Uncle J 23
Page 23
Kawaii ina dariya ne yadda naganka haka jiya sintir ashema kama da mata kakeyi ware idanun sa yayi akanta,eh kama da mata kake in kai ba mace bane meya hadaka da nono haba shiyasa kake abu irin na mata kana tafe kana yarfe hannu kamar wani dan daudu,kafarsa yasa ya tado ta Jalila saigata wanwar akasa jawota yayi har kusa da kafafunsa gaba daya kafafunsa ya dora
akanta duk yadda taso janye kafafun sa takasa tuni azaba tasata fashewa da kuka ko kallanta beba yaci gaba da aikinsa zai tabbatar mata dashidin ba mace bane saita gane kuranta adakinnan tunda itace ta kawo kanta.Tsabar mugunta irin ta Jalal hannayanta ya take yana sane har murza kafafun yakeyi akasa jitake kamar hannayanta zasu tsinke gashi da tafara kuka zai dalle mata baki da hannunsa azaba kan azaba tatsine masa yafi cikin kwando saida ya tabbatar da jikinta yayi Laushi sannan ya dagata gaba daya kasa tashi tai tsabar wahala sai matsar kwallah take lokacin ya gama aikinsa ya rufe laptop din.
Daka mata tsawa yayi batasan lokacin da tamike tsaye ba jikinta har rawa yake tsabar yadda ta tsorata hanyar kofa ya nuna mata har tuntube takeyi wajan fita tana gaba yana biye da ita harzata fita yagano Abincin data kawo masa keee!!! zonan da sauri ta dawo tana rarraba idanu zauna ki cinye wannan abunda kika kawo, murmushi ta saki cikin farin ciki dama cikinta ya fara kasa kamar zatai kuka take fadin na koshi.
Ko ki cinyeshi ko nazaneki yanzunnan wllh,harta zauna ta mike kallonta yayi alamun ina zataje dama wata doguwar rigace ajikinta dagata tai ta cire baki sake yake kallonta wannan yarinyar fa akwai damuwa a kwakwalwarta,daga ita sai pant ta zauna yayi cidin cidin da uwar dauda dankwalin kanta tacire tare da gyaran zama basket din ta janyo food flacks din ta bude Jallop ce aciki sai tashin kamshi takeyi Jalila har hadiyar yawu take.
Tunda tafara zabga wata uwar loma yake kallonta da tunanin zatace ta koshi amma ina shiru kake ji saidai Jalila ta cinye tas tea cup ta janyo saidata shanye ta bude ruwa ta kwankwada gaba daya kan Jalal ya daure aiyanzu shi kome za aimasa bazai iya cinye rabin abincinnan ba amman gashi wannan figaggiyar tacinye tas lallai,saidata gama tsaf tatashi tasa kayanta.
Kallon sa tai nagode dan India baka tabayimin abun arziki irin yauba tunda ka bani Abincin nan na cinye duk wasu lefuffukan ka sun goge saidai adora ana gaba amma na bayan nan dai babu su kaima ina so duk lefukan da naima ka yafemin kasan dai Mutuwa ake yi gwara ayafi juna,ni wllh yanzu har gyaran dakuma zandingayi maka dan India tsaninmu yanxu mutuncine da rukon amana.
Ko kallanta beba fitar min daga daki karna tashi na tattaka ki wllh,to sai anjima ni bana manta Alkhairi bana fita aini yau bazanyi fada dakai ba wllh tunda ka bani abunka nima nan gaba zan baka abuna,ke dallah fitarmin me kike dashi da zaki bani fitar min fita tai tana zabga mai Addu'a ALLAH ya saka a Aljannah dan India zanyima Addu'a kadawo namiji ba mace ba tashi yayi kamar zai biyo ta da gudu tafice zuciyarta fes dan India yabata abinci kuma harga Allah dagske ta yafemai har zuciyar ta.
Murmushine kawai ya subuce masa hakanan tasashi Nishadi,yadade azaune kafin ya tashi ya wuce bedroom sai da ya sake wanka sannan ya kwanta.
Washe gari tunda sassafe Jalila ta afka dakin Jalal da kayan shararta ahannu yanzu Jalila ta zama kwararriya wajan iya gyaran daki amma banda nata dakin zata Gyara na kowa banda nata, bedroom ta shige rike kugu tai lallaima bacci kake aiko zan janyoka kasa inna gyara na ciccibeka na mayar dakai,kodai bana barka ma karka tashi kamin jaraba, toilet dinsa ta shige saidata wanke shi tas.
Bedroom din ta fito ta gyara parlo ta wuce komai kal kal saidata goge har plasma ta goge komai sai walkiya yakeyi kayan ta fita dasu ta sauka kasa aikinta taci gaba dayi hankalinta kwance bata da wata sauran damuwa.
Tana gamawa ta koma dakinta hakanan taji tana so ta gyara nata dakin saidata dauke komai data hargitsa ta share ta shiga wanka Jalila dai yau tsafta ce tatashi,tana fitowa ta dauko kayanta cikas daya kayan duk sun kude dama basu da yawa haka dai ta samu tadan saka bata shafa komai a face dinta ba tai zamanta adaki.
Betashi ba sai wajan 11 yana kwance yana sharar bacci babu abinda ya dame shi,tunda ya tashi yaga alamun dakin ya canza ya kara fes fes toilet ya tashi ya shiga nan ma yasha mamaki komai qal tuninsa wanene ya shigo yamai wannan gyaran mekyau haka,saidaya gama duk abinda zaiyi ya fito parlo nan dimma ashare agoge zama yayi dan bayajin fita ko kadan plasma ya kunna ko kallon zai ragemai kadaici lumshe idanun sa yayi ya lula duniyar tunani kome yake tunanin oho.
Mrs Baba Bello Abubakar
No comments