Recent Updates

Uncle J 7


Page 7

Jalila kuwa saidata leka parlon babu kowa har yanzu Amma bacci ya dauke ta shiyasa bata san wainar da ake toyawa ba,dakinta ta shige sai lokacin taji yadda jikinta yake radadin azaba zama tai ta rafka tagumi su kuma waddan mutanan su wanene haka daga zuwan su zasu takurawa Rayuwarta.

Ko sune wanda Amma ke yawan yimata gargadi akan su inko haka ne tabbas bazata kyale suba koma wane matsayine dasu ita babu ruwan ta ko ciki daya kuka fito kaimata saita rama balle babu dangin iya babu na Baba,Murmushin mugunta tayi tuno abunda zatai musu sai sun sakan kance tukunna zata waiwaye su.

Babu wanda ta gayawa tai kus da bakin ta,haka taci gaba da warkajaminta da aikin ta dan yanzu Iya ta sake koya mata yadda yaka mata kuma Alhmdlh ta dauka bata da ganda ko kiwa Kichin ne bata damu da shigar saba al,adarta na cire kaya lokacin cin abinci babu abunda ta fasa kullum saitai sintir in zataci abinci.

Amma dakyar ta rabata da bujan nan datake ji dashi sababbin pants tasiyo mata guda 12 sai dinkunan ta kala uku takara akan kayanta kayan kwalliyar ta nakauye babu yadda basui da itaba awatsar asaya mata masu kyau amma fir taki yadda,maganar wanka mafa babu ita dan saitayi sati batai wanka ba data giftaka  zakaji wani tsamin dauda ya daki hancinka,haka suke hakuri da ita ahankali wataran zata daina cewar Amma intai maganar tayi takiji saidai tace ALLAH ya shirye ki.

Yau watan Jalila daya agarin Kaduna har kawo wannan lokacin ko bakin Get bata taba zuwa ba tsoran ta daya karta fito daganan amaidata kauye,duk uban abincin datake loda bata kara komaiba to da tana wanka nema a tantance daga fatar ta babu daya saidai taci tai kwaskwarima abada hoda jambaki da gazar aja jagirar nan har kunne.

Harkawo wannan lokaci bata rama abunda su Rufaida sukai mata ba bafa waidan ta manta ba a'ah tana sane kome take sakawa aranta oho.

Yau haka kawai taji tana sha'war hawa bishiya dan andade ba ahaduba bayan tayi kwaskwarimar ta tagado data saba aka caba kwalliya riga da sket da Amma ta dinka mata tasaka sunyi kyau kayan amma da Jalila ta sasu ita daban kayan daban wani dankwali ta dauko acikin kayanta taci dammara dan arayuwarta inbatai dammara ba ai wankan be hauba.

Harabar gidan tafito babu kowa shiru sai sassanyar iska dake kadawa ta La'asar sakaliya,lambun gidan takarasa tsaye tayi tana canki cankar wadda zata fara hawa,idunan ta ne yafada kan wani apple daganin sa bakaramin zaki zaiyi ba,yauwa gawanda yakama ta nahau nagaji dashan mangwaro da gwaiba tun akauye gwara shima wannan na dandana shi kar ayi babu ni.

Daraf tahaye bishiyar ko tsoro bataji saidata daidai ta zamanta sannan ta fara tsinko guda daya takai bakinta lumshe idanu tai kai kambalastin dama akwai wannan abun medadi bantaba ciba kanta ta gaurawa mari amma nacuci kaina datun zuwana banzo wajannan ba,saidata cinye guda biyar tanaci tana sambatu dasawa wanda yadasa bishiyar nan Albarka.

Mota ta hango tana shigowa cikin gidan aguje har nema akeyi atake megadin tsayawa tai taga wane mara mutuncine zaifito daga motar nan.

Salima ce tafara fitowa sai wani wizzy da yasha az down kansa yasha wani aski narashin da'a kamar zasu shige cikin juna haka suka nufo lambun wasu kujeru ne da suke jere reras awajan kan guda daya suka hau duk ko da yadda ta matse su haka suka mamuki juna kamar zata hau cinyar sa.

Zaro idanu Jalila tayi kaga arnan banza har gida kuzo kuna iskanci aiko zanci ubanku daga kai har ita yanzu zakusan wacece Jalila,kiss taga sun fara yiwa juna kamar zasu cinye bakin juna hannu tadora aka dole nai muku jifan shedan yau dinnan.

Ahankali ta sauko daga kan bishiyar cikin sandar karsu juyota bishiyar mangwaro tahaye dakyar damma gwanar hawa bishiya ce da dole sai sunji motsinta,maida Numfashi tayi wani shirgegen mangwaro ta tsinko tsabar nemar rigima irin na Jalila rigar Jikinta tacire aciki ta tara mangwaro saidata tabbatar yayi yadda bazai bata matsala wajan aikin jihadin dazatai ba amma fa afadarta wai jihadi zatai 🤣🤣🤣.

Zuwa wannan lokacin su Hajiya Salima anshagala anata shedanci kamar mijinta tuni yayi fatali da breezeya da take jikinta daga ita sai sket tik haka Salima tai agabansa ba kunya ba tsoron ALLAH.

Sai data daidaici kirjin Salima da suka fara takalewa kamar silifas sai data wana hannunta yadda yaka mata ta saita daidai abun harinta jikake nik akirjin Salima wani ihu ta zunduma jin wata bakar azaba data ziyar ceta kanta tantace abunda ya sameta tafara jin ruwan jifa tako ina adari da sittin tatashi dan iskan saurayin nata tuni Jalila ta fasa masa kai dan saidata duba wani jibgege tukunna ta sakar masa aka.

Ihun Salima ne ya jawo hankalin ma aikatan gidan duk wanda ya rugo dan ganin meyake faruwa suna hango Salima na sabar sabar da kirji ba riga sai su dare kowa sai kaga yasha kwana aguje  mazan su da matan su hatta Amma data fito dan ganin meke faruwa da gudu ta juya dan azaton su bakaken aljanu suka shiga jikin Salima hatta fara wurgi da kayan jikinta.

Mom da Rufaida fitowar su kenan suka hango abunda ke faruw amiliyan suka juya dan duk wanda zaiga Salima tabbas haka zaice ta haukace attachment din dake kanta tuni ya fadi sai wasu yan mitsi mitsin kalba da suke kanta ga Nono har kusan cibiya tana tafe tana zunduma ihu dakiran wayyo aljanu aljanu 🤣🤣🤣 basu tsaya ko inaba saida suka shiga daki suka sa sakata.

Muguwar kuwa tana kan bishiya tana tikar Dariya ko banza yau tarama fiye da abunda sukai mata ranta fes taci gaba da shan mangwaranta.

Sai data Tabbatar da sun bar wajan sannan ta sauko rigarta tasaka cikin farin ciki takoma part din su,tana shiga ta tarar da Iya da Amma anzuba uban tagumi cikin jimami kamar batasan komai ba haka ta waske Amma meyake faruwa naga kamar wadanda kukai gamo duk kun firgice,Uhm kedai bari Jalila ai gamon mukai gan samemiyar budurwa kamar wannan muganta sintir haihuwar tsohuwar ta ai ba lafiya gamon mukai.

Gumtse Dariyarta tayi haba Iya wace magana kike fadi haka wa kuka gani sintir cikin gulma dasan bada labari Iya ta gyara zamanta Amma dai ko kanzil bata ce musu ba,wa kuwa kika sani bayan wadan can kitika kitikan yan matan yayan kishiyar Hajiya,dafe kirji Jalila tai wace Hajiyar Amma mana wai dama wancan matar kishiyar Amma ce.

Au dake baki sani ba kishiyar tace mana da yayanta gansan gansan yau munga abu oh ni Habiba naga abunda ya isheni,wai nikam Iya kiyimin bayani amma sai kwana kwana kike kinkasa magana guda daya,to ai maganar ce bata fade ba shikenan nafasaji tunda abun jan raine eh naji bazakiji mutuwar sarki abakina ba nidai naga abunda nagani kawai.

Amma Iya wai dagaske Amma tana da kishiya af sai kuma kiyi dadina dake shegiyar tambaya,naga ke kika fara kawo zancan nan Iya amma shine zaki doramun lefi haka kawai,to naji gobe ma nasake ganin wani abu nazo nagaya miki tunda bakisan abun arziki ba.

     Uhm bana tashi natafi jaje jame Iya ta tambayeta jaje tam jiki magayi ALLAH ya bada sa'a Ameen.

        Mrs Baba Bello Abubakar

            ............✍️✍️✍️✍️

[7/28, 9:35 AM] +234 903 511 7917: UNCLE J

No comments