Sugar Mommies N
م افنان✍️💞: *N*
Tun a bakin gate da ya tambayi mai gadi uwarsa ,yanda yaga suna kame² ya fahimci lallai sun kwana biyu basa gidan.
Girgiza kai yayi a wajen ya koɗa mata kira .
Hajiya Kareema ta firgita ganin Number autar ta na 9ja
_Why he came without notice?_
Kara wayar tayi a kunne tana daidaita muryarta dukda a ƙwale take
"Hello autan momy"
"Momy good evening gani a gida nazo ba kowa kina ina?"
Daburcewa tayi "oookeeey...naje gidan ƙawata Zee sai gobe zan dawo can you sleep over night there?"
Salati ya fashe dashi jin muryarta na ƴan maye "Mom kina Ina ? Ki faɗa mun inda kike inzo in ɗakko ki "
"Son don't mind me kayi barci gobe zan dawo"
"Mom I'm not comprehending kawai kina ina? Dont tell me you're drunk"
Tsawa ta daka masa with all her brags "Ba shaye² ba giya nasha kaji ko?"
"I'm sorry mom kamar haka nace"
"Ok clear your doubt I'm going" ɓit ta kashe wayar .
Hankalinsa in yayi dubu ya tashi da sauri ya sake kiranta saidai ta kashe wayar ma gaba ɗaya.
Kareema Madam Gwale Idanuwarta ta ringayi tanason dawowa hayyacinta ,amma ta kasa tunani mai kyau ,don haka hannunta ta ɗaura a kanta ta soma bugun kan,tana ƙoƙarin daidaita nutsuwarta .
Bazan samu nutsuwa ba yarana suna state ina cikin hotel they're noterious , mutanen su zasu iya ganina and zasu faɗa masu .
Miƙewa tayi da sauri ta canja shigarta ta ɗaura Abaya ta fito tana tangaɗi tana bin bango ta fice a hotel ɗin .
Ahmed a zafafe ya dawo wajen gate din yana kwarara ma ma'aikatan gidan kira
Duk tsaitsayawa sukayi a bakin gate cikin tashin hankali
Yina zuwa ya shaƙo wuyar mai gadin "ina mamata take? Meye aikinka a nan?"
Kakari ya shigayi ya matse masa wuya kam kam ,haƙuri suke bashi amma yaƙi sakinsa ,can ƙasan maƙoshi yake ce masa "Zan faɗa...zan faɗa"
Wacakalan dashi yayi yaje ya bugu da ƙofar ɗakinsa "Oya ina sauraro ko sai na kira police sun tarkata mun ƙeyarku shashashu kawai?!"
"Eh wato Eh dama ...Drivernsu ne ya fita dasu Nadaiji suna cewa ya kaisu hotel"
"Driversu? Ko drivernta? Su nawane?"
"Ita da ƙawayenta su uku anan suke kwana"
"Ina drivern?"
"Yaje gida baya kwana a nan" dafe kai yayi duk dauriyarsa baisan sanda hawaye ya fara tsalalo masa a ido ba , wannan wani irin abun kunya ne ,da kimammu mun bari ana cin zarafin mahaifinmu da ya rasu?!
Kenan ma'aikatan nan a Sara,suke kallon mu duk sunsan abunda mahaifiyarmu take aikatawa.
Fiddo wayarsa yayi yafara laluben numvobin ƴan uwansa da basu ƙasan saidai duk basa tafiya don haka a fusace ya taka ƙofa zai fita da ƙafa daidai nan taxi ɗin hotel ɗin ya faka a gaban gidan ta fito daga ciki tana layi
"Mom!" Ya ƙwalla kiran sunanta daidai sanda ta shirmu a ƙasa ,drivern fitowa yai yina ƙoƙarin taitayota aikuwa ya daddage ya tsinkeshi da mari kamar shi ya aiketa hotel ,ɗago shanyayyun idonta tayi tana dakatar dashi da hannu "Son, stop naah" Kawaï sai ta fara sheƙo masa amai
Yina kuka ya ɗauketa ya shige da ita gida yina zage² "bazan yafe ma duk wanda ya koya ma uwa ta wannan mummunan ɗabi'un ba ,sai nasa an kamo su na kullesu"
_kunji ƙarfin hali wa ya koya mata shaye shayen da bin ƴaƴan mutanen?,ita ta koya masu ko su suka koya mata.Such a selfishness_
No comments