Recent Updates

Uncle J 29


 Page 29


Suna tsaye har wannan lokacin cike da hassada da bakin ciki jira sukeyi kawai ta futo su sake yimata shegen duka su cire kayan jikinta,kamshin turaransa kadai ya isar musu da sakon saukowar sa daga kanta tai ta kalli saman hada idanu sukai kumbura fuska tai dan taji haushi da dazu yaki zuwa ya rama mata dukanta,kauda kansa yayi daga kallon ta.


Muzurai su Mom suka fara dan basu so saukowar saba kwafa Mom tai dayi musu alamun su zauna zama sukai sun zuba masa idanu kamar tsofaffun mayu kwarjini yake musu matuka aduk lokacin da Mom tasu yimasa tijara kwarjininsa kesata kasa aiwatar da komai saidai taita cika baki amma ingata gashi saidai tai kus takasa furta abunda yake kan harshan ta.


Biyo ni abunda ya cemata kenan kamar bashi yayi maganar ba kai tsaye dining ya nufa binsa tai abaya da plet din Abincinta ahannu set kikam tai masa kamar wata soja zauna sai Lokacin taji abunda yace zama tayi akan kujerun da suka zagaye dining din idanun su Mom kamar zai fado kasa su zauna wata yar kauye tazo ta zauna aiko bazata sabuba ba.


Yana sane dasu a parlon sosai yakejin idanun su akansa amma ya basar kamar besan da suba,kadan ya zuba abincin kallon Jalila yayi datai tsuru kamar ba ita ba yau bakin tsiwar ya mutu,ci abincin ki to ta amsa mikewa tai kallonta yayi da alamar tambaya daga rigatai tana kokarin cire wa dan sarar Jalila haryau tana nan inzataci abinci saitayi tik da ita.


Rike rigar yayi tare da zabga mata harara zauna zama tai kamar zatai kuka dan inda kaya ajikinta batajin abincin yana shiga yadda ya kamata.

Zama tai badan taso ba cikin kwanciyar hankali yake cin abincin sa haka Jalila ta zage tana zabga loma tama manta da Allah yayi ajiyar su Mom awajan, Rufaida kamar ta hadiyi zuciya ganin sahibinta yana cin abinci tare da wata kucaka ba ita ba sakejin tsanar Jalila tai acikin zuciyar ta dacin alwashi kala kala akanta.


Yana gamawa ya yagi tishu ya goge bakin sa tsam ya mike daga dining din,Jalila har nishi takeyi tsabar yadda cikinta ya cika hannunta yaja suka fice daga maine parlo hannu Rufaida ta dora aka tafashe da kuka Mom kuwa aiji take kamar zata amayo da zuciyarta,har turiri zuciyar ta take tsabar bacin rai da bakin ciki.


Shikenan na shige su wannan matsiyaciyar zai hada hannun sa da nata Mom na yadda bakya kaunata tuntuni kingaza samomin abunda nake so nake kauna alkawari nawa kikai min amma haryanzu kin kasa cikawa kuka take bilhakki wani azababban kishin Jalilah takeji da bata nasan me suke ba.


Suna fita ya cika mata hannu dama dan ya kunna su Rufaida ne ya bakanta musu rai yanxu ya tabbatar yagama kunna su babbakewa kadai ya rage suyi,lambu ya nufa dan sosai sassanyar Iska take kadawa me matukar dadi da sanya nishadi,daya daga cikin kujerun wajan yaje ya zauna Lumshe idanun sa yayi yanayin yanai masa matukar dadi kamar bacci ya dauke shi haka yakeji.


Swimming pool ne yayi matukar burge Jalila bata taba zuwa wajanba ahankali take takawa kamar tana tsoron kar ruwan ya jata,ta saba da wanka arafin garin su shiga takeyi babu ruwansa koda mazane aciki suna wanka to itama fa afkawa takeyi tayi abunda yakaita tafito taitafiyarta.zama tai agefan ruwan ta zura kafafunta sosai sanyin ruwan ke ratsata har Lumshe idanu take da hannu take dibar ruwan tana wasa dashi.


Ai wllh sainayi wanka taya za'ai ma nazo har wannan rafin me shegen kyau natashi banyi ninkaya aciki kinsa ba mikewa tsaye tai saidata daddage ta buga tsalle sai gata tinjim ta fada ciki,a yanda Jalila ta zata abin ba haka yake ba rafin garin su ba wani rafi bane wannan zurfinsa yafi na garin su facal facal tafara yi ga kayan jikinta sun taimaka wajan sakeyin kasa gaba daya ta gigice tuni tashide ruwa ta hanci ta baki ta kunne duk shiga yake.

               Mrs Baba Bello Abubakar

             .........✍️✍️✍️✍️

No comments