Recent Updates

Sha'awar Shi Nake 15

 


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 *SHA'AWAR SHI NAKE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Zahra Surbajo*




*FREE BOOK*



*15*




Daddy da kanshi yaje ya samu Anwar a ɗakinshi jikinshi a sanyaye ya tura ƙofar ya shiga.

Zaune ya sameshi ya yi tagumi,fuskarshi ba walwala.


Ƙarasawa yayi kusa dashi ya taɓashi,da sauri ya ɗago kai ya kalli daddy,kusa dashi ya zauna sannan yace.


"Son bana so kasa damuwa a zuciyarka pls"


"dad dole in damu ace kamar  ni ina fitsari ban sani ba ay damuwace babba"ya faÉ—i kamar me shirin yin kuka.


"abun damuwane a da amma yanzu ay likita ya faÉ—i mafitar da za'a bi,dan haka ka natsu ni mahaifinka ne kuma raina ma fansa ne ga farincikin ka bare abinda na mallaka,ka faÉ—amin ko Æ´ar gidan waye ka keso aje ayi magana daga naira É—aya zuwa naira milyan dubu in hidimar auranta yakai haka zan bada son fatana kawai ka samu lafiya"


"bama se an kashe wainnan kuɗaɗe ba,Sofiyya ƴar aykin gidannan nakeso daddy,tunda kaga tasan lalurata,zata fi kowa maida hankali a kaina wajen ganin na samu lfy."ya ƙarasa maganar cikin yanayi na shauƙi.


Sosai daddy yaji daÉ—i,da zaÉ“in É—an nashi  dan ya yaba da natsuwar safiyya.


"inde wannan ce nan da sati guda ma tazama taka,ni da kaina zanje garinsu in nemama auranta ka bani sati guda son"cewar dady fuskarshi É—auke da murmushi.


"Nagode dady,Allah ya ƙara girma"


"Amin my son"


Sallama dady yay masa ya bar É—akin,yana fita Anwar ya dunÆ™ule hannunsa ya naushi tsakiyar tafin É—aya hannun nasa,ya fesar da iska daga bakinsa yace"kin shigo komata sofiyya,me fiddaki sede Allah,"ya Æ™ara kai wani naushin gami  da cewa "yessss"



Shiko dady gun mommy ya koma yay mata bayanin komai,ko kaÉ—an momy bata gamsu da cewa Anwar na son safiyya ba,amma a fili se tace"Allah sanya alkha'iri amma ay za'a ji ta bakin yarinyar ko ita in tana son nashi"


"Wanne ta bakin yarinya kuma hajiya,yanzu Anwar har akwai macen da zata kalle shi tace bata son shi?"


"Hakane amma ay kasan kowacce mace da irin mijin da take so,ta iya yiwuwa ita ba shi take so ba"


"bari de in fara ganawa da iyayenta first muji nasu ra'ayin ay sune zasu aurar da ita ba itace zata aurar da kanta ba"cewar daddy.


Shuru mommy tayi tana juya maganar aranta.


Safiyya ko da ta farka kuka take kamar ranta ze fita,tabbas se yanzu ta fahimci gargaɗin da ake mata,kan ta kiyayeshi,ashe baƙin mugune ze iya kashe ta ma wannan.


Duk lokacin da ta kalli hannunta wasu sabbin hawayen ne ke biyo idonta.


Kamar yadda dady ya tsara hakance ta faru,hajiya jummai yasa mommy ta kira masa,yasa tai masa jagoranci zuwa garin na su safiyya.



Koda furera taji abinda ke tafe dasu,bata amince ba,sabida ta fahimci hutun safiyya yazo,dan haka ƙin amincewa tayi.


Koda suka fito,hajiya jummai gidan ƙanin baban safiyya ta raka dady,ayko cikin mutunci ya tarbeshi.


Daddy ya faÉ—i masa abinda ke tafe dashi,sosai yayi murna da jin batun daya kawoshi,inda shima ya kwashe komai game da rayuwar safiyya ya faÉ—ima daddyn,sosai daddy yaji tausayin ta.


A taƙaice de A ranar ƙanin babanta da sauran ƴan uwanshi sika ɗaura auran safiyya da Anwar kan sadaki naira dubu ɗari biyar.



Koda furera taji an ɗaura auran yi tayi kamar tai hauka sabida baƙin ciki,abunka da ƙaramin gari tuni akai ta yayatawa safiyya ta auri me kuɗi.


Koda daddy ya tashi komawa Abuja tare da ƙanin babanta suka tafi dan yay mata bayani da kanshi.


 Shigowar dare sukayi dan haka masauki aka kai kawu nasiru in gari ya waye sa gana.


.Muje zuwa

No comments