Recent Updates

Sugar Mommies J

 


أم افنان✍️💞: *J*

Nuratu koda ta sauka a garin Kano ta kasa zuwa ƙauyansu saboda zullumin abunda zata taras ,don haka Nassarawa GRA ta nufa gidan Abu_Jafar

Tayi mamakin yanda suka samu walwala arziki yaci uban na da .

Um_Jafar tana ganinta ta fashe da kuka suka ƙanƙame juna 


"Ƴar uwata ashe zan sake ganinki? Ina kika shige duk shekarun nan?"


"Long story Antyna plz taimakeni da mix fruit mana I was craving wlh tun a jirgi da na ga wata tana sha" 


Dafe baki tayi cikin mamaki kawai sai ta fashe da dariya "But wow😍 ƙanwata alamu sun nuna duk inda kika kasance tsawon shekaru biyar ɗin nan ba ƙazamin hannu bane"


"Hum Anty nace maki dai akwai labari kala kala da na kuka da na jimami ,na farincikin ba yawa ki fara bani abinda na buƙata Ni ban zatama zaki gane Ni ba ,kuma nayi mamaki da masu gadinku suka Barni na shigo ba bincike"


"Hmmm jini ɗaya?! Na raba ki da jini Allah dai ka jiƙan babanmu 😭 " kawai sai muryarta ya sarƙe zata fara kuka 


"Aah Anty ba ƙoshin lafiya nake dashi ba in kuka zakiyi sai In bar maki Gidan ,in tun kafin in fara koro maki zance kika sani kuka to gaba me zanyi kuma?" 


Share hawayen ta tayi da bayan hannunta ta ƙaƙaro murmushi ,ta miƙe ta taɓa wani abu a falon kamar door bell 


Turanci abun yayi "Your message was delivered" 


Kenan anji ƙarar ƙararrawar a inda tayi transmitting 


Minti biyu sai ga wata matashiya cikin uniform mai gida gida 


Daga gani Cook ce daga madafa take 

Tana zuwa gaishe da Noor tayi sannan ta kalli um_jafar 


"Anty gani"


"Munyi babbar baƙuwa ayi gaggawar kawo mata fruit salad a hado da kayan motsa baki sai ai mata sassaukan girki"


"Yes ma!" Ta ɗan rusuna kadan ta fita a ɗakin .

Minti goma sai gashi ta dawo da fruit salad din ta jajjefa masa ƙanƙara sai tasa madarar gari saboda kar yayi ruwa sosai 


Habawa Nuratu sauke mayafin kanta tayi ta baje a ƙasan carpet ,cikin haɗama sai kace wacce zataci da wasu ta fara cika cokali tana sha hannu baka hannu ƙwarya tana faman zuba santi


Saida ta kusa shanyewa sannan ta ɗago ta kalli um_jafar 


"Wai ina mutunina Abu_jafar bawan Allah😃"


"Hhh yina Spain"


"Oh wow ke kuma kina me a nan?" Ta tambayeta tana tsatsare ta da ido


Dariya ta fashe dashi 


"Bazai yuwu inzauna a inda suke ba amma ina paying masa visit time to time wani daji ne aka yankan masu ake so su maidashi gari ,don haka gidaje,asibitoci ,kasuwa da makarantu da su bohol suke aikin ginawa yafi shekara biyu baizo Nigeria ba amma dai mun samu walwala komai ya dawo fiye da da,ko yanzu ban sati Uku da zuwa ba rabon dai zamu haɗu ne ya kawo Ni"


"Uhm Congratulations to all of you,to Ina yaran ko basa karatu sai yawo tsakanin Spain da Nigeria?"


"Kai Nuratu Yaushe kika zama mai tambayan ƙwaƙwa haka sai kace ƴar jarida ?


"Kamar kin sani ɗalibace mai sanin makaman aiki" 


Dariya suka fashe dashi suka tafa "ohk nidai a bani labari wannan desperate canjin yabani mamaki"


Miƙewa Nuratu tayi dukda gabanta hakanan taji ya faɗi amma ta miƙe ta gyara rigarta cikin tsokana ta fara wani karairaya tana juya mata bombom ta sigar wasa


"Sai nayi wanka an kawo mun Farfesu na bige 😃nayi sallah nayi barci sannan In na farka zamusha labari"


Sakin baki tayi tana kallonta,cike da sha'awar ta sosai taji noor ta burgeta komai nata mai kyaune ,yanda take gudanar da rayuwarta kamar wacce batayi rayuwa a ƙasar nan ba .


"Hey young lady Jan ran ya isa "


Fashewa tayi da dariya daidai sanda aka shigo da abinci yina tiririn ƙamshin daɗi


Da sauri takai mata yatsa baki "Shishhhh🤫 food is ready😂 sai fa nayi wanka,zoki nuna mun bathroom kafin Abu_jafar ya doka mun tsawa yanzun nan in Kira masa mala'ikansa( tana nufin inna Abu) duk tana maganar ne tana kallon rungujejen hoton Abu_jafar dake falon


Dariya um_jafar tai "Yarinyar nan a shekaru biyar kin ƙaro taɗi,ga tsokanan bala'i ,how I wish Abu_jafar na nan yazo ya gane mun shalelen Inna ,da ake zuwa ake bamu zafi da ita😃"


Saida ta kaita bathroom ta hada mata ruwan wanka ta dauko turaren wanka zata zuba tayi saurin riƙe mata hannu 


"Uhmmmm wayyo banason ƙamshinsa " turus tayi cikin mamaki hannunta sagale da abun turaren "Ke na strawberry ne fa" 


Gyaɗa mata kai kurum tayi saboda yanda bakinta ya fara cika da miyau da gudu taje gaban sink ta fara zubarwa tana ɗauraye bakinta wani na taruwa 


Ƙur ta kafeta da ido har ta gama ƙwaƙule ƙwaƙule sa su kakarin aman ta 


"Noor kinyi aurene banda labari? Noor kin sauya ,ciki gareki?"


Girgiza mata kai kawai tayi maana ta bata amsa a takaice kawai sai ta bugo ƙofar ta barta nan tsaye 


Zaman dirsham tayi a gefen jacuzzi tana kallon kanta a jikin mirror ɗin bathroom din komai nata ya cicciko nonuwanta sun ƙara cika sunja ruwa sosai ga ƙiba na musamman da tayi .

Kai hannu ƙasan maranta tayi ta ɗan shafa kaɗan 


"Ahmed ka cuceni ,kayi mun fyaɗe ,a dare ɗaya ka rabani da kimata na ɗiya mace cikakkiyar budurwa ,a dare ɗaya ka ƙunsa mun ciki ...gashi ka sani na fara tunanin rayuwar da zan koma ciki wanda na manta dashi har nayi bankwana da riskarsa ....Hmmm dama hakane farau farau ɗin banza a garin banza yaje ƙarewa,bariki bai yiba Iyayenmu sunyi gaskiya ba'a bawa namiji amanar budurwa ,kullum yina kirana da ƴar amana gashi ya bambara ma ƴar amana ciki😢"


Saida tayi kukanta ma'ishi sannan tamike ta fara wankan.


No comments