Sugar Mommies P
3] أم افنان✍️💞: *P*
Ahmed saida ya sauya kaf securitan gidansu da ma'aikatan gabaɗaya .
List ya basu na duk wasu members na family and friends dinsu ,duk wanda yazo indai bashi a cikin list ɗin to karsu barshi ya shiga sai in sunyi waya dashi .
Tsaurin fa yayi ma Hajiya kareema yawa amma ba yanda ta iya saboda kunyar Ahmed ɗin ma takeji don dai tasan yasan komai game da abunda take aikatawa a ɓoye in basa nan.
Yina zuwa gida bai awa uku cikakku ba ya ɗauki Nuratu suka juya Japan ,Dole yina buƙatar transfer a dawo dashi Nigeria kawai yanda zai kula da mahaifiyarsa sosai .
11 am
Ya masu a cikin gida ,Ko'ina ba tsari ga ƙura ya kwanta har wajen kayan Electronics din da suke falon tabbatuwar tunda suka tafi falon baiga ko dusting ba ,bare arziƙin shara da mopping .
A falo Nuratu ta zauna tayi shiru gamida rafka tagumi ,to gadaita ta dawo gidan a matsayin matan gidan mai cikakken iko ba ƴar aiki ba.
Kicin ya shiga ya hado mata tea ya kawo mata falon ,kallonsa tayi cikin tausaya wa
"Me yasa baka Barni nayi ba? Kuma Ni nace maka ina jin yunwa ne?"
"In ke bakiji baby na yina ji."
Girgiza kai kawai tayi ta karba ta soma sipping a hankali gabanta na mata wani irin matsanancin faduwa .
"My happiness" kasa amsawa tayi saboda kunyarsa da take ji .
Maimaita kiranta yayi a can ƙasar maƙoshinsa ,A galabaice ta ajiye cup din ta kafesa da ido
"Ina so zan raba maku kwana da Fauza"
"A'ah don Allah" ta bashi amsa da sauri
"Wai me yasa?"
"Anty bazata taba yarda da maganar auren mu ba ,kawai dai na yarda zan cigaba da zama a matsayin mai aikinku in na aihu kuma zan bar mata ɗan / ƴan "
Shiru yayi yina mamakin saukin kai irin nata "Baki ganin an shiga haƙƙin ki?"
Girgiza kai tai tana ɗan caɓe baki da Alamar irin ko a jikinta ɗin nan
"To shikenan zanyi maki kamar yanda kike so inshaalh" ya idasa magana tana ɗaukan meatpie tana kanga mata kusa da bakinta ,fuskarsa dam annuri kai daga ganin alama ta faranta masa rai
Fakaitan idonsa tai ta caɓe baki a ranta tace "Dama abunda kake so ne na fada maka ,kana tsoron Matarka ba ka son ta san ka aureni zamu ringa sharing Dinka Ni da ita ,to muje zuwa .."
****
Sai yamma sosai Fauza ta dawo ,lokacin Ahmed ya fita ya bar Nuratu tayi barci ,shikuma yaje nemo mata kayan ƙwalam ,ita kuma tana ganin ya fita ,ta miƙe ta saita gidan ta goge koina ta feshe lungu da saƙo da turare ,sannan ta je tayo wanka gamida sako Abaya mai yalwa ta fito living room din gidan da darduma ta yi sallar la'asar sannan ta zauna tana bin karatun Kur'ani ƙira'ar Sheikh sudais tana bi a hankali da ƙur'ani a gabanta.
Fauza tana shigowa compound din taji ƙamshi na tashi daidai da iskar gidan ya sauya ...Hmm tsafta rahma ce .
Da sallamarta ta shigo tana turo ƙofa ,Nuratu ta ɗago ido sukayi 2 eyes
Washe mata duk hakoranta tayi ta taho da gudu ta rungumeta
"My noor ,sai kika gudu kika Barni ko? Kinsan ya zanji kuwa? Babu ke babu my champ ya kuke so Inyi?" Muryar ta rawa ya kamayi alamun za tayi kuka "ko ina muku wani mugun haline da baku so ,plz ki fada mun in bari"
Sosai maganganun ta ya kashe ma Nuratu jiki tausayinta a take taji ya lulluɓe ta .
"Muna sonki mana sosai antyn mu ,I missed you Antyna ,plz kiyi hkry guilty question ne yake damuna na abunda nayi shi yasa na gudu kuma Ya Ahmed ya dawo dani"
Shafa mata baya ta shigayi cikin lallami da kulawa "Tsautsayine fa wanda baya wuce kan kowa ,nasanki keɗin natsatsiya ce ,kuma yaronki namune Ni na haifesa ba wanda zai sani a 9ja i promise"
Hawaye ne ya fara ɓulɓilo ma Nuratu na tausaya wa Fauza ,ita tana nufin taimaka mata kar ta wulaƙanta ,amma ita kuma ta haɗa mata miji da ita ,anya tayi mata adalci kuwa?
A wannan yanayin Ahmed ya riske su .
A da yayi mata tanadin rashin mutunci duk bala'in da za ayi sai ayi amma gwuiwansa yayi sanyi ganin yanda suka kulle cikin begen juna ,girgiza kai yayi "Allah ka haɗe mun kan Matana ya rab"
****
Fauza kuwa me ya faru bayan tafiyar su Nuratu?
Yina barin gidan itama ta fice ta figi motar a firgice sai hospital dinsu ,tun a shiganta ta ci karo da Dr lateef (Collègue ɗin ta ne yasan komai akan problem dinta ) ,yanda yaga ta wuce office a zaf zaf yasan ba lafiyaba don haka da sauri yabi bayanta
Tana shiga cilli da jakanta tayi akan table ɗin ta daura kanta akan table kawai ta rushe da kuka .
A haka lateef ya risketa ,don haka jikinsa yayi sanyi sosai ,jan kujera yayi ya zauna ya yi shiru bai ce komai ba ya barta tana rizgar kuka ,sarai tasan mutum ya shigo office din Amma ta kasa dakatawa da kukan sannan ta kasa ɗago kanta ,bare tasan ko wanene?
Sunyi zaman shiru kamar na 15mns kafin yayi gyaran murya "Dr. Fauza take heart plz , everything will be alright ok? ...kiyi shiru "
Cikin fuska mai majinjinu da hawaye ta ɗago ta kallesa "Dr kasan raɗaɗin rashin haihuwa kuwa? Dr kasan daɗin da nishadin da uwa take riskar kanta a ciki in tayi shinning eyes dinta a cikin na yaranta?..."
"Sorry lokacine ..."
"No doctor how I wish ...I wish I could turn back the hand of time ...da ban sha maganin hana ɗaukan ciki ba a baya ,da yanzu naga yarana suna ce mun momy ina jin daɗi" ta ƙare maganan tana dariya kuma hawaye na zubo mata a lokaci guda. tana misalta gata can cikin tsakiyar yaranta suna wasanni tare
Karki ɗaga ma kanki hankali da ƙaddarar da bazai goge ba ,ki tsaya ki fara tunanin future life ɗinku da mijinki"
"Haba doctor ,kana nufin Fauza will never ever conceive? Sannan kake cewa kar in tada hankalina in tunanin rayuwa mai kyau a gaba? Wani fruitful life zan enjoying apart from being with my children oh come on!"
"Fauza plz why these changes ? Mijinki bai matsa sai kin haihu ba "
"Amma yina son Yara tunda gashi yau ya gaura mun mari saboda mai aikina tayi cikin shege yace mu riƙe ta in ta haihu ta bamu ɗan ,to end the story short yarinyar ta gudu shikuma ya tafi nemanta yabarni a nan ,wannan ƙaramin abune da bazaisa hankalina ya tashi ba?"
Wani ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya ya ajiye kafin ya lumshe ido ya kalleta
"Dr Fauza ki buɗe mun zuciyarki in baki shawara na ƙwarai "
Jinjina mashi kai tayi irin tana biye dashi ɗin nan
"Dr duk wata wacce ta rasa haihuwa ku likitoci ku kuke basu shawaran suje gidan marayu suyi adopting child ,ke me yasa baza ki karɓi yarinyar mai aikinki ba ,bai tunanin yafi sirri ba sai kinyi cike ciken Form ba? Atleast kinsan tarbiyyar mai aikinki ,baza ki dauko yaron wanda maybe babanshi gawurtaccen dan fashi bane ,is that not a great favor to you?"
Lumshe Ido tayi tana girgiza kai cike da gamsuwa
"Dr kana nufin in amshi yaron Nuratu ?"
"Capital Yes Ma'am"
A kan wannan dalilin yasa Fauza zubar da duk makaman yaƙinta ,tayi niyyar zama da Nuratu tsakani da Allah har ta aihu ta bata yaron / yarinyar .
No comments