Recent Updates

Sugar Mommies X

 


Ahmed Æ™walwarsa É—aukan caji yayi a lokaci É—aya ogansa na wajen aiki ya kirasa a waya ga Matarsa na kiransa a falo da wanne zai fara? 


ÆŠaukan wayar yayi da sauri yina gaisheta bata samu amsa gaisuwarsa ba sakamakon ruÉ—anin da take ciki


"Can You come to the office now plz? One financial statement was missing and is so crucial"  dukda baisan exactly takardan da ya bace ba amma yasan ta office É—insa ne kuma ba Æ™ananan kuÉ—aÉ—e bane tunda har ogansa ta kirasa a yau ranar hutu .


"Yes ma, I'll be there shortly" a yanda yake takalmi kawai ya saka ya fito da key É—in mota a mugun urunce .


Carko ² ya gansu a falo a tsaitsaye "yawwa gwara da kazo" dakatar da ita yayi da sauri da hannu 


"Sorry ana jirana a office mahaukatan kuÉ—aÉ—e sun bace plz ku tayani da Addu'a"ya fice da sauri ba tareda ya saurare su ba ,wannan tashin hankalin shi ya shamakantar dasu rikicin da suke ciki kowa ya wuce É—aki cikin Alhini don sunsan in aka kasa gano kudaden nan zai wuya mijinsu bazai gidan yari ba .


***

Ahmed yina shiga office É—in Madam en tana É—aukan wayarta in readiness ta kirasa ta shaida masa an gani sai kuma gashi  


"Ayyah sorry sir Ahmed we've got it"


Wani sassaukan ajiyar zuciya ya ajiye a ransa yina fadin Alhmdllh .


BuÉ—e office É—in sa yayi ya shiga ya zauna kenan kirar abu_jafar ya shigo wayarsa ,Bayan sun gaisa ya fara tambayarsa dalilin da yasa ya saka ma hajiyarsu (Kareema Madam) takunkumin ba shiga ba fita a gidansu. Duk yanda yaso bin Æ™waÆ™wafinsa amma ya kasa faÉ—a masa kawai nauyin yayansa yakeji bazai iya fada masa halin mamansu ba 


Don dole ya ƙyalesa saboda yasan zurfin cikin ahmed don haka ya zarce da tambayarsa Fu'ad baby.


Washe baki yayi kamar wanda aka yiwa Albishir da Aljannah ,a hankali ya É—aura hannunsa akan kwantaccen sumansa yin shafawa ba 


"Hum Yaya kasan menene ? Ban taÉ“a yarda da karin maganar Hausawa ba da suke cewa ruwa yafi jini kauri ba sai yanzu ...kinsan yaya yaron nan yina ganina sai ya ringa washe mun bakin sanayya? Wato yasan Ni babansa ne ,kuma fa ko kuka yake da yaji murya na yake shiru...." 


Duk daurewan Abu_jafar saida yayi dariya  ,dariya kuwa sosai .wai jariri ake mannawa magana haka???😃🤭 


"Yaya abun ya baka mamaki ko?..." 


"Dole ya basa mamaki mana mazambaci maci amana....." A furgice ya waiga jin muryarta a saman kansa .

Dafe kai yayi "yaya ina zuwa Plz" yayi maza ya kashe wayar ya juyo ya kalleta 


"Ke jahilar inane da kika biyoni har office É—ina ,meye hadina dake don Allah?"


"Kai har Kanada liver din tsiya? Hmmm blood is thicker than water but wow....Anje an ɗirka ma mai aiki ciki ana can ana deceiving matar gida da sunan wai an amshi ɗa raino Ubangiji sai ya wulakantaka kuma ka sani sai na tona maka asiri, (kawai sai ta fara kuka tana tsatso hawaye) ba yanda banyi dakai ba ka kwanta dani amma ka ƙi ,na ɗauka kaidin ba garine ashe ƙazamine kai ,mai zina da kucaka ƙazamiyar ƴar aikinka so shamefullll ...."


"Aah fa ,is not correct" 


Rike ƙugu tayi ta kafesa da ido "ok correct me,what a disgust...🙊 Ahhh u slept with her ,Hmmm you choose her over me?"


"Akwai bukatar explntion bazaki gane ba "


"Ok Ina sauraronka "


Kama kansa yayi ya kasa magana ,kawai sai ta zarce da masifa "haba i'm doubting ,tayaya banziyar Yarinyar nan zata kwanta da mummunan mai gadin ka É—innan sannan ta haifi yaro kyakyawa irinka ? It sound fishy "


MiÆ™ewa yayi "Zo ki fita mun a office " 


"Bazan futa ba "


Yau bayida strnght É—in fada da ita kawai sai ya dauki car key É—insa ya fice ya bar mata office din ,da gudu ta biyosa tana haÉ—awa da sassarfa  


"Malam ko ka dakata mu gama maganar ko kuma Fauza ta ƙare mana komai dama na dakata da yin mata magana ne sai mun hadu one on one "


"You're such a devil😈 bansan mai ya shigo dake cikin rayuwa ta ba Amma ina rokon Allah ya kareni daga sharrinki " da sauri ya shige motarsa ya mata key ɓuuu ya bar wajen .


Da numfarfashi ya shiga falon yanzu ya fara hasashen Yarinyar ita taje gidansa yakejin hayaniya in kuwa haka ne ta gama haÉ—asa rigima da matarsa ya sani 


Yina shiga falon ya tadda Fauza tana ta ma baby Fu'ad wasa abunta 0 tension  


"Wata tazo gidan nan ko? Ya kukayi da ita" tattare giran sama tayi 


"Wata kuma? Ai ba wacce tazo gidan nan "


"Ha'ah mai gadi yace wata tazo"


"Ohhh Wai na'ima yes ayi haka" 


"Oh eh Yes " don shi bai ma san sunan ta ba .

tsatsaresa da ido tayi 


Furzo iska yayi a bakinsa gamida lumshe ido "bana son tarayyarku karta sake zuwa mun gida"

"Ha'ahhh wai wace?"


"Ita Na'ima"

" Meye hadinka da ita to,ya akayi ka santa kasan sunanta?"


"A bakinki naji yanzu mana" 


Bagarar da maganar tayi "man sassauta tie É—in wuyarka ka cika shaÆ™esa ,inajin ruÉ—un office bai sake ka ba go and have some rest" 


Gyara neck tie É—in sa yayi yayi loosing É—insa ma gabaÉ—aya ya wuce yina haki,tabbas shedaniyar tazo amma dai bata watsa ma matarsa wani magana ba .


Yina shiga ta mike zata kaiwa Nuratu yaro daki don ta gabatar da sallar zuhur taji wayarta na Æ™ara a É—aki da sauri ta je É—akin ta shimfide Fu'ad akan bed É—in ta taje ta dauki wayar kira na uku kenan yana yankewa ba amsa  ,ganin Number Na'ima saida yasa gabanta fadi haka siddan  


Bin bayan kiran tayi da sauri ,aikuwa ringing na uku aka dauka. 

"Hello Escaper ya ne?"

Bata maida mata martanin wasan da tayi mata ba kawai ta fara rattafo mata magana mai kama da saukar aradu


"Wannan yaron fa,É—an mijinki ne" rasss gaban Fauza ya fadi 


"What a hell of your fuck ?....I mean why you think so low ,ga mijina da har kike tunanin zai iya kwanciya da mai aikina ,an ordinary house help haba don Allah muna fadawa juna gaskiya mana wannan kinci fuskata ne...don yarona yai kama da mijina shikenan wani aibu...?" 


"Aaahfa kice yaron mai aikinki ,don dai kinsan baki aihuwa kuma a gabana tazo amsarsa zata bashi nono " 


"Yes you know...wannan shine asalin dalilin da bana tara Æ™awaye ,gashi kin maimaita É—aya daga ciki ...do have a good day na barki lapiya"  É“irit ta kashe wayan.


Tsuki Na'ima taja "kaji banzayen matan auren nan masu yarda da miji da yawa ,wallahi i just hustle to break this trust " 


Cigaba da nacin kiranta a waya tayi ,amma da sauri Fauza ta shige toilet ta kama Alwala tazo ta tada sallah 


Daƙyar ta idar da sallan saboda yanda take distracting dinta ,a ƙufule ta ɗauki wayar "Plz what exactly you're phoning for"


"Gani nan zuwa gidanki I've a plan "


"Karki zo Mijina bayason muamalar mu da Æ´an duniya irinki" sosai maganar ta ya soketa,amma ta shanye "Karki damu bazanyi 5 mns ba kawai zan nuna maki wasu hujjojine and zan hadaki da Æ™wararren likitan da zai iya dauraki akan maganin da ya dace inma ta kama yayi maki laparotomy surgery kodai menene dondai ki aihu zaiyi" 


"Naima na fada maki Yayi warning É—ina karki sake zuwa masa gida ,amma ke kina ina sai inzo in sameki".....



****

Suna haÉ—uwa juya mata baya ta yi ta fara tafiya hannayenta goye a bayanta ,itakuwa Fauza sai zare ido take ta kasa mata magana ko tace Na'ima zauna . 


Sai kuma a zafafe ta tako gabanta ta tsaya suna kallon juna ,ƙasa da muryarta tayi "Zakiyi matukar mamaki in mace maki nasan mijinki?"


Waro ido tayi "oh no!"


"Yes I do! Mijinki ba Ahmed shettima, yaron Hajiya kareema mazaunin Kano ma'aikaci mai wakiltar mashiga da mafitar kuÉ—aÉ—e abankin...." Dakatar da ita tayi da hannu "Eh kin sanshi sai akayi yaya?"


"Shima kuma ya Sanni ciki da waje ...Yes mijinki yayi ,kinyi sa'ar miji Ni kuma nayi sa'ar kwarto "


Miƙewa tayi suna kallon juna kamar zakaru a take ta nuna ta da yatsa "Ki shiga taitayinki ƴar budurwa ...choose your word carefully"


Lashe leÉ“en kasan ta tayi da halshe gamida rolling Idanuwarta ,ta cigaba da karairaya tana yabon halittar jikin Ahmed 


"ShiÉ—in dogone ,duck ,sexy kai bansan ya zan wassafa maki yanda mijinki yake ba ,amma nasan kema kin sani....oh Allah inama zan iya bude maki zuciyata kiga É—imbin Memories É—in da nike dashi akan mijinki da muamalar da muka shude lokuta munayi tare?" 

.kallon wawuya Fauza ta yi ma Na'ima kawai sai ta bushe da dariya 


"Gaskiya ke karya ce Na'ima ,me yasa na biyo ballagaza irinki har nike tunanin akwai wani magana meaningful a tattare dake ,Plz jeki da kwantanki mudai Allah ya bamu miji saura kuma ku Allah ya baku Æ´an baya ku huta da bibiyan mazan mutane..."  Wayar Naiman ne ya fara tsuwwa yina neman agaji 


Tana kallon screen É—in wayar tayi maza ta daura a Æ™irjinta ta rungume wayar 

"Oh my sugar plumbs"


Cabe Baki Fauza tayi ta juya zata tafi "hey madam Ahmed ,ga mijinki nan shi yake kirana!" 


"Mijina bazai taba kiranki ba"


Nuna mata screen É—in wayar tayi ,to zo ki gani mana


Kamar zata wuce kawai kuma zuciya Batada Æ™ashi sai ta dawo ta leka kanta jikin screen É—in tabbas Number mijinta ne 


A tsorace tace "É—auki kiran ki sashi a speaker" 



"Bazan É—aukan ba"


Muryar ta rawa ya kamayi alamar za tai kuka ta fara rokon Na'ima ta dauki wayar 


Kallonta tayi kawai sai ta É—auka "Hello Na'ima ki saurareni "


"Dalla yi mun shiru mayaudari kawai" 


"Duk na É—auka nidai yanzu ki fada mun a ina zamu haÉ—u ina son magana dake so Vital"


"Ni? Allah ya kyauta in yawo da wanda ajinsa bai kai ba ,kaje ka kwanta da wannan disgusting bad ugly looking house girl yanzu kazo kace mu haÉ—u ?...oh wow congratulations na tayaka murna da ta baka yaro sak kai"


"Duk naji dai don Allah ki rufamun asiri Na'ima ko nawane kike so zan baki" 


"Youre such a fool"


Da sauri ta kashe wayar .aikuwa Fauza É“arkewa da kukan da take riÆ™ewa tayi ta falfala wajen motarta da gudu tanaji tana kiranta amma ta kasa tsayawa 


Tana shiga gidan ta taras shikuma ya fice ,bakajin komai sai shewan su Nuratu da umjafar sai Æ™ananun kukan baby Fu'ad 


Ji tayi gaba-daya ta tsani rayuwar cikin gidan kwata kwata.

No comments