Recent Updates

Sha'awar Shi Nake 4


 ðŸŽ€ðŸŽ€ðŸŽ€ðŸŽ€ðŸŽ€ðŸŽ€ðŸŽ€ðŸŽ€

  *SHA'AWAR SHI NAKE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Zahra Surbajo*




*PAID BOOK 500*



*4*




ICU akasa jannati dan haka jira sukayi,tukunna na wasu awanni kamin abasu damar shiga.


Addua ba irin wacce basayi tare da fatan ganinta cikin kyakkyawan yanayi.


Lokacin da aka basu damar ganinta muniba har gudu take wajen son ganin jannat É—in,iso aka musu kan gado da take.


Kukane yaci Æ™arfin muniba lokacin  da tayi arba da jannat kwance tsakanin mutuwa da rayuwa.ko kamanninta baa ganewa sabida Æ™onewar da tayi a fuska


Oxygen ne ke taimakawa numfashinta,zamewa muniba tayi ƙasa ta durƙushe tana kuka,kamar wacce akace ta ɗago carab idonta ya sauka kan ƙafafun na jannat,da sauri ta miƙe tsaye tana bin ƙafar da kallo bakinta har rawa yake wajen faɗin.


"wannan ba jannat bace,wannan ba jannat bace,jannat babu cindo a ƙafarta"take faɗi cikin ƙaraji tana ƙara bin ta da kallo.


A gigice Alhaji bukar ya kamo muniba,yana faÉ—in"mun shiga uku muniba in ya tabbata jannat ta mutu"


Likitan dake tsaye akansu ne ya fara yimusu bayani cikin harshen turanci.


"jannat na buƙatar agajin gaggawa,in ana so ta rayu,dan zuciyarta kanta tayi week akwai buƙatar ay mata dashen zuciya in har akwai damar yin hakan bayan wainnan manyan raunuka dake buƙatar kulawa ta musamman"


Cikin ƙaraji muniba ke faɗa masa"wannan ba jannat bace ba ita bace!!!!"


Sosai likitan ya firgita,da jin cewa ba itan bace,gashi munibar kuka take kawai kamar ranta ze fice taƙi tsayawa ma tai musu cikakken bayani.


Gadon dake gaban na jannat ɗinne mara lafiyan kai ta fara tari da Sauri suka kai dubansu kanta,da wani mahaukacin gudu muniba ta ƙarasa jikin gadon tana faɗin "jannatin baba"tana ƙarasawa ta kamo hannunta,tana kuka.


Da sauri mijinta da likitan suka ƙarasa jikin gadon,inda likitan yace"itace wannan?"


"Itace doctor itace wannan"


"mu kuma an kawo mana ita nan a matsayin victim na mazauna yankin da jirgin ya faÉ—i,wanda akasarinsu  baÆ™in haurene,suke Æ™arasa rayuwarata ashe mistake akayi"cewar likitan yana sake binciko bayananta ajikin computer gabanshi 


Daga muniba har mijinta rufuwa sukayi akan jannat suna kiran sunanta amma bata ma san sunayi ba.


Likitan ne ya katsesu da cewa"sede kuyi haƙuri dan yanayinta yafi na wancan muni,ita acan ma an ɗauka ta mutu,kawosu nan ne ma ta farko,sede bincike ya nuna bazata wuce 24 hours zata mutu,sabida komai na jikinta ya dena ayki se zuciyarta ce kawai ke da amfani"



Iya tashin hankali sun shigeshi muniba sunan Allah kawai take kira,dan ji take kamar zata mutu sabida É—acin da zuciyarta ke mata.


Shiko Alhaji bukar tuni ya tafi tunanin mafita wacce kuma ya samota,zartarwa kawai ya rage yayi.

.

A tsanake yace da muniba ta tashi zasuyi magana ba musu tayi abinda ya buƙata.


Fita sukayi harabar asibitin bayan sun raƙi alfarmar likitan kan ya jiracesu su dawo.


"muniba mafitace na samo game da wannan ƙaddara data faɗa mana,sanin kanki,Alhaji baze jure rashin jannat ba,haka ita ma hajiya,right"


Natsuwarta ta tattaro gu guda sannan tace"hakane dear"


"good to kinga ko dole ne miyi taimako yanzu mu jefi tsuntsu da dutse É—aya,in har ya tabbata jannat ta mutu,to dole aciro zuciyarta adasawa yarinyar nan ta gefenta,sannan yazama wajibi mu saki kuÉ—i,ayiwa yarinyar plastic surgery,amaida kamanni ta sak da jannat.bayan ta samu sauÆ™i mu sanar da ita taimakon da zata yi mana,in tana da iyaye da zaran ta kammala tai tafiyarta,in kuma yazamana bata dasu se ta  maye mana gurbin jannat,amma ke ya kika gani "


Ko kaɗan muniba bata da ja akan batun na mijinta,dan hakan shine mafi sauƙi dazasu kwantar dahankalin daddy.

.

Bayan dogon bayani,da rarrashi,da ƙyar likitocin suka amince da batunsu.sosai suke murna.


Yadda Allah yaso haka yakeyi jannat bata wuce awannin da likitocin suka É—iba mata ba tace ga garinku nan,muniba tayi kuka kamar ta haÉ—iyi zuciya.


Cikin abinda be wuce awanni goma ba aka gama dasa zuciyar jannat ajikin wannan mara lafiya cikin ƙwarewa da sanin makamar ayki komai ya gudana.




Muje zuwa

No comments