Recent Updates

Uncle J 15

 


Written and Narrated

By Kulsoom Ismail Idris

Page 15

Iya ya kalla dan Amma takasa magana har zuwa wannan Lokacin,wllh yallabai Jalila ce tun safe ake nemanta haryau ba aganta ba babu inda ba aduba ba amma babu ita babu dalilinta,rasss yaji gabansa yafadi shi bamà ya manta da wata Jalila ba karfa yar mutane ta mutu,Allah y bayyana ta abunda yace kenan ya tashi da sassarfa yake taka

matattakalar Ammah ce ta bishi da kallo cike da takaici 'yar mutane ta bata amma bazai tsaya asan yadda za'ai atafi nemanta ba zai tashi ya barsu awajan.


Da sassarfa ya karasa bedroom din key din toilat ya dauko tare da budewa tana ta kure waje daya tayi kuka harta gaji fuskarta ta bushe gaba daya babu alamun Numfashi tattare da ita tsugunnawa yayi cikin kyan kyami y fara tabata kara kunnan sa yayi daidai hancinta bayan ya kwance mata baki babu wani alamu daya ke nuna tana numfashi goshin sa ya dafe wannan yarinyar tana neman jawo masa matsala.


Kanta ya kalla ya kumbura yayi suntum buguwar datai adazu cak ya dagata ya fito da ita daga toilat din akan carpet ya shimfide ta dan bata isa tahau masa bed ba fridge yaje ya bude ruwa me shegen sanyi ya dauko murfin ya balle yana zuwa ya kwarara mata aka,sanyin ruwanne yayi matukar ratsa dukkan sassan jikinta Numfashi ta sauke cikin tsananin wahala da azabar ciwo.


Sam kasa motsawa tai dan ba karamar kirba Jalal yayi mata ba dukkan wasu kasusuwa dake jikinta be barsu ba saidaya tabbatar yayi musu mugun duka na gani kashe ni wasu zafafan hawaye ke kwaranya afuskarta gatsananin yunwar dake addabar yayan hanjinta.


Wannan azaune take saita dauki fansar abunda yayi mata saiya gwammace be taba sanin taba izayar daya gana mata saitayi masa fiye da abunda yayi mata,keeee tashi kibarmin daki kazama kawai me kwarkwata gobema kisa ke gigin shugomin daki saina kakkarya kasusuwanki saidai akwasheki amaidaki kauye kije can kikarata wannan somin tabi nai miki matukar bazaki fita daga harkata ba har lahira zan iya kaiki.


Tsawa ya sake daka mata zaki tashi ko saina sake ragar gazarki banza tayi masa dan ayanzu bata da lokacin sa ko yatsanta tanajin bazata iya motsawa ba balle tayi tunanin maida martani,amma matukar ita yar halak ce saita dauki fansa akan Jalal.


Kafarta ya kama feee yajata har kofar part din sa ya watsa ta waje kamar wata shara dan jiyake gaba daya dakin sa ya kauraye da tsamin dauda,yayi daidai da isowar Amma rass gabanta yayi mummunar faduwa ganin yadda Jalal ya watso Jalila waje cikin fitar hayyaci da alama bata cikin hayyacin ta hannun ta har rawa yake wajan tattaba jikin Jalila wanda tasake buguwa dif Numfashinta yasake daukewa.


Gaba daya Amma ta ciccibe ta tsabar kidima rasa inda zata nufa da Jalila tai bedroom dinta ta wuce da ita kan makeken bed dinta ta kwantar da ita gumi take sharewa tana mamakin meya hada Jalal da Jalila dama shine ya boyeta tome yayi mata,abinda take ayyanawa azuciyarta kenan,cikin sauri ta sunkuya tana sake kare mata kallo sket dinta taja kasa dole saita duba dan zuciyarta barazanar tsagewa take.


Pant din jikinta tai kasa dashi ajiyar zuciya ta sauke ganin ba abunda take zargi bane cikin tausayawa take kallon Jalila yadda gaba daya jikinta yayi rudu rudu kanta afashe haka bakinta afashe,to dama bakine arube ba brush yake samu ba dole duka daya ya fashe ya zama dole tadau mataki akan Jalal dan tabbas wataran kashe musu yarinya zaiyi.


Toilat ta fada saidata tara ruwa me dumi yadda tasan zaimata dadi sosai  futowa tai ta dauketa bayan ta karasa cire kayan jikin ta towel ta dauramata kafin tawuce toilat din da ita a bathtub ta tsullama ta,zafin ruwan ne yafara ratsata wata ajiyar zuciya take saukewa ajejjere ajiyar zuciya Ammah ta sauke ganin Numfashinta ya dawo gangar jikinta.


Sosai Amma ta zage ta wanke Jalila fes saidatai mata sabi biyar sabin farko gaba daya ita kanta kumfar baka ta zama saboda tsabar daudar data dankare ajikin Jalila ba dole ba matar da bata wanka saitai sati biyu batai wanka ba ita kanta Ammah mamaki take wai wace irin kazama ce Jalila dama bata wanka haka take zama da datti shiyasa data gifta su sai sunji wani shegen wari da hamami na dukan hancin su.

Fes ta wanketa tasake nadota a towel kan bed ta kwantar da ita tuni tafara rawar sanyi hakoranta har haduwa suke da junan su,har awannan lokacin bata daina kwararar da hawaye ba najin zafin abunda Jalal yayi mata tea Ammah ta hada mata da kyar tasamu tadan sha kadan tana gama sha ta amayar dashi sosai Amma ta shiga damuwa ganin yadda jikin Jalila yake sake rikicewa rigar sanyi ta dauko  ta jibga mata amma har Lokacin azabar sanyi take ji ga azababban ciwon kai daya rufto mata lokaci guda ga Kukan da takeyi kai abu dai goma da ashirin ya hadewa Amma.


Afusa ce ta fada dakin Jalal daya bararra je yana hutawa har bacci ya fara daukar sa wani mugun duka ta maka masa,a zabure ya mike ganin Amma tsaye akan sa tana huci kamar tarifeshi da duka haka takeji eh sannu Jalal nace sannu na gode da abunda kaimin ambani Amanar yarinya kasata adaki bansan uban da zakaci ajikinta ba in har sonta kake bazaka fada ba saika fara da sace ta.


Duk fa wani bacin rai Jalal jiyayi duniya har wani juya masa takeyi shine zai so wancan Abun mezaiyi da ita ya Aureta to yace ya Auri wa,badan Amma ce tai masa wannan furucin ba wllh ko wanene da saiya gane kuran sa,tashi muje ka duba yarinyar mutane tun kafin ta mutu kar ranka ya baci kaji dai abunda na gayama ka ,kamar zai fashe da kuka haka ya tashi wai Meyasa Amma takeyi masa haka box din sa ya dauka kamar zai hadiyi zuciya.

Yana gaba Amma na biye dashi kamar wadda take tsoron kar ya gudu oya maza kai mata taimakon gaggawa indai ba so kake kaga bacin raina ba,ajiye box din yayi harara yake makawa Jalila kamar idanun sa zasu fado oho ita batama san yanayi ba,tome akai kenan shine zaiyi jinyarta kome beci riba akanta ba kenan itace taci, wai tunanin me kake yi kayi abunda ya kawo ka mana,Allura ya fito da ita da srinji cike da mugunta ya tashi ya tsikara mata allurar duk da bata hayyacin ta saidata zabura dan aduniya ba abundata tsana sama da Allura yana zare allurar yafice Fuuu.


Jeka ala raka taki gona zama tai ta zabga tagumi da tunanin mezata ce da mutanan gidan aina taga Jalila adakin Jalal kai ina bazatai gangancin fadar hakan ba sarai tasan da Wadanda take tare zance dai toilet tashiga ta kasa budewa wannan kuwa akan wannan shawarar ta tsayar da zuciyarta.

Ahankali Zazzabin jikinta ya fara sauka saiga gumi ya fara karyo mata rigar sanyin ta cire mata wata vest ta dauko mata tatace data sakawa Jalila tazo iya cinyarta baccin wahala ne ya dauke Jalila cike da mafarkai marasa dadi.


Ajiyar zuciya Amma ta sauke tasamu nutsuwa sosai amma Mamakin ta me Jalila taje ta aikata masa haryayi mata irin wannan danyan hukuncin kwafatai zaka gane kuranka.

      Mrs Baba Bello Abubakar

No comments