Recent Updates

Uncle J 24

 


Page 24


Dad dama wai nace mezai hana a hada rufaida da Jalal, zamansa ya gyara mekike nufi da fadin hakan Saratu, fari tai da idanu,nufina tunda  gida be koshi ba ai ba akaiwa dawa ba tunda yaran nan

ALHAMDULILLAH duk suna da hankali sun san abunda ya kamata zasu hada kansu shida yar uwar sa babu mejin kansu haka kawai Allah ya doramun kaunar Jalal kamar ni nahaifeshi haka nakeji shiyasa nake son hada zuri'a dashi.


Sai data gama tsaf Dad ya kalle ta kina nufin wai nahada dana Aure da yarinyar da tagama lalacewa ko angaya miki bana sane da dukkan abunda sukeyi agari anata zagina dafadin banyiwa yarana tarbiyya ba yawon club inane basa zuwa sai haka kawai nadauki tsarkakakken dana na aurawa wadda tagama yawon kwararo to tun wuri Saratu ki farka daga Mummunan baccin da kika fara ni Ma'aruf ba haka nake ba bana tilas tawa dana abunda baya ra ayinsa.


Kuma inamai jadda da miki ki jawa yaranki kunne na soke fitar dare ba agida naba indai zasu fita to saidai su hada kayan su su kona gidan uban su baza su gogan bakin fenti ba ke bama suba harke zaku iya tafiya tare karna sakejin makaman ciyar maganar nan a bakinki inba hakaba rankine zaiyi mummunan baci,bige babbar rigar sa yayi yabar Mom kamar an dasata.


Kambabakeran Uba harni zai kalli tsabar idanuna ya gayawa haka to boka yaudarata yayi ko maganinne be faracin Dad ba infa ran Mom yayi dubu toya baci dakyar take jan Numfashi yayan natane tambadaddu gantalallu zesan yayi da yar halak ita tasan mezatayi wllh saiya gane kuransa saiya gane bashi da wayo saita tabbatar ta dasa masa bakin cikin da zaikai shi kushewar sa badai da dan yake takama ba zatagani ai muzuba ni dakai shege ka fasa.


Rai bace Dad yabar part din gaba daya kai tsaye part din Ammah ya wuce har wani huci yakeyi saboda bacin rai dannasa guda daya tilo zai hada Auran sa da marasa tarbiyya ko ta dauka baida labarin inda ta samo yaran zai hada zuri'a da kazan taccen ahali shi saiyanzu ma yake godewa Allah dayasa be haihu tare da Sarah ba baya fatan hakan ko kadan Jalal ya ishesa fatansa Allah ya nuna masa Auran sa.


Ammah ce tashigo jiki asanyaye ganin yadda Dad din ya fito afusace ya razanata dan sam shi ba Mutum ne meson hayaniya ba kokadan kullum Fuskar sa dauke take da fara'a babban bacin rai kesa har agane akan fuskar sa.

Fridge tawuce ta dauko masa ruwa me sanyi glass cup ta dauko tsiyaya masa tai ta mika masa dan yaji sanyi aransa karba yayi dan yana bukatar hakan dama saida yasha sosai nutsuwa tazo masa dan Zuciyar sa ta lafa matuka gaya, Ammah ya kalla data zubamai ido cikin damuwa murmushi ya sakar mata Allah ya yimiki albarka ameen Dad.


Dan Allah Dady kadaina saka damuwa aranka duk da bansan abunda ya bata maka raiba ina mai baka hakuri mijina kai kadaine farin cikina inka shiga wani hali bansan yadda zanyi da kaina ba,kalaman kauna taci gaba dayiwa Dad kallon ta yake cikin tsananin kauna soyayyar ta na kara dulmiya a cikin Zuciyar sa yana matukar san Ammah macece tagari yana Alfahari da ita akoda yaushe.


Madallah da samunki matsayi matata Madallah da samunki mar'atussaliha Madallah da samunki ma'abociyar kwarjini da kamala Allah yayi miki albarka Uwar Gida sarautar mata, murmushi kawai take sake ita kanta tasan tayi sa'ar Miji me sonta da kaunar ta kokadan bata nemi sanin abinda akai masaba saboda daga part din kishiyar ta yafito ba hurumin ta bane shiga abinda babu ruwanta.


Hirar su suka ci gaba dayi cikin Nishadi da kaunar juna tuni ta mantar dashi bacin ran da Mom ta dasa masa.Da sallama ya shiga dakin Ammah dan murmushi ya saki akullum iyayan nasa basa tsufa koyaushe cikin nuna Kulawa suke wa junan su suna matukar birgeshi yana fatan suyi irin wannan rayuwar da matar sa to wacece ma matar oho ya ayyana aran sa tuna bashi da wadda yake so har kawo wannan lokacin.


Son harka tashi kaima dai Dady yanzunne haryau tashi 11:30 fa ko baka gani rana ta bude tarwai asararin subahana,to Ammah ai dannaki ne so nake naga yayi kiba amma sai tsawo yake kamar taliya dariya suka sa gaba daya.Zama yayi akasan kafafun Good Morning Ammah Morning Habiby shafa kansa tai hole kana lafiya daiko I'm fine Ammah cike da kauna Dad yake kallon su.


Kifada masa yariga ya girma ya kamata ya kawon suruka hakanan Ammah ce ta rike haba yanzu Jalal din har nawa yake 28years fa saiya kai 30 zan masa Aure au kece ma zakiyi masa ehman nida kaima zan zabo masa matar har nayi masa tanadinta jira nake kawai tagirma,gimtse face yayi Ammah kice jaririya ce kawai dariya kawai tayi zaka ganta gaba kadan kaidai kazuba idanu murmushi kawai yayi dan Ammah badai zolaya ba zama take taita tsokanar sa babu ruwanta da wani shidan farine bazata jashi ajiki ba jan abunta takeyi.


Sunjima suna hira,fitowar ta daga daki kenan ta rangada sallama adakin Ammah tana yan tsalle tsallenta ganin ba Ammah ce kadai adakin ba tajuya da sauri zata fita yanzaki koma Jalila tsayawa tai naga Ammah bake kadai bace kuma kince nadaina zama inda maza suke,tagefen ido ya kalleta ji munafuka kamar jiya bata je dakinsa ba.

Ahto kin kyauta amman wannan ai Dad dinkine wajan Jalal dama na hanaki zuwa.

      Mrs Baba Bello Abubakar

No comments