Uncle J 10
By Kulsoom Ismail Idris
Page 10
Zagaye parlon suke tayi amma ba Jalal ba labarinsa daga karshe harabar gidan suka fice suna kwalla masa kira,Lambu suka shiga har zasu fito suka hango shi abayan wata bishiya cikin sauri suka karasa wajan sa
fuskarsa tai hadu tayi jajir bakaramar tsorata yayi da ganin Jalila ba sak kura haka tadawo,son Dad yafada tare da tsugunnawa agabansa bawan Allah tuni zazzabi ya rufe shi gaba daya besaba da wahala ba.Gaba daya Jalila tagoge mai hodar dake fuskarta da bakin kwallin data gambaza fararan kayansa sunyi cidin cidin hannunsa suka kamo da kyar ya mike yana tangadi,parlon suka shiga dakyar suka haura stairs dashi dakinsa suka bude suka shiga wani hadaddan dakine sai tashin kamshi yake komai blue ne acikin dakin ga wasu kwaikwaye da suke kawowa suna daukewa.
Bedroom suka wuce dashi cikin tsananin damuwa da halin da sukaga gudaliyar dan nasu kan bed suka kwantar dashi tare da jamasa blanket har kansa AC suka ragemai tukunna suka fice daga room din gaba daya,daidai lokacin Jalila ta bude kofar dakinta turus suka tsaya suna kallon kallo gaba daya Amma ta manta da wata Jalila daga sama har kasa take kallonta.
Dama itace tasa su wannnan Uban gudun Dad kuwa kallon Amma yake yana neman karin bayani,ina kika samo wannan yarinyar cike da takaici Amma ke kallon Jalila cikin hade fuska ta kalleta dazu kece kikafita harabar gidannan washe baki tai nice Amma bakiga yadda nacaba kwalliya ba harnaje na gano dan India amma ya gudu na rasa inda ya shiga.
Waro ido Dad yayi ya sake kallon Amma waini Rukayya ina kika samo wannan da alama tana da tabin hankali kika kawo mana ita gida,yar aikina ce Jalila maimaita sunan yayi aransa Jalila bece komai ba yayi gaba yabar Amma atsaye kamar ta maketa dan haushi,yanzu abunda kikai kin kyauta kenan Jalila kinsan sarai firgita Musulmi babban zunubine kinsan yadda kika firgita Al ummar gidannan kuwa.
Faritai da ido nimafa Amma wanka naci saboda bana so bakin da suka zo su rainani suyimin kallon yar kauye kankance idanu Amma tai to aigashi yanxu kallon Mahaukaciya ma sukai miki kifita daga idona Jalila kidaina firgita mutane yanxu ga Jalal can akwance babu Lafiya sanadiyyar arba da wannan mahaukaciyar kwalliyar da kikai.
Jalal wane ya satar mun suna haka wllh Amma yazama dole ma asiyo rago kodai ayankamin acanzan suna ko kuma shi ayanka masa acanza masa suna gaba Amma tai tabarta tsaye awajan dan ta lura intaci gaba da tsaiwa sai su zama daya.
Jalal be farka daga baccin wahala ba sai kusan karfe 4 na yamma ahankali ya bude idanun sa da sukai masa wani irin nauyi kansa har Lokacin sarawa yake Lumshe idanu yayi yasake budewa yadade azaune kafin ahankali ya sauko daga kan bed din kaynsa ya fara ragewa kafin ya fada toilet.
Bathtub yashiga tare da lushe idanun sa dumin ruwan yana ratsashi,Fuskar aljanar daya hadu dazu da ita kawai yake tunawa gaba daya tunin sa yakasa banbance mutum ce ko aljan jin yana neman bawa kwakwalwarsa wahala fara wankan sa yayi gaba daya jikinsa babu dadi.
Daure da bathroom ya fito yana yarfe gashin kansa tsayawa yayi gaban mirror applying cream yayi me matukar sanyin dadi kamar wani mace haka ya zauna yana shafe shefe jallabiya y saka tare da shimfida praying mat ya Kabbara sallah.
Ya jima azaune kafin y sake mikewa ahankali ya fara taking steps babu kowa a main parlo sai karar AC da plasma da take famanyi ita kadai kai tsaye dining y nufa kujera yaja ya zauna sam bakin sa babu dadi kamar wanda yadade yana cuta haka yakejin jikinsa.
Kwas kwas yafara jin karar tafiya alamar za ashigo parlon Rufaida ce sanye da wasu riga da sket sun bala,in matseta ajiyar Zuciya ta sauke hango shi datai shikadai sake gyara tafiyarta tai tana karairaya tare da yarfe hannuwa sarai yaga tahowarta amma yayi kamar be ganta ba,hade rai yayi kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa.
Hi yaya Jalal kamar ta ta watsa masa ruwan zafi haka yaji dan Aduniya ba wadanda ya tsana sama da Rufaida da Salima kai har Uwar suma ya tsane ta basu ba,karya wuyatai cike da kiss banai serving dinka daga mata hannu yayi am fine kamar zatai kuka haka takoma ta zauna wai meyasa yaya Jalal yakeyi mata haka gashi ita kuma aduniya babu wanda take so da kauna sama dashi dole ne saita same shi kota halin kaka.
Tsam yatashi ya barmata dining din kan sofa yaje ya lafe duk da yana jin yunwa ya gwammace ya hakura dacin abincin da dai Rufaida ta zuba mai.
Sosai ranta ya sake baci da wannan wulakanci na Jalal kwafa tai tana niyar tashi Jalila ta sauko da gudu kamar ankorota tana tsalle tsalle da wake wake hango Rufaida datayi yasata nufar wajan da sauri,Allah ya kamaki bayan iskanci kuma har sata kukeyi ko kunya ki shigowa mutane hargida kiyi musu sata wannan aiba adalci bane.
Fisabilillahi tunda dai Amma tana sammuku abincin basai ku hakura ba kuje can ku karata da iskancin ku dan Allah kitashi karkisa Amma ta gogi arnan cinku,kura mata idanu kawai Rufaida tayi cike da bacin rai wani wawan mari ta kawo mata jikake tas sosai marin yashigi Jalila amma bakinta be mutuba ni kika mara aiko wllh kin matar wa kanki masifa.
Sai data shammaci Rufaida abazata tai wata irin sun kuyawa takwa so gaba daya kafafun Rufaida sai gata akasa dim kanta ya daki dining table wata kara tasaka tare da fashewa da kukan azaba duk Abinda sukeyi Jalal yana kallon su tunanin sa wace aljanar yarinya ce wannan agidan su kwalliyar fuskarta ya kallah ras yaji gabansa ya fadi kardai itace ta razana shi dazu tabbas itace aiko zakici Ubanki.
Mrs Baba Bello ABUBAKAR
.......✍️✍️✍️✍️✍️
No comments