Sha'awar Shi Nake 9
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHA'AWAR SHI NAKE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*PAID BOOK*
*9*
Safiyya Abdullahi shine aynihin sunanta,ƴar wani ƙauye ne da ake kira Jirɗeɗe dake can ƙasar daura.
Mahaifinta malam Abdullahi mutum ne nagari me kuma tsoron Allah.Matan shi biyu furera da hajara,furera itace uwargida se hajara amarya,
Ƴaƴan furera biyar yayinda ita kuma hajara keda guda ɗaya tak wato safiyya.
Tsangwama ta gidan duniya safiyya da uwarta suna shanta agurin furera da ƴaƴanta,amma koda wasa hajara bata taɓa ɗaga baki tayi magana ba,saɓanin ƴarta safiyya akwai tsiwa ko zata sha duka a gurinsu se tayi magana matuƙar taga anyi musu ba daidai ba.
kulasun da takeyi shi ke sawa sui ta dukanta wanda ita kuma mahaifiyarta koda wasa bata son damuwar Æ´ar tata.
Haka rayuwar tasu take garawa yau fari gobe tsumma,dan malam Abdullahi mutum ne me ƙaramin ƙarfi.baya iya ɗaukar nauyin gidan duka hakanne yasa kowaccen su ke neman abun rufawa kai asiri.
Hajara tayi ƙoƙarin saka safiyya a makarantar boko,tunda mahaifinsu ke koyar da su ilimin addini ita da sauran ƴan uwanta.
Wainar rogo safiyya ke soyawa a ƙofar gida gami da awara,kuma ba laifi ana siya.
Da ribar suke adanawa a biya mata kuÉ—in makaranta
Safiyya yarinya ce me tsiwa tun tasowarta bata tsoron girman ka in ka mata se ta rama,sede tai ta shan duka a vanza amma bazata dena ba.
A fannin makarantar da take zuwa ko ba laifi tana da basira sosai.
To komai ya samo asali ne bayan rasuwar iyayen Safiyya,mahaifiyarta ta fara rasuwa sannan mahaifinta,kasancewar mahaifiyarta ƴar garin medugurice kuma yawan faɗa da ake yasa sukayo gudun hijira ita da mahaifinta wanda shi kuma ya rasu a sansanin ƴan gudun hijira,mahaifiyarta kuma da ɗan uwanta lokacin basa nan akaci garin nasu da yaƙin taaddanci.
Acan malam Abdullahi ya ganta ya aureta,to duk yadda dangin baban safiyya sukaso abasu ita bayan mutuwarshi furera hanawa tayi,acewarta malam yace kar ta raba masa kan Æ´aÆ´a.
Wannan kenan
Wahalhalu na gidan duniya safiyya ba wanda furera bata ba ta ba,kowanne ayki na gidan ita zatayi shi,hakan be damun safiyya shiyasa takeyi,
Hajiya jummai me kai yara aykatau birnice ta sauka a ƙauyen dan ɗaukar yaran da zasu je aykatau,
Ayko furera ba tare da tunanin komai ba ta bada safiyya,wayyo safiyya ranar tayi kuka kamar ranta ze fita,dan wani zuwa da hajiya jumman ta taɓa yi lokacin mahaifiyarta na raye,tace ta bata safiiyar takaita gidan aykatau,ƙin amincewa tayi yau gashi bayan babu ita kishiyar uwa ta bada ita an tafi da ita.
ABUJA
Can hajiya ta kaisu inda kowa aka kaishi,gidan aykinsa,ciki harda safiyya inda aka mata masauki agidan wani Ambasador,Alhaji Kabiru,da matarsa Hajiya Zainab,se yaransu guda uku É—aya namiji se biyu mata.
Namijin shine babba,me suna,Anwar me shekaru talatin se me binsa Hamra me shekara 23,se autarsu Nauwara.wacce ita kuma shekarunta 14.
Gidan Alhaji Kabiru ne gidane da sika ginashi kan so da ƙaunar junansu su duka,duk wata damuwa ta ɗayansu tasu ce su dika.
Anwar kyakkyawane ajin farko dan ba abinda ya rabashi da mahaifiyarsa,komai nashi me kyau ne,ko kaÉ—an beson hayaniya,kasancewarshi muskili.
Sosai mahaifinshi ya narkar da dukiyarsa wajen ganin Anwar ya zama likita,a can ƙasar England,hakan ne ta faru,sede koda ya cika burin na mahaifinsa,shima tuburewa yayi kan se shima nashi burin ya cika nason zama ɗan ƙwallon ƙafa.
Abunka da É—an so,haka mahaifinsa ya goya masa baya ya kashe manyan kuÉ—aÉ—e wajen ganin hakan ta tabbata.
Bayan kuɗi da aka kashe,shi kanshi Anwar ɗin ya iya kwallo ba kaɗanba,dan club da dama sun so yaje ya taka leda acan amma yaƙi shi burinshi ya ganshi sanye da jar jessy da fari,wato ƙungiyar Masu gida Asnal,a wannan club ɗin kawai yake so ya taka ledarsa.
Haka mahaifinsa yabi duk wata hanya da burin É—an nashi ze cika kuma hakan akayi.
Kasancewar Anwar farine bana wasa ba yasa kida ya shiga ƙungiyar ya saje da sauran turawan duk da farinshi be ƙarasa nasu ba.
Ba kasafai yake zama a nigeria ba shiyasa da yawa mutane vasu sanshi ba anfi sanin sauran Æ´aÆ´an nasu.
Lokacin da safiyya ta dira wannan gida sosai mutanen gidan sukayi marhabun da ita.
Muje zuwa
No comments