Recent Updates

Uncle J 26

 


By Kulsoom Ismail Idris

Page 26


Sai da yakashe motar akallah yakai 5mnt kanya bude ya fito wow wasu yan mata dake fito suka fada kai amma guy dinnan ya hadu ya bala'in birgeni,hade ransa yakara yi dan yatsani kallo a rayuwar sa,budewa Jalila yayi ahankali ta fito sai zare idanu take sai

Lokacin ya kalli kafarta ko takalmi babu harara ya maka mata kazama kawai wuce muje,to ina zanje bakaine kasan hanyar ba salan haka kawai naje na bata asace ni ganin zata mata mai lokaci yaja hannunta suka shiga.


Zo kuga Jalila kamar wata shashasha haka ta bude baki tana kalle kalle kamar sabon kamu haka ta koma Jalal ba karamin dana sanin zuwa da ita yayi ba duk Inda suka wuce kallon su akeyi ana dariyar kauyan cin Jalila itako ko ajikinta,kaya yake diba kamar besan zafin kudadan ba Jalila ke tura basket din daya bata saida ya cikashi taf da kaya suka je wajan biya,awasu manyan ledoji aka zubamai kayan har mota suka kai masa kayan.


Ganin Jalila batada niyyar shiga motar ya jata ya turata ciki,bata rai tayi amma wllh kaidai akwai marowa ci yanzu muje wajannan harmu fito amma baka siyamin ko dan tamatsitsin da nagani awata leda ba,banza yayi da ita yanajinta tanata mita,ko kimin shiru kona maidaki kauye yanzunnan shiru tai alabaka hakuri kwafa yayi kimaci gaba,kai tsaye wani salon ya wuce da ita.


Waya yadaga ya daddanna wasu Numbobi wata matace tafito babba ce da alama itace me wajan cikin girmamawa suka gaisa,kallon Jalila tai da murmushi a face dinta ma sha Allah ita ce kanwar taka dan murmuwasa kawai yayi,haka yace miki ni kanwar sace to karya yake babu abunda muka hada ni aiki nake agidan su haka kawai dan mugunta kaje kayo wata tsokanar azo ahuce akaina bazata yiwuba make mata baki yayi cikin takaicin yarfin da tai masa agaban madam Zarah.


Sosai taji Yarinyar ta birgeta,kina cewa karya yake ai yagirmeki bana son rashin kunya kuma dan yace ke kanwar sace ai girmamawa ce kobakisan in anji ke yar aikin Gidan su bace za adinga tsokanarki ko kin girma kinzama yammata anaganin kinci kwalliya za ace kun ganta yar kauye tasha ruwan binni ta waye,bata fuska tai toko yanzu aiba wanda zaice daga kauye nafito,injiwa ya fada miki matukar baki gyara bakinki ba kowa ma zai gane.


Madam ki kyaleta kawai zamu tafi tunda batasan mutunci ba ita zan maidake yadda na daukoki, a'ah Jalal ai baza ai hakaba tunda kayi nufin alkhairi karka juya baya,fito kekuma me shegen bakin rashin kunya,kama hannun ta tai suka shige hadaddan wajene na gyaran jiki gyaran gashi zaunar da ita tai akan kujera oya bude kan to Nanfa akeyin ta bata fuskatai ni banda gashi andade dayimin aski tun na askin jarirai da akaimin haryanxu be fito ba.


Uhm kawai Madam tace zare dan kwalin data dankwafa aka tai tun kafin ataba kan Jalila tafara Kuka banza tai mata tsabar dadewa tsagar kitson ma ta hade ba aganin ta takosha azaba madam kuma tasha zami ga wata kura data dinga tashi akan ankai awa 1:30 ana fama dakannan kafin ya fara dawowa hayyacinsa tsaf ta gyara matashi sai ga gashin Jalila ya sauko har wajan kafadarta ashe dama tanada gashi rashin gyara ne yasa gashin ya cukurkude ya dankare awaje daya.


     Toilet ta jata tas tai mata wanka da brush anyiwa bakinnan kusan safi biyar kafin ya fara dan washewa danya dade da dafewa tun tuni,fita tai mintuna kadan ta dawo da kaya ahannun ta,wasu riga da wando ne masu azabar kyau help gawn ce iya cinya sai jins sai wata bandana da akasa acikin kayan tsaf ta sakawa Jalila kayan ita kanta madam ba karamin kyau Jalila tai mata ba Jalila kuwa sai jujjuyawa take farin ciki kamar tayi me sai kallon kanta takeyi kamar ba ita ba 


     Waya siyamin kayannan masu kyau wanda kika gama yiwa rashin kunya mana waro idanu tai wai kina nufin dan Indiya ne ya siyamin kayannan dariya tayi wane dan India ni Fatima wanda mukazo tare mana lallai kina da shirme to shine ya siya miki.

Marairai ce fuska tai Allah sarki ashe yanada kirki haka to daga yau yama babban abokina ba cuta ba cutar wa kome zaimin zan hakura tunda ya siyamin wadannan kayan dadai yafi miki,muje kayan da ta cire mata take kokarin dauka me zaki dasu gida zan tafi dasu ajiye zubda su zanyi kinyi gaba amma kina kokarin maida kanki baya,lallai ma wato matar nan sotake na barmata kayan ta samu takaiwa yarta.


Jan hannunta tai ganin ta gaddame saita dauki wadannan yamutsatstsun kayan,yana wajan duk wannan uwar dadewa da sukai sai jan tsaki yakeyi tunda suka fito ya zuba mata idanu anya Yarinyar nan ce kuwa tayi wani irin kyau saiyaga kamar ma ta kara haske kallonta yake daga sama har kasa dariya ce tazo masa ya kunshe abarsa tana tsaye kamar 1 suna tafe suna magana da Madam kome take gaya mata kuma oho.


Gaba ta bude ta sakata har zaiyi magana yayi shiru to Jalal angama sai Gani na biyu amma zaka kawon ita mudinga gaisawa ko watakila aah kadai dunga kawon ita nifa ita ai munzama kawaye bakiyi sa'ar kawaba kuwa,sallama sukai yaja motar Yayi gaba,kallon sa tai dan India ashe haka kake da mutunci daga yau mudena fada munzama kawaye hararar ta yayi ke ni macece to aikaima naga kama da matan kake yi nidakai babu wani ban banci.


Banza yayi da ita dan ya lura so take tamai dashi wani bican,Hon ya danna megadi ya wangale masa kofa kamar bakin Jalila zai yage dan farin ciki tadawo gidan jindadi kamar yadda ta samai suna, Ammah na tsaye tana kaikawo a parlo dan tuni su Rufaida sun fesa mata Jalal yatafi maida Jalila kauye takira shi wayar sa akshe shiyasa takasa zaune ta kasa tsaye sotake taji Inda yakai musu yarinya.


Ta widow ta leko Jalal ne ya fara fitowa daga motar saiwata kyakykyawar yarinya data ga tafito dafe kirji Amma tai tana jiran taga Jalila tafito amma shiru babu ita babu alamarta to ita waccan din dayaje ya kwakuso wacece tayi taf jira kawai take ya shigo ta sauke mai abunda yake damunta saiyaje ya dauko Jalila duk ma inda ya kaita.


Hartayi gaba ke nine dan dakonki dawo kidebe kayannan dawowa tai da baya dan yanxu tsakanin su fa biyayya ce injita dauka tayi sun mata nauyi kallon sa tayi kamar zatai Kuka dan India karufamin asiri kadauki daya nima na dauki daya,ganin da gaske bazata iya ba rankwashi ya zuba mata sannan ya dauka,shine agaba Jalila na bayansa.


Gidan ubanwa akace kadauki Jalila kakaita wllh tun kafin raina ya baci kako ma kadauko min yarinya ta nagaya ma,tsaywa yayi yana kallon Amma da idanunta ya rufe kawai fada take zazzagawa ganin yayi mata shiru abun ya sake kular da ita ba magana naje maka ba,jitai anrungumeta ta baya Ammah kin ganni fa da sauri Ammah ta juyo kara bude ido tai akan Jalilah kamar ba itaba kallonta take Daga sama har kasa jujjuyawa tai ya kika ganni Ammah.


Baki sake Ammah ke kallonta anya Jalila ce wannan kuwa gashinta ta kalla da yasha gyara harwani walwali yakeyi Jalilah kece kuwa nice mana Ammah kinga nazamo yar gayu ko dan India ne yasiyamin kayan nann na jikina har wanka fa akaimin Ammah bakiga gashina ba ya kara tsayi awani inji aka sakani.


Kallon Jalal tai tuni fuskar Ammah ta washe bakinta yaki rufuwa sake kallon Jalilah take kamar ba itaba Allah Yayi maka Albarka Jalal,dan Murmusawa yayi arayuwar sa yanaso  yaga ya farantawa Ammah rai hakan yana matukar sanyashi nishadi part dinsa ya wuce danya watsa ruwa yayi alwalar magari ba.


Hannun ta Ammah takama kai Jalila kinga yadda kikayi yanzu ke bakiji dadin jikinki bama amma aita fama dake kiyi tsafta kikiyi yanzu dakikai tsaftar nan bakiga yadda kika zama budurwa ba,dariya tasa ALLAH Ammah sosai kuwa matukar kina wanka kullum to naman ki zai kara yawa kullum zakita cin nama babu yankewa amma fa in kina tsafta.


Zandingayi Ammah ai tunfarko kece bakimin zancan nama ba da babu yadda za'ai nabar wannan dadin ya wuce ni to koke fa,banaje nai sallah Ammah muje nima yi zanyi ledojin ta dauka sai nishi take to kawo na tayaki mana àah Ammah kayan amanane ba atabawa to aishikenan saikije ki karata kya hau dasu da wahala kuwa tunda bakisan abun arziki ba.


Dakinta ta shiga da kayan kara kallon kanta tai saitaga wannan kwalliyar bata dace da kinba tayi kaca kaca dashi dole nema ta gyarashi ganin baai kiran sallah ba zagewa tai ta gyara dakin fes sai kullin kayanta da yake ajiye akasa,Alwala ta daura tana idar da sallah ta ciccibi kayan tayi dakin Jalal yana bedroom dinsa zaune akan dadduma daya idar da sallah.


Har gabansa ta ajiye tana ta uban nishi,zama tai kawata ga kayanka hararar ta yayi bazaki daina kirana mace ba ko,to me zan cema bakisan sunana ba kenan nasani mana ainaga sunan mu iri daya ne kaima ba mamaki macene shiyasa aka saka maka,ke ya isheni meya kawo ki kayanka na kawo ma kayan matan zan saka da kika kawon kallon sa take cikin rashin fahimta kayan kine kine kita sawa bani da hadi dasu.


Kuri tai ta zuba masa idanu nuna kanta tayi duk nawane nikadai gyada mata kai yayi dan gaba daya ta dameshi da surutu,gani yayi kawai Jalila ta fashe da Kuka abun ba karamin daure masa kai yayi ba,wllh bansan haka kake da imani da Tausayi ba sai yau dana san haka kake da tun farko ban takaleka fadaba ni yanzu kota kaina zaka dinga bi bazan ji haushi ba,dagaske fa Jalila Kuka take kashirban gaskiya wannan yarinyar tanada damuwa a kwakwalwarta.


Kinga ya isa haka kawai bazakizo kaisani agababa kinamin Kuka kamar wadda na doka to ai kukan farin ciki nake kasan akwai kukan farin ciki dana bakin ciki yanzu da kukan bakin ciki nake da yanzu nafara ya kushinka da cizonka amma da yake kukan Farin ciki nake bagani azaune ba,sabida ke kura ce ko dole kihau cizo da ya kushi.

             Mrs Baba Bello Abubakar

No comments