Recent Updates

Sha'awar Shi Nake 2

 


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *SHA'AWAR SHI NAKE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Zahra Surbajo*




*PAID BOOK 500*



*2*




"jirgin nasu na dare ne,pls muniba yazamana kina airport ze sauka,kinga bata taɓa zuwa ba se wannan lokacin"cewar daddyn jannat lokacin da suke waya da muniba kan tasowar jannat ɗin yau.


"daddy karka damu insha Allahu zamu jira isowarta,karka damu game da hakan"muniba ta bashi amsa.


"ba damuwa yanzu zamu kaita airport"ya faÉ—i sannan ya kashe wayar ya juyo ya dubi mamy fuskarshi ba walwala yace.


"ji nake kamar zan rasa wani sashi na jikina,hajiya,ko kaÉ—an banson tafiyar yarinyar nan,dan de kawai kar suga na musu ba daidai bane yasa zan barta ta tafi"


"in banda abunka Alhaji sati biyu ne fa kawai zatayi kamar yau ne zaka ga ta dawo"cewar hajiya cikin sigar rarrashi.


Jannat ce ta fito sanye da riga da wando kanta ba kallabi se gashinta da ta É—aure da ribon ya sauka har gadon bayanta,bame kallonta ya É—auka bahaushiyace dan tafi kala da turawa,kyakkyawa ajin farko.


Cikin Takunta na burgewa ta iso gaban iyayen nata tace a shagwaɓe "dad time is going fa,kasan by 3 zanyi caching flight akwai buƙatar in isa airport yanzu"


Ba musu suka miƙe su duka suka mara mata baya dan tuni komai nata ansa a mota.


Suna shiga mota,driver yaja suka fice zuwa airport,se hira suke a motar kamar karsu rabu.


Isowarsu tayi daidai da fara kiran fasinjoji,dan haka basu wani jima tare ba sukai sallama tana tafe,tana waigo su suna ɗagawa juna hannu har ta ɓace musu.


Su daddy na nan tsaye jirgin su jannat ya tashi,sosai kewarta ta mamaye zuciyarsu da jikinsu,fatan sauka lafiya sukai mata,sannan suka dawo gida.


Haka suka isa gidan kowa jiki asanyaye na kewar jannat É—in,wanda suka alaÆ™anta hakan da  sabo.


Wayyo rayuwa,awanni biyu da  tashin jirgin,ba tare da ansan musabbabin faruwar matsalar ba ya kama da wuta tun daga sama,har dirowarsa Æ™asa.


inda ya faɗo a wani ƙaramin ƙauye,da ke yankin ƙasar ethopia,ya raunata mutane da dama mazauna ƙauyan.


Motocin agajin gaggawa ne suka iso gurin,inda akai ta ƙoƙarin kashe wutar,sede kafatanin jamaar dake cikin jirgin ba wanda ya fita da rai ciki ko harda jannat,


Se wata matashiya wacce baa cikin jirgin take ba,hatsarin ne ya rutsa da ita,bata mutu ba,sede ta ƙone sosai,itako jannat tuni rai yayi halinsa😭


Tashin hankali ba'a sa maka rana.



Surbajo for life

No comments