Sha'awar Shi Nake 17
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHA'AWAR SHI NAKE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
PAID BOOK*
*
*17*
Jagwab ta koma nakin gado ta zauna,sannam ta ɗora hannunta me lafiyar akai ta saki wani marayan kuka yayinda kuma bakinta ke furta"wayyo Allah na ni safiyya wacce irin mummunar ƙaddarace wannan,ya Allah ka kawowa marainiyarka mafita,"takai ƙarshe tana kuka.
Shi ko yana barin ɗakinta nashi ya nufa zuciyarshi fess yasan ya ɓata mata rai.
Wanka ya sake yi sannan ya kimtsa cikin kaya na alfarma yayi ɓarin turare ajikinshi sannan ya ɗauki key ɗin motarshi ya fito da ɗan saurinsa yana diba wayarsa.
A kan stairs suka haÉ—u da mummy,tana haurowa shi kuma ze sauka,É—an rusunawa yayi,yace"mummy se na dawo"
"ka sameni a É—akina"ta bashi amsa ba tare data sake sauraronsa ba ta wuce zuwa É—akin nata.
Shuru yayi yana wasi wasi a zuciyarshi da saƙe saƙe,ganin be kamo bakin zaren bane yasa ya juya ya mara mata baya zuwa ɗakin nata.
Zaune kan kujera ya sameta,hakanne yasa shi kuma ya zauna akan carpet ya lanƙwashe ƙafafuwa.
Shuru ce ta biyo baya na ƴan sakwanni kamin momy ta gyara zamanta ta fara da cewa"Anwar duk abinda yake faruwa acikin satin nan ido kawai nasa muku kai da mahaifin naka in ga iya gudun ruwanku,to nagani,kai da ka jajibo kuma yanzu zaka ga irin nawa gudun ruwan,Anwar ka sa an aura maka safiyya badan da gaske kana sonta ba sedan biyan wata buƙata taka,sede kasani safiyya me rangwamen gatace shiyasa duk hakan ta faru,kasantuwarta marainiya,wallahi ka cutar da safiyya ubangijinta baze barka ba,kuma wallahi dede da rana ɗaya naga cutarwa agareka sena saɓa maka,wallahi Anwar zan iya yafeka acikin ƴaƴan dana haifa"
A gigice ya É—ago ido yana kallonta bakinshi na rawa yace "mum akan Æ´ar aykin ki kike cewa zaki yafe ni?nufinki tafini kenan?"
"ta fika Anwar!!!! "ta faɗi cikin ƙaraji sabida sosai suka ɓata mata rai,na auran sa da safiyya,sosai takejin haushinsu.
Sosai yanayin na mummy ya razana Anwar,dan be taɓa ganinta a haka ba.
"ka tashi ka bani guri na sallameka"ta faɗi rai a ɓace.
Be musa mata ba ya miƙe guiwowinsa a sanyaye ya fice daga ɗakin.
ÆŠakinsa ya koma ya sauya shiga,duk ransa ba daÉ—i shiyasa fitar da zeyi ma ya fasa falo ya dawo ya zauna ya kunna tashar sport yafara kallo.
Be jima ba mummy ta dawo falon itama,zamanta keda wiya safiyya ta kunno kai falon dan zuwa kitchen samawa kanta abinda zata ci yunwa takeji.
Tana fitowa mummy takai dubanta inda Anwar yake,da sauri ya miƙe ya nufi inda safiyyar take,ransa na masa zafi amma a fili se murmyshi yake sakar mata,
Safiyya tsorone ya kamata ganin ya nufo ta,rasa yadda zatayi tayi,yana ƙarasowa ya miƙa hannu da nufin ruƙota,itako ta ɗauka dukanta zeyi da Saurinta ta kare fuskarta da hannunta me lfy gamida dojewa tana faɗin"kayi haƙuri don Allah"
Janyota yayi jikinshi yana murmushi yace "relax baby girl me kika min?"yayi maganar yana leƙa idanunta da suka kumbura sukayi luhu luhu sabida kuka.
Hannu yasa yana shafa idanun a hankali sannan yace cikin sigar tausayawa da nuna soyayya,"tun ɗazu nace miki banson kukan nan amman kinƙi ki dena,ko so kike nima inyi kukan?"yayi mgnr cikin yanayi na so da ƙauna.
Safiyya wacce tsananin mamakinsa yasa ta saki baki tana kallon shi kasa cewa komai tayi,dan ita makircin nasa so yake ya shallake tunaninta.
Ƙoƙarin ƙwace jikinta take daga ruƙon da yay mata amma yaƙi sakinta,hakanne yasa ta buɗi baki a hankali tace "abinci zanje in zubo yunwa nakeji"
Ji yayi kamar ya shaƙeta amma se ya daure yayi murmushi yace"ay ɗazu dana baki ƙin karɓa kikayi amma yanzu naji daɗi da zaki ci,jiran in zubo mki muje ɗaki kici ko madam ɗita "ya ɗaga mata gira.
Shuru tayi tana binshi da ido,sakinta yayi ya juya zuwa kitchen da saurinsa,itako ƙarasawa tayi cikin falon dan tasan inde yakaita ɗaki ba lalle ya bari taci abincinba.
Koda Anwar ya É—ebo abincin ya dawo ya ganta a falo gun momy a zaune ji yayi kamar yasaki ihu,dan ya gama shirya mugintar da ze mata in sunje É—akin,se gashi ta watsa masa shiri.
Jiki ba ƙwari ya kai mata abincin,ya ajiye,sannan ya fara bata abaki,mummy se kallonsu take suna burgeta aranta se adduar Allah yasa su ɗore take,dan har ranta tana son safiyya.
Haka de safiya ke buɗe baki anwar na ciyar da ita, mamakin abun ne yasa ko taunawa ta arziƙi batayi take haɗiyewa.
Ay kamar jira,momy ta jiyo motsin dady a falonsa hakan yasa ta miƙe ta nufi falon.
Safiyya na ganin haka kan Anwar ya farga itama ta kwasa da gudu,jin takun gudunta ne yasa hankalinshi ya dawo jikinshi ,dan yana can yana wassafa cin mutincin da ze mata in momy tabar falon,
Da gudu shima ya mara mata baya sede ta rigashi shigewa ɗakinta gamida rufo ƙofarta da ƙarfi tasa key.
Jin ƙarar gudun su ne yasa momy saurin dawowa falon dan taga ko me ke faruwa,Anwar dake tsaye ƙofar ɗakin safiyya ta mirror ya hango momy na leƙensu hakanne yasa yace "dan Allah in kowa yayi bacci zan dawo ko ke ki sameni a ɗakina kinji baby na"ya faɗi yana murmushi.
Momy na jin haka tai murmushi ta juya ta koma tana jinjina rashin kunya irin ta Anwar.
Hmmmmm
Muje zuwa
No comments