Recent Updates

Uncle J 6


 Kulsoom Ismail Idris


Page 6


Amma zama tai kawai ta tsura mata ido anya yarinyar nan bata da aljanu haka take ayya nawa acikin zuciyar ta,Jalila kuwa saida takai kusan karfe 10 tatashi tana mitstsika idanu hango TV tayi akunne zumbur tamike

abunnema fa ya samu,gaban plasma ta zura da gudu samun waje tayi ta tankwashe kafa kamar idanunta zai fado saboda yadda take zazzaro shi in anzo wajan Dariya tayi ihu da tafi sannan takoma ta zauna.

Babu kowa a parlon sai ita kadai Iya nacan tana aikinta dan bata tsayawa jiran Jalila talura ba aikin tazo ba kuma taga Amma tasa mata ido bata takura mata da tuna mata abunda ya kawo ta.

Alhmdlh abunda Salima tace kenan hango Mahaukaciyar da suke nema kallon juna sukai ita da Rufaida murmushin mugunta suka saki sket din jikin su da yayi matukar damesu suka tattare gaba daya tabada hankalin ta wajan film din da ake haskawa cak taji andaga ta dama aba banauyi ba tana shirin kurma ihu ruf Salima ta toshe mata baki da dankwalin hannun ta.

Basu direta a ko inaba sai gaban Mom,yauwa yaran albarka aini nasan dama bazaku bani kunya ba haba Mom taya wannan abar zata gagare mu ko Uwar ta basai mudauko ba balle ita,tsai Jalila tai tana kallon su da Mamakin mene dalilin dazaisa suje sudauko ta kamar wadda tai musu sata.


Mom ce tajuyo tana kallon Jalila wai wannan yarinyar ce ta kayar da ita rabonta da faduwa tun zamanin kuruciyar ta amma shine wannan village girl din zata sata faduwa,daga hannu tai kawai ta kwashe Jalila dawani azababban Mari duk taurin rai irin na Jalila wannan marin ya shigeta amma tsabar kafiya sam bata nuna ya shige taba,su kansu sunyi mamakin ganin ta dungurgur azaune kamar wadda aka sosawa kumatu.

Haduwa sukai su ukun suka dinga jibgarta kamar Allah ya aiko su bawai batajin zafin dukan bane a'ah tanaji kukan data fahimci suna so tayi shine bazasu gani ba amma sosai lugudan da takesha yake shigarta.

Sai da suka gaji dan kansu saigashi suna ta haki kallon su tayi daya bayan daya ta fashe da dariya ko banza taba su aiki kuma bashi suka ci ba ataba ta bama tayi balle kuma antakale ta.

Dama kwana biyu neman wanda zasu kara take sai gashi Allah ya kawo su har inda take,cikin mamaki suke kallon ta tome takeyiwa Dariya wace irin shedaniyar yarinya ce wannan,Salima ce takawo mata hanbari da kafa ke dan ubanki waye sa anki anan da zaki samu agaba kinai mana Dariya,wata dariyar kularwa tasake saki ta ya mutsa fuska ni dama kunji nace akwai sa'ana acikin nan aiku kunriga kuntashi daga aiki kunzama guzumayan mata gaku arna aikunga bana hada kaina da kuba.

Kuma kusani wllh bashi kukaci ni Jalila nice murucin kan dutse ban fito ba saidana shirya,nice kabewar kan kabari bakin cikin me taushe,ba aimin bama nayi balle kuma an takaleni kusa aranku saina wajiga rayuwar ku sai kunnemi hada kayan ku kunbar Gidannan.

Mom ce tasake kawo mata mari wani tsalle tai kamar birinya sai gata acan tsakiyar parlon haba dai inna zauna kuka sake duka na aiban cika Jalila ba wanda kuka daka yanzu ma kyale ku nai yadda innatashi ramawa Allah bazai kamani da laifin na zalince kuba bana manta ranar daukar fansa sai mun gauraya.

Ku sake kamomin aljanar yarinyar nan tara tara sukai dan su kamata amma saidata hargitsa musu parlour gaba daya su basu kamata ba ita kuma bata gudu ba wani glass cup ta hango dagani zaiyi tsada tana sane da suka biyota gadan gadan dama hanyar glass cup din tayi garam tai gaba dashi saidayayi sama sai gashi akasa tush ya tarwatse.

Hhhh kafin su ankara ta fyalla waje da mugun gudu tana dariyar mugunta Rufaida wadda idanunta ya rufe burinta kawai ta kamota cikin gudun da take sha tana daga kafar ta ta dora akan kwalba kara ta saki tuni jini ya fara tsar tuwa jabar tazauna ashe akwai wata akasan wata kara tasake kwallawa tare da fashewa da kukan azaba kwalbace ta shige mata bom bom.

🤣🤣🤣🤣Azaba kan azaba gata kafa gata bom bom kanta sukayo gaba daya suna tsinewa Jalila da danasanin dauko ta da sukai da kyar Rufaida ta mike kwalba tariga tanitse jini kawai ke shatata,cikin hanzari Mom ta dauki wayar ta doctor ta kira akan yayi sauri babu lafiya cikin 20mint ya karaso dan Rufaida babu dama ta zauna tana kwance ruf da ciki tana kukan azaba.

Da kyar yasamu ya zaro kwalbar ta kafarma ansha fama kan tafita saiga Rufaida da plaster a bom bom dan danan kuwa zazzabi ya ya rufeta cike da sakijin tsanar Jalila wadda ko sunanta bata sani ba amma tajawo mata wannan bala,in tana zaman zaman ta.

Haka Salima da Mom sai cin alwashin abunda zasiyiwa Jalila sukeyi dan baza su  kyaleta tasha su abanza ba.

😁😁😁Haryau baku daddara ba muje zuwa.

Taku Mrs Baba Bello Abubakar

           .......✍️✍️✍️

No comments