Recent Updates

Sha'awar Shi Nake 11

 


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

  *SHA'AWAR SHI NAKE*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀



*Zahra Surbajo*




*FREE BOOK*



*11*




Ta wutsiyar idonshi yakai dubansa gareta,lumshe ido yayi sannan ya sake buɗesu akanta,bece komai ba ya maida kallonshi fuskar iyayenshi,wanda ko beyi magana ba sun san ƙarin haske yake so game da wacece ita.


Dariya mummy tayi sannan tace"safiyya kenan,sabuwar me aykinmu"ta faÉ—i tana nuna ta.


Itako safiyya gyara tsayuwarta tayi gami da riƙe ƙugunta,tana kaɗa idanu.


Shuru yayi yana tauna cingum ɗin bakinsa bece komai ba se murmushi da yayi ta gefen bakinsa sannan ya miƙe yana gyara tsayuwar glass ɗinsa a fuskarsa.


Ta gefenta ya wuce ba tare daya ce mata komai ba,matakala yabi zuwa sama inda É—akinshi yake.


Tsaki safiyya tayi gami da É—aga kafaÉ—arta,kiran da mummy tai mata ne yasa ta kauda tunanin komai ta isa gabanta da sauri.


Tana zuwa durƙusawa tayi tace"gani hajiya"


"abinda nake so dake,safiyya kiyi takatsantsan da Anwar,ko kaɗan beson raini,kuma baa shiga gonarsa,ko mu da kikaga kina ma sauran yaran gidan suna ƙyaleki,tausayin iyayenki muke ji dan munsan komai ma zaki iya yi mana dan mu koreki tinda ba son aykin kike ba"cewar hajiya cikin sigar nasiha.


"to hajiya nagode"cewar safiyya cikin ladabi.


Shiko Anwar yana shiga É—akinshi wanka ya shiga,sakarwa kansa ruwa,yayi ko zuciyarsa ta masa sanyi bisa turirin da take masa na É“ata masa rai da safiyya tayi.


Se zuƙar iska yake yana furzarwa,alamun dake nuna ranshi ya ɓaci.


Kasancewarshi ma'abocin shan shisha shiyasa yana fitowa wanka sallah kawai yayi ya shirya a cikin wani three quaterwando baƙi gamida farar singlet ya kwanta akan doguwar kujerar dake ɗakin yana busa hayaƙin shishar.


"ban É—auka zeyi amfani da É—akinshi na sama ba,shiyasa ban ce ki gyara ba,maza kiyi sauri safiyya kije ki gyara masa kan yayi wanka,"cewar mummy tana duban safiyya dake shirin ficewa a falon.


Duk da bataso hakan ba,amma haka ta amsawa mummy É—in,ta kwashi kayan share É—aki ta nufi É—akin nasa tana turo baki gaba.


Da sallamarta ta tura ƙofar ɗakin,ƙamshi gamida hayaƙin shishar daya bugi hancinta ne yasa tayi saurin yar da mopper ɗin hannunta,ta riƙe ƙugu kallonta takai inda yake,kwance yake hankali kwance yana fesar da hayaƙi,idonshi a limshe.


Sosai fuskarsa ta Æ™awata ganinta,amma a fili ko takawa tayi ta isa gabanshi,tace cikin fushi"kai bafa ze yiwu ba wallahi,ba uban da ba É—a ba agurin iyayensa,akan me tun shigowarka gidannan ka taho mana da mugayen É—abiu wanda mu bazamu yarda da hakan ba,yanzu in banda mai da kai salansar mashin ina É—an adam ina  hayaÆ™i ,toni bari kaji komai nawa akan tsari nake yinsa,dan ina ayki a gidanku baze yiwu aÆ™i karemin lafiyata ba,wannan hayaÆ™i cutarwa ce ga lafiyata ehe,kuma wlh dole adena sha aduk inda aykina ya ratso"tana kaiwa nan tasa hannu ta amshe igiyar ta É—auke tukunyar kacokam ta jashe wutar,sannan ta ajiye a inda ta dace.


Wannan karon ko arziƙin kallon bata samu ba dan ya lura kamar attention ɗinshi take nema.


Haka ta gyara  komai ba tare da mgn ta haÉ—asu ba,ta fice a É—akin.


Koda dare yayi nauwarace ta shigo É—akin na Safiyya dan  ta lura akwai buÆ™atar ay mata bita na zaman gidan nasu in yayansu na nan.



Kuyi hkr da wannan kai na ke ciwo




Surbajo for life.

No comments