Sugar Mommies E
[12/6, 08:12] أم افنان✍️💞: *E*
A bakin fada kam ,koda Nuratu tayi arba da kwamacalan da suke cikin jakan da aka zazzage sa a bainan nasi.
Wani ƙara Nuratu ta kwarma ta ɗaura hannu a ka
Shikam sarki take anan wani abu mai kaifi kamar mashi ya sokun masa a zuciya ƙyam ya dakata hannunsa riƙe akan ƙirji ya rimtse ido yina salati
Tafa hannu jama'an ƙauyen suka shigayi suna Allah wadai da Nuratu
Ba'a ankare ba saidai akaji wani abu nannauya ya faɗi rikicaaa kamar buhun dawa ,waigawa sukayi a furgice nan sukaga sarki kwance a ƙasa ashe shine ya faɗi bakinsa na bulbulowa da kumfa (dafari) idonsa ya kakkafe yayi sama hannunsa ƙanƙame da ƙirjinsa ,a take halshensa ta karye ya fara salati gwabura gwaburà babu mai fahimta sosai
Ihu nuratu ta fasa "Babana!!! Kar ka mutu wallahi banda laifi"
"Naa sani nuratu Allahu akbar na tausaya maki ƴata ..." Dakatawa da yin mata magana yayi ya carke da salati ya maimaita sau biyu kafin yayi na ukun an zare RAN!!!
Ƙanƙamesa tayi tana kuka amma tanajin ɗiff komai na jikinsa ya ɗauke kamar wutan nepa ,batasan sanda ta daddage ta fantsama ihu ba ta soma birgima
Shantali yanka mata mari yayi wanda ya sata sakin fitsari a wajen
"Yi mana shiru tsinanniya ,yau ina tarbiyyan da aka baki? To ki sani baki ba ƴaƴanmu!.......,kai fagaci kamashi a kaisa asibiti"
Cikin tsiyayar hawaye yace "Ai kun kashe shi ! Ya tafi ransa na suya yasan baza kuyi ma ƴarsa uzuri ba"
Waigawa sukayi suna kallon mai maganar
Ahmed suka gani sunkuye akan gawar sarki cikin shigan larabawa jallabiyya ya lulluɓe kansa da hirami dawowarsa kenan daga sallar juma'a ya biyo yayi ma sarki Barka da Jumu'a
A hankali yakai hannu ya rufe idon sarki "Allah ya jikanka mai martaba" ya cire mayafin kansa ya rufe masa fuska
Wani ƙara ta tsaga kawai sai ta yanka daji da gudu ba uban da yasan inda zata. Kamar yanda ba wanda yayi yunƙurin bin bayanta ,saima haushinta da yaƙaru a zuciyoyin wasu mutanen
Kakabi suka ɗauka ,tuni mutuwar sarki ya kewaye gari ,iya Talatu kam salati ɗaya taja ta zube a ƙasa sumammiya
Shikenan har aka kaisa bata farfaɗo ba
shikenan rai baƙon duniya
Itakuwa inna Abu in ta fito cikin jama'a tayi kuka ta la'anci Nuratu,da tayi masu silar mutuwar miji kuma uban ƴaƴanta kuma jagoran Al'umma.
Amma da ta fakaice a ganin mutane ,ta koma ɗaki,sai ta goge ido ta fara tiƙan rawa har ta gode Allah
"Gado... Gado...Ahayye mun kuɗance" da wannan waƙar tayi ma Hajiya karima sallama bayan ta kirata a waya , ma'ana shine Mabudin kunnenta
"Ya akayi haka tun kafin mu turo yaranmu su gama mana dashi ko dama ciwo yake?"
"Ke dai bari sai mun hadu uhm uhum su sarki an daki duro wayyo Daɗi "
Ana kai sarki gidansa na gaskiya aka taru wajen zaman makoki a wajen ƴan fada suka fara taƙaddamar wa zai zama sarki ,ya kamata su zaɓa su waye suka dace kafin Sarkin Kano ya aiko a kawo sunayen mutanen da a cikinsu za'a zaɓi sabon Sarki ranar sadakar uku!
Takaicine ya ke neman kashe Ahmed lallai ƙauyanci ba bala'in da ya kaisa
Miƙewa Yayi ya fara faɗa akan duk wanda mutuwar bata shafesa ba ya tashi ya bar wajen
Waziri miƙewa yayi yina masifa da bala'i don shi yakeso a basa sarki don haka bayaso a dakata da zancen mulki ,yanda YIKE tujara haka shima Ahmed yake maida masa da martani don bai basa girma ko na ƙwarar zara kamar yanda mutanen garin ke shayinsa ,don haka gab ya rage a baiwa hammata iska shi da Ahmed ..
"Ga sabon doka daga ofishin waziri ,an haramta ma yarinya Nuratu shigowa garin nan har abada ,don tsira da martabar masarautar mu da ƴaƴan mu mata!"
Kabbara suka ɗauka ana Allah wadai da Nuratu
Ahmed miƙewa yayi ya bar wajen ya haye motarsa ya dauki hanyar komawa Kano yina daf da shiga gari ya hangota kwance akan gada kowa na raɓata yina wucewa kowa ya aza sabuwar hauka ne kasantuwar iska ya hura
Bakinta ya bushe ga yunwa ga ƙishin ruwa ga damuwa ga raɗaɗin rashin mahaifi.
Faka motarsa yayi ya nufi inda take saidai tana ganinsa ta wani zabura kamar taga dodo ta falla da gudu
Ihu ya kwarma "Gudunmuwa jama'a ƴar uwatace zata shige ma babbar mota ya taka ta"
Daƙyar aka kamo ta aka jefa a mota ya figeta ya wuce da ita asibiti don tabbas da gaske kanta ya motsu.
#Bamalli's care
No comments