Uncle J 5
By Kulsoom Ismail Idris
Page 5
Kai tsaye parlon suka nufa kamar baza su taka kasa ba Uwar ce agaba yayan nabiye da ita,cikin takama da tun kaho tashigo parlon gaba daya idanunta ya rufe sam bata lura
yadda parlon yacika da ruwa da kumfa ba suuuuu tatafi jikake tim tamaku da kasa,kan su ankara da abunda yake faruwa sun sako kafafun su kusan tare suka kai kasa gaba daya jisukai kugun su yayi azabar amsawa kai anyama basiyi targade ba.Faduwar yan matanne tajawo hankalin Jalila da aiki yayi aiki ganin mata yashe akasa sunyi tsamo tsamo kamar akuyar datasha ruwa fashewa tai da Dariyar mugunta tana nuna su hhhh kai amma wllh anyi girman banza yanzu wannan dan ruwanne yasaku faduwa kun tabbata ragwaye ne ku.
Kuluwa iya kuluwa sun yita wannan wace matsiyaciyar Mahaukaciya aka kawo musu Gida ko yar gidan Uban wacece sai jikinta ya gaya mata,wani ashar Hajiya Luba ta durowa Jalila dan lokaci daya sukaji tsanarta ta mamaye musu Zuciya wallahi muka tashi sai jikinki yagaya miki wace irin Mahaukaciya ce ke zaki zo kicikawa mutane parlo da ruwa.
Dan Uwarki ba Magana nake miki ba,karki sake zagin uwata wallahi dan ba sa arki bace yo wa yakawo ku tsabar Munafurci kushigowa mutane Gida da sassafe kusu Uban wane da bansan ku ba dan daganin ku maula kukazo.
Tashin hankali har su wata kucaka yar kauye zata tsaya tana gaya musu magana harda zagin Mom,kayan jikin su tatsaya tana karewa kallo fashewa tai da wata dariya tana nuna su ashema arnane nake bata wakaina lokaci karku damu in sha Allah bazan gaji dayi muku wa aziba saiku musulunta.
Wannan kowa ce shegiya ce Allah kadai zai raba su da ita,cigaba tai da aikin ta tabarwa banza ajiyar su tana rawa da raira waka irin wanda sukeyi adandali dakyar Mom ta daddafa tamike tsaye haka Rufaida da Salima kallo daya da sukaiwa Jalila sukaji tsanarta aran su balle kuma wannan lefi data sake yimusu komawa dabaya sukai cikin dabara suka fice daga part din gaba daya.
Da kyar suke tafiya kamar agwagi hardiga sukeyi sabida cikin ruwan da suka shiga part din su suka nufa da Jalila batasan dashiba tun zuwanta gidan,saida suka canza kaya tukunna suka samu bakin magana.
Yanzu Mom kina tunanin kyale wancan yar iskar yarinyar ne mukaga kinyi shiru,ai wllh Mom matukar baki dauki mataki ba muzamu dauka ba ataba dizgani irin yau ba ace wata kucaka yar kauye ita zatai mana wannan danyan aikin bazai yiwu ba Salima tafada cike da bacin rai wllh nayi alakawarin sai na yiwa yarinyar can dukan mutuwa saita manta sunan ta gaba daya.
Kwafa tayi itakadai take ayyana Abunda zatayiwa Jalila haka Rufaida take ayya nawa balle Mom da gaba daya bacin rai ya hanata magana intai magana ma aita bata bakin ta akan wata kucaka mewarin baki kwafa tai alamar zasu gauraya.
Iya ce tafuto daga dakinta suuu tatafi saura kadan tasha kasa fadi take kalu innnalillahi nashige su mezan gani nijikar furaira,dafe kirji tai tana kallon Jalila data zuba mata idanu tana kallonta haba Iya kamar wadda kikaga wata masifa kikejan wannan kalu haka ko gyaran nawane ya gigitaki yatafi da imanin ki dakuwa Iya tai mata ungo nakinan Jalila wane irin shirme kikeyi wannan dubafa kiga yadda gaba daya kika lalata parlon.
To bazan gyaraba aiduk acikin aikine eh naga alama kuwa,dai dai lokace Amma ke sauko cak tatsaya tana kallon aika aikar da Jalila tayi,sai washe baki takeyi ita alallai Amma tayabeta,yanzu haka kika maida wajannan Jalila kalli waje kin maidasa kamar wani kududdufi haka aka koya miki to matukar bazaki Iya aikinnan ba Gida za'a maidake.
Kamar wadda akasawa shorking haka tazabura tai baya saura kadan tasha kasa tsugunnawa tai ta dora hannu aka iyakar karfinta ta daddage tafasa kuka baki hangame Amma ke kallon ta,nidai dan ALLAH karki maidani aimini Aure tayama zanbar wannan dadin danake ci aka ciyar da arnema balle Musulmi.
Arne wane arnan bayanzu wasu gan sama gan saman arna suka fitaba tare da wata lutiyar mata dagani itakuma shugabar arnace,duk yadda Amma takai da shan kunu saida tayi dariya,su Hajiya sun dawo kenan fitina tadawo abunda tafada kenan aranta.
Kewaya cemiki arnane to itama matar gidannan ce kamar ni yadda zakimin aiki haka itama zata iya saki kiyi mata aiki kinjini ai,waro ido tai kema musulunta kikai daga baya kenan tanayi tana fata hanna yanta kin auna arziki Amma dayanzu ashe dagake se wannan bujan najikina zakina yawo,fashewa Amma tai da Dariya toko zata tafi tsirara aibaxa ta iyasa wannan bujan na Jalila ba daya hada uwar dauda kamar me.
Zata sake magana Amma ta daga mata hannu dan in zasu kwana suna muhawara bazata gajiba kimin shiru haka,Iya ta kalla temaka kitayata ku gyara parlon to kawai tace harara ta zabgawa Jalila haka kawai tabasu aiki da sassafen nan kai wannan yarinya bataji dadin halinta ba.
Sun shafe kusan awa biyu kafin parlo yadawo hayyacin sa gaba daya sun gaji anan kasa Jalila ta bingere takama baccin gajiya to wannan aiki aidole kisha bacci.
........✍️✍️✍️
No comments