Recent Updates

Sugar Mommies S

 


افنان✍️💞: *S*

Nuratu da Ahmed sun gurji amarcinsu son ransu har yamma ,in Ahmed yayi yayi yace "kai Nuratu kin ƙara daɗi na yarda akwai sirrin daɗi a jikin masu matashin ciki" tun tana jin kunyar katobarar sa har ta soma sabawa ,yau sam batajin kasala ,ras takejin

kanta ashe duk ƙananun laulayin nan rashin miji a kusa ne ,tana ganin yamma tayi kennan Fauza ta kusa dawowa ta soma jin ƙunci a ranta kenan Fauza zatazo ta katse masu jin daɗi ,yanda ta kasance da noor haka ma ta ɓangaren Ahmed don haka oya oya sukayi wanka tare suka sauya kaya aikuwa yina cikin tayata kimtsa ɗakinta sai ga Fauza ta shigo .da fara'arta tayi ɗakin noor da sauri 


"Oyoyo my Noor " taje ta ɗan raɓa jikinta da kafaɗar noor ɗin ta rungumeta 


"Anty sannu da dawowa"

"Sannu da gida noor ya jikinki? Ina can ina aiki amma hankalina na wajenku keda unborn ɗina,gashi bansa mu excuse ba bare in kiraku a waya ...to ya jikin?"


"Anty na warke yau ban ciwo ba ,ya Ahmed ya..yi...ya..yi " daburcewan da tayi ya samo usuline sakamakon ƙur da Ahmed yayi mata da ido daidai sanda ya shigo ɗakin.


Waiga bayanta tayi jin yanda ta daburce tasan mala'ikarta ta gani ,ilai kuwa shine don haka Fauzan haɗe rai tayi


"Haba my champ meye kake mun haka? Wai yaushe zaka sakin ma yarinyar nan mara ? Kullum harara gaskiya banjin daɗi ,ko baka ƙyaleta don Allah ba ka ƙyaleta don cikin jikinta...amma kai kamar mai mood swing"


Murmushi yayi "An daina uwargidata"


"Uwargida kuma Amarya gwara kana ƙarasawa don bana son barin wani giɓi"


Fauza ta bashi amsa cikin raha da barkwanci ,itakuwa Noor hakanan taji batajin dadin taɗin Fauza , Don haka dukar da kanta tayi kurum


Shikuma Ahmed da ya rasa amsar da zai bata ga noor ta gama tsaresa da ido kafin ta sunkuyar da kai yasa cikin rawar baki yace mata "Au haka!"


Ɗaukan jakar aikinta tayi ta biya ta jikinsa ta rungumesa ta masa kiss a saman goshi "Nayi kewarka mijina ,bari inje in wanka I've gist da zan baka" murmushin yake yayi "Nima nayi kewarki love"  tana fita yabi bayanta da kallo batare da ya bita ba 


Ɗagowa noor tayi ta kallesa "me kake jira kuma? Ka bita mana. .hohoho Wai lovveee ah ah ba love ba hate"

Ta kwaikwayi maganarsa cike da tsiwa


Sakin baki yayi "Aah Nuratu kishina akeyi? Meye don nace mata love kema ba Happiness nake kiranki ba ?"


"Aah Ni bana wai kishinka amma atleast ku rage wasu abun a gabana ,kuma Ni  a gabanta ai Nuratu kake kirana"


"To shikenan zan koma ce maki Happiness din a gabanta "


"Karka ma so ma ,bana so kirani da sunan yanka na ,Nuratu ya fi kawai"


Murmushi yayi "uhm uhm baby rigima.." shiru yayi jin Muryar Fauza na ƙwalla masa kira "My champ zo muje ka cuɗa mun baya na soson baya kaiwa "  


Tsayawa yayi yana kallonta ,aikuwa ta banka masa harara 


"To kaje mana Ni mai ka tsaya mun a kai ƙerere?" Gyaɗa kai kawai yayi ya fita 

"Lallai akwai bala'i kwance a ƙasa ,wato itama Nuratu ta iya kishi? Ni yaya zanyi ne?" Da zancen zucin nan ya tafi dakin fauza,yina shiga ya tarar da ita tana zaune a gefen gado tana amsa waya da wata ɓingilar towel  fari tar ta ɗan ɗaura daga ƙirji zuwa kwatan cinyarta ,ta cusa gashin kanta a hular wanka 


Samun stool din mirror yayi ya zauna yina kallonta ,yina jiran ta gama wayar 


"Na'ima my friend Ina jinki "


Na'ima are u kidding ? Kina nufin kice mun kina gari? I just can't beleif it,how many years has it been?"


Ta ɓangaren Na'ima ɗin ce ta bata amsa

"It actually 4yrs ,banzo Japan ba fa "

"Oh wow naji daɗi sosai kuma a gidana zaki sauka gaskiya hmm ,har kin sani na fara tunanin irin daɗaɗan hiran da zamuyi dake "


"Yes exactly ,karki damu ai dole In zauna a gidan sahibata amma ƙarya nike maki Ba yanzu zanzo ba amma dai zanzo soonest possible"



"Kai na'ima wallhi bakiyi ba ,kin sani gabaɗaya na ruɗe meye haka ,this is childish attitude"



"Hehehhe I'm a baby girl for life" 

Itama Dariyar Fauza ta ƙyaƙyace dashi jin kurin Na'ima wato ita bata taɓa yarda ta girma


"I still can't belief it nasan yanzu kinyi kyau wai me kike yi ne ina kika ɓoye ,fara mun kwatancen yanda kika koma in rage mamaki ranar da muka hadu"


"Wallahi muna nan muna enjoying rayuwar mu ,kinsan in baka da aure kafi samun ƴanci to ina nan na zama wata shegiyar me kyau ga kudi ga class"


"Oh i see,Inaso fa mu haɗu ki tuno mun da memories din baya,tun daga zagin teachers da mukeyi a aji,makara da guduwa kafin a tashi school ...Hmmm inason inji abubuwa fa ,yaushe zaki zo to? "


"Uhmmmm yeah ynz Ina tare da wani Alhaji ne a Dubai muna ɗan cilawa amma daga nan zai wuce Spain to kafin In koma 9ja Ni kuma zanzo gidanki 


Ai nima inason inga yanda ƴar gayun ƙawata ta sauya tana nan ƴar caras ko aure yasa kin zama cusss!"


"Haba wane ke ina nan caras ras dani I met a caring husband I tell you"


Tayi maza ta katse maganar don sosai tana kishin taji matan auren ƙawayenta suna yabon mazajensu"Thats good for you durling bye" 


"Na'ima you're crazy ,as crazy as ever "


"Kai kai niɗin wallahi bazan yarda ba"

Tayi magana cikin shogoɓa

Dariya Fauza ta daɗa fashewa dashi


"Bye bye Allah ya shiryeki"


A taƙaice ta daƙale hiran ganin Ahmed ya fara hura hanci



Itama Na'iman dariya tayi ta cikin wayar 


"🤣bye see you"


Haɗe rai yayi "Dawa kike magana?"

"Ƙila zaka iya tuna Na'imaaa,childhood friend maƙoftane mu sanda muka zauna a nasarawa GRA kafin mu rabu amma har muka gama secondary school dinmu daya ina sonta sosai but she's crazy Ina fada maka"


Caɓe baki yayi haka kurum yaji bayason hiran ta 

"Kin fasa wankan kenan?" Ya tambayeta a taƙaice. 


Zumbur ta miƙe "oh no zanyi Mana kaima ka cire kaya muyi tare "


"Muje in tayaki Ni ban daɗe da wanka ba..."





Wazai iya canko mana badaƙalar da ke kwance a shigowar Na'ima rayuwar su Fauza bayan shekaru biyar basu haɗu ba???



No comments