Sha'awar Shi Nake 10
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SHA'AWAR SHI NAKE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*Zahra Surbajo*
*10*
Ba komai yasa suke son Æ´ar ayki ba sedan me musu ayki ta rasu,masu dafa abinci daban,me musu shara da mopping ce ta rasu shiyasa suka ce akawo musu yarinya,,
Sabida momy batason manyan mata badan komai ba sedan ita mace ce me kishi shiyasa duk da kuÉ—insu bata sakarwa masu ayki ragamar gidan ba,
Tun shigowar safiyya rayuwarsu kusan komai na gidan ya sauya,dan ita kai tsaye zata tuhumi mutum dalilinsa na É“ata gun data gyara.Bata yarda kuma asata aykin daba shi aka É—auketa ba sosai take tsayawa akan aykinta
Kasancewar momy mace me Sauƙin kai yasa take ɗaukar safiyya tamkar ƴarta,koda ta jiyota da nauwara akan ɓata guri sede tai dariya bata cewa komai.
Yau ma kamar kullum safiyya na kwance a É—akin da aka bata,tana hutawa bayan yini da tayi tana ayki.
Wayar ɗakince tai ƙara dake nuna ana son magana da ita daga wani sashi na gidan.
A Hankali ta miƙa hannu ta ɗaga wayar ta kara a kunne,ga mamakinta momy ce.
"barka da dare hajiya"cewar safiyya cikin girmamawa.
"barka de safiyya,ko har kin kwanta ne?"cewar momy cikin nuna kulawa.
"eh na kwanta amma in akwai abinda kike buƙata zanzo yanzu"
"ba abinda nake buƙata safiyya zande sanar dake ne gobe ki tashi da wuri muna da ayki dan muna da baƙi,so banaso ki makara"
" ba komai hajiya yadda kikace haka zaayi"
Daga haka sukai sallama kowa ya ajiye waya.
Tun asuba ta tashi ta fara gyara koina na gidan duk da ba datti yayi ba amma seda ta gyara komai ta goge,sannan taje tai wanka tasa kayanta da nauwara ta bata.
Sha É—aya na safe tajiyo sautin jiniya na tashi a harabar gidan,yayin da taga sauran Æ´aÆ´an gidan da iyayen sun kaure da murna suna faÉ—in"ya iso"
Dukansu taga sun rankaya zuwa harabar gidan,itama batai ƙasa aguiwa ba tabisu.
Fitarta tayi daidai da fitowarshi a mota,"hasbunallahu waniinal wakil"itace kalmar dake yawo abakinta,lokacin datai arba da kyakkyawan saurayi Anwar sanye cikin suit baƙaƙe fuskarsa zagaye da saje me kyan tsari,yayin da kuma ya tara gashin baki da ya dace da kyan fuskarsa,kanshi kuma akwai yawaitar gashi amma an mishi aski irin na ƴan kwallo,daya dace dashi.
Ko ya ya motsa bakinsa dimple ne ke bayyana,gamida kyakkyawar wushirya data dace da fararen haƙoransa.
Da gudu su nauwara sukai kansa ana faÉ—in "big bross big bross"
Ga mamakin safiyya ko rungumarsu be yi va kamar yadda su suka yi masa se wani shan ƙamshi yake,
Gun iyayen ya nufa ya rungimesu,sannan suka É—unguma zuwa cikin gidan,fuskokinsu É—auke da faraa.
Nanfa aka shiga gabatar masa da abinci da kayan maƙulashen da aka tana dar masa,ƴan uwan duk sun kewayeshi suna murna da ganinsa.
Itade safiyya na gefe tana kallon ikon Allah ji tayi sam be yimata ba dan ta tsani mutum me ji da kanshi da yawa.musamman daya shigeta ba tare da ya ce mata sannu ba.😆
A bincin kaÉ—an yaci sannan yasa hannu a aljihu ya É—auko cingum,ya É“are takardar ya yar a inda yake zaune,wanda karab akan idon safiyya,ayko sosai ranta ya É“aci
Tsam ta miƙe ta isa inda yake,tasa hannu ta ɗauko takardar cingum ɗin ta tura masa agaban aljihunsa tana faɗin.
"ƙarfe huɗu na miƙe na safiyar yau,ba dan komai ba se dan in gyara gida sabida zuwanka,ba baiwa bace biyana ake,in can da ka baro basa saka shara a dustbin mu nan muna sawa,ka adana wannan inka fita ka yar a waje amma ba anan ba,ka kiyaye da haka a iya zamanka na cikin gidan nan,"ta faɗi ba tare da tsoron komai ba har wani gyatsine take haɗawa fashi.
Anwar tsananin mamakin me masa maganar ne ya sa ya kasa É—ago kanshi yaga ko waye ke masa wannan cin mutuncin agaban jamaa.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[8/1
No comments