Recent Updates

Sugar Mommies F

 


م افنان✍️💞: *F*

Saida Nuratu ta kwana bakwai tana amsar kulan psychiatric doctors kafin ta dawo hankalinta ,Ahmed shi ya dinga amso mata ayoyin dangana daga hannun mamanta yina kawo mata asibiti tana amfani dasu 

Ranar da aka watse sadakar bakwai ranar aka naɗa sabon Sarki aka raba gadon sarki saidai duk an nema takardun muhimman ƙadarorinsa an rasa ,amma dukda haka su Hajiya abu an zama manyan mata don yawan gonakin da aka bata saida ya tsorata ta ,nan ta kira wayar Hajiya kareema don neman shawarar abunda zatayi in ta gama takaba .

Aikuwa ƙawa ba ta arziki ba nan ta fara karanto mata baitocin lalacewa ita kuma ta amsa ta hardace .

Sunyi tarayya a ra'ayin shagala iri ɗaya saidai kowa da manufarsa ,Inna Abu so take ta waye tayi ƙara'in da ya wuce ta na lokacin ƙuruciya

 _(Erick Erickson kayi gaskiya😄 sorry only Nurses can relate.)_

_(Erickson's Theory ne da yake magana akan matakan rayuwar ɗan adam tun daga yaranta har tsufa ,Misali jariri daga haihuwa ya yrda da komai (trust) da abunda ke sonsa da wanda zai cutar dashi duk daya ne ,idan akai maintaing wannan yarda sai yaro ya girma ya yarda da kowa ,amma ina aka dinga cutar dashi shekarun nan suka wuce a haka yi ƙarshen step ɗin sai a sama mistrust (Cizo ,faɗa ,rigima dss) to daga mutanen da suka rainesa ne har ya zama hakan sa ake step na gaba ...To haa rayuwar da adam yake duk step ɗin da mutum ya kamata yayi bai yishiba ma'ana ya tsallake bai yi ba zaita bibiyarsa kamar carry over kuma,sai fa yayi shi ...kira ga iyaye masu yima ƴaƴansu auren dole ko ince auren wirwuri ,sai aga aure yaki lasting yarinya tana ɗaknta tana hangen ƴan matan ƙawayenta da basuriga sunyi aure ba,tana kaso auren ko dai ta  zama bazawara sai ta zama ballagaza tana ɗabi'un da ƴan mata ma basu irinsa ,in kin bibiya da kyau lokacin ƴan matancinta ne ba'a barta tayi ba ,don haka dole tayi shi da girmanta so ba laifinsu bane ...Iyaye mu gyara Plz ba a Auren dole bane kadai har wasannin yara wasu iyayen basa barin yaransu suna wasan ball ɗin nan ko na teddy da sauransu saidai koda yaushe karatu ,sai karatun ya fara ginsarsa sai ya kasa samun lokacin da ƙwaƙwalwarsa zai bude irin na saoinsa saboda ba'a barsa yayi wasu a lokacin da shekarunsu na ƙereƙere da ƙirƙiro dabaru bane an azabtar dashi da karatu gaba-daya ...duk irin negative feedback din da ake samu na irin wainnan abubuwan su ake kira da ƙara'i)_



Rasuwar mahaifin Nuratu ya zama tushen ƙulla ƙawance da baƙincikinta ,kowa ya gujeta saikace wacce ta kashe mutum ƙauye an hanata shigansa,damuwa tayi mata yawa Ahmed kafin ya koma Japan ya ɗauketa ya sakata a boarding school .

Ta fuskanci ƙunci iri da kala a wannan makarantar iyayenta ba wanda ya taɓa takowa inda take ,itama ko anyi hutu bata zuwa hutu gida 

_Kowa ya ɗauki makarantar nan makaranta ne Ni kuwa kiransa nike gida babbar zullumina shine ranar da na gama karatun ina zani?_


Wannan shine zancen Nuratu a duk sanda yara suka tafi hutu suka barta itakadai a Hostel .


Nasan mai karatu za ce ina mahaifiyarta da ta bari ana cin zarafin ɗiyarta ?


Waziri suna gama takaba yayi kutun kutun ya aureta ,ya kulleta a gidansa dama ya daɗe yina sha'awarta ,kana ya rabata da ɗiyarta Nuratu ,ya haramta mata nemanta ,idan ta zo inda take sai ta koreta saboda  darajan miji sa darajan Aure .


Haka ta cigaba da lallaɓa rayuwarta har takai SS1 lokacin Ahmed sau biyu ya taɓa kawo mata ziyara ,kuma a lokacin duk wasu alamomin girma sun fara bayyana mata ,a lokacin suka fara soyayya da Labour master ɗin makarantar su 

Sunyi soyayya mai tsafta yaci burin aurenta saidai iyayensa na zuwa ƙauyen sa niyyar nema masa aurenta ƴan ƙauyen suka soke auren .


Bai faɗa mata yanda akayi da iyayensa ba saidai ya ginu akan labarin da aka basa a kanta don haka soyyayrsu na aure a da sai ya rikiɗe ya zama na sha'awa so yake kawai ta bashi hadin kai ya lalata ta,tunda dama lalatacciyar ce a cewarsa .


Allah sarki Nuratu baiwar Allah sam bata fahimci manufarsa ba tayi masa kyakyawar fata .

A haka watarana ya gayyaceta suje outing ,batasan manufarsa ba saida suka shiga mota ya fara shafa ta dakatar dashi tayi cikin mamaki saidai kawai taga ya ciro mata wuƙa ,yina bata tsoro sannan yina zazzaginta da aibata ta akan dama ita er iskance 


Bata karaya ba suka fara dambe a motar ,Dukda tana tsoron wuka amma bata son ta rasa budurcinta maganar ƴan ƙauye su ya tabbata a kanta 


Dambe sosai sukeyi shi dama baida niyyar soka mata wukar sai don barazana ,Abun ilah! Garin ta kauce ya daɓa ma kansa wuƙar a cinya ,nan take jini ya goce ya fara sharara 


Ta firgita haiƙam don haka ta ɓalle mota ta fice a firgice gudu take bata san inda zata ba ,haka ta shiga kasuwar kurmi tana numfarfashi ta gama sadaƙarwa zai mutu 


Ƙarƙashin gada taje ta ɓuya har dare yayi ,a lokacin taga yara da yawa sa'oin shekarunta suna shiga ƙarƙashin gadan suna kwanciya ,kenan yarane _Homeless children_ wanda basu da gida a titi suke kwana 


A take tai joining ɗin su dama wajene na wani baisan wani ba ,suka amsheta kuwa a yanda take ta zama er titi ,saidai in safe yayi su fita Bara ,in dare yayi suzo ƙarƙashin gada su kwana in kuma ana sanyi sosai sai su shige rumfunan mutane . Haka rayuwarta ya cigaba da gungurawa fiye da wata shida .


Har watarana 

Fauza ta gama karatunta na medicine tana project dinta akan yara nakasassu (Disabilities) da abubuwan da ke kawo yawaitansu a Nigeria ,wanda aciki harda rashin kulan iyaye don mafi yawancinsu Almajiraine da homeless children Wanda suka rasa iyayensu saboda gobara ko wani disaster 


Gurin naɗan bayanai da samun hujjoji akan aikin da takeyi aka mata kwatancen wajen su Nuratu 


Yanda ta gansu ya bata tausayi taci kuka ta gode Allah don gaba ɗaya ta alakanta laifin da gomnatine ba iyaye kadai ba 


Interview ta farayi da yaran ɗaya bayan ɗaya tanajin ra'ayoyinsu 


Wannan yaron zaice “Ni babu abinda yike sani in shiga damuwa sai in na kwanta barci gari ya fara wayewa nayi tunanin bansan inda zanje in samu abinci ba...”


Wata yarinyar kuma tace “Mu matane amma a titi muke kwana munkai munzalin da mun fara tasawa ,yunwar cikina baya damuna yatankacin zullumin fyaɗe! In mun kwanta bama yin ƙwaƙwaran motsi har sai gari ya waye ,saboda yanda lalatattun maza suke farautan mu kamar kaji..”


Daganan tazo kan Nuratu ,sam bata gane Nuratu ba saboda dama a rayuwarta sau ɗaya ta soma ganinta don haka yanda tayi baƙi ta wulakanta bazaisa ta gane ta ba 


Tambayar ta wulla mata kamar yanda tayi ma sauran yara ,tana saita mouthpiece ɗin wayarta a kusa da bakin Nuratu don naɗan jawabin ta 


Tana kallon Fauza hawaye ya surnano mata ,bawai don ta gane ta itama ba A'ah don rasa ma me zatace ,zata fadi ciwonta ne ko zatayi shiru ne


"Ina sauraronki ƴan mata mene sunanki?"


“Suna na Nuratu ,Ban taɓa damuwa da rayuwar da nike ciki anan ba domin shine abinda Allah ya zaɓar mun ,saidai kullum ina kwanciya barci da fatan yaushene zan ganni tare da mahaifiyata? Yaushene zanje in kwanta a gado ɗaya da mahaifiyata ,muyi hira nida ita taji damuwata ta rarrasheni ,ba tareda ta kyareni tasa an koreni ba?"


Maganar Nuratu ya tayar ma Fauza da tsikar jiki yanda yarinyar take magana cikin tsiyayar hawaye zai tabbatar maka da raɗaɗin sake damun zuciyarta ba kaɗan bane 


"Ina iyayenki suke ?"

”Wannan ba maganar sawa a radio ko gidan TV bane kamar yanda kikayi Alƙawari ,magana ne na rayuwata ! My very personal life ɗina ...Amma nasan sai na fito daga ƙauyen da jahilci da rashin adalci ya zama questionable bana tuhumar kowa ,Amma nasan maraicin mahaifi shine ya ja mun!"


Janyeta tayi a cikin mutane ta kaita motarta,ta ciro ruwa ta miƙa mata 


Aikuwa tasha ruwan nan ba kaɗan ba 

Sannan taja ajiyar zuciya ta ɗaga kai ta kalleta 

"Idam mukaga mutane sun jawo mu a jiki sun bamu masauki a inda suke mukanji daɗi har ƙoƙon zuciyoyinmu....mutane da dama suna tunanin mu mabarata bamu jin takaici in muka ganmu cikin ƙazanta wallahi munaji Anty in matsala tayi yawa naka kawai muke tarewa ,abun tunanin shine mai kaya ɗaya ta yaya za wanki ya fito fes? Da dare muke wanki mu zauna da underskirt da asuba mu maida a jikinmu,don haka kaya sai yafi wata uku bamu sauya ba haka zasuyi ƙwarƙwata to yaya zamuyi??"


Kuka wiwi Fauza takeyi ita yarinyace ƴar gata bata taɓa sanin akwai masu fama da talauci a rayuwa irin haka ba.


Kallon Nuratu tayi "Ki bani dama naga ke kin taɓa karatu zan gabatar dake wajen manya ,zan zame maku _Advocacy_ a wajen gomnati inshaalh sai anyi _Eradicating_ matsalar nan sanadiyyar ki.


Kin yarda zaki bini?"


Ƙurr tayi mata da ido "Anty ki sani koda zaki kaini inda za'a yanka ni ne babu mai nema na ,Don haka nauyin kula da Ni ya rataya tsakanin ke da ubangijinki nidai marainiyace banda kowa" 


Gabaɗaya jikin Fauza ya mutu ,haka ta tuƙa mota suka biya eatry ta musu take away kana suka gangaro gidan su 


Ɗakin baƙi ta kaita ta nuna mata duk wani abun bukata ,ta ajiye mata abinci takeaway biyu da ruwa da rabin kaza ta fita taje ta dauko mata doguwar rigarta na Atamfa da bata sawa ta ajiye mata 

Ta barta ta kimtsa.


No comments