Recent Updates

Uncle J 2

 


[7/28, 9:35 AM] +234 903 511 7917: UNCLE J

Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

Page 2

Inna ce azaune ta zuba Uban tagumi gaba daya tayi zurfi acikin tunaninta gaba daya tunanin yadda Rayuwa ta juya musu takeyi

ada inhar tai mafarkin zata wuni da yunwa saita karyata balle harta kwana da ita jitai hawaye sun taho mata tunawa da adalin Mijinta dabai taba gajiyawa da ciyar da suba harma ya taimakawa wasu Allah y jikanka Malam tare da share hawayan ta.

Assalamu Alaikum wata murya tayi sallama Wa,alaikumussalam Inna ta amsa lale maraba shigo yau kece agari wllh nice Inna kallon gidan tayi komai abushe kayau kayau kaida gani dai kasan ana cikin wani hali kujera ta dauko mata tazauna gaisawa sukayi tayi mata gaisuwar Malam cikin jimami Inna take amsawa.

Ina Jalila cewar matar uhm kema Indo kinsan tana can wajan neman maganar data saba yaushe kika shigo garin wallahi yau nazo shine nace aikuwa sai nazo mun gaisa nayi miki gaisuwa,aiko Nagode ALLAH yabar zumunci Ameen bakomai wallahi.

Dama nace Inna ko zaki bada Jalila saimu koma birni tare dan uwar dakina tacemin kawarta tana cigiyar yar Aiki kuma matar bata da matsala tana da kirki sosai bata da wulakanta talaka shiru Inna tayi dan gaskya batason ta rabu da yarta a halin yanzu gashi ta fara girma fatanta kawai tasamu Miji tayi mata Aure nanda shekara daya ko biyu.

Banki ta taki ba Indo amma kinsan rawar kan Jalila banaso taje ta jawo mana magana gata bata da hakuri duka wanda yayi mata sai ta rama.

Murmushi tayi haba Inna ai kowa yasan yarinta kuma zan jamata kunne ahankali zakiga ta sauya namiki Alkawarin zan rike miki amanarta dan ko basu fadaba ta hango babu atare dasu to zanyi shawara da Gwaggo yaushe zaku tafi gobe in ALLAH ya kaimu zan tafi to abunda muka yanke da Gwaggo zan gaya miki saiki shigo da safe in Allah y kaimu to Inna ba Damuwa.

Har waje tarakata sannan ta dawo gidan Gwaggo ta fada tana zaune itama cikinta na kiran curoma dan bata taba haihuwa ba danginta duka sun kare dama Malam ke taimaka mata gashi ALLAH ya dauke shi saidai su bishi da Addu,a.

Shigo mana amma yanaga fuskarki kamar da damuwa aidole kiganni haka Gwaggo nan ta zayyane mata komai shiru Gwaggo tai na wani Lokaci kindai san halin Jalila kartaje ta jawo mana abunda yafi karfinm mu kuma ance yan birni basa daukar irin hakan karsu koreta daga aikin kotayo barnar daza'a daure mu gaba daya.

Nima abunda nake tunani kenan Jalila ce ta shigo kafarnan tai bududu taci dammara daga sama harkasa suke kallanta yanzu wannan aka kaita birni aiba asan barnar da zataiba jin an anbaci birni kawai Gwaggo jitai ta fado kanta tana ihun murna za akaita birni itadai Gwaggo wahala ta isheta dama gashi cikinta be cikaba tazo ta dira akan cinyarta ke dalla dagata sokike ki karyata wazai kaiki birnin kina wannan haukan.

Kuka ta fashe dashi nidai Inna akaini birni wallahi nadaina duka wata fitina zannutsu nidai akaini Kuka take harda su birgima kallonta kawai suke da sukaga abun nata bana kare bane Gwaggo tafara rarrashinta dayi mata Alkawarin za'a kaita matukar tagyara halayanta.


Cikin Murna tatashi tana washe bakinta wani tunani Gwaggo tayi dan tana matukar so taga Jalila ta kintsu tazama kamar kowacce mace me aji da kamunkai amma shashancin da take yayi yawa gashi ba wanda yataba zuwa yace yana santa dan tasha fashe kawunan samarin da suka furta mata suna santa daganan duk suka rabu da ita dan tsira da lafiyarsu.

Za'a kaiki birnin amma da sharadi dole ki gyara halayanki kidaina kazanta da rashin kunya kidaina zagin nagaba dake duk abunda zaki bawa babba kiduka har kasa aikin da akace ke zakiyi shi to kisani kullum kar atuna miki kisan aikinki matukar kin yadda da hakan za akaiki sannan banda ramuwa akan duk abunda akai miki kice zaki rama ban yadda ba tabbas sai andawo dake gida ammiki Aure.

Kuka tasa dan tatsani ace za'ayi mata Aure nidai Gwaggo kidai maganar nan dan Allah ni banason amin Auren to naji yanzu kitaso atsefe kannan to nanfa ake yinta tuni ta bata rai dan ta tsani ace za'ai mata tsifa yanzu za'a samu matsala aidama me hali baya fasa halinsa kina gani Gwaggo wannan tafiya bazata yiwuba zanje atsefemin tafada badan ranta yaso ba Innace ta fara tsifar da kyar aka gama tana gunjin Kuka wankema ta shi tai tas sai Uwar dauda kuwa tana da gashi sosai sai muguwar kazanta batason ko yaya ataba kan.

Wankama Inna da kanta ta wanketa tas saigata takara haske dan ita kanta taji iska na ratsata bakinnan gawayi aka daka aka wanke mata shi shima sai gashi ya fara dawowa hayya cinsa,yan kayanta masu kyau Inna ta hadata mata awani buhu da sabon silifar dinta ranar Inna kasa bacci tayi dan sosai takejin rabuwa da yar tata kwaya daya tilo sosai tayi mata Addu,a sai da Asuba bacci ya kwasheta cikin banncin ta jiyo Sallamar Indo tashitai taleka tare da cemata ta shigo.

Dakin fes dan Inna akwai tsafta dakinta tas ashare zauna mana Indo tashin Jalila tafarayi wadda tun asuba ake tashinta tayi sallah taki tashi bazaki tashiba saita tafi tabarki zaram ta tashi kamar wata saliha har kasa ta duka tana gaida ita da fara'a ta amsa dan taji dadin yadda ta girmama ta dan Akallah zata haifeta.

Alwala taje tayi tazo tai sallah tana idarwa ta dauki jaka Innace ta dubeta babu abunda ya dameta itadai burinta atafi kawai.

Kya bari kiyi kalaci aiko a'ah Inna zamuyi amota zan siya mata dama inna tafadane kawai amma ko kwayar gero basu dashi itama Indo fahimtar hakan yasa tace tabarshi maganar Albashinta zan dunga turowa kanina sai ya dinga kawo miki In sha Allah.

Bakomai Nagode dan ÀLLAH ki kulamin da ita amanarta nabaki tuni Inna tafara share hawaye haka Jalila duk taurin Zuciyar ta batason rabuwa da Innarta rungume ta tayi suka fashe da Kuka jitake kamar tace tafasa bada yarta amma tariga ta amsa babu yadda zatai kuma batason mutum yayi nufin yimata Alheri ta nuna bataso zata bisu da Addu,a.


           Mrs Baba Bello Abubakar.

No comments