Uncle J 17
Written and Narrated
By Kulsoom Ismail Idris
Page 17
Tsaki taja tare da ficewa daga room din gaba daya zuciyar ta fes tasoma ace har hakwara ya cire mata kwashewa tai da dariya tuna yadda bakin Rufaida zai koma babu hakora.
Dafe kansa yayi cikin karajin tsanar duk wani ahali na Mom Sarah sosai yake jin tsanar ta kai bama ita ba har wadanda suka shafeta shiko mezaiyi da yayanta ko mata sun kare gwara ya gama rayuwar sa haka,sauka yayi daga kan bed din gaba daya alwala ya dauro ya fito parlo ko kallan abincin data kawo mai beba tsanar da yayi mata ya shafi abincin.
Ahankali tafara bude idanun ta da sukai mata nauyi har lokacin kanta sarawa yakeyi zuciyar ta cike da kunci da bacin rai dan tana farkawa kirbar da Jalal yayi mata adazu da safe dashi ta farka fashewa tai da kukan takai ci da bakin ciki arayuwarta ba ataba yimata duka makamancin haka ba koda amafarki ne bare agaske katon gardi dashi yazage yaita laftar ta ta tabbata so yayi ya kasheta da kwanan ta ya kare dayanzu tana can kabari cikin karkashin kasa akwance dan naman data samu tana ci kullum ya cuceta tabige da zama a karkashin kasa.
Kwafatai dan bazata taba yadda ba wllh alkawarine saita kaishi gadon asibiti kamar yadda yayi niyyar kasheta ita kadai tasan abunda zatayi masa babu duka ba zagi amma zaiji ajikin sa sai ya gwammace betaba taba.
Motsawa tai da nufin tashi taji bayanta yayi wata muguwar amsawa ga inda akai mata allurar wani shegen zafi yake mata mamakin ta wane yazo yayi mata allura,shinshina jikinta tayi dayake tashin qamshin turare data rasa a inama tataba jinsa zumburo baki tai koma nawane ina ruwana.
Ammah ce tashigo dakin dama ita tazo dubawa kota tashi,ma sha Allah Jalila kin tashi kasa magana tayi tana karewa dakin kallo ta tabbatar wannan ba dakinta bane kodai dakin Ammah ne hakane ma dakin Ammah ne sai tashin kamshi yake hakanan taji dakin ya birgeta tana bala'in son kamshi amma itafa bazata iya zama ta gyara dakinta haka ba.
Ruko hannayanta tayi ta zaunar da ita yajikin naki da sauki ta amsa cikin muryar marasa lafiya Allah y kara sauki tashi kije kiyi brush ki dauro alwala to kawai tace,ahankali take tafiya harta shige binta da kallo Ammah tai tana girgiza kanta gaba daya abun be mata dadi ba yadda lokaci daya Jalila tasake wani ramewa sai idanu awaje kamar kazar dataga wukar yanka.
Karewa toilet din kallo tai yayi matukar burgeta komai yana ajiye a mahallinsa tabe tabe tafara yi batai abunda yakaita ba shiru Ammah taji ta kwallah mata kira Jalila ko kwanciya kikai a toilet din sai lokacin ta farga da abinda yakaita toilet din sauri tai tayi brush ta daura alwala tafita sai rarraba idanu take.
Hijab ta miko mata ta zumbula ko ganin ta ba ayi acikin sa Kabbara sallah tai saidata rama duka sallolin da ake binta sannan ta zauna ta zabga tagumi,fita Amma tai ta zubo mata Abinci dama Jalila yunwa ta isheta gyara zama tai duk yawan abincin nan sai data hallakeshi itafa Jalila komin cuta bata taba kasa cin Abinci saita ci tayi kat tukunna zata sake kwanciya,sosai Ammah take kallon ta tana mamakin cinta amma ba agani ajikinta kamar kazar mayu.
Ruwa ta miko mata ta kwankwada saigashi tana maida numfashin wahala wata nutsuwa taji tana shigarta kai yunwa madai masifa ce kwarin jikinta ta sakeji har wani gumine yake yanko mata,saidata tabbatar ta samu nutsuwa Ammah ta kalleta Jalila inna tambayaeki zaki gayamin tsakani da Allah jijjiga kai tayi alamar eh gyara zama Ammah tai meyakai ki dakin Jalal.
Bata fuska tai jin an ambaci sunan makiyinta amma tsokanata yayi shine naje daukar fansa baki bude Ammah ke kallonta meyayi miki haka,rannan daya maran agaban sufadi wace sufadi ni Ammah namanta sunan ta yawwa fidah Ammah ce tayi dariya fida rufaida dai ko eh ita,wace irin fansa kika je dauka akan na tafi da almakashina na yanka shegun kayansa daba sufi dari biyar biyar agarimmu ba shine ya kamani yamin wannan dukan kamar wadda tai cikin shige.
Duk yadda Ammah taso gintsewa saida tai dariya kayan nasane dari biyar biyar meyasa ke bakya yafiya ne arayuwar ki Jalila ai mace da hakuri aka santa kunya da kamewa amma ke babu ko daya atare dake mezai kaiki dakin Namiji kinsan ba kyau mace da Namiji sudinga zaman waje daya ko,kallon Ammah tai to amma kema banaga kina shiga dakin Dady ba kidade acan aishima Namiji ne.
Ya salam wace irin Yarinya ce wannan toni ai babba ce kuma muna tattaunawa akan wani aikine daza mudinga samun kudi muna siyan Kazar da kikeci kullum,washe baki Jalila tai wllh Ammah kici gaba da zuwa dan bana son wannan dadin ya wuce kidinga kwana acan ma dan afi samun kudin sosai,kunshe dariya Ammah tayi eh inda yiwuwar kwanan ma zanyi sanda akaga kudin siyayyar yayi kasa dole na zauna atattauna sosai.
Amma kedai haramunne na sake ganinki adakin Jalal kebama shiba kowane Namiji babu ruwanki dashi,to abinda tace kenan amma bataji zata kyale Jalal yanzuma ta fara zuwa dakin sa sai ta tabbatar yayi laushi taci nasara akansa sannan zata barshi.
Amma nasiha taci gaba dayiwa Jalila tana wucewa ta bayan kunnanta dan abu kadan zatace tadauka aciki shine yin wanka ko bayan kwana biyu ne wannan ne zata iya daurewa tayi amma bayanshi bataga abunda zata iya bari ba kamar yadda Ammah take fatan hakan ya kasance.
Mrs Baba Bello Abubakar
No comments