Sugar Mommies O
م افنان✍️💞: *O*
Washenkari
Zeemaama da ƙure daɗi kusan kwana sukayi ana abu guda ,saidai nishinsu ya farkar da zuli ,haka zataja siririn tsaki ciki² ta juya masu baya .
Don haka safe sai wajen 9 ƙuredadi ya fara wanka ya fice bayan ya rokesu alfarmar zaije ya sauyo kaya zai dawo nan da awa guda.
Zeemaama rungumesa tayi ta basa sumba suka rabu ta wuce toilet tayi wanka ta sauya kaya taci break ɗin da zully tasa aka kawo masu ta sake miƙewa a gado ta cigaba da barcinta.
Karmu manta batayi sallah ba fa,ta sa ke miƙewa a gado.
Zully na ta hidindimun ta kamar babu komai a ranta .
Tana ganin tayi barci taje ta ɗauko sigari da lighter ta ajiye a gefe ,ta samo kwalbar giya da glass cup ta ajiye a bedside ɗin da Zeemaama take ,in ka shigo zaka rantse da Allah Zeemaama ta shawune tana barci .
Tana jin ana taɓa ƙofa tayi maza ta kunna sigarin nan ta laɓaɓa a hankali ta soka ma Zeemaama a baki .
Hayaƙin sigarin haka yake tashi sama fuuuuu...baya Zully tayi da gudu tana rufe baki tana tari .
Jan gwarti Zeemaama tayi da ƙarfi takuwa ja hayaƙin sigarin har cikin ta ,hangame baki tayi za tayi tari aikuwa wutan taban ya coye mata leɓe batasan sanda ta fashe da ihu ba .
Ƙure daɗi kam yina shigowa yayi arba da bakin Zeemaama sagale da taba ,tana kwance hayaƙi na bulbula.
Baya yai da sauri yina bibbige gefen hancinsa da hannu saboda ya kore hayaƙin .
Zugin raɗaɗi ya sata mulmulowa a gado sai ji kake tifff! Ta rimo ƙasa ,kamar kayan wanki
Aikuwa ta 'karasa buɗe baki ta fasa ihu tana tari ƙwahal! ƙwahal!!
"Wayyo ƙure daɗina ƙure daɗi na!"
Da gudu zully ta shigo "Haba Abu saida nace karki shawu kika ƙi ji"
Shafa leɓenta tayi da ya kwaile da wutan sigari
"Habawa zulai banda giba ,nine zakiyi mun sharri saboda kinga nayi sabon saurayi ɗanyen jini?....kayya yanzu na Gane makircinki...kaji ƙure daɗi shigo"
Kafewa yayi a ƙofa "Ni?! Ai bana shiri da warin sigari kedai ki biyoni in kin matsu "
Daƙyar ta muskuta ra dafa gado ta mike ta dauki siririn veil ta cukuikuya a kanta a dole tayi rolling kai ƙwandalele ba tudun ribom ya tafi shapeless
Kama hannunsa tayi suka fito suna tafe suna ɗan hiransu na masoya ,har gaban kujerun hutawan da ke gefen hotel ɗin inda jiya su Noor suka zauna da Ahmed .
Nan suka yada zango aka kawo masu drink a ƙananun can da dogayen straw kamar yara a wajen birthday.
Saita bakinsa zeemama tayi da bakin straw ɗin tana masa magana cikin kirsa a dole ga er duniya za'a ba Handsome abu a baki .
"Let's talk about sex baby...let's talk about you and me" haka ta hangame baki tana masa waƙa ta kai yatsanta kan kuncinsa tana jajjan masa kumatu kamar mai rarrashin small baby
Shikuma yina wani kumburi yina kakkautar dakai tana doɓala masa a baki .
Nuratu gajiya tayi da zaman room ɗin ta fito mike ƙafa ga yunwa na ƙwarzabanta ga ciwon kai ,don haka tayi deciding ta fita mike ƙafa ko zai kawai mata da yunwa da ciwon kan
Tazo daidai sit ɗin su karaf idonta ya sauka akan wata balamar mata tana lallaɓa ƙaramin yaro ɗan cikinta.
Sosai ranta yaso gane mata wacece ,yanda zataji daɗin bada labari
Wa idonta zai gani?
Inna Abu!
Batasan sanda takai gabansu ba saidai inna Abu taji an ƙwalla mata kira "Inna Abu?!" Noor ta doka mata kira gamida bugun ƙirji da alamun mamaki
Ta tsorata gaya ,amma ta wani dake ta caɓe baki "ke lafiya? Meye kikazo kina Min hayaniya a kunne kamar saukar markaɗe ...baby sorry it sound like thunder ko?" Ta waiga tana kallon ƙure daɗi tana matso turancin dole "
Sarai ta gane Noor kuma tasha mamakin wayewar noor amma sai tayi mata irin na ƴan bariki
"Inna Abu baki Gane Ni ba?"
"Gashi kuma kin fada ƴan mata waye ke Ni ba abu bace sunana Zeemaama"
"Hukumullahu la ajabun ,au Zeemaama? To Zeemaama kin Gane Nuratun ki ko?"
"Ke ban sanki ba saki bar wajen nan or you want me to call d security and bounce you out of here"
Jinjina kai Nuratu tayi ta juya kawai mamaki ya kosar da ita sam ta daina jin yunwa.
No comments