dace wa, na san Yaya Sulaiman ustazu ne babu ruwan sa da ƴan mata".
Sai kawai Batool ta hau mata dariya
Ita kuma ta saki baki tana kallon ta. "Me kike wa dariya ne?"
"Babu. Bar zancen nan".
🔵🔵🔵🔵🔵
Sanda Sulaiman yazo suna nan zaune a parlour'n
Da murna Maimuna ta tare shi tana mishi sannu da zuwa
Sai da ya zauna kafin ya amsa ta shima yana murmushi yace, "yauwa ƙanwa ta Amarya".
Dariya tayi kawai
Itama Batool tayi masa nata sannu da zuwan
Yace, "ban amsa naki ba".
Sai ta langaɓe kai tace, "to Yaya Ni me nayi?"
"Dawo kusa dani sai in faɗa miki".
Waro idanu kawai tayi ta kasa tashi
Sai yayi murmushi kawai yana amsan ruwan da Maimuna ta zuba mishi a Cup ya sha, kafin yace da ita, "kin ga ke ya kamata ki tarbe Ni ba Amarya ba, amma ke kin zauna kin bar ta da aiki".
Da sauri Batool ɗin ta tashi tace, "ayya Yaya ai dama Ni zan ɗauko maka ta riga Ni".
Dariya suka yi su biyun
Ya ƙara da faɗin, "kin ji wasa nake miki dawo ki zauna. Ina Angon ne wai? Kar dai ace na zo ba ya nan?"
"Yana nan Yaya, amma yana ciki". Cewar Maimuna tana neman wuri ta zauna
"Ok Kira shi mu gaisa to, baki faɗa mishi zan zo bane?"
Kamar zata yi kuka tace, "Eh. Amma yaya.." sai kuma tayi shiru don bata san me zata ce mishi ba
"Mene ne?" Yayi maganar yana kallon ta
"Wai da zance ne ka kira shi a waya".
Jimm yayi kawai yana kallon ta, sai kuma be ce komi ba dai ya ɗauki wayan sa ya nemo Numban sa ya kira sa. Yana Ring ɗaya biyu ya ɗauki wayan. "Hello ɗan uwa gani a gidan ka fa"... "Ok." Sai ya cire wayan daga kunnen sa ya kashe tare da ajiye wa.
Two minutes ago sai ga ABUL KHAIRI ya buɗo ƙofa ya fito, daga shi sai dogon wando da Singlet har a lokacin be sanja ba, fuskar sa babu walwala haka ya iso wajen
While Maimuna da Batool ƙyam suka yi wuri ɗaya suna zare idanu
Sai da ya zauna kafin Batool tayi saurin gaishe sa
Be kalle ta ba ya amsa ta yana mayar da idanun sa kan Sulaiman, kaɗan ya saki fuskar sa yace, "zuwan yaushe?"
"Yanzu na zo. Amma haka ake yi zaka shige ɗaki ka bar Amaryan taka ita kaɗai?"
Murmushi kawai yayi be ce komi ba, don ya san halin Sulaiman idan ya biye mishi surutu zai saka shi, shi kuma kansa ciwo yake masa yanzu
"Am.. dama Ina so muyi maganar nan da muka yi da kai kwanakin baya".
Sai da ABUL KHAIRIN ya kalli su Maimuna suka haɗa ido kafin ya janye nashi idanun yana sake haɗe rai, "ka bari zamu yi maganar a waya".
Sulaiman yace, "ok mu ma ba zama zamu yi ba yanzu zamu tafi, Batool tashi ki ɗauko gyalen ki mu wuce".
"Nima zaka sauke Ni a gida zan ɗauko mota ta, bari in saka kaya". ABUL KHAIRI yayi maganar yana tashi ya wuce nashi ɗakin. Be jima ba ya fito cikin shirin sa na ɗanyen shadda me ruwan ƙasa, ɗinkin tazarce ne amma tayi masa mugun kyau sosai, dai-dai jikin sa ga shi ya kafa hula kalan kayan ƙube, takalmin ƙafafun sa cover ne baƙi ya saka da agogon hannun sa
Yana fito wa suka fice da Sulaiman don a lokacin su Maimuna sun koma ɗaki
Batool ɗaukan jakan ta da gyalen ta tayi ta yafa suka fito tare, sai tsokanar Maimunan take yi wadda kamar tayi kuka da tafiyan Batool ɗin
A bakin ƙofa ta tsaya tana ɗaga mata hannu har suka bar gidan, ta saka hannu ta share ƙwallan ta kafin ta shige ciki, a kan kujera ta kwanta tare da rufe idanun ta, tana tunani a haka barci ya ɗauke ta. Bata tashi ba har sai da aka kira sallan azahar, har a lokacin kuma ABUL KHAIRI be dawo ba, sallah tayi a ɗaki ta sake kishingiɗa a saman gadon ta taci gaba da tunanin ta, dayake ko kaɗan ba ta jin yunwa shiyasa bata yi tunanin nema wa kanta abinci ba.
Sai yamma taji shigowar motar sa gidan, ko bata duba ba jikin ta ya bata shi ne, shiyasa ta sake lafe wa a kan gadon tana kallon ƙofa kamar wacce zata ganshi a wurin
Sai kuwa ga shi ya murɗo ƙofan ya shigo, ciki-ciki yayi sallaman idanun sa ƙirr a kanta
Da sauri ta tashi zaune kanta a ƙasa tunda tayi masa kallo ɗaya, ji take yi kamar ta nitse sabida ta cire hijabin jikin ta, duk tayi tsimu a wurin ta kasa jirga wa don bata san me zata yi ba
A hankali ya tako fuskar sa a matuƙar haɗe amma idanun sa a kanta don ya kasa ɗauke wa, ajiye mata ledan hannun sa yayi a saman gadon kusa da ita, be ce komi ba ya juya ya fice
Ita kuma kamar jira take yi sai ta saki wani gwauron numfashi har da dafe ƙirjin ta tana me lumshe idanu, haka ƙirjin ta ke faman buga wa kamar zai faso sakamakon yanda ta ɗauke numfashi tun zuwan shi kusa da ita shi ya jawo mata hakan, ta ɗan jima a haka tana mayar da numfarfashi kafin ta ware idanun ta tana kallon ledan da ya ajiye mata, ɗauka tayi ta soma buɗe wa don taga abinda ke ciki.
********
Shi kuwa yana shiga ɗakin sa Direct Kan gadon sa ya samu ya zauna tare da kame kansa yana me rufe idanun sa, sai kuma ya gyara ya kishingiɗa yana ɗago ƙafafuwan sa ya aza Kan gadon bayan ya cire takalman nasa, ya sanya hannayen sa yayi matashi da su yana me ƙure wa ƙofa idanu kasancewar nan side ɗin yake kallo, duk bayan sakon yana me lumshe idanun sa yana buɗe wa, yanda zuciyar sa ke son matsa masa da tunanin ta ne sai ya ja tsaki yana sake juya kwanciyar sa, da zaran ya rufe ido ita yake gani shiyasa duk second ya buɗe ya rufe ya kasa barin idon waje ɗaya, ya san be taɓa ganin ta a haka ba shiyasa zuciyar sa ta kwaɗaitu da son ganin ta, amma bayan haka ba ya tunanin akwai abinda ke birge sa a game da ita, be taɓa tunanin haka take ba sai a yau ɗin, dole ne ma ya hana ta saka wannan kayan in ba haka ba komi zai iya faruwa, sai ya sake jan dogon tsaki yana tashi zaune ya jawo wayan sa, don dai ya kawar da tunanin banzan nashi shiyasa yake ta latse-latsen wayan sa har sanda aka kira sallan magriba, ya tashi yayi alwala ya fito ya nufi masallaci, da nisa sosai da gidan sa, amma a haka ya taka ya nufi masallacin, be dawo ba sai da aka yi sallan isha'i
Yana shigo wa yaji wani ƙamshi me daɗi ya mamaye hancin sa, da sauri ya lumshe idanun sa yana sake ware wa a parlour'n, sai da ya gama ƙare ma ko ina kallo kafin ya kai duban sa ga wajen dainning, a nan yaga an jera cololi da alamu girki ne tayi, ɗauke kai kawai yayi ya wuce ɗaki har yana saka keey.
******
Ita kuma a lokacin har ta fito daga wanka ta shirya cikin riga da skert na atamfa, ɗinkin ya kama ta cib a jikin ta kamar wata ƴar baby, ga shi yarintan ta ya sake fito wa ainun, bata shafa komi a fuskarta ba haka ta gama gyara wa ta fito kanta tsaye ta nufi ƙofan ɗakin ABUL KHAIRI tunda ta ga ba ya parlour'n, ta san ya dawo tunda ta ji motsin sa shiyasa ta nufi ɗakin ta faɗa masa "ga abinci idan zai ci," duk da wani sashi na zuciyar ta na cike da fargaba don bata san me zata tarar ba, a haƙiƙanin gaskiya Allah ya dasa mata tsoron ABUL KHAIRI saboda kwata-kwata be taɓa mata wasa ba, be taɓa kallon ta da idon rahama ba, shiyasa take matuƙar shakkan sa domin be da mutunci a yanda yake nuna musu, amma sai ga shi ƙaddara ta haɗa su wuri ɗaya, ta haɗa su zaman aure, abun da bata taɓa tunanin zai iya kasancewa ba ko da a mafarki ne, wai yau ita ce igiyar aure ya haɗa su da ABUL KHAIRI.
*Whatsapp number don't calling*
07065334256
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 31*
*________* Nocking take ta Yi amma shiru, shiyasa ta saka hannu ta tura nan ta ji a kulle ne. A lokacin taji muryan sa yana faɗin
"Idan kika bari na buɗe ƙofan nan na cid da ke a wurin nan; wlh sai na haɗa miki jini da majina".
Kamar ƙiftawar ido sai gata a ɗakin ta har da saka keey tana rufe wa, a baƙin ƙofan ta tsaya tana mayar da numfashi, bata manta dukan da yayi musu ba ita da Batool wanda ya ja kwanciyar ta a gadon asibiti, idan kuwa ya kama ta yanzu ai me ƙwatan ta sai Allah, gwara ta shafa wa kanta lafiya ta fita a harkan sa, "ai ɗan ba ƙara wlh". Tafaɗa a fili tana nufan kan gadon ta ta zauna.
Ta shafe mintoci a haka tana faman tunani kafin ta tashi tayi shirin kwanciya ta kwanta abin ta, da haka barci ya ɗauke ta cike da mafarkai kala-kala.
Tun daga ranan kuwa ta fita a harkan shi, idan ta tashi da safe zata yi musu Breakfast ta Kai saman dainning, haka ma na rana da na dare kullum tana yi, amma be taɓa ci ba, be ma taɓa zuwa ya duba abinda take girka wa ba, ita kuma tsoro ya hana ta sake mishi magana, iyakanta da shi idan suka haɗu a Parlour ta gaishe shi, wani zubin ya amsa ta a ciki-ciki, wani zubin kuma yayi banza da ita, a haka suke rayuwar tasu tamkar basu san juna ba, amma abun mamaki da zaran ƴan uwa sun zo zai saki jikin sa har ya nuna musu kamar suna zaune lafiya
Shiyasa itama ta fita harkan sa ta saba da wannan halin nasa, dayake ko yaushe suna waya da su Mamy shiyasa take rage kewa, har Ummu tana kiran ta ta tambaye ta, "ko akwai matsala?" Amma sai tace mata, "a'a". Bata taɓa faɗa musu wani abu game da zaman su ba duk da ko yaushe sai sun tambaya, idan Mamy bata tambaya ba Ummu zata tambaye ta, ita Ummu ma har tsiya take mata a cewar ta, "idan ma tana ɓoye wa ne ita ta sani, dama ta san halin ta shegen zurfin ciki ne da ita". Ita dai duk faɗan da zata mata ba ta iya ko tari ne, haka zata ƙyale ta ta kashe wayan da faɗan, "ita ta sani baza ta sake tambayan ta ba," amma kuma gobe bazai hana ta sake ɗin ba
Ummu tana matuƙar son Maimuna sabida ta san halin ta ita ce kaɗai daban da ƴaƴan ta, shiyasa take bata tausayi, bare kuma ta san yanda ABUL KHAIRI ba ƙaunar ta yake yi ba, shiyasa take lallaɓa ta ta sanar mata halin da suke ciki tunda ta san ita ce a wahala, amma kuma duk rarrashin da faɗan amsar ta ɗaya ne, "wlh babu komi". Shiyasa ta ƙyale ta kawai tunda haka ta zaɓa.
Satin su biyu ABUL KHAIRI ya koma bakin aikin sa, hakan da ta gani ne yasa itama ta same shi da zancen, "zata koma school". A lokacin da ta sanar mishi be ce mata komi ba don yana zaune a Parlour ne, sai ma tashi da yayi ya shige ɗaki abin sa
Ita kuma sai jikin ta yayi sanyi har tana tara ruwan hawaye, gaba ɗaya gani take yi kamar kashi ma ya fi ta daraja a gidan, ko kaɗan be taɓa mata kallon arziƙi ba, kamar ita kaɗai take rayuwa a gidan sabida babu ruwan sa da ita, sai ayi kwana biyu magana ɗaya be haɗa su ba, tabbas idan tace tana jin daɗin zaman nan ta yiwa kanta ƙarya, har ga Allah har zuciyan ta ba son shi itama take yi ba, amma kuma takan damu da rashin nuna mata kulawa da be yi, ya nuna tamkar babu halittan ta a wurin, ita kuma a rayuwa tana me ƙaunar me kulawa da ita, tana matuƙar ƙaunar kulawa, tana son taga mutum ya damu da ita duk da ita ba me son hayaniya bane.
Abun mamaki kuma washe gari tana barci sai ji tayi ana buga mata ƙofa, da sauri ta wartsake jin muryan sa yana cewa, "baza ta buɗe bane?" Ta duro a Kan gadon da sauri ta nufi ƙofan ta buɗe
Shi ne kuwa tsaye a gaban ta yana bin ta da kallo
Duk ta kiɗime lokaci ɗaya ganin ya kafe ta da idanun sa masu saka ta sanyin jiki, har bata san sanda ta duƙa tana gaishe shi ba
Sai kawai dariya ta so kama shi ganin yanda duk ta diririce, be iya ɗauke idanun sa a kanta ba illa tamke fuska da yayi don hana kansa dariyan da ya zo mishi, murya a dishe yace da ita, "me kike yi har yanzu baki shirya ba?"
"Am.. uhm dama.. dama.."
"Na baki ten minutes ki shirya ki same Ni". Ya katse ta da faɗan hakan yana juya wa ya fice
Da sauri ta saki numfashi tana me miƙe wa, sai a lokacin ma ta kalli jikin ta daga ita sai vest da guntun skert, "oh Allah na na shiga uku. Haka nake?" Tafaɗa kamar zata yi kuka. Sai kuma ta juya da sauri tana faɗa wa kan gadon ta, kanta ta lulluɓe tana faɗin, "na shiga uku Ni Maimunatu, haka na fita ya gan ni? wayyo Allah Ni". Sai ga hawaye, da sauri kuma ta tashi tuna maganar sa da tayi, sai kawai ta fashe da kuka tana faɗa wa Toilet da gudu, "wlh idan na wuce lokacin nan kashi na ya bushe a wurin sa, to shi ne be ce min in shirya tun jiya ba sai yanzu, salon kawai mugunta". Da haka take ta surutai har ta gama wankan. Kafin ma ta shirya har mintuna goman da ya ɗiba mata ya wuce, sai ta koma kuka wiwi jikin ta na ta faman rawa, hijabi a hannu haka ma takalman ta ta fita da gudu tana faman share hawaye. A Parlour taci birki ganin sa zaune yana latsa waya
Shima ɗago kai yayi yana kallon ta ganin ta da yayi kamar an jeho ta, da idanu kawai yake bin ta yanda yaga hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta, sai mamaki ya cika sa amma be iya ce mata komi ba illa sake kafe ta da kallo da yake yi
Ita kuma tana tsaye tana share hawayen ta, sai ta soma saka hijabin ta duk jikin ta rawa yake yi
Tashi yayi kawai ya nufi bakin ƙofa
Har ta bi bayan sa ta tuna bata ɗauki jaka ba, sai ta koma da gudu ta ɗauko ta fita
Lokacin ya shiga mota har ya tayar yana kallon hanya, tunda ta fito yake bin ta da kallo, "ko meye ya firgitar da ita haka?" Yafaɗa a ransa yana me sake mamaki sosai. Ajiyan numfashi ya sauke jin ta buɗe ƙofan ta shigo, yaja motan suka tafi
A cikin motan ta saka takalman nata da socks tana faman ajiye numfashi wasu hawayen na sake zubo mata
Duk yana lura da ita amma ko ci kanki be ce mata ba har suka nufi school ɗin nasu, ya sauke ta a waje ya juya ya tafi ba tare da ya furta mata komi ba
Da kallo kawai ta bi motan tana tamke bakin ta jin wani kuka ya taho mata, "ga shi ko karya wa bata yi ba amma ya tafi ya barta babu ko sisi, wannan ai cin zalun ne". Haka ta gyara fuskar ta tana shige wa cikin makarantan
Sanda Batool ta ganta sosai tayi murna don bata yi zaton zata zo ba, nan suka rungume juna cike da ɗoki, tuni Maimuna ta manta baƙin cikin ta ta ga ƴar uwa
Sai da Malam ya shigo suka rabu, yana fita kuma suka dasa daga inda suka tsaya, Batool ɗin ta siyan musu abin break tunda ita ta ce, "bata zo da ko sisi ba".
Suna tare har aka tashi har su Amir sun zo wurin ta, ganin ABUL KHAIRIN be zo ba har zata bi Aƙilu ya sauke ta a gida sai ga shi ya zo. Dole ta sauko zata nufi motan nasa, amma Baby ta maƙale mata, "wai sai ta bi ta". Da gudu ta sauko ta nufi motan ABUL KHAIRIN
Shima yana ganin ta ya fito yana ɗaukan ta ya rungume yana faɗin, "Oyoyo Auta na ƴar makaranta".
Tana washe baki tace, "Yaya zan bi ku, wai Aunty Batool ta ce baza ku je dani ba?"
"O'o zamu je dake mana idan har zaki zauna damu".
"Yeeeeee". Tafaɗa tana murna a jikin nasa
Sumbatan ta yayi a kumatu yana kallon Aƙilu drever yace, "ka kawo mata kayan ta idan kun koma". Daga haka ya juya ya saka ta a motan; ta wajen zaman sa, sannan shima ya shiga ya rufe
Sai a lokacin Maimuna itama ta sami shiga, baya ta shige ganin Babyn har ta koma kujeran me zaman banza, haka yaja motan suka tafi Baby na ta musu surutu, shi kaɗai yake amsa ta don ita Maimuna nauyin sa yasa ta kasa ƙwaƙƙwaran motsi bare ta biye mata, sai murmushi kawai da take yi
A haka suka isa gidan suka fito, Baby na maƙale da ABUL KHAIRI har ɗakin sa
Ita kuma Maimuna ɗakin ta ta shige ta tuɓe kayan ta, sai da ta ɗan watsa ruwa don taji daɗi kafin ta shirya cikin riga da skert ƴan kanti, rigan me ruwan madara ne tana da dogon hannu sai collar a wuyan, sai skert ɗin ja da hulan sa, sun mata cif sosai kasancewar Robber ne kayan, sai a lokacin ta fita parlour'n don ta kira Baby itama tayi mata wankan
A lokacin suna zaune da ABUL KHAIRI a Parlour ya biye mata sai faman surutu take mishi tana ba shi labarin school, shi kuma yana latsa wayan sa yana amsa mata da, "um". Daga shi sai Singlet a jikin sa da gajeren wando. Tunda Maimuna ta fito ƙamshin turaren ta ya ziyarci hancin sa sai ya ɗago kai ya zuba mata idanuwan sa, be iya ɗauke su ba saboda wani irin abu da ya ji ya ziyarce sa a lokaci guda wanda ya haddasa mishi mutuwar jiki da wani irin faɗuwar gaba, har be san sanda ta ƙariso inda yake ba ta janye Baby a jikin sa, sai a lokacin ya dawo hayyacin sa yana janye ido a kanta tare da lumshe su
Ita kuma tuni ta ja hannayen Baby za su wuce ɗaki
Be san sanda ya furta, "ina kuma zaki je? A mean Ina zaki je da ita?"
Juyo wa tayi tana kallon sa, sai dai yanda idanun sa ke yawo a kanta sai ta duƙar da kai ƙasa tace, "dama na ce maka zan mata wanka ne ai". Domin lokacin da ta iso wurin tayi masa magana but be ji ba tsaban hankalin sa ba ya jikin sa
"Dawo da ita Ni zan mata, ki je ki sama mata abinci saboda bata ci komi ba". Yayi maganar a hankali a kuma wani yanayi me kama da yana cikin wani hali
Ita kuwa Maimuna sosai hakan yayi mata daɗi a rai, memakon yayi mata magana a yanda ya saba yau ne kaɗai ta ji ya taɓa mata magana a cikin sanyi matuƙa kuma a tausasan kalamai, shiyasa da sauri ta saki hannun Babyn tayi kichen zuciyar ta cike da farin ciki, haka kawai take jin matuƙar sanyi a ranta, duk da wani gefe na zuciyar ta ta dangana hakan ne da kasancewar akwai Baby a wurin shiyasa yayi mata magana a hankali. Cikin sauri take girkin har jikin ta na rawa, gaba ɗaya ta kasa samun nutsuwa don har ɓarar da abu take yi
ABUL KHAIRI ne ya shigo jin ɓari a tunanin sa ko wani abu ne, da kallo kawai yake bin ta
Ita kuma ta duƙa tana kwashe albasan da suka zube wanda ta yanka ta zuba a Plate
"Lafiyan ki ƙalau kuwa..?"
Da sauri ta ɗago kai tana kallon sa don bata ji motsin sa ba sai maganar nasa, hakan yasa har taji tsoro
"Ke wai lafiyan ki lau? Tsoron me kike ji ko wani abun kika gani?"
"A'a dama.." sai kuma tayi shiru
"Dama me? Idan ina miki magana ba kya iya ƙarisa min abinda na tambaye ki zaki ci tumu a gidan nan wlh, ki mayar da hankali a kan abinda kike yi". Daga haka ya juya ya bar kichen ɗin, a lokacin ne ya ji ana Nocking sai ya nufi bakin ƙofan don duba wa
Aƙilu drever ne da ɗan akwatin Baby ya taho mata da shi
Gaisuwar sa kawai ya amsa tare da amsar akwatin ya kulle ƙofan ya wuce ɗakin sa.
Shi ya shirya Baby don har yayi mata wankan, sannan suka dawo Parlour suka zauna, har ta fara surutu sai kuma ta fara mishi ƙorafin, "yunwa take ji."
Kallon ta yayi yana shafa mata kai yace, "Auta na rigima ki bari ta kusa gama wa yanzu zata kawo kinji? In kunna miki kallo ko?"
Gyaɗa mishi kai tayi tana langaɓe wa a jikin sa
Sai da ya kunna mata sannan ya miƙa mata Remote control ɗin yana faɗin, "yauwa Auta na ga shi kiyi ta kallon ki bari in duba Auntyn naki".
Amsa tayi, shi kuma ya tashi ya wuce kichen ɗin don duba Maimuna
Lokacin har ta gama sake taliyan da tayi a cikin coolar tana haɗa musu zoɓo fresh
Ya shigo yana faɗin, "wai me kike yi har yanzu?"
Da sauri ta juyo a tsorace har tana ɓaro da jug ɗin zoɓon ya kiɓe a ƙasa, "wayyo Allah". Tafaɗa tana saka hannayen ta biyu a baki idanun ta gaba ɗaya a waje tsaban tsoro
Wani kallo ya aika mata da shi cike da haushi yace, "wai ke kina da hankali kuwa? Uban me kike wa tsoro haka da duk shigo wa ta sai kin tsorata? Kina da hankali kuwa Ni ne kika maida dodon ki?"
Da sauri ta zame ƙasa jikin ta na rawa ganin ya nufo ta, "don Allah kayi haƙuri Yaya, wlh kuskure ne.."
"Kuskuren uban ki, da alamu baki da hankali ko zan koya miki shashashan yarinya".
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 32*
*________* Har ta fara hawaye don a tunanin nata dukan ta zai yi
Sai ya daka mata tsawa a kan, "ta tashi ta gyara wajen if not kuma zai sauya mata kamanni ne yanzu". Daga haka ya ɗau coolarn ya fice fuska ba fara'a
Numfashi ta saki da sauri wasu sabbin hawayen suna sake wanke mata fuska, gaba ɗaya sai jikin ta yayi sanyi Yanzu, ita kanta ta rasa meyasa take firgita haka duk sanda ya shigo.
Sai da ta gyara wajen kafin ta sake haɗa wani ta fita da shi Parlour. A ƙasa ta gansu suna zaune sun bararraje suna cin taliyan, sai kawai ta saki baki ganin har shi yake cin abincin. Ganin zai ɗago kai tayi saurin ɗauke idon ta a kanshi tana ƙarisawa wajen su tare da tattaro nutsuwar ta, a gaban shi ta ajiye ba tare da ta ce uffan ba ta miƙe zata wuce ɗaki
Sai Baby tayi saurin cewa, "Aunty ke fa baza ki ci bane?"
Juyo wa tayi tana kallon ta, sai kuma ta saci kallon ABUL KHAIRI
Kansa na ƙasa yana ta zuƙulƙulan taliyan sa don ba ƙaramin daɗi yayi masa ba
"Aunty zo mu ci mana".
"A'a ku ci Auta na Idan kuka gama zan ci Ni".
"A'a Aunty don Allah ki zo kinga tare muke ci ko a gida ai".
Ganin ta ƙi motsa wa sai ABUL KHAIRIN yayi magana ba tare da ya ɗago kai ba, "kina son ta fahimci wani abu ne salon ta kai mu gaba ko?"
Jin hakan ne yasa ta tako ta zauna gefen Baby suka saka ta a tsakiya, tuna wa tayi bata ɗauko nata Plate ɗin ba sai ta tashi ta je ta ɗauko ta haɗo musu da Cups, ita ta zuba musu zoɓon sannan ta zuba nata abincin. A hankali take cin abincin duk a takure, idan ta kai cokali ɗaya sai ta jima kafin ta sake ɗibo wani kanta na ƙasa
While Baby na ta musu surutu
"Ki yi shiru mana Auta, baki san ba'a surutu ba idan ana cin abinci?"
"Na sani mana Yaya, ai ana koya mana a islamiyya".
"Yauwa big Girl to ci abincin ki. Ki ɗauko min Coke".
Ɗago kai Maimuna tayi ta kalle shi, ganin shima kallon ta yake yi yasa ta gane da ita yake yi, sai ta tashi ta nufi wajen Fridge ɗin ta ɗauko ta kawo mishi, sai da ta zuba mishi a Cup kafin ta miƙa mishi
A lokacin da zai amsa sai da hannun su ya taɓa na juna, da sauri ta janye nata hannun jin wani abu ya tsarga mata wanda har ta so ta zubar da coke ɗin
Yayi saurin riƙe Cup ɗin yana sakar mata wani banzan kallo wanda ya sa ta lokaci ɗaya ta sauke kai ƙasa jikin ta ya fara rawa. Tsaki yaja yana miƙe wa tare da Cup ɗin a hannun sa ya koma kan kujera, sai da ya ɗaura ƙafa ɗaya a kan ɗaya kafin ya soma sha yana kallo
Daƙyar Maimuna ta ci gaba da cin abincin duk ta gama takure wa. Suna gama wa ta kwashe komi ta nufi kichen Baby na biye da ita a baya. Sai da ta wanke komi sannan suka fito, ɗaki ta wuce ita kuma Baby ta koma wajen ABUL KHAIRI suna ci gaba da kallon su
Sai da aka kira sallan la'asar kafin ya ce, "ta je wajen Maimuna tayi mata alwala". Shi kuma ya wuce ɗakin sa ya ɗauro nasa alwalan ya wuce masjid.
Da motan sa ya tafi shiyasa ya wuce yayi musu siyayyan kayan fruit da gashashshen kaza, ya haɗo wa Baby da su chocolates da zata riƙa tafiya da su school sannan ya dawo gida.
Ganin babu kowa a Parlour sai ya wuce ɗakin Maimuna kanshi tsaye, da sallama a bakin sa ya shiga
Wanda lokaci ɗaya kamar an firgita Maimuna ta tashi daga kwancen da take a saman gado sun kifa ciki tana koya wa Baby Home work, Kallon da yake mata yasa ta duƙar da kanta duk jikin ta rawa yake yi zuciyar ta na bugu
Sai da Baby ta rungume shi sannan ya ɗauke kai daga kallon ta yana bin Babyn da kallo, sai kuma ya mayar kanta ya ce, "Zo ki amsa".
Da sauri Maimuna ta sauko daga kan gadon don ta san da ita yake yi tunda ta ga ledojin hannun nasa, by mistake ta ɗago kai ta kalle shi ta ga har yanzu ita yake kallo, wannan karon harara ya dalla mata yana sake tamke fuska, hannun ta na rawa ta saka ta amshi ledan
Saurin haɗa wa da hannun ta yayi da ledan da ta riƙe yayi mata riƙon da dole sai ta ji zafi
Da sauri ta ɗago kanta tana kallon shi
Ya sake sakar mata wani irin kallo me haɗe da gargaɗi, a hankali ya furta, "muddin baki dena nuna firgitan nan naki ba zan koya miki hankali wlh". Daga haka ya zame nasa hannun yana jan Baby da ta kafe su da ido
A sage ta ja ƙafafuwan ta ta bar ɗakin tana me haɗiye kukan da ya taho mata, "shin ya zata yi da ranta? Bata san meyasa take firgita haka ba duk idan ta ganshi? Meyasa be gane wa ne?". Sai da ta fita Parlour sannan ta duba abubuwan dake cikin ledojin, sai ta saka fruits ɗin a cikin Fridge sannan ta wuce da Kazan kichen, sai da ta kai ta ajiye kafin ta ɗauki ledan Chocolates ɗin Baby ta nufi ɗakin ta
Suna nan a zaune, shi yana kan drowan gadon, Baby kuma na saman gadon ta manne a jikin sa, a haka ya ci gaba da koya mata Home work ɗin
Maimuna kanta tsaye ta wuce ta ajiye mata ledan don ta san na Baby ne tunda ana siyan mata ko a gida, sai ta juya ta fice don baza ta iya sama a ɗakin ita da shi ba
Bata daɗe da fita ba ya fito riƙe da hannun Babyn tana ɗauke da book ɗin ta, wajen Maimuna ta nufa shi kuma ya wuce nasa ɗakin
"Aunty ya ce ki ƙarisa min Home work ɗin". Cewar Baby tana zama gefen Maimunan
"To". Kawai ta ce mata ta amshi book ɗin ta ci gaba da koya mata yanda zata yi.
Bayan sun gama ne ta wuce kichen don ta nema musu abincin dare tunda lokacin kusan ƙarfe biyar da rabi ne, ganin ya ci abincin ɗazu shiyasa ta zaƙe yanzu ta soma shirya lafiyayyen abinci. Tare da Baby suke ta kai komon su cikin Kichen ɗin har ta gama komi wajen goshin magriba, don lokacin har wasu masallatan sun soma kiran Sallah, shinkafa da miya tayi musu, ta sake ɗumama gasashshen kazan tare da musu zoɓo me daɗi sosai, a lokacin har yayi sanyi don ta saka a Fridge, ta kwashe komi ta kai dainning ta shirya
Lokacin ABUL KHAIRI ya fito daga ɗaki ya wuce masallaci
Ita kuma Maimuna ta ja hannun Baby suka wuce ɗakin ta suka yi nasu sallan a can, sai da suka idar ne ta kira Mamy suka gaisa gaba ɗaya mutanen gidan, sannan ta ba ma Baby wayan tana ta musu shirmen ta; ita kuma ta shiga Toilet yin wanka.
Bayan ta fito ta amshi wayan ta sannan ta je ta yiwa Babyn wanka, ta ɗaura mata towul a jiki tunda babu kayan ta a ɗakin, ita kuma ta zira doguwar riga ta sa Hijab ta tayar da Sallan Isha'i. Baby na biye da ita don itama tuni ta saka nata hijabin a kan towel ɗin.
Suna idar wa ta cire rigan ta mayar da towel ta koma gaban mirror tayi shafe-shafen ta
"Nima aunty kiyi min kwalliya". Babyn tafaɗa sanda ta manne a jikin ta
"Nima ba kwalliya nake yi ba Auta na, kuma kin san dare ne idan kika yi barci zai caɓe miki a fuska".
"To nima ki saka min irin ƙamshin ki ina so".
"To zan saka miki bari in gama". Maimunan ta bata amsa tana ci gaba da abinda take yi
Sai kallon ta take yi Babyn sai kuma tace, "Aunty wai yanzu ke matar Yaya ce ko?"
"In ji wa ya faɗa miki?" Ta tambaye ta tana tsayar da abinda take yi
"In ji su Mamy mana, sun ce min yanzu nan ne gidan ki dana tambaye su ina kuke ranan nan? Shi ne suka ce min kuna gidan ku, amma aunty Nima Ina son ayi min aure ayi min irin gidan nan".
"To ai ba a yiwa yara aure sai kin girma". Maimuna tafaɗa tana dariya
"Allah na girma, kinga ai da kaɗan Yaya Amir ya girme Ni ko?"
"Eh haka ne".
"To ayi min aure da Yaya Shureim Ina son sa".
Waro ido Maimunan tayi tace, "kee. Waye ya faɗa miki ana ma irin ku aure? Ai sai kun girma, kar in sake jin kin faɗa kinji?"
"To Aunty, ki saka min kaya na".
"Ok bari in gama shafa miki man sai ki ɗauko a ɗakin Yaya".
"To".
Sai da ta gama mata kafin tace mata, "ta je ta ɗauko".
Tana fita itama kuma ta tashi ta zare hijabin jikin ta ta nufi gaban sif ɗin ta ta soma duba wanda zata saka, doguwar riga ta ciro na barci me ɗan kauri
Tana shirin zame towel ɗin ne ABUL KHAIRI ya shigo ɗakin riƙe da hannun Baby
Da sauri ta riƙe gam tana zare idanu lokaci ɗaya ta firgita sai ga ta a ƙasa a durƙushe
Da kallo kawai yake bin ta da shi kamar wanda zai cinye ta, saurin janye numfashin sa yayi yana sake tsare ta da ido, sai dai tuni ya sake ɗaure fuska yana faɗin, "uban meyasa kika aike ta ta ɗauko kaya ke baki da ƙafafu ne?"
Shiru Maimuna tayi kanta a ƙasa zuciyan ta na bugun uku-uku
"Ba dake nake yi ba?" Ya daka mata tsawa
"Kayi haƙuri don Allah".
Tsaki yaja yana faɗin, "tashi mu je ki gyara mata tunda ke kika aike ta ta zubar. Tashi mana".
Da sauri ta tashi sai dai ta kasa motsa wa, ganin kallon da yake mata baki na rawa ta ce, "um.. dama zan saka kaya ne".
"Wuce dalla uwar me kike da shi da zaki ɓoye min?" Yayi maganar a zafafe yana nuna mata hanya
Da sauri ta wuce lokaci ɗaya hawaye na sauko mata
Shima bin bayan ta yayi idanun sa a jikin ta suka shiga ɗakin nasa.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 33*
*________* Duk inda tabi yana bin ta da ido a sace har ta gama kwashe mata kayan ta mayar a akwatin
Ita kanta a takure take amma babu yanda zata iya, but ji take yi kamar tayi ta kurma ihu sabida a yanda take
Har ta gama zata fice da sauri ya tsayar da ita da faɗin, "shirya ta a nan ki wuce da akwatin ɗakin ki".
Babu yanda ta iya ta amsa mishi da sauri tana zuwa har gaban sa ta ja hannun Babyn, ji take yi kamar ta nitse sabida yanda ta kama shi yana kallon ta, da sassarfa ta isa gaban akwatin ta soma shirya ta
Babyn na mata ƙorafin, "ga kayan da take so a saka mata".
Amma ina ko jin ta ba ta yi, burin ta kawai ta bar ɗakin. Tana gama wa ta fice jaye da akwatin, kai tsaye ɗakin ta ta shige tana sauke numfashi, "oh Allah na kunya zata kashe Ni". Goshin ta ta kama tare da matse wa tana jin zuciyar ta kamar zata faso ƙirjin ta tsaban buguwan da take yi, ta jima a haka daƙyar ta daidaita nutsuwar ta kafin ta isa ga kayan ta ta saka, har da ƙara wa da hijabi don baza ta iya fita haka ba, kunya bazai bar ta ba, da ba don akwai Baby ba babu abinda zai saka ta sake fita, abincin ma ta yafe baza ta ci ba, shi kuma idan ya ci don kansa, ta san ko ta zauna ƙila zai kira ta ko don Baby. Tana fita kuwa ta gan su zaune a Parlour
Shi ya kwantar da kansa saman kujeran idanuwan sa a lumshe
While Baby na gefen sa tana masa surutu tare da danna Remote
Kallo ɗaya tayi musu ta kau da kai ta nufi Kan dainning, sai da ta zauna kafin ta ƙwala wa Babyn kira, "ta zo ta ci abinci".
Da sauri ta taso ta zo ta zauna itama a saman dainning ɗin. Har suka gama be taso ba yana a yanda yake
Maimuna gyara wajen tayi sannan ta wuce ɗakin ta
Ita kuma Baby wajen sa ta koma tana ta zuba mishi surutun da ba ta gajiya
Sai a lokacin ma ya samu ya tashi ya isa kan dainning ɗin ya ci abincin, bayan ya gama ya dawo parlour'n lokacin har Baby tayi barci, ɗaukan ta yayi ya nufi da ita ɗakin Maimuna
A time ɗin itama har barci ya soma fizgarta taji motsin shigowan su, da sauri ta buɗe ido tana ware su a kansa
Haɗa ido suka yi amma be ce mata komi ba illa ɗauke kansa da yayi ya ajiye Babyn saman gadon ta sannan ya fice, shima ɗakin sa ya wuce yayi shirin barci ya kwanta, gaba ɗaya ya kasa barcin sai juye-juye yake yi, duk idan ya rufe idanu surar Maimuna yake hango wa ya rasa ya zai yi ya kauce wa hakan, ba ƙaramin dauriya yayi ba da iya danne kansa a yau ɗin, amma kuma ba ya jin zai iya jure irin wannan rayuwan Gaskiya, wata zuciyan tace mishi, "to wa yace ka jure dama? Matar ka ce fa babu wanda zai hana ka zuwa gare ta, gwara ma ka cire komi a ranka ka je ka more auren ka, ai biyan buƙatan ka a wajen ta ba hakan ke nufin kana ƙaunar ta ba tunda matar ka ce ta sunna, kuma akwai haƙƙin ta ma a kanka". Mirgina wa yayi yana me kifa cikin sa tare da matse filon da ya riƙe, tunanin yanda zai iya fuskantar Wannan matsalan tasa yake yi amma ta ya ya? Taya zai iya zuwa wajen ƙanwar bayan-bayan sa domin biyan ɓukatan sa? Wannan ai raini ne ma, "kai amma wlh an cuce Ni, da ace wata ce ko ba na son ta sai na je gare ta". Yayi maganar a fili cike da haushin abinda iyayen sa suka yi masa na haɗa sa aure da Maimuna.
A wannan daren dai daƙyar ABUL KHAIRI ya iya yin barci wanda har ya so ya makara da safe, a lokacin da ya gama shirin sa ya fita Parlour har Maimuna su ma sun gama nasu, sun yi Breakfast sannan ta zuba wa Baby wani a coolar
Tana ganin ya fito tayi saurin gaishe shi
Be amsa ta ba don mugun haushin ta yake ji, hannun Baby kawai ya riƙe suka fita tare
Itama Maimunan sai ta tashi tabi bayan sa duk ranta babu daɗi ganin be yi break ba, kuma ta haɗa masa abubuwa duk dan ta faranta masa. A baya ta zauna ganin Baby a zaune a gaban
Be ce mata komi ba ya ja motan suka wuce, yana sauke su ya wuce abin sa ko magana ya ƙi yayi, sai ɗaga wa Baby hannu da yayi.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Wani mugun kallo Umma Sulaima ta sakar mata, cike da jin haushin ta tace, "amma wlh yanzu na san cewa ban yi dacen haihuwa ba Azeeza, yanzu dan uban ki duk abinda ya faru hakan be zamar miki ishara ba a kan ɗan iskan yaron can ba? To wlh ki ji da kyau da Baban ki zan haɗa ki bari ya shigo".
Kumbura fuska Azeeza tayi da cewa, "To Umma tsoron sa nake ji ne kin daɗe baki faɗa ba, wlh a kan ABUL KHAIRI sai dai idan ki kashe Ni amma bazan taɓa dena son sa ba, kuma na rantse da Allah sai na aure sa".
"Kan kutmar uba.. Ni kike cewa haka ko Azeeza? Wuyan ki har ya kai kaurin da zaki na faɗa min magana son ranki ko?" Sai ta kaɗa kai kawai tana ci gaba da tankaɗen garin ɗan waken ta
Kakar su dake zaune a bakin ƙofan ta duk tana jin abubuwan dake faruwa tace, "to ban da abin ki Sulaima mene ne aibun ta don ta so ɗan uwan ta? Ina ganin ai bata da wanda ya fi shi a yanzu, ke yanzu ba arziƙin ki bane Azeeza ta shiga cikin gidan nan mu dangwali arziƙi?"
"A'a Umma ki dena cewa fa arziƙi na, Ni tunda nake abun hannun Deebiza be taɓa tsole min idanu ba, wannan kuma sai ke da ɗan ki ku ne mayu amma ba Ni ba".
Shiru kawai Kaka tayi domin ta kasa magana ma, ta san abinda ya fi haka ma Umma Sulaima zata faɗa mata tunda bata gaji mutunci ba, iyayin ta ne ma yasa har ta tsulmiya musu baki a kan zancen su
Azeeza dake bakin rijiya zaune tana cuɗa wankin ta ta ɗago kai tana fito tare da dariyan shaƙiyanci tace, "Kaka kema me ya kai ki yin mata magana kin san ba shiri kuke yi ba? Ni dai tunda kina goyan baya na kawai idan Baba ya shigo ta faɗa mishi kika ga zai min faɗa, to ki ɗau mataki akai shi ne kawai abinda zaki iya min".
"To ai shikenan, bari ya shigo ɗin".
Dogon tsaki Umma Sulaima taja tana hararan Azeezan sai dai bata ce komi ba taci gaba da abinda take yi.
Suna a haka sai ga Uncle Sani ya shigo gidan
Babu wanda ya fara magana sai Azeeza da cewa, "Baba dama ina so muyi magana ne".
"To ƴar Baba Ina jin ki lafiya dai ko?" Yayi maganar yana dakata wa daga shiga ɗaki
"Baba a kan maganar ABUL KHAIRI ne, Ni gaskiya har yanzu na kasa haƙura da shi". Sai kuma ta soma hawaye tana ci gaba da faɗin, "haba Baba ya za'a yi ace ya yi aure amma a kasa sanar dani har sai da na dawo? (Dayake ta je Jigawa wajen ƙanwar Baban ta Halisa) Ni wlh Baba wlh na kasa cire sa a raina, ina ƙaunar sa, idan ba'a aura min shi ba na rantse da Allah zan bi duniya".
"To ka ji ko Sani sai kayi me yiwuwa tun kafin ɗiyar ka ta bi duniya, idan kuma hakan ta faru wlh Ni da kai ne". Inji Kaka kenan cike da fushi
"To Umma ya kike so inyi kina ganin dai yanda mutanen nan suka ci mana mutunci, wanda ba don Allah ya so ba da tuni ita Azeezan tana can a garƙame a gidan kaso an ɗaure ta a kan laifin da ba ita ta aikata ba, ƙiri-ƙiri Deebiza ta nuna mana bambanci a tsakanin mu, yo dama tun ba yau ba na san da haka ba mutunci ne da ita ba, tana ganin ta fi ƙarfin mu shiyasa, taya kike ganin ma zata bari ɗan ta ya auri ɗiya ta tunda ita ƴar matsiya ta ne? Gwara ma tun wuri ki haƙura tunda dai shi yayi aure hakan zai fi miki kwanciyar hankali".
Kuka sosai Azeeza ta saki tana miƙe wa tsaye tace, "yanzu Baba ka fi so in bi duniya a kan kaje ka nema min auren sa? Ni na yarda wlh zan zauna da shi ko mata uku ne da shi".
Umma Sulaima zagi ta ƙunduma mata tana faɗin, "saboda ke mara hankali ne mara tunani ina kika taɓa jin uban yarinya ne zai je neman aure gidan na miji? Kuma da kike cewa zaki bi duniya dama a kanki farau ne? Ai kafin ki yi nima nayi kinga kuwa tarihi sai ya maimaita kansa".
A lokacin Kaka ta fashe da kuka tana cewa, "kaico na wlh! kaicon hali na!! ki yafe min Deebiza tabbas alhakin ki bazai taɓa rabuwa da Ni ba, ga shi yanzu na cuci kaina na fitar da ke gidan ɗana kin je kin auri wanda ya fi shi, ƙazafin da muke miki kuma gashi shi Sani ya auro mana alaƙaƙai ta gurɓata mana gida, wai uwar arziƙi ne take cewa ɗiyar ta taje ta shiga duniya? Sani ka cuce mu wlh". Ta sake fashe wa da wani sabon kukan tana face majina
Umma Sulaima tace, "Oho dai can ta matse miki, in dai Ni ce na zame muku ɗuwawu dole ku zauna da Ni, kuma da kike ce min alaƙaƙai ai zamu je ne ya tarar da muje mu".
Shi dai Uncle Sani tuni ya shige ɗaki abin sa don ya san halin su idan suka fara fitinan nan nasu ba bari za su yi ba, shi kanshi Umma Sulaima ba ƙyale shi take yi ba bare yace zai shigar ma mahaifiyar sa, yanzu ne ma kura tayi lafiya.
Ai kuwa dai ko da ya shige Umma Sulaima bata yi shiru ba sai habaici take yiwa Kaka tana gaya mata magana
Ita ce dai tayi shiru ta ƙyale ta
Azeeza kuwa gurzan wankin ta taci gaba da yi har da saka waƙa a waya jin surutun Umman nata ya ishe ta, ta ƙure ƙara kuwa tana yi tana cashe wa
Sai kuma Umma Sulaima ta koma kan Azeezan sai ƙunduma mata zagi take yi tana la'antan ta
Amma ko ci kanki bata ce mata ba
Dama duk abinda kayi dole za'a maka, Umma Sulaima bata yi la'akari da abinda take ma uwar wasu ba shi ne ɗiyar ta take mata ba. A juri zuwa rafi dai...
Azeeza na gama wankin ta ta yafa gyale ta bar gidan, kai tsaye gidan Gwaggon su Maria ta wuce, tana shiga ta kwaɗa sallama tana kutsa wa cikin ɗakin su
Ɗiyar ta Ummi dake zaune tana yankan ƙumba a saman kujera ta amsa mata tana cewa, "oh Azeeza idanun ki kenan?"
Sai da Azeezan ta zauna kafin tace, "ke ba wannan ba ina Gwaggon take?"
"Yanzu ta fita ta je kasuwa".
"Ok me kuka dafa yau? Wlh bazan iya cin ɗan wake ba shi Umma tayi mana, kuma Ni ban da kuɗin siyan wani abu".
Ummi na dariya tace, "mu ma nan ai ba wani abu me daɗi muka yi ba, tuwo ne idan zaki ci".
"Eh sawo min, ai gwara shi wlh a kan wancan ɗan waken. Kin san Ni ba na shiri da shi".
"Ai kuwa Ni ina so, bari in aika a amso min rabon ki". Ummin tafaɗa tana fice wa. Kichen ta nufa ta sawo mata a Plate ta dawo ta miƙa mata
Tana zama ƙanwar ta ta shigo ɗakin tana faɗin, "laa Aunty Azeeza ke ce?"
Gyaɗa mata kai kawai tayi don ta rigada ta fara saka loman tuwo
Ummi tace, "yauwa Ruƙayya amso min Ɗan wake mana gidan su Azeeza".
"To Ni kuma fa zaki tsanmin?"
Sai da ta harare ta kafin tace, "Eh".
"A'a ba fa maganar harara bace, don wlh bazan amso ki hana Ni ba".
"Dalla ki je zan baki".
"To shikenan Aunty Azeeza kina shaida ko?"
"Eh".
Daga haka Ruƙayya ta kaɗa kai ta fice.
Ummi ta kalli Azeezan tace, "Wai ina Yaya Salihi ne kwana biyu ya dena zuwa gidan nan gaba ɗaya. Ko dai yayi tafiya ne?"
"Mtwssw tafiyan ƙaniya! Yana can dai yana sheɗanantan sa, nima yau ban saka shi a idanu na ba domin kafin in tashi ya bar gidan." Azeeza ta bata amsa.
Ruƙayya na dawo wa da ɗan waken
Ummi ta amshe tana faɗin, "ya naga ɗan waken ɗan mutsulu ko dai kin cinye a kan hanya?"
"Uwar na cinye ne, ki dube Ni da kyau kinga mai a baki na ko a hannu na?" Ruƙayya tafaɗa tana hararan ta
"To gaskiya Ruƙayya sai dai kiyi haƙuri in cinye wannan, kin san na fi ki son ɗan wake kuma bazai ishe mu ba".
"Ni don Allah idan zaki bani ki bani ba na son surutu, riƙe wannan kwanon ki zuba min".
Ummi dai bata ce komi ba ta amsa ta zuba mata kaɗan bayan tayi ƙwafa
Ita kuma ta wafce kwanon tana zama a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin da cewa, "gobe ma rana ne ai dani kike zancen".
Azeeza dake kallon Ummi tace, "ara min gyalen nan naki me ruwan madara don Allah".
"Ina zaki je?"
"Uhm gidan Ya ABUL zan je".
"Don Allah fa? Wlh ina ta son Nima in Koma in ga gida tunda ban je ba amma har yanzu ban samu dama ba, da Mama zata dawo yanzu ai da mun tafi tare".
Ruƙayya tace, "nima zan bi ki don nima ina son zuwa".
"A'a ba dai Ni ba, Ni kaɗai nake son zuwa, ɗauko min gyalen in tafi don Allah". Inji Azeezan tana fice wa. Wanke hannu tayi ta dawo, lokacin Ummi ta ɗauko mata gyalen; ta amsa tayi musu sallama ta fice. Kai tsaye gida ta wuce, tana shiga taga ruwa a kan murhu ta ɗauki bokiti ta sake ta kai bayi, ɗakin ta ta koma ta tuɓe kayan ta ta faɗa bayin. Wanka ta sillo ta fito ta koma ɗaki, nan ta soma shirya wa bata damu tayi sallah ba, ita shaf ta manta sai da ta caɓa kwalliya a fuskar ta sannan ta tuna, sai ta taɓe baki a fili tace, "idan na dawo na haɗa da sauran inyi". Tana gama wa ta shirya cikin doguwar riga me hannun fanka, sosai rigan ta ɗauki jikin ta sannan ta matse ta ainun, tayi kyau sosai domin sai maƙiyi zai kalle ta ya kushe ta, dama Azeeza ba baya ba wajen kyau shiyasa take gara kan Samari yanda take so, sai dai duk ba wanda take so ta aura sama da ABUL KHAIRI, ga shi ita kuma ba ta gaban shi ko kaɗan.
Sai da ta fito zata fice ne Umma Sulaima dake bakin murhu ganin an ɗibe mata ruwa ta soma masifa tana aiko tsinuwa ga duk wanda ya kwashe mata, ai kuwa tana ganin Azeeza ta fito daga ɗaki taci uwar wannan kwalliyan ta tabbatar ita ce sai ta koma kanta tana zagin ta, "shegiya matsiyaciya in zuba ruwa dan ke mara mutunci ne ki ɗebe sannan ki kasa zuba min wani ko?"
Yamutsa fuska Azeezan tayi tace, "kai Umma wai a kan na ɗiba ruwa ne kike ta wannan masifan har maƙota suna jin ki? Shikenan yanzu dai sauri nake yi amma idan na dawo zan zuba miki kar ki damu". Ta taka tayi bakin ƙofa zata fice
Umma Sulaima tace, "Allah yayi wadaran halin ki ke dai, saboda na miji kin zama kamar karya, insha Allahu idan ma kika je sai ya sauke miki baƙin halin nan nashi a kanki".
Bata kula ta ba ta ƙarisa fice wa a gidan, har da saka hannu cikin jakan ta ta ɗauko chewing gum ta jefa a baki ta soma tauna.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 34*
*________* Me Keke napep na sauke Azeeza a bakin Gate ɗin gidan ABUL KHAIRI ta sauka ta biya sa kuɗin sa, ta gyara ma jakan ta zama tayi bakin ƙofan, Nocking tayi kafin me gadi ya leƙo, tace da shi, "Masu gidan na nan?"
"Suna nan. Lafiya dai?"
"Ƙalau. Buɗe min in shiga wajen me gidan na zo".
"Amma Malama ai kin bari in shiga in Yi musu bayani ko?"
Tsaki taja tana hararan sa tace, "dalla buɗe min ƙofa ko ka ga nayi maka kama da masu satan mutane ne?"
"To wa ya sani abu a duhu a dunƙule a baƙin leda?" Shima ya faɗa yana matsa mata a hanya
"Kai Ni fa ba na cike da iskanci, ka kama kanka tun kafin ka shiga gona ta wlh, don billahil lazi sai in maka sanadin da zaka bar gidan nan, banza kawai a jawo".
"Can ta matse miki shegiya". Yayi maganar ƙasa-ƙasa
Ita kuwa dogon tsaki taja tayi ciki abin ta. Tana zuwa bakin ƙofan shiga gidan ta tura ƙofan, amma jin a rufe ne sai ta soma Nocking.
A Parlour'n Baby CE kawai a zaune tana buga Game da wayan Maimuna
Ita kuma Maimunan tana kichen tana silale musu farar shinkafa da miyan jiya da ya rage, dayake dawowan su kenan shiyasa take son sama musu abinci
Jin ana Nocking da gudu Babyn ta tashi ta nufi ƙofan ta buɗe
Azeeza washe baki tayi tace, "Babyn mu ke ce?"
"Yeee Aunty. Sannu da zuwa". Babyn tafaɗa tana me rungume ta
A time ɗin Maimuna har ta fito daga kichen don duba waye ne? Ganin Azeeza tsaye Baby rungume da ita sai ta tsaya a wurin ta kasa motsa wa tana kallon ta
Azeeza shigo wa tayi ta rufe ƙofan kafin ta bi Maimunan da kallo
Sai a lokacin Maimunan ta yafa wa fuskar ta fara'a tana mata sannu da zuwa
Ɗauke kai tayi a kanta tabi parlour'n da kallo tana me taɓe baki, sai kuma taja hannun Baby suka yi kan kujerun ta zauna tana ɗaura ta a kan jikin ta. Ta kalli Maimuna da har yanzu take tsaye a wurin tace, "Ina shi Yaya ABUL KHAIRIN wurin sa na zo?"
"Yana ciki". Ta amsa mata cikin sanyin murya
"To ki kira min shi".
Bata yi musu ba tayi hanyar ɗakin ABUL KHAIRI, Nocking tayi kafin ta tura ƙofan da sallama ta shiga
ABUL KHAIRI na kwance a kan gadon sa daga shi sai dogon wando yayi kifa ciki tare da ɗaura kansa a kan pilow, idanun sa a lumshe suke tamkar me barci, be buɗe su ba duk da ya ji sallaman Maimunan
Ita kuma ganin sa a haka da sauri ta duƙar da kanta murya na rawa tace, "dama Aunty Azeeza ce ta zo sai tace in Kira ka".
Jin hakan sai ya buɗe idanun sa da suka sauya kala suka sake ƙanƙance wa a kanta, da kallo kawai ya bi ta fuskar sa a matuƙar ɗaure. Sai da ya gama ƙare mata kallo kafin ya mayar da su ya rufe
while Bata san ma Yana yi ba domin kanta a ƙasa yake. Jin yayi shiru sai ta ɗago kai tana kallon sa, "ko dai barci yake yi?" Tayi maganar a fili tana sake leƙen sa
Sai ya buɗe idanu kawai suka haɗa ido
Da sauri ta sad da kanta ƙasa cikin ruɗe wa har ƙafafuwan ta rawa suke
"Out". Yayi maganar a maƙoshi fuskar sa a haɗe
Juya wa tayi da sauri ta fice tana rufo masa ƙofa, sai ta tsaya a wurin tana dafe ƙirjin ta kamar wacce tayi gudun tsere
"Ke ina yake?" Cewar Azeeza da ta hange ta
Shiru Maimunan tayi don bata san me zata ce mata ba
"Ba dake nake yi ba? Kar fa kiyi tunanin don kin aure shi kina da wani matsayi ne a gidan nan, da ke da banza duk ɗaya..." Maganar nata ne ya ƙage sanda taga ABUL KHAIRI ya buɗo ƙofan ya fito yana sakar mata wani banzan kallo
Hakan yasa itama Maimuna ta juya ga bayan ta ta ganshi, da sauri ta janye idanun ta ta soma taka wa zata wuce kichen
Shi kuma tuni ya tako ya isa kan kujera ya zauna a wanda yake kallon Azeeza. Sai ya mayar da kallon sa ga Maimuna da har ta kusa shige wa kichen ya kirayi sunan ta
Cak ta tsaya tana juyo wa ta sauke idanun ta a kanshi, duk da ta san sunan ta ya kira amma tsaban ruɗe wa don bata taɓa jin ya kira ta da sunan ta ba, sai tace masa, "na'am Ni kake kira?"
Kafe ta yayi da ido kamar bazai yi magana ba, sai kuma ya gyaɗa mata kai yana me lumshe idanun sa
Kamar an tsamo ta daga ruwan zafi haka take tafiya har ta ƙarisa wajen sa kanta a ƙasa
"Yaya ina ta gaishe ka baka amsa ba?" Inji Azeeza tana tauna chewing gum cikin salon son burge sa domin ta dawo da hankalin sa kanta, don ta ga ba ta ita yake yi ba
Be kalle ta ba ya sanya hannu ya jawo Maimuna yana zaunar da ita kan cinyoyin sa
A take ita da shi numfashin su ya ɗauke sabida abun da ya ziyarce su daga ƙasar ƙafafuwan su har ƙwaƙwalen su. Lokaci ɗaya ya lumshe idanun sa yana me tamke bakin sa. While ita kuma tsaban ruɗe wa har suman wucin gadi tayi don ta kasa gasgata itan ce a zaune a saman cinyan sa
Azeeza kuwa tsaban tashin hankali bata san sanda ta zabura zata yar da Baby dake jikin ta ba
Ai da sauri ita ta tashi da kanta tana zama dirshan a ƙasa tabi Azeezan da ido
Hannayen sa ya sanya ya zagayo da su a jikin Maimunan yana me ƙara ƙanƙame ta, daƙyar ya iya buɗe idanun sa da suka sake ƙanƙance wa ya kalli Azeeza fuska babu fara'a yace, "What did you come to do at my house?"
Kasa magana ma tayi tsaban baƙin cikin ganin Maimuna a jikin sa
Shi kuma ganin hakan sai ya saki killer smile yana sake matso da kansa kusa da kunnen Maimuna. Ganin tana mutsu-mutsu duk ta gama diririce wa a hankali yace da ita, "KE ba na son muna-furci ki kama kanki".
Tsit Maimuna tayi tana ƙara lafe wa a jikin sa idanun ta a rufe ruf
"Ehem ina jin ki, me kika zo min a gida?"
Daƙyar ta iya danne baƙin kishin da take ji tace, "amma da kai kaɗai nake son magana".
"Ok da Ni kaɗai? To yanzu Ni da wa kika gan ni?". Sai ya kamo hannun Maimunan yana matse shi cikin nasa yace, "ita mata ta ce, sai kuma Baby dake wurin, you can say whatever you want. Baby come here". Ya ƙare maganar da kallon Baby
Baby dake zaune dirshan a ƙasa tana kallon su da sauri ta tashi ta yo wajen sa ta zauna, tare da jingina jikin ta a nasa ta manne sa
"Ok I hear you".
Babu yanda ta iya Azeeza cike da haushin Maimuna ta kalle ta ta galla mata harara duk da kuwa ita ba ganin ta take yi ba, domin har yanzu ta kasa buɗe idanuwan ta, "Yaya How did you get married I don't know?"
Wani kallo ya sakar mata kafin yace, "Who are you and until I get married I will tell you?"
"Because Ni Masoyiyar ka ce, kuma ko ba komi Ni ƙanwar ka ce Yaya ABUL, be kamata ka wulaƙanta Ni ba, ina son ka Yaya, meyasa Ni baka aure Ni ba sai ita? Ai da Ni ka dace tunda ka rasa wacce kake ƙauna".
Tun soma maganar ta Maimuna ta buɗe idanun ta tana me ɗago kai tare da kafe ta da idanu
While ABUL KHAIRI ganin haka sai ya saka hannayen sa ya riƙo fuskar ta tare da juyo da fuskar tana kallon sa, ido cikin ido suke kallon juna kana yace, "Wai haka Wifey you agree we are not compatible?"
Ƙifƙifta idanu ta soma yi, sai kuma ta daure ta tsayar da su a cikin nasa kamar yanda shima yake bin ta da kallo, ta so ta jure abinda take ji amma ina tuni ta mayar da su ta rufe ruf
Ganin haka yasa ya hura mata iska. Tana buɗe ido ya sakar mata murmushi yana me ɗage mata gira, "You are silent. Are you ok?"
Gyaɗa masa kai tayi don ta kasa ma magana
Matso da fuskar sa kusa da nata yayi har yana ɗaura mata bakin sa a kan kuncin ta, a hankali ya furta, "wlh idan na sake magana kika yi min shiru zan baki mamaki". Ya ƙare maganar yana me ɗago kai still fuskar sa yalwace da murmushi, sai kayi tunanin wani abun kirki ya faɗa mata
Ita kuwa Azeeza kasa jure wa tayi ta ɗauki jakan ta da gudu tayi bakin ƙofa hawaye na kwaranya a fuskarta
Da kallo ya bi ta har ta fice. Sai lokaci ɗaya ya ɗauke murmushin nasa yana bin Maimuna da kallo da kanta ke ƙasa. Har ya buɗe baki zai yi magana sai ya tuna da Baby a wurin, hannun sa ɗaya ya saka ya ɗaura a kan Babyn, kana kuma ya ƙara matso da bakin sa kusa da kunnen Maimuna ya raɗa mata, "dalla tashi min a jiki Bagidajiya".
Kafin ma ta tashi tuni hawaye sun cika mata idanu, daƙyar ta iya motsa wa ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi ɗakin ta, tana shiga ta faɗa kan gadon ta da gudu ta soma kuka, bata san meyasa ba sosai taji haushin kalman da ya faɗa mata, shiyasa kawai taji kukan ya taho mata kuma baza ta iya riƙe sa ba
Baby ne ta shigo ɗakin tana faɗin, "Aunty Yaya ya ce ki zo ki duba girkin ki".
Sai a lokacin ma ta tuna ta aza shinkafa, da sauri ta ɗago tana me share hawayen ta a ɓoye, ta miƙe ba tare da ta kalli inda Babyn take ba ta fice, ita kuma tabi bayan ta
Yana zaune a parlour'n be tashi ba, sai dai yanzu wayan sa yake danna wa
Maimuna ko kallon inda yake bata yi ba tayi kichen da sauri kamar ana ingiza ta
Da kallo yake bin ta har ta shige, sai ya taɓe baki yana mayar da idanun sa ga Baby da ta zo ta zauna gefen sa tana mishi surutu, biye mata yayi yana ci gaba da latsa wayan sa.
Maimuna tana shiga kichen ɗin ta duba shinkafar ruwan da ta zuba har ya ƙone yana shirin ƙauri, dama dafa biyu tayi masa ruwan kaɗan ne a ciki wanda ta sauya, sai tayi sauri ta kashe gas ɗin ta kwashe shinkafan a coolar, ta sauke tukunyan kafin ta ɗauko miyan dake ajiye ta sake kunna wa ta ɗaura a kai don yayi ɗumi. Tana nan tsaye duk ta rasa me ke mata daɗi a jikin ta, gaba ɗaya ta rasa kuzarin ta jin ta take yi kamar har yanzu tana jikin ABUL KHAIRI, ƙamshin turaren sa duk ya mamaye mata jiki da hanci, rasa ma meye takamaiman abinda ke damun ta tayi, haushin sa take ji ko kuma haushin Azeeza ne da ta janyo mata har yace mata Bagidajiya ta kasa gane wa. Lumshe idanuwan ta tayi zuciyar ta na ci gaba da buga wa kamar wacce har yanzu take jikin sa, sai kuma ta buɗe su tana bin kanta da kallo a ranta tana tunanin, "meyasa yake ce mata Bagidajiya mene ne makusanta? Meyasa ba ya ƙaunar ta ne? Me tayi masa?" Tana son sanin, "shin meye aibun ta yake nuna mata tsana?". Janye tunanin tayi ta mayar da hankalin ta kan miyan, yana zafi ta juya ta kashe gas ɗin, ta ɗauki coolar ta sake shi tunda dama ɗan kaɗan ya rage, ta kwasa ta fita. Kai tsaye kan dainning ta nufa ta jera
Sai da ta gama wahalan jerawa kafin yace da ita, "ta kawo mishi nan".
Babu musu ta kwasa ta kai gaban sa, ta ajiye masa har ruwa da lemon Coke da tasan yana sha ko da yaushe, sai ta zuba mishi nashi a Plate sannan ta zuba wa Baby, ita kuma ta tashi ta nufi ɗaki
Da kallo ya bi bayan ta har ta shige kana ya mayar da idanun sa kan Baby dake wasa da wayan sa da ya ajiye, yace, "Ajiye wayan ki ci abinci".
Amsa mishi tayi ta ajiye tare da janyo nata ta soma kaiwa baki
Shima haka abincin ya soma ci a ransa kuma yana tunanin, "meyasa Maimuna ta tafi bata ɗibi nata ba?" Sai kuma ya taɓe baki a ran nasa ya sake cewa, "ita ta jiyo, idan yunwa ya illata ta zata fito".
Yana gama cin abincin ya shige ɗaki abin sa ya bar Baby zaune tana cin nata.
******
Ita kuma Maimuna tunda ta shiga ɗaki kwanciya tayi ta rufe idanun ta, duk abinda ya faru zuwan Azeeza komi ke dawo mata, ta rasa meyasa abun ya tsaya mata a rai, bata taɓa tunanin wai akwai ranan da ABUL KHAIRI zai bari ta hau jikin sa ba a yanda yake nuna mata rashin ƙauna. Saurin buɗe idanuwan ta tayi tana tashi zaune, a fili tace, "Oh me ke damu na? me zai sa hakan ya dame Ni bayan yayi ne don Aunty Azeeza." Sai taja tsaki tana tashi ta shiga Toilet, Bata jima ba ta fito tana koma wa ta zauna kan gadon, yunwa take ji sosai ga shi kuma ba ta ƙaunar ta zauna tare da shi tana cin abinci, hakan yana matuƙar takura ta baza ta iya ci gaba da jure wa ba. Tashi tayi kuma ta nufi ƙofa ta leƙa don ta duba ƙila ya gama ci, ai kuwa bata ganshi ba sai Baby dake zaune, da sauri ta fito ta nufi wajen tana tambayar Babyn, "ina yake?" Cikin raɗa
Baby ta faɗa mata, "ya shiga ɗakin sa".
Hakan yasa ta ɗan saki jiki ta zuba abincin taci. Tana gama wa suka wuce ɗaki don yin Sallan Asar da aka kira Yanzu.
Bayan sun idar book ɗin ta ta ɗauka ta soma karatu
Ita kuma Baby tuni ta fice Parlour wasan ta.
******
Koda ABUL KHAIRI ya je Masallaci yana dawowa mota ya ɗauka ya sake fita a gidan. Kansa tsaye gidan gonan sa ya wuce, me gadi yana buɗe masa Gate ya shigar da motan sannan ya fito, gaisuwar me gadin kawai ya amsa ya shige ciki. A kan sofa ya zauna yana sauke numfashi tare da lumshe idanuwan sa, shiru yayi na ɗan wani lokaci babu abinda ke dawo masa a rai sai rayuwar sa da suka yi da Ziyada a gidan. Duk tunanin ta ya addabe shi ya rasa ya zai yi, sai kawai ya tashi ya fita ya ja motan sa ya bar gidan, ko kaɗan yanzu ba ya iya zama a gidan duk da ransa na so, sabida kawai tuna Ziyada hakan ke sake ɗaga masa hankali matuƙa. Tuƙi yake yi gaba ɗaya babu kuzari a jikin sa, yana kaiwa gida ya fito ya shiga ciki. A kan Baby dake barci idanun sa suka faɗa, garin wasan ta barci ya kwashe ta a wurin. Janye idanun nasa yayi ya nufi ɗakin sa, har ya taɓa ƙofan zai shiga kuma sai ya fasa ya wuce ɗakin Maimuna.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 35*
*________* Murɗa ƙofan yayi ya shiga da sallama a bakin sa
Maimuna dake kwance a kan gado da littafin ta a hannu, ta ɗago idanu tana kallon sa ta amsa mishi sallaman tana tashi zaune da sauri
"Zo ki dafa min ruwan Lipton ki kawo min ɗaki". Yafaɗa sannan ya juya ya fice
Tashi tayi ta ajiye littafin ta fita, kichen ta shiga ta girka masa ruwan ta zuba a Cup ta fito, sai a lokacin ma ta hangi Baby dake kwance a ƙasa tana barci. Wuce wa ɗakin sa tayi ta bude ƙofan ta shiga bayan tayi sallama
Ba shi cikin ɗakin da alamu yana Toilet ne
Shiyasa tayi saurin ajiye masa ta fita, wajen Baby ta nufa ta ɗauke ta ta mayar kan kujeran, sai ta koma ɗaki taci gaba da karatun ta, bata jima ba ta tashi ta wuce kichen don nema musu abincin dare.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Azeeza kai tsaye gida ta wuce tana ta kuka
Tunda ta shiga gidan Umma Sulaima ta kalle ta sai ta hau mata dariya tana faɗin, "Allah na gode maka da hakan ta faru, kaɗan ma kika gani wlh muje zuwa".
Uncle Sani ne ya fito daga ɗakin sa jin kukan Azeezan na yawaita yake faɗin, "wai lafiya me ya faru ne Ƴar Baba me aka yi miki?"
Cikin kuka tace, "Baba ABUL KHAIRI ba ya ƙauna ta, gidan sa naje ya wulaƙanta Ni a gaban wancan shegiyar matar tasa, Baba wlh tallahi idan har be aure Ni ba mutuwa zan yi don Allah Baba ka taimaka min".
"Azeeza ya kike so in Yi ne? Taya zan saka ya aure ki bayan ba gani na da mutunci yake yi ba? Gwara ki haƙura ki samu wani ko wane ne zan goya miki baya amma ban dashi".
"Shikenan Baba tunda ba ka ƙauna ta, ai kana da hanyar da zaka bi domin ka ga ya aure Ni, ba damuwa tunda ka fi son in shiga duniya shikenan". Tayi maganar tana wuce wa ɗakin Kakar su
Bin Bayan ta yayi shima ya shiga yana kiran sunan ta
Kaka tace, "ka dai ji kunya wlh, idan har ka bari jika ta ta shiga duniya wlh Sani Ni da kai ne a gidan nan, tunda ita uwar ta ba ta ƙaunar haɗin kai meyasa baza ka goya mata baya ba tunda ta nuna tana son yaron nan? Aure fa ba wasa ba in kuma ka fin son shiga duniyar ai shikenan".
Ita dai Azeeza kuka take ta yi kanta a jikin Kakar tasu
Ita kuma tana rarrashin ta
"Shikenan zan je wajen Deebizan muyi magana tunda haka kike so ki zubar min da mutunci a wurin su".
"Yo ta zubar maka da mutunci ko dama tun tuni ka zubar da kayan ka? Ai ka bar shiri tun rani. Idan da ace Deebiza ba me kyakykyawar zuciya bace ba na tunanin zata sake kallon mu da idon rahama sabida abubuwan da suka faru a baya, ga shi ƙanwar ta ita ta ƙullace mu har yanzu ba ta mana kallon arziƙi, tunda tayi aure bata taɓa tako wa gidan nan da sunan gaishe mu a matsayin ƴan uwan ta ba. Hmm rayuwa kenan".
"Ni fa Umma har yanzu ba na tunanin na yiwa Deebiza wani abun da zai saka nayi nadama". Uncle Sani yayi maganar cike da fushi, kana kuma ya kalli Azeezan yace, "ki kwantar da hankalin ki ƴar Baba, muddin ina numfashi sai kin auri wanda kike so, ABUL KHAIRIN banza da hofi shi wane ne da har zai ƙi son ki yake son wulaƙanta ki? Ba abun murnan sa bane ma ace kina son sa? Da me ya fi ki da zai riƙa jan miki aji? Ki kwantar da hankalin ki goben Nan insha Allahu zan je gidan nasu in same Iyayen nasa kuma zamu yi magana".
Washe baki Azeeza tayi tana tashi daga jikin Kakar cike da murna tace, "yauwa Baba na na gode sosai, shiyasa na fi son ka a Kan Umma, na gode Baba".
"Ki dena min godiya kin ji? Wa nake dashi a duniya sama daku da zan kasa muku abinda kuke so? insha Allahu ABUL KHAIRI sai kin aure sa muna nan da ke".
Umma Sulaima dake waje tana sauraron komi tayi shewa tace, "hehehe yau ake yin ta, wahala ce bata ishe ka ba wlh muddin kace zaka biye mata".
Uncle Sani da ya fito ya shura takalman sa ya saka be ce mata komi ba ya wuceWar sa waje
Ita kuma sai habaici take musu tana faɗin, "ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta".
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
Jollof rice and veggies ta girka musu, sai ta haɗa musu kunun aya tunda duk tana da kayan haɗin. Sai da aka kira magriba ta gama komi ta shirya su a kan dainning
Har a lokacin Baby tana kwance tana barci bata tashi ba
Zuwa tayi ta tashe ta suka wuce ɗaki don yin alwala.
ABUL KHAIRI shima barcin ne ya kwashe sa tun sanda ya gama shan ruwan Lipton ɗin, sai da yanzu da yaji kiran sallah ya tashi ya shiga Toilet yayi alwala ya fito ya wuce masallaci.
Bayan sun gama sallan Kur'ani ta ɗauko musu suka yi karatun tare, har sanda aka kira sallan isha'i kafin su tayar suka yi, suna idar wa wanka ta shiga ta fara yi kafin ta yiwa Baby, ta shirya ta cikin riga da wando na Barcin ta, sannan ta iza ta Parlour ita kuma taci gaba da shirin ta, bayan ta gama itama ta sanya riga da wandon na barci masu santsi, sun lafe mata sosai a jiki kuma sun yi mata mugun kyau, hula ta sanya ta fita Parlour
A lokacin ABUL KHAIRI ya dawo daga masallaci suna zaune da Baby suna kallo. Fitowan Maimuna da ƙamshin turaren ta da ya bugi hancin sa shi ya jawo da hankalin sa gare ta, da kallo kawai yake bin ta ya kasa ɗauke ido a kanta har sanda ta dangana ga wajen dainning, sai ya lumshe idanu kawai yana saka hannun sa a goshi, tsawon lokaci yana a haka kafin kuma ya buɗe idon sa da suka soma kaɗa wa ya mayar kan Baby yace da ita, "get up and go eat".
Tashi tayi suka wuce kan dainning ɗin
Lokacin dama Maimuna har ta gama zuba musu tana shirin kiran Baby ne, ɗago kan da zata yi suka haɗa idanu tayi saurin janye nata tana zama kanta a ƙasa
Shima zaman yayi Baby ta Zauna a gefen sa da ya raba su
Abincin suke ci kowa yayi tsit
ABUL KHAIRI kansa na ƙasa sai cakuɗa abincin yake yi ya gaza ci, idan ya kai loma ɗaya sai ya jima kafin ya sake kaiwa bakin sa
Sai duk hakan ya saka Maimuna a tunanin, "ko abincin be masa daɗi bane?" Ta rasa yanda zata yi ta tambaye shi, dabara ya faɗo mata sai ta kalle sa tace, "Ko kana buƙatan wani abu ne?"
Ɗago kai yayi ya kalle ta yana me tsayar da cokalin cak, ido cikin ido suka kalli juna
Hakan yasa ta kasa jure wa ta sauke nata idon a ƙasa jiki a matuƙar sanyaye
Shi kuwa kasa janye nashi idon yayi a kanta ya hau bin ta da kallo sai dai a baɗini tunani ya faɗa... Wayan sa da tayi ƙara yasa ya mayar da hankalin sa ga wayan, ajiyan numfashi ya ja kafin ya miƙe yana faɗin, "ki ɗauki wayan nan ku yi magana, ki sanar mata ba na wajen, idan kin gama ki kawo min ɗaki". Daga haka ya wuce abin sa ɗaki
Sakato Maimuna tayi ta kasa motsi illa juya maganar nasa da take yi, "da ita yake yi ko kuma wace?"
Wayan Baby ta miƙo mata tace, "Aunty ga shi zai tsinke".
Kallon ta tayi sai kuma ta amshi wayan, a lokacin har ta tsinke sai ga wani kiran, wayan tabi da kallo ganin Number babu suna, ta kasa ɗaukan wayan daƙyar tayi ƙarfin halin amsa wa zuciyar ta cinkushe da tunani, sai dai koda ta kara a kunnen shiru tayi ta kasa magana
Sai da can ɓangaren ne Rahina tace, "Hello Aslm alaikum".
Jin muryan mace sai ta amsa
Shiru ne ya biyo bayan sallaman nata
A tunanin ta ko bata ji bane sai ta sake amsa mata
"Ina me wayan?"
Maimuna tace, "ba ya kusa".
"Ki kai mishi".
Bata san sanda ta samu kanta da faɗin, "ya shiga wanka". ba
Ƙitt ta kashe wayan
Ita kuma tabi wayan da kallo kamar ta sami t.v
"Aunty kawo in Kai mishi wayan".
Miƙa mata tayi ta koma taci gaba da cin abincin ta, amma zuciyar ta ta matsa mata da son sanin wace ce da har ya iya bata wayan? Shi meyasa be amsa ba sai ita? Sai kuma ta taɓe baki a ranta tace, "ta yiwu yan matan sa ne, dama ai ɗan iska ne". Wani iri taji a zuciyar ta da faɗar kalman, sosai ta ji wani abu ya soke ta amma kuma sai tayi tunanin, "to Meye nata da damuwa rayuwar sa ne". Tashi tayi tsam ta haɗa Plates ɗin, ko iya kaiwa kichen bata samu damar yi ba ta wuce ɗakin ta, kai tsaye kan gadon ta ta faɗa tana me lumshe idanuwan ta tana sakin numfashi.. shigowar Baby yasa ta ɗago kai tana kallon ta
"Aunty Yaya ya CE ki zo". Tayi maganar tana hayo wa kan gadon
"Ya ce in zo?" Ta maimaita maganar a fili ba tare da ta sani ba
"Eh haka yace in CE Miki".
Bata sake cewa komi ba illa miƙe wa da tayi ta fita ta nufi nasa ɗakin, sallama tayi ta shiga
Yana gefen gadon sa zaune da wayan sa a hannu daga shi sai dogon wando da Singlet, be ɗago kai ya kalle ta ba yace, "me nace miki idan kika gama wayan?".
Nan gaban ta ya faɗi, cikin rawan murya tace, "ka ce idan na gama in kawo maka wayan".
"Shi ne kika aiko ta? Kin kai girman da ke baki isa ki kawo min ba wato?"
"A'a wlh, kayi haƙuri ita tace in bata ta kawo maka".
Sai a lokacin ya ɗago kai ya kalle ta fuskar sa murtik, "duk ranan da na sake sanya ki abu kika sako min wani a ciki zaki ga yanda zan yi dake, ke a garin ku haka ake koya miki baza ki iya zuwa ki gyara min ɗaki ba? Common wuce ki wanke min bayi tunda ba a haka zan yi amfani dashi ba". Sai yaja dogon tsaki yana faɗin, "a rasa ma wacce za'a aura min sai wannan tatsitsiyar yarinyan, basu iya komin su ba sai an nuna musu".
Ita dai tuni ta wuce Toilet ɗin da sauri jikin ta na ci gaba da rawa. A ɗan ƙanƙanin lokaci ta gama wanke masa, Allah-Allah take ta fice kar wani tsautsayi yasa ya sauke mata bala'in sa a kanta. Tana gama wa ta fito ta fice ba tare da tace da shi uffan ba, tana jin sanda ya saki dogon tsaki ita dai ko tsayawa bata yi ba sai da ta ganta a ɗakin ta, oho dai tunda ta gama babu abinda yayi mata, ita lafiyan jikin ta ne kawai ba ta ƙaunar ya taɓa, tun sanda yayi mata wancan dukan take tsoron abu ya haɗa su.
Koda ta koma ɗaki kwanciya suka yi, babu jima wa barci ya kwashe su. Sai asuba ta farka, tashin Baby tayi suka yi alwala suka gabatar da sallah, ita Babyn ta koma barci yayinda ita kuma ta soma gyara gidan, daga Parlour ta soma gyaran. Tana cikin yi ne ABUL KHAIRI ya dawo daga masallaci, gaishe sa tayi kanta a ƙasa
Be amsa ta ba ya wuce ɗaki don da haushin ta ya kwana, shi idan ba dole ba taya zai zauna da ita kullum tana ƙara masa matsala, dole ne ma ya samo mafita gaskiya bazai yiwu ba.
Ci gaba da aikin ta tayi bata damu da rashin amsa mata ba. Duk wani ayyukan ta sai da ta gama har Breakfast, ta so ta shiga ta gyara masa ɗakin amma kuma tana jin tsoron kuma wani laifin, gwara zuwa anjima idan sun dawo sai ta gyara masa. Suna gama shirya wa suka yi Breakfast suka zauna zaman jiran sa
Yau ma be yi Breakfast ɗin ba koda ya fito, fita kawai yayi abin sa
Haka suka bi bayan sa suka shiga yaja motan suka tafi, yana kai su ya ajiye su ya wuce Company.. office ɗin Abban sa ya soma zuwa, amma lokacin be ƙariso ba shiyasa ya wuce nasa kai tsaye.
Kamar awanni 2 da zuwan sa Aka yi masa Nocking. Izni ya bayar
Rahina ce ta buɗe ƙofan ta shigo taci uwar kwalliya gyale a rataye a wuya
Yana ganin ta ya ɗauke kai a kanta yana sake tamke fuska, be ce mata komi ba har sanda ta samu wuri ta zauna
Sai tace, "yallaɓoi Barka da safiya, fatan na same ka lafiya?"
Shiru yayi be ce mata komi ba
Sai tayi dariya tana faɗin, "ba ma wannan ba. I called you yesterday but you gave your wife an answer. Why didn't you answer?"
Tsare ta yayi da ido, amma kuma ya kasa aiwatar da abun da yake shirin mata, sosai yake jin haushin ta a ransa amma kuma be san meyasaka ba gaba ɗaya ya kasa dakatar da ita a rayuwar sa, ya rasa meyasa ba ya iya mata abinda ke ransa
Be san cewa sai da ta shirya kafin ta dawo gare sa ba, ta san ta sauƙi baza ta taɓa samun sa ba, yayi mata nisan da ko a mafarki baza ta iya samun shi ba, shiyasa ta shirya tsab kafin ta sake tunkaran sa da soyayyar ta. Wannan dalilin ne yasa ba ko wani abu dake zuciyar sa yake iya sanar mata ba, ba don haka ba da tuni ya ci uwar ta ya saita mata hanya...
Katse sa tayi da faɗin, "kayi shiru My Love. Wlh Ina matuƙar ƙaunar ka meyasa baza ka bani dama in maye gurbin Ziyada ba?.."
Muryan sa na rawa ya katse ta da faɗin, "kar in sake jin kin kira sunan Ziyada a nan wurin, babu wanda ya isa ya maye min gurbin ta, Please Rahina ki fita a rayuwa ta kina ji ko?"
Dariya ta saki tace, "Fine. Bazan sake ambatan ta ba tunda nima ba daɗin abin nake ji ba, amma ka sani ABUL KHAIRI ina matuƙar ƙaunar ka, kuma bazan taɓa iya rabuwa da kai ba har sai ka aure Ni, don Allah mene ne laifi na idan na nuna maka soyayya? Meyasa baka da tausayi ne ABUL KHAIRI?"
Shiru yayi yana ɗauke kansa a kanta, sai dai ya kasa ci gaba da aikin da yake yi, zuciyar sa ke kawo masa tunanin, "shin me zai saka bazai iya amsar ta a matsayin maganin matsalar sa ba? Tunda wancan bata da amfani a wajen sa, infact ma bazai taɓa zuwa wajen ƙanwar sa da irin wannan matsalar ba, shi fa ganin ta yake yi kamar ƙanwar sa Batool," shiyasa kawai a ransa ya yanke shawarar ya sake aure wataƙil hakan zai fi mishi tunda bazai dauwama a haka ba... Kaɗa masa hannun da Rahina tayi a fuska shi ya dawo dashi hayyacin sa, ya dube ta ba tare da ya sassauta fuskar sa ba
"Kayi shiru Honey? Meyasa baza ka aure Ni ka tsamo Ni daga cikin ƙuncin da nake ba?"..
Katse ta yayi da faɗin, "Please don Allah ki bar Ni haka in huta, ki je zan neme ki".
Jin hakan yasa ta saki fara'a cike da farin ciki tace, "da gaske kake yi don Allah? Yau kai ne da faɗa min hakan?"
Gyaɗa mata kai kawai yayi yana ɗan sakin guntun murmushi
Wani farin cikin ne ya sake kama ta, "Ok zan jira ko yaushe ne Please ABUL KHAIRI, Kar kace zaka shanya Ni don Allah?" Ta ƙare maganar da shagwaɓa
Bata san cewa abinda ke matuƙar ɗaga masa hankali ba kenan, ya ga mace tana masa shagwaɓa, shiyasa be ja zancen ba daƙyar ya furta mata, "nayi miki alƙawari zan neme ki please ki je". Da haka dai ya samu ta bar masa Office. Kifa kansa yayi a saman table ɗin, "shin ta ina ma zai fara?" Dole shawaran zuciyar sa zai ɗauka gwanda ya aure ta hakan shi ne kaɗai maslaha, domin ko ba ita ba dole ne ya auro wata, tunda ga shi ya sami me son shi why not bazai aure ta ba? Ya san dai ya rasa wacce yake ƙauna har abada, duk wata mace da zata shigo gidan sa a babun lalura ne, yana ji a ransa har ya koma ga mahalicci bazai taɓa samun wacce zata maye mishi gurbin Ziyada ba. Duk da ta wani ɓangaren ko kaɗan Rahina bata mishi ba, amma kuma yana ji kamar akwai abinda ke ingiza shi gare ta, har idan ya ganta sai ya gaza sukuni kuma ya kasa taɓuka mata komi.. ajiyan zuciya ya sauke yana ɗagowa tare da dafe kansa, a fili ya furta, "to ya zan yi in je ma su Mamy da zancen ƙara aure na? Me za su ɗauke ni bayan two weeks kenan da auren?"
*Sunday 12 September 2021.*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 36*
*________* Wajen ƙarfe biyu da rabi Uncle Sani ya isa gidan Mamy, a lokacin Abba ba ya nan sai Mamy ɗin ya tarar, itama dawowar ta kenan daga aiki
Sulaiman na zaune a Parlour yaji Nocking, shi ne yaje ya buɗe masa. Gaishe sa yayi cikin fara'a
Amma sai be amsa ba illa sake kicin-kicin da fuska da yayi, sai da ya shigo ciki sosai sannan ne ya kalle sa yace, "lafiya. Ina ita Deebizan? kira wo min ita".
"Ok". Kawai Sulaiman yace yana nufan ɗakin Batool, Nocking yayi mata, da ta fito yace mata, "kira Mamy Uncle Sani ne yazo".
"To". Tace dashi tana fitowa, a nan ta hangi Uncle Sanin har ya hakimce a saman kujera, tace, "Uncle Ina wuni".
"Lafiya lau".
Wuce wa tayi kawai ɗakin Mamyn ta je ta sanar mata ta dawo ta shige ɗaki tana taɓe baki, "ɗan rainin hankali mutane sai baƙin hali kamar dangin fir'auna". Taja tsaki tana rufe ƙofan ta
Shi dama Sulaiman tuni ya fice haraban gidan abin sa.
Mamy na fito wa ta soma gaishe sa cikin faram-faram kamar yanda ɗabi'an ta ne hakan, sai ta wuce ta kawo masa ruwa kafin tace, "bari in sawo maka abinci Yaya".
"A'a dama kin bar shi don ba shi ya kawo Ni ba". Yayi maganar yana ciccin magani
Murmushi kawai Mamy tayi tana zama
Sai da ya sake ɗaure fuskar sa kafin yace, "maganar ɗiya ta Azeeza nazo miki dashi, yarinyan nan gaba ɗaya na kasa gane kanta ban san me ta gani a wurin ɗan ki ba da har ta nace sai ta aure shi, don haka nake son Idan da yiwuwa a haɗa su aure".
"Aure kuma Yaya Sani?"
"Eh Aure, shi nake nufi aure".
Mamy tace, "to yaya duka-duka yaushe ABUL KHAIRIN yayi aure da har za'a sake mishi wani maganar? Sannan ma ai shi ba ya son ta bare Ace zamu haɗa su".
Miƙe wa yayi yana ɗaga murya da cewa, "eh dole ki ce haka tunda ɗiyar ƴar uwan ki ta fi ta, kin fi son ta tunda ita ga shi kin haɗa su aure, sai ga shi nawa ɗiyar ne kike son ta shiga duniya a kan banzan ɗan ki, wlh Deebiza idan kina son zaman ki da arziƙi dole ne sai ABUL KHAIRI ya auri Azeeza".
Kawai sakato Mamy tayi tana bin sa da kallo kamar t.v, ganin faɗan nasa yayi yawa sai tace, "to shikenan Yaya ka bari zamu yi shawara da Abban su da shi ABUL KHAIRIN idan da yiwuwar hakan sai ayi, amma gaskiya sai dai ka bari ko nan gaba tunda bazai yiwu yanzu ayi musu aure ba saboda be daɗe da yi ba".
"Oho can dai ta matse miki, Ni dai na gaya miki bazai yiwu ace a sanadin ɗan ku ɗiya ta ta rasa farin cikin ta ba, duk yanda ma za'a yi sai dai ayi ku haɗa su aure kawai". Yana gama faɗar haka ya kaɗa bujen rigan sa ya fice yana ci gaba da tsiyan
Sulaiman dake haraban gidan a tsaye da kallo kawai ya bi shi, sai kuma ya juya ya shiga cikin gidan, ganin Mamy har yanzu a zaune sai ya isa wurin ta yana tambayar ta, "ko lafiya?"
Time ɗin itama Batool tuni ta fito jin hayaniyar Uncle Sanin da abinda yake cewa
Haka shima Amir da aka tashe sa daga barci wurjan-jan ya fito yana faman mitstsike idanu.
Mamy sai da ta sauke numfashi me ƙarfi kafin tace, "to ba lafiya ba dai za'a ce Sulaiman, wai maganar Azeeza ya kawo a haɗa su aure da ABUL KHAIRI".
"Wani ABUL KHAIRIN kuma?" Sulaiman ɗin yayi tambayar da mamaki
"ABUL KHAIRI dai na nan gidan".
Sai kawai ya fashe da dariya yana cewa, "amma dai Uncle Sani ya soma shan ƙwaya ne dai ko? Idan ba haka ba taya zai zo miki da wannan shirmen nashi?".
"Ka ga naka Sulaiman, yanzu Uncle ɗin naku ne yake shan ƙwaya?"
"Wlh kuwa Mamy idan dai ba ƙwaya yake sha ba Ni dai ban ga wani me hankalin da zai zo da wannan maganar ba, yaushe ma yayi auren da za'a sake kawo mishi wata?"
Batool na dariya tace, "nima abinda na gani kenan Yaya, ta yiwu wlh Uncle ya soma afa wani abun".
Hararan ta Mamy tayi kafin tace, "kai ba na son iya shege wlh ku shiga hankalin ku".
Su kuma sai dariya suke yi
A lokacin ne Abba ya shigo ya cidda su a haka, zama yayi yana tambayar ba'asi bayan da ya amsa gaisuwar nasu
Daga Sulaiman ɗin har Batool suka haɗa baki wajen sanar da Abban abinda ke faruwa
Kallon Mamy yayi yace, "Wai haka ne me ke faruwa?"
"Hmm Abban su da gaske ne, yanzun nan ya fita wai ya zo a kan haɗa auren Azeeza da Baba na, Ni wlh ban ma san me zance mishi ba".
Shima Abban dariya yayi yace, "lallai kam. To mu ina ruwan mu a ciki? Ai wajen ABUL KHAIRIN ya kamata ya je ya tambaye shi idan har zai iya auren ɗiyar sa tunda ba mu ne zamu zauna masa da ita ba, don Allah ma kar ki saka damuwa a wannan zancen kar ma ki sanar wa da ABUL KHAIRIN. idan shi Sanin ya dawo ki faɗa masa ya je can ya tambayi ABUL KHAIRIN idan zai iya auren ta, mu ina ruwan mu ai akwai rufin asirin da zai iya riƙe mata biyun ko? Maimuna da Azeeza duk ɗaya suke a wurin mu babu bambanci."
"Haka ne Abban su, amma ba ka ganin akwai matsala?"
"Babu wata matsala ki sanar masa haka idan ya sake dawowa, ki nuna masa ke kin amince amma ya je wajen ABUL KHAIRIN ya ji ta bakin sa, ta hakan ne kawai zaku samu zaman lafiya dashi".
"To shikenan Allah ya rufa mana asiri".
"Amin Amin". Duk suka amsa gaba ɗayan su. Kana kuma suka sauya hiran cikin nishaɗi bayan da Mamy ta kawo ma Abban abincin sa nan yana ci.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
*AFTER TWO WEEKS*
A wannan kwanakin abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da ɗinkewar ABUL KHAIRI da Rahina, domin tuni ya bi shawaran zuciyar sa ya amshi soyayyar ta, sun fara gudanar da soyayyar su cike da so da ƙauna, saboda tuni Rahina ta kama zuciyar ABUL KHAIRIN sosai kuma yana jin ta a ranshi
Kuma har yanzu zaman su da Maimuna bata sauya zani ba, kullum jiya-iyau haka suke zaune, tamkar dai ba mata da miji ba babu abinda ke haɗa su
Izuwa yanzu ita har ta saba da wannan zaman nasu, domin yanzu ta saki jikin ta sosai, daɗin ta ɗaya Baby na ɗebe mata kewa ko yaushe suna tare. Duk da har yanzu shi ke kai su school kuma ya dawo da su idan ya tashi daga aiki.
Zuwa yanzu ya yanke shawarar tunkarar iyayen sa da maganar auren sa tunda a halin yanzu ya kai inda bazai iya haƙura ba, yana buƙatar mata matuƙa kuma ya kasa ya baiwa kansa damar da zai tunkari Maimuna da buƙatar sa, gani yake yi kawai raini ne zai shiga tsakanin su duk sanda hakan ya kasance, sannan ma shi har yanzu ganin ta yake yi yarinya, sai dai ko gaba yake sa ran idan ta sake girma zuwa ta shiga babban makaranta sai ya haɗa su da Rahina yayi ta manage idan zai iya, idan kuma bazai iya ba a lokacin sai ya sawwaƙe mata auren sa ya ji da Rahina tunda yanzu ita yake ji a zuciyar sa.
*******
Yau ma suna zaune dawowar su kenan Maimuna tayi musu girki suka ci, sai ta wuce ɗaki ta bar su a parlour'n suna kallo
Wayan sa tayi ƙara ya ɗauka yana amsa wa ganin sunan Mamy, gaishe ta yayi
Ta amsa shi tana tambayar lafiyan Maimuna
"Ƙalau take Mamy". Yace da ita cikin sanyin murya
"Ok Masha Allah haka ake so, wai Ni kam yaushe zaka dawo min da Auta na tunda kun ƙi kawo ta na gaji nayi magana? Abban ku ma yanzu ya gama maganar ya kamata a dawo da ita".
"Mamy duka-duka yaushe ta zo? A bar ta a nan mana ko One month ta ƙarisa mana".
"A'a gaskiya ka dawo min da ɗiya ta ai mu ma muna son jin ɗumin ta, hakan ma ya isa wlh mun gode da ɗawainiya".
"To shikenan zan kawo ta anjima".
Mamy tace, "yauwa to ai gwara haka,". Daga haka ta kashe wayan bayan sun yi sallama
Ajiye wayan yayi yana kallon Babyn yace, "wai kin ji Mamy tace a mayar dake gida."
A tunanin sa ko baza tayi murna bane sai ta hau tsalle tana faɗin, "Yeeeeee zan koma gida inga su Mamy".
Riƙo ta yayi yana ɗaura ta a kan cinyan sa da murmushi a face ɗin sa yace, "ok wato ba kya son zama dani dama ko?"
Girgiza masa kai tayi da faɗin, "a'a yaya ina so, amma ina so in je in ga su Mamy ne".
"Hmm ba wani nan Ni zaki yiwa wayau, yanzu har Auntyn ki ba kya son zama da ita ko? Shikenan tashi ki je ki faɗa mata ta haɗa miki kayan ki zuwa anjima zan kai ki".
Da gudu ta sauka a jikin sa ta wuce ɗakin Maimuna don ta sanar mata
Murmushi kawai yayi yana mayar da hankalin sa kan kallon sa ya ci gaba da yi.
Ita kuma tana shiga ta sanar wa Maimuna abinda yace
Da sauri Maimuna ta tashi daga kwancen da take tana riƙe mata hannu tace, "yauwa Auta na nima ki je ki ce mishi in shirya zan bi ku."
"Eh Aunty tare zamu je ma, bari in faɗa masa". Tafaɗa tana juya wa da gudu ta fice
Murmushi Maimuna tayi a ranta tana addu'ar, "Allah yasa ya amince". Tayi kewar gida tunda tayi auren bata taɓa zuwa ba ga shi watan ta ɗaya kenan.
Tana zaune Baby ta dawo tace mata yace, "A'a".
Shiru Maimuna tayi bata iya cewa komi ba, ji take yi tamkar ta kurma ihu sabida baƙin ciki amma sai ta daure ta miƙe ta soma haɗa wa Baby duk wani kayan ta da babu shi cikin akwatin ta
Ita kuwa Baby murna ya rufe ta zata je ta ga iyayen ta, tuni ta tuɓe kayan ta tana faɗin, "Aunty kiyi min wanka sai in sanja Kaya".
"To bari in gama".
Bayan ta gama wankan tayi mata ta shirya ta cikin kaya har da mata kwalliya
Tana gama mata ta fice da gudu parlour don ta sanar masa ta shirya. Ganin ba shi a Parlour sai ta nufi ɗakin sa suka ci karo a bakin ƙofa
"Wow my angel kin Yi matuƙar kyau, wa yayi miki kwalliyan?"
Tana washe baki ta bashi amsa da, "Aunty ne tayi min, ka gani ma har da jan-baki ta saka min".
"Inyee kin yi kyau Auta na, amma bari in je in Yi sallah sai in zo mu tafi ko?"
Gyaɗa masa kai tayi
"Yauwa good Girl". Ya shafa kanta yana wuce wa don alwalan ya kai shi ɗaki dama.
Ita kuma ɗakin Maimuna ta koma ta tarar da ita tana sallah, sai itama tayi join ɗin ta ko alwala babu bare Hijab a jikin ta, saboda gani take yi tayi kwalliya baza ta goge ba. A haka suka yi sallah suka gama suka zauna zaman lazimi.
Lokacin da ABUL KHAIRI ya dawo sai ya kwaɗa mata kira daga Parlour
Da gudu ta fice har tana tuntuɓe
Itama Maimuna tashi tayi ta ja mata kayan zuwa parlour'n
Yana riƙe da hannun Baby za su fita. Kallo ɗaya kawai yayi mata ya janye idanun sa suka fice
Hakan yasa taja akwatin tabi bayan su, har bakin mota ta kai ta buɗe baya ta saka
Su kuma tuni sun shige ciki Baby nata ɗaga mata hannu tana ɓangale baki
Itama murmushin take mata tana me ɗaga mata hannu zuciyar ta na cike da kewar ta, har suka fice tana a wurin don ta kasa yin magana. Sai da me gadi ya ja gate ya rufe kafin ta juya tana share hawayen da suka sauko mata ta koma ciki.
******
Suna zuwa gidan bayan yayi parking suka fito, ya ɗaukar mata jakan ta suka tasar wa shiga cikin gidan
Ita Baby tuni ta ruga a guje ta shige ta bar shi a baya
A lokacin da ya shiga da sallama su Mamy na zaune a parlour'n gaba ɗayan su ban da Sulaiman da ya fita. Baby na Kan jikin Mamy suna murnan dawowar ta, yayinda ita kuma sai rattaba musu zance take yi suna mata dariya
Gaishe su yayi yana murmushi da kallon Baby
Suka amsa Abba da Mamy suna tambayar shi Maimuna?
Kafin ma yayi magana Baby tayi tsagal ɗin cewa, "ai ta ce zata biyo mu yace mata baza ta zo ba".
Kama haɓa Mamy tayi
Shi kuma Abba na dariya yace, "ki ce shi ya hana ta zuwa?"
"Eh mana Abba".
Shi dai ABUL KHAIRI shiru yayi yana faman shafa kai yana hararan Babyn
Sai a lokacin su Batool suka sami damar gaishe shi
Ya amsa su yana faɗin, "Amir samo mun ruwa in sha".
Tashi yayi ya kawo mishi
Batool kuma miƙe wa tayi tabar parlour'n tana amsa Call
Shima Amir yana ajiye ruwan ya wuce ɗakin sa
While su kuma suka ɗan soma taɓa hira.
Kamar shuɗewar mintuna sai kuma ABUL KHAIRIN yace, "Dama ina son mu Yi wata magana ne".
"To Baba na muna sauraron ka ai".
Sai da ya ɗan ja numfashi kamar bazai yi maganar ba don ya rasa ta ina zai fara
Jin yayi shiru sai Abba dake kallon sa yace, "ba magana kace zamu yi ba ko ka fasa ne?"
Girgiza kansa yayi kafin yace, "Dama a kan ina son zan sake aure ne.." shiru yayi domin ya kasa ci gaba sabida jin maganar tayi masa nauyi da ya furta
Su kuma saboda jin maganar a bazata sai duk suka kasa magana suna me bin shi da kallo
Abba ne ma ya samu ƙwarin gwiwan furta, "aure kuma? Aure kamar ya?"
Sauke kansa ƙasa yayi yana faman shafa ƙeya, cike da kunya yace, "aure nake so na ƙara Abba, sabida.."
"Ka buɗe baki kayi mana magana saboda me? Duka-duka auren naka yaushe aka yi shi ne da zaka zo mana da maganar sake wani? Kanka ɗaya kuwa?" Cewar Abban a zafafe jin kamar ma rainin hankali ne irin na ABUL KHAIRIN
"Abba na ga Maimuna tayi ƙarama da aure yanzu, shiyasa nake son sake wani auren sabida kada na shiga haƙƙin ta da yawa, kuma.."
Katse sa Abba yayi da faɗin, "in ji uban wa yace maka tayi ƙanƙanta da aure? Kawai dai kace kana son ka sake aure amma ba sai kace tayi ƙanƙanta ba, Maimunan yarinya ce da zaka ce tayi ƙanƙanta?"
Mamy tace, "Ban da abun ka Baba na Ni kaina lokacin da aka yi min auren fari ai kamar Maimunan nake, sannan ita kanta mahaifiyar Maimunan sanda tayi aure shekarun ta sha biyar ne a duniya, bata kai ma Maimunan ba a time ɗin, kuma tana da shekara 16 ta haifi Naana me ya same ta? Idan ma wani abun kake tunani gwara ka dena, ko wacce mace da haka ta saba kaji ko? Batun aure yanzu ma ba zai yiwu ba duk da dai ba hana ka yi zamu yi ba, amma yanzu duka-duka wata ɗaya ne da kwanaki da auren ku, ka bari sai sanda ta cika shekara ko fiye da hakan sai ka sake tunda kana da ra'ayi, mu baza mu hana ka ba tunda mun san ita ba zaɓin ka bane ba sai ka tunatar mana ba".
Shiru ABUL KHAIRI yayi kansa a ƙasa yana sauraron ta
"Yanzu kai idan ma aka ce kazo da maganar aure yanzu zaka zo mana dashi? Tukunna ma wace ce yarinyan da zaka aura ɗin?" Abban yayi masa wannan tambayar
Daƙyar ya iya furta, "Rahina".
"Rahina". Duk suka maimaita sunan a tare
Kana kuma Mamy ta ƙara da faɗin, "ba dai Rahina ƙawar Ziyada ba?".
"Eh ita".
"Ka rasa wacce zaka aura sai wannan yarinyan mara tarbiyya Baba na? Yarinyan da ta sanadiyyar ta ƙawar ta ta afka harkan zina shi ne har kake tunanin auren ta wato? Yanzu fisabilillahi kai baka ji kunya ba da har kake soyayya da ita?"
Abba yace, "ai bazai ji kunya ba tunda na ga alamun ba kunya ya cika ba. To tun wuri ka rabu da ita wlh tun kafin mu saka ƙafan wando ɗaya da kai kaji ko? Kuma batun aure idan ma auren zaka yi sai dai ka auri ƴar uwan ka Azeeza tunda itama tana son ka, ai gwara ita da wadda ka kawo mana, ko ba komi zumuncin Mamyn ku da dangin ta zai ƙarfafa. Kuma wlh ina faɗa maka duk ranan da ka biye wa son zuciyar ka itama ka je kuka aikata the same abinda kuka yi da wancan kai da Allah, tunda aure ne dai ga mata nan mun maka baka da hurumin da zaka bibiyi wata mace, gwara tun wuri ka rungumi matar ka ku zauna lafiya. Tashi dalla ka wuce mana a nan kana wani sim-sim da kai sai kace mutumin kirki".
Miƙe wa yayi ba tare da ya furta kanzil ba ya fice, motan sa ya shiga ya fice a gidan. Direct wani pharmacy ya wuce, sai da ya daɗe a cikin motan be fito ba sai saƙa da warwara yake yi, kafin kuma ya buɗe motan ya shiga cikin shagon. Ya jima kafin ya fito ya ja motan zuwa gida zuciyar sa kamar zata ƙone sabida baƙin ciki.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 37*
*________* horn yayi a bakin Gate ɗin gidan sa, ana buɗe masa ya kutsa hancin motan cikin gidan, kai tsaye parcking space ya wuce ya tsayar da motan, be fi minti uku ba ya fito riƙe da leda a hannun sa, wuce wa yayi cikin gidan ya saka keey ya buɗe ya shiga
Babu kowa Parlour don lokacin Maimuna na ɗaki tana karatun school
Dakin sa ya wuce ya buɗe ya shiga ya rufe har da murza keey. Saman gadon sa ya nufa ya zauna ya soma zare cover shoes ɗin ƙafafuwan sa, bayan ya gama ya buɗe lockern gadon sa ya ajiye ledan da ya taho da shi, kwanciya yayi kansa na kallon silling ɗin ɗakin yana me lumshe idanun sa. Shiru yayi kawai yana sauraron bugun zuciyar sa da kuma tunanin da ya hau masa kai. Sosai ya burma cikin tunani har be san sanda aka yi kiran sallan magriba ba, sai a lokacin sannan ya buɗe idanun nasa yana me tashi ya shiga Toilet, alwala yayi ya fito daga ɗakin zai fice
A lokacin ne itama Maimuna ta fito daga kichen riƙe da coolar a hannun ta zata Kai saman dainning, haɗa idon da suka yi yasa tayi saurin sauke kai ƙasa tana ci gaba da taho wa
Shima ɗauke nasa idon yayi ya ƙarisa ya fice abin sa
Numfashi kawai ta ja taci gaba da abinda take yi har ta gama kana ta wuce ɗaki itama tayo alwala ta gabatar da sallan ta, bata tashi a wurin ba illa Kur'ani da ta ɗauka ta soma tilawa har sai da aka kira sallan isha'i, ta tashi ta gabatar sannan tayi wanka tayi shirin ta kamar yadda ta saba, rigan barci ta sanya doguwa me ruwan toka, yanayin rigan ya sanya ta ɗauka Hijab Wanda ta kawo mata iya ƙasan gwiwan ta ta saka, sannan ta fito Parlour
ABUL KHAIRI na zaune ya tasa t.v a gaba yana kallo, sai dai a baɗini tunani yake yi jefi-jefi kuma yana kai kallon sa ɗakin Maimuna. Ganin fitowar ta be san sanda ya sauke ajiyan zuciya me nauyi ba yana me sake bin ta da kallo ganin ta da Hijab yau kuma. Lumshe idanuwan sa yayi sabida ƙamshin turaren ta da ya hautsina masa kai sanda ta gibta shi ta wuce ta gaban sa. Buɗe su yayi yana bin bayan ta da kallo har ta zauna a kan dainning ɗin
Ita kuma duk ta gama tsarguwa saboda ji take yi kamar yana kallon ta, amma bata ɗago kai ba har sanda ta dangana ga wajen dainning ɗin ta samu wuri ta zauna, abincin ta soma zuba wa kamar yanda ta saba, ta gama zuba nata kuma sai ta tsaya tana tunanin ta zuba masa ko ya? Kasancewar ganin be taso ba, kuma baza ta iya ce mishi, "ya taso ga abinci ba". Sai kawai ta soma cin nata ba tare da ta kalli inda yake ba.
Kamar shuɗewar mintuna biyar sai ABUL KHAIRI ya tashi ya nufi wajen Fridge ya ɗauko fresh milk ɗaya, kai tsaye wajen dainning ɗin ya nufa yana me jan kujera ya zauna. Be kalle ta ba yace, "zuba min kaɗan".
Da sauri ta ajiye cokalin hannun ta ta miƙe ta soma yunƙurin zuba masa
Da kallo yake bin ta kawai ganin yanda take ta ɓarin jiki, be san sanda ya ja tsaki ba yana sake haɗe rai, ji yake yi kamar ya make ta sabida shi kwata-kwata ya tsani idan yana wurin ta riƙa ɓare-ɓaren jiki, sai kace ta mayar dashi dodon ta
While duk ta rasa nutsuwar ta sabida jin yayi tsaki, a tunanin ta ko tayi laifi ne shiyasa har tana ɗago wa ta kalle sa. Kallon da ya sakar mata ne yasa tayi saurin mayar da kanta ƙasa lokaci ɗaya ta sake tsure wa. Daƙyar ta iya gama zuba abincin ta zauna sai dai ta kasa ci gaba da cin nata illa juya cokali da take yi
Shi kuwa tuni ya mayar da hankalin sa ga nasa yana ta faman kaiwa baki, sai dai fuskar nan nasa duk ta gama sauya wa sabida damuwan dake ran sa. Sai da ya ji motsin tashin ta ne ma ya dawo duniyar tunanin da yake yi yana bin ta da kallo. "Ina zaki je?"
Maimuna da har ta kusa sauka a wurin sai ta juyo tana kallon sa, yanda idanun su suka shige na juna hakan yasa ta janye nata cikin wani irin yanayi da ya same ta lokaci ɗaya. Bata iya magana ba sabida yanda bakin ta ya kasa buɗe wa bare ta ba shi amsa
"Dawo ki zauna".
Babu musu ta dawo ta zauna tana haɗe hannayen ta wuri ɗaya
Umarni ya sake bata a kan, "ta ɗauki Fresh milk ɗin ta shanye".
Jin abinda yace har sai da ta ɗago kai ta kalle sa da mamaki a cikin ranta, ganin dai ba ita yake kallo ba yasa ta sanya hannun ta na rawa ta ɗauka, buɗe wa tayi ta soma kurɓa a hankali, duk wani jarumta nata ta haɗo don ta sanya wa kanta nutsuwa amma ina hakan ya faskara, domin ta rigada ta sanya wa ranta tsoron sa sosai, haka kawai ba ta ƙaunar su kasance wuri ɗaya, abin da take ji ba ta iya jure wa wannan dililin ne yasa take rasa nutsuwar ta tayi ta rawan jiki. Kaɗan tasha ta soma yunƙurin rufe wa
"Ki shanye nace". Yayi maganar be kalle ta ba
Ci gaba tayi da sha ba tare da ta ce uffan ba, gaba ɗaya ta shanye bata sake yunƙurin ajiye wa ba duk da cikin ta ya cika fam. Kamar tayi kuka haka ta kalle sa tace, "na shanye".
Ko kallon ta be yi ba bare ya tanka mata
Sai ta tashi kawai ta wuce ɗakin ta. Tana shiga ta zauna saman gado tana kama kanta, sai kuma ta lumshe idanu tana buɗe su daƙyar ta miƙe ta shiga Toilet, bakin ta ta ɗauraye ta fito ta cire hijabin jikin ta ta haye kan gadon ta. Sosai take jin barci a idanun ta shiyasa lokaci ɗaya ya kwashe ta nan da nan ko addu'a bata samu tayi ba
******
Sai da ta shiga ɗaki da kamar mintuna goma kafin ya tashi daga inda yake ya wuce ɗakin sa, kai tsaye Toilet ya shige yayi wanka ya fito yayi shirin sa. Sai ya fito ya nufi ɗakin Maimuna, ya san maganin barcin da ya sanya mata iyanzu ta manta a duniyar da take. ai kuwa da ya shiga tayi ɗai-ɗai abin ta sai sharan barci take yi. Lumshe idanu kawai yayi yana sake ware su a kanta yana me ƙare mata kallo kamar idanun sa za su faɗo
Duk da ya san abinda ya shirya ba abu bane me kyau amma babu yanda zai yi, hakan shi ne kaɗai maslaha a wurin sa don bazai iya zuwa ya neme ta ido na ganin ido ba, shi a ganin sa zubar da kai ne ya rasa wurin da zai je sai wurin ƙanwar sa. Ba don yanda yake ji ba a wannan lokacin da ganin ta ba baya tunanin zai iya aikata abinda ya shirya, amma kuma tuni zuciyar sa da gangan jikin sa sun ingiza shi ga son kwaɗaita da ita, don be taɓa jin mugun sha'awar da ya sauko masa irin na yau ba, bazai iya haƙura da ita ba dole ne ya sauke duk abinda yake ji a yau ɗin nan, dole ne yayi maganin damuwar sa.
_Na gaji sai an kwana biyu sai mu ci gaba. 😥_
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 38*
*________* *WASHE GARI SATURDAY*
*10:30am.*
Ta soma buɗe idanuwan ta a hankali tana mayar da su, wadda daƙyar ta iya samu ta buɗe su tarwai tana bin saman ɗakin da kallo, kamar mintuna biyar tana a haka kafin tunanin ta ya dawo cikin jikin ta, sai wani irin zafi ya ziyarce ta lokaci ɗaya ta yunƙura zata tashi amma ina ta kasa, ƙara ta saki tana koma wa yanda take ta kwanta sai kuma ta koma bin jikin ta da kallo, sai kuma ta kama kanta da hannu ɗaya tana son tuna abinda ya faru da ita da har tayi mugun barcin nan sai da gari ya waye zata tashi. Bata iya tuna komi ba sai mafarkin da tayi da ABUL KHAIRI yana saduwa da ita, wadda ta ɗauka duk a tunanin ta mafarki ne sabida magagin barci, da sauri ta sake buɗe idon ta zuciyar ta na buga wa da ƙarfi, rigan jikin ta tabi da kallo yana a yanda ta sanya shi jiya, amma abun da take ji a can ƙasan ta da azafan dake ratsa ta shi ne ta kasa gane wa, "kar dai ace mafarkin da tayi ne ya bayyana mata a zahiri? Ina a'a ba haka bane". Ta sake ƙaryata kanta da sauri tana girgiza kanta, sai ta miƙe da ƙarfin ta domin ta sauka a kan gadon, wani irin ƙara ta ƙwalla tana koma wa kan gadon, lokaci ɗaya sai ta fashe da kuka tana faɗin, "na shiga uku Ni Maimunatu. Me ke shirin faruwa dani? Wayyo Allah na Mamana". Kuka take yi sosai.
******
ABUL KHAIRI dake ɗaki sai Safa da marwa yake yi ya gaza nutsuwa, ko abinci ya gaza ci sai sintiri yake yi daga ɗakin sa zuwa ɗakin Maimunan yana jiran ta farka, amma har yanzu shiru, ya gaji da jiran ta ne yasa yanzu ya shiga Toilet yin wanka wanda be samu yayi ba tun ɗazu. Yana fito wa daga bayin ne ya ji kamar ihun ta shi ne yayi saurin zira jallabiya ya fito ya shiga nata ɗakin, turus yayi a bakin ƙofan yana bin ta da kallo ya kasa ƙarisa wa
Ita kuma ganin sa yasa ta haɗiye kukan nata sai hawaye da suka ƙi tsaya wa a idanun nata, nan da nan jikin ta ya soma rawa
"Lafiyan ki mene ne?" Yayi maganar yana sake tsare ta da ido kamar wanda be san komi ba
Wasu sabbin hawayen ne suka sake wanke mata fuska sabida azaban dake ratsa ta, amma baza ta iya faɗa masa ba shiyasa tayi shiru tana sake duƙar da kai
Takowa yayi zuwa inda take ya sake maimaita mata tambayar, "me ya same ta?"
Shiru ta sake yi tana shashsheƙan kuka
Tsaki yaja yace, "ke ina magana kina banza dani, I said what is wrong with you?"
Cikin rawan baki da kukan da ya kufce mata tace, "na kasa tashi ne".
"Kin kasa tashi?" Ya maimaita maganar nata yana waro ido waje kamar be san Abin da ya aikata ba. "To saboda me?" Ya sake mata tambayar
Hannu ta sa ta share fuskar ta tana ci gaba da kukan ta a hankali
Shiru kawai yayi yana kallon ta, sai kuma ya wuce Toilet ɗin ta ya haɗa ruwa ya dawo
Tana nan a yanda take tana kuka
Ya zo ya ɗauke ta ba tare da ta ankara ba ya wuce da ita Toilet, ya sanya ta cikin ruwan da ya haɗa mata
Kuka ta saka mishi sabida kunya da azaban da ya ziyarce ta
"Kee ki rufa ma mutane baki tunda baza ki faɗa abinda ke damun ki ba, Ni taimakon ki zan yi ban son ki sake min kuka kinji ko?"
Rufe bakin ta kawai tayi zuciyar ta na buga wa da sauri da sauri don a tunanin ta wanka zai yi mata, duk ta fita hayyacin ta lokaci ɗaya sai ɓarin jiki take yi
Ɗan lumshe idanun sa yayi ya buɗe yana kallon ta, kana kuma yace, "ki cire rigan kiyi wankan". Sai ya juya ya fita. Har ya kai bakin ƙofa kuma sai ya kasa fita sabida hankalin sa ya gaza kwanciya, tabbas zai iya cutar da ita tunda bata gane me yayi mata ba, sai kawai ya koma ciki
Lokacin kuka sosai ta fashe dashi ta gaza motsa wa daga yanda take. Ganin sa yasa tayi saurin gimtse bakin ta tana bin shi da kallo
Ɗan sassauta fuska yayi yace, "kin yi mafarki ne jiya?"
Waro ido waje tayi sai kuma ta ɗauke kai daga kallon sa ta kasa amsa mishi
"Wai ba nace miki idan ina magana ki dena min shiru ba? Ke Bagidajiyan ina ne? Na ce kin yi mafarki ne jiya?" Ya ƙare maganar da daka mata tsawa
Bata san sanda ta buɗe baki ta amsa mishi ba saboda tsoro
"To ki gasa jikin ki sai kiyi wankan tsarki. Ina fatan kin iya?"
Nan ma sake ɗaga masa kai tayi da sauri
"Good Girl." Ya furta yana juya wa ya fice
Tsaban takaici ita kuma sai ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi. Sosai take kuka ta kasa yin komi har sai da lokaci ya ja sosai kafin ta samu tayi abinda ya kamata, daga baya tayi wankan ta ɗaura alwala ta fito. Daƙyar take iya tafiya saboda sauyin yanayin da take ji a tattare da ita ga kuma zafin da har yanzu be dena ba duk da ya ragu, sif ɗin kayan ta ta nufa ta ɗauko doguwar riga ta zira tare da Hijab sannan ta tayar da Sallah. Tana idar wa ta zauna a wurin tana hada kai da gwiwa taci gaba da tsiyayar da hawaye, tunanin ta ya tafi ga abinda ya faru da ita da kuma abin da ABUL KHAIRI yayi mata yanzu, taya ma ya san abinda ya hana ta tashi da har ya iya gane wa? Ko dama shi ya san ana haka ne? Amma meyasa tayi mafarkin nan yau bayan hakan be taɓa faruwa da ita ba? Ko kaɗan bata iya kawo komi a ranta a kan zargin ABUL KHAIRI ba sabida bata taɓa tunanin zai yi wani abu da ita ba, mutumin da ba ya ƙaunar ta ko kallon ta ma be son Yi shi ne zata zarga, taya to? Abin ma da bazai yiwu bane, ta fi dangana wa ga mafarkin shi ne tayi ya haddasa mata haka, ƙila na Mijin dare ne da ake cewa shi ne yau itama tayi. Amma ko idan haka ne ya cuce ta, ga shi ya sanya mata azaba da tsamin jiki duk ta rasa inda yake mata daɗi, sai kawai ta ɗaga hannu hawaye na zuban mata ta soma roƙon Allah a kan, "kar Allah ya sake ba shi ikon zuwa wajen ta, Allah ka gani Ni ban taɓa yin mafarki da na mijin dare ba, ko yaushe ina addu'a idan zan kwanta, jiya ma barci ne ya ci ƙarfi na shiyasa ban yi ba, Allah na roƙe ka kar ka sake ba shi damar sake zuwa wuri na.."
Wani irin dariya ne ya so kufce wa ABUL KHAIRI da ya shigo yanzu ɗakin ya cidda ita tana wannan addu'an
Da sauri ta juya tana kallon sa saboda jin kamar motsi, nan ta gan sa yana murmushi bcoz ya kasa riƙe dariyan nasa wanda har sai da murmushi ya bayyana a fuskar sa. Da sauri ta sadda kanta ƙasa saboda tsananin kunya da ya kamata domin ta san ya ji abinda tace, kunya sosai ya rufe ta har ta kasa motsa wa bare ta iya gaishe sa ma
Shi kuma daƙyar ya iya kautar da murmushin daga fuskar sa ya tako zuwa wajen ta tare da miƙa mata ruwan hannun sa dake Cup da ƙwayoyin magani yace, "ga shi ki shanye".
Ɗago kai tayi ta kalle sa, sai ta sanya hannu ta amsa a kunyace ta soma sha
Shi kuma yana tsaye yana kallon ta har sanda ya ga ta gama ya amshi Cup ɗin ya fice. A Parlour ya zauna ya ɗaura ƙafa ɗaya a kan ɗaya yana me jingina da kujeran tare da lumshe idanuwan sa. Haka kawai idan ya tuna abubuwan da suka faru a daren jiya yake shiga matsanancin farin ciki, tunda yake be taɓa kasance wa a cikin wannan yanayin me ban nishaɗi ba kamar daren sa na jiya, he is very happy this day and it is one of the most memorable days of his life. Murmushi ya saki bayan ya buɗe idanuwan sa yana me shafa sajen fuskar sa, all his eyes could see was Maimuna's beautiful body that had gone with his faith yesterday da ni'imar da Allah yayi mata, he feels as if he is going back to doing what he did to her, but he is also suppressing his heart with impatience. Fitowar Maimuna yasa ya kalli inda take, yanda take tafiya ne ya kasa ɗauke ido a kanta
Ita kuma tuni ta sauke kai ƙasa sabida tsananin kunyar sa da take fama dashi a yau, shiyasa tayi ƙoƙarin daidaita tafiyan ta kar ya gane akwai wani abun ta shige kichen
Ɗan lumshe idanuwan sa yayi yana me buɗe su, be san meyasa ba yau kuma tausayin ta ya shiga zuciyar sa ƙwarai, duk da ya daure sosai a jiya wajen bin ta a hankali sabida kar a samu matsala amma kuma ji be yanda take tafiya. shiyasa kawai ya tashi ya bi ta cikin kichen ɗin
Tana tsaye ne tana tunanin abinda zata sama musu su yi Breakfast duk da lokaci ya ja, dole ne yasa ta fito sabida yunwan da ya addabe ta ba don haka ba baza ta iya taɓuka komi ba sabida rashin ƙwarin jiki da ciwon da take ji. Motsin sa yasa ta juya da sauri tana kallon sa, sai duk ta taburce sabida tsare ta da idon da yayi
"Me zaki yi?" Ya tambaye ta yana saka hannayen sa cikin aljihun jallabiyan sa
Maimuna da kanta ke ƙasa tace, "dama zan mana Breakfast ne".
"Ki koma ki zauna zan nema mana abinda zamu ci, yau ki huta tunda baki da lafiya". Daga haka ya fice abin sa be tsaya ya ji abinda zata ce ba
Mamaki sosai ya bayyana a kan fuskar Maimuna da sauyin yanayin da ABUL KHAIRI yau yake nuna mata, ji take yi kamar ba shi ba sabida nuna tausayin da yayi mata a yau ɗin, sai dai bata da abinda zata ce illa tabi umarnin sa ta koma ɗaki abin ta ta kwanta.
Shi kuma sauya kaya yayi ya ɗauki keey ɗin mota ya fice, be daɗe ba ya dawo da gasasshen kaza da yoghurt da ya siyo, ajiye wa yayi a saman dainning ya wuce kichen ya haɗa musu ruwan tea da komi ya shirya a saman dainning table. Sai ya wuce ɗakin Maimuna. A kwance ya ganta tana ta faman tunani a kan sauyin ABUL KHAIRIN
Ganin sa yasa ta tashi zaune tana duƙar da kai
"Ki fito ki je ki karya". Abinda yace kenan ya juya ya fice ya koma ɗakin sa
Itama tashi tayi ta fita, ganin ba shi a Parlour sai ta ɗan samu nutsuwa ta wuce kan dainning ɗin ta zauna, abubuwan da ta gani a kai ne yasa ta saki murmushi ba tare da ta shirya ba, sosai take mamakin meyasa yake jin tausayin ta yau? Bata taɓa tunanin ko da wasa zai iya shiga lamarin ta ba ko wani irin hali ta shiga, shiyasa tana karyawan ne farin ciki na ratsa zuciyar ta.
Fitowa ABUL KHAIRI yayi ya zo ya zauna shima a kan dainning ɗin. Har ta tashi zata yi serving ɗin sa sai ya tsayar da ita a kan, "zai zuba da kansa". Shi yayi serving ɗin kansa kana ya kalle ta yace, "ki dena nuƙu-nuƙu da Allah ki ci abinci, ba na son Wasa kina jina?"
Gyaɗa masa kai tayi jiki a sanyaye taci gaba da cusa wa a baki tana jin zuciyar ta kamar zata faso sabida yanda take buga wa
Wayan sa ne tayi ƙara ya ɗauka, ganin Rahina sai da ya ɗan kalli Maimuna da kanta ke ƙasa kafin kuma ya amsa call ɗin yana kara wa a kunne. "um ina jin ki".
Daga can Rahina tace, "Honey Wai lafiya yau na ji wayan ka a rufe? Kuma jiya ka ce min zaka zo but sai na ji shiru".
"I'm sorry akwai abinda ya hana Ni zuwa ne jiya, kuma matsalan ne yasa na kashe waya na but kiyi haƙuri".
"Babu komi honey ai ba na iya fushi da kai. Amma gaskiya yau ina son ganin ka ko don maganar auren mu da kace zamu yi. Fatan ka faɗa wa su Mamy sun amince?"
Idanu ya ɗago ya kalli Maimuna kafin ya lumshe su yana me sake ware su, a hankali ya furta, "ki bari zuwa anjima zan zo zamu yi magana ko?"
"Ok then I'm waiting for you".
Yace, "ok bye". Sannan ya kashe wayan. Miƙe wa yayi kafin ya kalle ta yace, "idan kin gama ki ajiye sauran anjima ki ci, kar ki shiga kichen yau". Ya juya ya tafi
Da kallo ta bi shi har ya shige ɗaki, kana ta lumshe idanuwan ta tana murmushin da bata san dalili ba, yau rana ɗaya da ya sauya mata ji take yi kamar su dauwama a haka, kulawan yau kaɗai ya sanya ta a cikin farin ciki mara misaltuwa. Ko ba komi yau tana jin nishaɗi a ranta saboda nuna kulawan sa a kanta. Tashi tayi ta kwashe komi ta kai kichen sannan ta wuce ɗaki ta kwanta tare da dasa tunanin ABUL KHAIRI da ya tsaya mata a rai yau.
Shi kuma a lokacin ya shirya cikin ƙananan kaya ya sha kwalliya ya fice abun sa.
Babu abinda ke tashin Maimuna illa sallah sai ta koma ta kwanta, wunin yau a haka ta wuni a kwance, sai ƙarfe huɗu ta sake shiga tayi sabon wanka, yanda ta gasa jikin ta yasa ta sake samun sauƙi sosai, kichen ta wuce ta ɗauko raguwan kazan ta da yogurt ɗin taci ta ƙoshi ta samu wuri a saman kujera ta zauna. A nan ta wuni har aka kira magriba har a lokacin kuma ABUL KHAIRI be dawo ba. Ɗaki ta wuce tayi sallah sannan ta zauna tayi karatun ta kafin ta gabatar da sallan isha'i, har barci ya ɗauke ta ABUL KHAIRI be dawo ba.
Sai wajen goma na dare ya shigo gidan, sai da ya shiga ya duba ta kafin ya wuce ɗakin sa yayi wanka ya shirya ya kwanta. Yau be yi ninyan mata komi ba duk da sosai yake tsananin buƙatar ta. But dole ne ya bari ta samu sauƙi don ma yana ganin yarinyan tana da juriya ne, amma kuma yayi mamakin rashin wayon ta da har ta kasa gane komi, sai kawai abin ya bashi dariya ya saki yalwataccen murmushi yana me sauya kwanciyan sa. Daƙyar a ranan ya samu barci ya ɗauke shi sabida tsananin ɓukatar Maimuna da yake fama dashi.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 39*
*________* Tun asuba da Maimuna ta tashi daga barci bata koma ba sai da ta gyara ko ina na gidan, kafin bakwai har ta gama komi nata har Breakfast sai ta koma kawai ta kwanta barci ko wanka bata samu tayi ba, sosai take jin barci a idanuwan ta kamar wacce bata samu tayi ba.
ABUL KHAIRI kuma zuwa takwas da rabi ya fito cikin shirin sa na farar jallabiya da gajeren wando itama fara a ciki, ya zauna a Parlour Yana ɗan kalle-kallen ta inda Maimuna zata fito, jin shiru sai ya miƙe ya wuce kan dainning, ganin an shirya komi sai ya zauna yayi serving ɗin kan sa ya hau karya wa yana tunanin, "me ya hana ta fito wa?" Sai wata zuciyar nasa ta raya masa, "ƙila fa ba ta jin daɗi ne," da sauri ya miƙe yana barin wayan sa a wurin ya nufi ɗakin nata, tura ƙofan yayi da sallama a bakin sa ya shige. A kan gado ya ganta sai sharan barci take yi ta ƙudundune kanta da pilow ta matse, sai ya taka ya nufi gaban gadon yana bin ta da kallo, be yarda da ko lafiyan ta lau bane tunda ba ya ganin tana koma wa barci sai ya saka hannun sa ya taɓa wuyan ta ya ji ko da zafi ne
A dai-dai lokacin ne ta farka tana ware idanuwan ta a kansa, sai da ta ɗan sake rufe su ta sake ware su sabida ta tabbatar shi ɗin ne, sanin shi ne yasa tayi saurin tashi zaune kamar wacce aka tsikara
Shi kuma sai ya ƙi ɗauke idanun sa a kanta yana me bin ta da kallo kawai, yayinda fuskar sa a sake kaɗan
Gaishe shi ta hau yi bayan ta sauke kanta a ƙasa
Be amsa ba sai ya tambaye ta, "lafiyan ki kuwa?"
Gyaɗa masa kai tayi
"Baki da baki ne?"
Cikin rawan murya tace, "lafiya ta lau".
Shiru ya ɗan yi kana kuma sai ya juya ya fice
Da kallo ta bi sa don ta kasa ma gane tunanin me zata yi. Tana nan zaune ita bata koma barcin ba ita kuma bata tashi ba, sai da ta shafe kamar mintoci a ƙalla goma kafin ta miƙe ta shiga bayi don yin wanka. Bayan ta fito ta shirya cikin riga da wando na Pakistan me ruwan zuma da kalan kuka, simple make-up ta yiwa fuskar ta don ba gwana bace wajen kwalliya, sai ta saka room slippers ta ɗauki wayan ta ta fita Parlour
Har a lokacin ABUL KHAIRI na zaune a saman dainning yana karya wa, sai dai yanzu ɗin waya yake yi da Rahina. A dai-dai lokacin da Maimuna ta fito yana dariya ne idanun sa suka faɗa kanta. Kasa ɗauke ido yayi a kanta har ta iso cikin parlour'n ta samu wuri a kan sofa ta Zauna don ta kasa ƙarisa wa wurin bare tayi Breakfast ɗin. Kasa ci gaba da wayan yayi saboda hankalin sa sosai ya rabu gida biyu, sai kawai yayi mata sallama yana ajiye wayan yaci gaba da abinda yake yi, can kuma sai ya ɗago kai fuska a ɗaure ya kalli inda Maimuna take zaune yace, "me kike yi a wurin baza ki zo ki karya ba?"
Tashi tayi kawai ta taho da sanyin jikin ta, a hankali taja kujera ta zauna a wanda yake facing ɗin sa. Sai da tayi ƙoƙarin daidaita nutsuwar ta sosai kafin ta ɗaga hannayen ta dake faman rawa ta soma serving kanta
Shi kuma da mamaki yake kallon ta har ta gama abin da take yi, kamar bazai yi magana ba kuma can sai ya dube ta yace, "wai ke in tambaye ki Ni dodo ne a wurin ki?"
Da sauri ta ɗago kai tana kallon sa sabida jin maganar a bazata, yanda ya zuba mata ido sai tayi saurin mayar wa zuciyar ta na faman buga wa kamar zata faso ƙirjin ta, ta kasa ma ba shi amsa don bata san me zata ce ba
Tsaki ya ja ya tashi ya bar wurin
Bata sake motsa wa ba har sai da ta dena jin motsin sa, kana ta ɗago kai a hankali kamar mara gaskiya tana kallon cikin parlour'n, ganin babu shi sai ta sauke ajiyan zuciya ta soma karyawan. Bata san meyasa ba take rasa nutsuwar ta duk idan yana wurin ta, duk yanda ta so ta riƙa daure wa kasa wa take yi, ta rigada ta sanya wa kanta tsoron shi, ko a wani irin yanayi ne ba ta jure wa. Bayan ta gama ta kwashe komi ta wuce da su kichen tayi wanke-wanke sannan ta fito
A lokacin ne ABUL KHAIRI ya fito har ya sauya shiga ya bi ƙofa ya fice ba tare da ya kalle ta ba
Ita kuma ganin haka yasa ta wuce saman dainning ɗin ta ɗauki wayan ta sai ta dawo parlour, sai da ta kunna t.v kafin ta zauna ta soma latsa wayan ta ta kira Ummu. Sun jima suna waya har da su Shureim da Yayan ta Aliyu kafin ta kashe ta kira Mamy, itama sun jima suna wayan tana ta tambayan ta, "ko akwai wani matsalan?" Amma tace mata, "a'a". Sai da suka yi waya da kowa, kafin ta koma ta kira Batool ta wayan ta suka soma hira cikin nishaɗi, a nan Maimunan take ce mata, "ya kamata yau ta zo tayi mata weekend".
Dariya Batool ɗin tayi tace, "a'a Ni da gidan ki ai sai da babban dalili sabida tsaro, kin san halin yaya ABUL haka kawai bazan riƙa zuwa masa gida ba wlh."
Cikin marairaice murya Maimuna tace, "don Allah ke kuwa haba Batool, wlh babu abinda zai miki ba ya nan ma ya fita, kuma na san bazai dawo ba ƙila sai yamma".
"Ni dai bazan zo ba gaskiya. Idan gani na kike so kiyi ai gobe akwai school zamu haɗu."
"Yanzu baza ki zo ba?"
"Eh". Tafaɗa tana mata dariya
"Shikenan." Tace tana kashe wayan nata cike da haushi. A fili kuma ta furta, "nima wata rana zan rama insha Allahu". Kwanciya tayi taci gaba da kallon ta a tashar Hijira T.v. Dayake Film ɗin Indon ƙauye suka saka shiyasa ya ɗauke mata hankali sai kwasan dariya take yi. A haka ta wuni currr har sai da ta ga ƙarshen Film ɗin. Ƙarfe ɗaya suka gama sai ta wuce tayi sallah ta shiga kichen. Tun tana yin girkin cikin sauri kar ABUL KHAIRI ya dawo har dai ta koma yi a natse. Zuwa biyu da rabi ta gama ta shirya a saman dainning taci nata sannan ta wuce ɗakin sa, gyara masa tayi da sauri da sauri don kar ma ya zo ya ganta. tana gama wa ta wuce ɗakin ta, books ɗin makarantan ta ta ɗauka ta soma revision tunda exams ma ya kusa. Tana nan zaune ta jiyo ƙaran buɗe Gate, hakan ya tabbatar mata ya dawo kenan. Karatun ta taci gaba da yi.
*******
ABUL KHAIRI na shigowa parlour'n kai tsaye ɗakin sa ya wuce, ya rage kayan jikin sa sannan yayi wanka ya sanya farar Singlet da three qwatern wando, computern sa ya ɗauka ya fita Parlour, zama yayi a saman sofa ya buɗe ya soma aiki. Yana nan zaune but hankalin sa ya rabu gida biyu yana jiran ko zai ga wulƙawan Maimuna. Jin shiru ya sa shi tashi tsaye yana jan tsaki ya nufi ɗakin ta, ko me ya tuna sai ya juya kawai ya wuce dainning ya zauna yayi serving ɗin kansa. Ba ya son ko kaɗan ya matsanta wa kansa da tunanin ta shiyasa gwara ya saba wa kansa da yin abu babu ita.
Yana gama wa Parlour ya koma ya ci gaba da aikin sa, har sai da aka kira sallan la'asar kafin ya tashi ya mayar da computern ɗaki ya ɗauro alwala ya fice.
A wannan daren ma ABUL KHAIRI haka ya sanya wa Maimuna maganin barci me ƙarfi a cikin fresh milk. Suna cikin cin abincin ne sai ya aike ta ɗakin sa ta ɗauko masa wayan sa bayan wayan na cikin aljihun wandon sa. Tana tashi ya buɗe na gaban ta ya sanya mata, dayake ta ɗauko nashi daya nata ɗaya
Sai da ta jima tana duba wa bata gani ba kafin ta dawo ta sanar masa
Ce mata yayi, "ta zauna taci abincin ta".
To dayake a takure take sai ta tsakula bata ci sosai ba ta tashi zata tafi ko taɓa fresh milk ɗin bata yi ba
Ya mayar da ita yace, "dolen ta taci abincin tunda ba asaran hatsi zata riƙa masa ba. Kullum ta dafa abinci sai ta ƙi ci sai kace shi ne uban masu kuɗi da zata riƙa masa albazaranci".
Maimuna dai babu yanda ta iya haka ta zauna taci gaba da cin abincin. Tsautsayi yasa ta ɗauki Fresh milk ɗin ta kora dashi, sosai ta sha kafin ta gama cin abincin
Shi kuma tuni ya tashi ma a wurin ya koma Parlour ya barta don ta sake
Ai ko tas ta shanye before ta tashi, dayake baki na son kwaɗayin. Bayan ta gama ta rufe coolarn ta kwashe komi ta kai kichen ta wuce ɗaki. Wanka tayi ta shirya cikin rigan barcin ta ta haye kan gado sai barci.
Haka ma wannan dare ABUL KHAIRI ya sake kusantan ta ba tare da sanin ta ba. Duk a tunanin ta wani mafarkin ne ta sake yi sai dai nauyin barci ya sa ta kasa tantance a gaske ne komi ke faruwa. Tun daga wannan ranan ABUL KHAIRI duk idan yana buƙatar ta babu ruwan sa sai dai ya ɗura mata maganin barci ya je gare ta
Al'amarin na bata mamaki domin tun tana jin canji a jikin ta har dai tazo ta saba da yanayin nan, kullum kuma sai ta roƙe Allah a kan ya yaye mata wannan matsalan amma abu sai ci gaba yake yi har ta gaji ma yanzu ta soma saba wa.
Da haka rayuwa taci gaba da gudana ga shi har lokacin jarabawan su ya zo na fast time.
****
Fannin Uncle Sani har gida ya zo ya sami ABUL KHAIRI da zancen auren Azeeza
Amma shi furr yace, "bazai iya auren ta ba".
Uncle Sani yace, "wlh sai ya aure ta muddin yana so ya zauna lafiya, dole ne sai ya auri Azeeza don be isa ya wulaƙanta masa ɗiya ba, gwara ma ya shirya tun yanzu lokaci kawai ya ɗiba masa sai ya aure ta".
Maimuna duk tana jin abun dake faruwa daga ɗakin ta saboda ɗaga murya yake yi, a zuciyar ta sai da ta ji babu daɗi gaba ɗaya a ranan sai ta rasa nutsuwar ta sabida maganar ya tsaya mata a rai, idan ABUL KHAIRI ya auri Azeeza ya rayuwar ta zata koma? ta san tabbas akwai matsala baza ta iya kishi da Azeeza ba, inuwar su ma ba ta zama wuri ɗaya bare su zauna lafiya. Haka kawai ta ji sam duk ta damu
Shi kansa ABUL KHAIRIN ya ga ta sauya masa amma be tambaye ta ba tunda har yanzu ba wai shiga harkan ta yake yi ba, iyakan ya ci abincin ta idan ya ga dama ya amsa gaisuwar ta, idan yana da abinda zai saka ta ya sanya ta tayi mishi, sai kuma idan dare yayi ya je kamar muna-fuki yayi bidirin sa da ita ya gyara duk wani abu da zata iya zargin sa ya waske ɗaki, a haka kullum yake domin shi har yanzu ya kasa tausan zuciyar sa ya je wurin ta da yardan ta ya amshi hakƙin sa, gani yake yi ba son ta yake yi ba shi kuma bazai iya zama ya lallaɓa ta ba. Kuma har yanzu suna tare da Rahina suna soyayya, tun tana nacin ya turo su yi aure har ta gaji sabida ya ce mata, "ta bari sai auren sa ya ɗan kwana biyu sannan su yi." Duk da ya rasa mene ne ya ja hankalin sa da har yake soyayya da ita, shi fa a cikin zuciyar sa ko kaɗan ba ya ƙaunar ta amma kuma yana jin zai iya auren ta, ko yana son yayi mata wulaƙanci ya rabu da ita da zaran ya ji muryan ta yake kasa wa tunda tuni har yanzu sai bibiyan malamai take yi don dai ta mallaki zuciyar sa, sai dai Allah da ikon sa yana iya bakin ƙoƙarin sa wajen addu'o i da sallan dare wanda hakan ke sa wa duk wani asiri da take mishi ba ya tasiri sosai a jikin sa.
********
Sai da su Maimuna suka gama jarabawa kafin ya kai ta gidan Mamy, ai kuwa ranan kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha tun sanda yayi mata albishir ɗin ta shirya su je, har suka kai gidan bakin ta ya ƙi rufuwa sai murna take yi
Haka ma Mamy babu wanda ya kai ta murna tsaban farin cikin ganin yanda Maimunan ta sauya, ta yi haske abun ta ta ƙara kyau sosai, har ƙiba ta ƙara da girma tubarakalla, kowa ya kalle ta sai ya ji sha'awar ta
Shiyasa ABUL KHAIRI yanzu ba ya gajiya da kallon ta sabida ba ƙaramin sauya masa tayi ba, yarinyan da yake kallon ta ƙarama amma haka ta girma ko wata ƴar shekara 25 ɗin baza ta nuna mata komi ba. Sai yanzu ma yake ƙara ganin kyakykyawar surar ta da kyawun da Allah yayi mata, amma ada idanun sa sun rufe saboda wata. (Dama an ce sai an rasa wani abun ake gane muhimmancin wani abun).
Mamy dai sai nan-nan da ita take yi domin tunda tayi mata kallo ɗaya ta gane tana da shigan ciki a jikin ta, abun har mamaki ya bata sai kuma ta koma dariya a ranta tana cewa, "oh su Baba na manya ana so ana kaiwa kasuwa, sai kace ba shi ne ya gama hatsaniya a kan auren ba amma ga shi har da guzuri muka samu, Kaii Allah ya shirya Baba na maza basu da kunya ko misƙala zarratan, ya gama ciko baki kuma ya zagaya ya bumbura wa ƴar mutane ciki ɗan ƙwal uba".
_Ina ma ɗaukacin masoya na fatan alkhairi. Allah ya bamu albarkatun wannan rana ta juma'a. Sharrukan da ke ciki Allah ya kare mu Amin ya Allah. JUMA'AT MUBARAKH FAN'S. 🤩💃💃💃🤸 🤸🤸 ayi weekend Lafiya._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 40*
*________* Sai dare suka yi haraman tafiya. Da za su tafin ne Abba ya ce, "ya saka rana a wannan satin ya kai Maimuna can Kaduna tayi hutun ta, inyaso idan sun koma school sai ya je ya ɗauko ta".
ABUL KHAIRI dake zaune yana jiran Maimunan ta fito sai da ya ɗago ya kalli Abban, kamar bazai yi magana ba sai kuma ya kasa jure wa yace, "Abba kana nufin har two weeks zata yi a can?"
"Eh mana. ko da wani matsala ne? Ka san dai bazai yiwu ka hana ta zuwa ba, yarinyan nan tun kafin auren ta take nan garin; sannan za'a yi auren nata ma bata je can ba sabida kara irin na iyayen nata, ka ga kuwa dole yanzu ta je ta zauna na kwanaki don ta gaisa da dangi, ai sun mana mutunci wlh".
Be dai sake cewa komi ba har suka fito suka hau mota suka wuce gida, suna shiga ko kallon inda Maimuna take be yi ba ya zarce ɗaki, maganar Abban ne duk ya tsaya masa arai, "to a kan me zai bar matar sa ta tafi wani uwa duniya har na tsawon sati biyu bayan shi kuma yana tsananin ɓukatar ta? kai gaskiya bazai iya ba dole akwai sake".
Koda washe gari yayi haka ya tashi duk a cikin fushi, ko kallon Maimuna ya ƙi bare ya ci abincin da ta dafa mishi, abu kaɗan sai yayi mata tsawa kamar tayi masa wani laifi
Hakan yasa itama ta kama kanta ko fito wa a ɗaki ta kasa yi gudun kar ya bige ta, sai dai duk ta damu sabida ganin sa a cikin damuwa, but baza ta iya tambayar sa ba tunda ma bata ga fuska ba har yanzu
Shi kuwa ya so ya kaita gidan Hajiya Mama ne da gidan su Abba a yau ɗin, amma jin abinda Abba yace duk sai ya fasa acewar sa, "bazai kai ta ɗin ba".
Bayan kwana uku ko maganar be sake yi ba sai da Abba ya kira sa ya tuna masa kuma yayi masa umarnin, "goben nan su wuce Kaduna". Dalilin da yasa kenan ya sanya ta ta shirya kayan ta ya sanar mata inda zai kai ta
Ai murnan da ta nuna sai kuma abun ya zame mata matsala, domin a ranan rufe idon sa yayi ya dinga mata faɗa wai, "gasa ta yake Yi a gidan ko kuma gidan nasa gidan yari ne da har take murnan fita a cikin sa?" Ta inda yake shiga dai ba ta nan yake fita ba, har so yayi ya mangare ta tsaban haushin ta da yake ji
Ita kuwa baiwar Allah Maimuna saboda tsorata har kuka tayi jikin ta sai rawa yake yi
Har ya tafi ɗaki sai kuma ya dawo yace, "idan bata rufe masa baki ba sai ya gasa ta a gidan nan, kuma idan tayi wasa babu inda zata je ko sama da ƙasa zata haɗe ita da gidan su har abada." Daga ƙarshe ma sanya ta yayi ta biyo sa ɗaki tayi masa tausa
Abun tamkar a mafarki ta ji zancen sa, sai dai kuma a yanda take a tsorace dashi babu musu ta bi shi ɗakin jiki na rawa ta soma masa abinda ya saka ta. A taƙaice dai bata baro ɗakin ba sai washe gari, tunda take a gidan bata taɓa kwana a ɗakin nasa ba sai yau. Yau ido buɗe ya amshi haƙƙin sa a wurin ta babu maganar ma tuna wa da raini
Bazan iya misalta muku yanda Maimuna ta kasance a lokacin ba. Har suka tafi ta kasa haɗa ido dashi tsaban tsananin kunya da ganin abun da tayi tamkar a mafarki, ko kaɗan ko kusa bata taɓa tunanin tana da matsayin ma da ABUL KHAIRI zai iya haɗa ɗaki da ita ba bare har ya haɗa shimfiɗa da ita, amma yau kuma abun sai ya zo mata a matuƙar bazata har ta kasa ma tantance anya shi ɗin ne ko kuwa wani ne?.
Gidan Mamy suka je don su yi musu sallama, duk ta kasa sakin jikin ta gaba ɗaya sabida kawai abun da ya faru da ita a daren jiya, gani take yi kamar ma kowa ya san abun da ta aikata, ko magana ba ta iya yi
Mamy har dai ta gaji ta cire baki ta tambaye ta, "ko bata da lafiya ne?"
Amma ina ta kasa bata amsa don daƙyar ta iya girgiza mata kai idanun ta a ƙasa ko kallon su ba ta iya yi
Shi kuwa ABUL KHAIRI kallon ta yayi yana taɓe baki a ransa yana mamakin halin ta, kwata-kwata bata waye ba, shi yana son mace wayayyiya ba irin Maimuna ba, halin ta yana ɗaya daga cikin abubuwan da ya tsana a rayuwar sa, kullum ka ganta kamar wata muna-fuka, magana ma wannan yana mata wahalan yi.
Duk yanda Batool tayi da tsokanar ta itama ɗin sai dai ta gaji ta kyale ta, ta zama tamkar sokuwa kamar wata za'a yanka ta a gidan.
Zuwa biyu suka kama hanyar Kaduna. Har suka kai ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta iya yi a motan. Shima ko bi ta kanta be yi ba bare ya kalle ta.
Dayake can Kadunan sun san da zuwan su, koda suka isa an yi musu tarba me kyau kamar za'a goya su domin sun ji daɗin zuwan su ba kaɗan ba
Be wani jima ba yace, "zai tafi".
Shi ne Ummu ta sanya ta ta je su yi sallama
Har bakin motan ta je ta same sa sabida a lokacin har ya shiga mota suna magana da Aliyu
Aliyun ya fara hango ta shiyasa ya saki dariya yana cewa, "oh su Maimuna me miji. wai kin zo rako sa ne?"
Duƙar da kanta tayi tana murmushi don ta kasa magana ganin har ABUL KHAIRIN kallon ta yake yi
Shi kuwa taɓe bakin sa yayi yana kallon Aliyun yace, "ka dena tsokanar min mata kaji ko? Idan ba haka ba ka san hali na".
Still dariya Aliyu yayi yana faɗin, "sorry bro baran ƙara ba, Ni kaga na tafi ma, ka gaishe da su Mamy don Allah".
"Babu komi za su ji".
Hannu ya ƙara basa suka gaisa kafin ya wuce gida
ABUL KHAIRIN ɗago kai yayi ya kalle ta ganin har yanzu tana a inda take ta ƙi ƙariso wa, sai da ya ja gajeren tsaki yace, "me kike jira kuma a wurin?"
Ɗago kai tayi ta kalle sa, sai ya ballara mata harara, hakan yasa tayi saurin ɗauke nata idon a kansa tana matsowa wurin sa, sai dai ta kasa ma magana don bata san ma ta ina zata fara ba
"Idan baki da abun faɗa Ni zan wuce".
Hannayen ta take ta mulmula wa daƙyar ta iya buɗe baki still kanta na ƙasa tace, "dama Ummu ce tace in zo muyi sallama".
"Ok idan bata ce ba baza ki zo ba kenan?" Yayi maganar idanun sa a kanta
Shiru tayi
Shima sai yayi shirun kawai yana jingina kansa a motan tare da rufe idanuwan sa
Sun fi mintuna goma a haka babu wanda ya sake magana. Ba ma ta ɗago kai ba bare ta san a halin da yake ciki domin kunyan abun da ya faru da su jiya yasa gaba ɗaya ko kaɗan ba ta iya haɗa ido dashi sai a tsautsayi, tsananin kunyan sa da take ji yanzu ya ninku sosai.
"Wai me kike jira ne?" Yayi maganar a fusace bayan da ya ɗago kai yana kallon ta
Murya na rawa tace, "kayi haƙuri don Allah".
Yanda tayin ne sai ta ba shi tausayi, gaba ɗaya tsoro ya nuna a tattare da ita har ɓarin jiki take yi. Be san meyasa take jin tsoron sa sosai ba, yana ga kamar hakan ne yasa ba ta iya sakin jiki da shi, shi kuma gaskiya bazai iya zama da ita a haka ba, shiyasa yanzu ɗin ya ɗan sassauta murya yace da ita, "babu addu'a?".
Har ɗago kai tayi ta kalle sa saboda jin muryan sa a matuƙar sanyaye kamar ba shi ba
Murmushi ya sakar mata
Wannan dalilin ne yasa ta ɗan ji sanyi a ranta, murya a raunane tace, "Allah ya tsare hanya Allah ya kai ka lafiya".
Hannu yasa ya riƙo nata ba tare da ya amsa ba yace, "ɗago ki kalle Ni".
Kasa ɗago wa tayi
"Ɗago mana ƙanwata wai meye na kunyan ne? Ina ce Ni mijin ki ne?"
Hoi! Maimuna tamkar ta nitse a ƙasa take ji a wannan lokacin, sai dai babu yanda ta iya dole ta ari jarumta sosai kafin ta iya ɗago wa ta kalle sa, bata bari sun haɗa ido ba ta sake mayar da kan ƙasa
Shi fa abun nata ma ya fara basa dariya, shiyasa yace, "ta zagaya ta shiga motan".
Babu musu tayi abun da yace
Hannun ta ya sake riƙo wa yace, "ta ɗago ta kalle sa".
A wannan time ɗin ma daƙyar ta ɗago ido ta kalle sa, still dai ta ƙi haɗa ido da shi
Shi kuma sai ya juya sosai yana facing ɗin ta tare da kama fuskar ta da tafukan hannayen sa duka ya ɗago kanta sosai ta yanda dole ko tana so ko bata so sai ta haɗa ido dashi
Ai kuwa tana saka idanun nata a cikin nasa ta mayar da su ta rufe don ta kasa jure wa
"Wai ke ina wasa da ke ne baza ki buɗe ido ki kalle Ni ba? Yau dole sai mun yi kallon ƙuda kafin na bar ki ki koma, idan kuma ba haka ba sai dai mu koma Kano a yanzun nan tare dake".
Jin abun da yace yasa ta buɗe ta zuba masa idanuwan nata bata da yanda zata yi
Guntun murmushi ya saki yace, "lallai ne yarinya kina da aiki. Amma meyasa kike jin kunya na ne haka?"
Bata iya basa amsa ba sai sauke kwayar idon nata ƙasa tayi domin ta kasa jure irin wannan kallon da yake mata, ji take yi tamkar wani abu yana jawo ta izuwa cikin idanun nasa, kuma duk soconni bugun numfashin ta na ƙara ƙarfi kamar zai faso ƙirjin ta ya fito tsaban yanda take ji, tafukan hannayen ta da ta tamke su duk sun jiƙe sabida tsoro
"I said if I'm talking to you don't keep me quiet."
"Kayi haƙuri". Tafaɗa da rawan murya
Kallon ta kawai yake yi be sake cewa komi ba yana examines how beautiful her face is. Sai kuma ya matso da fuskar sa ya haɗe bakin su waje ɗaya ba tare da tayi tunanin hakan ba. He had been sucking her mouth for a long time before releasing his breath his eyes on her face which had already ta rufe idanuwan ta ruf ko motsin kirki ba ta iya yi, domin har yanzu yana rike da fuskar ta ya ƙi saki. "Ki kula min da kanki, ban da magana da maza ko waye ne har a cikin family ɗin ki, so be careful". Sai ya shafa fuskar nata har saman idanuwan ta yana zagaye su kafin ya sake kai bakin sa yayi kissing ɗin idanuwan sannan ya koma kan kujeran sa sosai yana ajiyan numfashi. Ɗan dafe kansa yayi na ɗan wani lokaci
While ita kuma tuni ta ja jikin ta ta sake cure wa wuri ɗaya, yanda ta shiga shock da abinda yayi mata ko yatsan ta ba ta tunanin zata iya ɗaga wa because of kunya
"Ki sauka zan tafi kar nayi dare". Yayi maganar a kasalance bayan ya mayar da idanun sa kanta
A hankali ta sanya hannu ta buɗe motan ta fice, ko juyo wa bata yi ba ta shige cikin gidan su
Shi kuma ƙofan yake ta bi da kallo ya kasa tafiya, ya jima a haka kafin ya ja motan ya wuce.
_Kun rage Comments. Ko a tafi hutu ne tunda naga kun gaji. Nima ɗin haka?. Bani da lafiya ina buƙatar addu'ar ku._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
_Masoya na na nesa dana kusa, waɗanda na sani da waɗanda ban sani ba, ina matuƙar ƙaunar ku sosai, Wannan shafin naku ne domin Allah. Allah ya bar mu tare. Amin._
*________________________________*
*PAGE 41*
*________* Maimuna da ta shiga parlour'n su Aliyu da Shureim ta gani, Ummu kuma na ɗaki. Tana shigo wa Shureim ya taso da gudu ya rungume ta
Aliyu kuma tuni ya soma tsokanar ta
Itama kuma sai murmushi take yi ta samu wuri ta zauna kafin tace, "Haba yaya ka dena don Allah".
"Babu wannan zancen, idan kin ga na dena to sai dai kin bar gidan nan ne, Kaii! amma wlh kun dace sosai kin ga yanda a ɗan lokaci ƙanƙani kika sauya? Wooo Yaya ABUL ya iya kiwo alƙur'an".
Buga ƙafa ta soma yi zata yi masa kuka
Sai yayi dariya yace, "to kiyi kukan mana ai ga Shureim nan sai yayi miki dariya babu ruwa na".
Kallon Shureim ɗin tayi da cewa, "Wai haka Baby na?"
Girgiza mata kai yayi yace, "a'a Ni bazan miki dariya ba, kuma zan haɗa shi da Baba ne idan ya dawo".
"Yauwa sweet Baby na. Bani hannu mu kashe".
Ya miƙa mata hannun kuwa suka kashe suna dariya
Aliyu yace, "Ni Ko Shureim? Ai zamu haɗu ne idan ta tafi bazan riƙa zuwa da kai shan ice cream ba".
"Kaji nima ai zan siya maka ko?"
Gyaɗa mata kai yayi
Tace, "yauwa Baby na, Ina Ummu ne?"
Shureim yace, "tana ɗaki".
"To bari in je in dawo akwai tsaraban da zan baka kaji?"
Ai ko tsalle ya fara yi
Ita kuma ta tashi tana murmushi ta shige ɗakin Ummu
Ummu na zaune a bakin gadon ta tana shafa mai kasancewar daga wanka ta fito. Bayan Maimunan ta shigo ne take tambayar ta, "har ABUL KHAIRIN ya tafi ne?"
"Eh ya tafi tun ɗazu".
"Ok ki je kema ki ɗibi ruwa a kichen kiyi wanka kafin a kira magriba, famfon Toilet ɗin ya lalace ne sai ki ƙara min zan yiwa Shureim".
"To". Tace da ita tana fice wa
Da kallo ita kuma ta bi bayan ta, a ranta tana me farin cikin ganin ɗiyar ta cikin kwanciyar hankali, tabbas ba kamar yadda suka zata bane da alamu suna zaune lafiya tunda ga shi har sakamako ya nuna, domin tun kallon farko ta gane tana da ciki. Murmushi kawai tayi tana ci gaba da shafa mai ɗin ta.
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
ABUL KHAIRI ba shi ya shiga Kano ba sai takwas da rabi, kai tsaye gida ya wuce yayi wanka ya rama sallolin da ake bin sa, daga shi sai Singlet da gajeren wando ya fito ya shiga kichen ya haɗa tea ya koma Parlour ya zauna. Tea ɗin yake kurɓa but hankalin sa yana wani wurin, tun yanzu har ya soma jin zuciyar sa da gangan jikin sa suna kewar Maimuna, shi kansa mamakin hakan yake yi domin tun sanda ya baro wurin zuciyar sa ta hana sa sukuni. Shin meyasa kwana biyun nan take yawan tsaya masa a rai ne? Meyasa ko wani abun yake yi sai ya riƙa tunano ta zuciyar sa na fasalta masa yanda take da yanayin ɗabi'ar ta, kyawun ta da komi nata? Har yana jin tamkar zuciyar sa tana son kamuwa da soyayyar ta, amma kuma shi ya san SO ɗaya ce, kuma ita ya yiwa Ziyada, ba ya tunanin akwai wata ɗiya mace da zai sake ƙauna makamanciyar yanda ya so Ziyada, shiyasa ya kasa gane abun da yake ji a game da ita, idan har so ne, kenan ana iya ƙaunar mutum biyu a lokaci ɗaya? Wata zuciyar nasa tace, "tabbas ana iya wa, idan kuma ba ayi kai za'a fara ta kanka, abubuwan da kake ji a game da ita iri ɗaya ne da yanda kake ji a kan Ziyada, ta yiwu rashin Ziyada a gare ka yasa duk wani ƙauna da kake mata yake son juye wa izuwa ga Maimuna". Cup ɗin hannun sa ya ajiye yana me jingina kansa da kujeran tare da lumshe idanuwan sa, a ransa ya furta, "kenan dai zai iya kamuwa da son Maimuna kamar yanda ya yiwa Ziyadan shi? Amma taya?" Gefe na zuciyar sa tace, "sabida ta cancanta domin ita matar ka ce". Numfashi ya ja bayan ya buɗe idanun nasa, sai dai be sake motsa wa ba saboda tunanukan da suka sha masa kai. Sai kuma can ya ɗauki wayan sa da zummar kiran Maimuna domin ya kasa jure wa, muryan ta kawai yake son ji, ga kuma tsananin buƙatar ta da yake fama da ita, amma kuma sai ya tuna be da Numban ta, be san sanda ya saki wayan a saman kujeran ba yana kwantar da kansa yayi shiru abun sa
Wayan nasa ne tayi ƙara saboda kiran da Rahina tayi masa
Daƙyar ya iya ɗago kansa don ganin wa ke kira? Arba da yayi da sunan Rahina sai ya ja dogon tsaki cike da tsananin takaicin ta a zuciya, har wayan ta katse be ɗauka ba, wani ta sake shigo wa, nan ma be ɗaga ba har ta katse sannan yasa hannu ya kashe wayan gaba ɗaya, ya miƙe da wayan a hannu yayi ɗaki. A wannan ranan daƙyar barci ya suri ABUL KHAIRI, yanda zuciyar sa ta ƙwazzabe sa da tunanin Maimuna har yake ji bazai taɓa iya jure rashin ta har na tsawon sati biyu ba, ba don dole Abba yayi masa ba babu yanda za'a yi ya barta ta je can uwa duniya ta bar sa, haba ai wannan cin zalun ne ma a ganin sa. Shiyasa washe gari da ya tashi duk ya rasa walwalan sa, be san meyasa ba har kuzarin sa ya rasa kawai harkokin sa yake yi ba don yana jin daɗin jikin sa ba. Yana tashi a wurin aikin sa kuwa gidan Mamy ya yiwa tsinke, zuwan sa ne ma yasa ya ɗan samu natsuwa sabida sun haɗu da Sulaiman suna ta hira.
Har dare yana gidan be tafi ba, duk kan su suka haɗu a Parlour suka ci abincin dare, bayan sun gama kuma suka koma hira, a nan ne ABUL KHAIRI ya cewa Batool, "ta ɗauko masa wayan Mamy". zuwa tayi ta ɗauko ta miƙa masa. A nan ya laluba ya cire Numban Maimuna
Duk a tunanin sa babu wanda zai fahimci abin da yayi, nan kuwa tuni Mamy ta harbo jirgin nasa, haka kawai zuciyar ta ta bata Numban Maimuna yake nema, sai kawai tayi murmushi tana kallon sa tace, "kuɗi zaka sanya min ne Baba na da kace a ɗauko maka?"
Murmushi yayi yace, "a'a wane Ni Mamy? Ai ke ce milonia, mu kam sai dai mu roƙa a wurin ki".
Dariya suka yi gaba ɗaya har su Abba da suke jin su
Sai ya miƙa wa Batool ɗin wayan yana me miƙe wa tsaye da cewa, "zai tafi". Sallama yayi musu sannan ya fice ya wuce gida. Sai da ya gama shirin sa ya kwanta kafin ya soma laluban Numban Maimuna.
*********
Lokacin Maimuna tana shirin kwanciya itama, tana saka rigan barcin ta ta ji wayan ta tana ring, tsaya wa tayi tana nufan wajen gadon ta ta ɗauki wayan dake saman gadon ta duba, ganin baƙuwar number sai bata ɗauka ba ta mayar ta ajiye sannan ta ƙarisa sanya rigan, sai ta zauna a gefen gadon a lokacin aka sake kiran nata, wannan karon ɗaukan wayan tayi bayan ta kara a kunne, sai dai bata yi magana ba
Daga can shima ABUL KHAIRI shiru yayi kawai yana sauke numfashi tare da jin sanyi a ransa jin ta ɗauki wayan. Ganin baza ta yi magana ba sai yace, "ba kya magana ne?"
Da sauri ta ciro wayan tana duba wa saboda jin muryan ABUL KHAIRI, zuciyar ta bata yarda ba sai da ta sake mayar wa tace, "Hello wane ne?"
"Wano ne, baki iya magana bane nace?"
"Na iya". Ta furta cikin sanyin murya da tsananin mamakin jin shi ne dai ya kira ta. "Ina wuni?" ta sake faɗa da sauri bata jira yayi magana ba
Sai da ya mirgina kwanciyar sa kafin yace, "Ƙalau. Ya mutan gidan?"
"Lafiya lau".
Sai kuma shiru ya biyo baya. While itama tana tunanin ta yanda aka yi ya samu Numban ta har ya kira ta
Shi kuma yana tunanin abun da zai ce mata, domin sai yanzu ma tunanin nasa ya dawo jikin sa tare da mamakin ya aka yi ma ya nemi wayan nata? Numfashi ya sauke kana yace, "yanzu me kike yi?"
Tace, "babu komi zan kwanta ne".
"Ok". Ya furta yana yin shiru
Kamar shuɗewar mintuna biyar babu wanda ya sake magana illa sauraron hucin numfashin su dake fita a hankali da suke yi
Tuni shi ya lumshe idanun sa yana ci gaba da sauraron numfashin ta dake dukan kunnen sa yana sake saukar masa da kasala. "Wai ke baki iya hira bane?" Yayi maganar a matuƙar sanyin murya
Daga can Maimuna saukar da kai ƙasa tayi kamar yana gaban ta, ta soma wasa da rigan jikin ta ta kasa furta komi, domin jin ta take yi a wani baƙon yanayi da bata taɓa tunanin kasancewar ta ba
"Duk ranan da na kama ki zaki sha mamaki na, I'm telling you don't keep quiet when I'm talking but ba kya jin magana ta".
"Kayi haƙuri don Allah bazan sake ba". Tayi maganar cikin rawan murya
"Shi kenan ya wuce. Ki kwanta kiyi barci, da safe zan kira ki".
Tace, "to".
Daga haka ya kashe wayan.
Ta kasa motsa wa daga inda take zaune sabida sosai abubuwan da ABUL KHAIRI yake mata daga shekaran jiya zuwa yau suka saka ta cikin wani irin yanayi, har mamaki take yi anya shi ne? Duk ya gama sauya mata kamar ba wanda ta sani ba. Tunanin sa yasa ta kasa kwanciya ma, ta jima a zaune a wurin daga ƙarshe ma sai ta koma ta kwanta tana me matse filow fuskar ta ɗauke da murmushi, "kar dai ace maganar Batool ne zai tabbata gaskiya? Ko dai ya fara son ta ne? Maybe ta fara shiga zuciyar sa". Da wannan tunanin yasa zuciyar ta tayi fari ƙal, one by one take tuna abun da ya faru a daren da zata taho, da kuma sallaman da suka yi jiya da zai tafi. A taƙaice dai daƙyar ranan Maimuna tayi barci saboda tunanin ABUL KHAIRI.
Haka shima a fannin sa ya gaza barcin, ganin zai ɓata wa kansa lokaci sai ya tashi ya soma jero salloli har zuwa asuba kafin ya samu yayi barcin, zuwa takwas ya tashi ya yi shirin sa, a lokacin ne ya ɗauki waya ya sake kiran Maimuna
Lokacin suna Parlour suna karin safe duk kan su, dayake suna kan dainning ne wayan kuma ta ajiye a can kan kujeran Parlour, ta ji wayan na ƙara, tuni zuciyar ta ta bata shi ne shiyasa tana rawan jiki ta miƙe ta nufi wurin
Su Ummu kuma sai suka bi ta da kallo babu wanda yayi magana sai Aliyu da ya ɗaga murya yana cewa, "Ƴar ƙanwata Yaya ABUL ne ya kira? Ki kawo mu gaisa to idan kin gama".
Baba yace, "kai dai kayi ƙaton banza Ali, ka bar yarinyata ta huta a gidan nan duk ka gama saka mata idanu fa".
Ita dai Maimuna tuni kunya yasa ta shige ɗaki da sauri, kamar yanda tayi zaton shi ne ya kira ta shi ɗin ne kuwa. Bayan ta ɗauka ita ta soma sallama
Ya amsa mata sallaman cikin cool voice ɗin sa
"Ina kwana yaya?"
Sai da ya ɗan ɗau soconni kafin ya amsa ta yana tambayar mutanen gidan?
"Lafiya lau suke suna gaishe ka, har da Yaya Aliyu".
"Hmmm ina amsa wa. Ya kwanan baƙunta?"
Maimuna idanu ta ɗan buɗe da mamaki ta furta, "baƙunta kuma?"
"Eh mana".
A karo na farko ta dara sabida yanda maganar nasa ya bata dariya
While lumshe idanuwan sa yayi sautin dariyan nata yana hautsina masa zuciya. A hankali yace, "why are you laughing?"
Shiru tayi, sai kuma ta tuna kashedin sa tayi saurin faɗin, "babu komi".
"A'a ban yarda ba sai kin faɗa".
"Allah yaya babu komi". Tayi maganar cikin shagwaɓa
Wani irin yarrr ABUL KHAIRI ya ji daga saman kansa har ƙasan tafukan ƙafafuwan sa, da sauri ya sami wuri ya zauna a gefen gadon sa yana me sakin numfashi a hankali a hankali. Tsit yayi be sake furta komi ba
Ita kuma jin shiru sai tace, "Hello Yaya".
"Umm". Ya furta cikin wani irin murya
Itama kasa magana tayi saboda yanda muryan nasa ya saukar mata da kasala, sai ta koma wasa da kwalliyan rigan ta tana sauraron bugun numfashin sa da a yanzu ya sauya sosai
"Tell me you miss me?" He spoke in a very low voice
Take ta lumshe idanuwan ta tana me kwanta wa a kan gadon, ta kasa ma magana sabida jin abin da ya tsarga mata daga cikin zuciya zuwa ilahirin jikin ta, Suddenly her heart rate changed
"You are silent?"
Cike da tsananin kunya har tana rufe idanu tace, "Yes I miss You".
"Really?"
Gyaɗa masa kai tayi, sai kuma ta tuna ba ya ganin ta sai ta amsa masa da, "um".
Numfashi ya sauke kafin yace, "ok in zo in ɗauke ki gobe kin fi son zama da Ni ko?"
Tsit tayi tana sake ƙudundune fuska
Cikin sanyin murya ya kira sunan ta, "Maimuna".
"Umm".
"Ko kar in zo ɗaukan ki?"
"Eh".
Numfashi ya sauke be sake cewa komi ba, sai kuma can yace, "wato ba kya son zama dani ko?"
"A'a ina so". Tayi maganar da sauri
"Ok amma kin ce kar in zo? Why?"
"Babu komi".
"Shikenan. Zan tafi Office Kar in yi late, take care". Daga haka ya kashe wayan be jira cewar ta ba
Ita kuwa kasa motsa wa tayi daga kwancen da take, haka kawai take ji gefe na zuciyar ta ta shiga ƙunci da kashe wayan da yayi, bata so hakan ba, ji take yi kamar su dauwama suna tare a haka. While wani sashi na zuciyar ta kuma tsananin farin ciki ne ya cika ta, tana ji tamkar babu wanda ya kaita farin ciki a wannan time ɗin, gaba ɗaya ta kasa sukuni sai juye-juye take yi tana faman tunani, ta rasa wani irin yanayi ne take jin haka a wannan lokacin. Ta fi ƙarfin mintuna goma da gama wayan nasu amma bata tashi ba. Sai da Shureim ya shigo ɗakin ya kira ta, wai in ji Ummu, "idan ta gama wayan ta fito haka nan". Shi ne fa ta tashi tabi bayan sa. Duk ta tsargu daga kallon da Ummu take mata, domin a lokacin ita kaɗai ce a zaune a parlour'n; Aliyu da Baba sun fita
"Ki zauna ki ƙarisa karin naki lokaci na ƙure wa kar su ji ki shiru kin zo kuma baki shiga kin gaishe su ba".
"To". Kawai tace tana wuce wa kan dainning ɗin, abincin ta ci gaba da ci har ta gama kafin ta taso ta je ɗaki ta ɗauko gyalen ta, babban mayafi ne baƙi ta sanya tun daga saman kanta, jikin ta kuma sanye da riga da skert na lees me ruwan madara da ratsin baƙi-baƙi na kwalliya da aka yi, sun yi mata kyau kayan sosai domin ba ƙaramin sake haska ta suka yi ba, ga shi yanda ta ɗan yi ɓul-ɓul da ita tayi fresh kowa ya kalle ta sai ya sake kallon ta babu hassada
Ummu tace, "su tafi da Shureim ya raka ta".
Tare suka fice suka wuce gidan Kakannin su wajen Mahaifiyar Baba. Dayake mahaifin sa ya rasu ita kaɗai ce a gidan sai kuma kusa da gidan da sauran dangin su suke, can kuma babban gida ne da Yayyin Baba da ƙannin sa suke ciki da iyalan su. Gidan Umman suka soma shiga
Ganin su yasa tayi farin ciki matuƙa domin basu da labarin zuwan nata sai yanzu da Baba suka fice yake faɗa mata. Tayi murna matuƙa musamman da ta ga yanda ta sauya gaba ɗaya har da ɗan tsaraban ciki da ta ƙyalla ido ta gani. Hakan yasa take ta haba-haba da ita ta kawo mata wannan ta kawo mata wancan na abubuwan ƙwalama da su tsofaffi ba a raba su da shi
Sosai kuwa Maimuna ta ji daɗin hakan, shiyasa ta ci ta ƙoshi kamar ba yanzu tayi karin safe ba, to ranta ya biya musamman kwaɗon zogalen da ta bata, shi har a leda tayi guzurin sa. Ta fi awa ɗaya a gidan kamar baza ta tafi ba ta shantake sai hira suke yi da Umma suna kwasan dariya. Sai daga baya suka wuce babban gidan nasu tabi sasa-sasa tana gaishe su
Ai kuwa sun yi murna da ganin ta, kowa yace, "Maimuna.. Maimuna.."
Ita dai sai murmusawa take yi cike da kunya irin nata
Yayinda yaran gidan duk inda ta saka ƙafa bin ta suke yi, kun san Amare da farin jini bare ita ta jima ba ta garin sun yi kewar ta matuƙa, har da sa'annin ta na gidan suke biye da ita, kowa ya kalle ta sai ta ba shi sha'awa kamar ba ita ba sosai tayi musu girma a idanu ta sake sauya kamanni
Shiyasa da ta tashi tafiya har gidan su suka bi ta. A can suka ƙarisa zaman su suna tare da Maimunan har dare sannan suka tafi.
Washe gari kuma sai ta wuce gidajen su ƙannin Baba da ƴan uwan sa mata. Haka dai Maimuna tayi ta biye-biyen dangi. Har gidan su Aunty Rufaida da Aunty Naana duk ta je ta yi musu wuni. A can ne ma Aunty Naanan ta sake zaunar da ita tana ta koya mata dabarun zama da miji da yanda zata riƙa sace zuciyar mijin ta da kuma tattalin sa, musamman yanda ta ga ta sauya don itama har ta gane tana da shigan ciki shiyasa ta ɗibi kayan gyaran ta duk ta zuba mata a jaka tayi mata bayanin yanda zata riƙa amfani da su, ta kuma koya mata wasu daga cikin kayan fruit da yanda zata riƙa sarrafa su tana sha don amfanin kanta
Dayake Maimuna ta san halin Aunty Naana shiyasa ko tari ba tayi, ta natsu sosai ta fahimci komi da ta koya mata.
Satin ta ɗaya a wannan lokacin kullum sai sun yi waya da ABUL KHAIRI, har wani sabo ne ya shiga tsakanin su domin ɗayan su ba ya iya barci be ji muryan ɗaya ba, gaba ɗaya sun kamu da tsananin soyayyar junan su amma babu wanda ya amince da hakan.
Ana saura kwana huɗu ta cika sati biyun ne ta wuce Zaria gidan Aunty Fatima shima a can zata yi mata kwana biyu before ta koma Kaduna, daga can kuma ABUL KHAIRI zai zo ya ɗauke ta.
_Idan da yiwuwar gobe zaku ji Ni to.. har yanzu ina bukatar addu'ar ku ina fama da matsanancin ciwo sosai. I do this for your joy because of my waiting you do. Sai kun sake ji na._
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*ABUL KHAIRI*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
💧💧 *LABARIN DEEBIZAH RETURN* 💧💧
*MALLAKAR:*✍️
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PARFECT*🧝🏻♀️
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
'''(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*✍️
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar ga Mahaifiya ta Abar alfahari na, Uwata maganin kuka na, I love You so Much Momma_ ❤️
*________________________________*
*PAGE 42*
*________* Kwanan Maimuna biyu a Zaria kafin ta koma Kaduna. Sanda ta cike sati biyu sai ga ABUL KHAIRI da ƙarfe 10:20am. Ya dira a gidan
A lokacin itama har ta gama shirin ta don shi kaɗai take jira tunda ya sanar mata ta shirya ɗin
Suna Parlour ita da Ummu ya shigo. Sai da ya zauna kafin suka gaisa da Ummu tana tambayar sa hanya
Maimuna da tun shigowan sa ta mayar da kai ƙasa sai a lokacin ta gaishe sa
Ya ɗago kai yana kallon ta, amsa mata yayi idanun sa ƙyam a kan ta sabida mugun sauya masa da tayi, tayi wani irin cika sosai tayi luwai-luwai kamar wacce ya shekara be gan ta ba, a ransa yace, "ko dai Ummu wani abun take bata ne?"
While Ummu kuwa farin ciki ne sosai ya sake cika ta ganin gaba ɗaya hankalin ABUL KHAIRIN ya tafi ga ɗiyar ta, wannan ya nuna mata tabbas Maimuna tana a cikin zuciyar sa, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba. Ita ce ta kalli Maimunan ganin ta kasa tashi bare ta ɗauko mishi ko ruwa ne, sai tace, "haka zaki bar sa babu wani abun? Ki tashi ki ɗauko mishi drinks mana".
"To". Tace mata tana tashi ta wuce gaban Fridge ɗin nasu
Har ta je ta dawo ta kawo masa a gaban sa kallon ta yake yi ya kasa ɗauke ido a kanta. Bayan ta zuba masa ya amsa ya sha kafin ya kalli Ummun yace, "ina su Baba ne?"
"Sun je wajen aiki, amma dai yanzu zai dawo don ya ce idan ka zo in Kira sa kuyi sallama".
Jinjina kansa yayi yana ɗan sake ɗago kai ya saci kallon Maimuna
Itama duk ta takure saboda sosai ta ji a jikin ta yana kallon ta, ga tsananin kunya da ya rufe ta duk da ta saka mayafin ta a jiki domin a shirye take tsab tafiya kawai za su yi.
Babu jima wa Baba ya dawo suka gaisa da ABUL KHAIRIN, basu wani jima ba suka yi musu sallama suka kamo hanyar Kano
Tunda suka shiga mota babu me magana haka yake ta tuƙin nasa. But jefi-jefi yana mayar da hankalin sa gare ta amma ya kasa furta mata komi
Ita kuwa sai wasa take yi da yatsun hannun ta, kaɗan-kaɗan kuma tana jefa idanuwan ta saman kwalta tana kallon hanya.
A haka har suka shigo Kano, kai tsaye gidan su Mamy suka wuce
Sun yi murnan ganin su ba kamar Mamy ma, sosai taji daɗin ganin Maimunan ta sake sauya wa hakan ya sake tabbatar mata tabbas akwai ciki a jikin ta.
A can suka wuni sai dare suka wuce gida
Kai tsaye Maimuna ɗakin ta ta wuce ta soma wanka saboda gajiyan mota, gaba ɗaya ta gama gajiya ga mugun barci da take ji, shiyasa tana gama wanka ta saka kayan barcin ta tabi lafiyan gado tunda sun ci abinci a gidan Mamy.
Shiru-shiru ABUL KHAIRI yana tunanin zai ganta a Parlour amma ya ji ta tsit, dole ya taso ya biyo ta ɗakin ya hange ta har tayi nisa da barcin ta ma. Tsaya wa yayi kawai yana kallon ta ya kasa koma wa. Sai da ya ɓata lokacin sa a tsaye a wurin kafin ya juya ya wuce ɗaki, wanka yayi ya shirya ya wuce ɗakin nata cox he would never tolerate her because he missed her so much
Maimuna na barci ta ji mutum a jikin ta, bata ma gama tantance a magagin barci take ba taji muryan sa yana raɗa mata magana, dole ta wartsake a barcin. But she could not, so they spent the night together sai da asuba ya bar ɗakin.
Haka rayuwa taci gaba da gudana, a ɗan ƙanƙanin lokaci rayuwar auren su tana neman sauya wa domin abubuwa da dama yanzu sun sauya a zamantakewar su. Tun Maimuna tana jin kunyan sa sosai tana ganin abubuwan ne tamkar a mafarki, sai dai kuma a haka take jure wa tana yin duk abun da zai faranta masa rai, duk abinda ta san yana so tana yi domin farin cikin sa, bata da buri a yanzu sama da su kasance a haka, shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakanin su, ba sa iya jin daɗi idan ba sun ji ɗumin juna ba, ko a yaushe suna a tare, ko a Office yake yana ƙoƙarin ya ga ya kira ta sun yi waya, ko yana son hana zuciyar sa amma ba ta hanuwa dole sai ya ji muryan ta kafin yake samun sukuni, haka itama, shi a yanzu sosai ya fahimci ya kamu da ƙaunar Maimuna, domin duk abubuwan da yake ji a game da ita the same abubuwan da yake ji ne sanda yake soyayya da Ziyada, tabbas ya yarda son ta yayi masa kamu a lokacin da be taɓa tsammani ba, shiyasa ya saka a zuciyar sa da ita zai rayu, zai koya mata yanda yake son matar sa ta kasance, duk wani kunya nata da rashin waye wa yana iya bakin ƙoƙarin sa wajen ya ga ta dena ta saki jiki sosai da shi, sai dai kuma abun a jinin ta yake, amma ita kanta ta fahimci ABUL KHAIRI yana son rayuwar wayewa shiyasa dai-dai gwargwado tana iya bakin ƙoƙarin ta koda daga baya zata koma tana jin kunyan sa ne, idan har zata faranta masa to zata yi
Duk wani sauyi da ya samu yanzu a tattare da matar sa shi ne dalilin da ya fara sanja akalan tunanin sa ga Rahina, yana ga kamar bata da abun da zai so ta da ya fi wadda Maimuna take dashi, shiyasa be ga amfanin auren ta ba, duk da dai har yanzu ya kasa yakice ta a jikin sa, wani ɓangare nasa yana jin son tarayya da ita, amma kuma kaso mafi yawa a zuciyar sa mugun haushin ta yake ji, shiyasa a yanzu ya tashi tsaye sosai yana sallan dare da roƙon Allah ya tsayar masa da zuciya wuri ɗaya, yanzu haka har yana samun damar gaya mata magana wanda a baya be samun hakan, kullum cikin faɗa suke da ƙorafin, "ta ishe sa".
Ita kuma sauyin da ta gani ne yasa ta sake bazama neman malamai duk dai ta siye zuciyar ABUL KHAIRI, ta zama tamkar karya a kansa. Ana haka tsautsayi ya gifta mata garin zuwa wajen Malamin ta tayi hatsari, take a nan ta mutu ko shurawa bata yi ba
Shi kansa ABUL KHAIRI be da labarin mutuwar nata domin tunda ya samu ta dena kiran sa ya goge numbobin ta. Ta fannin Azeeza ma tuni ya taka wa Uncle Sani birki domin yanda ya sako shi a gaba da sai ya auri Azeeza, shi kuma ya ce, "wlh bazai taɓa auren ta ba". Duk yanda aka juya sa ya ce, "bazai aure ta ba matar sa kaɗai ta ishe sa rayuwa". Har su Mamy da Abba sun shiga maganar sabida yanda maganar take so ta zama tsiya raga-raga, amma firr ya ƙi
Azeeza kuwa hakan yasa ta gudu ta shiga duniya tunda uban ta ya kasa mata abun da take so, baƙin cikin rasa ABUL KHAIRI ya hana ta sukuni shi ne ta gudu, tana ga kamar hakan zai sa ya ji tausayin ta a nemo ta ya aure ta
But shi ko a gefen hulan sa, ta matar sa yake yi domin yanzu soyayya sosai suke sha, ga cikin su yanzu da ya soma girma tunda tuni sun san tana da ciki, tun wani zazzaɓi da tayi na kwana ɗaya har suma tayi domin shi ya ɗauka ta mutu ma, hauka ne kawai be yi ba a lokacin. Sai da aka kaita asibiti tayi kwana biyu tana fama da zazzaɓi me zafi wanda yake saka surutai sabida zafin sa aga mutum kamar ya haukace
Su Ummu duk sai da suka zo gaishe ta sabida wannan rashin lafiyan da tayi
To ta dalilin hakan ne yasan tana da ciki tun sanda aka bincika ta aka gane musabbabin ciwon yana da alaƙa da cikin. Satin ta ɗaya a asibitin kafin ta warke. Tun daga lokacin kuma tattali ya sake sauya wa, babu Irin son da be nuna mata. Itama tuni ta gane ƙaunar sa yayi mata baƙe-baƙe a rai, gaba ɗayan su sun mayar da hankali kan junan su suna tattalin junan su. Har zuwa sanda ta haifu ta sami ƴa mace. Ranan suna yarinya taci sunan Ummu. Wato ADAMA za su na kiran ta da Ihsan.
A lokacin ne aka saka ranan auren Batool da Sulaiman tunda a time ɗin ne suka gama secondary School ɗin su, tuni soyayya me ƙarfi ya shiga tsakanin su. Zuwa watanni uku aka yi auren suka wuce Kaduna don a can yayi gidan sa.
*******
Sai da Maimuna tayi shekara ɗaya da haihuwa kafin ABUL KHAIRI ya nema mata addmition ta soma zuwa B.U.K. a yanzu dai komi ya ci gaba a wurin ta, domin dai-dai gwargwado ta zama wayayyiyar mace yanda Mijin nata yake so, baza kace ita bace saboda mugun sauyawan da tayi
A kullum ABUL KHAIRI alfahari yake yi da ita saboda samun ta da yayi a matsayin matar sa. Sai a yanzu yake sake godiya ga Allah da ya basa iyaye masu tsananin ƙaunar sa, waɗanda suka iya hangen nesa kuma suka gano masa nasa future ɗin, ga shi yanzu komi sai dai ya ce alhamdulillah sabida samun Maimuna a matsayin matar sa, mace ta gari me kunya da sanin ya kamata, a iya tsawon rayuwar su na aure bata taɓa ɓata masa a sanin ta ba sai dai a rashin sani, wanda dama aka ce zaman tare zo mu zauna zo mu saɓa, duk da a yanzu ta zama mace kamar yanda yake fata ya samu mata su yi rayuwa na ban birge wa, hutu da jin daɗi da kuma waye wa, duk ya samu but har a yanzu ɗin tana nuna kunyan ta gare shi, a kullum nuna wa take yi kamar yanzu suka soma sanin juna saboda tsananin kunyan ta, tabbas ya gane kunya a wurin mace wani babban jari ne da ƙawa da burge wa a wurin ta, duk macen da bata da kunya tabbas bata zama mace ba, mace me kunya ita ce mace, macen da duk abinda mijin ta yake buƙata zata yi masa amma ta cikin salo da jan aji da nuna kunyar ta ta ɗiya mace. shiyasa a koda yaushe yake sake jin ƙaunar ta na ƙara mamaye zuciyar sa, yana jin tamkar a yanzu ne ya fara son ta, kullum soyayyar ta sake zama sabo take yi a zuciyar sa, sabida iya mu'amalan ta da iya zaman ta, shiyasa a ko yaushe addu'ar sa Allah ya ƙara musu ƙaunar juna.
A yanzu haka shekara huɗu da ɗan watanni kenan da auren su, kuma a yanzu haka final exams suke rubuta wa a school, bata jima da sake haihuwar ɗiyar ta mace ba da Allah ya ba su don ko arba'in ma basu gama yi ba, yarinyan ta ci sunan Mamy Khadeejah, za suna kiran ta da Noor.
Itama Batool ta haifi ɗiyar ta mace me sunan Ummu ita suna kiran ta da Khairat, sai cikin na biyu da take ɗauke da shi.
Ko wani fanni Familyn suna a cikin farin ciki Masha Allah sai godiyar Allah.
_*ALHAMDULILLAH.. ALHMADULILLAH.. ALHMADULILLAH* Komi yayi farko aka ce zai yi ƙarshe, a yau na kawo ƙarshen littafi na me suna *ABUL KHAIRI* Alhmadulillah ina godiya ga Allah da ya nuna min wannan ranan, farin ciki na ba ya iya misaltuwa, kuma ina godiya ga duk FAN'S 🤩 ɗina da ta sanadiyyar su ne har na iya kammala wannan littafin, tabbas da ba don ku ba da tuni na ajiye alƙalami na, ina yi ne kawai domin farin cikin ku, Allah yasa hakan na isa gare ku, Allah yasa kuma ina faranta duk kan zuciyoyin ku? Ina fatan ya zame mana darasi da kuma tunatar wa a rayuwar mu. Na gode ga duk masoyana na fili dana baɗini. Love You so Much. 🤩_
Mu haɗu a sabon littafi na da yardan Allah idan Allah ya kai mu rai da lafiya. *MEEMA FAROUK*
*ƊANƊANO daga cikin littafin.
*RIYADH NORTH*
Hannun ta riƙe da bairo tana juya wa a kan book ɗin but ta kasa rubuta komi, tunani ne sosai a ranta wanda ya hana ta saƙat, shin yaushe ne zata kasance cikin farin ciki? Har yaushe ne komi zai wuce a rayuwar ta? Komi ya koma mata kamar baya? Idan ta zauna tana irin waɗannan tunanin sai taji da ace ba'a haife ta ba...
Faɗin da bairon nata yayi ne ya sanya ta dawo cikin hayyacin ta, idanun ta a kan bairon amma ba ta da alamun ɗauka, sai ta tsira mishi Sexy eyes ɗin ta a ɗan soconni kafin ta janye su tana jan ajiyan zuciya, lumshe idanun tayi a lokaci ɗaya tana buɗe su, ko kaɗan fuskar ta babu ɗigon fara'a wanda dama ta jima rabon da ta ganta cikin farin ciki, idan kuwa ka ga tayi murmushi sai dai tana gaban Abee ɗin ta ne, wannan kuma domin farin cikin shi take yi, ba ya ga haka babu wanda ke ganin dariyan ta bare murmushin ta a yanzu, ko yaushe a yanayi ɗaya take, walau farin ciki ko baƙin ciki, abin har ya zame mata jiki
Tashi tayi tana saka room silifers ɗin ta da ta zame su daga ƙafafun ta, sai ta taka a hankali ta nufi bakin windown ɗakin ta, hannayen ta ta sanya ta zuge cootin ɗin wanda haske ya bayyana a cikin ɗakin da ada babu, kanannaɗe hannayen ta tayi a ƙirji tana bin wajen da kallo, yayinda ta faɗa duniyar tunanin da ya zame mata jiki ko yaushe, tana tuna abubuwan dake faruwa a rayuwar ta
Daga ita sai guntun riga me ruwan Powder, dressed sleeping ne, sai gashin ta da ta ɗaure shi a ƙasan ƙeyanta ta sanya baƙin hula me kauri wanda ya fito mata da tuntun gashin nata, har kunnen ta ta rufe a cikin hulan wanda da alamu garin da akwai sanyi ne, duk da haka be sa ta sanya kayan sanyi ba, illa hulan dake kanta na sanyin, kuma ba wai don ba ta jin sanyin ba, sai dai ta saba da yanayin ne.
Ta jima a nan a tsaye kafin ta janye idanun ta tana wuce wa cikin Toilet, wanka tayi ta fito ɗaure da Towel a jikin ta, a lokacin ne ake mata Nocking a bakin ƙofar ta.
_Kar in cika ku da surutu bari in bar ku haka. Sai dai ina muku albishir salon na daban ne. coming soon. *MEEMA FAROUK*_
No comments