Recent Updates

Sugar Mommies W


12/20, 21:04] أم افنان✍️💞: *W*

Gadan gadan Fauza ta cuna kan motarta gaban gate en gidan ,ta fara zuba masa hon

.

Waigawa Naima tayi a mamakance "Ina ne gidan naki?" Murmushi tayi ,tana kallon gabanta ba tare da ta lura da rxtn ɗin fuskar Naiman ba ,saboda wage gate en da mr John Yayi.

"Ga gidana nan kuma kinga mun shigo" 

Muƙus tayi da bakinta ,lallai dara za ta ci gida ,kardai mijin Fauza ne crush ɗin ta?


Bata sake magana ba har Fauza tayi parking motar suka fito ,shikan mr John bai ma lura da Halittar da suka shigo tare da Dr Fauza ba ,don haka Yina kulle gate ya koma ɗakin sa ,su kuma Fauza tayi mata iso zuwa cikin gidan. 

Duk rashin kunyar Na'ima haka nan taji tana jin tsoron ganin Ahmed don tana kyautata zaton yanda aka bata labarin yina tsoron ɓacin ran matarsa in ya ganta a gidan zai iya zaneta ,don gani kawai zaiyi tazo ta kashe masa aure ne.


A ɗarare ta ɗosana ɗuwawunta akan ɗaya daga cikin jerin kujerun falon ,itakuma ta shige ciki tana ƙwalla ma Nuratu kira 

"Noor ....my Noor kuna Ina I'm home...Nasan kuna can kun ƙule ana hira" tana shiga ɗakin ta tarda Nuratu tana breast feeding Fu'ad um_jafar da tafito daga wanka itakuma tana shafa body cream.


"Oyoyo anty Sannu da dawowa"

"Yawwa sannu mai jego...babbar yaya sannu da gida" ta waiga tana ma um_jafar magana

"Sannu Likita ya patient yau kin dawo da wuri" 


"Wlh kuwa rabon dai zan hadu da wata tsohuwar schl mate ɗina ne ,tazo ƙasar muka haɗu a can ƙasan layi shine fa na kawo ta gida ,Plz in kin gama Breast feeding din my boy ki kawo ta ganshi" 


Jinjina mata kai Nuratun tayi "Ohk Anty"


"Yawwa nury ta ,bari inje in Bata ruwa ko zamu samu abinci?"


Dariya suka fashe dashi a tare "wallh kinsan cikin jego tuwon semo ne "


"Auchhh kuci kayanku " ta fita suna mata dariya don dama sunsan batacin tuwo .


Kai kayanta ɗaki tayi ta biya ɗakin Ahmed yina wanka don haka ta dawo kicin ta kwaso drinks da snacks a ɗan madaidaicin tray ta fito masu dashi.


Ta zauna kenan Nuratu ta fito mata da Fu'ad ,da tarkacen handk da feeding bottle kamar yina shan wani abu.


Miƙa hannu tayi ta karɓi fuad ɗin "Oyoyo my boy umuh umuh 💋 your momy miss you bobo"


Ta karbesa ta manna a ƙirji kamar zata basa nono.


Shaye da matuƙar mamaki ta kalli Fauza "A'ah kin haihu ne?" 

"Ohyeah ga baby kuma kin gani"


"But wow " tayi saurin tashi ta karɓi yaron cikin mamaki Ita dai ance mata ,matar Ahmed bata haihuwa to kodai ba su kaɗai bane a compound ɗin?


Kallon Fu'ad tayi kyakyawar gaske fari tar tar ,da sauri ta manna masa kiss 

"Kai yaron nan ya tafi da imani na gaskiya kyakyawane,kice ke ɗin mai jego ce kike yawo abunki lallai Turai ya lalataki..." Washe baki ta farayi kafin tayi magana yaron ya fara mutsu mutsu zai kuka 


Nuratu da bata ƙarasa shiga ɗaki ba taji yanda ake mata ƙarfa² da yaro aikuwa buttt! Sai gata ta fito 


Tayi sauri ta miƙa hannu zata karɓi yaron "Plz sorry I need to breast feed him ,yau rigima yake  sonyi " tayi maganar tana ɗan gyara size ɗin Nonon kamar irin sun cicciko mata ɗin nan


Galala Na'ima ta saki baki aikuwa Nuratu ta warce ɗan ta tashige ɗaki


"Fauza ban gane ba " cikin borin kunya tace "me ya faru kuma?"


"Naji tana cewa ɗan ta kuma" 

"Eh...eh ɗan ta ne" 


Gyara zama Na'ima tayi irin na munafukan matar nan 


"Hu'um kikace kuma ɗan ki?"

Wayancewa fauza tayi irin na ƴan duniya ɗin na haka,ta ƙaƙaro dariyar dole ta dinga ƙyaƙyatawa .


"Oh i can understand your confusion ,I'm so sorry 😃by adoption I mean" 


Haɗe gira tayi disturb still "kinsan dai I'm not good on ƙumbiya ƙumbiya plz be straight forward me kike cewa wai ?"


Gyaran murya tayi "uhm wato ko ....wannan da kike gani ƴar aiki na ce ,so she got impregnated by my security man, an kai ruwa rana kafin mijina ya yanke shawarar kawai mu karɓesa tunda dai basu da ƙarfin da zasu iya riƙesa..."


Katseta tai da sauri "Ohk to yanzu dai kina nufin kun karɓi yaron nan ne officially? What I mean Is that,kunje an baku takardu da sauransu shedar kun karɓi yaron daga hannun house girl dinku ya zama naku yanzu?"


Katseta tayi "OMG Na'ima wa'innan tambayoyi haka sai kace ƴar jarida ko mai neman wasu bayanan sirri?...Ni dai ga drinks " ta ɗan miƙe zuwa gaban table ɗin tana tsiyaya mata drink a glass cup .


Ƙur na'ima tayi ma Fauza da ido , take ta lula duniyar tunani.


‘Kai amma dai Fauza babbar doluwa ce ,nidai ina questioning mai aikin nan nasu ....amma ya kamata in maza in gudu kafin ta gano ina dating mata mijinta’ 


Miƙa mata cup ɗin lemun tayi tana kwarara mata kira da mamakin abunda ya lulata duniyar tunani har haka. 


Gigif tayi ta warce lemun a hannunta 

"Tunanin me kike haka"?


Bata amsa mata ba ta gwaɓa lemun a baki ta kurɓa kaɗan ta ajiye ta sake kafe Fauzan da ido cikin son gano gulma


"To kina nufin mai gadinku ya dinga kwanciya da shegiyar yarinyar can mai kama da suffar Munafukai a haka sum sum da ita?"


"Kai Na'ima kiyi a hankali da er uwarta a gidan ,kawai tsautsayine kuma mun ma tufkar hanci inshaalh"


"Tafdijam ,ynz dai kina nufin wancan mummunar halittan mai gadin naku jaujau dashi kamar bayahude shi ya kwanta da wannan fara tar ɗin yarinyar ...?"


"Haba Na'ima ki bar zagin su"


"Ai gaskiya ne ,kina ganinta wata cusashiya da ita ƙugu fakatantan kamar na kura ,to wai sune suka haifa kyakyawan babyn nan ? Jibeshi fa chubby dashi ji kalar fatar jikinsa mai kyau chocolate mai haske ....don Allah ta ina yaron nan ya samo kalar kyau ɗin nan da kuma kalar fatar nan ,tunda dai bai gaji uwa da uba ba?



Sosai Fauza ta dawo hayyacinta "me kike nufi ?"


"Yaron can bai kama da dukkansu ba,dole dai akwai yanda akayi ki sake tuhumar mai aikinki"  


Um_jafar da take shirin fitowa falon ne ta hangi Nuratu zaune akan ɗaya daga cikin kujerun dinning tayi crossing ƙafarta ta cusa ma yaro nono a baki tana kuka riris

Za ta tambayeta me ya sata kuka kenan ta jiyo hiran da suke yi 


Aikuwa da sauri ta janyo Nuratu kiyyy har falon


"Amm ammm a dawo da baƙo yasha ƙwai ,kikace mene? Ban gane maganar adoption da maganar sheganta yaro da ake ƙoƙarin yi ba a gidan ubansa? Ke daƙiƙiyar ina ne da bakiga ruwan kamar ɗa da ubansa ba?" 


Miƙewa Fauza tayi "Anty Ta ina Fu'ad yake kama da mr. John lillahi wa rasulihi fa?" 


"Waye wani mr. John ,ke Nuratu waye mr. John ?"


Cikin rawar murya tace "mai gadin mu kuma mahaifin Fu'ad ,Anty kizo muje don Allah karkice komai🙏🏻"


"Wallahi baki isa ba Ni fa na kasa gane matsayinki a cikin gidan nan sai ina Ahmed ɗin ina Yike kirasa a yi komai a gabansa yau za ayi ta ta ƙare" 


Ai a furgice Na'ima ta fara wayar ƙarya "Hello boo are you home? Gani nan zuwa yanzu"


Ta sunkuci jakarta da gudu zata fice 


"Baiwar Allah dakata ai dake aka fara dole sai an gama dake "


Bututtukewa tayi da masifa tana ja da baya "To wallahi baku isa ba Ni ina ruwana da violence ɗin gidanku daga nazo ganin ƙawata?"  


Fauza kallonta tayi "Na'ima ɗan dakata kawai.....My loveeee" ta soma ƙwalla ma Ahmed kira daga inda take"



Habawa Na'ima furgicewa tayi ta duka ta kwasa takalmarta tayi wufff ta falfala waje da gudun gaske


Ba um_jafar da Nuratu ba harta Fauza saida ta sha mamakin gudun da Na'ima tayi saidai wani tashin hankalin yafi wani ,Fauza waigawa tayi ta kalli um_jafar 


"Anty don Allah kiyi hakuri da halin ƙawata tun asalinta trouble maker ne wallahi da nasan zatazo ta tayar mun da fitina a gidana da ban gayyato ta ba Amma ina neman yafiyarku Plz"

[12/23, 08:5

No comments