Recent Updates

Sugar Mommies A

 


12/4, 09:56] أم افنان✍️💞: *A*


_Ƴar ƙauye ABU a.k.a ZEE MAAMA kan ta waye_


Washekari 

Sarki zai tafi gona ya biya ta sashen Iya Talatu ,ya sa aka taso masa Nuradden ya tasa ƙeyarsa suka wuce gona tare 

Tafkeken gona ne yafi girman filin stadium goma ,don haka tun daga wannan garin har ya shiga wani garin 

Tafiya sukeyi a keken shanu yina nuna masa wuraren da suka kasance mallakinsa ,a ciki akwai ɓangaren kiwon kifi sashenshi daban ne ,akwai na kiwon shanaye da akuyoyi shima ya tafi iyakan ganinka ,don harda gidajen gona inda ma'aikatan da suke nome gonan suke zama da iyalansu 

Nura kallon babansa yayi "Baba Ni yarone me yasa kake nuna mun wuraren nan kuma,sannan ka dade baka zuwa gona meyasa yau?"


"Saboda halin rayuwa Nuradden koda na mutu kaine namiji kaɗai cikin ƴaƴana don haka kaine zaka kasance magajina,duk ƴan uwanka matane da sannu kai zaka riƙe su da iyayenka mata har ka aurar dasu ,in ƙasa ta lulluɓe mun ido"


Zaro ido Nura yayi yina kallon baban "Baba mutuwa zakayi ne?"


"Ina! Bazan mutu ba ɗan nan dukda mutuwa abace wacce ba makawa sai ta faru ,amma ba yanzu ba sai naga girmanka autana!"


Murmushi yayi yina kaɗa kai 

Sunyi rana sosai a gonar mutanen dake cikin gidajen gonan suka dinga aiko masu da abinci kama daga gasashen kifi zuwa fura da nono 

Da zasu tafi aka cika ma Nura kayan marmari irinsu gwaiba ya taho dasu gida .


***

Har suka je gonan suka dawo babu wanda ya sani cikin iyalan gidan sai da dare an hadu ana cin abincin dare sannan Nura ya kalli rafa'atu

"Ya rafa aiko baba yaje dani gonan mu ya nuna mun ko'ina ,harma an bamu kayan marmari saidai kafin mu kawo gida baban ya karba yayi kyauta dashi ,hum hum manya manya da kinga irin gwaban gonanmu" 


"Kai Nura shekaranka goma fa ,ai baka isa ɗaukan fatanya ba"


"Ai ba aiki zan ringayi ba yace ne ya nuna mun wajen mune ko bayan ransa nine babba,watarana zan aurar daku in ya mutu..." 

Dariya wasila ta fashe dashi "Kaji shashasha mai son girman tsiya Ni tashi ɗibo mun ruwa a randa ga moɗa can" ta nuna masa moɗa akan wani tsohon table.


Itadai duk abinda akeyi Nuratu bata sa masu baki ba sai saƙan kwarashenta takeyi ,suma ba wanda ya dauki maganar serious ,saidai Inna Abu zata shigo kenan ta soma jiyo hiransu nan kuwa ta tsaya ta gama jin hiran tas daga nan kuma ta banko kofa ta shigo yaranta ta tsintsince 

"Ke Wasila yaki,kema rafa'atu zo ku biyoni"


Nuratu kallon inna Abu tayi "har da Ni?"


"Yi zamanki"


Tayi magana fuskarta a daure ,to dama tasan halin mutuniyarta indai wajen masifa ne don haka ta cigaba da saƙa hulanta 


Suna keɓewa kallon yaranta tayi ta soma surfa masu bala'i tana aibata babansu 


"Haah wai me ya faru ne inna yau kuma kike zagin baba?"


"Eh shashashu bakuda wayo ubanku baya sonku don yaga Ni ban haifa da namijiba zai angaza ma Talatu da yaranta dukiyarsa kakaf inya mutu kun tashi a tutar babu"


"Inna yaushe yace hakan?"


"Bakuji mai Nura yake cewa ba? Shine ai bayida wayo ya tona asirin amma inda uwarsa tasan zai fada da ta kwaɓesa ,yanzu dai abinda za ayi kuje ku sama babanku kuce Lallai sai an raba gadon nan an bawa Kowa nasa tun yina raye in ba haka ba ko kayan daki sai kun rasa in kun tashi aure"


Duk zaman lafiya da kaunar junan dake tsakanin yaran nan saida ta hure masu kunne ta cusa masu ƙiyayyan ƴan uwansu nan take ,Suka kuwa ɗauki maganarta da zafi ,zaf zaf zaf suka nufi sashen babansu yina kishingide akan buzu yina wiridi da dogon carbinsa,suka fara dukan masa ƙofa kamar sa'an wasansu


Dam! Gabansa ya fadi baisan sanda ya katse abinda yakeyi ba ya fara cewa "Kaii...kaii ...kai waye nan?"


"Wasila da Rafa'atu ne Munzo ne a bamu haƙƙinmu!"


Mamakine ya kama mai martaba ,yaushe yaransa suka zama tsagera haka? Kodai mafarki yakeyi? What a nightmare? God forbid


Cigaba da dukan masa ƙofa sukayi jin bai sake magana ba yasa suka kware asabarin suka shiga ,inna Abu na masu sigina da ido tana ƙara masu famfo


Tsaya masa sukayi ƙerere a ka "Baba a bamu gadonmu kamar yanda ka baiwa Nura da ƴan ɗakinsu nasu"


Shiru yayi cikin ɓacin rai ,yanzu ya gano inda matsalar take ,kuɗi makullin sharri kenan!


Tsam ya miƙe ya ajiye carbinsa 

"Tabbas kunyi gaskiya haƙƙinku ko?"

"Eh" suka amsashi kowa tana kakkauda kai


Zuwa ƙarshen bango yayi ya zaro dorinan da ya sagale a ƙusa ya kuwa rufesu da duka


Tuni suka fara kururuwa 

Wufff sai ga Inna Abu ta shigo nan ta shiga tsakani tana yarfa masifa "Kunga rashin kaunar ko? Dama nace maku baya sonku yaudarace,ina kuka taɓa ganin ya daki yaran dakin Talatu ,to wallahi bazai saɓuba bindiga a ruwa babu wanda zai dauki hakkin yarana sai an bamu gadonmu"


"Abu ki kauce kar in hada dake in zaneku! "


"Ai zaka iya gwara ma ka dakeni sai in shiga gari da hujja ga sarkinsu ya tabbata mara adalci ya hana yaransa gado kuma ya zane uwargidansa. dakanni mana"


Jikinsa ne ya mutu a take kansa ya soma juya masa ya fara ganin duhu duhu laluban bango yayi ya zauna yina salati a hankali


"Abu ja yaranki ku fitarmun a ɗaki"


"Baba kawai ka bamu gadon mu zamu fita ,basai ka koremu ba"


Cashi! Ke kam kin cika shedaniya kece zaki rura mun fitina a gidana?! kece zaki ruguza mun tarbiyyan da nayi shekara da shekaru ina ma yarana ...kin cuceni abu ,abu ki fita kar fushina ya sauka a kanki" yanda yake magana as he is about to cry ,shi yasa Abun tsorata ta ja hannayensu "Kuzo muje amma tabbas sai an baku haƙƙinku sarki da Alƙali ba wanda ya isa "


Nuratu da su iya Talatu suna jiyo hayaniyarsu sama sama daga sashensu amma basu kawo fadan gaske akeyi ba don kowa dai yasan Abu batayin magana a kwanciyar hankali Kuma wai a hakan ba fada takeyi ba ,don haka koda sukaji ba wanda yabi ta kansu ,suna hiransu tana iza ma mamanta wutan dafuwar kan akuyan da sukeyi .


Kalma daya ya shiga kunnen iya Talatu "Sarki da Alƙali ba wanda ya isa ya hanani karɓar gadon ƴaƴana in an isa a cucemu in fisis"


Miƙewa tayi da sauri ta nufi sashen sarki nan taga Abu ta fito a harzuke 


"Lafiya yaya hayaniyar me nikeji"


"To makira ,kisina! Jikan mayu jikan matsafa ,ai baki yarba an tsotsi karuwanci da kisisina a nono ,Buzaye lafiya ne? To bari kiji in uwarki tana kwana a tandun tsafi ubanki na zina da mahaukaciya sai an bani gadon ƴaƴana don tsafinku bazai tasiri a kanmu ba"


"Subhanallh yaya kinsan me kuwa kike faɗa? Meye zafi kike zaginmun iyaye?"


"Ƙarya akayi? Waye baisan abunda ya baro iyayenku daga agadaz ba ? Shegu matsafa ,sadaka yallah baku bara baku karuwanci ,ko ba a haka aka ganki aka auro ki ba,Allah kadai yasan abunda kukayi aka koroku daga ƙauyenku ....wooo korarru wooo korarru " ta fara bubbuge zani tana buge baki tana yi kamar za tayi mata atule da ƙasa.


Matsawa baya iya Talatu tayi ta jingina da bango hawaye mai ɗimi ya fara gangaro mata a ido


"Kuka? Sannu makira ai baki fara kuka ba,kuka kamar an maki ƙarya ,Waye ma yasan asalinku ? Wayasani ma ko uwar naki shegiya ce bata da uba a yawon duniya tsoho ya nemota ya aura? Mudai fes muke tsarkakakku ƴaƴan sunnah daga nan zan gaya maku kakana na goma wata daga na biyu an ci birki an fara kame kame"


Daga baki tayi zata mayar mata da martani sarki yayi maza ya dakatar da ita "ƙyaleta aniyarta ne zai ƙare mata , tabbas ƙwaƙwalwar Abu ya taɓu kiyi mata uzuri" 


Daka tsalle ta somayi kamar Gada ,tsabagen fitina


"Itace dai mahaukaciya mu kaf danginmu ba me tarikhin hauka ku fa....(kawai sai ta fara mata waƙan da ake ma ƴan ƙabilansu talatun) Mahaukatan Bugaje baku gaji lafiya ba...Ana biki da rani ku da damuna kukeyi..."


Tsalle Nuratu tayi "kece dai mahaukaciya ba mamana ba ga aikinki ma ya nuna haka" 


Ai bata rufe baki ba wasila da Rafa'atu suka fizgo ta suka fara duka "uwarmu kike zagi don uwarki! Shegiya jikar maroƙa masu yawon maula" 


Sosai suke lallasa Nuratu ita kuma tana cafko hannunsu tana cizonsu da yakushi .


"Yawwa kuci mun uwar shegiya yanzu nasan na haihu ƴaƴan Albarka"


Ɗaki sarki yayi da gudu ya ɗauko bulala yabisu ya fara sauke masu a jiki ,anma kamar Turi sunki sakin Nuratu duka sukeyi ,kamar ba jini ɗaya ba.



Girgiza kai Talatu tayi kawai ta ja hannun Nura suka koma sashensu suna jin kukan Nuratu 

"Iya bazamu je mu amso Nuratu ba?"


Ko kulasa batayi ba ta ƙanƙame masa hannu ta na shiga ta cusashi a ɗaki ta garƙamo ƙofa.


Daƙyar ya ƙwaci Nuratu ya shige da ita ɗakinsa su kuma sukayi sasansu riiii kamar ƴan matan amare .

Ba wanda ya sake jin ɗuriyar juna har dare 

Lokacin Iya Talatu ta gama tuƙe tuwon jiƙaƙƙen masaranta ta ɗauresa da garin albo (busashen rogo) yayi tauri sai tsatsi yake ta mulmulesu a leda . ta yi masu miya kala biyu da na ɗan yan kuɓewa yaji kifi mara manja ,da kuma miyar ganda ya sha manja yayi kyau 


Barandan da suka saba haduwa suci abinci nan ta je ta shimfida taburma da ledan cin abinci ta jera kwanukan ta kunna turaren rushi ta aje a gefe ta ajiye farantai da ruwan wanke hannu .


Ana yin sallar isha'i dama ƙa'idane wajen cin abinci Kowa zaizo ,don haka kowa ya taru Tundaga kan sarki da Nura da Nuratu saidai ba Abu da zuriyarta 


Shiru sukayi na kusan minti ashirin ba alamun zasu zo 


Kallon Nuratu da aka kumbura ma goshi tayi 

"Je ki kirawo ƴan uwanki muci abinci lokaci na ƙurewa akwai karatun dare"


Turo baki Nuratu tayi "Iya duka na zasu sake yi"


Tsawa ta daka mata "Tashi mana!"


Miƙewa tayi ba don ranta ya so ba ta shiga sashensu ,suna zaune suna cin taliya er murjin gida (Na fulawa) 


"Assalamu alaikum ,wai ance kuzo muci abinci" 


Wurgo mata mahucin gefenta tayi "fita ki bamu waje in kika sake shigo muna sasa sai na karya ƙafanki na gaba shegu ƴan asara!" 


Da gudu Nuratu ta fito tana kuka "suna ganin haka basu tambayeta mai ya faru ba ,sarki yayi masu bissmillah kowa ya wanke hannu suka soma cin abinci ,ba wannan rahan da wasa da dariyar da aka saba aka gama ya mike ya nufi sashen inna Abu da kansa yace su fito karatu 


"Sunyi barci Ni kuma bazan ɗauki haƙƙinsu ba bana tashin mai barci ,karatun ba na tambayar kabari bane"


Girgiza kai kawai yayi ya shige ɗaki yana zancen zuci "Gida na ya watse Ubangiji ka yayyafa ma bala'in nan da ta Kunno mun kai ruwa!"


Kwana uku ana takaddama sarki ya doje lallai baya raba gado kuma ragamar duk dukiyarsa ya damkasu a hannun Nura ,ya kwaso duk takardun ƙadarorinsa ya samu fallen zani ya ɗaure gam ya saka a leda ya ɗaure ya tasa Nura sukaje bayan gidansa ya saka a wani tukunya ya hake rami ya burne 


"Nuradden kar a tono wannan sai bayan shekaru ashirin kana jina?"


"Baba don Allah ka Bama inna ABU abinda suke so"


"Kaima za kai jayayya dani ne?" 

Girgiza masa kai yayi ma'ana ‘A'ah’ "to mu tafi gida "


No comments