Sha'awar Shi Nake 13
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHA'AWAR SHI NAKE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*FREE BOOK*
*13*
Cikin gidan ta dawo jiki a sanyaye,mummy dake zaune tana kallonsu murmushi ne kan fuskarta.
Dan har cikin ranta safiyya na burgeta badan komai ba sedan ƙarfin halinta dan ko a tarihi ƴar ayki irin safiyya bata taɓa ji ba,
"safiyya manya,to in kin gama gudun kije ki gyara part É—in"cewar mummy tana dariya.
Shuru safiyya tayi tana kallon mummy,amma har ranta bata son gyaran part É—in da aka kirata mahaukaciya dominsa.
Hakanan ta amshi mukullin part É—in ta tafi gyarawa.
Sosai ta wahala gun gyaran kasancewar ya jima a kulle baa shiga,a ranta tace"mugu da fuska iwa jan ƙosai yasani sarai zan wahala gun gyaran yace a nan ze sauke baƙinsa"se mita take har ta kammala.
Da ƙyar ta iya yin wanka dan ƙugunta ciwo yake mata,tana tsaka da shiryawa ne taji dirin motoci a harabar gidan.
Da sauri ta isa jikin window ta leƙa,Anwar ne tare da baƙin nasa duka turawa biyu mata uku maza,ga mamakin safiyya ɗayar budurwar hannunta sarƙe cikin na Anwar tana mannewa ajikinshi.
Safiyya Batare da tasan lokacin da maganar ta fita ba tace"shegiya la'ananniyar Allah,ji banzar ko kyau,se wani manne masa take"ta faÉ—i har da É—an tsakinta.
Da sauri ta sa kayanta ko kwalliya bata tsaya yi ba ta fito har tuntuɓe take,hanyar wucewarsu taje taja tinga ta tsaya,tana haɗe rai.
Shigowa sukayi suna hirar su cikin kwanciyar hankali,safiyya ta lura da Anwar se ƙoƙarin ƙwace hannunsa yake daga riƙon da budurwar tai masa amma taƙi sakinshi,
Ayko batai ƙasa a guiwa ba ta nufesu,ita me gayya me aykin,tana zuwa,hannu tasa ta kama hannuwan nasu ta wara,sannan ta kalli baturiya,tana murmushi tace da hausa"shegiya da fuska iwa jan ƙosai,an shigo gida ma ay kya rabu dashi"yayinda ta sauya harshe zuwa turanci tace,"mamarshi nada faɗa in ta ganki riƙe dashi kwana zatayi tana dukansa"ta ƙarasa maganar tana kallon fuskar Anwar ɗin tana ɗaga masa gira.
Gaba ɗaya baƙin su kwashe da dariya,suna nuna shi,har haɗa baki suke wajen faɗin"captain guda amma ace ana dukanshi,kai wannan abu da mamaki"
Ga mamakin Safiyya babu ko alamar fushi akan fuskar Anwar se wannan nataccen murmushin da yake ta sakar mata.
Hannun budurwar ya sake kamowa ya riƙe yace cikin sigar rarrashi,"kishi take,kinsan da itace akace zan aura,to amma lalurar fitsarin kwance da take yi ne yasa nace bana sonta,ganinmu tare ne taji haushi karki kulata"yana kaiwa nan ya kai dubansa gun da safiyya ta daskare jin abinda ya faɗa musu,ya ɗaga mata gira gamida kama laɓensa na ƙasa da haƙoransa,yaja hannun budurwar sikayi gaba se waigenta sukeyi, da yanayi na ƙyamarta a fuskokinsu.
Wayyo safiyya durƙushewa tayi agurin tasa kuka,dan tabbas Anwar ya cuceta,daya kunyatata agaban baƙin nasa..
Ko waigota beyi ba ya wuce da baƙin nasa inda ze saukesu.
Seda sukaci abinci suka ƙoshi,suka ɗan huta,sannan yay musu jagoranci zuwa gun mummy suka gaisheta.sannan yay musu rakiya suka tafi.
Ranar har dare safiyya ta kasa runtsawa sabida takaicin abinda yay mata kuma tasha alwashin ramawa kota halin ƙaƙa.
Koda gari ya waye asubancin gyaran gidan tayi,inda kai tsaye ɗakin Anwar ɗin ta fara dashi, tana tura ƙofar a hankali,ta hangeshi kwance kan makeken gadonsa yana barci.
A hankali ta shiga toilet ɗinshi ta ɗebo ruwa,tazo dede kan wandonshi ta juye ruwan sannan ta ƙwala ihun kiran mummy da dukkan ƙarfinta.
Ayko kamar tasa amsa kuwwa kowa na gidan ya fito a firgice zuwa inda suka jiyo ƙarar,shima kanshi Anwar ɗin jin saukar ruwan ajikinshi yasa ya farka agigice,wanda hakan yay daidai da shigowar ƴan gidan suna tambayarta ko me ya faru.
Itako kuka tasa tace "na shigo gyara masa ɗaki ne na samu yana fitsari a kwance,to ban taɓa gani bane yasa na firgita"
"what!!!!"Anwar ya faɗi gamida kai dubansa jikinsa,ga mamakinsa ko ajiƙe yake ta yadda bame cewa ba fitsarin yayi ba.
Kasa magana yayi ya duƙar da kansa dan kunyar da yaji tana da yawa.
Cikin tausayawa daddy yace"gyara jikinka son bari na kira doctor,Allah ya sauwaƙe"
Tsananin jin kunya ne yasa ya kasa magana,dan kafatanin kowa na gurin seda yay masa sannu sannan suka fita.
Saɗaf saɗaf itama safiyyar ta juya da nufin tabi bayansu,ayko Anwar cafka guda yayi ya damƙota ya maida ƙofar ya kulle.
Hmmmmm
Muje zuwa
Surbajo for life
No comments