Recent Updates

Sugar Mommies Y

 5


, 08:08] أم افنان✍️💞: *Y*

Ahmed bai dawo gidanba sai dare ,sanyin Japan ya horasa idonsa yayi fari saboda sakkowar garin ƙanƙaran da ya dinga gantali a tsakankaninsu tun gabanin magriba 

Don haka a hukace ya dawo gidan kamar comerade😂 Fauza bata nuna ma kowa komai ba saidai ta kulle kanta a ɗaki taci kukanta ta gode Allah ta ma rasa wa zata kira suyi sharing damuwarta dashi .

Kamar munafuki ya shiga gidan ,tana kallonsa tun sanda ya ajiye motarsa ta window har shigewarsa dakinsa ,ba sai an fada maka bashi da gaskiya ba ,wanka yayi ya sauya kaya zuwa kayan sanyi masu kaurin gaske ya koma ya kwanta cikinsa na ƙugin yunwa .


Fauza shigowa ɗakin tayi hannunta riƙe da tray ɗauke da food warmers da cokali a gefe. Bata kallesa ba ta sama gefen  table ta ajiye masa 


Binta ya ringayi da ido kamar yaga zombiss 


Cikin dakakkiyar murya kamar na boss tace "Food is ready" washe mata baki yayi kai kana kallon dariyar kasan na yake ne


"Thanks mar'atus Saliha baza ayi serving ɗina ba " 


Kafesa da ido tayi hannunta ɗaya rike da Kwankwasonta .

Atake yaji tsoronta ya shigesa ,da sauri ya jawo tray din abincin ya daura akan cinyarsa ,jin shakwal ba nauyi yasa ya ɗago ya kalleta "Ehem" abunda tace masa kawai kenan ,shikuma kamar ƙaramin yaro ya buɗe food reserve ɗin 


Zaro idanuwarsa duk waje yayi sakamakon ganin food flask din babu komai a ciki sai fallan takardan memo anyi rubutu manya manya da Black biro. Ɓiririm ! Murfin hannunsa ya sufce ya fadi ƙasa ,da sauri ya ɗago ya kalleta itakam tama juya masa ƙeya tana girgiza in readiness to battle with him.


A sanyaye ya jawo takardan ya karanta ga abunda ke ciki 

"WAYE BABAN FU'AD NA GASKIYA"


"Love...."

"Hisshhhhh no answer the damn question first"


Bakinsa a take rawa ya kamayi "eh Ni dake duk munsan yaron Mr. John ne"


Cikin gatsali tace "Au Allah?...🤭😂 Uhm shiyasa naga kuma kuna mugun kama da yaron ko baka gani ba?" Jinjina mata kai yayi don maganar ma nauyi yake masa a halshe 


"To meyesa bakayi geno_t don a kore zargi ba ? Kodai fyade Nuratu ta maka ?" 


In_ina ya kamayi "Eh amma...amma kinsan baban yaron nan ya amsa cewa ɗan nan nasa ne " 


Dafa masa kafada tayi tana murtsike masa naman kafadan da hannunta "Naji Kana Inda inda ne...Aushhh ga zufa ma sai tsatsafo maka yake a goshi " tayi maganar tana shafe masa Zufan goshinsa tana nuna masa a hannunta 


"Aah ba zufa bane" jinjina masa kai tayi kurum ta juya zata fita ,duk wasu hujjoji sun gama tabbata me yayi saura?


Fuzgota hannun rigarta yai tayi lauuu zata faɗa jikinsa tai na maza ta dafa table "Nayi kuskure ki yafe mun don Allah Fauza" warce jikinta tayi a hannunsa ta fice da sauri ,biyo bayanta yayi shima da sauri amma ganin ta shiga ɗakin Nuratu yasa yaja burki yasan lallai yau akwai bala'i 


Tsidik sukaga mata ta shigo masu ɗaki babu sallama ,kuma kana kallonta kasan babu lafiya 


Duk miƙewa sukayi cikin kokwanto "Anty lafiya?" Wani irin kallo tabi Nuratu dashi kafin a hankali zuciyarta ta soma bata hakuri don haka ta kauda kai taje gaban baby Fu'ad Saidai ta kasa ɗaukan sa kamar yanda da take masa da zaran ta shigo 


"Noor roƙonki nazo inyi" 


"Me ke faruwa ne wai Fauza ki natsu mana mu duk nan fa mata ne ,ciwon ƴa mace na ƴa mace ne fa"


"To um_jafar ai na natsu...Noor kizo muyi magana ki tayani lulluɓe sirrin gidana ,sirrin yarona Plz"


"Anty me ke shirin faruwa ne wai ,me kike so Inyi maki? Anty Kin gama mun komai ,don haka ko me kike so nayi alƙawarin yin maki matsawar bai kaucewa Shari'a ba" 


"Koda zance ki auri Ahmed ? I mean Mijina Ahmed?" 


A zabure ta miƙe kawai sai bakinta ya kama rawa "Anty...Anty"


"No kinyi mun Alƙawari yardanki nakeso kuma wlh in har baki yarda ba zan bar gidan nan bazaku sake ganina ba ,Na daɗe da fahimtar akwai wata jiƙaƙƙa a tsakaninku ashe Fu'ad ne ,kun maisheni bahuwa ina nan ina neman magani don in haihu dashi ashe kuna zagayawa kuna cin amanar aure ....haba Noor wannan shine sakamakon yarda da amanar da na baki ,ki ringa kwanciya da mijina ? Haba noor haba😭" muryarta ya gama hawa sama kuka yazo ya dannesa kawai sai ta rushe da kuka .


Nuratu ma zubewa a ƙasa tayi ta fara rizgar nata kukan 


Da sauri um jafar taje ta fara rarrashin Fauza ,itakuwa Nuratu sai kuka take tana sambatu 


"Sai da nace ma ya Ahmed ya faɗa mata gaskiya ,gashi yanzu tazo tana zargina"


"Ke kina da wani gaskiya bayan wanda bincike ya nuna mun? Nasan Fu'ad yaronsa ne kuma ɗan gaba da fatiha did I complained? "


Cikin sassanyar murya Um jafar tace "Fauza ki natsu kiji maganar nan tabbas Ahmed shi ya lalata komai amma kisa a ranki Fu'ad ba shege bane da aure aka samesa ,saidai auren ne anyishi auren sirri shine kawai amma Ahmed mijin Nuratu ne itama !" 


Take kanta ya soma juya mata ,daidai nan Ahmed ya shigo "Haba Anty me yasa kika faɗa mata"


"Kamun shiru Ahmed sam baka kyauta ba ,dama wannan zaman kakeyi da matan ka? "


"Karki damu um jafar laifina ne da na gaza ma kula dashi...laifina ne da ban natsu na karance sa ba ....laifina ne da na kasa bashi ɗa....laifi na ne.." 


"Bakida laifi ko daya Fauza kuma ke aka zalunta ,amma kiyi hakuri "


Miƙewa tayi ta kallesu a gabaɗaya "Duk abunda kukayi baku cutar dani ba ɗan ku Fu'ad kuka cutar kunsa duniya tana masa kallon shege ,bayan kune iyayensa da shaidu ,Kun shegantar da ɗan ku a idon duniya saboda Fauza? Bakuson zamana a cikinku kuma yau zan barku , Allah ya sake hada kanku ya raya mohd Fu'ad" 


Tayi ƙofa da sauri zata fice. Da sauri ya tareta 


"Ka Barni in tafi kafin Inyi maka abunda zan dawo ina nadama"


"Kiyi Fauza indai hakan zaisa ki huce fushin abinda nayi maki"


"Bazaka huce wannan ba saboda bayan case ɗin Nuratu akwai na Na'ima shikuma me zakace na nemanta da kakeyi a waje ? Ehem malam mai mata dozin ko itama ɗin matarka ne nice kuka mayar bahuwa?" 


Salati Ahmed ya somayi yana rantse rantse don ta gaskata shi amma fafur taƙi sauraransa ,da ƙyar umjafar ta shawo kanta ta janye cewar zata fita gidan amma tace su ƙyaleta tanason ta huta ,tanason tai isolating kanta a ɗaki ita ɗaya.



Tana fita Ahmed ya waiga ya kalli Um_jafar Anty plz ki gyara mun gidana kafin ki tafi wallahi duk ba da nufi nayi ba tsautsayine 


"Na sani Ahmed kuma kaima mai laifine amma Fauza tayi fushi in ta huce sai ka sameta ka fada mata yanda abun ya wanzu matarkace tabbas zata fahimce ka." 


Godiya yayi mata yasa kai ya fice ,Nuratu na corner tana maƙale da babyn ta da aketa rikici duk saboda shi .

[12/25, 08:53] أم افنان✍️💞: Super ma'am


Sai yamma Zee maama ta tafi room ɗin Kareema madam nan ta iske bata ,har dare bata duk namiji ya watsa kansu ,Zuly ma ta tafi tana fushi da Zee maama ga Kareema Bata nan ,don haka ta kira ƙure daɗi ya tayata zama kafin ta dawo amma har suka kwana gari ya waye bata dawo ba ,don haka ta yanke shawarar bin ta gida mayb ta wuce ne bata sanar masu ba ,ita ta tattaro masu kayan su ƙure daɗi ya nemo masu aron motar abokinsa ya kaisu har shettima road .

Nan badaƙalar take don tana tinkarar gate ɗin taga baƙin fuska an sauya masu gadin gidan gabadaya  ,sauka tayi ta samesu da maganar su bude mata ta shiga amsa daya suka bata ba sunanta a list ! daga nan suka rufe ƙofar suka barta a tsaye ƙotohhh!  Shiru tayi tana nazarin ina kuma zata nufa gashi kiran duniya wayar Kareema baya shiga ,dawowa motar tayi ta kalli ƙuredaɗi 


An hanani shiga wayarta kuma a kashe bansan meke faruwa ba kuma gashi Ni babu kudi a hannuna komai nawa yina wajenta,ko zan bika gidanka?" 


Fiddo ido yayi waje "ki bini gidanmu inada matane? Ni banma da takamaiman ɗaki a gidanmu ɗakin zaurene kuma ba nawa bane Ni kaɗai kawai Hajiya sauka mun a mota inje in ƙarasa da gwaramar da kika janyo mun don dole sai na biya mutunin nan kudin fetir ɗinsa da na shanye"


"Habawa ƙure daɗi ka tausaya mun mana wlh ko yanzu yunwa nikeji gashi banda ko sisi" 


Ko kallonta baiyi ba ya soma fiddo mata da kayanta ƙasa ,saida ya sakkosu duk ya zo ya warce wayar hannunta ,ya shige motar sa ya rufo bam! Yasoma mata key


Ƙwalla masa kira tayi kamar goluwa "Ƙure daɗi?" 


"La'adan kwana ina sukuwa a kanki keda ƙawarki na amsa sauran kuma kije asibiti ai maki test" 


Dukan motar ta shigayi da hannun ta "Haba kaiko ina kake so inje bansan kowa ba fa bayan kai da su super ma'am"


"Mtseww ashe ke baki ma san kan barikin ba ,to tunda har ƴaƴanki suka sallamaki kika fito biɗan bariki da tsuhwan ki dama sunsan mu zaki taras .... Malama ki faje gida tun da suturanki kafin ciwo yai fata fata dake kije gida suƙi karbarki"


"Me kake nufi?" 


"In kinje asibitin zasu fada maki, a huta gajiya sugar mummy" 


Ya figi motar da gudu ya bar layin da sauri ,rusunawa tayi akan kayansu ta rasa ma da wanne zataji.


Komawa wajen masu gadin tayi tana roƙonsu subarta ta shiga wani mai suffar marasa imani ne ya mata magana da kakkausar murya 


"Ke jibeki da an ga shigarki an ga kilaki ne zamu bari ki shigar masu gida? To wallahi in Baki tafi ba kika sake bugun ƙofar nan sai mun maki ɗan banzan duka "


Take taji tsoro ya shige ta "To Allah ya baku na me Bara"


Ta je wajen kayansu ta tattara ta soma jan kayan ta haye saman layin,saida ta yi tafiya mai nisa kafin ta sama mai adaidaita ,tace ya kaita gidan ƴarta um_jafar .


Suna isa ta shiga karɓo masa kudinsa ,aikuwa um_jafar na ganinta a wannan yanayin sai kuka  ,wai uwartace ta zama kamar er tasha haka ? 


"Ke don uwarki meye kike kallona kike mun kuka sai kace an kawo maki gawaa nayi raga² ,in bazaki bani ba sai In fita waje in biɗa sadaka ,na annabi baya ƙare wa" 


Haƙuri ta soma bata tace bari taje ta ɗauko kudin a basa ,tana shiga ɗaki ta ɗauki waya ta fara shaidawa ƴan uwanta halinda uwarsu ke ciki ,nan babbansu ta Lagos ta roƙeta ta san yanda za tayi kar ta barta ta fita ,kafin suyi zama na musamman akan matsalar .don haka fita tayi ta ƙofar baya ,ta baiwa mai gadi kudin ya ba mai adaidaitan ai kuwa mai adaidaita yina dafa kuɗi yayi gaba da jakunkunan su hajiyoyi sugar mummies . 




Ƴan special da vips kunyi hkry dani na kwanaki na sani saboda hidimar school ena ne as u knw amma , inshaalh daga yau posting zai cigaba on progress 



Bamalli's care

[12/27, 10:04] أم افنان✍️💞: Kareema Madam


Zaman waje ɗaya ya dameta ga masu aikin da aka kawo mata wasu ƴan ƙauye dasu ga girman kai bazai barta tabi ƙaxaman en aikin ta ba ,don haka holewa dai ya gagara yiwuwa ,kullum tana trying number Ahmed don ta zazzagesa ta ci masa zarafi amma batasan me yasaba sam bata samunsa don haka saidai ta ƙarashi sababinta akan ƴan aikinta ko ta kira sauran yaranta tayi ta masu ƙorafi haƙuri suke bata ,sannan suce idan sunzo hutun azumi za'a hadu sai aji dalilin da yasa ya saka mata takunkunin ,ai suna faɗin maganar haduwa a tattauna Matsala sai ta diririce ta ce fafur batasan jin maganar haduwa ,su ba yara bane a nan suka gane ko me Ahmed yayi solution ne wanda yake kan dai dai ,don haka ma suka daina takura masa da maganar hajiyarsa 



Sannu a hankali ahmed ya shafe watanni shida baizo 9ja ba ,wannan abu sabone a cikin halayyar sa ,Hajiya kareema ta zama tamkar Mutuniyar kirki daga zaman ɗaki sai kallon TV sai kuwa in ta gaji taje garden ta karanta jarida kamar tsohuwar professor ,Abinci dai kalar wanda takeso takeci amma babu adeqt exercice don haka ƙafafuwa suka fara ciwo ,kullum itakenan sa house girls dinta suna matsa mata ƙafa ana shafa mata man zafi ,Kullum balainta duk Ahmed ya ja mata . 


***

A ƙauye kam babu wani sauyi ko ci gaba daga halin ƙuncin da Iya take ciki ,gadon su Nuratu ne sarki ya amsa ya cinye da ya tabbatar ya ƙare kuma sai zaluncinsa ya daɗu kullum fitinar safe dabam na yamma dabam ,bata taɓa tankasa ba sai ranar da Nura ya bar gida har dare bai dawo ba taje ta samu sarki da maganar aje a nemosa yace baisan maganar ba ,wai ai Nura ya daɗe da gane tafarfakunsa zai lalace ne ,don ana yawan shaida masa an gansa da marasa ji don haka Yina can yawan iskancinsa ba mai ɗaga masa hankali . 


Bata taɓa masa musu ko sunyi musayar miyau ba sai a ranar ,aiko ta xari mayafi a igiyar shanya "Malam naje neman yarona ,zamani mai wuya" tsawa ya daka mata "Babu inda zakije"  

"Sai dai fa kayi haƙuri yanzu goma shaura yarona bai taɓa kaiwa War haka ba ,bai dawo gidan nan ba" 

Tasa kanta a hanyar zaure


"Talatu....Talatu Ni nake magana kike tafiya? To wallahi da kin fita a bakin igiyoyin auren ki ,shegiya ƙadararriya"  


Tanaji ya cigaba da ɗura mata zagi Ita dai ba magana ta fice bilayin neman ɗan ta. ,Saƙo da lungu har wajen gonaki haka ta ringa haskaka da futilar ƙwai wai ko zata riski gawarsa amma ko mak kama da Nura babu ,gidansu iyayenta ta nufa tana kuka don lokacin sha ɗaya ta gota. 


Tana shiga tsakar gidan ta gansa kwance a tabarman karauni shi da tsohonta suna ta jan gwarti 


Salati ta rafka ,kenan yazo nan ne zai kwana amma bai sanar da ita ba ya sata tayi ta damuwa har suka saɓa da mijinta ? 


Maka masa duka tayi a baya tana ƙwalla masa kira ,wannan dalilin ya farkar da babanta da Nura ɗin kansa  


"Kai...kaii...kaiii Lafiya dai ,wanene?"


"Baba nine" 


"Ai talatu...Kece da tsakar daren nan ? Ina mijin ki kuma?" 


"Baba Nura na fita nema ashe yazo nan zai kwana bai gaya mun ba" 


Tsaki yaja "Aii Nuraddenin jaririn goyane da zai ɓata? Gsky son ƴaƴanki Yayi yawa Talatu ,to ga nuraddenin tunda kin gansa sai ki wuce gida " kunya ne duk taji ya rufe ta kawai sai tayi hanyar ɗakin mamanta 


"Talatu....ya ki nan " dawowa tayi ta tsuguna a gabansa "Gani malam"


"Maza jeki gida gari yayi shiru karkija mana magana" 


"Baba ai yace in na futa a bakin aurena Ni kuma na fita" 


Tafa hannu yayi ya fara salati "au shi inusan yace maki hakan? " Gyada masa kai tayi "ke kuma sai ki ka fiton saboda baki san darajan auren ba ?" 


"Aah Baba fargaba ne"


"Shikenan shige gida Allah ya kaimu gobe nasa ayi mun kiran inusan inji ba'asi...kai kuma Nura mu shiga ɗaki hakanan dare yayi sanyi zai fara sauka" 


Shida Nura sai wuƙi wuƙi yake da ido shi ya ma manta halin uwarsa na ƙulafuci ne har yazo ya kwana ɗin.



Washekari tun jijjifi baban Talatu ya aika ayi masa kiran Sarki amma yaƙi zuwa har kwana biyu yina aiken bai zo ba,sai ranar kwana na uku yazo da daddare  


Malam haƙuri ya soma basa ba tareda ya saurari bahasin maganar ba ,saidai abun takaicin haka yake ɗaga halshe yina tujara wai basu ba yarinyarsu tarbiyya ba waye waye ,tun tsohon na basa hakuri har ya fara hassala 


"To ynz dai ranka ya daɗe mai ye mafita?"


"Mafita ya rage naku ai Ni na rigada na yanke hukunci ,kuma nace in ta fita a bakin aurenta kuma ta fitan kaga banda bakin magana ta SAKU!!" 


Rimtse ido Baba yayi cikin damuwa amma yace "To shikenan Allah yasa hakan. Ne Alkhairin" ko amsa sa baiyi ba ya haura takalmarsa ya fice .



20days Later 

Iya Talatu tana natse a gidansu tana zaman idda sai ga saƙo daga wajen sarki tazo ta kwashe kayanta yina buƙatar ɗakin zai saka amarya (Zully Madam) .


Abun bai bata mamaki ba tunda zulli dama kowa yasan ta zama ƙwaƙwararriyar er duniya ,don haka tana mata fatan aure ya natsa ta don haka ta aika aka kwashe mata kayanta tazo ta Nafa'a a gaban iyayenta ,wannan kenan.


Inna Abu ko bata da zaɓi sai na zama a gidan um_jafar ,tunda dama barikin bata iya shi ba ,kuma zaman ƙauye tana jin tafi ƙarfin sa don haka ta zauna tareda ƴarta tunda mijinta ba mazauni bane ,amma fa kullum tana aikin fada da jikokin ta da masu aikin gidan .

A bakin um_jafar taji aihuwan Nuratu kuma um_jafar ta wuto Japan wajen su Nuratu ta bar inna Abu da yara.

[12/27, 11:14] أم افنان✍️💞: Fauza har ga Allah tayi niyyar yafewa Ahmed zunubin da ya aikata dukda tana jin haushinsa amma tunda yazo ya bata hakuri ya kuma fayyace mata yanda akayi auransa da Nuratu sai ta gamsu aurene ba na shiri ba .

"To me yasa ka kasa faɗa mun ka aureta kuma me yasa ka munafurceni kuke kwanciya da ita a ɓoye ,kana tunanin zan zama shedaniyace da zan gina katanga tsakaninka da halaliyar ka?


" A'ah ko ɗaya ban shirya plan din tarewa da Nuratu ba ,sai sakamakon tafiya England da kikayi kika Barni cikin mugun sha'awa at that night da kika kirani ranar ne komai ya faru a ranar ma zan iya cewa fyade nayi mata ,sannan a dare ɗayan ta samu shigar cikin kuma wallahi ita kanta Nuratu batasan Ni ɗin mijinta bane sai bayan mun koma Nigeria ..." Katsesa tayi da cewa 


"Sai kuma daga lokacin ka cigaba da kusantarta ba kwaɓo ko ni kun mai dani sha ka tafi?"


"No Fauza ki saurareni kema fa kina da laifi da ace kina bani haƙƙina kina tsaftace makwancina kina mun girki da bazan taba sha'awar Nuratu ba bare har abunda ya faru ya faru"


"Aah ba abunda ya faru sai Alkhairi rabon zakaga ƙwanka ne a doron duniya ,Ni kuma Allah ya sani ƙaurace maka danayi a shimfida ba yin kaina bane doctor's order ne saboda nima inaso in baka ɗa shiyasa nakesa maganin da ya bani kuma dokar ba'a Sex ,Ni naƙi fada maka ne karyazo kayi juriya ka saka ran in na Gama zaka samu yaro ta wajena yazo ba'a samu ba ,shiyasa naki fada maka nafison in na samu cikin sai ka ji dadi kaji dalili kuma yanzu ma na gama maganin,saidai kuma I'm too late ko yanzu tunda ga baby Fu'ad Allah ya bamu ai shikenan"


Ya tausaya mata sosai kuma ya fahimceta kowa ya ba ɗan uwansa hakuri ,sosai ta karɓi uzurinsa amma ta rokesa ya fita ya barta ,ta gama yanke hukuncin cigaban zamansu ko haƙura da auransa.


A ranar Ahmed yini yayi da zullumin outcome ɗin hiransu da Fauza  don haka shi kadai ya zauna a falo har goma da rabi na dare yina kallon Tv daganan baisan sanda barci ɓarawo ya saceshi a wajen ba .



Fauza dambe ta ringayi da zuciyarta wutar kishi na balbalarta ,tayi kuka tayi kuka tayi nadamar shan maganin hana daukan ciki a rayuwarta.

Na'ima ta kirata a waya ba Adadi amma bata ma sani ba sai wajen karfe goman dare tana zaune a cikin duhu idonta sunyi luhu luhu sannan ne ta laluba ta Dauko wayarta ta haska da hasken screen ɗin wayar ta kunna makunnin wutar dakin ta shige toilet ta wanko fuskarta ta dauro alwala ta fara jero nafilat tana addu'ar Allah ya huce mata zuciyarta ya bata ikon karban Nuratu a mazaunin abokiyar zama kuma ƙanwa ba kishiya ba . 


Na'ima kamar mayya har shadaya saura tana cigaba da nacin kiranta a waya 


Sai sannan ne taga haske yina fita ta wayarta ,a nutse ta shafa adduarta ta mike ta dauki wayar ,missed calls din Na'ima ta gani rududu don haka da sauri ta bi bayan kiran .


Da dusashiyar  murya tace "Hello Na'ima".

"Fauza badai har yanzu kuka kike ba kin kasa tunkaransa kuyi uwar watsi"


"Nayi Na'ima kuma Nuratu matarsa ce an daura masu aure a ƙauye nice Basu fada mun ba so Fu'ad ba shege bane da ubansa !"


"Kam bala'in nan ,wannan irin cin amana ne ? To ke me kikace wani mataki kuma kika ɗauka?"


"Me zanyi bacin hakuri naima ?"


"La'ilaha illallahu ashe Fauza bakida wayo? Kinsan illan kibar dan kauye ya waye kuwa? To billahillazi kin shiga uku ,don in har baki ɗauki tsatsauran mataki ba kina kallo za'a maisheki bora a gidan ki ,barin ma gata da yaro ta bashi ke banza saidai kici kiyi kashi ki masu raino tayi ta haifo masa ƴaƴa kin zama nanny" 


Rausayar da kai  tayi cikin sallamawa "To Ni ya zanyi dole hakuri shine mafita ku kuma masoyana in kuna ƙaunata kuyi ta mun addu'a Allah ya bani ɗan kaina amma ynz ba lokacin fada bane tunda kinga yarinyar nan ma noor tsorona takeji har yanzu nice shugabar gidan in nayi maintainng"



"Shikuma gogan fa? Ina nufin Ahmed bada karamin ɗan duniya bane ko baki sani ba ,dole sai kin tauna tsakuwa don aya taji tsoro" 


"Kaina ya kulle me ye SHAWARAR ki"


Ajiyar zuciya tayi ,cikin fatan cikar burin ta ,ba abunda take so illa ta auri Ahmed ta kori Fauza waje 


"Kizo gidana yanzun nan a zuwan kinyi yaji sauran plan din ki bar komi a hannuna "


"Kina ganin hakan mafita ne?"


"Wai ba sanadiyyata kika san Ahmed suna tare da noor ba ,to nafiki hangen nesa ynz ma ki Barni dashi" jinjina kai tai "To ganinan zuwa ynz"  


Ta kashe wayar tana taune leɓe ,yanzu zaki fada tarkona Fauza sai nasa mijinki ya tsaneki na kore wannan mayataccen soyyayr naku na rashin ganin aibun juna .da kinzo gidana kin shiga tarko wlh "



Fauza daga kai tayi ta kalli agogo karfe 11.23 na dare 


Jimmm tayi cikin fargaba ,lallai fa dare yayi anya bazata hakura sai gobe ba ? Kiran Na'ima ta sake yi a waya don ta shaida mata ta fasa zuwa amma Na'ima tana kallon wayar tama ƙi ɗauka  .

Shegiya nasan kin sauya tunani ne I'm Keen fiyeda tunanin ki, a lokacin da kike lulluɓe a inuwar aure mu bariki muka fita to koda ɗan yatsa akayi magana ma gane .



Fauza ganin bata dauki wayaba yasa taji kawai gwara ta tafi ɗin don haka ta haɗa kayanta a ɗan ƙaramin box ta fito da mukullin mota ta zo giftwa ta falo ta ganshi kwance a kujera a takure yina barci ,wani haushinsa ne ya ƙumeta ,kaɗan ma ka soma gani ka tari auren mace fiye da 1 bayan bakada karfin juriyar rikesu?


Tada mai gadi tayi ta sashi ya buɗe mata gate ,bai wani damuba don yasan tana fita call a asibiti ko cikin dare ne ,saidai bayan ya wangale gate ne ya lura da ƙaramin akwatin da ta fita dashi ga idanuwar ta a kumbura ma'ana tasha kuka ta gode Allah. 



Kamar wawa haka ya saki baki yina kallonta har ta kaɗa kan motarta ta fice. 


Kamar wanda aka mara yaje da gudu ya rufe gate din sai kuma ya sheka falonsu da gudu ,yina shiga yaga ogan naka yinata barci a takure a kan kujera ko kayan jikinsa bai cire ba.


Zuwa jikin kujeran yayi yina dukan kujeran ta gefen fuskarsa yina kiran sunan Ahmed ɗin a ruɗe.


Walai Ahmed ya buɗe ido jin muryar mr John yana kiransa kamar a mafarki 


Cikin Muryar barci yace "John what's going on?"


"Oga...oga madam fa yanzun nan ta sani na bude mata kofa ta fice da motarta da akwati kuma kamar tayi kuka ..." 


Neman ɗungurungum barcin da ke idonsa yayi ya rasa .yayi zubut ya mike 


Kai wani irin dakikine kai wani irin wawa ne ,meye amfanin daukanka aiki da nayi da zaka bar matata ta fice a gida cikin tsohon daren nan?"


Cikin in_ina yace "Oga oga naga ita likiciyace kuma ta saba fita komun dare..." Daukesa da mari Yayi "Ko mun dare kana nufin Matana namijine ? To bari kaji wallahi in wani abu ya faru da matata sai na daure ka"





Bamalli's care

[12/27, 13:17] أم افنان✍️💞: Daukan wayarsa yayi da sauri ya fara kiranta a waya saidai bata ɗaukan wayar "She's not picking" 


Kallonsa yayi bata daukan wayar "topah oga dama kun samu matsala da itane ?" 


Tsawa ya daka masa "shiru!!!!!!" Ɗif John ya dauke wuta harda sa hannu a baki ya danne bakinsa "will you leave mu room? Da sauri ya doshi hanyar ƙofar 


"Mtsewww irresponsible nonentity" zarya ya farayi a falon kafin ya wuce ɗakinsa da sauri ya kwasa key din motarsa shima ya fita nemanta



***

Washekari

11am 

Labarin guduwar Fauza ya daki mazauna gidan ,Ahmed ya shiga babban tashin hankali ya gama kai report wajen ƴan sanda da airport in an ganta zata fita a tareta don yasan option dinta daya ne tace zata gudu . 


Yanzu ma duk suna zaune ne a falon lauyansa ya kira yazo gidan um_jafar ta gama zama speechless saboda rikicin gidan ya fara Isarta ,ta rafka uban tagumi itakuwa Nuratu ta saɓa yaro a kafada sai jijjigasa takeyi  


Lawyan kallon Ahmed yayi da ya kasa zama "wai ya akayi ta fice ne?"caraf mai gadin ya karɓe maganar 


"Kawai ina barci ta leƙo ta windown ɗakina wai ina buɗe zata fita nikuma bansan matsala bane hakan sai na bude mata"


Ahmed ji yayi kamar zai fashe da kuka a harzuke ya kalli lawyan nasa "Look at the person I employed to take care of my wealth and I.... shashasha" 


Kayi hakuri Ahmed tunda ba ɓacewa tayi ba za'a ganta ,and beside shifa mai gadine bazai iya disrespecting ɗin ta ba ita fa ogansa ce"


To naji Amma Ina so ka sani Na'ima is answerable to me ,Yarinyar nan shedaniya ce ina zargin matata tana wajenta don haka yau zansa a nemota kuma wallahi sai na turata gidan yari,haba ta fitini rayuwata"


"Ahmed ka natsu don Allah You can't sue her for just a mere thought ,had it been ka kamata dumu dumu ta fice maka da Matane then zaka iya komai amma yanzu zarginta kake yi kuma ba'a haka"



"Lawyer No ,I must arrest that lousy girl Ina zargin ta da kidnapping din matata ,wlh inada hujja fa daga haduwa a mall ta rabani da farinciki da nutsuwar zuciyata daga ƙarshe ta rabani da matata..." 


"Take it easy sir,ynz dai natsuwa zakayi ka bani bayani a nutse mukuma zamuyi aikinmu in ya kama sai mun gayyato ita naimar zamu nemota duk inda take " 


Jinjina kai Ahmed yayi "Ok nagode barrister ,Happiness ku shiga daga ciki ki kula mun da yarona sosai ina gaya maki rayuwar yaron nan is in great jeopardy....


Dakatawa da maganar yayi jin ƙarar ƙofa da takalmi ,duk ɗaukacin ɗakin kallon ƙofar sukayi ,da gudu Fauza ta shigo ,aikuwa Ahmed ma miƙe ya Nufeta da gudu ya rungumeta sai kuka ya ƙwace mata tana bashi haƙuri ,shima yina bata hakuri duk shiru sukayi itakam Nuratu sunkuyar da kai tayi  .


Daƙyar suka rabu ta ɗago tana kallon yanda duk gidan suka hadu a falo kuma tasan dole tattaunawa ake a kanta 


"Plz I'm so sorry the devil was trying to split our relationship ,I almost loose my family kuyi hakuri don Allah it was a bad friend of mine planned it...and I obeyed with a blind eyes Amma daga ynz komai zai daidaita hakan bazata sake faruwa ba nayi Alƙawari"


Rungumeta ya daɗa yi yina ɗan bubbuga mata kafada "Baby na damu sosai kayi hakuri hakan bazai sake faruwa ba i learnt a lesson...bansan Ina mahaukacin sonka ba saida naga an gina mun gadan zare zan rufta ...I love You more my love"


"I love you endlessly my wife" 


Duk abun yayi exciting mutanen dake cikin dakin ,a take Nuratu ta fara tafamasu hannu fuskarta dauke da fara'a haka ma sauran ƴan dakin suka dauki clapping ,sukuna sun ruƙunƙume juna kamar wani zai ƙwace masa ɗan uwansa ,a hankali ya ke raɗa mata a kunne


 "It's ok,ki natsu kinji ki bamu labarin mai ya faru wannan barrister ne na gayyato shi saboda case ɗinnan so ki bashi bayanin abinda ya faru..."


Samun waje tayi ta zauna ta fara koro nasu zance tun daga wayarsu da Na'ima har gayyatar ta gidanta with the intention zata tayata maganin Ahmed last...last cikin dare taji tana waya ta aza barci takeyi akan za'a bata magani tasha a lemu za'a gayyato kwarto ya danne ta sai a kira mijinta ya ganta daganan dole zai saketa itakuma sai Naiman ta faɗa ma Ahmed cewar salihanci ba yana daga kalar shigar mutum bane gadai matarsa na iskanci da wani a waje ta gayyato shi gidanta without her consent ....Wai dole zai saketa itakuma sai ta shigar da kanta a wajensa ya aureta ..kuma tasha Alwashin bayan ta shigo gidan zata sa ya kori Nuratu da yaronta su cigaba da rayuwarsu su kaɗai.


Kowa saida yayi alawadai da Na'ima ,daga ƙarshe Fauza ta kalli Ahmed 


"Love meye tsakaninka da Na'ima wai?" 


Shiru yayi cikin taune Halshe kafin ya soma koro mata bayanin abinda ya faru from A_z 

 


Sunji tausayin Ahmed da wahalar da Na'ima ta basa daga ƙarshe barr. Yace zaije ya karasa bincike kafin a aika ma Naima da sammaci .


Ya ɗauki jakarsa zai fita Fauza tayi saurin miƙewa "Oh no! Bari a kawo drinks a sha ,ayi sharing farinciki". Da sauri taje ta ɗauko drink babba guda ɗaya da glass cups ta mika ma Ahmed ya buɗe tushhhh!!! Gas ya tashi , suka ɗauki tafi raf raf raf


Daganan Fauza ta karɓa ta zuzzuba a glass cups din ta fara miƙa ma Ahmed


"My gorgeous husband" ta miƙa masa karba yayi "thank you I love you"


Sannan ta miƙa ma barr. "Talented barrister bacin kai da kila kowa yasan bana gidan mijina God reward you" murmushi yayi ya karba gamida amsawa da Amin


Sannan ta juya ta miƙa ma um_jafar "my surukassss😂" ta kashe mata ido guda ,itama dariya tayi "Recounciler dai" ta bata amsa tana tattare gira cikin sigar wasa "Awwwn kaji yabon kai" Fauzan ta bata amsa ,duk aka fashe da dariya .


Sannan ta dauki wani ta miƙa ma ne John "Baban unknown baby😂😂😂" tasowa yayi jikinsa na kyarma ya miƙa hannu biyu zai karba wai yau shine zakisha abunsha tareda iyayen gidansa


Da sauri Fauza tace "Easy ...easy kar a fasa mun glass cup " amsa yayi yana godiya ya danna a baki kafin ma a umurce kowa yasha shi ya shanye nasa yina mur mur mur da idanuwa ƙarfin gas da sanyin drink ɗin yasa kunnuwarsa sun tsaya cakkk da aiki na wucin gadi ..


Dariya dakin aka bushe dashi ,sannan ta dauko wani ta miƙa ma noor 


"Hasken rayuwata ,our very joy giver ,ƴar uwata abun alfahari na the great me jego"  


Sunkuyar da kai Nuratu tayi cikin tsananin tausayin Fauza sam Batada riko Itako in vatayiwa Fauza biyayya ba me zatayi mata bayan ta aure mata miji still Bata daina sonta ba 


Sa hannu tayi ta fakaici ganin kowa na dakin ta share hawayen da suka dan zubo mata ,ta miƙa hannu zata karba um_jafar tace "Uhm uhm mai jego batashan abu mai sanyi...kar a bata mun wanka ahaaa"


Dariya duk akayi still dai Nuratun ta karba glass din drink din daganan Ahmed yace " cheers "  kowa ya miƙo glass cup din yana gwarawa a na ɗauwansa harda Mr.john da ya shanye nasa saida ya gwara cups ɗin kafin kowa ya soma shan nasa cikin farinciki ,da fatan daidaituwar Al'amari na har abada haka sukayi addu'a barrister ya fice cikin begen wannan familyn.


***

Bayan Barr. Ya Gama tattara bayanan sa ya shigar da ƙara kotu ya amso takardan sammaci ya tafi hotel ɗin da Na'ima ta sauka saidai yana zuwa receptionist ya shaida masa ta saki ɗakin ta tafi ,bincike ɗaya ya gano ta bar ƙasar ɗungurungun tun bayan da ta gane Fauza ta ganeta  


***

Fauza da um_jafar sun cigaba da kula da mai jego da baby Fu'ad inda Ahmed yake ta cuku cikin hada takardun transfer dinsa da fauza daga Japan zuwa Nigeria .yanzu komai ya kammala kawai jira suke Nuratu ta gama wanka suyi ƙaura gabadayansu daga Japan su dawo gida ,don tuni aikin sabon  gidansu da ya bada ƙwangila ya gama kammaluwa .

No comments