Recent Updates

Sha'awar Shi Nake 22

 


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SHA'AWAR SHI NAKE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀





*Zahra Surbajo*





*FREE BOOK*


*Bana tura wannan littafin ta pc, sabida free ne Ku nema a group, karki tambaya ban turaba kiji haushi*



*22*



Gaba É—aya hankalin Anwar kusan barin jikinshi yayi dan komai nashi na gun safiyya,burinshi ta fito ya ganta yaga halin da take ciki.

Ita ko tana can in banda kuka na baƙincikin rabata da budurcinta da Anwar yayi ba abinda takeyi.


Ranar yini tayi bata buɗe ƙofar ta ba,hakan sosai ya ɗaga hankalinsa,dan haka momy ya samu hankali tashe yace"momy sofiyya fa bata fito break fast,ba bata fito lunch ba bare ayi batun dinner,pls momy kije da kanki ki bincika kome ya hanata fitowa"yayi maganar kamar me shirin yin kuka.


"nima na lura da hakan Anwar bari in dubo da fatan de ba wani abu kai mata na É“acin rai ba?"


Kai kawai ya gyaÉ—a mata dan ya kasa magana,burinshi kawai a sata ta buÉ—e É—akin.


Momy ɗakin na safiyya ta nufa da kanta ta ƙwanƙwasa,gamida faɗin"safiyya buɗe ƙofar nice"


Safiyya dake zaune kan abun sallah,jin muryar momy ne yasa tayi ƙoƙarin miƙewa da ƙyar tazo ta buɗe mata ƙofar,ta koma gefe ta tsaya da kumburarrun idanunta.


Shiga cikin É—akin momy tayi shima da sauri yabi momyn a baya,ayko sosao É“acin rai ya bayyana akan fuskarta na shigar shi cikin É—akin.amma bata da yadda zatayi se ta koma gefen gado ta zauna,


"safiyya lafiya kike zaki kulle kanki a É—aki kina kuka,?me ya sameki?"momy ta tambaya cikin nuna kulawa,

...


Wasu hawayene suka biyo idanunta,da sauri Anwar ya runtse ido dan baya son kukanta ko kaɗan soya masa zuciya yake yi.da ƙyar tace"kaina ke ciwo momy shine yasa"


"maza ki tashi kuje can É—akinshi kici abinci kisha magani,ba kya zo ki kulle kanki ke kaÉ—ai a É—aki ba"cewar momy tana kallon Anwar.


Ayko ji yayi kamar ya goya momy dan daɗin da yaji na hukuncin data yanke,dan haka da sauri ya matsa kusa da safiyyar yace a tausashe "pls,sweetheart"ɗago idanunta tayi ta saukesu akan nashi ɗauke da tsantsar ƙiyayyar da take masa,wanda shi da kanshi ya karanto hakan.

..


Miƙewa tayi badan taso ba,ta yi gaba tana ɗan ware ƙafa alamun har yanzu zafin takeji.


Be ko saurari momy ba ya mara mata baya da sauri,dan kar ta faɗi.da kanshi ya buɗe mata ƙofar ta shiga shima ya shiga ya turo ƙofar.


Suna shiga ta zame hijab ɗin dake jikinta,ba riga se ,zani kawai data ɗaura daidai ƙugunta,ko bra babu ajikinta,hannu tasa ta kwance zanin ya faɗi ƙasa,tace cikin kuka.


"kazo ka Æ™arasa amsar sadakin naka!!ka taso ka amsa nace !!!ko  ba shine yasa aka kira maka ni ba,kazo ka gama amsa nace"tayi maganar cikin Æ™araji tana kuka.


Shima da yake gefenta kukan yake,dan shi baze iya misalta son da yake mata ba,duƙawa yayi ya ɗauko zanin nata ya nufi ɗaura mata ayko taƙi yarda,



Ƙarfi yasa ya rungimeta ajikinshi cikin sautin kuka yace "sofiyya ba shi nake buƙata ajikinki ba,wallahi gaba ɗayanki nake so,ko ada dana aureki banyi haka dan shaawa ba,don Allah ki sassautawa zuciyata,wallahi zan iya macewa"yayi maganar yana me ƙara riƙeta ajikinshi.


"ƙarya kake,wallahi ƙarya kake, baka sona nasani dan da bakinka ka faɗi, cutar kuma da kamin Allah ya isa ban yafe ba"


Da sauri ya manne bakinshi kan nata ayko ta kwace tana faɗin "yauwa maza ka ƙarasa ay dan haka ka aureni maza ka sake kwanciya dani baƙin mugu"



Maganganun ta suna masa zafi a zuciya hakanne yasa ya saketa itako ta durƙushe a gurin tana kuka,gamida faɗa masa duk maganar data zo bakinta.



Zaninta ya É—aura mata sannan ya maida mata hijabinta.


Fita yayi zuwa kitchen ya É—auko mata abinci da ruwan tea me kauri ya  kawo mata.harara ta watsa masa lokacin da yake Æ™oÆ™arin zama ya ciyar da ita, fasawa yayi ya tura mata plate É—in,ya koma gefe,yana kallonta.


Safiyya bata ƙi ba taja abincin taci tasha tea ɗin,wayyo Anwar jikinshi har ɓari yake,gurin miƙa mata ruwan sha.


**********




Haka zaman yaci gaba da tafiya,ko kaɗam safiyya bata ƙaunar ganin shi,shi ko ji yake kamar ya maida ita ciki.


A haka yaje yay mata passport da visa na tafiya turai sati me zuwa,dan baze iya tafiya ya barta ba.

.

Koda ya tuntuɓi iyayensa kan ƙudirinsa na tafiya da ita dukansu suka goyi bayan hakan.



Yayinda ita kuma tayi tsallen albarka ta dire tace in ya tafi da ita yace É“atar da ita zeyi acan anemeta arasa kowa ya huta.



Sosai aka kwashi dramer dan har seda ƙanin babanta yazo sannan aka shawo kanta.



Ranar litinin sukayi bankwana da kowa,jirgin su na campanyn ethopia airline ya É—aga dasu cikin aminci,


Ko a jirgin sam taki yarda koda magana ta fatar baki ta haɗasu,har suka iso ƙasar ta ethopia zaa musu transit.



Suna fita daga jirgi,tace masa rai a É“ace zatayi fitsari.



"muje in nuna miki toilet É—in,"cewar anwar cikin faraa.


"kwatantamin zakayi "ta buƙata.



Ba tare da tunanin komai ba ya kwatanta mata,ya koma gefe ya zauna zaman jiranta.



Itako tana É—anyin gaba ta fece da gudu daga harabar inda yake,cikin dabara ta fice daga airport É—in sakamakon passport É—inta dake hannunta.



Koda ta fita gudu kawai takeyi,kasancewar gurin duk ƙauyukane yasa ta yanke shawarar shiga wani ɗan ƙaramin gini da ta gani a gefen hanya.


Shigarta wannan gini yayi daidai da faÉ—owar jirgin dake É—auke da jannat,har wannan tsautsayi ya rutsa da ita.



Tana kaiwa nan a ba Aunty muniba labarin nata ta sake rushewa da kuka wacce itama munibar kukan takeyi na tausayin safiyyar wacce ta rikiÉ—e ta komo jannat.


To labari ya É—auko seti se ku dage da comments


Mije zuwa

No comments