Recent Updates

Uncle J 4

 


28, 9:35 AM] +234 903 511 7917: UNCLE J

Page 4

Iya Iya Amma ta kwalawa wannan matar kira gani Amma yauwa dan ALLAH kawowa Jalila abinci dan da alama yunwa take ji,

kallon Jalila tai cikin Dariya gaskiya da alama kuwa bana kawo mata minti 2 tafito da plate ahannun ta taf taciko shi agaban Jalila ta dire shi makwat Jalila tahadiye yawu kallon Iya tayi amma yanzu saboda ALLAH kirasa acikin abinda zaki samim abinci sai wannan dan mitsitsin farantin.

Baki bude suke kallonta azatan suma bazata iya cinye waba duba da yadda take yar firit da ita,keyanzu wannan abincin kadan yayi miki to aini wannan ko yayan hanjina bazai gama tasar suba zai kare,wannan din inji Iya cikin mamaki shidinfa cike dajin haushin Iya tana nema tai mata bakin ciki.

Kinga cinye sai akara miki cewar Amma data zuba ido taga yadda zatai da Abinçin tsam sukaga Jalila tatashi tafara kici kicin cire riga tofa abinda Iya kefadi azuciyarta haka Amma datake kallon ikon ALLAH atakaice dai saida Jalila tai tik daga ita sai wani bujan wando da Inna tasa aka dinka mata na atamfa komawa tai tazauna tare cire dankwali dan abincin yafi shiga sosai.

Batama san suna yiba cinyar kaza tadauka gam taruketa a hannunta fashewa tai da Dariya kai yau ALLAH ya hadamu wallahi saina yimiki cin rashin mutunci kamar yadda kika barar mun da abincina rannan wani cizo takaiwa cinyar waifa duk dan taiwa kazar mugunta ne🤣🤣🤣.

Tuni suka fara tunanin kodai tanada tabin hankali ne kafin mintuna uku tatashi da shinkafa da miyar kamar bata ci abuncin ba haka takeji lasar hannu take kamar zata cire yatsun hannunta, Hajiya ban koshiba kalli cikina tashitai tana jujjuyawa ko alamar tashi beba,uhm abunda Amma tace kenan lallai aiki ya same su.

Karo mata Iya karbar plate din tayi cike da jimamin dawa ALLAH ya hada su kara ciko mata shi tai tas takara hallakewa hakamma badan fa taji cikinta yakai geji ba maleji tayi dan kartai abun kunya abun kunya nanawa kuwa saidai kar akuma Jalila.

Tas tatashi tamaida kayanta Amma ce ta kalleta dauke da murmushi sannu da kokari shiru tai tana muzurai tashi muje nakaiki dakinki yan kullin kayanta tadauka tare da dorawa aka tabi bayan Amma ganin zasu hau bene taja tunga ta tsaya tana daga kanta tundaga farko zuwa karshe ina zasuje haka waiwayowa Amma tai tana kallonta taho mana Jalila

Hajiya nan kuma inane zaki kaini bene ko baki taba ganin saba a Tv din da kike kallo washe baki tai ina ganinsa yan gayu suna hawa Dariya tayi to aikema kinzama yar gayun ko da gaske ta kurawa Amma idanu cikin shakkun abunda take fada mata ehman amma sai kinfara wanka da kwalliya bata rai tai itafa indai saitayi wanka zata zama yar gayu saidai karta zama.

Ganin zata bata mata lokaci baya tadawo taruko hannun Jalila kamar gurguwa haka tadinga hawa benan akalla saida suka shafe kusan 10mnt dakyar Jalila takai karshe gani take kamar zata fado,ita kanta Amma tagajiyar da ita haka nan taji tana kaunar yarinyar shiyasa tashiryawa duk wani shirman ta amma tana tunanin zaman ta agidan dan tabbas mutanan gidan sukai arba da ita tofa bakaramin yaki za aiba dan sun tsani mutumin kauye.

Kunjifa wata sabuwa inji yan caca.

Wani daki dan madaidaici ta shigar da ita babu abunda babu adakin wani dan karamin bed ne ya matukar birgeta sai jujjuyawa takeyi adakin duk wannan nawane gyada mata kai tayi eh nakine amma bana son wasa kullum da safe zakidinga sauko wa kikama aikinki sharar parlourn da Moping shine aikin ki saiki shiga kiching kitaya Iya aiki kinjini ai gyada kai tayi.

Sannan banda tsokana da rashin Kunya kowa ki girmama shi karnaji karna gani sam ba sauraran Amma takeyi ba burinta kawai Amma ta futa tahau gadon can da take  hange tayi tsalle akansa tamike tayi rawa akai shine burinta, toilat taja hannunta saidata koya mata duk yadda zatai amfani da kayan ciki sannan tafuta ta kyaleta.

Da gudu ko ta haura kan gadon tana birgima da ihun murna zata kwanta akan gado me laushi ba irin na Inna ba duk tauri tadade tana tsalle tsalle gaba daya ta hautsine dakin kamar bashiba duk abinda tagani saidata taba tai kaca kaca da dakin babu abunda ya dameta.

Da yake akwai Masjid a gidan ana kiran sallah taje tai Alwala duk fitinarta bata wasa da sallah ta inda taciri tuta kenan dan Inna saidata jajirce wajan ganin bata wasa da sallah.

Yau dai kwanan Jalila biyu agidan haryanzu bata fara aiki ba Amma tace sai tayi kwana uku zata fara bayan Iya tagama koya mata abubuwan da zatayi,har wannan kwanakin bataga motsin kowa ba da Amma tasha gargadin ta akan mutanan gidan tasha tunanin to ina mutanan da Amma take yawan jamata kunne akan su.

Yau Jalila zata fara aikin ta duk tsawon kwana kinnan batayi wanka ba kullum saidai tawanke fuska da ruwa talafka mai da hoda dan harda kayan kwalliyar ta tataho tun Amma namata magana har tagaji ta kyaleta.

Tana saukowa tadauko wani katon baho harabar gidan tafita  takunna panpo taciko shi da ruwa da kyar takawo shi parlourn gaba daya tajike wajan mopar ta dauko kilin data gani a kiching ta dauko tsaf saidata juye leda guda abahon da hannu tafara dibar ruwan tana watsawa gaba daya sai data tabbatar wajan ya jiku yadda ya kamata yadda zaiyi dadin wanki dan sosai takejin haushin Iya akan bata iya aikiba yau kam babu wanda bazai tafa mata ba.

Zagewa tai ta dinga dirzar parlon baji ba gani aiko kumfa sai tashi take,tsayawa tai ta rike kugu tare da fadin wash alamar aiki yayi aiki itakanta nema take tasha kasa amma haka ta daure taci gaba da tsaiwa.

Megadi ne yaji ana zabga Hon da sauri ya tashi ya wangale kofar motoci biyune suka shigo kalu Innalillahi kawai yakeja kwana biyu da basanan bakaramin wata yawa sukai agidan ba,amma yau Masifa ta dawo shikan sa Direba beji dadin da wowar su ba kamar yace su koma haka yaji.

Wata hamshakiyar matace ta fito bayan Direba ya zagayo ya bude mata kofa dakyar ta fito tana baza hanci cimgom ne abakinta tamkar yarinya haka take taunar cimgom din.

Wasu yammata guda biyu ne suka fito suma cikin wasu matsatstsun kaya kamar ba yayan musulmai ba, wani uban hills ne akafar su me shegen tsini.

Sannu da zuwa Hajiya Get Man yakara so yana musu sannu amma ko kallo be ishe suba ko kusa ma basu nuna dasu yake ba daga uwar har yayan abun yayi masa zafi amma shanyewa yayi tunda babu yadda zaiyi sune masu gidan.

        Taku har kullum

No comments