Recent Updates

Sugar Mommies G

 


م افنان✍️💞: Page *G*

*Labari ya riskeni  ƴan Vip ɗina suna fita mun da littafi. Tabbas kune saboda inda aka turo mun ƴan regular ma basu kai page din ba ,don Allah ku tausaya mun ku bari kafin In dauki nawa matakin ,in kinji lallai sai kin fitar ne ba dole ko yanzu ki zo ki amshi 500# ɗinki in cire ki a grp ɗin*


Fauza tana fita daga ɗakin da ta bar Nuratu study room dinta ta shiga ta fara kunna laptop dinta ta shiga shafin ta na twitter tayi maza taso ma rubuta _write up_ a matsayin jawo hankalin wanda abun ya shafa 


Heading din write up din ya fara da 

_To whom it may concern_


Sannan ta cigaba da rubutu a zube


_An undergraduate found her self in the midst of street kids in this very Monday morning in conclusion of her research plans_

_The kids were in both gender and all of them naked,Hazy and disconcerted and obvious to what time during the night they had stripped off thier clothes and what exactly they had done with their nakedness.sucked into life on the street and reachibg out to new day with a ever_increasing hopelessness ._

_A teenager among such homeless kids were asked by the researcher about their passionate dream._

_I truly thought the kids would be craving for material things like shoes and dresses or more on blanket for warmth at night ._

_It was swerved !_

_Yeah,they craved for warmth all right ,but a kind that many secure of ,and the assured love of a parent (Especially mothers) at least,took for granted. Plz where is our Political people ,where are the NGOs(Non govemental organization) Ooops my dear mothers where are you ?Can't you lay your sympathetical views over this demanded kids?_

_Hey I as a citizen i questioned the govement rulers what is your hidding agenda over this children please?_


Tana Gama dogon write-up dinta tayi maza ta sauka ta dauki biro ta jawo file dinta  ta je ga advanced study dinta da zatayi a chapter five din project dinta ,ta fara rubutu aka suggestions(Shawarwarin da zata bada) din da ya kamata ta bada a matsayinta na researcher 


Tana cikin rubutun wayar Ahmed ya shigo wayarta kallon wayar tayi take wani murmushi ya ƙwace mata "Oh my world"


Ɗaukar wayar tayi "Hello my man"


"Moh love ya research ɗin akwai nasara?"


Ajiyar numfashi tayi "my champ kasan dai a da na tsani project topic dinnan ko? Kai ka sakani dole na daukesa ko? Wallahi yau nayiwa Allah godia ban sani ba sanadiyyar yaran nan in samu Aljanna ban sani ba ko sanadiyyar yaran nan da tausaya masu da zanyi Allah mu ma ya bamu namu yaran..." Muryarta a take ya fara rawa kamar za tayi kuka


"Hey raguwa me ke faruwa kuma?"


"My champ komai ya faru wlh i weepd huge saboda yaran nan da na gani musamman yarinya guda daya ..."


Murmushi yayi "hhh naga write up ɗinki yanzu a Twitter ,Niko nace to yaushe matata ta soma aikin jarida? ,ta fara zuwa naɗan bayanai ta fara kai rahoto?"


Murmushi ita ma tayi "my champ kar kace mun na shiga aikin da ba nawa ba?" Dariya yayi na ƙarfafa gwuiwa 


"Wajen taimakon Al'umma ba wanda aka ƙayaje wajen bayyana damuwoyin mutane ,so i support You 💯 "


"Tom Yaushe zaka dawo kaga yarinyar wlh tana da kirki gata kyakyawa zanso mu taimaki yarinyar nan a jikina nikeji akwai abu mai girma a tare da ita"


"Love kenan ,kin sani sarai meeting Nike dashi da duk manajojin bankunan Nigeria ennnan ,yanzu duk sun hadu saura manajojin GT da Zenith ne basu ƙaraso ba da sun zo na masu orientation din da zan masu zan dawo ....Ai mu aiki dai ya same su😄 (yai magana cikin tsokana) turo baki tayi kamar yina kallonta ta yi magana a shagwaɓe 


"Ammma...amma" 


Dariya ya sake fashewa "Baby rigima ta ,ok ce mun Bye sai nazo"


"Bye I miss you"


"Me too" 


Ya bata amsa yina sakar ma wayar kiss ya kashe wayar 


Sai da ta yi waya da mijinta sannan taji wani abu mai sauki ya faɗa mata ciki 


"Kai rayuwar ƴa mace bai taɓa tafiya saida taimakon ɗa namiji" 


Ɗakin da ta ajiye Nuratu ta shiga ta ganta ta cinye abincin tas ta taune ƙasusuwan 


Ta shanye ruwan duka tayi wanka ta sauya kaya ta rafka tagumi basai ance maki tunani take ba


"Noor" wani banbarakwai taji yanda ta kirata sa wani “Noor” kamar sunan ƴan gayu 


"Noor sorry ba a ƙasan nan muke zaune ba a gidana na Japan inada masu mun aiki da bazakiyi rashin abinci ba anan kuwa yake away mukeyi so sorry plz nasan baki ƙoshiba bari in kawo maki kayan tea sai ki ƙara dashi 

Kafin honey ya dawo "


Kunyane taji ya rufe ta "Aah na koshi kinga na cinye da sauri ne? Wlh ynz haka cikina zafi yake mun idan muka ci abinci irin wannan sai munyi ta amai ko zawo saboda hanjin mu ya nannaɗe ,farau farau(koko) shine yake zama lafiya amma bacin haka wuya muke sha"


Girgiza kai tayi cikin tausayawa "Zaki zauna dani? In zaki zauna dani zan saki makaranta bakida matsalar abinci zan hadaki da iyayenki kinji ?"


"Antyna a jikina nikejin ke Mutuniyar kirki ce kuɗinki da kyawunki baisa kin wulakanta dan adam ba hakan kadai naji dadi ,kuma idan har a kasancewata almajira bakiji ƙyamar kasancewa dani ba,wacece Ni da zanki yarda in zauna da mutane masu kirki irinku? Saidai ina tsoron haƙƙin aure Anty na kema a ƙarƙashin wani kike ,ƙila baya maraba da baƙi musamman irinmu" 


Matsowa gabanta tayi tana shafa mata kai "Annabi (s.a.w) yace ka shafa kan Maraya yina da tarin lada ,babu Marayan da yakasance asalin Maraya sai wanda yarasa mahaifi ,kawai naji inasonki noor ,mijina yinason abinda nikeso kuma mutum ne mai karamci badon kar in yabesa ba da sai ince ya fini kirki amma zaki ganin ma kanki"



****

Sai bayan Asr Ahmed ya shigo lokacin har Fauza sun sake fita sunyi wasu take away din ,tayi mata shopping ɗin kaya ready made daidai jikinta don kayan Fauza sunyi ma noor yawa .


Ahmed yina dawowa shima sai gashi ya shigo da nasa take away din abincin .


Sudai kalar nasu rayuwar su kenan😄


Saida yayi wanka ya huta yaci abinci sannan Fauza taje ta kirawo masa ita 


Yina zaune a falo yina tura ma ogarsa na can Japan ɗin feedback din meeting din dasukayi da manajojin bankunan Nigeria din ta Email 


Da sassanyar muryarta ta shigo ɗakin hakanan yaji gabansa ya faɗi


A hankali ya ɗago ya kalleta ,dama idonta akansa yake taja ta tsaya .


Rawa bakinsa ya farayi baisan sanda ya mike a firgice ba "Nuratu !"


Haba kamar tana jiran ya kira sunanta hawaye ya ɓalle mata kamar an kunna famfo


Ina kika shiga Nuratu na nemeki kin ɓace mun naje makarantar ku ance kin gudu"


"Love wata Nuratu ? Badai Nuratun inna Abu ba ?"


"Itace!"


Shock tayi sosai taje gefen kujeran da mijin ya tashi ta zauna tana tunanuka iri da kala....


Ta kasa cema dukkansu komai



Tunanin me take ? Anya itama zata karɓe ta ko zatayi rejecting dinta ?


No comments