Sugar Mommies V
أم افنان✍️💞: *V*
5days
Um_Jafar tazo gidan cikin ɗinbin mamakin ganin halin da ƴar uwarta take ciki da mijinta ,da yanda Fauza ke nan nan da Ahmed ko a gaban waye bata jin kunya ko shayin kishiya taji ba daɗi ba.
Itakuma tana lura da Nuratun bata iya gudanar da komai ta rigada tayi limiting kanta a ɗakinta ƙwara ɗaya jal da toilet .
Wannan yasa ta fara questioning ɗin ta ko basa zaune lafiya da Ahmed ɗin ne.?
Amma fafur Nuratu taki bada fuska ,don haka itama um_jafar ta lanƙwashe hannayenta ta jira taga iya gudun ruwansu.
Yau sunday ne babu aiki
Ahmed yina zaune akan armless chair a varendan gidan yina shan hantsi ,dagashi sai gajeran wando da T_shirt ,jarida yake karantawa jifa² mr. John yana jefo masa zance daga bakin gate ɗin sa.
Knocking sukaji anayi daga ƙofar gidan .
"Wanene?" Mr. John ya tambaya yina leƙen wajen ta hujin sauƙin gate ,Naima ce cikin wata matsatsiyar gown pitch ya wuce gwuiwa da kaɗan ,kanta yasha attachment har ɗuwawu ,fuskarta zuii da makeup dukda light ne amma tayi kyau sosai ,tana tsaye tana taunan bubble gum
Ta wajen ta amsa shi da "Baƙuwace buɗe ƙofan?"
"Baƙuwa daga ina ?"
"Hey young man can u open? I wanna meet your boss you're telling me silly" Tsurewa yayi don ya tabbatar matar nan Jarabbabiya ce
Zumbuɗawa yayi gaban Ahmed da gudu "sir wata ruwan ƴan bariki ce tazo wai wajenka tazo in buɗe mata?"
"Wata kuma? Ni ba wacce nayi zatazo wajena ,ammaaaa...buɗe mata"
A guje ya kwasa yaje ya wangale mata ƙofar ta shigo
Cikin wani irin salon tafiya mai jan hankali ta nufo inda yake ta hau takalmi mai tsinin gaske ,sakin baki dahanci yayi cikin tsananin mamaki ya ma kasa magana kuma ya kasa motsi a wajen har ta ƙara so gabansa
"Hey durling" tayo magana tana miƙa hannunta a gaban rigarsa tana ƙoƙarin taba masa ƙirji
Bakinsa rawa ya kamayi ya nunota da yatsa "You again?"
Kaɗa masa Idanuwarta tayi "Yes baby" tayi magana ta na ƙoƙarin kai hannunta jikinsa ,wani tsawa ya daka mata
"Don't dare torch me ,wallh kina taɓa Ni zan dalla maki mari"
Dakatawa tayi kamar wata Mutuniyar ƙwarai ɗin nan mai jin magana
"Sorry i didn't mean any harm to you ,ka ji Ni shiru kwana biyu ko ban dameka da kira ba? Nayi sabon kamune shine da muka gama dashi nace bari in biyoka gida in fada maka zamu iya haduwa daga yanzu kaine a layi "
"Tir da halin banza irin naki ,Allah kar ka bani ikon haduwa da gantalalliyar mace irin ki a rayuwata ,Ni na sanki ne da zaki biyoni har gida kina neman kashe mun aure?"
Ɗaga masa hannu tayi da alamar dakatarwa
"Dallah malaminsu ɗan rage sautin ka ɗan bar mun ihu akai"
Waigawa Ahmed yayi ya kalli mai gadin da ke tsaye yake kallon drama
"John meye amfanin ka ? Kana kallo ana cin mutuncin oganka akan gaskiyar sa kana tsaye ?"
Kai hannu yayi ya fizgo hannun rigarta "kai yanzun nan zaka jika a gidan maza (prison) can't you see he's harassing me?"
"Dallah zo ki fita "
"Sharraf"
"Out...out quick zo ki fita kawai"
"Kai dallah rufemun bakin ka da muryarka kamar na karnuka ,zan fita a wannan ƙuntataccen gidan yanzu kuwa"
Handbag ɗin ta ta zuge ta ciro rafan kudi iri daya da wanda ya bata kwanaki ta shiga karkaɗa masa a fuska
"Saboda wannan mint ɗin kudin da ka ba nine kake jin kai wata tsiya ne? Dalla jeka da talaucinka ,Ni nafi karfinka ,coz I'm dating someone responsible,gayen da Yike more handsome and hot ,ba lusari ba irinka ,mutunin da bazai iya sa matarsa tayi ciki ba ....mtseww Lusari kawai" ta wulla masa kuɗin a fuska .
Sandarewa yayi ya kasa ko motsi ,yina kallo ta raɓasa tana wani irin cat walking har ta fice ,shikuwa mai gadi sai barking enta yakeyi na borin kunya,tana zuwa jikin ƙofar fita ta nuna mai gadin da yatsa ta karkaɗa masa yatsan "I must punish you ,zakasan ba kowa ake ma hargowa ba ,bastard kawai!"
Da sauri Nuratu ta fito ɗakin da babu Fu'ad a kafadarta ta gama basa nono kennan tana shafa masa baya tanaso yayi gyatsa taji hayaniya ya cika masu gida ,ga um_jafar tana wanka itakuma Fauza ta fita shopping so gidan ba kowa da zata tambaya meke faruwa don haka da sauri ta fito
Tana fitowa Na'ima tana ficewa a gidan ,anan tayi arba da Ahmed yayi sukuti ba uhm ba uhm uhm
"Ya Ahmed meke faruwa a nan?"
Cikin fusata ya raɓata ya wuce ciki ,tunda yake a duniyarsa baa taba cin masa mutunci ba irin yau wai shine lusari bazai iya ma mace ciki ba?
Bin bayansa tayi da kallo kafin ta kalli mr. John kamar zata tambayesa mai ke faruwa kuma sai ta share ta koma ciki da sauri don tun sanda cikin Fu'ad ya ɓullu a jikinta kuma aka alaƙanta shi da na mai gadi ta tsani mai gadin,sam basa magana ko ya kulata bata tankasa.
Fauza na shawo kwanan gidansu itakuma Na'ima na fitowa .
Ko cikin dubu taga Na'ima komun ɓacewar zamanunnuka sai ta ganeta ,don haka da sauri ta ringa sakar mata ham .ɓiyyyy ɓiyyyy ɓiyyyyy
Cak taja ta tsaya ,har yanzu da fushin Ahmed kwance a ranta ,nikuwa nace me yayi maki wai?
Miƙo fuskarta tayi ta glass en motar "sissssss hey babe "
Daƙwaƙo ido tayi cikin son ganin mai kiranta ,kawai sai ta sheƙo da gudu
"Oyoyo my love "
Fitowa tayi da sauri suka rungume juna tsantsan ,Naiman na ɗan bubbuga ma Fauzan baya
"Nayi kewarki badly"
"Baki kaini ba asswe...amma dakata da wucewa zakiyi bazaki zo gidana ba ? Ina Alkawarin da kikayi mun?"
"Sorry i missed your contact "
"To ynz ina kikaje a layin mu?"
Tsaki taja fuskarta a take ya hautsine da bacin rai "Just forget"
Baya Fauza tayi da sauri tana washe baki "I do I do zo muje gidana ma ƙarasa labarin"
Bamalli's care
09065990265
No comments