Recent Updates

Uncle J 36


 Page 36


10mnt  wash cikina murdawa yake sai kun taho har gudu ta hada dashi kafin ALLAH y bata sa'ar afkawa toilet,ko gama daidaita batai acikiba Rufaida ta fara buga kofa dalla malama kiyi sauri kifito cikina murdawa yake,banza tai da ita kamar bataji ba aiko tasha zagi wajan Rufaida sai data gama tsaf sannan tafito,bangajeta tai ta afka toilet din itama kamar jira ake ta fito cikinta ta yasake wata azababbiyar kartawa durkushewa tai cikin tsananin azama.


Dakin Mom ta ruga asukwane ta afka toilat tana shiga Mom na fadowa dakin a hargitse sai uban gumi take hadawa ko ganin gabanta batayi burinta kawai taganta a toilat,amma me tana tura kofar tajita gam tashin hankali masifa Mom ta fara yayyafawa,wace yar iskar ce ta shigarmin toilet koma wace acikin ku tai gaggawar futowa tsit Salima tai.


Mom bugu take kamar mahaukaciya durkushewa tai jin yadda wata shegiyar gudawa ta matsota bata ankara ba taji tanabin kafafunta,Salima ce ta fito aguje Mom ta fada Toilat dakin ya dumame da wani shegen wari kamar mushe ya mutu hanci Salima ta toshe.

Gadon Mom tanufa da nufin ta huta ko gama zama batai ba cikinta yabada wani zuuuuuu kululu durowa tai da rarrafe takaraso kofar tafara bugawa da hada Mom da Allah akan ta fito kememe Mom taki fitowa,tsananin wahala tasa Salima fashewa da kuka jitake kamar ana hura mata wuta aciki,zuwa wannan lokaci ta dade da sakin abunta a wando sai dakin ya sake bada wani kafirin wari mara dadin shaka ko kadan.


Awannan dare tun suna iya kai kansu toilet saida suka kasa mikewa gabadaya kamar andadduke musu guiwowin su haka suke ji,suna daga kwance suke sakin abin su gaba daya sunyi zuru zuru,kafin gari ya waye gaba daya basu san inda kansu yake ba.


Karfe 7 Dad ya sauko daga bangaran sa yay sauri yake zai fita yana da meeting shiyasa yau zaiyi sammakon fita,har zai wuce part din su ya dawo da baya dan yana da tabbacin iyanzu dai basu tashiba. 


Tunda ya doshi hanyar part wane shegen doyi ke masa welcome,to wannan doyin mene haka yana bude dakin Mom saida ya dawo da baya wani shegen wari ne ya bigi hancin sa toshe hanci yayi subahanallahi Sarah menene ya mutu acikin dakin nan jin shiru yasashe kundun bala ya shiga dakin,yadda ya hangisu ragaje ragaje kamar ma tattu ras yaji gabansa ya fadi da sauri ya karasa in ya kalla daidai kamar basa cikin hayyacin su.


Hannun Mom ya rike sai gashi koma,juyawa yayi ya fita da sauri dakin Jalal ya wuce kai tsaye,my son yana jamai kafara sa cikin bcci yaji kamar Dad din na kiransa farkawa yayi ganin Dad tsaye akansa yasan babu Lafiya mikewa yayi cikin alamun bcci be ishesa ba,maza ta so kaduba min su Sara gasu can akwance ita da su Salima kamar basa cikin hayya cin su.


Saukowa kawai yayi ya bishi abaya ba karamar dauriya yayi ba wajan shiga dakin sun jage jage da jikin su,to she hanci yayi Dad sunci wani abune da ya bata musu ciki abun yayi worst da yawa ko yaushe zasu iya rasa rayuwar su kwalara ta kama su ba da wasa ba,to kayi musu temakon gaggawa mana dage kafadar sa yayi wannan ba aiki na bane saidai akwashe su akai su hospital.


Kaine zakayi wai Jalal meyasa kakeyin haka badan yaso ba ya amsa da to dan Aduniya ba mutanan da ya tsana sama da su.daga waya Dad yai ya kira Ammah tana zaune tana lazimi cikin azama ta sauko dan jin wannann mummunan labari dakin Iya ta wuce sai data tasota suka taho tare su kansu sun girgiza da ganin yadda suka koma kamar basu ba,yanzu taya za'a dauke su agyara su kema Ammah banda abinki duk gidannan wazai Iya daukar wa yannan fafaromar ai saidai yallabai.


Wani kallo ya watsowa Iya tsit tai tana sunkui dakai ko zasu mutu babu wadda zai dauka acikin su saidai su shekara anan,allurai ya hada drip kowacce ya daura mata dan danan ya kare saidai kowaccen su tasha leda biyar sannan ya rage musu gudun ruwan ya daura musu ta shida kamar yayi bindiga dan takaici.


Waini son me sukaci haka ya sasu wannan kwalara da da tsautsayi fa sai dai azo aga gawar su kafada ya daga su suka sani koma me suka ci gobema sa kara,kowa dauriya yayi da ya tsaya adakin dan babu yadda zasi ne yana sa musu ta 7 yayi waje dan shi ya gama aikin sa kosu warke koma kar su warke ba shi da asara.


Rukayya ko zaki gyara musu jiki kin gan su cikin kazanta fa abundai ba dadi,Dad ta duba gaskiya bazan iya ba karya da ciwo mari da zafi in sun tashi sayi da kan su waje tai Iya ta bita abaya wannan dinma tayi ko kari ta tabbata da itace ko kallo bazata ishe su balle kuma suzo su jima adakinta alhalin tana cikin wannan yana yin.

                Mrs Baba Bello Abubakar

                  .........✍️✍️✍️

No comments