A SANADIN ABAYAR SALLAH Complete Hausa Novel
👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN ABAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘
Gajeren labari
By
Rabi'atu(Ummu Maher)
Wannan littafin nayi shine a ramadan domin ya fad'akar kuma ya ilimantar.
D'an d'ano daga littafin A sanadin a bayar salla.
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 1*
*Gidan Malam Tahir*
Salma yarinya ce mai hankali kowa a unguwarsu ya santa da hankali da hangen nesa, sai dai a gefe d'aya kuma Salma na da wata gur b'atacciyar k'awa mai suna Zuly wato Zulaihat, ta tura mata wata gur b'atacciyar a k'ida na cewa matuk'ar saurayin ta bai yi mata a bayar Sallah ta kece raini ba to ta rabu dashi tayi mai wulak'ancin da wani saurayi ba zai k'ara zuwa wajenta ba.
*GIDAN HAMISU*
Hamisu yana da mata kwaya d'aya mai suna Zeenat, Zeenatu dai bata tab'a haihuwa ba shekarar ta takwas, Amman hamisu bai tab'a yi mata gorin rashin haihuwa ba yana kula da i'ta dai dai k'arfinshi, Amman ita a b'angaren Zeenat ba haka yake ba domin i'ta Zeenatu gidan ta gidane na tara jama'ah ko wani kare da kiyashi kullum yana gidan, A saboda haka ne kullum Zeenat da Hamisu suke fad'a Saboda yayi_yayi tara mishi mutane tak'i a cewar ta wai i'ta ta Al'umma ce kuma ta jama'ah ce, don haka tare ya gansu i'ta ba za ta daina tara jama'ah ba.
Kwatsam wata rana ta tara y'an mata da matan Aure, da zawara , kawai sai wata mai suna Hauwa"tace Hmm kai ku tsaya kuji wani labari🤔 daya shigo mana kwana nan wai wannan Sallar yayin a baya za'ayi ta kece raini, nidai har mai gidana ya siyomun don ni kun san bana wasa da duk abunda ake yayi idan ba haka ba sai kaji a layi da cikin dangin ka ana gulmar ka ana cewa kai kullum kayan da kake saka wa baka saka na yayi, shiyyasa na dage akan saiya siyamun don nima in kece raini don ance baka yi bani waje🤔.
Salma ba tana jin haka i'tama ta d'orawa kanta dole dole saita saka abayar nan da akace sai anyi yayin ta da Sallah, don haka Hamisu yana dawowa ta saka mishi kuka akan cewa dole i'tama saiya siya mata abayar Sallah, Hamisu yace indai baifi k'arfinshi ba zai siya mata, Hamisu yace wa Zeenat ta tambayo kud'in.
Nanfa Zeenat ta kama murna, ta saka azuciyarta sai da safe zata tambayi Hauwa nawa aka siyo mata abayar Sallar ta don itama a siyo mata.
*Sai a shafi na gaba zaku ji yadda abun zai kaya don gane da gidan Malam tahir da Gidan Hamisu*
*Ummu Maher ce*
Ramadan kareem✍🏻
👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN ABAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘
Gajeren labari
By
Rabi'atu(Ummu Maher)Miss green💚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 2*
*Gidan Malam Tahir*
Where are u going?cike da tsiwa Salma tace kaga Bashir Abaya fa nace kayimun ta Sallah ka tsaya kana yimun wani k'arya k'arya sannan yanzu ka tambayeni ina zanje gidan ubana ma zan koma, Saboda na gaji da cizon sauro, kawai sai a kirawo mutum sauro yayi taci zanshi da sunan zance kai kuma ba za'ayi maka abun da kake so ba.
Wani wawan tsaki Salma tayi sannan tayi shigewarta gidansu tana sababi, Bashir kuwa kallon hanyar da Salma tayi kawai yake kallo, ya ambata afili yana mai cewa Ikon Allah yanzu abayar Sallar ce zata had'ani fad'a da Salma.
Yarinya mai tarbiyya da sanin ya kamata, A'iya saninshi yasan cewa Wannan ba tunanin Salma bane tabbas akwai wanda yake zuga Salmanshi?to waye wannan kuwa wanda yake son ya ruguza mishi farin cikinshi haka?.
*Gidan Hamisu*
Hamisu yana fita Zeenat ta fita daga gidanta zuwa gidan Hauwa don ta tambayeta nawa ne kud'in abayar?.
Hauwa i'na zaki je naga kina kulle gida?,dariya Hauwa tayi sannan ta ce"gimbiya ta gidanki nake son zuwa yanzu sai kuma ga ki kinzi.
Rik'e baki Zeenat tayi sannan ta ce yanzu Hauwa Har Deeni ya fita ne?.🤔Dariya Hauwa tayi"Tace Hmm ke dai muje kawai gidanki tunda na ga kema da magana a bakinki muje?.
Zeenat ta muskuta ta gyara zamanta sannan Ta ce"Hmm Hauwa daman tambayarki nake sonyi nawa ce a bayarnan ne?I'na son in saya don kinsan bazan yarda ace ana ya yin abu ba ni,kuma banyi ba.
Hauwa ta ce"No ai babu tsada Aminiyas dubu ashirin ce kacal babu yawa?.ta fad'i hakan tana dariya ciki_ciki don tasan da k'er Hamisu zai yarda ya siya.
Rik'e baki Zeenat tayi sannan ta ce"kai gaskiya tayi tsada da yawa,to amman babu komai zan gayawa Hamisu kinga komai tsadarta dole ne ya siyomun tunda i'na so.
Hauwa ta ce"Hmm ya dai kamata gaskiya ki samu kema ki saka abun ya yin nan don ance da abaka labari gwara ka bayar,suna cikin hirat Salma da Zuly suka shigo.
Zuly ta ce"kunsan Allah nifa koma meye zan i'ya yinsa don in samu wannan Abayar don nima i'nason in Faso gari,Dariya suka saka da shewa.
Salma kuwa tayi shiru tana d'an ya k'e wanda yafi kuka ciwi,Azuciyarya tana tunanin Masoyinta Bashir Irin wulak'ancin da tayi mishi duk A SANADIN ABAYAR SALLAH.
"Hamisu dakai fa nake kana jina kayi mun shiru?.
" To me zance miki kin ce in siya miki abaya na ce ki tambayi kud'in,kince dubu ashirince na ce miki bani da k'arfin siya miki sai ki sakani agaba kina zagi na kamar wani sa'anki,da za ki ringa gayamun duk abin da kika ga da ma".
*Ummu Maher ce*
👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN ABAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘
Gajeren Labari
By
Rabi'atu(Ummu Maher)Miss green💚
*💅💅Shalelen Jarumai Writer's Ass✍🏻.*
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 3*
*Gidan Hamisu*
Kai Hamisu tsaya kaji akan Nace ka saimin Abayar Sallah shine zaka zageni, to don Allah karik'e kud'inka banaso Amman kasani kome zanyi saina siya Abayar nan, Yanzu da kace baza ka siyamun yanzu haka nasan Ka saiwa Budurwar ka don duk abunda ka keyi ina nan gida ana kawomun maganarka.
Kuma Wallahi tunda kace baza ka siyamun ba ka yiwa kanka, don girki ma na daina yi maka shi tunda kai baka san mai yi maka ba 🤔🤨tana kaiwa nan ta saki wani tsaki tayi tafiyarta ba tare da tace komai ba.
Kallo Hamisu yabi Zeenat dashi na mamaki, don yaga alama idan ya cigaba da shiru watarana ma Zeenat zaneshi zatayi don A hallayar Hamisu baya son raini ko kad'an, badon son da ya keyiwa Salma ba da tuni ya mareta don bazai i'ya saka ido mace na yimai rashin tarbiyya ba .
*Gidan Malam Tahir*
Haba Aunty Salma yanzu akan Abayar Sallah shine kike yiwa Yaya Bashir wulak'anci mecece wata Abaya da akanta zaki zab'i k'unta tawa zuciyar da take sonki gaskiya baki kyau taba, Ke Habiba i'dan kika k'arayimun magana akan Bashir wallahi sai ranki ya b'aci kuma ki ficemun daga d'akina Nonsense kawai.🤨
Habiba"tace Yaya kiji tsoron Allah wallahi ki tuna fa babu abunda Yaya Bashir bai yi miki ba kina biyewa wannan mara tarbiyyar Zuly kuna abunda ranku ya keso agidan Zeenat ana zuga ku , kuma yanzu ma da kika ga baiyi miki ba, kinga bikinku bayan Sallah ne gashi yana gini kuma kinsan shike kula da gidansu, kinga kuwa dole....Fitarmun a d'aki ko in kwad'a miki mari banza kawai, zaki fita ko saina b'abb'alaki mara mutunci kawai, ke ki Aureshi mana muna fuka🤨.
Nanfa Salma ta mari Habiba kan kace meye An fara ko kawa Habiba ta kada Salma, Cikin Bacci Umma ta jiyo haya niya i'rin baccin nan na Azumi mai dad'i.
Habiba!Salma!!Habiba!!! Me zan gani haka?da k'er Umma ta raba y'ay'an nata sannan ta tambayesu abunda ya faru, Nanfa Salma tace wai Habiba ce tayi mata Rashin kunya, da sauri Habiba ta cafe ta bawa Mahaifiyarsu labarin abunda yake faruwa.
Salati Umma ta saki tare da kaiwa Salma duka, tana Cewa yanzu Salma daman haryanzu baki daina yawo da Zulaihat ba, yarinya fitsararriya wadda ta addabi kowa a unguwa i'ta kika zab'a ta zama k'awarki mai baki shawara, akan ki rabu da Saurayinki yaron kirki akan wata Abaya......
To bari kiji wallahi tallahi kiinji narantse duk ranarda na sake ganinki da Zuly saina b'allaki shasha kawai, Umma tana kaiwa nan tayi tafiyarta, Habiba kuwa kallon yayar tata tayi sannan tace A'i wanda baiji bari ba baya k'i gani ba, Salma tayo kan Habiba da sauri Habiba ta fita tana dariya.
Hmm Zuly ki samomin mafita akan wannan Matsalar don ni wallahi yanzu gaba ki d'aya na tsani Bashir da kayi mishi maganar kud'i saiya ce miki bashi dashi, akanshi aka fara babu.
Zuly"tace to ai ko me Bashir yayi banga laifinshi ba kece mai laifi, tun farko saida nace miki a zamanin nan ba'ah Saurayi 1 kika dage ke sai Bashir Ai gashi tun ba'aje ko ina ba ya nuna miki halinsu na maza🤔🤨.
"To yanzu Zuly ya za'ayi ne don ni kaina gaba ki d'aya ya kulle wallahi, " Zuly tace k'awata akwai mafita, Inada wani wanda daman ya soki sosai kece kika ce baki sonshi, gashi d'an masu kud'i.
"Me zai hana inyi mishi magana kinga shikkenan kin huta Abayarki za tazo hannu in Dubai ma kike so zaki samu
*Ummu Maher ce*
Ramadan karem👏👏
👏
👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN ABAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘
Gajeren Labari
By
Rabi'atu(Ummu Maher)Miss green💚
*💅💅Shalelen Jarumai Writer's Ass✍🏻*
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 4*
Shiru Salma tayi tana tunanin Maganar Aminyartata Zuly, Anya kuwa wannan shawara ce?Zuly take bata wai ta rabu da Bashir ta Auri Sooraj don tafi kowa sanin Sooraj bashi da mutunci ko kad'an...
"Salmancy wai tunanin me kike yi don Nace miki ki Auri Sooraj shine wani abun tunani, kinsan yana sonki yana k'aunarki, kece kika ce baki sonsa Amman duk da haka wataran har makaranta yake bina akan in shawo kanki.
" To sanin halinki ne na shegen kafiya da son wannan Bashir d'in matsiya ci😏gashi yanzu y'ar Abayar Sallah ma ya kasa yi miki i'ta, common Abaya ba wani abuba, Nidai abunda zan gaya miki kiyi tunani akan Auren Bashir don Aurenshi ba zai tab'a yi miki dad'i ba A'ishi Aure d'anjin dad'i ne ba wahala ba.
Kiyi tunani yanzu i'dan kika Auri Bashir babu abunda zai tsinana miki, Amman kika Auri Sooraj wallahi tallahi na kusa dake ma irinmu sai munyi Arzik'i ballan tana ke da iyayenki.
I're i'ren i'rin wannan zugar Zuly ta ringa yiwa Salma, Ahankali zugar Zuly ta fara shigar Salma, sai dai har yanzu Salma tana tunanin rabuwa da Bashir don har yanzu tana son Bashir sosai, A SANADIN ABAYAR SALLAH ne suka yi fad'a, ko kuma ace i'tace take fad'a dashi, don ko jiya yazo zance tace ace mishi bata da lafiya.
*Gidan Hamisu*
Haba Zeenat yanzu akan banyi miki abayar Sallah ba shiyyasa kike yimun irin wannan wulak'ancin?to bari kiji wallahi Zeenat abunki ya fara i'sata zan kai k'ararki wajen Baba saboda Wallahi na gaji da irin wannan wulak'anci.
Kina ta_ra mata agidanki suna zugaki kina jin dad'i, kamar kinyi abun arzik'i to bari kiji duk ranar da naga wata shegiyar mata tazo mun gida saina yimata wulak'ancin da tunda aka haife ta bata tab'a ganin irinshi ba wallahi.
"Da sauri Zeenat ta tashi tsaye tana kad'a k'ugu kamar wata y'ar danbe ta turo d'aurin d'an kwali a gaba " tace Lallai Hamisu ashe kuwa da baka sake yiwa wani d'an adam wulak'anci ba arayuwarka ba, saboda ranar sai kaga tashin balagar tsuntsaye don wallahi babu wanda ya i'sa yasa in rabu da k'awaye na da abokan arzik'i bak'in ciki ya kashe niba.
"in kafita tun safe sai dare kake dawowa sannan ni kace zaka hanani fita waje tsabagen bak'in hali, to wallahi bari kaji na rantse da Allah, ka sake kayiwa k'awaye na wulak'anci a bakin Auren ka wallahi.
" Haka kika ce ko?eh na fad'a d'in kayi abunda zakayi wani dare ne jemage bai gani ba, ai sai dai na ranar mutuwarsa.
Cike da b'acin rai Hamisu ya bar mata gidan baki d'aya saboda tsananin b'acin rai da dana sanin biyewa Zeenat da yayi gashi yanzu ranshi ya b'aci a banza.
"Kin san Allah Hauwa idan Hamisu bai siyamun abayar nan ba Wallahi a bakin Aurensa wallahi don na gaji da shegen son kud'inshi😏
Jamila d'aya ce daga cikin k'awayen Zeenat " tace subhana lillahi yanzu akan abayar Sallar ne kike cewa wai zaki rabu da mijinki maisonki haba Zeenat ki yiwa kanki fad'a wallahi Saboda abunda kike shirin yi ba dai dai bane, ni kinga bance ma ya siyomun ba amman ya kawomun tunda shi Baban Inayat Aikinsa ne siyar da Abaya kala kala, so kinga ke don Hamisu baiyi miki ba kada kiji hau.......
"Don Allah Jamila kiyimun shiru saboda ke an siya miki ni kada a siyamun ko, to ki ficemun agida.....
*Ummu Maher ce*😘
Ramadan kareem👏
👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN ABAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘
Gajeren Labari
Na
Rabi'atu(Ummu Maher)Miss green💚
*💅💅Shalelen Jarumai Writer's Ass✍🏻*
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 5*
"Jamila ki ficemun agida tunda ba da kud'inki aka had'a aka siya gidanba, munafuka kawai saboda ke an siya miki abayar Sallah kada ni asiyamun ke me miji ko?.
" Haba Zeenat yau ni kike kora agidanki saboda ina fad'a miki gaskiya saiki nemi ki zageni, to insha Allah gidanki ma na daina zuwa tunda daman ba abun kirki ake k'ullawa ba.
"To kada ki dawo mana munafuka masu zuwa lahira da k'ok'on bara, nan dai fad'a ya kaure tsakanin Zeenat da Jamila, akayi ta tonawa juna asiri, Da k'er Hauwa ta shiga tsakaninsu , Amman Zeenat ta jiwa Jamila ciwo ahannu sannan ta cijeta a kumatu don har jini saida wajen yayi.
Jamila kuwa tana ta zage zage tana cewa wallahi sai ta kai Zeenat polistation don a karb'ar mata y'an cinta na cizon ta da tayi.
Zeenat kuwa tace ta turo mata sojoji k'arewar y'an sanda, da k'er aka fita da Jamila daga gidan.
" Zeenat yanzu abunda kika yi kin kyauta kenan kije ki hau matar mutane da fad'a, duk kinbi kin b'ata mun suna a unguwarnan babu wanda yake ganina da mutunci, na hanaki tara mun mata agidannan amman kink'i ji kullum cikin tara mun y'an iska kike.
"Hamisu ka k'eleni inji da abunda yake damuna saboda yau ji na keyi amutu adawo, don wallahi Jamila sai tasan da ni take rigima don sai ta gwammace kid'a da ganga wallahi.
Wani mari Hamisu ya kaiwa Zeenat sannan ya nuna ta da manuniyar hannunshi yana cewa" Wallahi Zeenat baki isa kice zaki juya niba sai dai ni in juya ki, kuma ki saurare ni kiji duk ranar da na dawo naga kin tara mun mata agidannan sai ranki yayi mummunan b'aci wallahi.......
Ayyyiri yiri'daga b'acin ran saime?sai saki ko? Aini wallahi duk ranar da ka sakeni sai nayi sadaka nayi party tsabar murna, da zama da zumbuli irinka gwara ka sakeni.
Shidai Hamisu baice da Zeenat komai ba ya fita don bawa Mijin Jamila hak'uri.
*Gidan Malam Tahir*
"Bashir Yace Haba Salma yanzu akan wannan Abayar shine kika juyamun baya saboda ban kawo miki Abayar Sallah ba?ke yanzu ko kunya ma bakyaji ace akan wannan Abayar kin juyamun baya.
I'dan ka gama zancen daya kawoka ina da wajen zuwa don ayau wanda ya fika sona zai kawo mun abaya....Wayar Salma ce ta fara ringing ta d'aga tana cewa Yauwa my Sooraj ganinan zuwa kayi hak'uri Saboda y'an bak'inciki gwara muje inda ba za'ah ganmu ba.......
Sauri warce Wayar Bashir yayi ya jefar da i'ta ta tawarwatse a k'asa, idanun Bashir sunyi jawur kamar zaiyi kuka jijiyoyin kanshi sun mik'e gashin jikinshi ya mimmik'e saboda tashin hankali da matsanancin kishin Masoyiyarshi Salma.
Bai tab'a Tunanin akwai ranarda zata zo Salmansa ta juya mai baya ba akan wata Abayar Sallah ba sai yau.
Muryar Salma ya jiyo tana Cewa, wallahi saiya biya ta wayarta kuma kada ya sake zuwa wajenta, sai alokacin ya lura da zuwan Zuly k'awarta tana sake zuga ta akan ta taho su tafi kada Lokaci ya k'ure.
Dai dai lokacin Bashir yaji wani jiri ya kamashi atake ya fad'i a wajen......
*Ummu Maher ce*
Ramadan Kareem👏👏
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN ABAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
By
Rabi'atu (Ummu Maher). *Miss green💚*
*💅Shalelen Jarumai writer's Ass*✍🏻
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
Note✍🏻
Gaskiya wasu daga cikin Fans basa kyautamun abubuwa sunyi mun yawa idan kunce na turo muku Littafi ban turo ba abubuwane suka yimun yawa,sai Ku tambayi wani a GRP ya turo muku.
Abun mamaki akwai wadda tace in turo Mata na manta ban turo ba ta ringa masifa kamar wata uwata akan me?
mufa muna rubuta littafine don mu fad'akar Ga wad'anda suke wani Abu ba dai dai ba badon kud'i ba.
ni ban tab'a siyarda littafina a online ba sai dai in buga abuna na siyar,sai y'an film dana siyarwa kwara d'aya.
so banason samun sab'ani da KO wa don haka i'dan ka tambaye ni ban turo ba kayi hak'uri wani ya turo maka,saboda ni wani lokacin ma sai in dad'e ban hau online ba saboda skull.
🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻saboda
Haka aringa yiwa marubuta kyakkyawar mu'amala ta haka ne zamu isar da sak'on da mukeso mu i'sar.🙏🏻
*Shafi na 6&7*
__dai _dai lokacinne Malam Tahir ya sauka daga kan Mashin d'inshi idanunshi suka hangomai mummunan Abu don duk abunda Salma ta yiwa Bashir MalamTahir ya ga duk abunda ya faru har lokacin DA Bashir ya fad'i ak'asa su mamme. __
_da gudun gaske Malam Tahir ya nufi wajen yana kiran sunan Allah yayi saurin d'ebo ruwa acikin gida ya shek'awa Bashir,cikin rud'ani Bashir ya tashi tare DA wani matsanancin tashin hankali tare da danasanin zuwa wajen Salma don ayanzu koda Zai mutu ba zai Auri Salma ba,don ya tabbatar yanzu Salma bata sonshi KO kad'an tunda har ta iya tafiya tana kallonshi cikin wani hali Amman tayi tafiyar ta batare DA ta Lura DA halinda yake ciki ba tayi tafiyarta wajen wani ta barshi a wajen rai a hannun Allah._
" _Sannu Bashir duk naga abunda ya faru kayi hak'uri Salma kuma indai nine mahaifinta saita Aure ka tunda ba i'tace ta haifemu ba,Naso in tsayar da i'ta kafun ta hau motar data shiga Amman babu yadda zanyi saboda koda na ganka acikin wani hali baisa na tsaya kula abunda Salma take shirin Aikatawa ba._
Da k'er Bashir ya tashi Zuciyarshi tana yi mishi k'una ga son Salma daya dawo sabo acikin zuciyarshi,har yanzu tambayar da yake yiwa kanshi i'tace me yasa bai yiwa Salma abayar nan ba?Saboda duk i'tace silar komai,Sai dai yasan bazai iya siyawa Salma wannan Abayar ba saboda bashi da yadda zaiyi ya samo kud'in,saboda ga gini da ya keyi,ga lefe daya ke had'awa,ga kula da mahaifanshi da k'annenshi da wanne zaiji?
Malam Tahir ne ya raka Bashir har gida sannan ya koma gidanshi,har lokacin Salma bata dawo ba sai kusan k'arfe goma da Rabi na dare ta dawo,Malam kuwa ya kasa rintsawa yana jiran dawowar gantalalliyar y'ar shi.
Amman me zai faru?Salma ce ta shigo gidansu cikin maye tana had'a hanya tare da buge duk wani abunda yake gabanta tana surutai abun tausayi abun kuma ayi kuka.
Innnalillahi Wa inna Ilaihi Raji'un "Salma!Salma!!Salma!!!
Abunda kika koma kenan inji Malam Tahir yana zubarda kwalla tare da, takaicin halin da Salma ta canza Wanda ba halinta ba halin wata ne.
Jin Salatin da Malam Tahir ya keyi ne yasa Mahaifiyarsu Salma fitowa tare da k'anwarta,suka fito arazane,was zasu gani?Salma suka gani cikin halin maye sannan tana had'a hanya tana surutai.
Yawan Comments yawan tyiping.
*Ku yad'a*📩
Sannan
*kuyi Sharhi✍🏻*
kada kuga Ban Fara posting d'in littafi mai suna Akan Aikina
DA
K'addarar Rayuwa ba
DA
Inayatullah ba
Saboda Akwai wani Abu Dana ke jira ne shiyyasa.
Kuma ba'ah Comment sosai.
So shiyyasa guiwa ta ta Saki,Amman akwai lokacin da Zan k'arasa Ku yimun afuwa🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻
👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN ABAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
Gajeren labari
Na
Rabi'atu(Ummu Maher)Miss green💚💚
*💅Shalelen Jarumai writer's Ass✍🏻*
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 8&9*
*Gidan Malam Tahir*
DA sauri Habiba ta k'ara kallon Yayar tata cike da mugun mamaki "Tace gaskiya Aunty Salma baki kyautawa Rayuwar kiba da A SANADIN ABAYAR SALLAH kika zab'i ki zama y'ar maye kika zab'i ki k'unta tawa iyayenmu.
Anna Mahaifiyarsu Salma kuwa kuka kawai ta keyi tana salati tare da ta fa hannayenta,Anya kuwa wanna Salma ce kuwa?Yarinya mai kamun Kai da sanin ya kamata Amman yanzu yadda kasan y'ar karuwa haka ta koma kamar ba y'ar Malami ba.
Wani wawan Mari Malam Tahir ya kaiwa Salma sannan ya nuna ta da ya tsansa Yace" Amman Salma kinji kunya kuma ki tuna ni mahaifinki ne,kuma matuk'ar Nine Mahaifinki sai kin Auri Bashir Wallahi,Shasha wadda bata San inda yake Mata ciwo ba,yana fad'in haka yayi tafiyarshi d'akinsa zuciyarshi nayi mishi k'una.
*Gidan Hamisu*
"Yanzu Zeenat kinsan girman laifin k'auracewa Mijinki tsawon kwana ki, kuma akan wani abunda bai taka Kara ya karya ba?.
Cikin tsiwa Zeenat" Tace to sai me Kaine mai raba lada kome?DA zama zo ka isheni da wani wa'azi i'ta wadda ka shigarwa d'in har kazo kana yimun tujara agaban Jama'ah kaje ta baka k'anwarta ka Aura tunda abun ya zama rashin mutunci.
Shiru Hamisu yayi ba tare da yace komai ba yabarwa Zeenat d'akin baki d'aya,Rabon da kwanta da matarsa Zeenat don raya sunna i'dan bai manta ba,tun A Daren da yace Mata ba zai siya ABayar Sallah ba,tun ranar Zeenat ta gujesa koda yaje kusa da i'ta zagi ne da mumunan maganganu ke shiga tsakaninsu yau ma abunda yasa ya nemeta Sha'awarsa ce ta fito sosai,Amman koda ya samu Zeenat gaggasa mai maganganu tayi.
*Unguwar Tudun yola*
wata yarinya na hango wadda ba zata wuce shekara sha 18 ba tana sanye DA Riga da zani Na atamfa,ga k'aton hijabin ta na mutunci kyakkyawa ce Amman black beauty ce,ga Jan lallen DA Tasha y'an yatsun k'afa da hannu abun gwani sha'awa.
Tabarakallahu Ahsanin kalik'in🤲🏻☺️❤️
Hamisu ne ya fad'i hakan a lokacin da yake kan lifan d'insa dai dai zai shiga gidansa,yaga ta shiga gidan Jamila wadda suka yi fad'a da matarsa Zeenat.
A hankali ya jingine mashin d'in Nasa da yake ankusa Fara kiran Sallar magariba,Har lokacin kallon k'ofar gidan ya keyi kamar wani tsohon maye,hannu yaji a jikinsa yayi firgigit kamar wani Wanda ya dad'e yana bacci.
"Lafiya kuwa Hamisu?naga kana ta kallon k'ofar gidana ba dai fad'an suka k'ara yi ba?.
" A'ah ba fad'a bane Tukur Alkhairi kasan ni bana b'oye gaskiya ta fad'in ta kawai na keyi kasan asalin sakkwatawa basu da rufi.
"Eh kuwa gaskiya ne me ya faru?
" Hamisu Yace a gaskiya wadda ta shiga gidan nan daga ganinta k'anwar Jamila ce kuma wallahi Ina muradin Aurenta don gaskiya tana da hankali..
*🥺😔🤔Tab gaskiya akwai chakwakiya a wannan littafi Mijin Zeenat nason k'ara Aure*
Ku Fad'a mun irin rigimar da za'ah kwasa🤣🤣🤣🤣
*Yawan sharhi*
*Yawan rubutu*
*Miss green💚🤪*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN A BAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
Gajeren labari
Na
*Rabi'atu(Ummu Maher)*
Miss green💚
💅Shalelen Jarumai Writer's Ass💃💃💃✍🏻
________
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 10&11*
*Gidan Hamisu*
Tukur ya yi Shiru alamar tunani ya ke yi a ga me da wannan maganar da abokinsa Hamisu,Shi dai ya San Zeenatu ba za ta yarda Mijinta ya Auri Rabi'atu ba k'anwar matarsa Jamila,biyo bayan rikicin daya shiga tsakaninsu.
"Tukur lafiya kayi shiru ko dai zancen Dana zo maka dashi ne kake tunani akansa?Ko kuma kana tunanin Zeenat ba za ta yarda da Auren K'anwar matarka ba?to wallahi ka ji na rantse Neman wannan yarinyar yanzu na shiga yi kuma ba Zan fad'a wa kowa komai ba har zuwa lokacin da za'ayi Auren,don haka kata ya ni Neman Auren nan saboda KO babu komai Kai mijin Jamila ne ko babu komai zata sakko tun da Kai mijin tane...."
"Babu komai Hamisu zanyi i'ya bakin K'ok'ari na duk yadda ake ciki Zan sanar da kai,Insha Allah kuma komai zai zo mana da sauk'i Kai dai ka cigaba da Addu'ah komai zai zo cikin Sauk'i."
Godiya Hamisu ya yi wa Tukur sannan ya nufi gidansa cikin farin ciki dafatan Allah yasa yayi nasara acikin Neman wannan Auren,kuma daman yana saka ran wasu kud'i za su zo masa nan kusa.
*Gidan Malam Tahir*
"Salma ki bani da ma in nuna miki I'rin son da nake yi miki,saboda naga kamar baki yadda cewa inason kiba?sai wani d'a_ri d'a_ri ki ke dani,kuma kinga ni a tsari na ma a d'aura mana Aure nan da Wata d'aya.
Cikin tsoro Salma ta kalli Sooraj a ga me da abinda kunnu wanta suka jiye Mata.
" Haba Sooraj sai kace wata y'ar tsana da za kace wai na Aure ka nan da wata d'aya Ina laifin ma wata 5 Amman yanzu wata d'aya A'i ya yi kad'an..."
"Kinga Salma ba fa bariki na ce muyi ba Aure nace muyi saboda inasonki don haka bana son irin wannan maganar kinji KO?ya fad'i hakan yana mai zare idanu kamar tsohon maye.
Nan dai suka cigaba da hirarsu,sai dai ta kula Sooraj yana da wasu irin halaye saboda yana da Saurin fushi ga shi yanzu ya Saba da tab'a jikin ta tun tana Hana shi har ta gaji ta k'elesa saboda gaba ki d'aya yanzu abin ta Saba dashi i'tama har so ta keyi.
" Wai Salma me ki ka d'au ke ni ne?KO kuma shashan uba ki ka d'au keni da zaki zauna kina gaya mun abunda ranki yaso,to ki bud'e Kunnu wanki ki ji ni dole ne ki rabu da wannan d'an iskan yaron me yi wa mutane kallon y'an iska Alhali shine cikakken d'an iska Mara mutunci kawai"
"Cikin ra zana Salma ta mik'e tsaye tana hawaye don wallahi kome za'ayi ba zata i'ya rabuwa da Sooraj d'inta ba.
*Yawan sharhi*
*Yawan rubutu*
*Miss green ce💚*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN A BAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
Gajeren labari
Na
*Rabi'atu B Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green💚
💅Shalelen Jarumai Writers Ass✍🏻
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 12&13*
"Rabi'atu ki yarda cewa inasonki kuma babu ranar da ba Zan yi begenki ba,Ki kawar da tunanin da ya ke ranki na sab'anin dake tsakanin Yayarki da Matata,sab'anin fahimta ne idan ki kayi la'akari da Ada cen baya Jamila k'awar Zeenatu ce sosai"..
" don haka don Allah Rabi'atu nazo wajenki don Neman Soyayyarki har ta kaimu da Aure,saboda so nake yi miki na tsakani da Allah,kuma so nake yi miki na Aure.
"Kayi hak'uri Hamisu ba zance bana sonka ba,Amman kuma wani Dalila zai saka ink'i yarda da Aurenka saboda Zeenat ma'ana matarka,tun kafun ka furtamun so Zeenat tak'i jinina don kwata kwata bama shiri da Zeenat".
" To ta yaya kake tunanin Zan Aure ka Alhalin matarka ta tsaneni kaima kasan hakan ba zai tab'a faruwa ba,Amman don Allah Hamisu kayi hak'uri don Kai mutumin kirki ne kuma i'na d'aukarka A matsayin Yaya na.
"Kuma a yanzu na yiwa wani Alk'awarin Auren sa munyi Alk'awari da juna,don haka kayi hak'uri don Ina fatan ba kaji haushi na ba"
Wani i'rin ciwon Kai Hamisu yaji kansa ya shiga yi mishi yawo acikin sararin samaniya,saboda yana yiwa Rabi'atu wani irin son da bai tab'a ji koda akan matarsa Zeenatu ba.
Cikin zafin rai Hamisu ya hau lifan d'insa da ya sha wanki yayi tas,Rabi'atu kuwa wani tausayin Hamisu ne ya d'arsu a zuciyarta,tabbas ta San Hamisu yana cikin Wani hali saboda matarsa bata kula dashi a matsa yinsa na Mijinta na sunna.
Kuma ba don ta yi wa Saurayinta Alk'awarin Aure ba DA babu abinda zai Hana ta Auri Hamisu kodon ceton ranshi,kada kuce Hamisu mummuna ne?A'ah Hamisu kyakkyawa ne son kowa k'in wanda ya rasa farin ba fulatani ne do gone mai yalwar hanci da d'an karamin baki.
Hamisu sanyayyan mutum ne ta yadda ba zaka tab'a ganin fushinsa ba Sam,don mutum ne me yalwar ilimin addini Dana boko,ma'aikacin gwamna ti ne yana koyarwa a makarantar y'an Mata.
Sannan Hamisu yana son kula da iyalansa duk Albashinsa idan ya d'auka a hidimar iyalinsa Dana y'an uwansa ya ke k'arewa ba ya yi wa kansa Abu KO na kobo saboda ya ceto Rayuwar iyalinsa Dana y'an uwansa DA mahaifansa.
ya kasance yana son Matarsa Zeenat duk da kasan cewarta bata haihuba,y'an uwansa da mahaifansa har sun gaji akan ce masa yayi Aure Amman fa fur yak'i yarda k'arshe duk Wanda ya yi masa magana akan Zeenat b'a tawa suke yi.
Sai gashi yanzu da gumi tayi gumi yana son k'ara Aure don Zeenat bata tsoron Allah KO kad'an ta d'auke shi ba a bakin komai ba,duk a SANADIN ABAYAR SALLAH.
*Gidan Malam Tahir*
Malam Tahir yayi shiru yana kallon mutanen da suka zo Mutanen da y'arsa ta zab'i su zama surukai A gare ta, tabbas bai tab'a yi wa yi wa wani d'an sa ba ki ba Kuma Allah ya sani ba shi ne ya haifi Salma ba sun d'auko ta ne a Gidan marayu a lokacin basu samu haihuwa ba,suka d'auke a lokacin tana zanin goyon ta,Bayan wasu watanni da d'auko Salma matarsa ta samu ciki bayan wasu watanni ta haihu.
Amman duk wannan abun babu Wanda ya San cewa Salma ba y'arsu bace,kowa d'auka ya ke Salma y'arsu ce don haka babu Wanda ya tab'a sanin wannan tsohon sirrin.
Kuma ba zai tab'a yarda Salma ta Auri Wanda ba shida tarbiyya ba k'arshen ya sakar musu y'a.
"Gaskiya ni dai ba muyi haka da Salma,don bata sanar mun wasu bak'i za suzo ba,Amman don Allah kuyi hak'uri."
daga inda Salma take b'oye a soron gidansu bayan k'ofa ta jiyo wannan mummunan furucin daga bakin Mahaifinta.
tabbas ta tabbatar a yanzu Mahaifinta baya Sonta Kuma baya son Sooraj,i ta kuwa babu Wanda take so take muradin zama dashi a matsayin Mijinta sai Sooraj...
*Yawan rubutu*
*Yawan Sharhi*
Ummu Maher ce✍🏻
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN A BAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘
Gajeren labari✍️
_Na
*Rabi'atu.B.Abdullahi*
(Ummu Maher) Miss green_ 💚💚
*Alk'alami yafi ta kobi✍️*
🔔📚🔔
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W⚜️📚🖌️*
________
*Shafi na 14&15*
*Gidan Hamisu*
Sai da Hamisu ya yi kwana biyar bashi da lfy kuma baya fita Sam sai dai Sallah saboda k'aunar Rabi'atu ya ke yi ba kad'an ba,Saboda a yanzu ba bu abinda ya keso I'lla yaga ya yi Auri saboda masifar Zeenatu ta ishe shi.
D'an zaman da ya yi na rashin lafiya sai da Zeenat ta Addabe shi saboda ko Alwala i'dan ya fito sai ta yadda mishi da magana ba bu ruwanta KO tayi mai da d'i ko kada tayi mai ba bu ruwanta.
Duk abinda Zeenat ta ke yi Hamisu yana kallon ta ba tare da ya ce Mata komai ba shi dai ya barwa kansa sanin Mata kin da zai d'auka akan matarsa Zeenat.
*Gidan Malam Haris*
"Haba Salma kina son ki mayar damu k'ananun mutane da zaki turo mun Mutane wai sun zo Neman Auranki? ko kuwa kin manta ce wa akwai kud'in Bashir a kanki kuma harda sada kinsa ma a kanki.?
" To Bari kiji Wallahi baki isa ki jawo mun abun kunya ba sakarai kawai Mara tunani."
Wani i'rin kuka Salma ta fashe dashi na tausayin kanta, tabbas ta San i'tace ta zab'i Bashir a matsayin Mijinta ba wani ne ya zab'a Mata ba.
Amman ta rasa dalilin da yasa yanzu bata sonsa kwata_kwata? don yanzu ta tsanesa sosai,Baya burge ta ko kad'an.
Hmm Salma kenan ga dalilin nan kud'i abun duniya,kuma daman Hausa wa sun ce kuda wajen kwad'ayi ake kashe shi.
Y'an Mata Ku daina Auren kud'i Ku dinga Auren Can_can ta ba Auren son abin duniya ba,don komai na duniya fa _rarre k'a _rarre,Kuma komai na duniya yana k'arewa ya barka da mutum.
***************
"Aunty kizo Yaya Bashir yana kiranki?".
Habiba ce tsaye k'ofar d'akin tana kwalawa Ya yarta Kira Amman ko kusa bata amsawa Habiba kiran da ta ke yi Mata ba.
Sai da Habiba ta sa da kanta zuwa cikin d'akin don kiran Yayar ta.
A kwance ta samu Salma ta yi nisa cikin wayar da suke yi i'ta da Sooraj.
Suna magana a kan mutanen da ya turo d'azu Abbanta ya ce bai San da zuwansu ba.
"Hmm kada ka da mu saboda Mahaifina ya ce haka ka k'ara mun lokaci Insha Allah komai zai yi setling,tunda ka yarda ce wa ina sonka kada ka da mu komai zai wuce"....
" Haba Aunty Salma i'na magana Amman kinyi shiru kin da ge kina magana da wannan sha_shan Mara sanin hakkin d'an Adam"....
Wani Mari Salma ta wanke Habiba da shi wanda ya sa sai da Habiba ta durk'u she a wajen hannun ta na rik'e da kuncin ta,tana zubar da kwallah.
Tana yi wa Yayar ta wani kallo mai ci ke da ma maki,tabbas ba don karta k'arya ta ba to da sai ta ce can jin Salma a ka yi musu,don a i'ya sanin ta tasan ba halin Salma bane san zugar k'awa ye ce da kuma sharrinsu.
"Yanzu Yaya saboda na zagi wanda baya sonki,kuma bazai tab'a sonki ba sai dai son sha'awar da ya ke yi miki,Ga wanda ya ke sonki ya ke k'aunarki tare da tausayinki kin k'i ki Aure shi sai mai kud'i".....
" Don Allah Habiba ki fitar mun a d'aki saboda ba hiruminki ne ki zab'a mun mijin Aure ba don haka daman i'dan son Bashir d'in ki ke yi to kije ki Aureshi kinji.
Salma tana fad'in haka ta fice a d'akin tana zagin K'anwarta Habiba a kan shish shigin da ta ke yi mata.
"Salma Ina zaki je?.
Malam Haris ne tsaye a kan Salma yana tambayarta inda za taje,kuma duk ya ji i'rin zagin da Salma ta yi wa K'anwarta Habiba.
" Ki je ki kirawo mun Mahaifiyarku i'na son yin magana daku mai mahimmaci.
Cikin jin kunya da sunne kai Salma ta wuce don ki rawo Mahaifiyar ta su,tare da tunanin wannan wacce i'rin magana ce Mahaifinta ya ke son suyi,Cike da zargin kanta Ta ki rawo Mahaifiyarta .
"Malam ga ni Salma ta ce kana kira dafatan dai lafiya klau.?
" Eh to lafiyar dai zan ce domin A yau zan yanke wani hukunci a tsakanin Salma da Habiba,Hukuncin kuwa ba komai bane i'lla na dawo da Auren Bashir zuwa kan Habiba......"
*UMMU MAHER CE*
Vote
Share
And
Comment📲
👘👘👘👘👘👘👘👘👘👘
*A SANADIN A BAYAR SALLAH*
👘👘👘👘👘👘👘👘👘👘
Gajeren Labari✍️
Na
*Rabi'atu.B.Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green💚💚
*✍️Alk'alami yafi takobi⚔️*
*💫💫🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 16&17*
*Gidan Malam Tahir*
Ba ga Habiba ba hatta Salma sai da lamarin mahaifin na ta ya gir_giza ta matuk'a,wani tsohon son Bashir ya d'arsu a zuciyarta ka fun kace me har ta ji kamar ta ma k'ure Habiba ta kashe ta kowa ma ya huta don ba za ta jure cin mutunci ba, don ta ce ba ta son Bashir shi ne za'ah d'auki wannan mummunan matakin a kan ta?to wallahi ba za ta sab'u ba bin diga a ruwa.
🤔oh ka ji fa mai sauraro Salma fa da kanta ta ce ba ta son Bashir yanzu kuma ganin an baiwa k'anwarta Bashir d'in shi ne ta ke ba k'inci.
Malam Ya ce"to ku ta shi ku fita na gama magana ta don haka ku fita zan sha iska, ke kuma Salma ki tsaya za muyi magana."
Har lokacin ban i'ya ce wa komai ba kuma ban d'ago kaina ba, saboda tsananin da muwar da na ke ciki, har ga Allah har yanzu i'nason Bashir don ba don son da na ke mishi ba da bazan yi kishinsa ba.
"Salma i'nason ki yi wa wannan yaron magana ya turo a yi zancen Aurenku Saboda ba na son abun ya yi ni sa don tare na ke son had'a ku keda y'ar uwarki."
Sai alokacin ne na yi saurin d'ago idanu na na kalli Malam, shi kuwa bai ma san i'na yi ba saboda shi sha'aninsa kawai ya ke a lokacin ya d'auko qur'ani yana du bawa kuma da alama karatun zai fara, don haka dole in ta shi in ba shi waje.
Da k'er naja k'afa funa da suka fara yi mun tsami tsaba gen zama a kan k'afa ta,don ji na ke yi kamar k'afa funa ba za su i'ya d'au ka ta ba, ga damuwar da ta cika cikin zuciyata, na fi kowa sanin halin Sooraj da mugayen halayensa amman a haka na keson Auransa don kud'insa, wa su hawaye ne masu sanyi da zafi suka sauka a kan fuskata na go ge na shiga d'akin mu na yi rub da ciki i'na kuka.
sai a sannan ne na kula da Habiba da take Zaune tana kuka, don har cikin zuciyar Habiba bata ji da d'in abinda ya faru ba, ba bu yadda za'ayi ta ce ba ta son Bashir don duk wata nagarta da A ke so Namiji ya kasance da i'ta to fa Bashir yana dasu kuma yana da rufin asiri dai_dai ba kin k'ok'a ri, Amman sai dai tana da wanda ta ke so wato Sa'ad k'anin Bashir Amman ba bu yadda za tayi ta karb'i k'addarar ta ba bu wanda ta ke ji Sai Sa'ad sai dai tana yi mai fatan samun mace ta gari da fatan hak'uri da dan gana tare da juriya.
Wani haushin yarinyar ne ya d'arsu a zuciyata don haka na tashi na yi tsaki tare da ce wa"Hmm muna fuka kina so kina kaiwa kasuwa wai kema kin girma kina son Aure to bismillah, Auren talaka har wani Aure ne ballan tana a ce wani abu, don haka ba gilin gilin ba ta yi mai, Salma ta wuce fuu tare da jin haushin kanta da haushin k'anwarta Habiba.
Habiba ta kalli ya yar ta ta tare da mamakin yadsa a ka yi ta canza halayenta, don ta san a da ba haka ya yar ta ta take ba ko da ya ke ance a bokin b'arawo b'arawo ne saboda kaf duniya yanzu Ba bu mutumin da Salma ta fi jin maganar i'rin Zulaiha wato Zuly, Kuma kaf unguwarsu ba bu wanda bai san Halin Zuly ba na Yawan tara samari ga saka ma tsatstsun kaya tare da shegen son kud'i.
*Gidan Hamisu*
Mahaifiyar Hamisu ce ta gyara zamanta ta re da Ce wa "Wallahi tallahi Hamisu ba ka da kirki ko ka d'an yanzu da man Rabi'atu ka keso shi ne ka k'i fad'amun saboda ta ce maka anyi mata miji."
"Bazan ce maka ba'ayi mata miji ba tabbas anyi mata miji sai dai ba kowa ne mijin ba wanda ya wuce kai, saboda ni na yi maka ka mu sannan na nu na kada a fad'a maka hat sai yarinya ta amin ta tana son ka sannan komai ya tabbata."
"Kuma a da cen ba ya suna soyayya da wani yaro sai dai Mahaifiyarsa ta hana Auren wai ta fi son ya Auri y'ar k'anwarta to kaji yadda a ka yi."
"To Alhamdu lillahi tunda yanzu kai da kanka ka furta kana son ta don zan cen da na ke yi maka har an saka ranar Aurenku kai da Rabi'atu nan da wata uku masu zuwa."
Murna tare da wani ni shad'i tare da jin son Rabi'atu ya yi matuk'ar sha k'uwa a cikin zuciyarsa, ya ce"kai Inna ta kin gama yi mun komai wallahi tunda ki ka ba ni Rabi'atu Allah ya k'ara arzik'i."
*********
To kwana biyu da yin haka Hamisu ya fara zuwa zance suna soyewarsu da Rabi'atu don yanzu ga ba ki d'aya ya fita hanyar Zeenatu i'ya karsa ya ajje mata kud'in ce fanen ta kan windo ya yi tafiyarsa don gudun fitanar Zeenatu.
*Ummu Maher miss green💚*
*Vote*
*Share*
And
*Comments*
👘👘👘
*A SANADIN A BAYAR SALLAH*
👘 👘👘
Gajeren Labari📖
Na
Rabi'atu Bashir Abdullahi
*(Ummu Maher)Miss green💚📗*
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 18&19*
Gidan Hamisu
Zeenat ta ga abin Hamisu ya fa ra wuce gona da i'ri saboda gaba ki d'aya ya fita daga sab gar tun abin ba ya da munta har ya fa ra da munta don haka ta sa mu k'awar ta Hauwa don taba ta shawara akan Mijinta Hamisu don i'ta tana ganin ci baya ne ta ba wa Hamisu hak'uri saboda i'ta a ganinta ba wa Miji hak'uri tamkar ka zubar da mutuncin ka ne.
"Hauwa so na ke yi ki ba ni shawara akan wani hali da Hamisu ya d'auko Sam yanzu ya daina kula ni i'ya kacinsa dai ya ajje min kud'in ce fa ne ya fita,A i'ya Sani na kuma ba bu abinda na yi mai da zai dinga yi mun wannan abubuwan."
Hauwa Ta ce"Zeenatu ko dai tun a kan Matsalar nan ce ta Abayar nan? Tun da ya nu na fushinsa tun a lokacin ke ma kuma kin yi mai Rashin mutunci a kan wannan".
"To sai me don na yi mai rashin mutunci?".
" Shi ba kiga abinda ya yi mun ba shi bai yi rashin mutunci ba sai ni?"
"To na yi d'in ke tunda an yi miki A'i dole ki ce haka tunda ke da man mutun ba ya shawara da ke."
Shiru Hauwa ta yi don ta San halin mutuniyar ta Sam ba ta son ka fad'a mata gaskiya sai dai ka zuga ta,idan kuwa tsau_tsayi ya saka ka fad'a mata gaskiya to duk yadda Ku ke da i'ta sai ta zage ka son ranta,Zeenatu ke nan bata da mutunci ko kad'an.
Hauwa tana cikin wannan tuna nin.
Zeenatu Ta ce"don Allah Hauwa idon ba za ki ba ni shawara ba ki rufe mun ba ki ko kuma ki ta shi ki fita uwar yawo da man deeni ya kusa dawowa.
Nan fa Hauwa ta fara zuga Zeenatu nan kuwa Mutuniyar ta fara zuguwa tana jin da d'i tamkar an ba ta kyautar kud'i.
Gidan Malam Tahir
An kai kud'in Auren Salma da Sooraj an kuma saka ranar su i'ta da k'anwarta A Habiba tare da angonta Bashir.
In da a gefe d'aya gidajen Amaren da angwa yan a ke ta shirye shiryen Auren Su.
Hamisu ma an kai kud'i har da saka rana don haka Hamisu ya fa ra shirye_Shiryen yin Aurensa shi da Rabi'atu a cewarsa Sai yanzu zaiyi Auren Soyayya tare da k'auna.
************
Hauwa ta ce "Zeenatu wata jarida na kawo miki da d'umi _d'umin ta don wallahi maganar da na ke yi miki Hamisu na nan yana shirin yin Aure".......
A'i tun Hauwa ba ta k'arasa zan centa ba Zeenatu ta ta shi tsaye tare da ce wa" Wallahi tallahi Hamisu bai i'sa ya k'aro wata shegiya gidannan ba ko ya manta gidan nan Gidan mahaifina ne?to wallahi sai in ga ta inda zai kawo wata tsinanniya gidannan don wallahi ba zan yarda ba ko da na ke yi mai wulak'anci Ai inason abina".
Hauwa Ta ce"nima haka na gani dai,kuma kin san wa zai Aura?".
"K'anwar Jamila wato Rabi'atu wannan yarinyar da ba kwa shiri da i'ta saboda girman kan ta".
Zeenatu ta mul_mulo wani bama gujen zagi sannan Ta ce"wallahi Hamisu zaiga bala'in da bai ta b'a ganin irinsa ba.
Ana cikin haka Hamisu ya shugo Gidan.
Daga
*Alk'alamin Ummu Maher*
Vote
Share
And
Comments💌📩✉️
👘👘👘👘👘👘
🧚♂️🧚♂️🧚♂️🧚♂️
👘👘👘
🧚♂️🧚♂️
👘
*A SANADIN ABAYAR SALLAH*
👘
🧚♂️🧚♂️
👘👘👘
🧚♂️🧚♂️🧚♂️🧚♂️
👘👘👘👘👘👘
Gajeren Labari
*Na*
*Rabi'atu Bashir Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green📗💚
*_Shafi na 20&21_*
*Gidan Hamisu*
___________________
Da sauri Zeenatu ta sha gaban Mijinta Hamisu tare da fara rattabo mai tambayoyi kamar haka:
"Hamisu wai Aure za ka yi"?
"Wacce shegiyar za ka Aura?"
"To wallahi ba bu y'ar iskar da ta i'sa ta zauna min a gidana tunda ba Gidan ubanta ba ne e he".
Da mamaki Hamisu ya ke kallon Zeenatu a ko da yaushe sai yana yi wa matarsa Zeenatu kallon mahaukaciya saboda idan ta yi maka wani abin tilas ka ce mahaukaciya.
" Zeenat are u sense"Shin kina da hankali? and whatrong with u"?
Dariya Zeenatu ta yi harda buga k'afa sannan Ta ce"Hhhhh da man tabar mar kunya da hauka a ke na d'e ta,saboda ka raina min wayo shine ka ke yi mun wani turancin iska."
"To bari kaji Idan ma da gaske ne gwara tun wuri ka fa sa wannan Auren tunda ba dole ba ne,idan kuma ka ce dole za ka yi?to wallahi tallahi ko ni ko kai?".
Zeenatu tana kai wa nan ta yi tafiyar ta d'akinta ta barshi a nan,Hauwa kuwa tana ganin Zeenatu ta shiga d'aki ta rufe gefen fuskarta ta wuce ta gefen Hamisu simi_Simi kamar munafuka.
Wata uwar Harara Hamisu ya gallawa Hauwa sannan ya yi kwafa ya Hau mashin d'insa sai Gidansu ma'ana Gidan iyayensa don ya ga abin na Zeenatu idan ba had'a ta ya yi da Hajiyarsa ba komai zai iya faruwa don Hajiyarsa kad'ai ta ke tsoro,don ya San ko da ya kaiwa iyayenta k'ararta k'arshe su ba shi hak'uri kuma ba za suyi mata fad'a ba a game da laifin da ta yi ba.
👘🧚🏻♀️👘
*A SANADIN ABAYAR SALLAH*
👘🧚🏻♀️👘
Gajeren Labari✍🏼
*Na*
*Rabi'atu Bashir Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green💚🍀
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 22&23*
Sooraj ta gani da budurwarsa a kan screen d'in wayar sannan ga sunanta nan b'aro² akan wayar.
Saurin d'aga wayar Salma ta yi don taji me y'ar rainin wayon zata ce?.
"Wallahi Sooraj idan baka zo gidana ba yau komai zai iya faruwa wato shine zaka mayar dani y'ar isaka ko saboda kana ganin ka yi sabuwar Amarya wannan y'ar matsiyatan shiyyasa ka keson ka raina min wayo ko?"
"Sooraj da kai fa na ke magana shine ka yi shiru?.
" Hello"
"Hello"
Da sauri Salma ta kashe wayar tana haki,a take ta rik'e kanta da ya ke Sara Mata,Zuly tana ganin haka ta matso kusa da k'awarta tana tambayarta me ya faru?
Wata kwalla ce ta fitowa Salma daga idanunta ta ce"Zuly Sooraj ya cuce ni ya ci Amanata sai Allah ya sa kamin Allah yabi min hakkina".
"Ki bud'e bakinki ki fad'a min menene ya faru kina ta ce min Sooraj ya cuce ki da ya yi miki me"?.
Nan Salma ta fad'a wa k'awar ta duk abinda ta gani da abinda taji,Zuly ce ta ringa tausarta da bata hak'uri,sannan ta ce mata komai yazo k'arshe da zarar anyi Auren zasu je wajen boka a mallake Sooraj sai yadda suka yi da shi.
Sannan ta umarci k'awarta da kada ta kuskura ta nuna wa Sooraj abinda ta gani idan ya nemi yasan waye ya ki rasa ki nuna bakisan waye ba,kinga yanzu saimu goge kiran kwata²,da haka suka yi wa Sooraj wayo suka yi shiru da bakinsu har aka tashi daga Dinner d'in sai dai har aka tashi cikin zuciyar Salma tana jin babu dad'i a game da abinda Sooraj ya yi mata.
Zuly tafi kowa son ayi Auren nan saboda tasan Sooraj bakin aljihunsa a bud'e ya ke zata ringa samun Alheri shiyyasa tun farko ta had'a Auren don i'ta ma ta kwashi romon damukara d'iyya.
To wannan kenan.
A haka aka yi yini Amarya Salma zuciyarta babu dad'i don ma Zuly tana tausar k'awar ta,don tun safe tana kusa da k'awarta Babu inda taje a Daren ranar ne kuma aka kai amare gidajensu sai muce Allah ya bada Family na gari.
*Gidan Hamisu*
A b'angaren Hamisu ma yau ya ke angon ce wa da Amaryar zankad'a d'iyya zilla_Ziyya adawiyya matar Malam Hamisu.
Idan kaga bakin Hamisu kamar an bud'e gonar auduga saboda farin ciki jinsa ya ke kamar yau aka haifesa saboda murna yau ya yi Aure,Auren da ya ke fatan samun kwanciyar hankali acikinsa.
Zeenatu kuwa da k'awayenta sun cika gida ana ta famfa Zeenatu akan kada ta yadda ta basu k'ofar da zasu zauna lafiya,tunda har ya zab'i ya yi Aure.
Kunji fa mai karatu acikinsu fa harda mai kishiyoyi biyu akwai mai uku ma'ana wacce su hud'u ne awajen mijinsu.
Amman saboda Zeenatu mai do d'ad'd'iyar kwakwal wa ce sai ta ringa Hawa kan zugarsu tana hango yadda za ta yi wa Hamisu da Amaryarsa.
Gida mai kyau Hamisu aka bawa Hamisu ogan sa ne ya basa bisa don Allah ya had'a jininsa da Hamisu suna harkar mai wato man fetur kuma Alhmdh yanzu Hamisu yana samu.
plate ne Gidan kuma set contant ne,ma'ana mai komai aciki.
Abinda Zeenatu bata Saniba an da
d'awa Hamisu matsayi awajen aikinsa,kuma Alhmdlh yanzu yana samu,sai dai bai yi gan_gancin gaya wa Zeenatu ba don yasan halinta.
An d'aukowa Hamisu Amaryarsa inda aka kawota gidanta mai kyau Wanda aka cika mata kaya dashi mai kyau da tsari.
Bayan y'an kai Amarya sun tafi Hamisu ya shigo gidansa cikin farin ciki a cen k'arshen gadon ya hango ta ta rufe fuskarta tana kuka mai ban tausayi.
A take Hamisu yaji ya k'ara son Rabi'atu tare da jin tausayinta don shi Hamisu Allah ya d'ora mishi tausayi da jin k'ai Hamisu mutun ne shi mai sanyi hali da wuya kaji abinda zai had'a shi da wani sai dai abin babba ne ko Zeenatu ma halinta ne yasa suke fad'a da Hamisu Amman yasan Zeenatu ko giyar wake tasha baza ta tab'a iya rabuwa da Hamisu ba don ba za ta tab'a samun miji kamar Hamisu ba a wannan time d'in.
K'anshin turarensa ne yasa Rabi'atu sanin cewa Gwarzon Mijinta Hamisu ya iso gareta.
Sallama ya yi ya shiga yana mai samun waje a bakin gadon ya zauna yana k'ara kallon fuskar Rabi'atu da ke rufe.
Amincin Allah su tabbata ga wannan halitta mai kyau da zati ma'abociyar kyau da kwarjini,dafatan Amaryata tana cikin k'oshin lafiya kamar yadda angonta ya ke.
D'agowa ta yi a hankali tana mai kallon fuskar Mijinna ta ya yi kyau cikin shigarsa, shadda fara k'al har wani shek'i ta ke kyaunsa da kwarjininsa sun k'ara fitowa sosai,sajensa Wanda ya gaji da gyara ya yi kyau yana shek'i pink lips d'insa tabi da kallo Wanda ya yi kyau kamar Silva.
Murmushi Rabi'atu ta yi Wanda ya k'ara fito mata da kyaunta,azuciyarta kuwa tana jin son Mijinta har k'ark'ashin k'ahon zuciyarta tana ji aranta rana da zafi Inuwa da k'una,ba zata tab'a rabuwa da Mijinta ba.
Matsowa Hamisu ya yi yana k'ok'arin k'ara sa d'aga mayafin jikin Rabi'atu, inda ita kuma ta yi saurin rik'e hannunsa tana mai gyan gyad'a masa kai alamun ya bari,dariya Hamisu ya yi sannan ya rik'e hannun Rabi'atu wani yar ya ji tunda ga kansa har kwakwal warsa.
*✍🏻Real Ummu Maher ce*
Vote
Share
&
Comments.
👘🧚🏻♀️👘~
*ASANADIN ABAYAR SALLAH~*
~👘🧚🏻♀️👘
~Gajeren Labari~✍🏻
Na
*Rabi'atu Bashir Abdullahi*
(Ummu Maher)miss green💚☘️.
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*24&25*
*Hamisu*
"Masha Allah muna yi wa Allah godiya da ya nuna mana wannan rana,Allah ya bamu zaman lafiya ya kad'e mana duk wata fitina."
Cikin jin kunya Rabi'atu ta ce"Amin ya rabbi".
Nan ya umarce ta da suyi alwala suyi sallah don nuna godiyarsa da Allah mad'aukakin sarki da ya azurtasu da yin Aure bautar ubangiji.
Bayan sunyi Sallah Hamisu ya dafa kan Rabi'atu ya yi mata addu'ar da Manzon Allah(S.A.W) ya koyar damu aranar da ka yi sabon Aure.
Daganan ne fa zancen ya sauya salo,ni kuwa Ummu Maher na ce Asha amarci lafiya.
★★★
Zeenatu
Da k'arfi ta ke bugun k'ofar gidan kamar za ta b'allasa Allah² ta ke yi su bud'e au kwashi ruwan bala'i rabon da ta ga Hamisu tun jiya da safe.
Hamisu
Da magagin bacci ya ta shi Rabi'atu tana kusa da shi tana baccinta cikin kwanciyar hankali,ya shafi gefan fuskarmasifa yi murmushi ya tuno Daren su na jiya a ta ke yaji wani murmushi ya bai baye shi.
Jin k'arar bugun k'ofar bai tsagaita bane yasa shi fitowa da sauri yana mitar waye wannan da safiyar nan.
Turus ya yi ganin wacce ta yi musu Daren mikiya da sassafennan,Ya yi kamar bai gan ta ba ya shigo abinshi cikin gidan.
Zeenatu
"Wallahi tallahi baka i'sa ba Hamisu saboda ka mayar dani wawiya wacce bata San abinda ya ke damunta ba shine zaka barni a cen kai ka taho nan kai ga me Amarya ko?".
Har lokacin Hamisu bai da Zeenatu cikanki ba hakan ne ya bata damar cigaba da sirfa masifa had'e da rashin mutunci.
Rabi'atu tana cikin baccinta mai cike da wahala yadda kowacce mafi yawancin Amarya ta ke kasan cewa,kawai sai taji ana zage² daga i'ta sai sleeping dress ta fito ta tufke gashinta ta yi doughnut dashi tana tafiya da k'er kamar zata fad'i k'asa.
Da sauri Hamisu ya taro Amaryarsa Rabi'atu cikin so da kulawa ya ce"oh Sorry Baby da Sauri ya rungumeta had'i da d'aukarta kamar jaririya ya shigar da i'ta d'akin sannan ya lullub'eta ya rufo mata k'ofar.
Ganin Rabi'atu acikin halin da take ciki ba k'aramin d'agawa Zeenatu hankali ya yi ba,wai daman haka kishin ya ke oho,ni kuwa Ummu Maher na ce Zeenatu wa ya gaya miki barni gabas ta ke.
Damk'ar wuyan Hamisu Zeenatu Ta yi sannan ta ce"wallahi Hamisu yau sai dai ko ni ko wannan y'ar iskar matsiyaciya".....
Da sauri Hamisu ya d'aga hannunsa zai mari Zeenatu Amman kome ya tuno oho?don haka kawai sai ya janyo hannun Zeenatu sannan fita da i'ta gaba d'aya daga cikin gidan sannan ya rufe k'ofar yana mamakin hali irin na Zeenatu.
Salma
Kuka ta ke yi mai cike da nadama da Dana sanin Auren Sooraj,da ta yi rabonta da tasa Sooraj a idonta tun ranar da aka d'aura Auren su da safe bayan sun shigo gaisuwar iyaye,yau kwananta biyu a gidan shi ba bu kuma wani d'an uwanshi da ya tako gidan yazo abin yana matuk'ar bawa Salma mamaki,to waishi Sooraj Bashi da kowa ne kome?.
Tambayar da ta ke ta yiwa kanta kenan Amman ta kasa samun Wanda zai bata amsar kuma ko Zuly bayan da tazo da safiyar da aka kaita bata k'ara ganin ta ba.
Kanta ta rik'e da ya ke wani azababben Sara mata ta rik'e tana tuna irin cin amanar da ta yi,tasan Allah bazai tab'a barinta da hakkin Bashir akanta ba domin kuwa ta cuce taci amanarsa,Allah sarki yanzu yana cen da Amaryarsa k'anwarta Habiba.
Ta tuna sanda ya ke ce mata matuk'ar ya yi Aure sai ya yi sati biyu ba tare da ya fita Aiki ba,saboda ta bawa Amaryarsa kulawa.
Wani gumi ta share da wasu zafafan hawaye,yunwa ta ke ji kamar cikin ta zaici babu,rabonta da abinci tun jiya da rana, bawai don babu abincin bane A'ah akwai kawai dai tunani ya hana ta cin abincin.
Tun kafin a kawota Sooraj ya ajje mata kayan abinci kala² masu yawa hatta fridge an zuba komai na more rayuwa.
Sai dai kash!gidan babu wani armashi bare aji dad'in zama acikin sa.
Sooraj
Haba Momi me zaisa kiyi min haka kawai don bakison Salma sai ki saka a kulleni a d'aki.....
Yasin bazan k'ara sa zan cen ba idan banga ruwan Comments ba🤔🤔🤔🤔🤔🤔.
*REAL UMMU MAHER CE✍🏻*
👘🧚🏻♀️👘
*🌹ASANADIN ABAYAR SALLAH🌹*
👘🧚🏻♀️👘
~Gajeren Labari~✍🏻
Na
🌹Rabi'atu B/Abdullahi🌹(Ummu Maher)Miss green💚☘️
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*26&27*
"kai Sooraj kasani duk abinda na yi niyya babu Wanda ya i'sa ya hanani don haka yanzu yanzunnan na keson ka Rubuta wa wannan y'ar talakawan takaddarta don ba gidan ubanta bane wannan k'azamin Malamin don na Riga da na yi maka mata don haka ka Rubuta ta kadda yanzu.
Babu wasa a idon Momin Sooraj Sam,ta mrtuke fuskar kamar ta shanu,cikin k'ara ji ta k'ara cewa zaka Rubuta mata ko sai na tsine maka Albarka!"?
Hannu na rawa Sooraj ya fara Rubuta ta kaddar cikin mamaki Momin ta kallo shi taga abinda ya Rubuta da Sauri ta wafce ta kaddar sannan ta yaga ta,sannan ta fallo wata ta bashi.
" Saki 3 na keson ka yi mata idan kuma ka k'i yanzu in a'i watar da Mummunan k'idirina akanta don bani da imani ballanta na mutunci."
Da Sauri Sooraj ya amshi ta kaddar yana Rubuta wa yana kuka,don yana son Matarsa Salma so mai tsanani don kamillaliyar yarinya ce y'ar gidan mutunci ko hannunta bata yadda ya tab'a mata ba.
Dariya Momi ta yi sannan ta wafce ta kaddar ta gani sannan ta ce"ta shi muje gidan yanzu ka kai mata agabana don ban yarda kaje kai kad'ai ba ta lashe maka kuruwa d'iyar mayu.
*****
*Gidan Hamisu*
Rayuwa suke mai dad'i mai cike da so da k'aunar junansu.
A y'an kwanakinnan idan kaga Hamisu ya yi k'iba ya yi kyau tsofan dole da ya fara yanzu duk ya baje farinsa da kyaunsa ya k'ara fitowa.
Kwanansa Bakwai agidan Amaryar tasa ya fara had'a kayansa don komawa gidan Zeenatu,saboda cika umarnin ubangiji Amman hat zuciyarsa ba ya jin dad'in komawar da zaiyi gidan Zeenatu.
Rabi'atu ta fuskanci hakan don haka ta fara kwantar mai da hankali har k'ofar gida ta rakoshi tana mai bye bye har ya wuce a sabuwar motar da ya siya.
Kamar kullum a cike gidan ya ke ana ta zuga Zeenatu ana mata zugar keken b'era i'ta kuma tana d'auka,kamar kada ya shiga gidan Amman ya daure ya shiga.
Da Sauri Zeenatu ta juyo tana kallon Hamisu, shima ya yi mata irin kallon gefen idon nan,idonta ya hango daya kumbura tsabar kuka,ta rame ta yi wani fayau da i'ta.
Tausayinta ne ya tsargu a zuciyarsa harga Allah har yanzu yana son matarsa Zeenatu Amman halinta ne ya ke saka yaji haushinta.
Bata ce cikanka ba ,shima baiyi mata magana ba ya yi shigewarsa d'akinsa,kamar kullum yauma haka d'akin ya ke babu ko gyaran arzik'i dole ya cire rigarsa ya fara Aikin d'akin ya kunna Room freshener, nan da nan d'akin ya yi kyau gwanin sha'awa.
Aiki ne a laptop d'insa don haka ya fara dubawa bai k'ara bi takan Zeenatu ba don har ga Allah yana tsoron masifar ta.
"Haba Zeenatu yanzu kina kallon Mijinki ya wuce babu sannu da zuwa Ballan tana ma kibi mijinki don ki nemi yafiyarsa abisa duk abinda kika yi mai".
Mama mai magani sunan matar ta shahara awajen gyaran ma'aurata tare da basu magunguna ingantattu na mata.
Duk tsiyar Zeenatu saida jikinta ya yi sanyi ba tayi magana ba kuma bata tashi daga wajen ba.
" Zeenatu Mijinki har yanzu yana sonki kuma kina damar ki gyara abinda ki ka yi abaya don haka ki faran tawa Mijinki kafin kishiyarki ta kwace miki miji kinga wataran sai ki zama y'ar kallo."
Nan fa Mama ta ringa bawa Zeenatu shawarwari kuma akayi dace Zeenatu ta d'auki shawarar don gaskiya ba zata zauna wata ta kwace mata miji ba.
Nan fa Mama ta bata wasu magunguna a take Zeenatu ta fara amfani dasu ta tashi ta gyara gidanta tsaf ta gyara gashinta bayan ta wankeshi daman Zeenatu ga kyau ga komai,tsiyarta ce ta saka bata gyara wa sai yanzu da akayi mata kishiya.
*ANAN NAKE JANYO HANKALI MATA AKAN KADA SAI KINJI ZA'AYI MIKI KISHIYA KI FARA GYARAN KAWAI,TUN KAFUN AYI MIKI KISHIYA YAKAMATA KI GYARA DON HAKA MATA DON ALLAH MUDINGA GYARA HALINMU DA JIKINMU MATA.*
Ta gyara jikinta sosai sai tashin k'amshi sannan ta zira rigar baccinta mai shara shara mai kyau kalar white.
Ta yi kyau sosai ta zumbula hijibinta har k'asa sannan ta d'auka tiren abincin ta yi hanyar d'akin Hamisu.
A hankali ta bud'e handle din k'ofar d'akin ta shiga d'auke da sallama hatta magana aranar sai da Zeenatu ta canza ta.
Kallo Hamisu ya bu Zeenatu dashi kamar ranar ya fara ganinta.
*By*
*Real Ummu Maher ce✍🏻*
👘🧚🏻♂️
*🌹A SANADIN ABAYAR SALLAH🌹*
👘🧚🏻♂️👘
*~Gajeren Labari~✍🏻*
Na
*🌹Rabi'atu B/Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green💚☘️.
_*📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION💪🏻*_
_Mãrubutã Mãsu Aikî dà Jãrûmtã wãjãn îlimãn tãrwã bîsã hãrshén Hãûsã✍🏻_
3∅
Kallon Zeenatu Hamisu ya shiga yi kamar yau ya fara ganinta,sosai ta yi mishi kyau saboda daman Zeenatu kyakyawa ce gyarawa ne kawai ba ta yi.
Hamisu bai San sanda ya ware mata hannayensa ba alamun ta shigo,don yadda ya ganta ko ba'ah gaya masa ba yasan ta nitsu don yadda fuskar ta,ta nuna cikin happy ta shiga cikin jikin Mijin nata tana shak'ar k'amshinsa mai dad'i.
"Don Allah My dear ka yafemin abubuwan da na yi maka na rashin kyautatawa".
Kuka ta ke abin tausayi ya yin da Hamisu ya d'aga hannunsa yana godewa Allah na gyaruwar matarsa Zeenatu tare da jin wani irin sabon sonta ya dawo mai fil.
Bayan yaci abinci ne fa salon ya canza don a ranar masoyan sun nuna sun Dad'e basu had'u ba don sun nuna wa junansu kulawa.
Bayan komai ya lafa ne Hamisu yaga kiran Amaryar hau sau 5,Zeenatu tana kallonsa taje ta rungume shi nan fa aka fad'a sabuwar soyayya,ya yinda Amarya abin ya bata haushi sosai kishi ya tashi,Amman da ya ke Hamisu ya iya lago sai ce mata yayi wayarce ta fara samun matsala shiyyasa, haka Rabi'atu tana ji tana gani ta hakura.
Kwana biyu Hamisu da Zeenatu suka yi suna cin amarcinsu,sannan ya koma gidan Rabi'atu.
Watansu uku da Aure Rabi'atu ta samu ciki,cikin ikon Allah i'ta ma Zeenatu Allah ya kawo mata na ta.
Rabi'atu wata uku Zeenatu wata biyu,kuma a yanzu Hamisu ya had'e matansa ya yinda ya siyar da Gidan da Rabi'atu ta ke ya siya mai part biyu.
Zeenatu a yanzu duk ta yarda makaman yak'inta kula da Mijinta kawai ta saka agabanta,k'awayen banza kuwa duk ta zubar dasu kuma ayanzu ta nemi afuwar Rabi'atu da yayarta Jamila da kuma Mahaifiyar Hamisu.
*MU WAIWAYA SALMA KUMA*
🅱️ack to Salma.
Murd'a handle d'in falonta taji anyi cike da tsoro ta k'urawa k'ofar idanu,don rabon da ayi sallama agidan tun ranar da Zuly tazo.
Kafin ta k'arasa tunanin da ta ke yi kawai sai ganin Sooraj ta yi agabanta,ta dafe k'irjinta kafin ta gama tunanin kawai sai taga wata mata a bayan Mijinta Sooraj.
"Kai soko bana san haukar taka,ka mik'a mata ta kaddar ta ka taho mutafi don ba kallon kallo na ya kawo mu ba.
Ya bud'e bakinsa zaiyi magana Matar ta wafce ta kaddar ta cullomin tana ce wa" Ga shinan mun yarda kwallan mangoro mun huta da k'uda".
"Sai a koma cen gidan Malam mai almajirai a Auri dai dai mutum don kin san ance kwarya tabi kwarya."
Tunda matar ta fara magana Salma ta ke kallon ta don kawai hango kamar da ta ke yi da matar,kuma ta lura i'ta ma matar kallon ta ta ke yi sosai.
Tana fad'ar haka ta fita waje fuuuuuu,ta kama hannun Sooraj suka fita kwallah ce ta fara fito min daga idanuna sannan ina tunani wai yau nice aka yi wa wannan cin mutuncin.
Da k'er ta iya bud'e ta kaddar tana zubar da hawaye lallai tun kafin akai ko'ina ta fara ganin sakamakon bijerewa iyayinta duk kuwa A SANADIN ABAYAR SALLAH.
★<><><>★
"Salma daman nasan dole ne irin wannan ta faru saboda tun ba yau ba nasan ce wa hakan zata iya faruwa yanzu ga y'ar uwarki nan salin_alin suna zaman lfy da Mijinta".
Kuka na ke yi INA Neman gafarar Malam da Umma.
" Tashi ki shiga d'aki ki share ki zauna Allah yabi mana hakkinmu".
Tofa tun daga wannan rana ne Salma ta fara zawarcinta ya yinda ta fita a hanyar Zuly ko kusa bata shiga sabgarta.
★<><>★
Cikin bacci ta yi mafarkin Matar d'an nata wadda aka saka,tana Cewa "Umma me yasa kika rabu dani tsahon shekaru kika zab'i ki zauna ke kad'ai".
Cikin razana ta tashi tana dafe da k'irjinta,tunda ta saka Sooraj ya rabu da wannan yarinyar take mafarki da i'ta gashi yanzu duk ta rasa sukunin ta,tun y'arta tana jaririya ta Rabu da i'ta a sakamakon Auren Mahaifinta da ta yi ya sake aranar da ta fara nak'uda sanadiyyar haka i'ta kuma ta zab'i rabuwa da yarinyar saboda jin tsanar yarinyar ta ke har cikin zuciyarta bisa abinda Mahaifinta ya yi mata.
🤔Ni kuwa Ummu Maher na ce daman laifin uba yana shafar y'ay'a ne.
Oho umman Sooraj ta bani amsa.
Mahaifin Sooraj tun yana k'arami ya mutu,shahararren mai kud'i ne don haka ya mutu ya barta da dukiya mai yawa.
Shekarar Sooraj Tara9 ta samu Miji ta yi Aure shima kuma don kudinta ya Aure ta, shekara su biyu da Aure ta haihu shine fa ya gudu da duk wata kadarar da ta Tara.
Sai dai Allah ya taimaketa,bai had'a Dana Account d'inta ba.
Bayan shekara biyu kuma sai gashi ya dawo da wani mahaukacin kud'i Ashe shi d'an sarauta ne ya yi mata haka ne don ya jarabta ta.
Amman koda ya dawo ya tambayi y'arsa ko d'an sa ce masa ta yi babu rai y'ar tasa tazo.
Baiyi wani bincike ba tunda yasan halin Jamila wato matarsa yasan baza ta tab'a yi masa k'arya ba,sannan satinsa d'aya da dawowa ya kaita Bauchi don ya nunawa iyayansa matarsa daya Aura bayan da aka yi mishi kurciya ya bar gida, iyayansa sun aminta da i'ta suka yi musu fatan Alkhairi suka ci gaba da zaman Aurensu tsakanin mata da miji sai Allah.
Hajiya Jamila ta sharce wata uwar zufa da ta karyo mata.
Washe gari da sassafe ta shirya ta kirawo Sooraj,ta ce mai zai raka ta gidansu Salma,bai k'i ta ta ba saboda yana tsoron Mahaifiyarsa sosai.
Bayan sunje ne suka samu Mlm a k'ofar gida yana alwala.
By
*Real*
Ummu Maher ce✍🏻
👘🧚🏻♂️👘
*🌹A SANADIN ABAYAR SALLAH🌹*
👘🧚🏻♂️👘
*~Gajeren labari✍🏼~*
Na
*🌹Rabi'atu/B Abdullahi*
(Ummü Mãhër)Mïss grêên💚☘️
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
Ending✍🏼😜
31&32
Da mamaki Mlm ya ke kallon su duk da baisan Maman Sooraj ba Amman yasan Sooraj,bai nuna yasan su ba ya cigaba da alwarsa har suka k'ara so, Sooraj ne ya tsugunna har k'asa ya gaida Mlm Cikin ladabi kamar ba Sooraj ba,Umman Sooraj ma ta d'an rusuna kuma ko babu komai ya girme mata.
Mlm Ya ce"zanje Sallah ne na d'an makara"ya fad'i hakan yana gyara zaman bottle d'in rigarsa,don yana sane baice su shiga gidan ba,don Allah yasa ni ji ya ke kamar ya Zane su saboda yadda suka cuci yarinya marainiyar Allah.
Suna tsaye har ya fito daga masallaci,sannan suka zauna a tabarman da ke k'ofar gidan.
Har lokacin Hajiya Jamila bata ce komai ba tunanin ta ta ina zata fara,Sooraj kuwa kallon Momin sa kawai ya ke yi saboda ya matsu ta yi magana don yaji da wacce tazo.
Har lokacin kuma Mlm bai ce komai ba yana sauraron yaji da wacce tazo don ya lura mutanen suna da rainin hankali da kuma wayo.
"Mlm daman Na zo ne a game da matar d'ana,Ina zargin akwai wani k'ulli Wanda Allah ya b'oye,shiyyasa ma na tilas tawa d'ana ya saki Salma."
Da Sauri Mlm ya kalleta cike da matsanancin haushinta Amman baice komai ba,ba ya son ya katseta yafison yaji har k'arshen lamarin.
"Mlm tun da nake ko y'ay'a na ban tab'a basu wannan labarin ba sai yanzu,ta kai ga bana iya bacci tun ranar da naga Salma.
Nan fa Hajiya Jamila ta fara bada labari tun daga farko har k'arshe,tana yi tana kukan nadama da Dana Sani Wanda masu iya magana suka ce k'eya ce.
Shiru Mlm ya yi yana nazarin maganar ta,har ga Allah tun da Mahaifiyar Sooraj ta zauna ya ke hango tsantar kamannin da Salma suke yi da wannan matar.
Kuma babu shakka wannan itace mahaifiyar Salma Amman duk da haka sai anyi bin cike.
Baice k'ala ba ya tashi ya shiga gida don sanar da wannan maganar ga matar shi,Sooraj kuwa kallon Mominsu kawai ya ke yi yana mamakin hali irin nata kayarda d'an da ka Haifa a cikinka.?
Koda Mlm ya shiga gida Salma ya samu tana wanke wanke,ya ce" Salma ta shi ki saka hijabinki zamu je unguwa ne?.
Da Sauri ta d'auko hijabinta ta zura Mlm kuma ya k'arasa shiga gidan.
Babu abinda ya b'oyewa Umma,ita ma ta yi mamaki sosai.
Koda suka fito waje Sai da gaban Salma ya yi mummunan fad'uwa Amman bata ce komai ba iya ka dai kallon banza da ta ringa aika musu.
Gidan marayu suka nufa inda gaban Salma da Mahaifiyarta ta cigaba Da fad'uwa,Momi tana tuno ranarda ta kawo y'arta cikin wannan gidan tun tana jaririya.
Straight office d'in mai kula da sashen sunayen yaran marayu suka i'sa.
Nan Mlm ya fad'a musu abinda ya kawosu,gaban Salma kamar zai fashe saboda tashin hankali
Babu b'ata lokacin aka dubo file d'in Salma da kawo kwanan wata sa kuma wacce ta kawo ta.
Nan Momi ta hango hoton y'arta ta d'auka tana kuka ya tabbata ce wa Salma y'ar ta ce.
Rungume Salma ta yi tana kuka Salma kuwa zama ta yi kamar wata gawa don gani ta ke yi kamar shirin film.
Mlm ma kukan ya ke yi nan ya war_ware wa Salma abinda ya shige mata duhu.
Suma Salma ta yi,nan fa kowa na wajen ya fara salati aka d'auki Salma sai asibiti.
Koda Salma ta farfad'o kuka ta ringa yi tana kiran sunan Allah,yanzu daman ba Mlm da Umma ne suka haifeta ba duk yadda suka rik'eta amana basu tab'a nuna mata ban_ban ci ba tsakanin ta da y'ar su.
Ga kukan rashin dacen uwa da ta yi,babu uwarda za ta tsani y'arta har ta yi tunanin jefar da i'ta,ranar dai haka Salma ta yini tana tunani.
Ko kafin A sallami Salma Alhaji yazo Mahaifinta da k'annenta Safiyya da Mohd.
Kuka sosai ya yi na hak'ntarsa da matarsa ta yi Amman a tsakanin miji Da mata sai Allah ya ya fewa Hajiya Jamila,su Mlm ma sun yafe mata.
Sai dai har yanzu Salma bata yarda da Mahaifiyar ta ba,Hajiya Jamila kuwa wani so da k'aunar y'ar ta,ta ke ji har cikin zuciyarta sannan tana nadamar abinda ta aikata.
Har kullum Neman yafiyar y'arta ta ke yi har sai da Mlm da Umma suka saka baki sannan ta hakura ta sakko tasan Allah ya kawo Mata Sooraj ne rayuwarta don komai ya gyaru,shiyyasa ma har tak'i Auren Bashir ta Auri Sooraj Yayanta sai gashi Allah ya taimaka babu abinda ya shiga a tsakaninsu hasa lima
Ko kwana agidan bai tab'a yi ba.
Koda Salma ta warware Alhaji Mahaifin Salma bai b'oye wa y'an uwansa komai ba sai dai ya ce musu an sace yarinyar ne aka kaita gidan marayu sai yanzu Allah yasa aka ganta,ya yi hakanne saboda kada su zargi matarsa.
Mlm yasa aka kirawo Bashir da Habiba don ya shaida musu abinda ke faruwa don yanzu y'an uwa kaf sun San abinda ya ke faruwa harma da mutanen gari kowa ya shaida Mahaifan Salma.
Koda Bashir ya koma gida wani Abu yaji yana mishi yawo a game da Salma son Salma sabo ne yadawo mai yarasa Wanda zai nema don ya fad'a mishi don harga Allah har yanzu yana son Salma ita ma Salma a nata b'angaren haka yake.
Ayanzu Salma ta koma wajen Mahaifanta Do haka Mahaifin nata ya zab'a babu yadda Mlm ya iya dole ya yarda don Mahaifinta yana da hakk'i akanta.
Tana jin dad'in mahaifanta har cikin zuciyarta yadda suke ji da ita ga k'annenta da Yayanta Sooraj shima yana kyautata mata Wanda ayanzu shima ya shiryu har ansaka ranar Auren su.
Abinda ban Sani ba tare aka saka ranarmu da Yaya Sooraj da Na'ima,ni kuma da Bashir.
Habiba ma tasan da zancen Auren kuma tasan ya halatta Bashir ya Auri Salma,tunda ba iyayensu d'aya ba kuma sune suka shayar da Salma ba.
Habiba tana yawan zuwa wajen Salma sushq hira gwanin ban sha'awa kamar yadda suke ada cen baya.
Kullum Mama na tana bani wasu abubuwa amman ni bansan na meye ba?.
da masu gyaran jiki na musamman nan danan na yi wani kyau da haske kamar ba niba,Momina har Habiba sai da tasa aka yi mata gyaran jiki sannan ta canza mata dukkanin kayan d'akinta, su Mlm suka dinga godiya.
Ana gobe d'aurin Aure gidan ya cika da bak'i,Mahaifina ya sanarmin da komai kuka na dinga yi INA tunanin yadda zan zauna da K'anwata Habiba.
★<><>★
Bayan Aure
Bayan y'an kai Amarya sun tafi Salma tana zaune kan makeken gadonta na alfarma Bashir ya shigo cikin da kakkiyar shadda gezna fara k'al shi daman gashi fari ga kyau da kwarjini,Ahankali ya yi mata Sallama ta amsa cikin voice d'inta mai dad'in sauraro.
Ya hayo kan gadon ya yaye mayafinta,sai da gabansa ya fad'i ganin yadda Salma ta koma kamar ba ita ba.
"Allah Nagode maka da wannan baiwa sa kyautar da ka yi min na Auren Salma."
Salma tana jinsa ita godiyar ta ke yiwa Allah da ya bata Bashir Namiji acikin maza.
Nan ya rik'e hannunta suka nufi sashen Habibq,itama taci kwalliyarta nan fa ya fara yi musu Nasiha mai ratsa jiki.
Koda suka dawo shida kansa ya dinga ciyar da Salma daganan zancen ya canza,koda Safiya Kafin su fito Habiba da kanta ta yi musu GIRKI ta kawo musu.
Salma tana lullub'e da blanket tana baccin wahala don jiya Tasha azaba,dak'er ta sakko taci abinci kamar zata yi kuka Bashir Da kansa ya wanke matarsa tas tare da tausaya mata,kuma yana gode wa Allah d'aya karb'i budurcin Matarsa ba wani ba.
To wannan kenan.
Rayuwa mai dad'i kuma mai cike da k'aunar junanmu Mike yi,bana k'aunar abinda zai b'atawa Habiba itama kuma haka,haka ma mjinmu yana yi mana adalci,
Allah sarki rayuwa a yanzu Bashir har gidan Maine dashi tsabar arzik'i.
Shekara ta d'aya na haihu d'a namiji Wanda Habiba ma tana da ciki wata biyu.
Matar Yaya Sooraj ma ta haihu Twins duk maza.
Zuly kuwa rayuwa ta juya mata baya yayinda da k'er ta samu Wanda ya Aureta Amman matansa 3ita ce ta 4.
To wannan kenan.
*Back to gidan Hamisu*
Zeenatu ta haihu Y'an biyu duk mata,Rabi'atu kuma ta haifi Namji sune zaune cikin aminci da k'aunar junansu.
*ALHAMDULILLAH*
Ana na kawo k'arshen wannan LABARI nawa na ASANADIN ABAYAR SALLAH.
Wanda fad'a karwa ce akan Matansa basu hakuri akan talaucin mazajensu da kuma y'an matan da suke raina arzik'in samarinsu.
Domin sharhi akan wannan littafi kuneme ni a wannan number.
07068606171
Sai na jiku.
Taku har kullum
*UMMU MAHER MISS GREEN*
Sai kun ji ni asabon littafina mai suna
*AISHATU HUMAIRA*
No comments