Recent Updates

Uncle J 27

 


By Kulsoom Ismail Idris

Page 27


Aini ko kura haka taganni ta kyaleni dan baka sanni sanda nake kauye bane nakusa cirewa dije hanci sanda muka taba fada dakyar aka karbeta daga hannuna saboda inna fusata bani dakyau kullum amakarantar allo duk wanda ya tsokanan banayi masa ta dadi.


Nabar miki wannann kayan amma da shadi gyara zaman ta tayi sharadin me kafada ko menene yanzu zanyi maka ni wllh ko wankin kayan kane ma nadauki nauyin yinsa daka cire kayanka zan wanke,bana bukata kirike wankinki sharadina dole kidinga wanka kullum brush kullum gyaran daki karki yadda na leka dakinki naganshi kaca kaca hakan yana nufin nakwace duka kayana,Indai wannan ne me sauki ne indai zan dingasa kayan nan nazama yar gayu.


Kingama cika sharadi sai zuwa makarnata zan saki a school saboda na lura kanki ya gama dafewa da miyar kuka kamar ke wannan yar yarinyar ma za akawo ki aiki,ina ne garinku shiru tayi Allah ya kiyaye na fadama garimmu,am aini bamu da gari kaganni daga sama na fado nikaina bansan inane garimmu ba,nizaki rainawa hankali haba dan India kasan bazan yima karyaba har Zuciyata maganar nan take,hmm kawai yace dan yagane bazata fada bane dan karya mayar da ita.


Tashi kifatar min adakin to,mikewa tai ta debi kayanta hartakai bakin kofa kee juyowa tai sannan wannan tsummokaran kayan kisasu a shara karna sake ganinki dasu suna cikin sharadi suma,dan jim tayi kayan nawa danake wankan Juma'ar zan wullar wannan albazazzaranci ne,bazaki yar ba kenan aah nidin banza zanyar mana dama wai tunatar dakai nayi to kirike tunatar warki kezatayiwa amfani har mahaukatan kayan kwalliyar nan kiyi waje dasu.


Kamar kadangaruwa ta girgirza kai anya zata iya bin wadannan dokokin meyasa dan India zai gindaya mata wannan sharudan masu matukar wahala wanka kullum tab,dakin Ammah ta wuce bakinta kamar zai yake sai jan ledar take akasa Ammah zokiga kayana zan dinga daukar wanka dan India ya bani,amma dake kan dadduma ta zubawa ledar ido,kai Jalila dagaske kike duk nakine eh Ammah nawane bece harda ke ba Murmushi kawai Ammah tai Jalila danja.


To zomuga kayan zazzagewa tai kayan sunkai kala goma shabiyar kowannen su masu matukar tsadane inyeee Jalilan Amma ta shigo gari duk yan kantine babu kayan hausawa daga riga da wando sai riga da sket sai doguwar riga pants da vest sai kayan kwalliya da chocolate duk ya hado mata aifa Jalila dan dadi kamar zata ciji kunnan ta sai tsalle take tana murna Ammah nai mata dariya.


To aiba tsallan ba yanzu wanka ya zame miki wajibi kullum ba fashi,bama saikin fadan ba ninasan sauran in banyi ba bani basa kayannan haka ya fadamin Fuska amarairaice tafadi haka, Ammah ki taimaka kice yabarni ko kwana uku uku ne na dingayi meyasa ke baki fada masaba aini karyaga kamar na rainashi ne au nice marainiyar wayonki kenan da kike fadamin Allah ya baki hakuri Ammah ni banfada ba naraina babar dan India aida nacika butulu kinsan ni duk kankantar Alkhairi bana manta shi haka sharri shima bana mantawa saina mai da martani.


Allah ya shirye ki to ai matukar kina son cin ribar zaman duniya sai kin koyi hakuri,bana son ci Ammah matukar za aimin ban rama ba aidama ni ribar lahira nake so naci nashiga Aljannah nasha dadi na ganin bata da niyyar gajiya Ammah tace naji dauki kayan ki jera a wardrobe dinki kinkima tayi ta fice ranta fes,ko tinanin su Innah batayi hankalinta kwance take cin dadinta ita kadai amma wataran tana dan tunawa dasu kadan ga ciwon da jikinta ke mata narashin damban da batayi watanni masu yawa.


Tana shirya kayanta tana wakokin ta na kauye saida tagama tsaf samnan ta debi tsofaffin kayanta ta fita dasu tanaji tana gani ta zubar dasu har kuka sai datai to ya zatayi tunda tanasan sababbin kayan da dan India ya siyo mata dole ta hakura tabarsu ashara daki takoma anayin sallar isha'i ta bingire awajan tahau bacci.

          Mrs Baba Bello Abubakar

No comments