Recent Updates

Sha'awar Shi Nake 20

 


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

  *SHA'AWAR SHI NAKE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀e




*Zahra Surbajo*



*Sanarwa ga maabota bin rubutuna,littafina sabo me suna GIMBIYA SABRINA(THE KINGDOM OF ISOLATION) Ze iso gareku a sabon wata me kamawa,ashirin ga watan,sede na kuÉ—ine,300 kacal zaku biya ku sameshi, ga wainda suka siya da wuri kan afara,da zaran na fara sakinshi kuma 500 ne,*


*ku hanzarta siya dan nishaɗi faɗakarwa,ilimantarwa,da kuma salon soyayya da bata buƙatar maganin mata agidajenku na aure,karki bari abaki labari da abaki gwara ki bayar 300 kacal,surbajo ce for life*


*Ga masu kuma buƙatar group nawa na vip zaku biya 1k dan samun damar karanta duk wani littafina, da nayi ko zanyi tsawon shekara guda*


*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*


*07044600044*


*in kin biya ki turo shaidar yin hakan nagode sosai*


*FREE BOOK*



*20*



Mumy gurin dady ta wuce bayan fitowarta  daga É—akin safiyyar,

A falo ta Sameshi zaune yana karanta jarida,shigowarta ce tasa ya rufe jaridar ya ajiye ya maida hankalinshi kanta dan ya hangi damuwa a fuskarta.


kusa dashi  taje ta zauna babu kuzari,hannunta dady ya kamo yace cikin sigar rarrashi.


"uwar gida sarautar mata,me kuma ya faru na ganki a haka?in ni na ɓata ran ayi haƙuri"


Gyara zamanta tayi sannan tace"Alhaji kan auran yaran nan ne,duk kaine ka janyo komai,ɗazu fitar da mukayi yaron nan Ya je ya haikewa yarinyar can ta ƙarfi,in kaga irin yadda yama yarinyar nan se ta baka tausayi,tsakani da Allah halalin shi ce amma abun yayi muni da yawa"


"subuhanallahi,amma Anwar be kyauta ba,duk da gonarsa ce amma ay bata ƙarfi ba,yanzu ina yarinyar take hajiya,ya kuma jikin nata"cewar dady cikin yanayin damuwa.


"na mata duk abinda ya dace ta samu bacci yanzu,"


"to Alhamdulillahi,"cewar dady yana murmushi.


Shuru ce ta biyo baya kamin dady ya nisa yace"hajiya ni aganina in basu gida agidajena su tare kawai,kamin ya gama decorating nashi ko ya kika gani"


"aa Alhaji hakan ba mafita bace,tunda kaga hutu yasamu,abari hutunshi ya ƙare ya tafi in ya sake dawowa se su tare duba da yanayin jikin yarinyar"momy ta faɗi cikin damuwa.


"duk yadda kikace hajiya haka zaayi,,Allah ya kaimu lokacin,sannan aci gaba da kulawafa da yarinyar mutane sosai hajiya"


"insha Allahu,amma de ka kirashi kaja masa kunne kan yarinyar nan"


"zan kirashi hajiyata"cewar dady yana murmushi.



Momy bata jima ba a É—akin na dady ta dawo nata É—akin.


Fitarta ba jimawa dady ya kira anwar a waya koda yaga kiran yasan akan makircin safiyya ne,dan haka a sanyaye ya É—aga wayar.


"Son,meet me immediately in my room"cewar dady.ya kashe kiran.


Anwar hannayensa ya cusa acikin gashin sa ya yamutsa gashin gamida runtse ido ji yake kamar yayi kuka dan baƙin ciki.


Miƙewa yayi ya canja kayan jikinshi sannan ya goge kiss ɗin da safiyya tai masa ,yasa kai ya fice zuwa kiran na dady.



Da sallamarsa ya shiga falon na dady,


Fuska a sake dad ya amsa masa gamida bashi gurin zama.

..

Bayan ya zauna gaida dadyn yayi sannan yaja bakinshi ya tsuke.


Gyara zama dady yayi sannan ya dubi anwar É—in da dukkan natsuwarshi yace"Anwaruddin,me yasa kayiwa matar ka haka,?"


Runtse ido anwar yayi,gamida riƙe kanshi yace"ohhhhh shet sofiyya u finished me"



"no no no my son,ba abun damuwa bane ,kuma ba laifi kayi ba a addinance,a kamatance ne de baka kyauta ba,kuma banaso irin hakan ta kuma faruwa kaji ko"cewar dady cikin yanayin nuna É“acin rai.


GyaÉ—a masa kai kawai Anwar yayi,dan bakinshi nauyi yay masa..



Sosai dady yay masa faÉ—a kan safiyyar wacce yake ji dama shi sojane ya bindigeta a huta.



Tun daga wannan rana Anwar ya lashi takobin raba Safiyya da duk wani rashin mutunci da take taƙama da shi,iyayenshine matsalar,to ze ɗauketa daga inda iyayenshi suke zuwa tashi duniyar yay mata wulaƙancin daya ga dama,a ƙarshe ya saketa kowa ya huta.


Safiyya ta warke tass,yanzu bata da matsalar komai,dan Anwar ko zasu haÉ—u a hanya be bi ta kanta hakanne yasa ta É—auka abinda tai masa ne tai maganinsa.

.

Zagewa take taci ado na kece raini,sabida momy ɗinkuna sababbi tasa akayo mata masu yawa,daidai jikinta,ayko cikin ƙanƙanin lokaci ta mulka ƙiba,ɗuwawukanta sika ƙara fitowa,gamida kyawun fuskarta.


Koya ta motsa se sun motsa,gashi yanzu su nauwara sun sata agaba da koya mata nauin abinci kala kala,da yadda ake dressing,da magana.



Sosai safiyya ta sauya daga wacce aka sani a baya.



Tsawon watanni uku kenan da faruwar abinda tai masa.

Zaune yake yana amsa waya a falo kasancewar gidan ba kowa,ashe sofiyya na nan be sani ba.


Tana laɓe ajikin ƙofar kitchen,ta jiyoshi yana faɗin"ka bari kb,yarinyar nan ta wulaƙantani da yawa,amma nasha Alwashin koya mata hankali ta kowacce siga,wallahi da zaran contract ɗinmu da Bercelona ya ƙare,da ita zan taho dan anan nakeso nai mata hukunci"



Gabanta yayi mummunar faɗuwa,wato ashe tarko ya ɗana mata, yakeso ta faɗa shiyasa ya dena kula ta,lalle dole tayi duk me yiwuwa wajen ganin an raba aurenta dashi kamin tafiyarsa ko kuma taje ta bashi haƙuri ya sauwaƙe mata,

..Wasu hawaye na tausayin kanta ne suka zubo mata,tabbas ta shiga uku in ya bar ƙasar nan da ita.


Shiko yana kammala wayarshi ya kishigiÉ—e agurin yana kallonsa ba tare da damuwar komai ba har su momy suka dawo,bayan ya musu sannu da zuwa,ya bar falon zuwa É—akinshi,dan ya É—auro alwalar sallar magrib.


Koda dare yayi safiyya ta kasa samun natsuwa,hira suke da nauwara amma hankalinta baya gurinta.miƙewa tayi tabar falon ta haura sama, ba tare da tsoron me ze biyo baya ba taje ƙofar ɗakinshi ta ƙwanƙwasa.



Ko kusa Anwar be ɗauka ita bace yaje ya buɗe ƙofar,sosai yayi mamakin ganinta,a hankali ta taka ta fara ƙoƙarin shiga ɗakin nashi,gefe ya koma ita kuma ta ƙarasa shigowa,


Be ce mata komai ba ya wuce kan kujera yayi zamanshi yana latsa wayarshi.


Maida  Æ™ofar tayi ta rufe da kanta,wanda tun daga fara Æ™wanÆ™wasa Æ™ofar har buÉ—ewar har shigarta da rufo Æ™ofar akan idon momy ya faru, 



Raɓewa safiyya tayi can gefen kujerar,tace "Yaya gurinka nazo dan Allah"tayi maganar bakinta na rawa.


Ga mamakinta se taga yayi murmushi sannan ya ajiye wayar hannunsa,ya nuna mata,gefen sa da nufin tazo ta zauna yace"to bissimillah mana,"


A ɗarare ta miƙe,taje kusa dashi ta zauna,ƙamshin humurar ta ne ya daki hancinsa ya lumshe ido sannan ya buɗe.



"ina sauraronki"ya furta a hankali.



"dama haƙuri nazo in baka akan duk abubuwan da nai maka,don Allah kayi haƙuri na tuba"ta ƙarasa maganar hawaye na biyo idonta.


Murmushi yayi me ƙayatarwa sannan yace,"sofiyya ay na jima da yafe miki dama so kar ki damu"


Sosai taji daɗin amsar daya bata dan haka cikin zaƙuwa tace"to dan Allah tunda ka yafemin,ka sakeni wallahi bana sonka kaima kasani"ta faɗi wasu sabbon hawayen na zubowa.


Cije leÉ“ensa yayi na Æ™asa,ya lumshe ido ya fesar da iska, dan yau ne karo na farko,da É—iya mace ta dubi idonsa ta furta masa bata sonsa.amma se ya Æ™irÆ™iro murmushi yace 


"sofiyya nima na gamsu da wannan buƙata taki,sede kuma kinga ni ɗan kwallone bana buga wasan da baaa biyani ba,na biya sadakin ki,so kinga dole na mori kuɗina kamin in sakeki,ni a yanzu ma in kika bani hakkina na aure ina gama amsa zan miki sakin da kikeso"yana kaiwa nan ya ɗauki wayarshi yaci gaba da dannawa.



Shuru tayi ta kasa magana,tana tuno abinda amsar sadaki ke nufi,wato se ya kusanceta kan ya saketa,


Tirƙashi



Muje de zuwa




Surbajo for life.

No comments