Uncle J 22
By Kulsoom Ismail Idris
Page 22
Saida tagama aikinta tsaf sannan taje ta ludi tea da 🍞 dinta tun bata iya sha harta saba sosai take zagewa tasha abunta,zaman jiran fitowar Jalal tai taga yadda ya koma amma harta karaci zamanta befito ba tana zaman jiran ta bingire ta hau bacci,bata farka ba sai kusan azahar tatashi tana zabga uwar
hamma kamar batai baccin ba tashitai ta tafi dakinta alwala ta daura ta kabbara sallah.Tana idarwa tacire dukun kunannan hijab dinta da yake tsamin dauda yau Lambu take sha'awar zuwa babu kowa aharabar gidan kai tsaye bishiyar goba ta haye har Lumshe idanunta take saboda yadda tayi mata mugun dadi,hon aka danna da mugun karfi da gudu baba megadi ya wangale get din aguje ta shigo da motar kamar gidan tsohonta.
Mom ce ta fara fitowa sannan Rufaida daga Ganin su sunsha matukar gajiya,yan iska sai yanzu suka dawo tun safe ko gantalin me suka tafiyi oho harkar gabanta taci gaba dayi tsawon mintuna 30 taga Mom ta sake fitowa kai tsaye Lambu ta nufo sai waige waige take alamun bata da gaskiya,kura mata idanu Jalila tayi to kodai cutar jiyace bata sake taba can cikin lambun taga Mom ta kutsa kai duk abinda takeyi tana kallon ta.
Sun kuyawa Mom tayi ta tona rami wasu layoyi ta dauko a gefan zanin ta ta binne bazaka taba cewa antona rami awajan ba,tashitai tafice daga lambun tana sakin murmushin nasara yanzu saidai ta zuba ido taga yadda aikinta zai fara wakana,makira metaje ta binne aiko komene saina gani wllh saidata tabbatar Mom tabar wajan sannan ta sauko daidai inda taga tayi hakar ta tsugunna saidata tone tsaf saiga layoyin data binne tab lallai wannan matar bazataga Annabi ba wata binnewa wannan layar dagani dai wani zata hadawa mugunta aiko zaki sani wllh.
Maida kasar tayi ta binne waje daya ta samu ta zauna saidata farke layar nan tas wasu rubutu ne ajiki data kasa gane menene tabe baki tai ita tasani dama fitsari takeji tsugunnawa tai ta tsula fitsari akan layoyin malamin su ya gaya musu fitsari yana karya asiri tana da tabbacin shine wannan watsar da takaddun tayi ta kama gaban ta,tana shiga parlon ta tarar da Mom an kame akan kujera an cokala dauri Fuskar nan tata awashe da fara'a.
Uhm sannu da zuwa Mom ashe kun dawo amma ina kukaje naga kundade tun safe kamar masu yawan maula kinsan sune zakigansu sassafe sun nufi kwararo kwararo lungu da sako,kuma ni danaga kumdawo kafafunku busu busu kamar wadanda kukai tafiyar kasa,to tambayau ina ruwanki da inda mukaje meshegen kilibibin tsiya ko aikemmu kikayi kinga kishiga taitayinki Jalila wllh inna waiwayeki bazakiji ta dadi ba.
Wace irin waiwaya zakiyimin Mom badai fiddani zaki daga Gidannan ba kimin komene amma banda barin gidannan inanan ba inda zani dole ne na zauna na taimaki wanda suka taimakeni muddin rai kuwa bazan bar mutum ya cika mummunar kudirin sa, Kamar yadda kikace karna bari ki waiwayeni toni yanzu zan waiwayeki bazaki taba cika burin kiba saidai ki mutu da bakin ciki hassada ce zata kashe ki atsaye batare da kin farga ba.
Zumbur Mom ta mike ke nikike gayawa haka koni sa'ar wasanki ce wllh hawainiyar ki ta kiyayi ramata amma zakiga abunda zai biyo baya Fuuu tai gaba inga Alkhairi babu abunda zan gani ni Zuciyata babu mugunta acikinta fes take aha barin wajan tayi tana dariyar mugunta dan tasan tagama yiwa Mom illah zata zuba ido taga abunda take nufi da binne layoyin datai.
Har akazo dinnar babu Jalal ba dalilinsa yana dakinsa har wannan time din befito ba Ammah ce takai masa da rana ga daren ma befito ba duk Ammah da Dad sun damu matuka,waini ina Jalal Allah sarki haryanzu jikin nasane nidai ALLAH ya temakeni na warware kamar baniba kai jiya naga masifa ganin idona babu wanda ya tanka mata kowa da abunda ya dame shi,Ammah ce ta hadamai Abinci awani dan basket mekyau Jalilah ta kwallawa kira.
Gani Ammah yawwa ungo kikaiwa Jalal ki aje aparlo saiki fito kina jina eh Ammah daganan zanje daki nakwanta bacci nake ji ok hakan yayi kinyi sallah eh nayi Ammah tom ALLAH ya tashemu lafiya Ameen,harta juya mom tai tsagal aida kinba yan Uwansa sun kai mai haka kawai kyatura yar aiki ina matsayinta yakai tashiga part din Jalal.
Karba tai tatafi idanun su Mom kamar zai fado dan harara ita ko ko ajikiñta batama san sunayi ba,kamar yadda Ammah tace ta ajiye aparlo anan ta aje amma tsabar neman tsokana bedroom dinsa ta shige ya zaune laptop dinsa na kan cinyar sa da alama wani aiki yake me Muhimmanci gaba daya ya tattara hankalin sa waje daya.
Yaji shigowar mutum amma besan wanene ba dan gaba daya baya so abinda yakeyi ya tsaya da yinsa,saidata zo har kusa dashi tukunna tatsaya tana muzurai tsamin daudar da takeyi ne ya isar masa da sakon ko wacece,afusace ya dago yana harararta Mahaukaciyar ina ce zaki shigomin har bedroom kina tsamin dauda ko kala bata ce masa ba tana tsaye kamar andasata tana kallon sa shekewa tai da wata muguwar Dariyar cikin Mamaki yake Kallonta metakewa dariya haka.
Mrs Baba Bello Abubakar
.........✍️✍️✍️✍️
No comments