Recent Updates

Sha'awar Shi Nake 8

 


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 *SHA'AWAR SHI NAKE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀




*Zahra Surbajo*



🧺


*8*



A hankali take sake shafa fuskarta cike da yanayi na tsoro da firgici,ita de tasan ba haka kamanninta suke ba,to ya akayi ta dawo kama da wannan azzalumin mara imanin.


Tambayar da takewa kanta kenan amma kuma ta rasa amsarta,


Ƙwanƙwasa ƙofar da akayine yasa ta dawo hankalinta ta dedeta natsuwarta sannan taje ta buɗe ƙofar,Aunty muniba ce.


"ƙanwata bakiyi bacci ba,?"cewar aunty muniba tana murmushi.


Kallo jannat ta bita dashi na alamun rashin sani kamin ta koma gefe ta bata hanya ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin.



Tura ƙofar muniba tayi ta kulle da makulli sannan

 taja hannun jannat É—in suka shige can Æ™uryar É—akin kasancewar É—akin ciki da falo.


Gefen gado ta zaunar da ita sannan itama ta zauna,sannan ta kamo hannunta ta riƙe tace,cikin harshen turanci,"nasan kin ƙosa kisan ko mu suwaye,me yasa muka raboki da ƙasarku muka kawoki nan gami da sauya miki kamanni ko?"tai mata tambayar hawaye na biyo idonta.


A  sanyaye jannat ta É—aga mata kai,share hawayenta muniba tayi sannan ta É—ora da cewa."muna da dalilin yin hakan"daga nan ta kwashe komai ta sanar da ita har da mutuwar jannat,ta Æ™arasa maganar cikin matsanancin kuka.


Itama jannat É—in kuka take kamar an mata mutuwa,sosai daddy sa mamy suka bata tausayi duba da irin mugun son da sukewa jannat.


Durƙusawa muniba tayi agabanta sannan tace murya na rawa"bamu sanki ba,bakuma musan komai akanki ba,kawai mun aminta da umarnin zuciyar mu cewa zaki taimaka mana,alokacin kina buƙatar rayuwa muka baki zuciyar jannat,don Allah ku tausayawa iyayenmu halin da zasu shiga,kuma inda hali zanso insan labarinki,da kuma na iyayenki,"



A hankali ta lumshe idanunta sannan ta buÉ—e,ta goge hawayen dake biyo kumatunta tace"jannat ta mutu jannat ta dawo,kamin nan zanso kisan koni wacece kamin kiban ragamar rayuwaru gaba É—aya"cewar jannat tana share hawaye.



A hankali kanta ya fara tariyo mata abinda ya faru da ita   abaya,nisawa tayi sannanta fara ba aunty,muniba labarin nata.



Mije zuwa



Surbajo for life.

No comments