Sha'awar Shi Nake 3
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHA'AWAR SHI NAKE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*PAID BOOK*
*3*
A tsaye suke shida muniba a airport domin tarbar jannat wacce awa shida kenan da tasowarta.
"Dear sun kusa sauka nasan,inde ba transit aka musu ba"cewar muniba tana kallon mijin nata Alhaji bukar.
Murmushi yayi sannan yace"insha Allahu,ta kusa isowa sabida kinga....."sanarwar da ake yi ne a lasifikar airport ɗin ce tasa yay shiru be ƙarasa faɗin abinda yakeson faɗi ba,
Hatsarin ake faÉ—i,a gigice suka waiga kan allon tv dake nuna labarai na cnn,se hoton passport na jannat dake yawo a allon tv É—in,me sanarwar kuma na faÉ—in cikin harshen turanci.
"jirgi me lamba kl500 daya taso daga nigeria,yasamu hatsari akan hanyarsa ta isowa australia,inda fasinjojin cikinsa da matuƙa da maaikatansa baa samu me rai ba se mutum ɗaya me suna jannat mus'ab ɗanmusa,tana can a babban asibiti dake babban birnin ethopia wato birnin adisababa"
"innalillahi wainna ilaihirrajiun,"itace kalmar dake fitowa daga bakunansu.
A gigice sukayi sashin mahukuntan airport É—in,inda Alhaji bukar ya nemi shatar jirgin Æ´an kasuwa wato private jet,daze kaisu ethopian yanzu yanzu.
Baa sha wiyar samu ba abunka da batune na naira,cikin abinda be wuce awa guda ba aka ba jirgin izinin tashi,wayyo muniba kuka take kamar idanunta zasu faÉ—o,Alhaji bukar ke tausarta.
A Nigeria kuwa daga daddy har mamy jikinsu babu kuzari dan haka kowa É—akinshi ya wuce ya kwanta,dan sun rasa meke musu daÉ—i.
Se gabansu dake yawan faɗuwa wanda daddy ya alaƙanta hakan da rashin son rabuwa da jannat ɗinsa.kashe wayoyinsu sukayi dan su samu sukunin yin baccin.
Se bayan sallar magrib ne Daddy ya kunna wayoyinsa inda yaga saƙwanni rututu,wanda yaga mafi yawa na jaje ne daya rasa gane kan su,
Wayarshi ce ta shiga ruri,wani amininsa ne ya kirashi da hanzari ya É—aga.
Bayan sun gaisa ne yake ce masa"Ashe abinda ya faru kenan,tun É—azu nake neman wayarka in maka barka gami da jaje amma wayar akashe"
Cikin rashin fahimta daddy yace"Alhaji Aminu duk ka sani a duhu wai meke faruwane nifa bansan me ake ta jajantamin ba"
"ka kunna tv yanzu ka kamo cnn"cewar abokin na daddy cikin yanayi na tausayawa.
Jikin daddy har rawa yake yayi abinda ya umarceshi.
Hoton jannat É—i shi ce ke yawo as only survivor data fita a jirgin data shiga É—azu.
"innalillahi wainna ilaihir rajiun"itace kalmar da daddy yake faÉ—i yayinda wani gumi me zafi ya shiga karyo masa,
Shigowar mamy a gigice ne yasa ya ɗago ido yana kallonta,bakinshi har rawa yake wajen faɗin"kin gani ko hajiya,kinga abinda ya sami jannati na,shiyasa banaso tanayin nisa dani"ya kasa ƙarasa maganar sakamakon tarin daya fara,jini na biyo bakinsa.ya dafe gefen zuciyarsa.
Cikin kuka hajiya ta riƙeshi tana faɗin"godiya zaka yiwa Allah data rayu,Alhaji ka kwantar da hankalinka don Allah"
"jannati na ta faɗo daga sama shine kike tunanin hankalina ze kwanta ko bata mutu ba,kiramin manager ayi shirin tafiyata ethopia yanzu ta kowanne hali"da ƙyar yake maganar.
Likitanshi hajiya ta fara kira sabida gudun ita jannat bata rasa ranta shi ya rasa nasa dan taga bata ma lafiyarsa yake ba.
Baa jimaba likitan nasa ya iso,inda ya fara da bashi taimakon gaggawa.
"Alhaji akwai buƙatar ka kwanta ka huta dan zuciyarka ta huta itama dan ka samu heart attack"
"baze yiwu in kwanta ba doctor ethopia zan tafi yanzu haka Æ´ata ce tayi hatsari a jirgi kuma acan akayi addmiting É—inta"
"she is survivor Alhaji inaga godiya zaka yiwa Allah akan hakan kuma nasan duk kulawar data dace ita za'a bata acan É—in,ka bari a kula da taka lafiyar first in yaso zuwa gobe se ka tafi"
Da ƙyar daddy ya amince da akula dashi ɗin dan gaba ɗaya hankalinshi na kan jannatin sa.
Dik abinda ya dace shi likitan yay masa sannan ya bashi magunguna wanda tun kan yabar gurin daddy bacci ya É—aukeshi.
Mamy se alokacin tasamu sukunin fashewa da kuka dan dama ta daure ne dan karta ƙara jefa Alhaji cikin damuwa.ko a wanne hali jannat ɗin take yanzu oho.
Alwala ta ɗauro tazo ta fara nafila tana roƙon Allah ya tsare mata jannatinta.
A can kuwa Muniba da mijinta sun isa ƙasar ta ethopia lafiya inda basu wani sha wiya ba aka sadasu da asibitin da jannat take da sauran gawarwakin fasinjojin.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[8/18, 09:16] zahr
No comments