Uncle J 1
[7/28, 9:35 AM] +234 903 511 7917: UNCLE J
STORY AND WRITING
Kulsoom Ismail Idris
Mrs Baba Bello Abubakar
Page 1
Acikin Jahar Jigawa karamar hukumar rimgim wani dan karamin kauye ne me suna tsoma.
Wata yarinya na hango tana kyalla Uban gudu kamar fijo wata tsohuwa na biye da ita abaya tana sababi da tsine tsine amma tsabar tsokana tana Gudun tana juyowa tanaiwa tsohuwar dariya da gwalo,abun da yasake fusata tsohuwar kenan.
Wani gida tafada matsakaici dan baza'a kirashi babba ba,babu sallama haka ta afka.
Tana zaune akan wata kujera yar tsuguno tan kade takeyi acikin kwarya bum taji anyi gaba da garin sai ga garin ya tar watse akasa har Fuskarta saida tasa mu rabonta tai futu futu ko tsayawa batai ba ta afka daki turo kofar gidan akai wannan tsohuwar ce ta shigo ina tsinanniyar yarinyar nan take wllh yau sai naga wanda zai kwaceta agarinnan sainayi mata tsinannan duka Inna da tai sakare tana kallan Iya me kayan yara tama kasan magana gaba daya bacin ranta akan garin da yake kasane itako Iya kumfar baki take bata fasaba wani kara Inna ta hango sun kuyawa tai tadauke shi dakin da taga tashiga nan tabita tai shame shame agado tana tikar dariya saboda tuna muguntar da suka yiwa Iya ita dasu Talatuwa jin saukar karan kawai tayi a kafafunta aiko kara ta kwalla tana wayyo na shiga Uku Inna zata kasheni Gwaggo zoki ceceni wayyo ni naga takaina.
Gwaggo dake cikin bacci afirgice ta fado daga kan dan gadonta nakarfe ko riga babu haka ta fado gidan dan katangar su daya kome za'ai tana jiyowa Inna ko ta zage Iya karfinta take kirbarta da kyar gwaggo ta kwace ta duk kukan nan da take idanunta kamas babu alamun hawaye kawai kukan take da alama ma kukan Iya shege takeyi haba Hauwa kasheta zakiyi tsabar takaici Inna kasa magana tayi ga Iya dake tsakar gida tana jiran tafito ta biyata barnar da tayi mata.
Yanzu Gwaggo bakiga barnar da yarinyar nan tayi mana ba dan garin danake tankade wa zamiyi tuwo dashi gashican ta tambadar Gwaggo ce tadau salati dan dan baccin daya kwasheta baccin yunwane ba karamar yunwa ce ta addabeta ba saurin tureta tayi daga jikinta amma kedai bakiji dadin halinkiba Jalila yanzu saboda Allah dan abunda zamusa abakin salati shikika yasar akasa kyaci Ubanki kuwa zanga abunda zakici kema kuma fitinar da kikayo kece zaki kasheta da kanki tisa keyarta tai zuwa tsakar gidan da haryau Iya ke tsaye rike da kugu Jalila ce ta kalleta tare da murguda mata baki bam Inna ta buge bakin ina rabaki da rashin kunya kina cigaba waike wace irin yarinya ce da Allah ya yiki ba kyajin magana saiki biyata barnar da kikayo mata.
Ainaga bani kadai nayi mata ba har dasu Talatuwa to aikece shugabar su munafukar Yarinya me suffar ifiritai ni wallahi nafara tunanin anya ke mutum cema kuwa cewar Iya miko mata hannu tayi bani kayana kememe taki bada kayan saida Inna ta daka mata tsawa sosai take jin tsoron Inna dan batai mata da wasa kwance bakin zaninta tayi dayayi cidin cidin da dauda su tsami gayene kantu gullisuwa garin bididis duk suka kwaso mata kamar jira take kuwa ta wafci kayanta gayyar tsiya da kinci kayannan kinciwa kanki masifa kuwa fuuuu tafita sukabita da kallo zuciyar Jalila cike da takaici amma takudurta aranta saitaci kayannan kota halin kaka.
Nuna mata garin data zubar akasa tayi bakiga barnan da kikaiba kenan sai Lokacin ma ta lura zare idanu tayi dan yunwa take ji bata tsaya wata wata ba kuka tafashe dashi baki bude su Inna ke kallonta ni wllh Inna yunwa nakeji nidai kibani abinci wayyo cikina abinci zanci banza sukai da ita dama Gwaggo ce take kulata in tana tabararta harta lallasheta itama yau tabata haushi dan jitake kamar ta rufeta da duka zata ja musu kwanan yunwa dan wannan garin shi suke dashi daka da waje.
Saidata gama kukanta mara dalili tatashi tawanke fuska da kafa jiki sai tashin tsami yake ahaka ta dauko mai ta mummulka jar hoda tadauko badani jaka ta ambula afuska aka dauki kwalli akaja jagira dige dige tas ta dige Fuskarta jam baki ja tadauko akuya ta dumbuli dusa shita shafa bakinnan jajawur hakora ta washe bayan takalli madubin hannunta bakaramin kyau taga tayi ba hakorannan kuwa har gansa kuka suke kai tabude za'ai daurin dan kwali ko tsagar kitson baka gani tsabar dadewar da yayi akitse Inna har dukan ta tayi akan ta tsaya atsefe amma taki yadda.
Kayanta tabude wata tsohuwar doguwar riga ta dauko aka saka dawani mayafinta daya fara tattarewa sukwal dinta datake bala,in ji dashi tadauko kwas kwas aka fara taku bata yaddaba ita budurwa kirjinnan ashafe kamar allon sha.
Inna ce tabita da kallo Jalila ina zaki da kika gambaza wannan hodar afuska fari tai da idanu aka jujjuya Inna baki ganni bane kinsanfa yau Lahadi gidan Maman Ladi zanje kallo yau za'ayi film din yan gayunnnan danake baki labari nima irin kwalliyar su nayi Inna dariya kawai tayi lallai ashe suma mahaukatane irinki shiyasa kika kulla abota dasu nidai nagaya miki karki kai magariba da anyi la'asar kidawo gida batace komai ba tafice taci dammara gidan Maman Ladi ta nufa ba sallama bako mai ta afka daki suna zaune ita da Mijinta suna kallo suna hira kamar dakin gyatumarta haka ta fada dakin saida suka zabura dan kamar ancillota haka suka ganta.
Cikin jin haushinta Baban Ladi yake fadin waike wace irin tinkiyar Yarinya ce da ba ayi miki tarbiyya agidan ku ba ko gidan arnane kyafado mana daki haka baki sallama ba ko ajikinta saima kara matsawa datai kusa da TV din kamar zata fada ciki Maman Ladi ce ta kunshe dariya dan tasan mutanan fa an hadu yanzu za a haura tashi yayi afusace fusgota yayi kamar kayan wanki haka ya watsota waje kamar Mayya haka ta sake zabura ko zafin faduwar batajiba tafara kiciniyar komawa dakin nanfa fada ya kaure atsakanin su tanason shiga ya hanata shiga shammatar sa tayi gaba daya kafafunsa takamo gata da shegen karfi rikica saiga baban Ladi akasa kanya tashi ta fada dakin tsabar karfin hali harda saka sakata tanajan tsaki.
Wallahi Maman Ladi wannan baban naki baida mutunci shi baza'aci arzikinsa ba to wallahi yama yiwa kansa kallon bazaiyi ba cikin dariya Maman Ladi tace hoo Jalila danja mutum da gidansa kice bazaiyi kallo ba na hanaki yiwa nagaba dake rashin kunya Jalila amma kinkiji yanzu kitashi kibude mai dakinnan yashigo kuma kibashi hakuri ko yanzu nakashe kallon.
Jin zata kashe yasa tai saurin mikewa ta bude kofar Baban Ladi ko kallonta beba danya fara zaton wannan yarinyar ba mutum bace kamarshi ace wannan ficiciyar yarinyar zata kayar kamar mutuniyar kirki harkasa ta tsugunna tana bashi hakuri banza yayi da ita yashige Uwar daka tabe baki tai kaika sani karma Allah yasa ka hakura.
Komawa tai taci gaba da yin kallonta yamma nayi Maman Ladi takashe kallo ta korota gida bagidan tanufa ba bala me tsire ta hango da buta ahannu zai zagaya dariya tai na angamu zakasan baka da wayo wallahi, sai kasan ni ka daka saidata tabbatar ya shiga kewayen kalle kalle tayi babu kowa awajan wani tsohon kwano ta hango cikin sauri ta karasa tadauka dam tacikashi da Kasa kan tsire da balangunsa tatafi da kasar hannunta.
Tas tabade naman nan da kasa zanga tayadda zaka siyar da naman yarda kwanon tai tasamu wajan buya hango Bala tayi da butarsa ahannu yana yan wake wakensa cije yatsa tai tana babbaka dariya kamar ance ya kalli Naman sa gaba daya kasa ta rufe kan naman cikin matukar kaduwa yake zabga salati yama rasa ina zai kama wayyo dadi kamar ya kashe Jalila.
Saidata tabbatar hankalinsa baya inda take tai wuff tafada gidan Maman Ladi sake gyara nutsuwarta tayi.
Kanta akasa tafito tana tafiya kamar ba ita ba jin Bala nata salati ta isa wajansa da sauri Bala me tsire meyafaru kare mata kallo yayi tabbas dagani ba ita bace dan da alama fitowarta kenan daga gida bansan wani dan asara ne yayi min hakaba koma wane In sha Allah kan dare zanyi masa kulla ciki saidai aga gawarsa kululu cikin Jalila ya murda haba Bala ba'a wasa da rayuwa koma wanene kai masa addu,ar shiriya amma banda maganar kisa to koma dai kece haba Bala aini kasan banajin tsoron ta mutu balle tai rai nicefa Jalila sa maza gudu kawai dai yau imanine ya sauka a zuciyata.
Yadda yayi da maganarta wani katon botiki ya dauko da ruwa haka yajuye Naman nan aciki yana wankewa Jalila na tayashi ba karamar asara yayi ba kamar yayi kuka saiko tsinewa wanda yayi masa haka yakeyi Jalila nata kunshe dariya tsire dai yatashi daga aiki ana tsomashi aruwa ya zagwanye roman balangu kuwa tuni ya zama kasa saida suka gama gyara wanda ze gyaru Jalila tace saiya sallame ta ba kanwa takasoba da zatai masa aiki abanza haka yabata tatafi ranta fes gida ta koma da Namanta aleda saidata leka ta tabbatar Inna na daki wuff ta fada dakinta saidata tabbatar ta cinye Namanta sannan ta futo buta tazara tai Alwala sannan ta leka dakin Inna da cikinta ke kugi.
Inna meyake da munki balla mata harara Inna tayi ban saniba tasan kwanan zancan dariya ta sheke da ita wallahi Inna daganinki cikin ki zulai zulai yake kira banza tayi da ita saidata gaji tabar kofar dakin.
Washe gari saida kyar Inna tayi dabara tadan dama musu kunu haka sukasha badan dadi ba gaba daya wannan Talauci yana damun Inna tunda malam yarasu yan Uwansa suka wawashe dan abunda ya bari saboda tsabar rashin imani wai ajiyewa Jalila gadonta zasuyi Alhalin ko biyar haryau babu wanda ya taba taimaka musu da ita ada suna da dabbobi amma yanzu ko kaza tafi karfin su kullum gari yana wayewa zata fara tunanin meza adafa wani abu zasuci musamman Jalila duk da tasan bata da kwadayi badai taje Gidan mutane abata abinci ba taci amma rashin bata abincin na damunta kar hakan yasa ta canja dabi,unta wani yayi amfani da wannan damar ya cutar mata da ita.
Ita kadai take da ita bayan sun shafe shekaru Allah bebasu haihuwaba kwatsam Allah ya karbi Addu,ar su tasamu cikin Jalila bayan haihuwarta bata kara ba Jalila tasha gata babu damar tai lefi Inna ta tsawatar mata Malam zai hau fada tatakura mata shiyasa tatashi fitinanniya ga tsokana Gwaggo makociyar suce tazama kamar Uwa agare su sosai take son Jalila itama matsayin kaka tadauki Gwaggo shekara biyu kenan da rasuwar malam sun shiga tashin hankali Jalila ma tasha kuka haka suka gaji suka hakura shekarun Jalila goma sha biyu kenan amma haryanzu batai hankali ba sai daukar magana dangin malam babu ruwan su da su tunda suka cinye dan gadon da malam ya bari suka dauke kafafunsu babu wanda ya karajin duriyar su.
No comments