Sha'awar Shi Nake 5
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHA'AWAR SHI NAKE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*PAID BOOK 500*
*5*
Duk wata ƙofa da zata bayyana aynihin abinda ya faru seda Alhaji bukar ya rufeta.
Muniba ko kallon gawar jannat da tayi shi ya maida ita wata sususu,gaba É—aya hankalinta ya bar jikinta.
Sosai likitocin suka koma kan sabuwar jannat É—in suna bata duk kulawar data dace,inda nan da awanni biyu ake sa ran farfaÉ—owarta.
A can gida nigeria ko Alhaji se cikin dare ya farka kuma jikin nashi da sauƙi dan haka ƙosawa yayi gari ya waye yabar ƙasar,se kiran number su muniba yake bata zuwa hakanne yasa hankalinshi duk be kwanta ba.
Manager shi tuni ya tanadar masa komai na tafiyar tashi wayewar garin kawai suke jira.
*********
Sosai Alhaji ya tsarawa likitocin abinda yake so su faÉ—awa Mahaifin jannat in ya iso.
kamar yadda aka faɗi hakance ta faru sabuwar jannat ta farka,se kalmar shahada take maimaitawa raunukan jikinta ne sukasa ta kasa miƙewa zaune.
Shuru sukayi suna kallonta idonta arufe ta kasa buÉ—ewa. se ajiyar zuciya take akai akai.
Office likitan ya kirasu inda yafara musu bayani
"ayki yayi kyau ina tayaku murna,abu na gaba shine,ɗabiunta da tunaninta,ze koma irin na wacce ta mutu,zuwa tsawon wani lokaci kamin brain ɗinta ta saba da baƙuwar zuciyar ta dawo ta aynihi,sannan plastic surgery na maida kamanninta irin na wacce ta mutu zamu shiga da ita da ƙarfe biyar na yamma,ina muku fatan alkhairi "
"mungode likita,dan Allah ayi duk me yiwuwa ayi akan lokaci dan munsan Alhaji wato mahaifinta yana hanyar zuwa ƙasarnan pls doctor,"cewar muniba tana share hawaye.
"sannan doctor dan Allah akula da kyau kar abar wata alama da zata nuna ba ita bace ayi komai sak da sak"cewar Alhaji bukae cikin yanayi na damuwa.
"da gawar waccan jannat É—in zamuyi amfani kuma insha Allahu bazaa samu matsala ba,Allah yaga nufinmu ze taimakemu"cewar likitan yana murmushi.
Kamar yadda likitan ya faɗi hakan ce ta faru,ƙarfe biyar aka shiga da ita surgery ɗin,inda muniba da mijinta suka duƙufa adduar fatan nasara.
An shiga da ita kenan,Mahaifinta wato Alhaji mus'ab da mamy suka iso, gaba É—ayansu a firgice suke. dan ko lura da su muniba dake tsaye basuyiba,seda,muniba ta kamo mamy shi kuma Alhaji bukar ya kamo aminin nasa,
Muje zuwa
Surbajo for life.
No comments