Recent Updates

Sha'awar Shi Nake 12

 


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

  *SHA'AWAR SHI NAKE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Zahra Saurbajo*





*FREE BOOK*



*12*





"Safiyya inaso na baki shawara ne kan big bross"cewar nauwara lokacin da ta samu safiyyar.


"Nauwara waye kuma big bross,?meye alaƙa ta dashi da zaa bani shawara akansa?"cewar safiyya tana juya ido.


Dariya nauwara tayi sannan tace"babban yayanmu dayazo ɗazu shine big bross,alaƙar dake tsakaninku kuma itace ke me aykin gidansu ce,yana da kyau ki dinga kiyaye masa dan wallahi bashi da kyau"


"toni nauwara ina ruwana dashi,ko yayi kyau ko kar yayi ni ba damuwa ta bace dan nima ba kyan gareni ba mude kiyayewa juna,ni iyakaci kuce kun koreni,amma baze yiwu in gyara gu a ɓata ba, koma waye"ta faɗi tana kaɗa ido.


Miƙewa nauwara tayi sannan tace"to ni de na faɗa miki gaskiya in kinji ta amfaneki in baki ji ba ruwanki"tana kaiwa nan ta fice daga ɗakin.


Ƙyaɓe baki tayi gami da ɗaga kafaɗa ta koma tayi kwanciyarta,dan ita bata ga abinda tayi ba daidai ba anan.


Shiko Anwar sosai ya ajiyeta a ransa kuma yasha alwashin se tayi dana sanin zuwa duniya tumda ta shigo gonarsa se ta gane kurenta.


Tun daga wannan lokaci safiyya ta sako Anwar agaba,beda ikon yasha shisha agidan seta hanashi,in waƙa ya kunna yana sauraro zata kashe,acewarta hakan cutarwace ga lafiyar kunnenta,


Kuma har kama eh yanzu ta tafasa be taɓa ce mata ba,komai tayi da ido kawai yake bin ta.


Yau ma kamar kullum suna zaune shi da mummy a falo suna magana kan abinda ya shafi harkokinsa,inda magana yake amma se ka kalli bakinsa zakaji me yake faÉ—i,sabida magana na É—aya daga cikin abinda ke wahal dashi.


"mummy anjima zanyi baƙi ashirya duk abinda ya dace don Allah,sannan wannan mahaukaciyar me aykin taku asata ta gyaramin wancan part ɗim can zan saukesu" ya kai ƙarshen maganar yana duban agogon hannunshi.


Dariya mummy tayi sannan tace"Anwar É—iyar mutanence mahaukaciya?"


"In ba mahaukaci ba wake faÉ—a da me bashi abinci mummy"



"Allah ne ke bani abinci ba wani ƙato ba,kuma in har rabona ya rantse ko zaa bani ayi kuka wlh se an bani"cewar safiyya wacce shigowarta falon kenan ta kalli bakinshi ta fahimci abinda yake faɗi.


Be ko kalleta ba ya miƙe ze bar falon,da sauri tasha gabanshi tana faɗin"nifa Allah be wulaƙantaniba ba mahalukin da ya isa ya wulaƙantani,ehe iyakaci de ace an koreni in huta."



Se alokacin ya É—ago sexy eyes É—inshi ya juyesu akan nata sleeping eyes É—in,wani abu taji tun daga tafin Æ™afarta har tsakiyar kanta ya tsirga mata,a sanyaye yace mata 


"Sofiyya,Anwar ba kanwar lasa bane fa,ina gargaɗinki"ya ƙarasa maganar fuskarsa ɗauke da niimtaccen murmushi me tsayawa a zuciya.



kasa cewa komai tayi dan gaba É—aya ya kashe mata jiki,seda yayi nisa da barin inda take sannan ta taka da gudu tana faÉ—in"nima ba kanwar lasa bace wallahi"ko waigowa beyiba yasa kai ya yi ficewarsa .



Muje zuwa

No comments