Uncle J 30
Page 30
Karar ruwan dayaji yasa yadan bude idanun sa harya basar ya kasa hakan dan bega sanda wani yaje wajan ba ahankali ya mike gaba daya yau bayajin dadin jikinsa kamar Zazzabi ke son kamashi,ruwan ya hango tunda ga nesa yana motsi alamar akwai Abinda ya fada cikin sa karasowa yayi idanunsa alumshe yanayin yayi matukar yi masa dadi musamman da yazo bakin ruwan
.Cikin ruwan ya kurawa idanu ras yaji gabansa ya fadi kara ware idanunsa yayi in yaga daidai mutum yake hange akasan ruwa,cikin azama yacire rigar jikinsa yayi wulli da ita ruwan ya fada saida yayi can kasa yadago ta gaba daya tayi wani irin nauyi babu inda ke motsawa ajikinta harlokacin begane wacece ba,futowa yayi dauke da ita akafada ganin Jalila yasa zuciyar sa wani irin harbawa yaushe tazo wajan meya kawo ta.
Akasa ya ajiyeta idanunta arufe danna cikinta yayi saiga ruwa yana fitowa ta hanci ta baki har wannan lokacin Numfashinta bedawo gaggar jikinta ba cak ya dauke ta suna zaune har wannan time din suna kulla yadda zasu bullowa Jalal da Jalilah kai harma da Ammah da Dad,binsa sukai da kallo ganin yadda ya shigo asukwa ne duk kwakwarka bazaka taba shaida akwai wata razana afuskrsa ba amma acikin zuciyarsa razana ce me matukar yawa da tashin hankali.
Kai tsaye bedroom dinsa ya wuce da ita dagashi har ita sai digar ruwa sukeyi rasa ta ina zaifara yayi,akan bed dinsa ya kwantar da ita hancinta ya toshe iskar bakinsa ya hura acikin bakin Jalila,ajiyar zuciya ta sauke kusan tare suka sauke ita da Jalal da yake cikin tsananin damuwa ga Ammah bata nan taje Unguwa rasa mezai taimaka mata dashi yayi kamar ba likita ba gaba daya kansa ya toshe.
Rawar sanyi tafara hakoranta har haduwa suke da junan su kayan jikinta ya cire mata danya lura sune suka saka mata rawar sanyin da takeyi wardrobe dinsa ya bude rigar sanyi ya dauko ya saka mata sai wani wandon sa three quarter harkasa yaje mata amma bata daina rawar sanyin ba.
Blanket ya lulluba mata gaba daya bata cikin hayya cikin ta box dinsa ya dauko ya hada allura yayi mata sannan ya fada toilet ruwa me dumi sosai yayi wanka dashi tukunna yaji dadin jikinsa, still rawar sanyi takeyi kamar zata shide masa dafe kansa yayi da sauri ya tashi ya fita ko Ammah ta dawo bata dawo ba har Lokacin toya zaiyi da Yarinyar nan.
Rigar sanyin ya cire mata da wandon daya sa mata towel yadaura mata, toilet ya wuce da ita ruwa me dumi ya tara a bathtub yasakata aciki ajiyar zuciya take sauke wa saidaya tabbatar ta gasu jikinta ya rake rawa sannan ya fito da ita bathroom ya saka mata,dauko ta yayi ya dawo da ita applying cream yayi mata me kamshi da sanyaya zuciya kayan daya cire mata ya mayar mata.
Blanket ya sake rufa mata gaba daya haki yake ya matukar gajiya be saba da wannan aikin wahalar ba ga Jalila da shegen nauyi cikin wasu mintuna bacci ya dauke ta gashin kanta yasha ruwa gaba daya ya mammanne a gefen fuskarta takara wani haske zuba mata idanu yayi yana kare cute face dinta kallo uhm sleeping beauty yafada a zuciyar sa,mikewa yayi ya koma parlo zama yayi har Lokacin zuciyarsa bata daina bugawa ba yayi zatan tuni Jalila ta jima da mutuwa me za ace da iyayanta in Yarinyar su ta mutu shine kadai abunda yake zuciyar sa.
Kiran sallar magariba ne yasashi tashi Alwala ya daura yana idar da sallah wayar sa tai kara peaking yayi ganin sunan wadda yake yawo akan screen din,Jalal ina Jalilah dan kallon ta yayi kadan tana dakin ta Ammah ok babu dai wani abu dake damunta uhm babu Ammah,dama zan gaya mane bazan dawo yau ba Zainab ce ta haihu kuma ni yakamata ace nazauna a asitin kakula da Jalilah dan Allah duk Abinda take so kabata.
Dan Lumshe idanun sa yayi da tunanin ya zaiyi da Jalila ita da bata da Lafiya shikenan Ammah saikin dawo Allah ya tashemu lafiya ameen sallama sukai ya sauke wayar daga kunnan sa,Numfashi ya furzar daga bakinsa goshinsa yake murzawa cikin tsananin damuwa ina zaikai Jalilah yana da tabbacin ya kaita wajan su Mom kafin safiya zasu kashe ta ko wajan Iya zai kaita no hakan ma be masa ba.
Kallonta ya sakeyi ahankali take sauke numfashi dagajin yadda take fitar dashi kasan ba dadi takeji ba tunani bar katai su suka cikamai kwanyar sa,yana zaune awajan har akai sallar isha'i yana idar da sallah Jalila ta farka,duk ilahirin jikinta jitake yayi mata nauyi kamar wadda akasa madoki aka doddoke guiwowinta haka take ji.
Dan motsawa tai hakan ya sanar dashi tashinta,ahankali ya taso kamar me jin tausayin kasa zama yayi kuda ita goshinta ya dafa babu wani zafi ya sauka kuri tai tana kallon sa babu bakin magana saidai idanunta da suka kara wani girma sunyi ja alamar bata da cikakkiyar lafiya,yaye blanket din yayi dagata yayi ya zaunar da ita amma Jalila kasa zama tai akan jikinta tafiyatai zata sake kwanciya yasake zaunar da ita amma fa zama ya faskara.
Gaba daya tayi laushi hatta dan yatsanta jinsa take takasa motsashi sai idanu kawai dake kallon sa,cikin damuwa yake kallon ta Yarinya lafiya kalau amma kalleta ta koma kamar wata zautacciya to kodai gamo tai acikin ruwan shidai betaba ganin dan mutum ya fada ruwa ya kasa zama sai akanta,daga karshe dai saidaya jinginata da jikinsa ta dan zauna.
So yake yaji magar ta koda tsiwar ce duk yadda yake tambayar ta metakeji takasa bude baki tamai bayani bawai dan batajin sa bane sarai tana jinsa amma bakinne yaki bata hadinkai ta budeshi tai masa magana,saiya kara shiga cikin damuwa da taraddadin ko tasami wata matsalar ne.
Yakici abinci gyada masa kai tayi alamun eh kwantar da ita yayi da kansa ya shigo Kichin wajan Iya tai mamakin ganin sa ita zata iya cewa ma bata taba ganin sa a Kichin ba, yallabai me kake bukata dan jim yayi abinci zaki hadomin sai tea to ta amsa dandanà n tahada mai gaba tai zata kai masa dining no kawo karba yayi yafi ce tabishi da kallo tunda zu zuba idon ganin Jalila takeyi amma shiru bata ganta ba.
Har bedroom din yakai Abincin dagota yayi ya nufi toilet da ita brush yayi mata sannan ya dauro mata Alwala bata da hijab haka shima baida wanda zai bata,dakin Ammah ya bude ya dauko nata key yayiwa dakin sannan ya fito tana kwance kan praying mat din da yadora ta hijab din yasa kamata atakaice dai Jalilah daga kwance tai sallah.
No comments