Sugar Mommies C
✍️💞: *C*
Haulatu tana shiga ɗaki ta fara da karkaɗe gadon da suka kwanta akai ta buɗe drawer ta zaro sabom bedsheet zata sauya kenan sai ga Hajiya Kareem ta sake shigowa
Hajiya kareema bata sallama kuma kamar da sanɗa take zuwa don saidai kawai kaji an buɗe ƙofa,ko mai takeson gani ne oho?!
Haulatu tana ɗagowa ta kalleta ta kauda kai ta cigaba da abinda takeyi
Samun stool din kusa da ita tayi taja ta zauna
"Ke haule ji ni nan"
Yarfe hannu tayi ta tsaya tana kwaɓe fuska irin alamun nan na an dameni
"Ke wai bakida wani aikine a sha'anin abinda ya shafi aure sai gyaran gado da kwanciya da miji?"
"Momy me ya kamata inyi?"
"Tambaya na ma kike yi? Ke dakata ba girki ne ba kula da yara ne ba koya ma yara karatune?"
Hassala Haulatu ta farayi don a tunaninta duk abinda ta lissafa akwai masu yi basai ita ba
Cikin rashin kunya tace "akwai masu yi ai wanann ne ba mai masa sai Ni"
"Kai kai kai ,ke dakata iskanci a gado shine kadai abinda aka auro ki don ki ringa ma ɗana?...to fada mun meye banbancinki da karuwan kan hanya...?"
Cikin karaɗe ta kwatseta da hayagaga da masifa kamar zata wanka mata mari
"Aah momy kinga dakata _If some one is respecting you ,do your self a favor by respecting your self_"
"Eyyeh Isashiya don girman Allah karki girmamani kinji ko don uwarki da ubanki karki girmama Ni, A hakan dai nafi uwarki uwale mai tallan gwanjo a kwatas ɗin ma'aikata "
"Ya isheki zaginmun uwa"
"Na zaga dukana zakiyi ne tatacciya Isashiya? "
"Abunda yafi hakan ma zan maki kika sake zagin mun uwa don ta fiki mai tara yaran jama'a kina ƙwaƙulesu "
Yanka ihu tayi ta soma kururuwa ta fadi rikicaaa a ƙasa ,tana burgima tana kwantsama ihu ,ai da gudu sai ga Inna Abu ta shigo
"Lafiya ....meye haka dambe kukayi ta ka da ke?"
Cikin hawaye Kareema tace "wuce dambe Ni yarinyar nan zata kalli tsabar idona ta mannawa sharri wai ina tara yara ina ƙwaƙulesu ,na ce uwarki na ƙwaƙule ban sani ba...Ni haule zakiyi wa sharri saboda bansa ɗana ya sake ki ba ? To ki sani igiyoyinki na zama a gidan nan dai yina hannuna ne In naso a yau dinnan zansa a datse sa"
"Mtsewww aikin ɓur ,inji tusa . Don Allah ki sashi ya sake Ni ,shine zan yarda ke er maɗigo ce ,kuma wlh bazan iya zama gida ɗaya dake ba dole indai yinason aurena ya bini mu tafi ,ke kuma ki sashi ya sakeni zamuga wa yafi wani power.....kar dai ki manta bani ƙwaina saida zakara ina da adanannun hujjoji"
Cigaba da burgima tayi numfashinta na sama sama kamar mai asthma ,itakuma abu dik ta ruɗe ta soma dannawa Haulatu zagi
"Ku fita tsoffin banza ku sauka " ta je da gudu ta ɓazgo ƙarfen labule tasoma shimfida masu tana borin ƙarya tana watso duk abunda yike kusa da ita,itama tana rera kuka
Iridididd sukayi waje da gudu ta rakasu da ƙarfen labule
Da gudu Tukur ya shigo yina salati da tambayar lafiya?
Tana ganin mijinta ta daddage ta yanka wani irin ihu a dole Aljannunta sun tashine ,don haka ta daka tsalle ta wanke inna Abu da lafiyayyen mari .
Da gudu ya je ya rumfaceta yina kiran sunanta ita kuma tana wani gurnani kamar zakanya
"Shikenan sai mun kaita gidan ruƙiyya !me ya faru ne Aljannunta suka tashi ,ga Aljanunta ƙarfafa ga duka!"
Hada baki sukayi wajen cewa "Aljanu!?"
Kareema ta kasa motsawa sai ta fara rarrafe tayi hanyar stair case ɗin zata haura sashenta
"Kaiwa girman Allah Tukur ka tattara jaiban matarka ku bar min gida wallahi bazan iyaba ,inba kanason zullumi ya kasheni bane!"
"Bai sake bi ta kansu ba ya cicciɓeta tana turjewa har ya fita da ita gidan ,ya kunna karatun ƙurani a mota ai basuyi nesan tafiya ba ta wartsake irin a dole taji karatu aljannu sun gudu ɗin nan ,baisan duk aljanun ƙarya bane!"
Ƙatoton ajiyar zuciya tayi sannan ta miƙa hannu tana shafa masa hannunsa ,a sanyaye ta kira sunansa "Habibiy"
"Hurul'een ɗina"
"Habibiy ina zamuje banason fushin momy mu koma gida ya akayi nazo motarka ? Ina driver kake driving da kanka kuma?"
Samun waje yayi ɗan gefe da kan hanya ya faka
"Sannu laluranki ne yaso tashi Amma Alhamdulillah yanzu mun gode Allah kin dawo daidai"
Cusa hannunta tayi a gashin kanta tana yamutsawa ,gamida lumshe ido sai ga hawaye na surnano mata a kunci
Ruɗewa yayi ya rungumeta ya fara rarrashinta yina shafa mata baya
"Kiyi hakuri nasan kina da hakuri amma tun da naga hawaye suna fitowa daga wainnan golden eyes din naki abun yayi ƙamari "
Sa bayan hannunta tayi ta goge hawayen tana jan ajiyar zuciya ɗin nan irin wanda yara keyi kamar zai tafi da ranta
"Habibiy ba komai Muje gida kawai "
"Aah muje guest house ɗina kawai ,dole inyi jinyarki kar inje dake a sake cusa maki wasu damuwar kuma"
Langaɓe kai tayi akan kafaɗarsa tana shashafa masa kafaɗu da duk hannuwarta biyu tana ɗan murzasu kamar mai yin tausa
Lumshe ido yayi "Ahhh ahhh"
Dariya ta ɗanyi "muje ko?" Ta gyara zamanta tana kallon hanya
Ba shiri ya jinjina mata kai "washhh Zaki sani ne na lura haukaci ɗanɗane kike ta mun ai yau zamu goge raini"
Hannunta takai kan wandon jeans ɗin sa tana wurza masa cinya ta kakkafesa da Idanuwarta tana tura masa da wasu saƙonni masu tsada .
Shiru yayi ya kasa magana sai kawai ya tada motar ya fara tafiya a hankali ta kai hannunta kan maransa ta ɗan shafo gashin maransa
Ɗan zillo yayi "Keee zakisa muyi hatsarine wallahi na fara daina gani ,hangoni kawai nike ina caccakar tsuliya"
Murmushin side chks tayi "To an bari"
_(Ko ban faɗa ba next page kowa yasan akwai show ,don haka posting ɗin dare ne Inshaalh ,in bazaki iya juran karantawa ba ,Hajiya Mute the page *D* plz)_
A gida kuwa Su haulatu na fita Abu ta ɗago tana zare ido kamar baƙuwar mayya
"Hajiya kareema ke cikin surukan naki harda masu Aljanu? Kinsan fa in sunyi ƙarfi magani suke cewa zasu bada ,shikenan kinaji kina gani su rabaki da yaronki a maku firaƙu ke dashi sai gani daga nesa"
"Mtsew don Allah abu ki ƙyaleni da wauta ,waya fada maki matan zamani suna asiri? Wallahi sai ƴan ƙauye da gidahumai ai kissan wasu matan shine malintar su . Ni yanzu ba wannan ba Abu ke ƙawata ce idan ban fada maki sirrina ba wazan fada mawa? Wallahi abu ina jin sha'awa gashi yaran nan sunzo sun tare mun a gida bansan yanda zan yi in ɗan kira yaran da suke rage mun zafi ba
"Topah ! Kema? Haka wata ƙawata zulai ta kawo mun gindin maza na roba wai in ringa siyarwa nace wa zai siya ? Ashe akwai masu siya irinku!"
Cakumo rigarta tayi "Abu Inaso don Allah ki kawo mun wlh zan siya Ni inada kawaye ma da zasuyi maku ciniki,yaushe zaki kawo mun kije ki kawo mun gobe ki dawo dashi ko ki aiko Nuratu amma kar ki bari tasan meye a ciki"
Kwaɓe fuska tayi gwanin ban tausayi "Munyi fada da mai gidan da uwrta duk mun yi hannun riga yanzu ma hijira nayi masu sai Baba ta gani"
"Topah ke kuwa mai ya hadaku?"
Kwashe labari turyan turyan tayi ta bata ,ai kafin takai aya gaji kareema taja dogon tsaki "Bacin wani abu wallahi da sai na zageki abu ,ynz takan mutumin da ke da ransa da lafiyarsa kike tsiyar gado? Wannan ai jahilcine "
"To ya kike so Inyi banason yarana su tashi basu da gadon ubansu "
"Ke yanzu fa duniya ƴar sauki ce ,idan so kike a kashe maki mutum akwai wanda ake ba kwangila suyi ,idan fashi kike so ayi maki akwai ƴan fashin da zasuje su kwashe dukiyar mutum"
Gyara zama tayi tana kallonta idonta ƙemadagagas zuciyarta ya bushe "Kareema duka biyun nikeso a kashesa a yi fashin kudinsa nima inaso in fantama irinku don Allah jibi jikinki Kareema madam! Amma Ni jibeni hannu duk kanta sai tsiya na ajiye a rai...saidai mu ƴan ƙauye ba'a samun kuɗi a wajen mu saidai ƙadara irin su shanaye ,kifi sai hatsi a rumbuna ,sai kuwa ijiyayyun gonaki"
"Shanayen za'a kwashe ,hatsin ma a kwashe zaa juyasu su zama kuɗi da kamfanin masu sayar hatsin zamu hada baki mutane na kallo zasuzo da mota su kwashe ba'a san ɓarayi ba ne sai dai kiga kuɗinki cas!"
"Kaii Amma dai ƙawance da ɗan birni daɗi gareshi Ni an Barni da haƙilon gaba na koma ciyar da kaina da yarana saboda baƙar rai bazan iya cin abinci dasu ba"
"Aah saki jikinki ku dawo harka kamar yanda na sanki da yanda koda an kashesa baza a tuhumeki da rashin gaskiya ba"
Miƙewa tayi ta jefa kudin da aka bata a lalita "Hajiya Kareema zama bata ganni ba zanje in daidai ta da mutanen nan nasan basu da riƙo ,zama kiga na aiko Nuratu da kayan don yarana basu da sirri kuma ko na gargadesu kar su bude kayan nan sai sun bude itakuwa ƴar amana ce"
"Shikenan ki sauri ki kawo baby Ni kuma zan magana da kawata inji yanda fashin zai kasance"
Zuwa tayi ta rungumeta "Nagode ƙawata" kauda kai tayi saboda hamamin warin bakin ta da ke tashi na rashin brush
Haka sukayi sallama ta fice jikinta na rawa.
A ƙauye saida ta je gidan zulai ta amso kayan nan a Ghana must go ɗan ƙarami
Sannan ta biya dandalin masu kifi ta siyo gammo gammon kifi soyayyu masu yawan gaske ta taho gida ,tun a ƙwar gida take kiran Nuratu!...Nuratu
Nuratu tana jinta ta kashe kunne sai shiƙan masaran da aka kawo masu daga gona takeyi
Su Wasila fitowa daki sukayi suna masifa "Haba Inna sai kace wacce aka kai wajen malami ya turaroki ,daga dawowa Sai kiran sunan ƴar matsiyaciyar nan?"
Miƙewa tayi tasha ɗanmara "Ni uwata ba matsiyaciya bace saidai..." Kafin ta ƙarasa inna Abu ta nuna kanta da yatsa ta ƙarasa ma Nuratu zancen bakinta "Saidai Ni"
Da sauri Iya ta fito a ranta tana cewa ga jaraban nan ta dawo gidan mu zai kama da wuta .
"Ke Nuratu ba aiki na saki ba ,abun naki yakai ga shiga mutuncin babba dama?" Turo baki tayi gaba "Sune suka fara ai"
"Kinga Talatu kuyi haƙuri yanzu naje gidan yayana yamun nasiha yamun nasiha har kuka Saida nayi ,nayi ladama ,ku mun uzuri jahilci da gidadanci ke ɗawainiya dani amma yanzu na tuba shima ina jiran Sarkin ya dawo ne in rokesa gafara hakan bazata kuma faruwa ba
Iya Talatu washe baki tayi saiga hawaye sharrr ya zubo mata
"Allah mun gode maka da kika gane gaskiya wallahi kullum dare bana barci addu'a nike Allah ya daidaita ku da mijinmu dani kaina sheɗanin da ya raba Allah ya koresa"
Fakaitan idonta tayi ta caɓe mata baki ta ɗan yi ƙwafa a ciki ciki
"Ameeen kinga abokiyar zama ta gari ba ,Da ace duk matan duniya haka suke zama da abokan zamansu lafiya da kowa ya shiga Aljannah...Nuratu ƴar ɗakina zo ungo tsaraba naki yafi na kowa"
Ta ciro tarin ƙunshi kifi ta bata ,sam a jikinta taji bata yarda da Abu ba ,saidai inda sabo tasan abu da masifa amma fa bata iya makirci ba abinda ke ranta shi take fadi sai dai duk abunda za ayi ayi bata tsoron ko ta kwana
Hakan ya bata ƙwarin gwuiwar komai ya wuce ta a hannu ta amsa ta yi mata godiya
Su Rafa'atu daka tsalle sukayi "Kambuji Inna?! Makiyan namu da kika ce ko bayan ba ranki bamu basu su kike siyo ma tsaraba kike neman a shirya haka...To ke kika sani mudai muna nan kai da fata sai an bamu gadonmu
"To sai kuje ku zare masa rai lokacin mutuwarsa bai yiba ,ai nidai Allah ya saka ma Ya liman da Alkhairi wallahi ya tunasar dani ,yanzu duk sai mu mutu shi mai kuɗin bai mutuba bare muci dukiyar tasa ,to in kuwa hakane meye ya kawo haɗaman?,don haka ya zame maku dole ku zauna lafiya da ƴan uwanku kuma in babanku ya dawo kuje ku rokesa gafara shine zakiga haske a rayuwarku"
Sarki da shigowarsa kenan yaji bayanin Inna Abu irin na cikakkun masu hankali
"Kai Allah dai yayi Albarka abu ,ai Ni tun kafin ma su roki yafiyana da ke dasu duk na yafe maku Allah ya ƙara haɗe mun kan gidana ya kauda fitina da tarzoma"
Duk suka amsa da Amin har su Rafa'atun don yanzu in basu yarda ba cin ƙaniyarsu sarki zai yi ya zanesu da bulala bamai tare masu
Dama wani barakar daga uwa ake samo shi.
Kifin nan haka aka bajeshi ana wasa ana dariya ana dangwala yaji sarki na ta tsokalar Abu ta soma yin abun arziki an bata kyauta itama ta siyo kifi anci duka gidan... haka dai cikin raha aka cinye kifi komai dai ya wuce.
Washekari da safe
Dama ƙaidar gidan ne yara na zuwa daki daki gayar da mutanen gidan don haka yauma haka ta kasance Nuratu nayin sallah ta leka dakin sarki ta duƙa ta gaishesa ,yina cikin lazimi ya katse ya amsa cikin fara'a
Shiru tayi bata tashi ta tafi ba kamar yanda ta saba ba
Sosai ya maida natsuwarsa kanta "Lafiya Nuratu da magana ne?"
"Baba dama magana nikeso in maka"
"Ina sauraronki ƴar Baba"
"Baba meyasa baza a Barni in tafi makarantar nan ba ,ga ƙawayena nan duk sun tafi su ba ƴan ƙauye bane irina?"
Gyaran murya yayi ya fara sababi "Au ni a matsayina na wakilin jama'a ne zan yarda ki tsallake jiki kije wata makarantar kwana ? Ba kin iya karanta baki ba? Bakinyi primary ba to Allah ya bada lada ,amma waccan makarantar da kullum ake kawo mun karan lalata? Ynz jiya na samu labarin ƙawarki er wajen Mudi an dirka mata ciki an dawo da ita daga makarantar ana ta bugu taki fadin wanda ya mata ,wannan karatun bokon ne zankai yarana? Duk yayunki sunyi karatun ne da suke zaune a gidajen mazajen su cikin rufun asiri? Da suke da rabo ba mazansu sun sasu sunyi ba? To ke ki gode ma Allah ma Ahmadu ya matsa na barki kinyi primary .
Don haka karki sake zuwa mun da wannan maganar ko shi yasa ma ga ƴan uwanki nan su Wasila duk sun fito da tsayayye za ayi bikin su amma ke ko kare bai taba lekowa zauren gidana da sunan yina sallama dake ba?wato koronsu kikeyi ko kin talike ma boko ?"
Hawaye ne ya dinga gudu a idon Nuratu ,cikin rawar murya ta shiga basa hakuri "Bansan ranka zai ɓaci saboda boko ba inshaalh bani ƙarawa "
"Tashi kije Allah ya maki Albarka ya baki miji na gari In aurar dake da hannuna "
A ciki tace Amin ta mike ta fita ,tana fita tayi karo da su wasila sun lallaɓe a bakin ƙofa suna sauraron tijaran da Sarki yayi mata suna haɗa ido suka fashe da dariya
"Allah srki anyi baƙin baya yarinya ga kyau sai mugun baƙin jini kamar wacce ta sha hatimin jaɓa? Hahaha " Bata tanka masu ba haka ta raɓe suka shiga
Itakuma ta wuce ɗakin inna Abu.
Tana shiga da fara'arta ta tarbeta "Ha'ah wa ya saki kuka naga idonki ya tasa ,Ni fa na tsani wulakancin nan da sanyin safe baki karya da ruwan koko ba kin karya da kuka ? Fadamun wani ɗan kaza kazan ne ya ɓata maki?"
Ji tayi duk duniya ba ta da masoyiya irin inna ,ƙasa da murya tayi "Inna kiyi a hankali ,babane akan karatun boko kuma inshaalh bani ƙarawa,wai har yina mun gori su yaya rafa zasuyi aure su Barni wai baƙin halina ke koran samarin ,wallahi inna babu ne ke kin sani wallahi basu zuwa min bansan dalili ba."
"Ki shirunki zan masa magana kwata kwata nawa kike? Ina sai watan cika ciki zaki cika shekaru 13? To bazai yuwu ba"
"A'a wallahi na hakura kar kiyi masa magana don Allah "
"Shikenan ki shirunki yanzu ki je in mun karya bakinki ƙanin ƙafanki zan aikeki gidan su Ahmadu ki kaima mamansa wa'incan kayan ,kar ki bari kowa ya gani kinji kar a bude ,suna kallo zaki dawo da toshinki (tukuici) naga uban da zai karban miki"
Sai da ta tabbatar ta kwantar mata da hankali sannan suka rabu
10am bayan Nuratu sun dawo Allon safe ta harbatsa wankanta ta sa yamutsatsun kayanta tasha gayunta dai irin na ƴan ƙauye
Taje ta karɓi kayan Hajiya kareeman ta tafi
****
A fada waje ya cika Nuratu tazo zata rabe ta fita ta duka ta gaishesu ,zata wuce sarki yace "Ina zaki haka kika caɓa ado nuratu?"
Inda inda ta kamayi tasan in tace Kano zata bazai barta ba "Amm...eh dama dama inna ne ta aikeni gidan ƙawarta Baba zulai "
Sosai yaji bai yarda da ita ba ,tashin farko ransa ya basa kodai fadan da yayi mata ne ta haɗa kaya zata gudu....kinji zuciya mai saƙe saƙen sharri
"Yakinan, shine harda jaka? bani kayan In gani "
"Baba tace kar a buɗe"
Baba Mudi baban yarinyar da tayi cikine ya karɓe maganar
"Ke kinci gidanku ,mai martaba yina fadi kina fadi ? Dan bokon da kikayi ne ya baki wannan damar ko? Duk ƙaniyarku zamuci ,tun kafin ki riƙa mana irin ƙawarki zamu zane ki" .
Shiru tayi ta sunkuyar da kai ta na mamakin me yasa ake dangantata da wacce tayi cikin shege ? Wai karatun bokon laifine?
Tanaji tana gani suka amshe jakan suka buɗe
Ɓarkewa da salati shamaki yayi ya maza ya kame baki yina jinjina kai
"Shamaki meye a ciki ?"
Yanda gaban kowa ya fadi haka ma gaban Nuratu ya yanke ya faɗi,miƙa wuyarta tayi tanason ganin me ke a ciki da yasa shamaki rafka salatin nan
Anyi anyi da shamaki ya fadi yaƙi
Kawai sai sarki ya mike jikinsa na rawa ya daga jakan gabaɗaya ya juye a ƙasa
Subhanallh abun ba ƙyawun gani Buran maza ne na roba baƙaƙe da farare dogaye da guntaye.
No comments