Sha'awar Shi Nake 16
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHA'AWAR SHI NAKE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*PAID BOOK*
*16*
Da gari ya waye,bayan kowa ya kimtsa,dady yayiwa kawun safiyya iso zuwa cikin falon gidan,inda Anwar da safiyya tuni sin hallara,sakamakon tarasu da Dady yayi.
Safiyya zamansu guri ɗaya da Anwar jinta take a takure,ta ƙosa ayi ayi a sallameta ta bar gurin dan yau tasha alwashin guduwa garinsu duk da batasan hanya ba.Sabida bazata iya zama guri ɗaya da mugun mutum irin Anwar ba.
Shigowar kawunta falon ba tare data tsammaci ganinshi ba sosai ya bata tsoro gamida mamaki.
"kawu!!"safiyya ta furta gamida miƙewa tsaye tana masa kallon mamaki.
"naam É—iyata,kina mamakin ganina ko,to nemi guri ki zauna,ay dan ke nazo"ya bata amsa yana murmushi.
A sanyaye ta koma ta zauna,sannan ta gaishe da kawun nata gami da daddy.
Bayan sun natsa ne kawu ya fara magana.
"Safiyya,burin mahaifinki har kullum yaga ya aurar daku ga mazaje nagari,sede Allah yay masa rasuwa,wannan ayki da kika taho bada san ranmu hakan ta faru ba,munyi munyi ta sanar damu inda ta turaki taƙi amincewa muna shirin kaita kotu se ga Alhaji Allah ya kaishi,to Alhmdllh,safiyya bari inje kai tsaye Alhaji ya buƙaci na aurawa ɗansa Anwar Auranki sakamakon sonki da yake da dukkan zuciyarsa,kuma na gamsu da kamala irin ta Alhaji A jiya na ɗaura auranki da ɗansa Anwar ki zamo me biyayya ga mijinki"yakai ƙarshen maganar yana miƙa mata sadakinta.
Safiyya ji take kamar a mafarki,dan haka dagewa tayi iya ƙarfinta ta wankawa kanta mari,ayko abunka da jar fata take gurin yayi ja,zafin da taji ne yasa ta fahimci azahiri taji ba a mafarki ba,dan haka miƙewa tayi agigice ta fara magana hawaye na biyo idonta tana nuna Anwar ɗin da hannu tace"wannan baƙin mugun shi ka zaɓamin a mazaunin mujin aure kawu,to ni wallahi bana sonshi dole ya sakeni dan ni ko kaɗan be min ba in ba haka ba ya aurowa kansa masifa da kanshi"ta faɗi ba tare da tsoron komai ba,ay kan ta gama maida numfashi ta hangi Anwar tsugunne gaban kawu ya riƙe ƙafafunsa yana magiya"Sofiyya ce rayuwata kawu kullum da sonta nake kwana hakanne yasa na nemi da a aura min ita,dan cikar soyayya aure,dan Allah kar ka rabani da ita wallahi mutuwa zanyi in ta gujeni"ya faɗi cikin sigar a tausaya masa.
Tsananin makirci irin na Anwar ne ya kashe mata baki ta kasa cewa komai ta saki baki tana kallonshi.
"ba me rabaku Anwaru,sede kaji tsoron Allah ka riƙe ta amana kasantuwarta marainiya"
"insha Allahu kawu na É—auka zan kula da ita dede iyawata"
Daga haka sosao akai musu nasiha me ratsa jiki wanda yasa safiyya yin shurun dole,shiko Anwar faÉ—an ko É—aya ba wanda ya shiga zuciyatsa.
Safiyya naji na gani kawunta yay mata sallama ya tafi kan nan da sati guda Æ´an uwanta mata zasu zo.
Haka taita kuka kamar ranta ze fita,ita data gama tsarawa yau zata bar gidan se gashi ta ƙara tsayi ashe barin gidan ba rana,wani sabon kukan ne ya kuɓce mata lokacin data lura da hijab ɗin dake jikinta da ya hana kawunta raynin da yaji mata,ƙara fashewa tayi da wani sabon kukan.
Mummy sosai ta rarrasheta da kyau,gamida rakata har ɗakinta ta barota sannan ta wuce nata,ay kamar jira yake yayi wuf ya faɗa ɗakin na safiyya ya kullo ƙofar.
A firgice ta ɗago dan taga ko waye,ganin shi sosai ya tsoratata,a hankali ya ƙarasa gabanta yana bin ta da kallo na tsana yace"ba abinda zan so a jikinki sofiyya,baƙya cikin tsarin matar da nakeso na aureki nr dan kawai in wulaƙanta rayuwarki badan soyayya ba,ki shiryawa uƙuba ta,ni na wuce duk inda kike zatonaa da ido iwa na ƴan ƙwaya,ke bama haka ba ɗazu da kika sameni a falo ubanwa ya hanaki gaisheni kika gaisa da su dady cikinsu kwai wanda ya fini ne agurinki? to wlh ki kiyayeni,kucaka ƴar ƙauye kawai"ya faɗi yana doka mata harara.
Safiyya duƙar da kai tayi ƙasa dan karma yace ta kalleshi ya daketa burinta su rabu lafiya dan balain tsoronshi take yanzu.
Seda ya gama yimata wulaƙanci sannan yasa kai ya fice daga ɗakin se mazurai yake.
Muje zuwa
No comments